babu yarda za'ayi in ki daukar wayarta da gangan." Ya sa ki ranshi yana dariya, ya ce "Na yarda yanzu ina labari.?" Ta ce "Labari yana kannunka, tunda kaine idona." Yace "Ban yarda ba, kece idanuwan dai ni yanzu tamkar makaho nake kuma bani da dan jagora, me yiwuwa sai ranar da na dawo gare ki." Tа сe "To Allah ya nuna mana ranar zani fi kowa farin ciki, saboda nasan wani ci gaban mu ne dama kasar mu baki daya." Zuciyarshi ta yi sanyi, suka yi ira mai dadi ha baya son su rabu. Naja'atu nauyinshi ta rinka ji, da jina sauraren irin kalaman da yake fadi mota, tabbas kauna ce 'yar usuli, kuma a cikin zuciyarshi take tana sha'awar
15
halayyar Khalid zata so ta yi rayuwa dashi ta har abada
sai dai kashi Kaunarshi Ďaddy tarinja. Ya zuciyarta ta
yarda ita kanta bata son yarda zata sarrafa zuciyar ba har
ta sama ma wani matsugunni a cikinta don haka lokuta
da dama idan ta tuno Khalid din takan ji tausayinshi
kamar ta yi kuka so da banne, ta kanyi mashi addu'a da
fatan alkairi akan dukkan al'amurranshi. Har bayan
sunyi sallama tana jin kalamanshi sunayi mata karakaina a kwakwałwa, da tunanin ta kwanta ta dan samu
barci sai yamma ta tashi tayi wanka, ta sanya riga da
sike na wani leshi blue dinkin dan kib-kib, daidai jikinta
tana son yanayin rigar ta dace da tsarin hattar jikinta ta
zauna bakin madubi ta dauki tsawon lokaci tana gyaran
fuskarta ta fitofresh, ta yi kyau jikinta yana kamshin
body spray masu kamshin, kayan marmari, Daddy ne ya
zaba mata ya ce favorite dinshi kenan, yau da gobe har
sun kama mata jiki. Ta daidaita daurin kallabinta,
fuskarta ta fito ta tsaya tana kallon kanta ta madubi ta yi
kyau daidai gwargwado, sai ta yi murmushi zuciyarta na
kan Daddy ya ci ace zuwa lokacin ya dawo gida.
Ta saba duk asabar yana fita ya bada motarshi
wajan wanki ayi mashi 'yan gyare-gyaren da take
bukata, da wannan damar ne yake yi amfani yaje wajen
Farida, babu shakke yana can tare da ita.
Sai ta rufe idanuwanta ta jin watar kishin tana
ruruwa zuciyarta, daidai lokacin taji shigowa motarshi
cikin harabar gidan, sai ta saukar da ajiyar zuciya, wani
sanyi yana ratsa ta Daddy da banne a ranta, Ta daga
16
labule tana kallonshi ya bude sit din baya ya fiddo wata
katuwar jikkar Ibrahim ya dauko suka shigo tarc.
Da ta fito Ibrahim ya shi da jikkar cikin dakin
Mummy ta zuba ma fuskar Daddyn 10o, har yanzu ba ya
da walwala, bai ce mata komi ba, ya rabata ya nufi
fakinshi, sai tayi murmushi ta zauna falo tana jiranshi
ya fito cin abinci, amma shiru bai fito ba, tasan duk
fushin ne a kalla minti talatin da shigarshi, ta dauki
waya ta kirashi shiru kamar ba za ya dauka ba, sai ta ji
babu dadi, bata san abin da Daddy ya ke nufi ba, dan
abu karami sai ya dauki fushi da ita. Kafin ta tsinke ya
dauki wayar ta ce "Ka fito ka ci abinci mana." Ya ce "ki
barshi kawai na koshi bai jira ba ya katse layin."
Ya aka yi, sai kuma ta sake kiranshi ta ce "Daddy
ma kaci da zaka ce ke koshi.?" Ya ce "Abincin me zaki
matsa mani inci tunda baki son kwanciyar hankalina." ta
ce "Don Allah Daddy kayi hakuri ka aje maganar nan
gefe daya, kai fa musulmi ne riko baya da kyau, daga ni
har kai babu wanda yasan abin da zaya faru sai Allah, to
mu duka mu ci gaba da neman zabinshi, ba wai son
zuciyarmu ba, Daddy idan ban damu da kai ba, ba zani
rinka shiga harkarka ba irin haka." Ya saukar da ajiyar
zuciya ya ce "Shi kenan kawo mani abincin nan." Та се
"Gaskiya Daddy kayi hakuri bani son in rinka shiga
dakinka, ba kima ba ne, idan muna irin haka sai mu
shiga zargi." Ya ce "Babu wani zargi ai ba zama zaki yi
ba, ba ni jin dadi ne, zazzabi ya ke neman matsa mani,
Mummy kike gudu, to ta fi kowa sanin halin na tasan
17
abin da zani yi tasan wanda zani yi ba, ki shigo ni na
baki izini.
Ta rufc wayar ta shirya mashi abincin ta dauka ta
kai mashi. Ta same shi kwance ya sanya suwaita
tabkekiya, kuma ga AC ya kunna, da sauri ta aje farantin
bisa tebur ta rufe AC din tana yi mashi fada. "Haba
Daddy, ba ka da lafiya shi ne zaka kunna AC kuma." Ya
dube ta idanuwanshi sun kada sunyi jajir, ya cc "Ina son
in samu saukin zafin jikin ne." Ta cc "Amma ba da haka
ba." Ta yi mashi sannu, ta matsa mashi sai da ya danci
abincin, sannan yasha magani ya koma ya kwanta
jikinshi yana rawar dari, ga alama yana jin jiki, yau 'yan
maza balafiya. Duk sai ta ji tausayinshi ta damu kwarai,
ta fito ta shiga daki ta sanar da Mummy Daddy ba
lafiya.
Tare su ka shiga dakin tana tambayarshi abin da ke
damunshi ya sanar da ita zazzabi ne kawai, ya ce "To
kaje asibiti.?" Ya daga mata kai, jikinshi na rawa,
Mummyn ta sanya Naja'atu ta warware bargo ta lullube
shi su duka sun shiga damuwa. Har zuwa dare babu
wani sauki Naja'atu ta shiga damuwa sosai ta kasa ta
tsare ta kasa samun natsuwa, har dare jikin da zazzabi
Mummy ta matsa mashi sai ya sake komawa asibiti, shi
kuma ya ki yarda ya ce tunda ya ce babu wani dalilin da
zaya sanya ya sake koma masu tunda bai gama shan
maganin da aka bashi ba.
Kafin dare ya galabaita sosai, saboda amai da ya
rinka yi akai-akai Mummy ta shiga damuwa sosai, don
haka ta yi waya gidan kanin mahaifinsu aka turo Likitan
18
dake dubansu yazo ya duba shi ya yi mashi allurai ya
canza mashi wani maganin. To babu laifi ya dan samu
sauki har ya tashi ya yi sallolin da ake binshi, jikinshi
babu karfi, bakinshi babu dadi ya tashi ya zauna bakin
gado. Naja'atu ta shigo dauke da faranti kayan marmari
ne da abinci akai, ta aje gefc daya tana kallonshi, shima
kallonta yake yi, yana kara jinjina mata tana bakin
kokarinta akanshi, sai ya ji ya kara sonta ta taimaka
mashi sosai, ya danyi murmushi.ya ce "sannu Naja'atu."
Ta ce "kai zani yi ma sannu. ka wahala sosai ba ka gani
ba ka dan fada." Ya yi murmushi ya ce "Wallahi kuwa."
Ta ce "Allah ya kara sauki, ga abinci nan Mumny ta ce
ka daure kaci."
Ya zuba mata ido ya ce "Ba ni jin dadin bakina ba
zani iya cin wani abu ba." Ta ce "To ga fruits nan idan
kasha zaka ji dadin bakin, zuwa anjima sai ka ci
abincin." Ta dauki farantin ta mika mashi ya dauki
kamu yanka dayan yana sha, sai yaji dadi ya ci gaba da
sha. Naja'atu ta tashi zata fita ya dago yana kallonta, ya
ce "ina zaki.?" Ta ce "Falo zani koma." Ya ce "Don
Allah ki zauna bani jin dadin zama ni kadai kuma
kinsan ba zani yi barci ba yanzu." Ta kasa yi mashi
musu duk da cewa bata son zama dakinshi, amma yau
lalura ce ba zata iya tafiya ta barshi ba. Don ta koma ta
zauna a hankali suna hira.
Wayarshi dake aje gefen gadonshi ta yi kira,. mika hannu ta dauka Farida ce ke kiran saj ta mika
mashi ta tashi zata fita ya zuba mata ido, yana girgiza sai
ta koma ta zauna ya bude wayar ya amsa mata, tana yi
19
Korafi kan rashin zuwanshi, yau ya bata hakuri ya
mat da ita lalurar da ya samu ta rashin lafiya, a hankali
ya ci gaba da kallon Naja'atu yana yima Farida bayanin
rashun lafiyar yayin da yake nazarin Naja'atun ta canza
sosai yana ganin tsabar kishinta duk sai ta bashi tausayi
yarda ta damu dashi take kula dashi yayin Imanin Farida
ba za ta iya yi mashi irin haka ba, dole ne ta ji kishinshi,
don haka ne ma yanzu baya yin waya da Farida a gida,
sai da ofis ko kuma idan ya fita, idan ya kama a gidan
sai dai ya shiga dakinshi ya yi maganar shi, ya tsini abin
da zaya bata ma Naja'atu rai yarda take tattalinshi take
kokarin kyautata mashi bai kamata shi ya rinka yin abin
da ya sán bata so ba.
Da ya gama magana ya rufe wayar ya aje, sai ya
zuba mata ido yana nazarinta a hankali ta sauked kanta,
bata ce komi ba, ya jinjina kai ya ce 'Don Allah Naja'atu
abin da nake so da ke shi ne, ki rinka hakuri da wasu
abubuwa, na sani da ciwo, to amma duk abin da kika
gani nufin Allah ne, ba wai yina ba ne, Allah ya hada ku
dani sannan ya kaddara kaunarku gare ni, kowacce da
matsayinta a cikin zuciyata, don haka bani son in ga
kina nuna 6acin ranki don kinga ina magana da Farida ki
sanya ma zuciyarki hakuri, wani abu ne da ya zama dole
tunda wata rana ma tare zaku zauna." Ya sassauta muryà
ya ce "kin fahimta.?" Ta jinjina mashi kai, suka ci gaba
da hira.
Washe gari da ya tashi babu laifi jikin ya yi sauki,
sai dai rashin karfin jiki, don haka bai fito ba ya ci gaba
da kwanciya cikin dakin, yayin da Naja'atu ta yi tsayin
20
daka akanshi. kai kwannan kai wancan ita dai so take vi
taga ya warwarc. Ta gyara mashi dakin fes, yana
kamshin Airfreshner. Sannan ta dawo dakinta, tayi
wanka ta yi kwalliya ta daidai gwargwado, karfe goma
ta fita ta shirya mashi kalaci mai rai da lafiya, ta dauka
ta kai mashi yana zaune bakin gado, yayi wanka ya yi
fresh alamar lafiya ta fara samuwa, ya dube ta ya yi
murmushi itama ta maida mashi martani ta ida shiga ta
aje bisa tabur ya. zuba mata ido yana sha'awar
halayyarta, kwalliyarta ta yi mashi kyau ya ce "Naja'atu
ba ki gajiya da hidima dani ko.?" Ta yi murmushi kawai.
ya ce "Na gode, Allah ya bani ikon rike ki da kyau bisa
amana da gaskiya, Allah ya kara mana kaunar
junanmu."
Ta saukar da ajiyar zuciya, duk sai yasa ta ji
nauyinshi, ta sarda kai kawai bata ce komi ba, yayin da
shi kuma ya bude filet din, filentan ce da kwai aka soya.
sai kamshi suka yi da miyar kifi 'yar kadan, ya yi
sha'awarsu, don haka ya saki jiki yana ci, suna hira. Aka
kwankwasa kofa aka shigo, Mummy ce gaba sai Farida
da wata kawarta suka shigo, idanuwan Farida na kan Naja'atu, sai taji kishi matsananci ya dauke kanta tana kallon Daddy, ranta ya dan taba sai dai lura da yayin da Daddyn ya ke ya dan fada sai hankalinta ya koma kanshi. Tana yi mashi sannu.
Naja'atu ta mike ta basu waje, kawar Farida kadai
ta yi mata magana su ka gaisa, amma ko kallon arziki Farida bata yi mata ba, bata yi magana ba, ta fita ta basu waje to itama Mummy bata zauna ta fito. Farida taja
21
wani stool ta zauna gaban Daddyn, tana tambayarshi
jiki, ya dan lumshe ido, sannan a hankali ya bude su
yana kallonta ya ce "Da sauki Farida, yau kam na tashi
da sauki, amma jiya naji jiki, da da karar kwana sai dai
kiji bakin labarin ance maki babu ni." Ta dafe kirji ta ce
"Da na shiga uku, idan ka tafi ka barni yaya zan yi.?"
Ya yi murmushi ya ce "Sai ki samu wani ko.?" Та
zuba mashi ido da wata irin siga mai daga hankali, ta ce
"Ai ba ka san wani abu ba, kai kaďai zuciyata take so,
bani tsammanin idan wani da namiji zaya yi tasiri akan
zuciyata, idan har ka riga ni mutuwa, kila sai dai in
mutu ban yi aure ba." Daddy ya rinka yi mata dariya ta
ce "Balle ma insha Allahu ba za ka mutu ba, sai ka tsufa,
shima na fi son in riga ka mutuwa, saboda zuciyata ba
zata iya jure rashinka ba." Daddy ya jinjina mata ya yi
Imanin kaunarshi a zuciyarta cikin jiki take, su duka su
na son juna, haka nan Allah ne ya dasa mashi kaunar
Farida a ranshi, su duka ya na sonsu, ko wace tana da
nata tasirin ga rayuwarshi.
Su ka ci gaba da hira a hankali Farida ta rinka
nazarin dakin, tsarinshi ya yi mata kya, ko ina fes-fes sai
kace ba dakin namiji ba, koda ya ke tasan Daddy mutum
ne mai tsabta, don haka ba abin mamaki ba ne don ta ga
dakinshi da tsabta, cikin kalle-kallenta ne ta hango wani
hoto jikin dan karamin frem bisa wata loka, ta zuba ma
hoton ido daga nesa, bata gane wadda ke jikin hoton ba,
a zatenta nata ne, don haka ta mike ta isa in da hoton
yake, ta mika hannu ta daukoshi, hoton Naja'atu ne cikin
kananan kaya a millium pack ta yishi wata rana da su ka
22
fita tare da Zainab da ibrahim da shi Daddyn, sun yi
hottina da yawa, wasu tarc wasu daban-daban amma duk
ciki Daddy ya fi son wannan saboda tayi kyau sai kace
Balarabiya, don haka tunda su ka dawo ya fiddashi ya
aje shi cikin firem din ya na kallon shi koda yaushc.
Farida ta zuba ma hoton ido, zuciyarta na tafasa
kamar zata fashe saboda azabar kishi, cikin wani irin
tashin hankali ta juyo tana kalion Daddy shima kallonta
yakc yi, yaga abin da take yi, ga mamakinta sai taga ko a
jikinshi bai nuna damüwa ko jin nauyin abun ba, zuciyar
ta ta kara tunzura muryarta na rawa ta jefa firem din kan gado kusa da shi, ta ce "Daddy wannan menenc? Me hakan takc nufi.?" Ya zuba mata ido, ya ce "Ba ki gani
ba, Naja'tu cc fa.?" Ta ce "Na gani ina son in ji dalilin
da ya sanya ka aje hotonta cikin dakin ka.?"
Daddy ya sanya harshe yana lasar lebenshi da ya bushc, bai yi tsammanin tashin hankalin da ya lura ta shiga ba, to sai dai abin da ya ke tunani yasan dole ne dama tasan yana tarc da Naja'atu, ko da kuwa bayan
aurensu ne, tunda itama Naja'atun aurcnta zaya yi, to sai dai a tsarinshi ba wannan ne lokacin da ya yi niyyar fadi
mata ba. To sai dai bakin alkalami ya riga ya bushc, komi zaya fadi mata ba zaya yl tasiri ba, haka nan matsayin Naja'atu a zuciyarshi ya wuce ya боус та wani gaskiya, ba zaya iya karyata soyayyarta ba. Ya zuba wa Faridar ido, duk ta rikicc kamar zata saka mashi kuka, ya cc "ki kwantar da hankalinki zani yi maki bayani." Ta dakatar dashi, ta ce "Bayanin me zaka yi mani Daddy? Ga shi na gani da idona, dama abin da
emui kenan? Yanzw sakayyar da zaka yi mani
nDama Žuciyata ta karanta mani akwai abin da
y ke faruwa ina mamakin canje-canjen da ka bullo dasu
in wannan lokacin baka yi máni waya sai kaga dama,
ka nan sai ka jera kwanaki baka leka in da nake ba,
she dama wata ka samu, shi ne ka tsaya kana yaudara ta
kana bata mani lokaci, to Allah ya fika, kuma na gode
de abin da ka yi mani." Da sauri ta juya zata tafi, Daddy
rinka kiranta, ko juyowa bata yi ba taja kawarta su ka
Mummy da Naja'atu na zaune cikin falo, sai taji ta
ane su baki daya, tafi ganin laifin Mummy, ita ce
hbar manafukar, dama don ta hada Daddy da
aja'atun ne ya sanya ta jajibo ta, Mummy ta dago kai
yana kallonsu, ta ce "Farida har kun fito? Ta yi kokarin
danne damuwarta ta ce "Eh Mummy tafiya zamu yi." Ta
ce "To mun gode kwarai, ku gaida gida, ki gaishe mani
da Mamanki." Su ka fice ko kallon Naja'atun basu yi ba,
ama haka bata kula su ba tana kallonta har su ka fice ba
ce masu'komi ba:
Ta tsaida zuciyarta tana tunanin dalilin wannan
na da Farida take nuna mata, alhalin bata ma san
wa Daddy yana nemanta ba, ko idan ta sani yaya zata
vi? Tun farko jininsu bai hadu ba, sai ta rinka ganin
laifin shi kanshi Daddyn, ita bata ga wani abin so ba ga
arida, mace sai kace kalmar daya, dan hasken ma na
nan kanti ne, kila yatsunar da take yi ce yake so, ita kau
dai sai ta yi irin wannan karuwancin za a so ta, to sai
24
dai in kar a so ta, wata wayewar in ta yi yawa abun har babu kyau.
Ba ta sake komawa dakin Daddy ba, ta yi zamanta
falo tana kallon kishi ne kome duk sai ta ji shima ya bata
haushi ta rinka jin zafin ganinshi da Farida, waya san abin da ya fadi mata? Maza daban ne, tana mamakin
yarda suke kokarin hada kaunar mata daban-daban a
ransu, kuma wai su duka sonsu suke yi dole ne
munafunci ya shigo, saboda duk yarda za'ayi sai ya yi ya
fi son wata ko cikinsu ita da Farida wa yafi so?
Idanuwanta suka yi jajir zuciyarta kamar zata fasha idanuwanta sunan neman tara hawaye ta tashi ta shige
daki, sai ta kwanta kan gado, tana jin har wani sanyi sanyi yana kada ta, duk ta takura kanta kan gado har aka yi sallar azuhar bata sake fita ba.
A can shi kuma Daddy ya yi shiru yana nazarin matakin da Farida ta dauka, bai ji dadin abin da ta yi ba,
to sai dai yasan an Gata mata, matsalarshi da ita daya сe,.
ya dace ta tsaya ta saurari abin da zaya fadi matga, koda kuwa ba zata amince dashi ba. Ya koma ya kwanta, yana tunanin yarda zaya shawo kanya yasan tana can cikin damuwa, yau akwai kuka kenan ya yi murmushi bai damu ba tunda yasan zaya sauko ne sai ya lumshe ido, yana tuno shagwa6ar Farida, amma koda wasa bai yi tunanin wai ya canza maganarshi kan Naja'atu ba tana nan daram, komi zasu yi zasu yi su sauko su daidaita, sai da ya tabbatar ta isa gida sannan ya kira ta waya, wayar ta rinka kara har ta tsinke bata dauka ba, bai damu ba ya
25
sake kira, nan ma shiru ya rinka kina tana katsewa ba ta
Jauka sai ya rabu da ita.
Ya kwanta yana tunanin rigimar da ya dauko ma
kanshi, amma da ya ke yasan kan Faridar sosai, bai
đamu ba đa zaran yaje gare zaya shawo kan yan
kayanshi. Da wannan tunanin ya samu barci, har karfe
biyu ya tashf va yi sallah, sannan ya zauna, to kuma sai
ya rinka jin yuhwa gashi shiru bal sake jin Naja'atu ba,
yasan itama damuwar ce, mata akwai kishi kowace da
Kalan nata, Shi Rahar yanzu eikin daki take Kwance, ta
dauki Wayal wr laRs fubawa kamar ta share shi, amna ta
kasa ta ansa masti, muryarta ta yi kasa ya ce "Naja'atu
kema
pat
bå
za
EšGo
kitusayd manf ba, so kike yi ki bata mani
SK9
ral. Ta се e nayi maka?Ya ce "Babú komi,
kuzo yanzu MESSA ASUS ina jirankia 1 rufe wayar ta aje gefe daya
sái ta taso ta fithia shiga ta same shi zaune bakin gado, yhhe
60 sb gics Vazub 88b dAkitaccen kallonshi, sal taji
55 sysb sti sh idare zuciyarta tay tai sani tafihea Kokarin boye damuwarlá.
oK Bgaba da Kalioita ya te "Are you okey.? ta
daga mashi K To e yasa kika tafi ki ka barni ni
dayha.? 8Tlangabe kai tana kallonshi, ta ce "Daddy
Kwanciva Hayi la.Vsankar da ajiyar zuciya, ya ee "To
mebani in çi yunwa nake i.Ta ce "Me kaké so.?"
b8 "Duk abin da kika bani ina so. Ta yi murmushi ta
ce "Inaz Tito tana tmanin Daddy, tausayinshi
ise stishish we a daga hi ta san akwai damúwa táre dashi fa
alama basu rabu da dadi ba da Faridár, koda yake ta lura
64 60 UA iki Baci rar ta tati, 16 don mi itama zäta
rinka bata mashi? Dole ne ta bi a hankali tunda yana
26
kokarin akanta, idan har yana tsoron Farida ba zaya sake
kula ta ba, tayi Imanin rigimar ba ta rasa nasaba da
zuwan da ta yi ta same shi tare da ita, sai ta jinjina kai.
zuciyarshi ta yi sanyi.
Cikin kicin ta shirya mashi salad fan kadan yasha
hadi da kayan kara jini ta zuba mashi shinkafa kadan da
peppe meat, ta hada mashi lemun abarba da kwakwa
bata sanya sukari ba sosai, saboda yanayin bakinshi, ta
dauko ta kawo mashi ya ji dadi sosai, ya saida ya kusa
cinyewa. Don haka da dare tun wuri, ta fidda kaza daga
firij ta yi mashi gashi na musamman mai romo-romo
yasha attaragu da albasa da ya ji mai kayan kamshi tasha
curry da reyco, gidan ya cika da kamshi Mummy ta yi
mata korafin ta yi son kai, dole ta kara, ta gasa har da
su. ya ji dadin gashin ya ci naman har baya son ya bari
sauran da ya rage ya ce ta aje mashi sai da safe zaya
kara çi.
Cikin falo suka yi hira har darc ya mika ya hana
Naja'atu tafiya ta kwanta wai ya kasa barci, saboda
barcin da ya yi da rana, sai da Mummy ta sanya baki
sannan ya sallame ta taje ta kwanta, to itama sai ta kasa
barcin tana tunanin Daddy, shu'umin mutum kenan, ya
daure ta sosai da igiyar kaunarshi, har mamakin kanta
take yi ba ta taba tsamınanin cewa zata samu kanta cikin
irin wannaı yanayin ba, a hankali ta fera tuna Khalid da
irin muhimmancin da ya ba kaunarta, ko yaya zav iї
idan yasan cewa ga halin da take ciki? Sai ta iumshe ido
tana kissima wani abu dake kara shaukin kaunarshi
cikin zuciyarta, shi ne wani abu mai tsananin tasiri da
27
take hangowa cikin kwayar idonshi tabbas wannan true
rove ne, Daddy yana sonta ta yarda da kaunarshi gare ta to sai dai koda yaushe dan adam tara ya ke bai cika goma ba, sai ta rumtse ido tana addu'ar Allah ya mallaka mata Daddy." Da wannan addu'ar tayi barci.
Cikin kwanaki biyu ya warke garas, kamar bai yi
ciwo ba, ya jinjina ma Naja'atu sosai, ya sani har da taimakonta wajen kulawa dashi da bashi abinci mai kyau, don haka ranar da ya fara fita, ya shiga super market ya yi ma ta sayayya, tarkace iri-iri, ya kawo mata
ya ce gift ne. Murmushi kawai ta yi ita dai tasan komi
zata yi mashi ba ta fadi ba yanzu ma kenan idan su ka yi
aure sai ya yi mamakinta, bata hada kaunarshi da komi
ba a ranta, ita kanta bata san dalilin da yasa ta ke yi
mashi irin wannan mugun son ba, ita dai tasan tana sonshi, so kuma mai tsanani. To takura shi ma Daddyn
ya na kara daukar lamarin da muhimmanci.
Kwana da kwanaki yana neman layin Farida,
amma fir ta ki yarda ta saurare shi, idan ya kira ba ta
dauka ya yi mata text babu amsa, abun ya kan dan taba
zuciyarshi, baya son yaje wajenta cikin. halin da take
ciki, ya fi son ta tsaya ko magana daya su fara yi ta
waya, idan ya so in ya jai su ida warware
matsalolinsu, to-ta ki ba shi dama,yanzu har ya fara
ganin laifinta, a ganinshi zafin kishinta ya yi yawa, bai
dace ta dauki wannan matakin ba tashi daya ba tare da
ta tsaya ta saurari abin da zaya ce ba, to ita kam Farida
ta shiga damuwa, duk sarda ta tuno hoton Naja'atu dakin
Daddy, sai taji kamar-zuciyarta zata fashe, musamman
28
ganin da tayi mata cikin dakinshi, babu irin zargin da ba
ta yi masu ba, gani take yi babu abin da basu yi. kuka
take yi sosai tana zarginshi da cin amanarta, don haka ta
ke kokarin ganin ta fiddo sonshi kwata-kwata daga
zuciyarta, hakan ya fiye mata sauki, to sai dai abun
takaici duk irin yarda take tunanin abun ya wuce
tunaninta, kullum rana kaunarshi kara zurfi ta ke yi
cikin zuciyarta, don haka kishinshi ya ke karuwa, duk ta
sukurkurce.
Mamarta ta damu sosai, ta na sane da abin da ya ke
faruwa, to sai dai ta fadi ma Farida cewa tayi hakuri
wannan ba matsala ba ce, komi żaya warware ta се
kuma daga ganin hotonta a dakinshi sai kice ala dole
sonta yake yi? Tun yaushe ta ke gidan? Ai in har yana
sontga ba zaya yarda ayi maganar aurenshi da ke ba, ki bi komi a hankali matsalarki ba ki da hakuri." Farida
kuka ta rinka yi mata tana rantsuwa kan cewa Daddy
son Naja'atu ya ke yi. Mama ta yi dariya ta ce "To idan
ma sonta ya ke yi, sai me? Shi fa mijin mace hudu ne, kiyi hakuri in binciki lamarin a hankali, babu abin da
zaya faskara, ni dai fatana ki shiga gidanshi, idan yazo hannu cikin ruwan sanyi za ki kama shi ta yarda ba zaya sake tunanin wata diya mace ba, balle har ya yi tunanin aurenta.
Zuciyar Farida ta danyi sanyi, sai dai har yanzu ba
ta huce da Daddy ba, sam ta ki daukar wayarshi. To bai damu ba, yasan dai babu fashi, duk idan komi ya karato ta tsaya ta saurare shi.
29
A bangaren Mummy shirinta ta ke yi, so ta ke yi
Kaishen satin akai lefe ya zamto ta ture shi, sai sauran
hidimomi. Ta hada lefenta akwatuna seti daya masu
guda uku da kit dinsu, sai kuma na jikkuna suma guda
hudu masu kyau 'yan yayi, lallai kam abun nayi ne
Naja'atu tunda taga kayan sai jikinta ya yi sanyi,
mamakin uwar dukiyar da aka nautsa take yi, an kashe
kudi kamar banza, lallai abun nayi ne, sai lokacin ta
gane wautar da ta ke yi, Daddy ba ajinta ba ne ya fi
Karfinta, saboda duk in da za'a kai lefe irin wannan to
tabbas suma zasu so a maido masu abun arziki wanda
tayi Imanin cewa iyayenta basu da halin yi mata karya
irin wannan an ce kwarya ta bi kwarya, Khalid shi ne
ajinta ko ba komi,