Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels SIRRIN ZUCI NA SA ADATU SAMINU KANKIA (Mrs. Sani Abbas Hakkin Mallaka (M) Sa'adatu Saminu Kankia Copy Right (c) Sa'adatu Saminu Kankia An Rubuta A Shekara Ta: 2008 ABUN ALFAHARI NA Mahaifiyarmu H. Sa'adiya Samiru Kankia, Uwa ta gari abin alfaharin mu, muna godiya da irin kyakkyawar tarbiyar da kıka gina mu da ita, da kuma wadda kike bamu a halin yanzu. Hakika kin cancanci yabo, Allah ya ja da rai, ya yi maki sakayya da Aljanna Firdausi, amin. Hakika addu'arki gare mu mai amfani ce muna ganin albarka a dukkan al'amurranmu. ALLAH YA RAYA MIN KU: 'Yayana Umar, Ahmed da Fahad, Sani Abbas, Allah ya albarkace ku, ya sanya masu jinkan mu ne, amin. 2 SIRRIN ZUCI..3 ati biyu bayan tafiyar Dr. Khalid, Naja'atu har Sta saba da kewar shi, sai dai sukan yi waya, ya na sanar da ita halin da ya ke ciki, tare da kara jaddada ma ta matsayin kaunarta a cikin zuciyarshi, yakan roke ia cewa ta rinka yi mashi addu'a, Allah yasa ya yi karatunshi lafiya ya dawo gare ta." Ita ta rike shi a ranta, ta kanji kewarshi, haka nan idan ta natsu ta na tuno irin kalaman da ya ke fada ma ta masu ma'ana, da tasiri a zuciyarta, wadanda tayi Imanin cewa gaskiya ne babu yaudara a ciki. Wani lokacin kuma tausayinshi ta kanji ganin yarda ya dauki kaunar da muhimmanci ya sanyata a ranshi alhalin ita kullum kokari take yi taga ta sama mashi mazauri na din-din-din a cikin zuciyarta, amma kullum abun kara rikice ma ta yake yi, musamman cikin wanna lokacin da Daddy ya kara rikicewa a kanta. Zainab ta koma makaranta, sai ita daya kullum rana tana tare da Daddy, ya na bullo ma ta da salo iri-iri na takun soyayyarshi, amma har tsoro ya ke bata, sai dai ta lura shi ko a jikinshi ya rufe idanuwanshi, ba ya shakkar kowa, a gaban Mummy nuna kaumarshi yake yi garc ta tun tana jin nauyin Mummy har ta kai itama ta daskarc. Duk irin yarda taso ta danne zúciyarta game da shi, abun ya faskara, kaunar da ya ke nuna ma ta kaunace da ta jima ta na mafarkin samu daga gare shi sai ya zamto, ta kasa sarrafa zuciyar. Cikin ruwan sanvi ya same ta yarda ya ke so, idan su na hira sai su dauki 3 Naiokaci ba tare da sun sani ba, duk wani jin dadin ray awarta ta ta'allaka shi ga Daddy. Abun da ban tsoro ita kanta ba zata iya cewa ga abin da ya ke faruwa ba, illa dai tasan tana son Daddy, son da ita kanta ba za ta iya fassara shi ba, akan kaunar Daddy ya sanya ta raina duk wani da namiji, idan yana kallonta ya kan tsuma ta da wata irin mahaukaciyar soyayya, hakan ya sanya ba ta iya ketare maganarshi, matsawar ya ce ya na son kaza, ko kuma ba ya son abu kaza, to kuma duk runtsi tabarshi, haka nan idan ya ce yana so, zata jure ta yi ma shi, idan har suka yi fada da Daddy ta kan shiga damuwa, ba za ta samu natsuwa ba, har sai sun daidaita. Ta na yin taka tsan-tsan akan dukkan lamarinshi, abu guda ne ke saurin tada ma ta hankali game da Daddy, shi ne idan ta tuno cewa wata zaya aura ba da dadewa ba, sai taji ranta ya 6aci, tana jin matsanancin kishi, har sai ta gwammace ta rabu da shi kawai ya fiye ma ta kwanciyar hankali, tunda tasan dai duk irin kaunar da zaya nuna mata ba ta kai wadda zaya yi ma Farida ba, matsawar ya fara aurenta, tausayin kanta take ji sosai, idan ta tuno har kuka take yi takan shiga damuwa. Amma kuma idan ya zauna yana fadi mata matsayin kaunarta a zuciyarshi, sai ta amince da shi, idan ta kalli kwayar idonshi ta kan hango wani abu a ciki, da ita kadai tasan ma'anar hakan, da bakinshi ma ya fadi mata yana sonta, son da shi kanshi ba za ya iya cewa ga lokacin da ya dasu cikin zuciyarshi ba, sai dai aka wayi gari ya samu kanshi dumu-dumu cikin kogin kaunarta, kaunar da ke barazanar raba shi da abin da ya dade ya na so." Zuciyarta ta shiga rikici sosai, saboda shima Khalid idan ya kirata abin da ya ke fadi mata kenan koda yaushe, to amma da ya ke shi Daddy tare take dashi koda yaushe, ya rinjayi zuciyarta sosai. Mummy na lura dasu, abun ya na damunta, ta fi ganin laifin Naja'atun, ba ta ga dalilin da zaya sanya ta biye mashi ba, yana 6ata mata lokaci, to sai dai ba ta son ta cika takura mata, don haka yau da safiyar ranar Asabar, Naja'atu ta yi shiri ita da Ibrahim su ka fita zata je saloon ayi mata gyaran kai. Har su ka fita Daddy bai fito ba, don haka da ya fito cikin falo, ya rinka zuba ido yaga in da za ta fito, ga shi ya kira layinta a rufe ya ke, sai ya zauna falo ya na kalaci shi daya duk kuma sai ya ji babu dadi, Naja'atu ta saba mashi, duk sarda zaya ci abinci ko ba zata ci ba, zata zauna kusa da shi har ya gama hakan yana yi mashi dadi. Cikin yanayin Mummy ta fito daga cikin dakinta ta zauna falon sai ya dauko filet dinshi ya dawo cikin falon, ya na saurarenta tana waya da wata Hajiya Ladi da ke zuwa Dubai, ta ba ta sautun sawo mata wasu kaya cikin na lefe. Da ta gama ta rufe wayar ta dube shi tana murmushi, ta ce "Ni da Hajiya Ladi ce ta ce kaya sun iso, don haka in anjima idan ka fita ka biya ta gidan ka taho dasu, so nake yi a hada komi cikin sati mai zuwa akai, yau duka saura sati uku ya rage fa." Ta dan saurara taji ko zaya ce wani abu, shiru bai ce komi ba sai ya dai ya jinjina kai ya ci gaba da kurôar shayinshi. 5 Hajiya ta yi murmushi ta ce "Ko da yake na lura ni daya ke fa shirme na, kai nema kake yi ka saki maganar." Ya zuba ma ta ido, bai fahimci maganarta ba sosai, ta yi murmushi ta ce "Ban san shirin da kake yi ba, naga jana neman canza sheka, kafi daukar maganar Naja'atu da muhimmanci akan ta Farida." Ya yi murmushi ya ec "Mummy ba haka ba ne, kii sani ina son Farida, kuma aurenta zani yi." Ta ce "Naja'atun fa.?" Ya ce "Itama haka." Hajiya ta yi dariya ta ce "Daddy rigimarka ta yi yawa, ina kai ina tara maia har biyu? Gaskiya bani jin dadin abin da kake yi, ka rabu da Naja'atu ka ci gaba da harkarka, gaba ki daya ua yarda ka dauki soyayyar da zafi yana damuna, yair zako ame ta ko gobe? Wanhan sakarci ne, kuina abin da ke cikin zuciyata ne na fadi ma ka, bani son yaudara, yarinyar nan amana takc a hannuna, bani son wani abu ya faru da ita, yanzu ji ba yarda ka jata jikinka, ka dauki hankalinta a karshe ba aurenta zaka yi ba, to meyc amfanin abin da kake yi.?" Daddy ya rinka girgiza kanshi, ya ce "Muuiat ina son ki dasa ma zuciyarki cewa har abada ba zani taba yin wani abu don in 6ata maki rai ba, ko don in son zuciyata haka nan har abada babu yaudara tsakaniua da Naja'atu, Mummy ina sonta, sonta nake yi son dani kaina ban san adadinshi ba, Mummy ki yarda da ni idan har zani iya cin amanar Naja'aiu to zani iya cin ta Zainab da muka fito ciki daya, sonta nake yi úa zuciya daya, kaunar ta a cikin jinina take, kuna insha Allahu zaui aure ta ba da dadewa ba." Mummy ta jjina kai ta san halin Daddy duk abin da ya yi rantsuwa akanshi tayi Imanin cewa haka ne, ta yarda yana son Naja'atu da kanta ta lura da haka, sai dai abin dubawa, abin da ya ke shirin yi an ya mai yuwuwa ne? Tara mata ba sauki ba nc, shi kanshi ya kwari kanshi, sannan itama Naja'atun yaya zata yi da maganar Khalid idan ya dawo alhalin ita kanta ta daukar mashi alkawarin cewa zata tsaya mashi taga cewa Naja'atun ta jira shi har sai ya dawo, to wane irin bayani zata yi mashi idan ya dawo?" Ta sake jinjina maganar a ranta, ta ce "Daddy ban ki ba, kuma kada kayi tsammanin ko bani sonka da Naja'atu ne, zan fi kowa yin farin ciki idan har haka za ta faru na sani Naja'atu alkairi ce gare ka, kuma idan zaka tuna da kaina na yi maka magana akan ka neme ta, kaga kau idan bani sonta hakan ma ba za ta faru ba, to sai dai abin dubawa a nan shi ne, Daddy rayuwa canzawa take yi, yanzu ka yi mata alkawarin cewa za ka aure ta, ta amince da haka, sai azo daga baya idan ka yi aure kaji ba ka da ra'ayin kara auren yaya zaka yi da ita? Sannan ni kaina bani goyan bayan a shekarunka ace ka aje mata biyu a gidanka, yanzu ba zaka fahimci ain da nakc nufi ba, sai nan gaba., Don haka ka samu lokaci ka nutsu kayi nazari, idan ba kai ba babu mai kashe wannan wutar don Allah ka janye ta." Shiru ya yi ya na juya kofin da ke hmunshi, zuciyarshi ta natsu da tunanin abin da ya dace a yi, sai dai duk irin yarda ya so ya ce ya rabu da Naja'atu abin ba mai yiwuwa ba ne, ba zaya iya ba, koda wasa zaya 7 iya yin hakuri da komi amma ban da ita, ya sani sarai Mummy ba ta son tarayyarsu, kuma tun lokacin yana Kokarin yaga bai yi abin da zaya bata mata rai ba, sai dai zuciyarshi ta gaza hakure mashi, ya rinka juya abun a ranshi yana tausayin Mummy ba ya son damuwarta, tunda ta yi mashi magana yasan abun aranta yake to sai dai ya ya iya da rayuwarshi.? A hankali ya saukar da ajiyar zuciya yana kallonta, ya ce "Mummy kiyi hakuri, amma wallahi ko nace maki zani rabu da Naja'atu, wallahi karya nayi maki, a karshe ba za ki ji dadi ba, idan kika ganni tare da ita, Mummy idan ba za ki damu ba, zan iya hakura da auren Farida, in auri Naja'tun shi kenan." Cike da mamaki take kallonshi, yayinda shi kuma duk ya marairaice mata, sai ta ji tausayinshi ta ce "Daddy idan aka yi haka ai an zama kananan mutane, kuma kai ma ba ka yi mata adalci ba." Ya ce "To Mummy yaya zani yi, ni dai gaskiya na fadi maki kiyi hakuri kici gaba da yi mani addu'a, Insha Allahu komi zayazo da sauki." Mummy ta rinka jinjina maganar a ranta, don so kam tafi son ace Naja'atun ya aura, to sai dai abin dubawa shi ne yarda aka dauki tsawon lokaci ana wannan maganar, yanzu da rana tsaka azo ace an fasa ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, an yi karanta, ita kanta ba za ta ji dadin irin daukar da Hajiya Hassatu mahaifiyar Farida zata yi mata ba, haka nan idan ta duba yarda shi Khalid ya dauki maganar Naja'atun da muhimmanci, ba girma ba ne ya dawo ya tarda wannan abun? Yanzu su duka tausayi suke bata, shi Daddy ga halin da ya ke ciki, kuma tayi Imanin abin da ya lada gaskiyarshi kenan, tafi kowa sanin halinshi. idan ba at: da ya damu dashi ba da wuya ka ji yana magana akanshi, itama Naja'atun ta lura ta rufe idanuwanta ta makance akan kaunar Daddy abun har tsoro ya ke bate ganin yarda abun ya ke ta kara ta'azara, ba ta son ta bat mashi rai, idan ta ga ranshi a bace, shi kenan hankalinta ya tashi, ba zata sake samun natsuwa ba har sai su daidaita, komi zata fadi mata ba zaya yi tasiri ba yanz ta damu dashi idan suna hira har bata son wani abu gifta, bata son abin da ya ke fadi mata ba. A bangare daya kuma tana jin dadin yardu Naja'atun take kula da Daddy, abubuwan da take y mashi ya nuna ma ta cewa ita ce mace ta gari, tasan duk wata hanyar da zata bi ta kyautata mashi don haka cikin ruwan sanyi ta yi saurin saye zuciyarshi ta karkat: akalar kaunarta gare shi tabbas kyautatawar da take mashi ta yi matukar tasiri akanshi tunda ga halin da aks ciki, wai yau Daddy ne da bakinshin ya ke fadin cewa "Zaya iya yin hakuri da Farida akan Naja'atu, abin da ban mamaki, to sai dai itama Faridar abin dubawa се, kowa ya sani Farida tana kaunar Daddy fiye da komi, ita kanta. wani lokaci mamaki take yi akan mahaukaciyar kaunar da ta lura Faridar tana yi ma Daddyn, ta yi Imanin matsala ce babba a halin yanzu ace an wayi gari Daddy ya rabu da ita, idan ya yi mata haka bai yi adalci ba. "To meye mafita.?" Matsalar da Mummy ta kasa warwarewa kenan, don haka ta tattara komi ta bar ma Allah, su ka yi sailama su ka shigo Ibrahim na gaba tana biye da shi, hannunta rike da 'yar Karamar jaka da ta zuba kayan gyeran gashi. Idanuwanta fes akan Daddy, sai ta sakar mashi wani sassanyan nupnushi, shima ya maida mata martani. Mummy ta dube ta taba murmushi ta ce "Naja'atu ha kun dawo? Amma kunyi sauri." Ta zauna bisa kujera a gajiye, yunwa tana damunta, ta ce "Da yake mun fita da wuri ba mu samu layi ba." Mummy- ta yi murmushi ia ce "Gashi nan kau kinyi kyau." Sai ta sunņe kai tana rauriaushi, duk ta ji nauyin Mummyn, ga shi Daddy yr tsare ta da idanuwa. А hankali ta sauke kwaym idora akanshi, ya jefe ta da wani mayen kallo, ta ji wani ii a jikinta, Daddy da banne ya iya saurin narkar mata da zuciya, ba za ta iya jure kallon da ya ke yi riata ba a gaban Mummy sai ya sanya ta ji kunya. Muryarta ta dan sarke ta ce ma shi "Ina kwana.?" Sai ya yi murmushi, sannan a hankali ya dago kai ya na kallon Mummy, itama kallon su take yi, ta ce "Naja'atu kin biye ma Daddy ko? To yaya zaki yi da Khalid idan ya dawo.?" Daddy ya zuba mat ido ya na sauraren amsar da zata ba da, to itama tambayar ta yi ma ta nauyi, ne za ta ce? Ita kam ta riga ta maida dukkan al'amurranta a hannun Allah, addu'a take yi ba dare ba rana, Allah ya yi mata zabi mafi alkairi, saboda daga Daddy har Khalid su duka ba na yarwa. Ba ta ce komi ba, ta yi murmushi ta tashi ta nufi daki, ta aje jikkarta ta cire hijabinta, sannan ta fito falon suna nan in da ta barsu, sai ta nufi teburin cin abinci 10 ji suma ci ia da Ibrahim idan ta dago idanuwanta sai taga Daddy yana kallonta, yayin da su ke magana akan wani abu da ya shafe su ita da Mummy, nauyin Mummy takc shi kuwa bai damu ba, ya rinka yi mata nuna da tazo su ci tare, ta yi shiru kamar ba ta ji abin da ya ke fada ba, sai ya buda baki ya kirata don kunya, Mummy ta ce "Rigimarka ta yi yawa Daddy, ka matsa ma yarinyar nan, ba har zama kayi zaka yi kalacin ba, amma ka fasa, taso." Ya zuba ma Naja'atun ido daga in da yake sai ya yi murmushi ya ce, "Kada kiga laifina Mummy, duk laifinta ne, ita ta saba mani, ba ni iya cin abinci sai a gabanta." Mummy ta yi murmushi kawai lamarin Daddy ya fara zarta hankali, amma a cikin zuciyarta sha'awarsu take yi, suri hada kansu inama ace Naja'atun ce zaya fara aura, ta yi Imanin zasu hada gina rayuwa mai albarka da za su yi alfahari dasu. Bata yi magana ba ta mike ta nufi kicin wajen Mick, ta ji abubuwan da ya ke bukata ya je kasuwa ya sawo. Daddy ya sake sosai, ya maisa mata sai da ta taso ta dawo cikin falo, tare cuka yi kalacin, ya rinka yi mata korafin wal ta cika kunya ta ce "Deddy a gaban Muminy ne la.?" Ya zuba mata mayatattun idanuwansbi ya ce "To meye? Na fi. son itama ta fabimci irin kaunar da nake yi maki, yarda zata aje maganar kowa ta rungumi tawa. Har yanze dauker maganata wasa kike yi, b san me zani fadi maki ba ki yarda dani." Ta yi murmni ta ce "Ba maganar rachin yarda ba ce, Daddy ni abin da nake dubawa kada in shagalta akan kaunarka, kazo 11 bayan kayi aure ka manta dani, Daddy ina gudun halin ku na maza." Ya ce "Da muka yi me.?" Baku da tabbas." Ya ce "Ki fadi mani abin da kike so in yi maki ki abbatar da cewa da gaske nakc har abada ba zani iya udararki ba." Bai rufe baki ba, wayarta dake aje bisa tebur tayi kira, ta zuba ma wayar ido, tana kallon sunan mai kiran octor ne, ita kuma ta tsani tayi waya dashi a gaban Daddy, takura ta yake yi da kallo, tana ganin matsanancin kishi cikin kwayar idonshi kafin ta kai annuntaa wayar Daddy ya yi sauri ya dauki wayar, sai kawai ya daure fuska, sai ta kasa ce mashi komi, bata an yarda zata yi da fitinar Daddy ba, ashe haka maza suke da tsananin kishi? Akan Daddy ta shaida haka, duk m yarda suke zaman dadi matsawar Khalid ya kirata to wa sai ta kai zuciya nesa, idan ba haka ba ka, sai sun yi rigima. Ba ta gama wannan tunanin ba, wani kiran ya sake shigowa, ta zuba mashi ido, zuciyarta na bugawa, duk da cewa tasan yanzu kaunar Daddy tafi komi muhimmanci 2 gare ta, amma bata son ta yi saurin sakin Doctor halid saboda ba ta da tabbas akan Daddyn, to shi abin va ke so wai ta kira shi ta sanar da shi cewa ta yi miji, n haka ya yi hakuri kada ya sake yi mata waya. A ninta wannan cin fuska ne, Doctor bai cancanci haka ga gare ta ba, ta fi son ko rabuwa zasu yi su rabu cikin erziki, tunda dama mutunci ne ya hada su. Idanuwanta sun dan canza launi, ta rinka girgiza mashi kai bata son ya bude wayar, shi kuwa niyyarshi 12 sana da tunda ita, ba za ta iya yin magana ba, shi zaya shi da bakinshi ko ya samu sanyin zuciyarshi, saboda a halin yanzu idan da akwai wani abu da ke yi mashi barazana ga rayuwarshi bai wuce Khalid ba, ya tsani ya ga ya kira Naja'atu ya na kishin hakan, saboda haka ne ya sa duk lokacin da su ka yi waya da Khalid da ta gama zata goge shi daga cikin lambobin da aka kirata, hakan ya fiye mata sauki, saboda idan ya gani sanya ta yake yi a gaba ya tsare ta sai ta fadi mashi duk abin da ya се mata, ko ta fada ba a zama lafiya, sai ya ce ta boye mashi wani abu, duk irin yarda zata yi mashi rantsuwa ba zaya yarda ba, ya rinka fushi kenan. Daddy matsala ce kishinshi har ya fi na wata macen. Gaba ki daya ya rufe wayar ya aje ma ta bisa tebur, ta ci gaba da kallonshi yanayin shi ya canza tana ganin azababben kishin a cikin kwayar idonshi sai dan cije lebentà ta ce "Daddy menene.?" Ya ce "Yaya kike so in yi, na fadi maki bani son wayar da guy din nan ya ke yi maki, ki fito ki fadi mashi gaskiya, ya yi hakuri ni zaki aura, don mi za ki rinka bata mashi lokaci, alhalin kin san ba aurenshi za ki yi ba, na lura har yanzu ba ki yarda dani ba." Ba ta ce ma shi komai ba, ta saba da rigimarshi, sai dai zancen wai ta fito fili ta ce ma Khalid ba ta son shi ma bai taso ba, ba za ta yi sakin na hannu kamun na waje ba, dole ta jira taga abin da Allah zaya yi, shi kuwa laifinta ya ke gani, a ganinshi yana iya bakin kokarinshi wajen ganin ya nuna mata tsantsan kaunarshi, ta yarda don kanta zata iya fahimtar matsayin kaunarta a zuciyarshi, amma ta ki fahimta ta tsaya tana 13 sawaven Khalid. Kila ta fi son shi ne. Kishi ya ke ji sosai a cikin zuciyarshi. Bai sake kula ta ba, ya share ta ya ci gaba da kallon wasan kwallon kafa a talabijin, to itama sai ta fita harkarshi. Idan ya sauko don kanshi zaya neme ta. Su ka ci gaba da zama shiru, idan ta dube shi sai ya hararc ta ya kusa sanya ta dariya, sai ta kwashi filet din ta nufi kicin, shima bai jima ba ya dauki makullanshi ya fice daga gidan baki daya. Ta gama sallar azuhur tana zaune bisa abun sallah, tana lazumi lamarin ya zauna mata a rai, ta rinka kissima yarda zata warware matsalolinta, a karshe sai ta karkata adda'arta akan Allah ya yi mata zabi mafi alkairi, matar mutum Kabarinsa, Allah shi kadai yasan daidai bata da zabi sai abin da ya za6a mata. Ta saukar da ajiyar zuciya tana tuno Daddy yanzu haka yana can yana fama da fushinshi, tasan halin shi idan aka bato mashi rai, laifin sai ya shafi kowa. Sai tayi murmushi ita tasan kan 'yan kayanta. Wayarta tayi kira, ta duba taga Doctor ne, sai ya bata tausayi ta dauka tana murmushi ta amsa mashi da sallama, shima cikin damuwa yake, ya ce "Naja'atu ki fadi mani me yake faruwa.?" Ta ce "Da aka yi me.?" Ya ce "Meye ba'ayi ba? So kike yi sai kin fasa mani zuciya ko? Ko kuwa so kike yi in tsallako karatun nan in taho.?" Ta sassauta murya da shigar lallashi ta ce "ka yi hakuri naji nayi laifi, amma idan ka saurari bayanina zaka san cewa ba laifina ba ne, tun safe na fita saloon, wanke kaina, sai yanzu na dawo naga miscall din ka har 14 biyu, saboda na bar wayar tana caji na duba wayar naga babu kudi. na ba maigadi ya sawo mani don in kirawoka, bai dawo ba yanzu na gama sallah na ji ka sake kira." Tana jinshi ya saukar da ajiyar zuciya sai ta lumshe ido tana kara jin tausayinshi, bata san wando ya fi sonta ba tsakanin shi da Daddy, su duka suna da isananin kishi, ko' yaya zaya ji idan ya san Daddy yana nemanta? Ko giyar wake tasha ba zata iya fadi mashi ba, ta bar komi a hannun Allah." Muryarshi ta yi kasa-kasa "Hankalina ya tashi sosai, da na ga na kira har sau biyu baki dauka ba, wallahi babu irin zargin da bai zo mani a raiba, sai naga kamar kina yi mani kora da hali ne, har Zainab na kira na tambaye ta ta ce mani. Iya sanin ta babu komi sai dai in baki kusa ne abin da ya sanya na dan ji sanyi kenan." Naja'atu ta yi murmushi ta ce "Ka yi hakuri, kasan dai

Chapter 1 of 6