ya
tsare kayi tafiya da kula." Ya ji dadi sosai da ba ta nemi
takura shi ba, amma ta tsare shi sai da ya yi kalaci,
sannan ya fita.
ta
Tun safe Naja'au aikin gyaran dakin Inna take yi,
sai da ta fiddo kayan dakin kaf waje, ta share lungu da
sako, sannan ta maidasu ciki. Dakin yayi tsari fes-fes da
shi, sai yamma ta yi wanka ta yi sallar la'asar sannan ta
ci abinci ta shirya cikin wata shadda ja siket da riga,
jikinta yana kamshin turare mai sanyi ta fito tsakar gida
ta zauna tana karatun wani. Littafin Hausa, wani yaro ya
shigo ya ce "Wai an ce ana sallama." Ta dago kai tana
kallon dan makwabtansu ne, ta ce "In ji wa.?" Ya ce
"Wani mutum ne anan waje." Ta ce "Wa yake nema?"
Ya ce "Bai fadi mani ba ya ce dai in shigo lu ce ana
sallama." Та се "To ka tambayo wa ake nema." Inna ta
fito daga cikin daki ta ce "Kina nan dai da gardamarki ki
leka da kanki mana ki gani kilama bakon Babanku nc,
ba sai ki fadi mashi aaya wurin aiki ba bai dawo ba,
amma ai babu dadi, babban mutum ayi mashi irin
wannan aiken."
Sai ta mike rike da littafin ta fita cikin zaure bata
ga kowa ba sai da ta leka suka yi ido hudu da Daddy ya
na tsaye rungume da hannayenshi ya jingina da mota. Ta
45
ji zuciyarta ta na bugawa da Karfi, duk wam kuzarin da take da shiya katse, ta sarda kai ba ta ce komi ba, ta
dawo cikin zauran don haka shima ya biyo bayanta, ya
tsaya kawai ya na kallonta sai yaga ta kara yi mashi
kyau, muryarta duk ta sarke ta ce mashi "Ta na zuwa."
Ta koma cikin gida.
Inna ta na tambayar ta "Wayc.?" Ta ce "Daddy
ne." Ta dube ta cike da mamaki, ta ce "Ba dai angon
ba.?" Ta ce "Shi ne." Ta cc "Ina fatan lafiya ko." Та се
lafiya lau, ina makullin dakin su Mas'ud in shiga dashi
ciki." Inna ta mika hannu ta dauko mata maku!lin kan
taga ta bata yayinda zuciyarta ke raya mata abubuwa da
dama, amma ta barma Allah komi.
Naja'atu ta dawo zauren, yana nan tsaye ta bude
dakin, sannan ta yi mashi magana ya shiga dakin
samarin, ya zauna sannan ta juyo zata fita, a hankali ya
kirata "Naja'atu.?" Ta tsaya cak tana kallonshi, ya ce "Zo
zauna, ina za ki? Ta ce "Ruwa zani kawo maka." Ya
girgiza kai ya ce "Bar shi zauna muyi abin da ya kawo
ni." Yanayin da yake maganar ya tabbatar mata ya na
cikin damuwa, sai ya bata tausayi, duk ya fada yayi
duhu, babu kwanciyar hankali da walwalar da ta san shi
da ita. Ta koma ta zauna ya tsare ta da ido, akwai rikici
sosai a cikin su, sai dai yana kokarin danne damu'varshi
A hankali ya saukar da ajiyar zuciya ya ce "Yanzu abin
da kika yi Naja'atu kinyi mari adalci kenan? Kin f son
ki jagoranci rugujewar rayuwatə ko? Sai naga ina bakin
kokarina wajen ganin na kauce ma damuwarki, amma
duk wannan bai yi maki ba, shi ne kika tsallako ki ka
46
taho, saboda ba ki so na, ba ki son kwanciyar hankalina,
ba ki damu da damuwata ba? Naja'atu kin fi son kanki
ba ki tunanin halin da zani shiga? Yanzu look at, me,
kalle ni sosai, haka ki ka baro ni?" Ya jinjina kai ya ce
"Shi kenan kin samu yarda kike so, ga shi na biyo ki
Katsinar sai mu zauna tare."
Kuka ya kubce mata, ta zame gabanshi ta na bashi
hakuri, ta ce "Ka yi hakuri Daddy, ba nufina kenan ba,
na yi haka ne don in samu kwanciyar hankali, zuciyata
ba zata iya jure ganin wannan lokacin ba." Ya ce
"Amma kinsan nima ba zani iya jure ma rashin ganinki
ba, sannan akwai abubuwa da dama da kika yi mani
saboda su yanzu nayi nissing din su ko abinci yana yi
mani wabalar ci, kina tsanımanin da haka mima zani
samu kwanciyar hankalin.?" Sai ya bata tausayi, ta
kwantar da kai tana ba shi hakuri.
Zuciyarshi ta yi sanyi ya ce "Ki rinka hakuri
Naja'atu, duk abin da kayi hakuri akanshi wata rana
zaya ba da baya, idan kika duba wannan abun ba yinmu
ba ne, nufin Allah ne, to sai ki bar komi a hannunshi mu
ci gaba da addu'a sai kiga ya zame mana alkairi, to
amma kin kwaso kin taho, na yi Imanin ba za ki samu kwanciyar hankalin da kike cewa ba, haka nima can ki
tada mani hankali, yaya kike so in yi.?" Ta jinjina kai ta
amsa laifinta, ya ce "Yanzu yaya ki ke son ayi.?" Ta
zuva mashi ido, ta ce "Yadda kace." Ya ce "Kin yarda za ki bi ni mu tafi gobe da safe.?" Ta sarda kai tana tunani,
ya ce "Idan kuma ba za ki tafi ba, to rima ina nan ba in
47
du zani je zan yi waya in sanar da Mummy su dakatar
da bikin sai sadda kika shirya."
Ta rinka girgiza mashi kai, ta ce "Shi kenan na
yarda zani bika mu tafi." Sai lokacin ya saki fuska yana
murmushi, ya ce "Don Alah Naja'atu ba yanzu ba ko
can gaba, kada ki sake yi mani irin wannan horon kin
wahalar dani, cikin kwana biyu kina ja yunwa tana
shirin kama ni." Sai ta kara jin tausayinshi, ta taso ta
shigo cikin gida ta shiga kicin yau Inna dashishin
shinkafa tayi fari sol, da miyar kifi sadin, tasha attarugu
tana kamshi. Ta zubo mashi cikin kwano mai tsabta da
filet ta kawo mashi, sai ta fita da kanta ta sawo mashi
ruwa da lemu masu sanyi, tazo ta zauna tana zuba
mashi, ai kuwa ya ci abincin kamar ba zaya rage ba, ya
ji dadin girkin, ga kuma yunwar kwana biyu tana cinshi,
don haka ya ci sosai sai da ta yi mamakinshi ya ce ai
duk laifin ta nc."
Farida ta kira shi tana yi mashi korafin taji shiru ba
ta ganshi ba, gashi suna ta shirye-shiryen mother
evening. Ya ce "kiyi hakuri, ni yanzu ma ina Katsina,
amma insha Allahu gobe da wuri zani taho, na bar ma
abokina Aliyu sallahun yazo wajenki, duk wasu
hidimomin ku za ya yi." Farida kamar zata fasa kuka,
zuciyarta ta raya mata cewa kila Naja'atu ya kai
Katsinar, tunda ba ta san cewa bata nan ba, amma sai ta
kyale shi a ganinta aski yazo gaban goshi, a dai gama
bikin yazo hannu zata raba shi da tunanin duk wata diya
mace. 48
Da ya rufe wayar ya na kallon Naja'atu sai tayi
nurmushi kawai, Daddy ya jinjina kai ganin kokarin
mazan da ke tara mata har hudu yake yi, suna fama. Та
wani Gangaren kuma, dole su zama makaryata, saboda
kowace da irin tata rigimar, yanzu shi duka su biyu ne,
amma kamar su haukata shi, mata shu'umai ne kowace
da rigimarta.
Awa biyu ya shafe da Naja'atu, ya cika ta da
kalaman soyayyarshi, yana kara jaddada mata kaunarshi
gare ta, sai ta ji zuciyarta ta dake, ko don ta faranta
mashi rai, zata bishi su koma Abujar, itama tasan
kusanta kanta dashi, shi ne kwanciyar hankalinta, har
yamma ta yi Malam Abdu ya dawo, ya rinka mammakin
katuwar motar fa ya gani kofar gidanshi, sai da ya shigo
ya wuce su Naja'atun cikin zaure, ya shiga cikin gida,
Inna ta yi mashi bayanin cewa Abubakar ne dan Hajiya
Halima yazo. Malam Abdu ya jinjina abun a ranshi, bai
ce komi ba ya shiga dakinshi. Ba'a jima ba Naja'atu ta yi
ma Daddy jagora har cikin gida ya fara gaisawa da Inna
ta na tambayarshi mutanen gida, ya ce "Kowa lafiya,
suna gaishe ku." Inna ta ce "To madallah mun gode, su
ka wuce dakin Malam, ya shiga har ciki su ka gaisa a
mutunce, Malam ya ce "Malam Abubakar ga hidima
kuma ka taso ka taho.?" Ya yi murnıushi ya na kallon
Naja'atu, sai ya kalli Malam ya na shafa kanshi ya ce
"Ga wadda nazo biko nan."
Malam ya tsura ma Naja'atu ido, shi dama ya zargi
wani abu dangane da tahowarta cikin lokacin, alhalin su
na ta shirin biki. Ya ce "Wani abu ya faru.?" Daddy ya
49
yi murmushi ya ce "Laifi nayi mata Baba, to sai dai na
fadi mata ba laifina ba ne, nufin Allah ne, duk abin da
ya faru da bawa rubutacce ne, abin da ya ke faruwa shi
ne an yi maganar aurcna da ita wanna yarinyar da zani
aura, yanzu to kuma Allah cikin ikonsa, sai ya kawo
mani Naja'atu cikin dan lokaci Allah ya jarabe ni da Kaunarta, dor haka mu duka muna son juna, namiji ne ni
mijin mace hudu don haka na yi ma ta alkawarin cewa
ko bayan na auri wannan yarinyar itama zani aure ta in
hada su su biyu, to yanzu da ake ta shirye-shiryen auren,
shi ne duk ta damu, ba tare da sanina ba ta taho, don
haka na biyo sawunta."
Naja'atu ta sarda kai tana jin nauyin Malam, yayin
da shi kuma ya jinjina maganar a ranshi, tabbas wannan
magana ce mai dadi, to sai dai ina zancen wancan yaro,
da ta kawo mashi har yayi mashi alkawarin cewa zaya
jira shi har sai ya dawo ba zaya matsa ma Naja'atun ba,
da maganar aure.?" Ya saukar da ajiyar zuciya ya ce "Na
ji bayaninka Abubakar, kuma na yi farin ciki, babu abin
da zance tsakanina da ku sai addu'a sai dai akwai wani
abu guda, ke Naja'atu ina maganar yaron da kika kawo
mani nan ki ka ce zaya tafi karatu sai ya dawo zaku yi
aure.?"
Guyawunta su ka yi sanyi, ko dama abin da take
gudu kenan, tasan halin Babanta magana daya tal ya ke
yi, tunda kau ta fara kawo ma shi maganar Khalid to
kuwa yana nan bisa ita, sai dai in dama Allah ya kaddara
Khalid din ba mijinta ba ne. Malam ya gyara zama yana
kallonta, ya ce "kin gane ko, a harka ta aure babu zancen
50
kunya a ciki, saboda kace mai yi kuma keke tara da
mutanen nan, don haka ki buďa baki kiyi mani bayani."
Naja'atu ta kasa cewa komi sai Daddy ya yi murmushi
ya cc "Baba ni kaina nasan da maganar Doctor, to sai
dai shi aure nufin Allah ne, mu duka Allah ne ya jarabe
mu da son Naja'atu, kuma shi ya san mijinta a cikinmu
mu bar wannan lamarin hannun Allah, mu ci gaba da
addu'a Allah ya warwarc mana lamarin ba tare da kowa
ya kwaru ba, yayi mana zabi ma fi alkairi."
Malam ya rasa abin da zaya ce, Daddy ya daure
shi da igiya, tun da ya sanya Allah a gaba ya gama komi,
don haka yayi masu fatan alkairi Daddy ya ce zaya zo da
safe su tafi safko ya ke so su yi." Malam ya ce "Babu
komi." Su ka fito tare ya yi ma Inna sallama, suka fita,
cikin zaure ya ci karo da su Badiyya sun taso daga
Islamiyya don haka ya ja su wajen motarshi ya bude but,
ya rinka fiddo masu tsarabar da yayi ma Malam suna
shiga da su, dankali ne da doya, sai kayan miya da na
marmari. Naja'atu ta zuba mashi ido tana tuhumarshi
hidimar tayi yawa, shima ya yi mata kyar da ido, tana
hango matsahanciyar Kaunarta cikin idonshi, sai ta yi
murmushi ta dan cije lebe ta ci gaba da kallonsu, har
yaran su ka gama kwashe kayan ya cika masu hannu da
kudi sabbi fil su ka shiga gida s murna.
Ya jingina da mota, ya na jiíarta da mayataccen
kallonshi, baya son tafiya ya barta, sai dai ya gaji sosai,
so yake yi ya isa gida ya dan watsa ruwa, da wuri yake
so ya kwanta saboda daren jiya bai rumtsa ba. Ya zuba
hannayenshi cikin aljihu yana kallonta, ya ce "kinsan
51
wani abu.?" Ta girgiza kai ta ce "Sai ka fada." Ya cc
"Na gaji da yawa so nake yi in tafi in huta, sai dai
Kwayar idona bata gaji da ganinki ba, ina son in rinka
sauraren muryarki, ki shirya mu tafi can gida mu kwana
da safe kawai sai mu wuce." Naja'atu ta bude ido tana
dariya ta ce "Dady kasan abin da kake fada kuwa.?" Ya
ce "Ina sa ne." Ta girgiza kai ta cc "Gaskiya kayi hakuri,
wannan ba kimar mu ba ce ina gudun sharrin shaidan
kuma Baba ma ba zaya yarda ba, ni ma haka." Ya tsura
mata udo, ya ce "Don kada dodo ya cinye ki?". Тa се
"Mu bar maganar nan Daddy nema kake yi ka take.
gaskiya ka bi son ranka, kaje ka kwanta ka huta, insha
Allahu zani yi shiru da wuri, karfe nawa zan iso.?" Ya
ce "Karfe shida da rabi, ki zama cikin shiri." Ta yi
murmushi ta ce "Shi kenan Allah ya bamu alkairi." Ya
shiga mota tana tsaye sai da ya bace, sannan tayi
murmushi ta koma cikin gida, tana tunanin Daddy ya
san kanta da yawa, abun har mamaki yake bata.
Washe gari karfe bakwai daidai ya iso gidansu ta
tsare shi sai ya yi kalaci, ya co "Tayi hakuri sun taushe
hannu sosai, yana so ya isa da wuri." Don haka ta dauki
abincin su ka tafi dashi, Inna ta yi masu fatan alkairi har
waje Malam ya rako su, su ka tafi yana son isa da wuri
saboda jiya ya sha korafi wajen Farida wai ya
wulakantata, sun gayyato mutane yawancin kawayen
Mama, nata son su ganshi amma baya nan, ya bata
bakuri ya ce "Insha Allahu yau zaya halarci lunchen
party din. Don haka ya ke son ya koma da wuri kada
52
lokaci ya kure, ya kara wani laifin, so yake yaga
kyautata ma kowace cikinsu.
Kan hanya ma ya rinka kokarin kwantar ma
Naja'atu da hankali yana kwatanta mata yarda abubuwan
suke, to babu laifi Naja'atu ta fahime shi tana tausaya
mashi, don haka ta kwantar da hankalin ta tana kyautata
mashi suka rinka tafiya cikin dadin rai, ya na nuna mata
kauna da kulawarshi, ya tabbatar mata da cewa kada ta
damu, insha Allahu ba za'a ďauki lokaci mai tsawo ba,
zaya yi maganar aurenta ya ce "Ta fadi mashi lokacin da
take son ya rinka zuwa suna gaisawa tunda ba zaya iya
zuwa kullum ba, ko ba koni akwai nisa tsakanin
gidanshi da wajen aikin shi baya da lokacin da zaya
dawo daga aiki kuma har ya fito yazo gida akwai tazara
sosai."
Naja'atu ta yi murmushi ta ce "koda ka samu
damuwa, duk lokacin da ka samu lokaci kazo ba komi."
Ya zuba mata ido ya ce "Ba fushi kika yi ba ko.?" Ta yi
murmushi ta ce "Wailahi ba fushi nayi ba, ai nasan
yanzu rayuwa ta canza, dole ne ka ba iyalinka lokacinsu,
idan nace sai kazo cikin lokacin ai na shiga hakkinta,
tunda idan ka dawo aikin kana son hutawa, kuma
lokacin kurarre ne, tunda ga waya ai babu matsala." Ya
zuba mata ido kaďan, sai ya ci gaba da kallon gabanshi a
hankali ya ce "Na gode Naja'atu, kinga daga jiya zuwa
yau, kin kwantar mani da hankali, rabon da in ji zuciyata tayi mani sanyi irin yau har na manta, don Allah kada ki kara barin wani abu ya sake shiga tsakaninmu." Ta jinjina kai ta ce "Insha Allahu." Ya zuba mata ido ya сe
53
'promise' ta yi murmushi ta daga mashi gira sai yayi
dariya har zikin zuciyarshi yana kara Kaunar yarinyar.
Karfe biyu daidai suka isa gida, Zainab ta fio da
gudu ta rungume Naja'atu tana murnar dawowarta yayin
da ita kuma Mummy ta rinka yi masu fada, wai sunyi
gudu don mi Naja'atun ta kyale shi ya yi gudu sosai irin
haka.?" Naja'atu ta yi murmushi ta ce "Kiyi hakuri
Mummy ya ce ana jiranshi ne."
Gidan cike yake da mata 'yan biki, don haka basu
da wani hutu Sallah kadai suka yi suka fita saloon
gyaran gashi ita dada Amina diyar kanwar
Babansu ce tana karatu a Danfodio University, tana da
sakin fuska don da nan su ka shaku. Tun a saloon din su
ka fara gardama, sabcda su Zainab sun ce da sun koma
shiri zasu yi su je wajen lunching party din, yayin da ita
kuma Naja'atu ta kafe kan cewa ba za ta je ko ina ba,
haka kawai taje a wulakantata." Amina ta ce "To mu dai
sai munje." Naja'atu ta ce "To ai dama ban hana ku ba,
ku shirya kuje kawai zani zauna gida." Zainab ta Kule ta
kasa ce mata komi, ta rasa irin Naja'atu tasan saboda
Farida ue zata ce ta ki zuwa, to ina ruwanta da ita, ta
shirya taje, idan yaso ita kada ta zauna ruwanta, amma
sai ta rinka ware kanta tana takura ma kanta, alhalin shi
Daddyn ya fi son yaga ta saki jiki ana yin komi da ita, ta
yi imanin cewa zaya yi ſarin ciki idan ya ganta a wajen.
Da su ka koma gida, su Zainab na a shirinsu,
Naja'atu ta zauna tana shirya kayanta cikin wadrof
Zainab ta gama shirinta ta fita. Daddy ya na cikin
dakinshi yana shiri ta kwankwasa mashi kofa ya ba ta
54
izinin va shiga, sai ta murfa kyauren ta shiga ya ce
Zainab lafiya dai ko." Ta yi murmushi ta ce "lafiya lau
Rarar Naja'atu na kawo maka, ta zauna wai ba zata je
Wurin lunching din ba, alhalin ga shi mu mun shirya
lafiyá zamu yi." Bai yi magana ba, ya dauki wayarshi ya
kirata, ya ce "Tazo yanzu yana sön ganinta a dakinshi."
Zuciyarta ta rinka raya mata abubuwa da yawa,
tunaninta ya tsaya kan cewá Zainab ce ta hafa ta da shi.
a taso ta fito zuwa dakin, ta vi sállama ta shiga yana
saye yana daura agogo, sanye ya ke da wani farin
fallausan yadi, dan ubansu, bata san me zata kira shi ba,
ya yi mashi dinkin zamani mai fadin hannu rigar ta
saya mashi iya guiwa, da nmanyan atjihu kana ganin
farar shimin da ya shimfida a jikinshi, kafin ya sa rigar.
Farin mutum dogo AHah ya zuba ma Daddy-ruwan
kyau, mai dauk ar hankali idanuwanshi makimanta farare
ol masu tsananin haske da saurini daukar hankalin duk
wanda ya kalka sajenshi mai kyau da tsari yasha gyaran
zamani, sai ya kara mashi kyau na musamman.
Ya zuba mata ido da wata irin siga ta nana kaunar
Bshigare t ta yi murmushi ta sarda kai, tana kallon
Zainab Zatonta ya zama gaskiya, sai ta dubi Daddyn tana
sauraren abin da zaya ce mata. Va mika bannu ya dauko
firarenshi yana fesawa sai ya cần koisita ya.co #Me
svasa kika ce ba za ki je duncing oe?saboda ba ki son
kWandiyar harikalina Ko? ta ce "Ha haka ba nejni bani
Boninyi dbin da wani zaya ga banyi mashi daldai ba,
bah son tashin hankali"Ya/zuba mata ido ya ce 'Dawa
zaki yi tashin hankalin.? Ta darr cije lebenta ana kallon
55
wani sashin ba ta ce komi ba, ya ce "Kije ki shirya ku
fito in tafi da ku." Bai saurare ta ba ya ci gaba da
shirinshi, ta juya tana kallon Zainab sai dariyar mugunta
takc yi mata, ita kam Daddy yana neman takura mata ne,
da yayi hakuri sunyi tafiyarsu, ya fiye mata sauki.
Zainab ta kama hannunta ta ce "Zo muje don Allah kina
bata mana lokaci kin san fa ana jiranshi."
Daga Zainab har Amina suka yi tsaye kanta sai da
ta yi kwalliya sosai, da wani leshi lallausa, mai jinin
kare riga da zani rigar 'yara karama daidai jikinta, tayi
kyau sosai cikinsu, ta shafa jambaki kalar kayan abinka
ga farar mace sai ta yi kyau kamar ita ce amaryar ta
daura kallabin kayan ta kara haskawa, jikinta na kamshi
na musamman su ka tito Daddy na jiransu, Zainab da
Amina su ka zauna baya, yayin da ita kuma ta kame
gaba kusa dashi ya dube ta sai ya ji nufashi ya na yi
mashi wuyar dauka ta yi kyau kamar fure ina ma ace ita
ce amaryar? Sun dace da juna, ya rinka satar kallonta ta
madubi, da ya son ya yi mata wata magana gabansu
Zainab su raina shi, Daddy akwai tsare gida.
Harabar otel din da ake yin partyn ta cika makil da
mutane 'yan biki wayayyun 'yan boko, ya dace ace an
fara gabatar da komi amma rashin zuwan ango yasa aka
dakata, Farida har ta fara cika, ta hango motarshi na
shigowa, sai tayi murmushi yayin da motar ta shigo ta
isa wajen da aka kebe don aje motoci ta tsaya ya bude
aljihun motar ya fiddə bandiran kudi sabbi fil ya manna
ma Naja'atu nata a hannu, ya mika ma su Zainab nasu ya
ce "ku yi amfani dasu." A hankali ya sauke kwayar
56
¡donshi akan Naja'atun sai ta sakar mashi murmushinta
mai sanyi. Ya ji dadi a ranshi, ya cc "Takc care." Suka
fito tare Zainab taja hannun Naja'atu, su ka kama
gabansu, yayin da shi kuma ya tsaya yana gaisawa da
wani abokinshi, sannan su ka nufi in da amaren su ke.
lAkan idanuwan Farida duk abin da ya faru, sai ta ji
kamar ya soke ta da mashi, ta rumtse ido cike da takaici.
Zee da ke kusa da ita, ta dafa ta ta ce "Ga Angon nan ya
iso fa, wadancan kannenshi ne.?" Farida ta dan cije lebе
ta ce. "Akwai kanwarshi ciki, amma waccan da ta fito
kusa dashi yarinyarshi ce, wai itama aurenta zaya yi."
Zainab ta bude ido tana mamaki ta ce "Shi ne kuma ya
taho mana da ita nan.?" Farida ta cije lebe ta ce "In haka
aka ce mashi ba dole yayi ba, ai yarinyar cikin gidansu
take, uwarshi ce ta jajibota ta kawo ta don kawai ta hana
shi aurena, Allah ne bai nufa ba." Zee ta ce "kuma shi
yana sonta.?" Та се "Ba ga alama nan kin gani ba, ki
duba kwalliyar da ta yi mana, ko ita ce amary sai
haka." Zee ta ce "Lallai kina da aiki ja a gabanki, ashi
zaki yi tsaye ki raba shi da ita:" Farida ta yi dariyar
mugunta ta ce "Daina wannan maganar Zee, ai kin dai
sanni, ki bani 'yan kwanaki ki gani, ko ita uwar idan ba
ta bi a sannu ba, raba su zani yi don ba za ta zame mani
matsala ba.
Su Daddy su ka karaso wajensu, yana fara'arshi
lallai kam ya yi ma ta kyau shima ganin kyawunta ya ke
yi, ya dan rusuna yana kallonta cikin idonta ya ce "kiyi
hakuri na 6ata lokaci ko.?" Ta ji wani iri cikin jikinta,
sai ta sarda kai ita dai tasan tana cikin mata masu
57
tsanamin sa'a a rayuwa, auren kyakkyawan mutum irin
Daddy abun alfahari ne a gare ta, sai ta ji ya wanke duk
laifin shi da take gani aka shiga hidima, ga abinci da na
sha nan kala-kala, yayım da makadan rundunar
'yansanda su ka kayata wajen da kidansu mai dadi,
kowa ka gani yana cikin farin ciki da annushuwa. Daddy
na tarc da Amarya a wajen zaman da aka keße masu na
musamman amma idanuwanshi suna kan Naja'atu, ta
saki jiki suna ta hirarsu da su Zainab, sai dariya suke yi,
ya rinka kallonta yana son ta kalle shi, amma ta ki
kulawa dashi bata son taga abin da zaya bata mata rai.
Ango da amarya su ka fita fili, su na taka rawa, su
Zainab su ka fita suna liki, amma Naja'atu ta ce ba za ta
je ba, ta yi zamanta tana kallonsu, fili ya kacare ana ta
cashewa don haka yayi amfani da wannan damar ya
kefe kanshi ya kira ta ta waya, da ta duba taga shi ne sai
ta rufe wayar gaba ki daya, ta dago kai yana kallonta sai
ta yi murmushi ta girgiza mashi kai, ta share shi ta ci
gaba da kallonta. Ba zato sai dai ta ji kamshin turarenshi
ya baibaye wajen da take. Ta fago idanuwanta a hankali
tana kallonshi sai ta yi murmushi ta ce "Daddy abin da
kake babu kyau fa, idan ni kayi ma haka ba zani ji dadi
ba, kayi hakuri ka koma ku ci gaba da hidimar ku." Ya
ce "Amma don mi za ki takura kanki ki zauna waje
daya.?" Ta ce "Shi kenan ka tafi zani taso."
Ya jinjina kai ya koma sai da aka dauki lokaci
sannan ta tashi ta shiga fagen rawar bata takaba, amma
ta rinka zubda Naira kamar ruwan banza. Farida na
kallonta ta kara kulewa, amma Naja'atu ba ta je kusa da
58
jta ba, ta tsaya in da su Zainab suke su ka rinka yi ma
junansu liki.
Da aka tashi ba su jira Daddy ba, abokinshi Aliyu
ya dauke su ya maida su gida, haka nan bata sake
ganinshi ba, bai kwana gidan ba, saboda yawon mutane
sai đai ya yi mata Text ya na godiya kan abin da tayi
mashi.
Washe gari tunda su ka tashi ba su da lokacin
kansu ana ta hidimar yinin biki da daurin aure, gidan ya
cika da mutane maza da mata yan faurin aure. Su.
Naja'atu Hajiya ta fora ma hidimar ba baki abinci don
haka gaba ki daya hankalinsu ya tafi wajen hidima da
jama'a, da ke ta durarowa ta ko'ina 'yan'uwa sumyi ma
Hajiya Halima kara sosai, bata yi tsammanin Inna zata
zo sai gasu cikin bus, tare da sauran 'yan'uwan Hajiya,
taji dadi kwarai, an ce kayi ma mai yi maka. Mummy ta
cancanci ayi mata komi.
Karfe daya saura tana cikin kicin tana fidda
abincin baki maza da suka zo daga Katsina, Zainab ta
shigo ta ce "Ba ri in ida zubawa kijc Daddy ya na
kiranki, ya na dakin shi." Naja'atu ta dan yatsuna fuska,
ta ce kai jama'a in yi yaya da wannan aikin? Yanzu idan
naje ba zaya barni in fito ba, kije Zainab in abinci yake
so ki zuba mashi. Zainab ta ce "Amma ai ya ganni kuma
ya ce in zo in kira ki, sai dai in ba za ki je ba in koma in
fadi ma shi don kar ya ga lailina" Naja'atu ta jefa mata
harara, ta fito ta nufi dakin ta dan kwankwasa sannan ta
shiga ya na kwance dai dai bisa gado ko alamun shiri
bai yi ba, ga shi daurin auren na karfe biyu da rabi ne,
59
lokacı yana Karatowa. Ta yi mashi sallama ya fago kai a
hankali yana kallon ta duk sai ya ba ta tausayi, ya yi
wujiga