Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bango, tunanin ta inda za ta ɓullo wa al'amarin ya tafi cikin sauƙi take yi, don a yadda ta ga yanayin mijin nata ba ƙaramar fafatawa za su yi ba kafin ya yarda su gana da tsohuwar matarsa. Duk yadda yake nuna mata ba ya son ko da jin sunan Hafsan ba ta taɓa zaton abun zai fusata shi haka ba....✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [5/11, 12:13 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGT PENS* (FREE BATCH) *36.* Jiki a sanyaye ta shiga toilet ta yi alwala ta fito ta tayar da sallah. Ina nan zaune kamar mutum mutumi Sultan ya shigo yana yi mini magana amma ban fahimci me yake cewa ba, Naja ɗauke da cikin Anas kawai nake gani a idona, na dinga tambayar kaina ya aka yi haka ta faru? Ko da ma can suna soyayya ne ban sani ba? Yaushe suka fara har ta kai su ga aure? Ya aka yi Mama ta amince ta bar ta, ta auri mijina? Inna wa inna ilaihir raji'un kawai nake maimaitawa a fili da zuci. Saboda al'amarin ba ƙaramin girgiza zuciyata ya yi ba, ya kaɗa ni sosai, hakan ya sa na kasa yarda nake tunanin ko mafarki nake zan farka. "Mami Maamah ta ce ki je ki alwala ki yi Sallah." Sufyan ya faɗa yana girgiza ni, alamar ya yi mini wata maganar kafin wannan ban ji ba. Kai kawai na gyaɗa masa, ya nuna mini ƙofar toilet ɗin da ke cikin ɗakin ya ce na yi a ciki. Idan da mutum yana yi wa kansa Hisabi da tabbas na ce sallar da na yi ba ta karɓu ba, saboda bana cikin nutsuwata, ga tunane-tunane da ya kanainaye mini zuciya, abin da na sani kawai na yi addu'a sosai akan Ubangiji ya sassauta mini abin da nake ji a cikin raina. Da na san abin da zan tarar kenan da ko da wasa ba zan yi gigin zuwa gidan nan ba, sai dai na nemi inda yake aiki na je can mu haɗu, tunda yanzun da na zo ba ni da tabbas ɗin ma yana gidan ko ba ya nan. Sai yanzu ma na ga wautata na zuwa gidan, don da wata ce matar tasa ba Naja ba ban san me zan ce mata ba, ko kuma idan ta ji ni ce tsohuwar matarsa ta yi mini korar kare. Allah ma ji roƙon bawa, a hankali na ji abin da ya cunkushe mini a ƙirjina ya fara yayewa cikin sakanni. Hakan ya sa na fara sakin ajiyar zuciya. A lokacin Naja ta dawo hannunta ɗauke da jug da ƙananun cups, ta ajiye a gabana tare da faɗin. "Me ya sa ba ki ci abincin ba?" Kallon plate ɗin gabana na yi ina son tuna wanda ya kawo da lokacin da aka kawo, kamar ta san abin da yake raina ta ce. "Idan ba ki ci ba Sultan ba zai ji daɗi ba, ya kawo miki cikin ɗoki da murnar ganin ki amma kike ƙoƙarin ba shi kunya." Girgiza kaina na yi na ce. "Ba zan iya cin komai ba Naja a halin da ake ciki, kawai ni ki faɗa mini ya aka yi haka ta faru? Ya aka yi kika auri Abban Sultan? Ko da ma kuna soyayya ne tun da ban sani ba?" Gyarawa ta yi ta zauna da kyau tare da sauke numfashi, cikin taushin murya ta fara magana da faɗin. "Abubuwa da yawa sun faru kam, kuma labarin da tsayi, amma zan taƙaita miki shi. Ko da wasa ban taɓa tunanin zan auri mijinki ba, soyayya kuma ke ma kin san ni da Anas ba za mu taɓa yin ta ba ko da zai zama mu kaɗai muka rage mace da namiji a duniya a lokacin da kina matarsa, don haka ba mu taɓa soyayya ba, ƙaddara ce kawai ta haɗa mu a inuwar ma'aurata, a lokacin da babu zaton mu babu tsammani. Satin da kuka rabu da Abban Sultan satin Allah ya yi wa Usman saurayina rasuwa yana shirye-shiryen kawo lefensa gidanmu, na shiga tashin hankali da ɗimuwa ba kaɗan ba a lokacin, nai ta kiran wayarki na sanar miki bana samun ki, sai na kira Anas na faɗa masa ya faɗa miki, a nan yake sanar mini kun rabu. Ban san ya zan kwatanta miki yadda abun ya daki zuciyata ba, don tsakanin mutuwar Usman da rabuwar auren ku ban san wanda ya fi saka ni a cikin damuwa ba. Da na faɗa wa Mama na ba ta labarin abubuwan da kika dinga yi masa kuka saka, ta ce ta fi tunanin asiri aka yi miki, ba kya cikin hayyacinki, a ruɗe ta karɓi nunbern shi ta kira shi ta ce ya zo tana son ganin shi. Da ya zo tai ta yi masa faɗa ta ce me ya sa bai kawo ƙarar ki gurinta ta cicci ubanki ba, ya ce ya yi tunanin zai iya saita matsalar ne sai kuma abin ya gagare shi, kuma shi bai iya kai ƙara ba. Tai ta yi masa faɗan sakin ki da ya yi, ta ce da ya sani gurin masu roƙiyya ko masu karya sihiri ya kai ki, don ita ba ta yarda kina cikin hankalinki akwai abin da zai ruɗe ki ya sa ki iya rabuwa da shi ba, ya ce mata sai da ya tabbatar lafiyarki ƙalau, iskanci ne kawai da wulaƙanci, sannan ya yi miki abin da kike so. Sosai dai Mama ta ji takaicin rabuwar ku, don sai da ta yi watanni kullum sai ta yi zancen, tare da yin Allah wadai da ke. Ta so zuwa gidan Kawu ni na hana ta, saboda na gane blocked ɗina kika yi, hakan ya sa raina ya ɓaci sosai, na ce in sha Allah na fita daga rayuwarki, kamar yadda kika nuna ba kya buƙata ta a cikinta, don ban taɓa tsammanin ko dambe muka yi da ke a yadda muke za ki iya yin blocking ɗina ba. Bare daga faɗar gaskiya da nusar da ke illar abin da kike aikatawa. Sai dai na kasa cire ki daga cikin raina kamar yadda na so, kullum sai na tuna ki tare da yi miki addu'ar shiriya da ta kaucewa daga faɗawa hallaka. Duk da Anas bai faɗa mini ba amma na san ba ƙaramin tashin hankalin rashin ki ya shiga ba, ya bar garin nan ya koma ƙauyensu, ya canza nunber. Idan su Sufyan suka dame shi da kukan son ganin ki ni yake kawowa su, su yi mini kwana biyu, idan suna yi mini zancenki sai na ji kamar na kai miki su, sai kuma na fasa na ce ke ma ki ɗanɗana zafin rashin su, don na san dole ki yi kewar su, daga nan za ki fara gane har kanki kika cuta ba Anas kaɗai ba. Ba ku fi wata huɗu da rabuwa ba ya jewa wa Baba da batun yana son aure na, na san ya san tabbas ba zan amince ba, shi ya sa ya tafi gurin shi direct. Ya ce masa ya san ni kaɗai zan kula da su Sultan na riƙe su tsakani da Allah, don yana son ya yi aure a lokacin ko zai fi saurin mantawa da abin da kika yi masa, ga kuma karatun su Sufyan ya tsaya, yana son ya dawo nan da zama su ci gaba da karatunsu, tunda a can ƙauyensu babu schools, a zaune kawai suke ba sa zuwa ko'ina. Baba ya amince ya ce lallai ya yi tunani mai kyau, kin san su maza babu ruwansu da abin da bai dace ba in dai ba a addini ne ya haramta ba. Ni da Mama kam yana zuwa da maganar muka ce sam ba mu san zance ba, Mama ta ce ba za a yi wannan cin amanar da ita ba. Ni kuma kamar zan yi ɗan ƙaramin hauka saboda tuburewa ganin Baba ya dage, yana ta yabon hankalinsa da cewa abin da ya faɗa akan hujjar aurena ya sa ya amince, saboda tausayin yaran, sun saba da ni kuma yana da yaƙinin ba zan cutar da su ba, zan riƙe da su da amana. Na kafe kai da fata ba zan aure shi ba, don gaskiya ba zan iya auren mijinki ba. Har nunbern shi na goge a lokacin, idan ya kira na ƙi ɗauka, idan ya kawo su Sultan na daina raka su don kar mu haɗu, na yi masa text na ce ni bana son shi, kuma ba zan iya auren shi ba, ya je ya nemi wata, akwai mata na gari sosai a duniya da za su riƙe masa ƴaƴansa da amana. Amma duk da haka ya ƙi haƙura ya ci gaba da naci. Mama ta kira shi ta zaunar da shi, ta nuna masa illar aure na da irin idon da duniya za ta kalle mu, amma ya ce tunda ke kika nuna kin gaji da zama da shi, kuma aure tsakanin ku ya ƙare kawai mu manta da ke mu yi aurenmu, ya san ko kin samu labari ba za ki ji komai na rashin daɗi ba. Ya faɗa mata maganganu masu ratsa zuciya da kafa mata hujja da dalillan son aure na, sai ta ce to Allah ya tabbatar da alkhairi. Ganin tana ƙoƙarin amincewa ita ma na zauna na dinga yi mata kuka, tare da faɗin, yanzu ita ma ta goyi bayan na ci amanar ƙawata kenan? Gaskiya ni ba zan iya wannan butulcin ba. Kuma har ga Allah ni da gaske nake bana so, ba don bai cancanta ya zama miji a gare ni ba, sai son saboda ke kawai. Har ƙoƙarin barin garin na yi don su rabu da ni da zancen. Amma da Ubangiji ya ƙaddara sai da aka yi, ba bisa son raina ba bisa tursasawar Baba tare da yi masa biyayya, don kafewa ya yi sai na auri Anas ko ina so ko bana so, tunda ban da tausayi bana ganin halin da yake ciki shi da yaransa. Wallahi Hafsah a ranar da aka ɗaura aurenmu kamar zan yi hauka, na dinga kuka ina jin kamar na mutu, saboda ban san da idon da zan kalle ki ba, har addu'a na dinga yi Allah ya ɗauki raina kafin a kai ni gidansa, kuma ƙarin abin takaici ba a saka bikin da nisa ba, cikin ƙanƙanin lokaci aka yi komai aka gama. Kuma abin mamaki babu abin da bai yi na hidimar biki ba daidai ƙarfinsa, don Baba ya ce ya bar lefe ma, amma ya dage sai ya yi. Direct Abuja aka kai ni, saboda wata kwangilar aikin wani kamfani da ya samu a can, ya siyar da gidansa da kuka zauna ya kama mana haya a can, sai da ya gama aikin za mu dawo ya siya wannan gidan. Na aure shi ba don zaton za mu yi rayuwa irinta kowanne ma'aurata ba bare har mu yi soyayya, sai dai kawai na riƙe masa ƴaƴa na kula da su na dafa masa abinci. Amma ko kwana ba mu yi ba sai da ya sauya mini wannan tunanin, ba sai na faɗa miki ba, don na san kin fi kowa sanin shi a wannan fannin, duk yadda na so da turjewata da ƙin kar mu yi wannan rayuwar sai da al'amarin ya sauya. Zuciya ba ta da ƙashi, kuma tana son mai kyautata mata, a hankali na fara sabawa da shi a matsayin miji, na fara ba shi kulawa da kyautatawa kamar yadda yake yi mini. Cikin lokaci kaɗan muka zama abu ɗaya, shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu. Duk yadda nake tunanin Anas sai na ga ashe ya wuce nan, nagartarsa da kyawawan dabi'unsa sun zarce yadda nake tunani kafin mu fara rayuwa tare. Hafsah kin yi rashin miji, kin YI WA KANKI babbar cuta da kika bari kuka rabu. Don Anas mutum ne har da rabi, ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, amma kyawawan halayensa sun saka ba a ganin munanan idan ma yana da su. Kuma ya so ki, har yanzu ma na san yana son ki, kamar yadda na san har abada ba zai daina son ki ba. A kanki fa har aikinsa ya haƙura da shi, ya bar garin nan duk dan ya yi nesa da inda kike ko zai samu sauƙi a cikin ransa, anya kuwa za ki samu mai son ki da ƙaunar ki kamar shi a rayuwar nan?" Ta ƙarashe maganar tana kallo na. Ban cewa komai ba sai hawaye da nake yi. Kamar za ta yi kukan ita ma ta ce. "Ki yi haƙuri, na san ba mu kyauta miki ba, amma ki yafe mana don Allah, wallahi ƙaddara ce kawai wadda ta riga fata." "Haƙuri? A kan me za ki ba ni Haƙuri Naja? Ko me ya faru ai ni na janyo wa kaina, wallahi ko kaɗan ban ga laifinku ba, sai ma kyan kan Anas da na gani da ya aure ki, saboda yadda yake da kyawawan dabi'u ke ma haka kike, kuma za ki riƙe masa ƴaƴansa tsakani da Allah kamar yadda yake fata, ni ce ma zan ba ku haƙuri, akan abubuwan da na yi muku, ki yafe mini don Allah Naja, na gane ban da masoyiya a duk duniyar nan sama da ke, sannan kuma ki ba wa Mama haƙuri, ita ta taimaka ta yafe ni ɓacin ran da na saka ta a ciki, sai kuma abu na ƙarshe, ki lallaso mijinki na nemi gafarar shi, da ma shi ne abin da ya kawo ni, Allah ya ba ku zaman lafiya." Na faɗi haka cikin matuƙar ƙarfin hali, don ni kaina na san yaudarar kaina kawai nake yi idan na ce ban damu ba, ta yaya ma zan ƙi damuwa? Mijina my first love yau ni da bakina nake kiran shi da na wata? Ji nake zuciyata kamar za ta tarwatse saboda wani irin zafi da take yi mini. Numfashi ta sauke ta ce. "Kin faɗa ne kawai amma na san tabbas kin damu, wannan kukan ma da kike yi na zallar kishi ne, da zan iya da sai na goge miki dukkan wani raɗaɗi da kike ji a cikin ranki, amma ba zan iya ba, sai dai kawai na ba ki haƙuri na kuma taya ki da addu'a. Fatana kawai Allah ya sa ba ki hallaka ba bayan rabuwar ku da Anas." Kuka na saka mai shashsheƙa na labarta mata komai da ya faru da ni, a gidan Idonnera da Sani da cin amanar da Maman Nasmah ta yi mini. Salati ta saka cikin jimantawa ta ce. "Kin ga abin da nake faɗa miki ko? Abin da nai ta jiye miki kenan da ma tun farko." Cikin karaya da rayuwar ma gabaɗaya na ce. "Na gani Naja, na ga aya ai, na YI WA KAINA, shi ya sa rayuwar auren gabaɗaya ta fice mini daga kai, na haƙura da aure har abada in sha Allah, zan zauna in yi sana'ata kawai da bautar Allah, har zuwa lokacin da zan koma gare shi." Tana hawaye ta ce. "In sha Allah za ki ji daɗi ƙawata, Ubangiji yana son bayinsa masu tuba, tunda har kika yi kuskure, kuma kika gane kin yi, kika yi nadama, to zai sauya miki da ma fi alkhairi in sha Allah." Ban ce komai ba saboda maganar ma da ƙyar nake yi, ga numfashina sai harharɗewa yake yi. Ta dinga ba ni baki, tare da nasihohi cikin kalaman kwantar da hankali. Na yi shiru kawai ina bin ɗakin da kallo, ba tare da ina fuskantar komai ba. So nake na tashi na koma gida kar dare ya mun, amma na san idan na miƙe zan iya faɗuwa, don daga zaunen da nake ma jiri nake ji. Jin dawowar su Anas ya sa Naja tashi ta fita, a ɗakin su Sultan ta same shi, wani kallo ta yi masa ta ce. "Ka taso za mu yi magana." Bai musa ba ya miƙe ya fito tsakar gida ta biyo bayansa. Hannunta ya kama ya ce. "Ga ni Madam." Cikin damuwa ta ce. "Don Allah ka je tana son ganin ka, tana son magana da kai, tana son ta nemi yafiyarka." Canza fuska ya yi ya ce. "Ni ba ta mun komai ba ki faɗa mata, don haka ba sai na je ba." Ƙwace hannunta ta yi, idanunta cike da ƙwalla ta ce. "Ban san ka da rashin tausayi ba Abban Sultan, ko don darajar ƴaƴan da ke tsakanin ku ka taimaka ka je ta gan ka ta samu sassauci a ranta, ba ka ga yadda ta koma ba ne, abun tausayi." Rufe idonsa ya yi na sakanni sannan ya buɗe ya ce. "Shikenan mu je." Murmushi ta saki cikin farinciki ta ce. "Na gode sosai." Yana share mata hawayen kuncinta ya ce. "Don ke zan je, don ki bar wannan damuwar da yi mini asarar hawayenki masu tsada da daraja." Wani murmushi ta yi ta ce. "Zuciyarka kuma don ita za ta je na sani." "Sai na fasa fa." Ya faɗa yana tsayawa a bakin ƙofar ɗakin da Hafsah take. Cikin marairacewa ta ce. "Sorry nawan." Da sauri na toshe kunnena, don wannan maganar tata gara a ɗiga mini dalma a kunnen da ita. Ina jin suka shigo, ban ji sallamarsa ba sai ƙamshin turarensa. Da sauri na ƙara runtse idona ina jin wata irin faɗuwar gaba, tare da laluben idon da zan iya kallon shi da shi. "Ka zauna mana, Maman Sultan ga shi nan ku yi magana." Ta faɗa tare da juyawa ta fice. Shiru muka yi a zaune har wasu mintuna suka shuɗe, na kasa ko da buɗe idona, sai ajiyar zuciya kawai nake saukewa. "Ba ki da abin cewa da ma kika saka a kira ni?" Na ji saukar muryarsa ya faɗi haka har cikin ƙwaƙwalwata. Bugun zuciyata ne ya ƙaru, na ji na dibibice kamar kamar wadda ta yi wa Sarki ƙarya. Still ban ce komai ba sai ƙamshinsa da na baza hanci ina shaƙa. Sanin halinsa ba ya son yana magana a yi shiru ya sa na buɗe idona a hankali, ba tare da na yi gigin ɗagowa ba na ce. "Ba abin cewa ne ban da shi ba, rashin sanin da kalmomin da zan yi amfani da su gurin neman yafiyarka da ba ka haƙuri ya sa na yi shiru, don Allah Abban Sultan ka yafe mini duk abubuwan da na aikata maka, na san ban kyauta maka ba, kuma ga shi haƙƙinka yana ta bi na, na kasa samun kwanciyar hankali da nutsuwa kwata-kwata tun bayan rabuwarmu." Na ƙarashe maganar ina sakin wani marayan kuka mara sauti. Muryarsa da alamun sassauci ya ce. "Shikenan komai ya wuce, na yafe miki, Ubangiji ya yafe mana gabaɗaya." Wani irin sanyi na ji yana ratsa zuciyata, ƙaƙƙafar ajiyar zuciya na sauke ina goge hawayen fuskata na ce. "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, ya ji ƙan mahaifa, ya raya zuri'a." Bai amsa ba sai idonsa da na ji yana yawo a jikina. So nake na kalle shi amma na kasa duk da yadda zuciyata take azalzalata, daurewa na yi na ɗago kaina na shiga bin shi da kallo, idan ba idanuna ne suke yi mini gizo ba ya ƙara haske da cika, ko kuma don na daɗe ban gan shi ba ne? Abin da yake raina da na kasa dannewa na furta na ce. "Ka yi aure Allah ya sanya alkhairi." Ya ce. "Amin." A taƙaice. Ina da maganganu da yawa a bakina da nake son yi masa amma na kasa, saboda kwarjininsa da ya cika ni, gabaɗaya sai na ga ya sauya mini. Muka kuma yin shiru a karo na biyu kamar wasu baƙin juna ko surukai. Yana latsa wayarsa cikin basarwa ya ce. "Ya jikin Kawu?" Na ce. "Da sauƙi Alhamdulillah." Ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi, kin ga cikin abin da nake tunanin ba zan yafe miki ba a duk laifukan da kika mun shi ne sanyawa da kika yi na nesanta da shi, har shekara guda cur ta wuce ban je na duba shi." Cikin jin daɗin yadda ya fara sakar mini fuska na ce. "Ka yi haƙuri don Allah, na san ni mai tarin laifuka ce a gare ka, amma shi ma wannan ɗin ka taimaka ka yafe mini." Ya ce. "Hmm, wasa nake yi miki, amma kin wuce komai a gurina har abada, ban san me ya duk da yadda nake jin zafin ki a cikin raina ina zama yanzu a gabanki sai komai ya sauya, a yadda na tsara idan na zo bai fi kalmomi biyu ko uku ne za su haɗa ni da ke ba, hakan ya sa na gane matsayinki da darajarki suna nan a cikin raina, kuma har abada ba za su goge ba. Kamar yadda ba zan taɓa son wata mace kamarki ba, ke na fara so, ke kika fara haifa mini ƴaƴa, har gobe ina kallon ki da wannan ƙimar, don haka ki saka a ranki kamar wani abu na rashin daɗi bai faru a tsakaninmu ba. Komai ya riga ya wuce ni a gurina." Daga haka ya miƙe ya fice. Na bi shi da kallo idona cike da ƙwalla, kyakkyawar zuciyarsa da rashin ɓoye-ɓoyensa yana matuƙar burge ni, na tuno yadda na ƙi yafewa Maman Nasmah, amma shi ina neman gafarar shi ya ce ya yafe mini. Lumshe idona na yi a hankali ina tuno rayuwarmu ta baya. A parlour ya tarar da Naja, ta tarɓe shi da sauri tare da faɗin. "Har kun gama?" Hararar ta ya yi ya ce. "Da kin tsaya ba ki gudu ba ai da kin gani da idonki kin huta tambaya." Yalwataccen murmushi ta yi ta ce. "Daga ganin fuskarka tsohuwar zuma ce ta tashi, yanzu sai ka faɗa mini lokacin da yanke a mayar da auren don na fara shiri." Bai ce komai ba ya wuce ta da niyyar shiga bedroom. Saurin shan gabansa ta yi ta ce. "Babu inda za ka je fa sai ka ba ni amsa." Ya ce. "Me kike so na ce ne don Allah?" "Ka amsa za ka mayar da matarka." "Bana jin zan iya hakan gaskiya." Ta ce. "Saboda me?" Ya ce. "Kawai." Gyara tsayuwar ta, ta yi ta ce. "Amma kana son ta ai har yanzu, kuma ita ma tana son ka, ga su Sultan, idan suka ci gaba da rayuwa tare da mahaifiyarsu za su yi farinciki sosai, ko don su ai ka dawo da ita." Ya ce. "Tabbas ina son Hafsah har yanzu, amma son ta ba zai saka na dawo da ita ba, musamman idan na tuna irin abubuwa marasa daɗin da ta aikata mini, ina jin zafi sosai kamar a lokacin da take mini. Kuma na riga na haƙura da ita, na fitar da ran ƙara ci gaba da rayuwa da ita, ina fatan kuma Ubangiji ya sa haka shi ya fiye mana alkhairi gabaɗaya." Cikin rashin jin daɗi ta ce. "Amma ai abubuwan da ta yi maka na kyautatawa sun ninka na rashin kyautatawar, ka duba su mana, ka bar tuna marasa daɗin." Ya ce. "In dai zan tuna masu daɗin su ma dole na tuna su, wai ke ba kya kishina ne kike ta nacin na mayar da ita?" "Kishi daban tausayi da cancanta daban, duk kishin ka da zan yi dole na ajiye shi a gefe, na saka ka yi abin da ya kamata, Hafsah ba ta da uwa, ba ta da uba, ba wa ba ƙani, daga Kawu sai ƴaƴanta kawai take da su a duniyar nan, sai kuma nagartaccen miji irinka." Ya ce. "Haka ne, amma a yanzu gaskiya ba zan iya auren mata biyu ba, saboda ɗawainiyar za ta yi mini yawa, ke kina haihuwa, ita ma idan ta zo haihuwa za ta yi, kuma kin san ni mutum ne mai son faranta wa iyalina da kyuatata musu, bana son su yi rayuwar takura ko rashin wani abu matuƙar Ubangiji ya hore mini. Saboda haka na yi miki alƙawari in dai Allah ya ƙara buɗa mini, na ji na yi wadatar da zan iya riƙe mata biyu to zan dawo da ita da yardar Allah." Ganin yadda ya yi maganar cikin serious ya sa jiki a sanyaye ta ce. "Tom shikenan, Ubangiji ya nufa, ya sa Lokacin a nan kusa

Chapter 23 of 24