ƙarya da dukkan ƙarfina. Galala ya dube ni ya ce. "Mene ne haka?" Cikin shaƙaƙƙiyar murya ina tarin kaɗan-kaɗan na ce. "Ulcerta ce ta tasar mini, da ma haka take yi time to time." Na ƙarasa maganar ina lumshe idona. Cikin takaici ya ce. "Me ya sa ba ki nemi magani ba? Ina nunbern my family doctor ɗin da na tura miki na ce idan ba ki da lafiya ki kira shi?" A wahalce kamar ciwon gaske na ce. "Bayan na baro ɗakinka bacci na yi ne, sai yanzu na tashi na yi wanka, rashin cin abinci ne." Bai ce komai ba ya samu gefen gado ya zauna. Sai da na gama sassauke numfarfashina sannan na tashi na zubo abinci, na sako spoon biyu. A gabansa na ajiye na ce. "Sakko mu ji." Fuskarsa babu fara'a ya ce. "Na ƙoshi." Karyar da murya na yi na ce. "Ka ƙara ci mana, yau ne fa farkon amarcinmu, ko ka taɓa ganin inda amarya ta ci abinci ita kaɗai ba tare da angonta ba?" Taɓe ya yi ya ce. "Ai ni ba irin sauran angwayen ba ne kin sani." Ƙara marairacewa na yi na ce. "Please, ko kaɗan ne ka ci." Tsaki ya ja ya sauko yana faɗin. "Ban taɓa auren macen da ta yi mini haka ba sai ke, anya kuwa haka kika bar ni?" Murmushi na yi na ce. "Babu abin da na yi maka, kawai ni ɗin ce ƴar baiwa." Ƙura mini jajayen idonsa ya yi, har lokacin spoon ɗin kawai ya riƙe bai kai abincin bakinsa ba, tabbacin akwai abin da yake nazari. Ban bari ko da wasa wani abu ya bayyana akan fuskata ba, ban kuma ƙara yi masa maganar ya ci abincin ba gudun kar ya yi wani tunanin daban. Sai ma ƙasa da na yi da kaina na ci gaba da cin abincina, cikin mamakin yadda har yanzu bai nemi wani abu ya suturce jikinsa ba, kuma hankalinsa kwance yake sha'aninsa, ya bar ni da aikin kau da kai. Sai day na kusa cinyewa ya yi three spoon. Hakan ya sa na tashi da sauri na zuba masa juice a glass cup, ya ɗauka ya ɗiɗɗike, na ƙara masa ya ƙara shanyewa. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, na tattara kayan na fice da shi ba tare da na sha drink ɗin ba. Na yi kusan five minutes kafin na dawo ɗakin, ina taku bugun zuciyata yana ƙaruwa da sauri da sauri saboda fargabar abin da zan je na tarar. Har na mayar da ƙofa na rufe ban kalli inda yake ba, kaina a ƙasa na ƙarasa bakin gadon. Ina neman taimakon Ubangiji a cikin raina na ɗago na kalle shi, kallon da na ga ya yi mini ne ya saka ni jin mummunar faɗuwar gaba. Kafin na yi magana na ga ya nuna ni da hannu tare da faɗin. "Keee! Me kika ba ni ne na ji kaina yana juyawa?" Daga yadda ya yi maganar na san maganin ya fara aiki kenan. Ban ce komai ba na ja baya na ɗauki wayata tare da tsayawa ina kallon shi yadda ya riƙe kansa yana yin wasu irin abubuwa. Jikina har rawa yake saboda rashin sanin takamaiman abin da nake ji, tsoron abin da zai biyo baya ko farincikin samun nasara ne ban sani ba? Kamar mai tafiya a kan ruwa haka na ja ƙafata na koma gabansa na ce. "Mansur." Ya ce. "Uhm." Tare ware jajayen idonsa a kaina.
"Ka san ni? Idan ka san ni wace ce ni a gurinka" Na tambaye shi ina nuna kaina.
Ya ce. "Eh mana, matata ce ke." Ina sauke ajiyar zuciya na ce. "So nake ka sake ni, ka ce na sake ki Hafsah har sau uku." Baya ya yi ya kwanta ya ce. "Ba zan faɗa ba ɗin, banza kawai." Ban karaya ba na ce. "Sai ka faɗa, saboda ni bana son ka, ba na ƙaunar zama da kai." Hannunsa riƙe da kansa ya ce. "Kaina zai tarwatse, ki cire mini abin da kika sa mun a cikinsa." Sai da na ɗauko takarda da biron da already na tanade su na miƙa masa na ce. "To sai ka yarda za ka rubuta duk abin da na ce maka, in ba haka ba, ba zan cire maka ba." Da sauri ya karɓa ya ce. "Me kike so na rubuta? Zan rubuta, in dai za ki cire mini wannan abun daga cikin jikina!"
"Saki, ka rubuta ni Mansur Ibrahim Idonnera na saki matata Hafsah har saki uku." Na faɗa cikin tarar numfashi. Kamar ɗan koyo haka ya riƙe pen ɗin ya rubuta ya cillo mini." Ban ɗauka ba na danna record cikin rawar jiki, muryata ɗauke da kukan ƙarya na ce. "Me ka rubuta? Ka faɗa da bakinka na ji."
"Na sake ki! Na sake ki! Na sake ki! Tunda kashe ni kike son yi, kin zuba mini tsutsa a kaina sai yawo take mun." Ya faɗa slowly tare da lumshe idonsa gabaɗaya. Wata irin ajiyar zuciya na sauke kamar zuciyar za ta daina aiki, na yi saved ɗin recorded da tun a gurin cewa na sake ki na uku da ya yi na yi stopping ɗinsa, ban bari sauran maganar tasa ta fito a ciki ba. Hannuna kamar ana kaɗa mazari saboda rawa na ɗauki takardar na linke na miƙe. Bin sa na yi da kallo, ya yi ɗaiɗai a kwance kamar gawa, ƙirjinsa da yake ɗagwa da sautin numfashinsa shi ya tabbatar mini a raye yake. Tamkar mai tafiya a kan wuta Saboda sauri haka na bar bedroom ɗin na fice parlour, a kan tiles na zube ina mayar da numfashi kamar wadda na sha tseren gudu. Tamkar a mafarki haka nake ganin faruwar al'amarin, ji na yi kaina yana juya mini, dafe shi na yi ina maimaita Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un a fili. Na rasa me ma zan yi? Barin gidan ko kuma jiran ya farko ya dawo cikin hayyacinsa? Wani irin tsoro da ban taɓa tsintar kaina a cikin irinsa ba ne ya lulluɓe ni, na fargabar kar ya mutu ko kuma wani abun ya same shi na shiga uku. Ban san lokacin da na ɗauka zaune a gurin ba kafin na tashi na koma ɗakin, a gurguje na ɗauki jakata da na gama haɗa duk wani abu mai muhimmanci nawa na fice, har lokacin yana nan yadda na bar shi.
Ɗakinsu Lami na je na zauna, suka bi ni da kallo amma babu halin tambaya. Ko ta kansu ban bi ba na kira Kareema a ruɗe na ce. "Na kammala komai fa, kuma successfully yadda muka tsara."
"Alhamdulillah! Na taya ki murna sosai wallahi, Ubangiji ya ba ki wani na gari." Ta faɗa cikin farinciki.
Ban amsa ba na ce. "Ni halin da na baro shi ne hankalina bai kwanta da shi ba, ina tsoron kar wani abu ya same shi." Ta ce. "Babu abin da zai faru, nan da mintuna za ki ga ya miƙe, sai da na tabbatar da ingancin ƙwayar sannan na siyo ta, wallahi Hafsah ba ƙaramin shiri na yi ba saboda kawai na taimake ki." Cikin ƴar nutsuwar da na fara samu na ce. "Shikenan, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi." Ta ce. "Amin, ki kwantar da hankalinki fa, na ji duk a ruɗe kike, bari na je na ɗauko Maman Hanif mu shigo tare." Na ce. "Kar ya gane haɗa baki fa muka yi abin ya shafe ku?" Murmushi ta yi mai sauti ta ce. "Kar ki damu, komai cikin dabara da wayo za mu yi, ke dai kawai da ya fito ki kira ni." Na ce. "Tom shikenan." Tare da katse wayar. Runtse idona na yi na dafe ƙirjina saboda bugun da yake yi mini kamar zai bar jikina. Addu'a kawai nake a cikin raina, don ban taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba a rayuwata. Na rasa sunan da zan kira wannan ƙaddararren auren da yin shi ya zamar mini bala'i, saki kuma yana ƙoƙarin saka mini ciwon zuciya saboda fargaba. Kamar na yi tsuntsuwa na gan ni a gidan Kawu haka nake ji.
Daf da Magriba na hango shi yana saukowa ta windown da na yaye labule saboda ganin wajen, lokaci ɗaya ajiyar zuciya da faɗuwar gaba suka yi mini rufdugu. Cikin azama na kira Kareema na sanar mata, ta ce suna bakin gate ga su nan shigowa. Ina zare ido kamar mara gaskiya na tashi na fita, bayan na ƙanƙame wayata da takardar sakin. A bakin ƙofa na tsaya a ɗarare ina kallon shi, tsaf da shi ya sha babbar riga, kamar mutumin ƙwarai. Wani mugun kallo ya jefe ni da shi ya ce. "Well-done! Ƴar matsiyata, sannun ki da ƙoƙarin ha'intata." Mannewa na yi a jikin ƙofar na fara rarraba ido ban ce komai ba. Yatsun hannunsa ya harɓa suka bayar da sautin daf-daf sannan ya ce. "Ba zan kula ki ba a nan a gaban masu aikin gidana, saboda kar mutuncina ya zube, amma za ki yi mini bayanin abin da kika saka mini da dalili anjima." Daga haka ya nufi ƙofar barin parlour'n, kafin ya ƙarasa doorbell ta fara ƙara, Laure da ke kitchen ta fito a guje ta je ta buɗe bayan ta yi mana sannu, babu wanda ya amsa mata.
Kareema ce ta fara shigowa, sai mijinta sai Maman Hanif. Kallo ɗaya na yi musu na sunkuyar da kaina ƙasa. Da fara'a ya tarɓe su kamar ba shi ya gama yi mini magana cikin hargagi da murtukewar fuska yanzu ba. Shi ya ba su gurin zama, suka gaisa cikin mutuntawa. Daga inda nake na gaishe su, Mijin Kareema yana duban shi ya ce. "Ɗazu da safe zan fita na ga shigowarka, da na dawo na tsaya na tambayi maigadi kai ne maigidan? Ya ce eh, yau ka dawo. Shi ne na ce idan na huta zan shigo mu gaisa, tunda na tare ba mu taɓa haɗuwa ba, kuma gidana ne na bayan naka." Murmushi Mansur ya yi ya ce. "Allah Sarki, ka kyauta kuwa, na gode sosai." Ya nuna Kareema ya ce. "Wannan ce mai ɗakin tawa, wannan kuma ta nan gidan jikin gidanka ce, mun fito muka haɗu da ita za ta shigo ita ma." Sheshsheƙar kukana ce ta hana shi maganar da ya buɗe baki zai yi, da sauri Maman Hanif ta ce. "Kamar kuka ko?" Kareema ta ce. "Eh, Aunty Amarya ce kuma take yi, lafiya?" Ta ƙarashe maganar idanunta a kaina. Cikin pretending ina cikin matsanancin tashin hankali na ɗora hannuna akai na ce. "Don Allah ku ba shi haƙuri, ni na ba shi ya ƙi haƙura, ku taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ku!" Cikin mamaki Maman Hanif ta ce. "A'a, me ya faru? Ba rakiya za ki yi masa ba da ma ganin kun da muka yi?" Girgiza kai na yi na tashi a haukace na cilla mata takardar hannuna na ce. "Duba ki gani, wai ya sake ni, kuma ban da kowa, ban da wani sauran gata sai shi, don darajar Allah ku ce masa ya mayar da ni. Ya ɗauki wani matakin a kaina kowanne ne zan jure amma ban da wannan, ba zan iya ɗauka ba, ya yi mini tsauri da yawa." A firgice ta miƙe ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Har saki uku!" Tashi ya yi shi ma ya ce. "What?" Tare da tsare ni da ido cikin wani irin yanayi. Sai a lokacin mijin Kareema ya yi magana ya ce. "Subhanallahi! Ashsha! Saki kuma? Alhaji me ya yi zafi?"
Karɓar takardar Kareema ta yi fuskarta ɗauke da tashin hankali ta ce. "Ko dai ba ki gani daidai ba ne Aunty Hafsah?"
"Zan fi kowa farinciki idan haka ne, shi ya sa na ba ku, ku duba ku gani ko idona ne yake yi mini gizo." Na faɗa ina ƙara rushewa da kuka.
Dafe kanta ta yi tana salati, Maman Hanif da sosai ruɗu ya bayyana a kan fuskarta ta ce. "I'm speechless!" Satar kallon Idonnera na yi na ga ko motsi ya kasa yi, alamun suman tsaye ya yi saboda tsananin mamaki. A hankali na sauke numfashi tare da ɗauke idona daga kansa, mijin Aunty Kareema da ya karɓi takardar ya duba ya ce. "Aikin gama ya riga da ya gama, har saki uku! Irin wanda Allah ba ya so, garin yaya haka ta faru Alhaji? Da na san abin da za mu tarar kenan da ba mu shigo ba." Dogon numfashi ya ja ya sauke, yana karɓar takardar tare da dubawa ya ce. "Ƙaddara ce kawai, ka san aure rai ne da shi, idan Ubangiji ya rubuta ya ƙare ko second ɗaya ba zai ƙara ba sai an rabu, ko ana so ko ba a so." Mijin Kareema ya ce. "Haka ne, Allah ya sa mu dace mu fi ƙarfin zuciyarmu, har an shiga sallar Magriba, mu za mu tafi Allah ya kiyaye gaba."
Zubewa na yi a ƙasa na ɗora hannu aka, ina kuka na ce. "Kar ku tafi ku bar ni ba ku saka ya mayar da ni ba don Allah." Cikin tausayawa Maman Hanif ta kama ni ta miƙar da ni tsaye, tana gyara mini hijabin jikina ta ce. "Ki yi haƙuri, ki yadda da ƙaddara, shi ne cikas imani." Ban ce komai ba na ci gaba da kukan da babu yadda za a yi mutum ya ce ba har cikin zuciyata yake ba. Sosai na hangi mamaki da ruɗu da shock a fuskar Alhaji Mansur, bi na kawai yake yi da wani irin kallo da na kasa gane ma'anarsa. Bai kuma magana ba ya juya ya fita bayan ya yar da takardar. Lallami da ban baki Maman Hanif tai ta mun kamar za ta yi kuka, sai haƙuri take ba ni, gami da yi mini nasiha. Kareema kuwa ba ta koma gida ba sai da ta tabbatar na bar unguwar, ko tsinke ban ɗauka ba daga ni sai jakata, ko kayan sakawa ban bi ta kansu ba, ni dai tunda burina ya cika ji nake kamar an tsunduma ni a cikin aljanna, sai godiya ga Allah kawai nake yi.
Kawu da ke riƙe da takardar sakin bayan na yi masa bayani ya ja gwauron numfashi ya ce. "Na rasa abin cewa saboda tsabar kiɗima, abin da zan ce kawai Ubangiji ya ba mu ikon cinye wannan jarrabar gabaɗayanmu, Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi, ya tsayar iya haka." Na ce. "Amin, Kawu har yanzu ba a kawo su Sultan ba ko?" Ya ce. "Hmm, sai haƙuri, jarrabawa ce, ki ta addu'a kawai kar ki gaza, fatanmu kawai Allah ya sa suna cikin kulawa da ƙoshin lafiya." Cike da kewa da ƙaunar ƴaƴana na ce. "Amin."
Sosai nake cikin farincikin yar da ƙwallon mangwaron da na yi na huta da ƙuda, ina jin Gwaggo tana ta ya da habaici amma ban bi ta kanta ba. Juyi na yi a kan tabarmar da nake kai ina ji na sakayau, gabaɗaya damuwar da ke danƙare a cikin raina ta tafi. Ɗanmitsitsin ɗakin da nake ciki a yanzu mai ɗauke da tarkace ya fi mini tangamemen da na baro mai cike da kayan alatu.
Ban san da bakin da zan gode wa Kareema ba, na wannan farar dabarar da ta samar mini. Ban taɓa zaton kuma abun zai zo da sauƙi haka ba, duk da na san addu'ar da na dage da ita ba dare ba rana ce ta sanya Ubangiji ya taimake ni ya ba ni nasara.
Wajen ƙarfe goma Kareema ta kira ni, bayan mun gaisa ta ce. "Ya kike je gida?" Na ce. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, na gode na gode, na rasa ma abin da zan ce miki saboda farinciki." Dariya ta yi ta ce. "Babu komai ai,kar ki damu, ni kaina nan murna nake yi miki ba kaɗan ba, barkanki, kin tsallake rijiya da baya, wai yaushe ma ya dawo ne?" Na ce. "Yau fa, ga shi cikin ikon Allah an yi komai an gama, gaskiya kina da basira sosai, ni ina zan yi tunanin yin haka? Kuma abin da ya ba ni mamaki yadda bai musa ba, ko record ɗin ma ban saka ba ya amince ya yi sakin." Ta ce. "Ai ya san dalili, ya riga ya gane ke kika haɗa komai, shi ya sa ba zai ce ƙala ba." A raunane na ce. "Allah ya sa kar ya ce zai yi mini wani abun da zai cutar da ni a matsayin ɗaukar fansa."
"In sha Allah babu abin da zai iya, ai kuma an riga an gama, wata mai tsautsayin kawai zai nema ya ƙara aura, ba ni labarin yadda lamarin yakasance, ya aka yi ya sha drink ɗin ne?"
Kwashe labarin komai na yi na ba ta.
Cikin dariya ta ce. "Amma ke ma fa kina da wayo, kin yi ƙoƙari sosai, ga kukan da kika yi kamar gaske, gaskiya za ki iya acting, kamar a Film fa." Dariya na yi na ce. "Mene ma ba zan ba, yadda nake gudun mutuwata haka nake gudun gidan nan, ba ki ji yadda nake ji na ba yanzu, farinciki mara misaltuwa." Ta ce. "Ma sha Allah, Maman Hanif ta ɗauka ƙin sakin kike da gaske, ta damu sosai." Na ce. "Allah Sarki baiwar Allah, mijinki fa? Ya san komai?" Ta ce. "Eh, na ɗan tsakura masa, shi ne ya ce mu je ba matsala, ya san me zai masa da ba zai kawo komai a ransa ba, ban san ya aka yi ya san yau ya dawo ba, amma na fi tunanin maigadi ya tambaya kamar yadda ya faɗa." Na ce. "To an gode, kun yi jihadi Allah ya ba da lada." Ta ce. "Amin ya hayyu ya ƙayyum, wannan miji naku ai ba na zama ba ne, Allah ya raba mu da zuri'armu da irinsu." Na ce. "Amin." Daga haka muka yi sallama ta ce da safe ma yi waya.
Daren wannan ranar shi ma ban runtsa ba, na dinga tunanin Anas da kulawar shi a gare ni, duk yadda na so kawar da tunanin amma na kasa. Na dinga tambayar kaina me kuma zai faru da ni a gaba? Wacce irin rayuwa zan shiga kuma? Zawarci ko kuma wani auren zan yi? Na yi auren kuɗin amma gara gidan talatan da na guda sau dubu a kansa, amma duk da haka har yanzu ina nan da burina, musamman idan na tuna maganganun Maman Hanif da ta ce masu kuɗin na gari suna nan da yawa, ko dan kar a ce na ci baya ba zan auri talaka ba a gaba, sai mai hali amma sai na zaɓa na darje da na ƙwarai. Kamar mafarki na yi na farka haka nake ganin aurena da Idonnera, na saka a raina ko a cikin masu kuɗin shi ne ba na gari ba, wataƙila a gaba na yi dace. Har Faisal da ban san lokacin da ya bar gidan ba sai da na tuno. Addu'ar fatan shiriya na yi musu na watsar da lamarinsu.
Washegari da safe Gwaggo Habi ta zo ta dinga yi mini faɗa kamar za ta dake ni, da kaicon barin da na yi mai kuɗi kamar Idonnera ya sake ni, ban ji nauyinta ba na ce ba shi da lafiya ne, don ko idda ma ban da ita a kaina. Da ta ji haka ne ta sauko, amma duk da haka sai ta ce ban da jaraba irin ta yaran zamani da na zauna a hakan ai, tunda ga kuɗi ba sai na yi haƙuri ba. Na ce shi ya sauwaƙe mini da kansa saboda kar ya dinga cutar da ni.
Wajen azhar sai ga direba da kayan sakawata niƙi-niƙi, wai Alhaji ne ya aiko shi da su. Hakan ya ƙara kwantar mini da hankali, na tabbatar ya haƙura kenan, na yi nasara.
Da daddare ina zaune na yi tagumi ina tunanin rayuwa da yadda ta zo mini kira ya shigo cikin wayata. Ko kallon ta ban yi bare na ɗauka, ƙishirwar son ganin ƴaƴana ita ta fi komai damu na a yanzu, na yi mamaki sosai da har yanzu Anas bai kawo su ba, ji nake kamar na tafi ƙauyen nasu na je na gano su. Gefe guda kuma ina tunanin inda Maman Nasmah ta shiga da ta yi wannan ɓatan dabon, ba ƙaramin son mu haɗu na ba ta labarin abubuwan da suke faruwa nake yi ba. Ganin an ƙi daina kiran ya sa na janyo wayar na duba, baƙuwar number ce, hakan ya sa na ɗan yi jim kafin na ɗaga bakina ɗauke da sallama. Muryar Alhaji Mansur na ji ba tare da ya amsa ba yana faɗin. "Sannu ƴar matsiyata, kin yi ƙoƙari fa sosai da tarkon da kika haɗa mini, ga shi kin yi nasara ya kama ni. Na daɗe ina mamakin yadda aka yi kika iya ƙirƙirar wannan dabarar, to abin da na kira faɗa miki shi ne, har yanzu a tafin hannuna kike, kuma tanadin uƙubar rayuwar da na tanadar miki da ƙuncin da zan saka ki a ciki sai kin ji gara zaman gidan nawa da kike gudu sau miliyan da shi, don haka ki shirya, sai kin yi nadama da danasanin rainin hankalin da kika yi mini. Sai na wulaƙanta rayuwarki na ɗaiɗaita ta, nan ba da jimawa za ki yi bankwana da farinciki na har abada. Ba ki da kowa ba ki da komai, bare ki samu mai tsaya miki, za ki gane kin tsokano tsuliyar dodo. Kuma ki sani duk inda za ki shiga a faɗin duniyar nan ba za ki taɓa tsere mini ba, ko'ina sai na saka an ƙwaƙulo mini ke. Bayan na gama illata ki na saka a bazar da ke, kin fi kowa sanin ba ki da wanda zai iya ja da ni a kaf danginku da mutanen da kika sani, bare ki yi tunanin kai ni ƙara." Ya ja tsaki cikin tsananin ɓacin rai sannan ya ci gaba da faɗin. "Ba a taɓa raina mini hankali irin wannan ba, amma kanki kika yi wa ba ni ba, don ba zan taɓa bari ki ƙara wani jin dadi ba a rayuwarki har abada!" Daga haka ya kashe wayar........✍️
_*ALHAMDULILLAH! Sai kuma Ubangiji ya kai mu bayan Sallah zan ci gaba, Allah ya nuna mana watan Ramadan lafiya, ya karɓi dukkan ibadunmu, ya sa mu yi su lafiya mu gama lafiya.*_🙏🥰❤️
*Zeey Kumurya*✍️
[5/11, 12:10 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*28*
Ban san me ya faru da ni ba, ban san adadin ruɗun da na tsinci kaina a ciki ba, sai ji kawai ji na yi wayar ta faɗi daga hannuna, alamun komai nawa ya tsaya kenan, jikina ya yi lagwab tamkar babu sauran jini da ruwan da ya rage a cikinsa. Na daɗe ina sassauke numfarfashin tsantsar razani kafin na dawo cikin nutsuwata.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allah ka shiga tsakani na da wannan bawan naka, Allah kana gani ba zaluntar shi na yi ba, mafita na sanar wa kaina, Allah kar ba shi ikon cutar da ni." Na faɗa a fili cikin hawaye. Sosai tsoron da ban san ya zan fasalta shi ba ya cika mini zuciya. Kareema ce ta faɗo mini a rai, da sauri na ɗauki wayata na kira ta. Bayan ta ɗaga na labarta mata komai da yake faruwa. Cikin son kwantar mini da hankali ta ce. "Kar ki wani ɗaga hankalinki Aunty Hafsy, na san duk abin da ya faɗa zai iya, amma barazana ce kawai babu abin da ya isa ya yi miki in sha Allah, ki kwantar da hankalinki, ki ta addu'a kina kai wa Allah kukanki kawai, ki haɗa shi da Ubangiji shi kaɗai zai yi miki maganinsa." Cikin jin daɗin shawararta na ce. "In sha Allah, na gode sosai."
Washegari da safe Inna Habi ta zo, lokacin ina kwance ina sana'ar tawa ta tunani. Fita na yi muka gaisa a gurin Kawu, tana duban shi ta ce. "Ni fa tafiya na zo yi da Hafsah gidana, don na lura a nan sai dai ta yi ta wunin ɗaki damuwa tana ta cin ta a rai. A can kuwa islamiyya zan saka ta, ta matan aure, ta dinga fita tana jin daɗi a ranta." Kawu ya ce. "Ba zan hana ba Yaya Habi, amma a saka mata ido da kula sosai akan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 24