Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi kaɗai zai iya yi mini shi duk duniyar nan.' Wani daga cikinsu ya ce. "Ƙwarai Hajiya, mu da shi ai duk ɗaya ne." Idanunta a kan shagon nasu da ba ta iya hango cikinsa sosai ta ce. "Yanzu dai yana nan ko ba ya nan? Idan aiki ne ba ku da damuwa, gabaɗaya tare za ku yi." Washe bakinsu da ya bushe raƙau saboda azumi suka yi suka ce. "Ƙarasa ciki ki tambayi Oga." Ba ta kuma magana ba ta tafi a ɗokance. Bayan sun gaisa ta tambaye shi Anas ya ce. "Ayya, Malam Anas mai mutane, duk wanda ya yi wa aiki sai ya dawo, ga shi kuma kin tari gurbi Hajiya, don ɗazun nan ya bar nan, ya zo yi mana sallama tare da sanar mana ya bar aiki." A ɗan rikice ta ce. "Subhanallah! Saboda me?" Cikin jimami ya ce. "Ban sani ba gaskiya, amma ya ce mana wani ƙwaƙƙwaran dalili ne ya saka mu yi haƙuri." Da sauri ta ce. "To yanzu don Allah a ina zan same shi?" Ya ce. "Ban sani ba wallahi, don ya ce mana zai bar garin ne gabaɗaya." A ruɗe Maman Nasmah ta ce. "Innalillahi! To ya tafi ina?" Cikin mamakin yadda ta rikice Oga ya ce. "Lafiya dai ko Hajiya? Ina fata ba kuɗin aiki kuka biya shi ba kuma ya tafi da su." Girgiza kai kawai ta yi amma ta gaza cewa komai. Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin. "Yawwa, don na san Anas ba halinsa ba ne wannan, ba a taɓa kama shi da abu makamancin haka ba." Tattaro dukkanin sauran nutsuwa da dauriyar da suke ƙoƙarin tarwatse mata ta yi ta ce. "To zan iya samun nunbern wayarsa?" Ya ce. "A'a, ba ma shi da waya yanzu gaskiya, ta da kuma ba ta aiki." Ta ce. "Shikenan, na gode sosai Malam, sai anjima." Ba ta jira cewar shi ba ta juya ta fita a rikice. Oga ya bi ta da kallo, haka kawai ya ji matar ba ta yi masa ba, yana da nunbern Anas, ya ce mata babu ne saboda bai san me za ta yi da ita ba. Tana ji mutanen bakin shagon suna cewa. "Hajiya yaushe za a yi miki aikin?" Amma ta yi banza ta wuce fuuu, ta rasa me ya sa ba ta da sa'a akan Anas, duk lokacin da take murnar abu ya zo daf sai ya koma baya, masu yi mata aiki a kansa sun ce ba ƙaramar wahala suke sha ba, da ƙyar suke samun information a kansa. Ita ba ta taɓa tunanin talaka zai yi wahalar gani haka ba, ta ɗauka available suke a kodayaushe kamar ledar pure water. Kamar tai ta zunduma ihu ko za ta ji daɗi haka take ji, ga shi ƙarin damuwarta bayan ta gama wannan fighting ɗin akwai wani a gaba, na neman yardarsa da kuma na rabuwa da mijinta. Jiki a saɓule na ƙarasa parlourn na zauna ina ƙare wa baƙon da aka ce na yi kallo shi da yaran gabansa. Yana bi na da wani irin shu'umin kallo ya ce. "Sannu da fitowa ranki ya daɗe." Na ce. "Yawwa sannu, an ce kana nema na." Bai ba ni amsa ba sai da ya tura yaran waje sannan ya ce. "Haka ne, gurinki na zo." Gyara zama na yi na ce. "Sai dai ban gane ka ba." "Da ma ba ki san ni ba bare ki gane ni babbar mace." Ya yi maganar yana zunkuɗowa daga kan kujerar da yake. Ban ce komai ba na bi shi da ido kawai, hakan ya sa ya ci gaba da faɗin. "Sunana Faisal, mijinki Alh. Mansur shi ya turo ni don na ɗeɓe miki kewa, na taho da yara ne saboda na ɗauke hankalin ma'aikatan gidan nan daga zargin wani abu, zan zauna a matsayin ni ɗan'uwanki na kawo miki yara ziyara su yi Sallah a nan." Cikin rashin fahimta na ce. "Ban gane me kake nufi ba, ɗebe kewa kamar ya?" Wani munafukin murmushi ya yi tare da tashi ya dawo hannun kujerar da nake, cike da duniyanci ya ce. "Haba Madam, sai na yi gwari-gwari sannan za ki gane? Mu huta mu mori junanmu a bed nake nufi." Ya ƙarashe maganar tare da ɗage mini gira gami da kashe ido. Nemar komai nawa da zan iya sarrafa kaina na yi saboda ɗimaucewa, sai bayan wasu sakanni na fara dawowa daidai, idanuna ƙyam a kansa na ce. "Idan na fahimce ka zina kake nufin mu dinga aikatawa?" Ya ce. "Yeah ƴar gari." A fusace na miƙe ina jin wani abu ya tokare mini ƙirji, nuna shi na yi cikin ƙaraji na ce. "Ni ba ƴar'iska mahaukaciya ba ce da zan aikata zina a ɗakin aurena, kuma tsabar dabbanci da hauka a cikin watan Ramadan, da azumi a bakunanmu kake furta wannan asararren zancen, to ka tattara ka bar mini gida kamar yadda ka shigo, ba da ni za a yi wannan jahilcin ba." Miƙewa ya yi ya ce. "Calm down Bab, ba yanzu za mu yi ba da ma ai, sai an sha ruwa." Cikin hargagi na ce. "Ko haɗiye shi za a yi ba sha ba sai ka bar gidan nan, get out!" Na ƙarashe maganar ina nuna masa ƙofa. Murmushi ya yi ya ce. "Abin duk ba na zafi ba ne babbar yarinya, wannan harkar mun saba yin ta da sauran matan Alhaji, tunda shi ba lafiya ce da shi ba sai ya kawo muku irinmu ku dinga rage zafi, saboda kar ya cutar da ku, kuma ko da kin samu ciki kin haihu zai yi accepting abin da kika haifa a matsayin ɗan cikinsa, zai yi masa hidima ya yi masa komai, ƙarshe idan ya mutu ma har gadonsa zai ci, babu wanda zai sani." Ban iya kuma magana ba saboda yadda zuciyata take tafarfasa na fice daga parlour'n ina haɗa hanya, ikon Allah ne ya kai ni parlona, na faɗa kan kujera da ruf da ciki, hannuna riƙe da kaina da nake jin yana mun wani irin tururi kamar zai tarwatse. Wannan wacce irin ƙazamar rayuwa ce mai cike da jagwala-jagwala, a ce mijinka na sunna shi zai turo maka gwarton da za ku dinga lalata a cikin gidansa? Har gwarton yana proud da ko ka samu ciki zai riƙe shi a matsayin ɗansa. Na rasa sunan da zan kira wannan ƙaddararren auren nawa, rayuwar jin daɗi da watayawar da nake so ga ta nan na samu, amma farinciki da walwala gabaɗaya sun ƙaurace mini kamar yadda rai yake barin gangar jiki, ba kuma na ganin alamar ko burbuɗin dawowar su, matuƙar ba sakin raina zan yi na amince da rayuwar da na saka mata sunan JIN DAƊI A DUNIYA, SHAN WUYA A LAHIRA ba. Faisal kuwa da kallo ya bi Hafsah, bayan ta fice ya taɓe baki tare da komawa ya zauna. Wayarsa ya ɗauko daga aljihun gaban rigarsa ya fara ƙoƙarin kiran Maman Nasmah. Wadda ita ta turo shi, bayan ta gama tsara masa duk abubuwan da zai ce wa Hafsah. Amma saboda kar sunanta ya fito sai ta ce masa ya ce mai gidan ne ya turo shi, don ta san Hafsah za ta yarda da hakan tunda ta san halin mijinta, kuma babu wata hanya da za ta same shi nan kusa bare ta yi masa magana akan lamarin, kafin ya dawo garin kuma ta san ta gama samun abin da take nema. Faisal ɗaya daga cikin yaran da take hulɗa da su ne. Tana zaune tunanin Anas ya addabe ta kiran Faisal ya shigo wayarta. Tsaki ta ja ta ɗauki wayar da niyyar yin reject sai ta ga shi ne, da sauri ta ɗaga ta kara a kunnenta. Kafin ta yi magana ya riga ta da faɗin. "Madam an samu matsala fa." Ta ce. "Matsalar me kuma?" Ya ce. "Ta ƙi amincewa fa, kuma a yanayinta gaskiya za ta yi wuyar sha'ani." Ɓata fuska ta yi ta ce. "Na sani da ma, duk da wawancinta tana da tsatsttsauran ra'ayi akan addini, amma a hakan za ka shawo kanta, ina ƙwarewarka a sace zuciyar mace da yaudara suke? Ko mu kaɗai kake yi wa?" Dariya ya yi ya ce. "Kin san wargi ma guri yake samu, ku da ita da banbanci ai, duk iskancin mutum sai ya samu guri yake iya baje shi." Ta ce. "Na ji, ni dai ka samu ka yi duk yadda za ka yi ko da sau ɗaya ne ta amince." Da sauri ya ce. "Dole na ma ai, don na matuƙar yabawa da ita." Taɓe baki ta yi ta ce. "Ta nan ka fi kauri da ma, saura ka je garin azarɓaɓi ka manta da abin da na saka ka." Ya ce. "Ba zan taɓa mantawa ba, jira nake dare ya yi na saita, da komai ya kammala kawai sai dai ki ga na tura miki." "Good, fatan nasara." Ya ce. "Ki saka a ranki ta tabbata, kamar an yi an gama." Ta ce. "Allah ya sa." Tare ka katse kiran. Numfashi ta sauke cikin takaici, ga rashin samun Anas ga Hafsah ma tana ƙoƙarin ba ta matsala. A yanzu burikanta biyu ne, na farko ta mallaki Anas, na biyu kuma ta ɓata Hafsah a idonsa, ya daina ganin darajarta ko kaɗan ya kuma ƙara tsanar ta, ta yadda ko da ba ta da aure a gaba ba zai yi gigin mayar da ita ba. Duk da a yadda suka yi alƙawari da Mansur duk rintsi duk wuya ba zai rabu da Hafsah ba, sai dai in mutuwa ya yi, wanda ba ta fatan hakan nan kusa. Sai da na yi kwana uku ko ƙofar ɗakina ba na takawa, sai dai masu aiki su kawo mini komai su dawo su ɗauke. Duk da uban sintirin aiken da Faisal yake yi, ƙarshe da na gaji sai na buga wa masu aikin da yake aikowa warning, na ce kar su ƙara dawo mini da zancen shi. Ban yi yunƙurin korar shi daga gidan ba tunda maigidan ya san da zamansa, na bar shi ya gaji don karan kansa ya ƙara mai. Yau Sallah saura kwana biyar, ina kwance a ɗaki na tasa uban tsadaddun kayan sakawana a gaba ina kallo, sarƙoƙin gold's ɗin da wata mata ta kawo jiya na ɗaga, ta ce Alhaji ne ya turo ta, ta kawo mini na yi kwalliyar Sallah da su, a gurinta yake siya wa matansa kodayaushe. Ko kaɗan kayan ba su burge ni ba, ajiye ta na yi ina girgiza kai. Duk da uban kayan lefen da ya ba ni na siya sai da ya aiko mini da kayan Sallah, tunda na jibge su ma ko kuma kallon su ban yi ba sai yau na kwaso na duba. Ajiye sarƙoƙin na yi a kan kayan na ɗauki wayata na shiga Camera, Lokacin da nake ta fata da burin zuwan shi ga shi ya zo mun, mafarkina ya cika na ganin na tara abu na bajinta irin haka na ɗauka na tura a group ɗinmu na ce ga shi ni ma mijina ya siya mini kamar yadda kowa yake yi, amma na rasa me ya sa bana farinciki kamar su, su da walwala da nishaɗi a cikin muryoyinsu a lokacin da suka videon, alamun suna cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Dangwarar da wayar na yi ina jin wani irin ƙunci a cikin zuciyata, so nake na fita daga gidan nan ko na awanni ne na sha iska, amma da na ce wa Kawu zan je na gaishe shi hanawa ya yi, ya ce na bari sai Sallah, ya yi wuri na fara fita yanzu. A hankali na ɗago kaina jin ana knocking, ban motsa ba na ba da umarnin shigowa. Laraba ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, na amsa kamar mara lafiya. Jug ɗin hannunta da ke cike da kunun aya ta ajiye a gabana tare da faɗin. "Ga shi Hajiya na kammala." Na ce. "Sannu." Tare da janyo shi a zalamance na bude, ko tsiyayawa ban yi a cup ba na fara sha, kasancewar na sha azumi sai yau na yi tsarki na ɗora ya ba ni wahala, shi ya sa na saka a haɗa mini kunun ayar mai sanyi don na sanyaya maƙoshina. Ajiyar zuciya na sauke bayan na dire jug ɗin, ina jin yadda sanyin ke ratsa ƙirjina. Bayan wasu mintuna ina son na tashi na yi Sallah amma na ji kasa, jikina ya yi mun wani iri kamar ba nawa ba, kwanciya na yi akan kayan gabana saboda yadda nake jin kamar iska za ta ɗaga ni daga zaunen da nake saboda rashin ƙwari, ko ɗanyatsana kasa motsawa na yi, ni ba mai bacci ba, ni ba matacciya ko sumammiya ba. Fuskar Faisal ɗauke da murmushin nasara ya kira Maman Nasmah, tana ɗagawa ya ce. "Yes! Na ci kuɗina." Cikin murna ta ce. "An yi nasara ne?" Ya ce. "Eh, yanzu mai aikin ta gama faɗa mini har ta sha drink ɗin, maganin da na ba ta, ta zuba mata kuma sha yanzu magani yanzu ne, na san tuni ya fara aiki, nawa aikin ne kawai ya rage." "Amma ba ya saka bacci dai ko? Don na fi son a ce idanunta biyu tar." Ya ce. "Ba ya sakawa, kawai jikinta ne zai yi weak, ba za ta iya komai ba sai yadda aka yi da ita." Ta ce. "Yawwa, haka nake so, ka yi sauri ka je, sai na ji feedback, saura kuma garin zumuɗi ka manta da yin videon, don na ji duk ka wani gigice." Dariyar ƙeta ya yi ya ce. "Kar ki ga liafina, Beb ɗin ce ta haɗu ta ko'ina, za a amfana da ita." Tsaki ta ja cikin kishi ta ce. "Ni dai ga abin da na ce maka." Daga haka ta katse kiran. Da murmushi a kan fuskarsa ya nufi sama inda Hafsah take, wanda already Laraba ta riga ta buɗe masa kowacce ƙofa da za ta sada shi da ciki, tutturawa kawai zai yi ya shige.......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 1:44 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGH PENS* (FREE BATCH) *25.* Laure da ke laɓe a bayan labule ta yi saurin barin parlour'n ta bi bayan shi cikin tashin hankali, duk da ba ta san me yake shirin aikatawa ba amma ta san ba alkhairi ba ne. Tun lokacin da ta ga sun keɓe suna ƙusƙus shi da Laraba ta saka musu ido, hakan ya sa yanzu tana ganin Laraban za ta shiga parlour'n da ya mayar da shi kamar nasa ta bi bayanta ba tare da sun ankara da ita ba. A ruɗe ta zagaya ta ƙofar kitchen da gudu ta riga shi hawa upstairs na biyu, tana rufe ƙofa tana jiyo takun tafiyarsa yana hawowa, hakan ya sa ta ƙara ƙarfin gudun nata, da haki ta shiga bedroom ɗin da Hafsah take ta fara laluben key, a kan drawer ta hango shi, da sauri ta ɗauka har tana tuntuɓe ta kulle ƙofar ta bar shi a jiki. Dogon numfashi ta ja ta sauke tare da sakin ajiyar zuciya, idanunta akan Hafsah da ba ta da maraba da matacciya. Matar da ba ta taɓa wulaƙanta su ko yi musu wani cin mutunci ba kamar yadda wasu matan suke yi idan ana aiki a ƙarƙarshinsu, ta sakar musu komai na gidan su yi yadda suke so, ko dan wannan ba za ta taɓa bari a cutar da ita ba. Tana jin shi yana ta murɗa handle ɗin ɗakin. Cikin mamaki Faisal yake tura ƙofar kamar zai karyata. Ganin ko motsi ba ta yi ba ya ja tsaki tare da sauka ƙasa a fusace ya fara ƙwala wa Laraba kira. A gigice ta fito tana waige-waige ta ce. "Ga ni yallaɓai." Kamar zai rufe ta da duka ya ce. "Kika ce duk kin buɗe ƙofofin? Ya aka yi kuma na je na ji ɗakin nata a rufe?" Da sauri ta ce. "Wallahi na buɗe, sai dai ko ba ɗakin da take ciki ka je ba." Tsaki ya ƙara ja ya ce. "Ba shi ne na farko ba?" Ta ce. "Shi ne." Taune lip ɗinsa ya yi tare da yamutsa fuska, kamar yay ta naushin iska haka yake ji saboda takaici, a ƙufule ya ce. "Ko dai ba ki zuba mata maganin ba ne ƙarya kika yi mini?" A tsorace ta ce. "Na zuba mata, kuma ta sha, a yadda na baro ta ma ya fara aiki a jikinta." Harara ya zabga mata ya ce. "Dalla wuce ki ba ni guri, sakarya kawai." Baki ta zunɓura ta bar masa parlour'n. Yana huci ya ɗauko wayarsa ya kira Maman Nasmah ya sanar mata halin da ake ciki. Cikin baƙinciki ta ce. "Me ya sa haka ne wai? Me ya sa nasara ta yi mini ƙaura a game da Hafsah? Ka koma ka saka ido sosai, don dole akwai abin da ya faru, ba haka kawai aka samu akasi ba." Cikin ƙunar zucin ganin samu da rashin da ya yi ya ce. "Na fi ki takaicin abun nan wallahi, don ƙofar ɗakin aka rufe da key ta ciki, kin ga babu yadda za a yi ta buɗu ta waje kenan, sai dai in ɓalla ta za a yi." Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ba fa zan karaya ba, sai aikin nan ya yiyu ko ta halin yaya, ka samo wata hanyar da za mu cimma burin mu kafin Sallah, don maigidan za su iya dawowa a kowane lokaci, gara ka yi abin da za ka yi ka tattara ka bar gidan." Ya ce. "In sha Allah za mu yi nasara, don ba zan taɓa bari duk zaman da na yi a gidan nan ya tashi a banza ba." Ba ta ce komai ba ta kashe wayar don takaici. Tun ina ganin dishi-dishi har na daina ganin komai, ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai can cikin dare na farka a firgice. Salati na rafka tare da tashi zaune, hakan ya farkar da Laure da ke zaune a ƙasa tana bacci. Da mamaki na dube ta bayan na latsa wayata na ga lokaci na ce. "Laure?" Ta ce. "Na'am Hajiya." Numfashi na sauke ina jin jikina wani irin lagwab kamar an yi mini duka, ga kaina da ke sara mini. Ina rarraba ido bayan na gama tuno abin da ya faru kafin hankalina ya gushe, na ce. "Lafiya? Me kike yi a nan a wannan daren? Me ya same ni?" A raunane ta ce. "Ban sani ba Hajiya, kawai hakan da na yi shi ne kariya a gare ki, ki yi haƙuri don ban san yadda zan yi miki bayani ki gane ba." "Kariyar me?" Na tambaya a gigice. Shiru ta yi ba ta ce komai ba, a tsawace na ce. "Ki yi mini bayanin mana, ina sauraren ki." Kanta a ƙasa ta ce. "Wannan baƙon da ya ce shi ƙaninki ne, shi ne ya faki idonmu ya zuba miki abu a cikin kunun ayar da Laraba ta kawo miki, bai san na gan shi ba, a lokacin na rasa mafita, sai bayan da kika sha na samu na shigo, na tarar da ke cikin wani irin yanayi, duk da na ruɗe amma ban fita ba, don na fuskanci ɗakin yake son shigowa ya yi wani abun." Jijjiga kai na shiga yi cikin matuƙar mamaki, don na gane nufin Faisal a kaina. A tsorace kamar za ta yi kuka ta ce. "Amma don Allah Hajiya kar ki ce ni na faɗa miki." Cikin ƙaunar yarinya na tashi na koma kusa da ita na kama hannunta na ce. "Ko zancen ba zan yi masa ba, bare sunanki ya fito a ciki, kawai zan yi takatsantsan da shi daga yanzu, na gode sosai, na kuma ji daɗin taimako na da kika yi." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Babu komai Hajiya." Jikina fayau na tashi ina tunanin mafita, babu abin da zan yi wa Faisal face na haɗa shi da Allah kawai, shi zai yi mini maganinsa. Tun daga ranar na koma yin duk wani abu da zan ci da kaina, ina gamawa na tattara na kai ɗaki na kulle. Saura kwana biyu sallah na kira mai kitso da ƙunshi ta yi mini, ranar sallah na shirya driver ya kai ni masallaci na yi idi. Kamar kar na baro masallacin, saboda ganin hada-hadar mutane ba ƙaramin sanyaya mini zuciya ya yi ba. Ina komawa gida aka aiko wani almajiri ya kawo mini abincin sallah ya ce ga shi daga maƙota. Na karɓa na ce an gode bayan ya yi mini kwatancen gidan. Tsabar halin da nake ciki ma na manta da ana yin wani abincin salla, don a kwanakin nan sosai tunanin su Sultan da kewar su ya addabi zuciyata, hakan ya sa na ƙara lalacewa duk na rame. Washegari na shirya na je na gaishe da Kawu, daga nan na tafi gidan Inna Habi na yini, don ba ƙaramin ɗasawa muke yi yanzu da ita ba. Ta dinga nan-nan da ni tana cewa ciki ne da ni, ramar da na yi daga gani ta laulayi ce, ni dai na bi ta da ido kawai, a raina ina cewa. 'Ba ki san dawar garin ba ne.' Sai murna take na kusa haihuwa a gidan mai kuɗi. Sai bayan isha'i na koma gida, kamar kar na tafi, don kwana na so yi Inna Habi ta hana ni, duk da na ce mata ba ya gari ya yi tafiya. Rayuwa ta ci gaba da juyin wainar ƴar koyo da ni a gidan Alhaji Mansur Idonnera, na ja watanni huɗu amma babu shi babu dalilin shi, ba waya ba chat, sai dai aiken kuɗi kawai. Ban san haka nake da buƙatar namiji da kulawar shi ba sai a wannan lokacin, ga shi babu wanda nake da shi da zan faɗa masa damuwata ya ba ni shawara, Maman Nasmah har sau biyu ina zuwa unguwarsu ina bulayi amma ban yi dacen samun gidanta ba. Har a group ɗinmu na yi cikiyarta, su ma suka ce neman ta suke yi. Ranar wata Lahadi ina zaune na tasa TV a gaba da sunan kallo, amma babu abin da nake fahimta wanda ake yi a ciki. Knocking aka yi na bayar da umarnin shigowa, Laura ce. Cikin ladabi ta ce. "Hajiya kin yi baƙuwa." Da mamaki na ce. "Baƙuwa kuma?" Don tunda na zo gidan babu wanda ya taɓa zuwa, ko nawa ko nasa. Cikin fatan ya kasance Maman Nasmah ce na ce. "Je ki shigo da ita." Tare suka dawo da matar, na bi ta da kallo don ban san ta ba. Fuskarta ɗauke da fara'a ta ce. "Sannu da hutawa." Murmushi na yi na ce. "Yawwa, Bismillah ki zauna mana." Tare da ba wa Laure umarnin ta kawo mata abin taɓi. Bayan mun gaisa ta ce. "Kin ga baƙuwar fuska ko? Maƙociyarki ce, tun lokacin da aka kawo ki nake ta zuba idon ganin amarya za ta shigo a gaisa na ji shiru, yau dai na cewa maigidan bari na shigo mu gaisa, haƙƙin maƙota ba a rayu ba a san juna ba." Na ce. "Allah Sarki, kin kuwa kyauta, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ina ta son na shishshiga ɗin kuma Allah ne bai nufa ba." Ta ce. "Babu komai, ni gani ai na zo." Murmushi na yi na ce. "Kin samu ladan, Allah ya bar zumunci." Ta ce. "Amin." Da na tambaye ta ina ne gidan nata, ta yi mini kwatance sai na ga ashe ita ta aiko mini da abincin Sallah kwanaki. Mun taɓa hira da ita, hakan ya sa na ji daɗi kamar an rage mini damuwar da take damu na. Washegari sai ta ƙara dawowa tare da yaranta masu kyau mace da namiji, har ta bar su suka ɗan jima a gurina. Yara masu da hankali da shiga rai. Bayan kwana biyu ta ƙara zuwa muka gaisa, ta ce amma tunda na ƙi zuwa ba za ta ƙara zuwa ba ita ma. Hakan ya sa ni ma na fara shigar mata. A hankali a hankali muka fara sabawa da ita, tana da kirki sosai, ga ta da addini da sanin darajar ɗan'adam.  Yau ta zo muna cikin hira ta dube ni ta ce. "Aunty Amarya ni kuwa ina so na yi miki wata

Chapter 15 of 24