a gidana sai na ji duk na ƙuntata, kamar ba na samun wadataccen nunfashi ma tsabar ƙanƙantar gidan.
Sai wajen goma ya shigo gidan shi da su Sultan, bai kula ni ba, ni ma ko kallon shi ban yi ba. Na ɗauki abincin da na taho da shi muka ci tare da ƴaƴana, muna ci suna labarin gidan da suka je, bayan na gama shan uwar tambayar ina na je na tafi na bar su.
Ni kaɗai na kwanta a ɗakina don Anas ko parlour'n bai shigo ba, na gane nufin shi, so yake na je na ba shi haƙuri, ni kuma abin da bai isa ba kenan a yanzu, don ba zan iya fama da talauci da faɗin rai ba.
Kusan raba dare muka yi muna hira da Maman Nasmah, ta ba ni labarin abubuwan da aka tattauna bayan na taho, ni kuma na faɗa mata yadda muka kasance da Abban Sultan. Ta ce ko za mu shekara a haka kar na sake na ba shi haƙuri, don ita mijinta tunda suke ba ta taɓa ba shi haƙuri don ta yi masa laifi ba, ko ita ce mara gaskiya shi yake bin ta yana lallaɓa ta. Ina ta son na ba ta labarin biyo nin da mijin Aunty Billy ya yi amma har ta sauka daga online ban faɗa mata ba. Yau ma sai na ji na kasa bacci, saboda yadda gadona tun na aure yake ta ƙarar tsufa, ga katifar duk ta lotse, ta wani gurin har layi-layin katakon karagar gadon ana jiyowa. Luntsumemen gadon da na kwana a kai jiya kawai nake tunowa, na san da shi ne da tuni bacci ya ɗauke ni yadda na kwaso gajiyar nan. Tashi zaune na yi ina firfita saboda zafin da ya addabe ni da sauron da yake ta mun kuwwa a kunne duk da na ɗaura net. Na san in dai ba nepa aka kawo ba, ba zan taɓa iya bacci a cikin wannan izayar ba. Jiya na kasa bacci saboda kewar ƴaƴana da mijina duk da ina cikin ɗakin da babu wani abu na wahala zai hana ka bacci, yau kuma ga ni a tare da iyalin nawa, amma azabar sauro da zafi sun hana ni bacci. Kenan da a irin gidansu Maman Nasmah nake tare da ƴaƴana da mijina babu abin da zai dame ni bare ya hana ni bacci? Jinjina kaina na yi ina ayyanawa a raina ko ta halin ƙaƙa sai mun bar gidan nan mun koma wani ƙato wanda ya haɗa komai na rayuwa nan kusa, don na gane kamar yadda ba zan iya rayuwa ba su Sultan ba haka ba zan iya ci gaba da zama a cikin talauci da ƙuncin rayuwa ba. Tilas ko ni ko Anas mu nemo kuɗi ko a ina ne mu yalwata rayuwarmu.
'To amma ni a ina zan samo?' Zuciyata ta yi mini wannan tambayar.
Mijin Aunty Billy da one million ɗin da ya ce zai ba ni don kawai na saka kati ne ya faɗo mini a rai, tamkar shi ne amsar tambayar da zuciyata ta yi mini........✍️
*Zeey Kumurya*
[3/8, 1:41 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*16.*
Saurin girgiza kaina na yi. A fili na ce. "Ba zan iya yin abin da yake buƙata ba, ina kuma roƙon Ubangiji ya tsare ni da aikata hakan har abada. Zan nemi wata hanyar dai daban." Ci gaba na yi saƙawa da kwancewa har bacci ya ɗauke ni.
Washegari bayan sallar asuba na janyo wayata na hau online, har su Sultan suka tafi school ban sauka ba bare na yi yunƙurin yin aikin gida. Shi ya shirya su ya yi musu komai, tsakani na da su gaishe nin kawai da suka zo suka yi na amsa ne. Kafin ya dawo daga kai su na fita na ɗauko ragowar abincin jiya don na fara jin yunwa na ci na yi wanka na shirya. Ina zaune a bakin gado Anas ya shigo ɗakin ya buɗe wardrobe, kamar na share shi kamar yadda ya yi mini sai na fasa na ce. "Ina kwana?" Ba tare da ya juyo ya kalle ni ba ya ce. "Lafiya ƙalau." Ban san me ya hau kaina ba na tsinci kalmar haƙuri ta subce daga bakina zuwa gare shi, don ganin da na yi masa yanzu sai na ji wata irin kewa da son kasancewa da shi sun baibaye ni. Duk yadda na so ɗaurewa amma na kasa, sai da na bayyana masa abin da yake nuƙurƙusa ta. Bai ƙi ba ya biye mini ba tare da ya nuna mini wani abu na ɓacin rai ko kaɗan ba. Sosai ya nuna mini soyayyar da na yi wa kaina buƙulun samun ta na tsawon kwanaki, ni kaina na san samun namjin da ya iya soyayya da taraiyar mace kamar Anas zai yi wahala.
Wajen ƙarfe sha daya ya shirya ya fita a gaggauce saboda makarar da ya yi. Ya na ficewa na bi bayansa zuwa gidan Maman Nasmah saboda uban kiran da take doka mini. Ina zuwa gidan nata ko zama ban yi ba ta dube ni cikin faɗa ta ce. "Wai me kika tsaya yi a gidan ne? Ina ta kiran ki kika ƙi ɗauka, kin san kuma dalilin kiran." A ladabce na ce mata. "Ki yi haƙuri, bari na yi sai ya fita, don yanzu ma ko tambayar shi ban yi ba na fito." Baki ta taɓe ta ce. "Aikin kenan, tsoron miji kamar wani mala'ika, sai ki je ku tafi, don su Maman Suhail suna ta kira na wai za su taho, ke ma sun kikkira ki ba ki ɗauka ba." Na ce. "Eh, duk na ga missed call ɗin da ina hanya."
Sai da ta ba ni wata abaya mai kyau sabuwa na saka sannan muka tafi, don cewa ta yi kayan jikina ba su yi ba, marasa tsada ne, duk da ƙurewar adakar da nake ganin na yi.
Madaidaicin gida ne mai kyau guest house ɗin nasu, sama da ƙasa ne, ga shi ya sha kayan furnitures masu kyau da tsada. Sai na ji da ma zai zama gidan nawa a gaske, don ko iya shi na samu burina ya gama cika. Kusan su goma ne suka zo, muka sha hira da hotuna. Na dinga kai wa da komowa ina jin kaina na kumbura. Akwai komai na amfani a gidan, kuma fes muka tarar da shi kamar mutane suna rayuwa kullum da kullum a cikinsa. Abinci da drinks ɗin da Maman Nasmah ta aiko sun wadata sosai, don har ragowa suka yi. Sai yamma lis suka tafi, ni kuma sai bayan Magriba na bar gidan ba don na so ba na koma gidan Maman Nasmah. A gaggauce na yi mata sallama na wuce gida, bayan ta nace sai na kwana ni kuma na ƙi. Don na ga Abban Sultan yana ta kira na. A gidan na tarar da shi ya cika ya yi fam, na yi sallama ya amsa ciki-ciki. Sai da su Sufyan suka koma ɗakinsu na dube shi na ce. "Ka yi haƙuri don Allah, wani babban uzuri ne ya fitar da ni." Jinjina kai ya yi ya ce. "Shi ne kuma ya sa kika ƙi neman iznina? Kika je kika kai har dare? Kin san yaran nan za su dawo daga school amma ba ki damu da halin da za su shiga ba idan sun dawo ba kya nan? Ba ruwanki sabgar gabanki ce kawai ta dame ki." Ɓata fuska na yi na ce. "Yanzu fisabilillahi daga dawowata sai ka tarɓe ni da faɗa? Ko hutawa ai ka bari na yi, kuma ba ka san lafiya nake ba ko ba lafiya ba." Cikin takaici ya ce. "Na san ƙalau kike Hafsah, a zatona maganganun da muka yi ɗazu komai ya wuce, za ki yar da sabbin halayen da kika tsiro ki zo mu koma rayuwarmu kamar da, amma tunda har yanzu da saura ki ci gaba, sai dai ina so ki sani ba zan ɗauki wannan gantalin yawon da kika tsiro da shi ba." Daga haka ya miƙe ya fice daga ɗakin. Raka shi na yi da harara tare da jan dogon tsaki, don ni ta gidan da na baro mai AC da wutar nepa kodayaushe nake ba ta shi ba. Bayan na yi Sallah na kira Maman Nasmah muka sha hira, na dinga kwarara mata godiyar fitar da ni kunyar da ta yi, har za mu yi sallama na tsayar da ita na ba ta labarin duk yadda muka yi da mijin Aunty Billy. Shiru ta yi har na yi tunanin ko kiran ya katse ne sannan ta ce. "Hmmm, ai shiru kawai na yi miki na ji ko za ki mun zancen da kanki, don bayan an tashi daga taron ya bi ni har gida ni ma. Har na tsorata ya ce ya kwantar da hankalina, wadda ya gan mu tare ya gani yake na so, kuma da aure yake son ki shi da gaske yake, saboda bai taɓa tunanin matar aure ce ke ba, shi ne ya ce bari ya gwada ki da farko ya ga irinki, don tun kafin magana ta yi nisa gara ya san irin matar da zai aura." Ajiyar zuciya na sauke na ce. "Haba, ni fa na yi mamaki sosai, na ce ga shi kamar kamilalle ashe ba haka ba ne." Da sauri ta ce. "Taɓ, ai mutumin kirki ne sosai, don ko a unguwarsu ba ki ga yadda ake yabon shi ba, ga shi da kyauta da sadaka, kawai ya yi hakan ne don ya gwada ki, ai ya faɗa mini komai bai ɓoye mini ba." Na ce. "Allah Sarki, har ina munana masa zato." Dariya ta yi ta ce. "Ai kuwa kin ɗauki haƙƙin shi, don son tsakani da Allah yake yi miki, so na gaskiya. Saboda a maganganunsa na fahimci ba ƙaramin so yake yi miki ba, ga dukkan alamu ya kamu da yawa." Na ce. "Uhm, shi ya sa abin da yake ta damu na, ni kaɗai na dinga cewa ya san ina tare da matarsa ya yi mini maganar banza, ko tsoron na faɗa mata bai ji ba." Da sauri ta ce. "To kin gani? Wannan ma kaɗai ya ishe ki gane ba halinsa ba ne, don ba haka ƴan iskan mazan suke ba, daga ganin ki ya fara yi miki magana wadda ba ta kamata ba, ba tare da ya san wace ce ke ba, kuma a sanadiyyar matarsa ya san ki. Ai ƴan iskan sai sun ja mutum a jiki sannan suke bayyana musu buƙatarsu." Na ce. "Haka ne kuma." Ta ce. "To yanzu dabara ta rage wa mai shiga rijiya, ke ce wuƙa da nama suke hannunki, don wannan wata gwaggwaɓar dama ce da kika samu ta cikar burinki cikin sauƙi." Cikin rashin fahimta na ce. "Ban gane ba, kamar yaya?"
"Ya kamata ki gane kuwa, saboda abin a zahiri yake, ki rabu da wannan faƙirin mijin naki ki zo ki auri mijin Aunty Billy, ki zama matar mai kuɗi ke ma kamar yadda kike fata."
Dafe ƙirji na yi cikin zaro ido waje na ce. "Na kashe aurena kenan?" Ta ce. "Eh mana, mene a ciki to?" Na ce. "Gaskiya da akwai damuwa, ina son mijina kuma ban san rabuwa da shi da ƴaƴana, sannan kuma na rasa wa zan aura sai mijin Aunty Billy? Duk yadda muke da ita?" Tsaki ta yi ta ce. "Daɗina da ke ƙwaƙwalwarki ba kodayaushe take ja ba, ai idan kun rabun da ƴaƴanki za ki tafi ba barin su za ki yi ba, wannan mijin naki kuma mene abin damuwa a rabuwa da shi? Kin samu dama amma kina ƙoƙarin yin wasa da ita. Idan kin auri mutumin nan ba ƙaramin hutawa za ki yi ba, ki wataya son ranki, ƙasashen waje kuwa duk wadda kike so ita za ki je ki shana a lokacin da kike so. Aunty Billy kuma duk yadda muke da ita ai bai kai yadda muke da ke ba, ina son ganin kin ci gaba ke ma a rayuwa kin zamto kamar mu, don haka akan wata can Billy ba zan ƙi taimakonki ba. Ki tsaya ki yi tunani da kyau kar ki yi wa kanki sagegeduwa, mutumin yana da bala'in kuɗi, kuma a zuwan da ya yi muka zanta ba ƙaramin son ki na fuskanci yana yi ba, da na ce masa kina da aure ba ki ga yadda ya ruɗe ba." Numfashi na sauke ina hasaso kaina a ƙaton gida matsayin mallakina, ina hawa mota driver yana ja na, ga suturu na alfarma da zan dinga sakawa. Na tuno tarin masu aikin Aunty Billy, na san ni ma idan na aure shi haka zai ɗibar mini su, su dinga mun komai ina daga kwance. Jin na yi shiru ya sa ta ce. "Bari na bar ki, ki yi tunani, amma ni da za ki ɗauki shawarata da kin amince kawai, sai ki bar komai a hannuna, na san me zan tsara na faɗa masa. Ƙarin abun daɗin kuma bai taɓa haihuwa ba, matsalar kuma daga Aunty Billyn ne ba daga shi ba, don mun taɓa maganar da ita. Kin ga da kin je kin fara haihuwa zai ɗauki son duniya ya ɗora miki ke da ƴaƴan, da ma ga shi ke uwar maza ce, sai ki ta haifa masa su, dukiyarsa da komai nasa su zama mallakinsu." Cikin ɗaurewar kai na ce. "Yanzu ni na rasa ta cewa ma, amma ki ba ni zuwa dare, zan yanke shawara." Ta ce. "Tom shikenan Allah ya kai mu."
Bayan mun gama wayar na miƙe na fara safa da marwa ina saƙawa da kuncewa. Tabbas Maman Nasmah gaskiya ta faɗa mini, wannan wata dama ce da na samu, amma inda matsalar take Kawu nake ji da hukuncin da zai ɗauka a kaina idan ya san ni na kashe aure na, sai kuma kallon da ƴan group ɗinmu za su yi mini idan suka ji labarin na auri mijin Aunty Billy, da ita kanta ma. Amma duk wannan bai kai son rayuwar kuɗin da nake yi tasiri a cikin raina ba, don sosai nake ji a jikina na kusa kaiwa matakin da nake so na zama matar hamshaƙi. Hango mutumin kawai nake da cikar kamalarsa da yadda kuɗi ya bayyana ko ta ina a jikinsa, alamun ya jiƙu a cikinsa.
A ɓangaren Maman Nasmah kuwa tsalle ta doka cikin farincikin murnar samun wani chance ɗin a sauƙaƙe na raba Hafsah da Anas. Za ta yi amfani da hakan tai ta ƙara cusa mata son rayuwar gidan kuɗi har ta yi nasarar raba sun. A cikin mazan da take hulɗa da su za ta haɗa ta da guda ɗaya su dinga waya da chatting a matsayin shi ne mijin Aunty Billy. Don ba ƙaramin daɗi ta ji ba da Hafsah ta ce mata ba ta karɓi card ɗinsa ba, bare ta kira shi ya ci gaba da yi mata maganar banza asirinta ya tonu na ƙaryar da ta zabga mata. Ita kanta ba ƙaramin kaɗuwa ta yi da ta ji mijin Aunty Billy ya bi Hafsan, kuma tsabar ƙwanƙwararre ne shi ya bayyana mata manufarsa ba tare da tsoron komai ba. Murmushi ta yi a fili ta ce. "Ashe ba namu mazajen ne kaɗai bunsuraye ba." Za ta ci gaba da nuna wa Hafsah son ta take yi tsakani da Allah da kuma burin taimakon ta, yadda duk abin da ta ce mata ta aikata za ta yi ba tare da jinkiri ba.
Wuni na yi ina abu ɗaya wato tunanin mafita, a ƙarshe na yanke shawarar amincewa da abin da Maman Nasmah ta faɗa, na rabuwa da Anas na fita na auri mai kuɗi irin mijin da nake fata da burin samu. Idona ya rufe gabaɗaya, ƙaton gida da rawuwar jin daɗi kawai nake hangowa, na manta da ƙalubalen da za su biyo bayan faruwar hakan. Da kaina na kira ta na sanar mata na amince, ta nuna mini ta ji daɗi sosai, don mutumin mai suna Alhaji Kyauta ya ƙara kiran ta a kaina, ta ce masa wasa take yi masa ba ni da aure za ta haɗa mu. Na nuna mata ba zan iya mu'almala da shi da aure na ba, ta san abin da za ta faɗa masa kafin na rabu da Anas sai mu fara magana a lokacin. Ta ce tom shikenan babu damuwa, amma na yi komai cikin sauri kar a ja lokaci, na ce mata in sha Allah.
Tun daga ranar na fara sauke wa Abban Sultan tsibiri-tsibirin kwandon rashin mutunci da tijara, wulaƙancin yau daban na gobe daban. Duk abin da na san ba ya so shi nake yi, wanda yake so kuma na daina yi. Ci gaba da maganganun abubuwan kuɗi da turo su a group ɗinmu shi yake ƙara tunzura ni, don na sha alwashin ba zan bari wani taron da za mu kuma yi ya zo ina cikin wannan akurkin gidan ba. Saboda an tsayar da cewar duk bayan wata shida za mu dinga yin taron, amma ba za a sake yi a gida ba sai dai a kama guri..........✍️
*Zeey Kumurya✍️*
[3/8, 1:41 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*17.*
Yau ta kama Laraba, wanda ya yi daidai da watanni uku da fara takun saƙar mu da Anas. Ina zaune a ɗaki da hantsi ina chatting tare da kallon su Sultan da suke ball a tsakar gida, da yake ana cikin hutu ne babu school.
Ƙara kishingiɗewa na yi cikin jin daɗin hirar da muke yi a group ɗinmu. Don yanzu ban da matsalar data, Maman Nasmah tana saka mini ishashshiya tare da kati, chaji ma ban da matsalar shi saboda ta aiko mini da sabuwar power bank. Wani video Aunty Billy ta turo, da sauri na yi loading na buɗe, don yanzu duk wani motsinta akan idona yake. Wani haɗaɗɗen gida ne da ya gaji da tsaruwa gurin gini da kayan alatun da suka ƙara ƙawata shi. Gidan mai hawa uku ne, bedrooms da parlourn cikinsa kuwa kasa ƙirga su na yi, kuma kowanne da kaya a cikinsa. Na maimaita kalla ya yi sau biyar sannan na haƙura ba don na gaji da kalla ba. Abin da na ga ta rubuta ne ya saka ni tashi zaune a zabure ba tare da na shirya ba. Sake watching video ɗin na yi cikin zazzaro ido kamar zan saka su a cikin wayar. Ina nuna gidan da ɗan'yatsana na ce. "Kan uba! Da gaske ko da wasa?" Ban kai ga samun amsa ba kiran Maman Nasmah ya shigo, cikin rawar jiki na ɗaga. Ba tare da mun gaisa ba ta ce. "Kin ga abin da Aunty Billy ta turo?" Da rawar murya na ce. "Gidan da ta turo ta ce za su koma a Abuja ita da mijinta?" Ta ce. "Eh, kin ga abin da nake faɗa miki ko? Kina nan zaune sai ta gama tatike shi, wannan uban gidan ko ni mijina ba shi da kamar shi, ki yi ki yi ki bar gidan talakan nan amma abu ya gagara, na tabbata da tuni yanzu ke za ki shiga gidan, don yana ta damu na akan maganarki, ko ɗazu da safe ma ya kira ni, kuma ya ce da an yi auren naku Abujan zai kai ki." Wani yawu na haɗiye mai ɗaci cikin takaici na ce. "To ya zan yi? Anas ya ƙi saki na, na yi masa tijarar, na yi bala'in amma ya ƙi, ba fa na yin komai a gidan shi yake yi, sai ya kai shabiyun dare bai yi bacci ba yana ta kujiba-kujiba da aikin gida." Maman Nasmah ta ce. "Taɓ! Amma wannan mijin naki wanne Iri ne shi? Kamar ba zuciya a ƙirjinsa?" Na ce. "Bala'in haƙuri ne da shi, kuma idan bai ga damar yin abu ba babu wanda ya isa ya saka shi, kuma yana so na sosai, da ma na san da wahala ya iya rabuwa da ni." A zafafe ta ce. "Ba wani so, da yana son ki ai da ya yi miki duk abin da kike so, kawai dai ya san idan kuka rabu ba zai samu wadda zai dinga cuta ya dunkume a gida kamar ki ba ne, shi ya sa. Ni dai abin da na kira na faɗa miki ki yi sauri ki dage ku rabu a cikin satin nan, ki san duk yadda za ki yi ku rabu a wuce gurin. Saboda na gaji da yi wa Alhaji Kyauta ƙarya, kullum ta yau daban ta gobe daban, don ya ce mini shi aure yake da buƙata cikin gaggawa, idan abin nan ba zai yiyu ba ya haƙura kawai ya nemi wata." Da sauri na ce. "A'a, ba ni iya yau zuwa gobe kacal, na san me zan yi." Ta ce. "Ya fi miki dai."
Bayan mun gama wayar na ci gaba da kallon gidan ina hasaso kaina a ciki, da tuni ni ce zan wataya a cikinsa amma Anas ya yi mini buƙulu, ƙwafa na yi ina ayyana abin da zan yi masa yau idan ya dawo, wanda na san duk nacin shi dole ya rabu da ni.
Ina nan zaune na ji an buga gida, Sultan ya je ya buɗe suka dawo tare da mai bugun, Naja ce, kuma da alama daga gurin aiki take, don sanye take cikin fararen kaya na nurses. Ba yabo ba fallasa na amsa mata sallamar da ta yi. Bayan ta shigo ta yi wa kanta mazauni ta ce. "Hajiya Hafsah, ana ta sana'ar ne? Don na ga yanzu U are always online, ko garin ma ba kya ji." Fari na yi da ido tare da faɗin. "Na kusa zama Hajiyar dai in sha Allah." Ta ce. "To Ubangiji ya tabbatar ya nuna mana lokacin, da fatan kin gama fushin da kike yi da ni?" Yamutsa fuska na yi na ce. "Fushi kuma? Akan me?" Ta ce. "Eh mana, tun daga ranar da na zo ɗin nan shikenan ba kira, ba magana a chat bare ki zo gida kuma." Taɓe fuska na yi na ce. "Au babu komai to, Allah ne kawai bai nufa ba." Ba ta ba ni amsa ba sai wayar hannuna da na ɗaga ta ƙura wa ido, kamar wadda ta ga abin tsoro haka ta nuna wayar ta ce. "Hafsah! A ina kika samu wannan Iphone 14 ɗin?" Jujjuya wayar na yi na ce. "Tsohon zance, tun yaushe na yi ta, wata ƙawata ce da take auren hamshaƙin mai kuɗi ce ta siya mini, ta ce idan mijinta ya dawo ma za ta saka ya siya mini 15." Kamar Naja za ta yi kuka ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hafsah kina da hankali kuwa? Da kika karɓi wannan wayar mai tsada kin tabbatar saboda Allah ba da wata manufar ta baki ba? Kin ma ce wanda ta ba ki da farko an sace, ganin kayan kika yi ko kuma wasu ta ƙara siya miki?" A gadarance na ce. "Wasu ta sake siya." Shiru ta yi na wasu sakanni sannan ta ce. "Anya ba da wata manufar ta yi miki wannan kyautar ba? Hafsah ki dinga tunani da ƙwaƙwalwarki fa, kar son duniya da ruɗun shaiɗan su kai ki su baro." Tsaki na ja na ce. "Babu wata manufa sai ta alkhairi, kuɗi ne kawai da su, wannan ai ba wani abu ba ne a gurinsu." Ban jira cewar ta ba na buɗe wayata na koma kusa da ita na fara nunnuna mata abubuwan da suke turowa a group ɗin, tare da ba ta labarin gidajen waɗanda na je na gano. Tana kallon gidan da Aunty Billy ta turo ta ce. "Don Allah na tambaye ki mana?" Na ce. "Ina jin ki?"
"Wa ya saka ki a group ɗin nan? Yaya aka yi kika tsinci kanki a cikinsa?"
Murmushi na yi na ce. "Ke ma ya burge ki ko? Ai group ɗin nan yana da shiga rai, duk wanda ya zauna a cikinsa ba ya iya fita, ga shi mutanen ciki duk ƴan gayu ne masu haɗin ka..." A ƙufule ta katse ni da faɗin. "Ni ba wannan na tambaye ki ba, yadda aka yi kika kasance a group ɗin nake son ji." Tashi na yi na koma inda
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 24