Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wankan tsarkin hailar da na yi kwanaki biyar ina yi, tun kafin ya fita yake ɗoki, da rana ma da ya muka yi wayar da muka saba yi kullum idan ya fita sai da ya yi mini zancen. Na ɗauka ya haƙura amma sai na tsinkayi muryarsa a raunane yana faɗin. "Shikenan Hafsah tunda haka kika zaɓa, ba zan takura ki dole sai kin faɗa mini abin da yake faruwa ba tunda kin ɓoye, amma don Allah ki daina bayyana ɓacin ranki, kin fi kowa sanin yadda hakan yake taɓa ni sosai ya kuma sanya ni a cikin damuwa, ba ki ji yadda nake ji a cikin raina ba, gabaɗaya na rasa nutsuwata, don Allah ki yi mini wannan alfarmar." Ture tausayinsa dake ƙoƙarin mamaye ni na yi na ce. "Shikenan, in sha Allah zan yi hakan." Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da faɗin. "Na gode tawan, Allah ya yi miki albarka ya ji ƙan Umma, ya raya mana su Sultan, ya kawo ƙannensu dozen masu albarka." Ya ƙarashe maganar cikin sigar tsokana. A daƙike na ce. "Amin." Ban yi niyyar tanka masa ba, amma don ya ƙyale ni na samu na yi tunanin sama wa kaina mafita na biye masa muka yi magana. Sai dai abin da nake so ɗin bai samu ba, don jin shi kawai na yi a jikina a maimakon na ga yana shirin yin bacci. 'Mutum sai jarabar tsiya amma ba ko sisi.' Na faɗi haka a cikin raina cikin takaici da haushin shi da yake ƙara cika mini zuciya.......✍️ *Zeey Kumurya ✍️* [3/8, 1:34 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 3. Washegari bayan na yi sallar asuba na koma na kwanta duk da ba bacci nake ji ba, don ban saba yin shi a irin wannan lokacin ba. Kuma na san su Sultan za su tafi school, amma rashin data ya sa duk takaici da ɓacin rai ya cika mini zuciya. Bayan Anas ya gama karatun Alkur'ani da azkar ya dube ni ya ce. "Wai har yanzu wannan yanayin bai bar ki ba? Ba mun gama magana jiya ba?" Fuska babu walwala na ce. "Na ce maka akwai wata matsalar ne?" Ya ce. "A'a, alamu dai kawai na gani." Siririn tsaki na ja na juya masa baya. Bai ce komai ba ya tashi ya fita, ina jiyo shi suna buruntu shi da ƴaƴansa. Har bakwai na safe ta wuce ina inda nake ban ko motsa ba, na ɗora da daga inda na tsaya a tunanin da ya aure ni. A lokacin su Sultan suka shigo ɗakin bakinsu ɗauke da sallama, juyowa na yi na kalle su tare da amsa musu, ganin jikinsu da ruwa alamun wanka ya yi musu ya sa tilas na tashi na fara shafa musu mai. Bayan sun gaishe ni Sultan ya ce. "Mami ba ki da lafiya ne yau ba ki fita kin yi mana girki ba?" Gyaɗa masa kai kawai na yi. Cikin marairacewa Safyan ya taɓa goshina ya ce. "Sannu Mamina, kin sha magani?" Shafa kansa na yi na ce. "Ai ban da maganin ciwona a yanzu, amma idan kuna addu'ar da na ce shi ne maganin zai samu." Sultan yana saka wandonsa ya ce. "To mene yake miki ciwo?" 'Talauci.' Na faɗa a cikin raina. A fili kuwa ban ce komai ba. Tare muka fita parlour, na tarar har Anas ya dama mana kunu ya siyo ƙosai, yana kallo na ya ce. "Zuba musu su ci mu tafi, sun kusa latti, bari na yi wanka kafin su gama." Kamar wadda ya faɗawa mutuwa haka na ɗaga masa kai fuskata a cuskune. Duk da ba na kallon fuskarsa amma na san tsayawa ya yi yana kallo na, kamar ban san yana yi ba na tsugunna na fara tsiyaya kunun a ƙananan cup. Ina jin shi ya ja dogon numfashi sannan ya fita, raka bayan shi na yi da harara. Na Kunna wayata ina dube-dube ya dawo ya shige ɗaki, ya ƙara fitowa kamar mai neman wani abu ya koma. Na san me ya sa ya yi hakan, a tunaninsa ko ban gan shi ba ne ko kuma tuni yake yi mini, saboda ya saba kullum ni nake shirya shi tsaf. Bayan ya gama ya fito ya kama hannun su Sultan ya tafi kai su school. Ina tunanin ranar da mafarkina na ganin lokacin da drivers za su dinga kai su Sultan school a haɗaɗɗiyar mota na fita tsakar gida, na gan shi fes har shara ya yi, da ma kuma kusan kullum shi yake yi, don tun ina amarya indai yana gida tare muke yin aiki, yanzu kuma da hidimar su Safyan ta ƙaro sai muke raba aikin, shi ya yi shara da wankin toilet ni kuma na yi wanke-wanke da abun kari da gyaran ɗaki. Idan kuma ba zai fita da wuri ba har wanke-wanken yake yi da dama kunu ko tafasa ruwan tea, ni kuma na shirya su Sultan. Cups ɗin da yaran suka ɓata na wanke na koma ɗaki na fara gyarawa. A haka ya dawo ya same ni, yana duba time ya ce. "Mu je mu karya kar ƙosan ya ƙara yin sanyi." Ɗan yamutsa fuska na yi na ce. "Ba na jin yunwa, ka je ka ci kawai." Fuskarsa da maɗaukakin mamaki ya ce. "Hafsah! Wai kina cikin hayyacinki kuwa? Ni ne fa Anas mijinki amma kike yi mini irin wannan abubuwan, me yake damun ki ne?" Ban ce komai ba na ci gaba da aikina, duk da na san hakan ba ƙaramin ƙular da shi zai yi ba, don ya tsani yana yi wa mutum magana yay masa shiru. Ganin ya ƙi fita na juya na kalle shi na ce. "Ka yi haƙuri, mu je mu ci abincin." Girgiza kai kawai ya yi ya fice daga ɗakin. Ina son mijina da ƴaƴana, kuma ba na son ɓacin ransa, amma burina na son zama hamshaƙiyar mace matar mai kuɗi ya canza mini komai a cikin raina, don a yanzu ban da wani fata sama da haka. Kuma gabaɗaya a da ban san ana irin wannan rayuwar kuɗin ba, saboda a cikin talakawa na tashi a nan na rayu, ina dai jin labarin masu kuɗi, amma ban taɓa tunanin jin daɗin rayuwarsu ya kai haka ba sai a SANADIN WAYA. Zuciyata ta kwaɗaitu matuƙa da irin wannan rayuwar. Duk wani rarrashi da nasiha sai da Anas ya mini kafin ya fita, hakan ya sa na ɗan saki raina, muka rabu lafiya kamar yadda muka saba kullum. Fitar shi babu jimawa message ɗin kati ya shigo wayata, da ma na faɗa masa ban da data ne, ya ce yana fita zai tura mini. Da rawar jiki na loda katin na siya data, har wani zuƙo jikina yake yi mini saboda zumuɗin shiga group ɗinmu na ga abin da aka yi da ba na nan. Hirarraki burjik na tarar an yi, a hankali na fara bi tun daga farkon inda na yi offline. Rabin hirar ta yabon hotunan juna ce, daga nan aka fara zancen kaya, lace ɗin jikin wata ne ɗaya daga cikin admin ta ce sun yi ankon shi a wani biki, kuɗinsa dubu ɗari biyu da wani abu. Zaro ido na yi na koma kan pic ɗin matar na yi zooming na ƙara kallon kayan da kyau, a anko kawai an yi na sama da 200k? Ina kuma ga normal kayan sakawa na gida ko na Sallah? Ci gaba da bin hirar na yi, na ga wadda ta saka kayan tana faɗar kuɗin ɗinkin da aka yi mata 30k. Haka dai nai ta bi ina kallon hirar tare da haɗiyar yawu, jin yadda suke zancen maƙudan kuɗaɗe a kayan sakawa kawai da takalmi da jaka. Abin da ya fi komai ɗaukar hankalina videon bikin da wadda ta ce sun yi ankon lace ɗin ta turo. Wani haɗaɗɗen hall  ne da ban taɓa jin labarin irinsa ba a rayuwata balle na gani. Ga hamshaƙan mata sun kame a kan kujeru, wuya da kunnuwansu duk gwala-gwalai ne. Na maimaita kallon videon babu adadi, kamar na yi tsalle na faɗa cikin wayar saboda yadda abun ya yi mugun ƙayatar da ni. Wasu mahaukatan kuɗaɗe ake liƙawa kamar ana watsa duwatsu. Ba don na gaji da kallon videon ba na haƙura na koma na ci gaba da bin chat ɗin nasu, don tsabar kallo sai da na haddace duk wani abu da ake yi a cikin videon da maganganun mc. A cikin hirar na ji wata ta ce ta ga bikin a Instagram, daga nan aka fara zancen ƙayatattun bukukuwan da ake ɗorawa a manhajar ire-iren waɗannan da ma wanda suka fi su. A take na ji ina son na shiga Instagram ɗin ni ma na gani. Da wannan zumuɗin na fita daga Whatsapp na koma play store na ɗauko app ɗin, bayan ya gama installing na yi ƙoƙarin buɗewa amma ya ƙi saboda ban da email account, ga shi ban san ta yadda zan buɗe shi ba. Na koma group ɗin da nufin na tambaye su ko sun sani amma sai na ga kamar ajina zai zube, hakan ya sa na fasa na miƙe na zari hijabina na rufe gida na fita. Wani gida a layinmu dake da wadatuwar samari na je suka buɗe mini a nan take, na yi musu godiya cikin tsananin farinciki sannan na dawo gida.  Zaman dirshan na yi a tsakar ɗaki ina kallon video's a Instagram baki buɗe, ashe ko rabin tsaruwa da haɗuwar bukukuwan ba su fasalta ba a group ɗin. Ban ajiye wayata ba har sai da na ga sun daina buɗewa, alamun datata ta ƙare. Ni da take yi mini kwana shida amma yau a cikin awanni ta ƙare, ashe shiga kowane apps a social media ɗin ma sai masu kuɗi, kullum ina ji suna ta zancen apps kala-kala, ashe ba ƙaramin data suke jibgawa a wayoyinsu ba. Wannan tunanin ya ƙara girmamar burina a cikin raina, na ji a yanzu babu abin da nake so sama da na ga na je irin waɗannan bukukuwan, ko kuma ya kasance an yi akan wani nawa ko wanda na sani da za a gayyace ni, duk da zan fi so a ce a bikina shagalin ya kasance. Tunanin ƴar walimar da aka yi lokacin aurena ya sa ni jan dogon tsaki tare da cizon yatsa. Sai sha biyu na rana saura na iya tashi na ɗaura girki, ina aikin ina imagining ranar da zan gan ni a cikin irin manyan haɗaɗɗun halls ɗin bikin da na gani, ni ma na tura a group ɗinmu aita mun fatan alkhairi da yaba bikin. Don yadda aka yiwa wadda ta turo sun yi bikin Allah ya sanya alkhairi abun ya burge ni matuƙa, don na san da irin namu gajari-gajari ta turo ba ballai a kula ba, amma wannan kowa sai rububin yi mata fatan alkhairi yake yi. Lokacin da su Sultan suka dawo ban kammala girki ba, kuma ba na jin na taɓa yin hakan in dai ba cuta nake ba, kafin su dawo na gama komai, amma yau sai da suka makara a islamiyya. Na dinga mita ni kaɗai ina cewa. "Da matar mai kuɗi ce ni ina za a samu wannan matsalar? Ina daga kwance kamar matan cikin group ɗinmu ina latsa waya masu aiki za su yi komai su gama, throughout suna online saboda ba sa aiki a gidajensu, amma ni hura gawayi ma kaɗai ya ishe ni, Allah ka kawo mini karshen wannan wahala da jarabar, don sai a yanzu na fuskanci auren talaka ba ƙaramin jidali ba ne." Na ƙarashe maganar kamar wadda take cikin wani mugun tsananin taskun rayuwar.......✍️ *Zeey Kumurya* [3/8, 1:34 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 4. Bayan na yi wanka na fita na siyo kati, fita biyu kenan a yau ba tare da izinin mijina ba, abin da ban taɓa yi ba kenan a rayuwar aurena. Na yi sa'a ina dawowa ana kawo NEPA, da ma chajina ya yi ƙasa sosai wayar tana gaf da mutuwa. Sai da na saka ta a chaji sannan na loda katin na siya data, direct Instagram na hau na ɗora daga inda na tsaya. Nai ta ganin abubuwa kala-kala, sai da aka kira sallar la'asar sannan na tashi. Ina idarwa na koma kan wayar, amma wannan karon Whatsapp na shiga, replying messages na fara yi sannan na shiga group ɗinmu. Na tarar sun ƙara cika shi da hira kamar marasa aikin yi, haushi ne ya kama ni, don na tsani a yi hira ba na nan. Sallama na yi tare da gaishe da kowa da kowa, waɗanda suke online suka amsa mini tare da yi mini ƙorafin kwana biyu ba na leƙowa gidan, na ce abubuwa ne suka ɓoye ni. Cikin zolaya Maman Nasma ta mun voice da faɗin. "Ko dai Oga ya ɗauke ki kun tafi sabon honeymoon ne? Shi ya sa kika manta da mu saboda kina can kina ƙonewa." Yaƙe na yi na ba ta amsa da faɗin. "Ba haka ba ne." A raina kuwa na ce, 'Wannan ai sai mazajenku masu zuciyar yi.' Daga nan na yi sama na fara bitar chats ɗinsu. Na ga an yi maganar za a yi taro, tare da shawarwarin yadda taron zai kasance. Ƙarshe dai an yanke shawarar za a haɗa kuɗi a yi abinci sannan za a fitar da anko, kuma har mayafi duk iri ɗaya suke so a saka. Inda za a yi taron kuma a gidan ɗaya cikin admin ne. Majority sun yi amanna da wannan shawarar, don haka sai aka bar ta a matsaya. Aka yanke kuɗin da za a bayar 5k, sai kuma atamfa anjima za a turo wadda za a yi tare da price ɗinta ita da mayafi. Yadda kowa ya aminta da abun da murnar taron da suke na san maganar ba ta wasa ba ce. Ban da zaɓi ni ma haka na nuna amincewata tare da fatan Allah ya nuna mana lokacin. Sai da daddare da Abban Sultan ya dawo na samu damar yin karatun Alkur'ani, da ma kusan kullum sai mun yi a tare kafin mu kwanta, da rana kuma duk Sallar da na yi ba na tashi sai na karanta ko da shafi biyar ne, amma yau ko buɗe Alkur'anin ban yi ba, saboda duk kusan wunin nawa akan waya na ƙarar da shi. *One week later* Zaune nake a tsakar gida na yi tagumi ina tunanin inda zan samo kuɗin atamfar ankon taron group ɗinmu, atamfar 12k ce, sai kuɗin ɗinki da na mayafi, ga takalmi da jaka duk ina son na je da sababbi masu tsada, yadda zan fito cas da ni kamar kowa don kar a raina ni. A kullum idan Anas zai fita yana ajiye mini Naira ɗari ya ce ko zan ji sha'awar wani abun na siya, ko in an kawo talla, saboda ba ya ba ni kuɗin cefane, komai shi yake siyowa, hatta kayan miya, daddawa, kuka da kanwa. To ita nake tarawa idan ina buƙatar wani abun na siya ba sai na tambaye shi ba, duk haka sai na daɗe ban siya abu da kuɗin ba, don ko unguwa zan je yana ba ni kuɗin mota, in haihuwa aka yi ko biki a dangi yana ba ni abin da zan kai na gudunmawa daidai ƙarfinsa. Ganin ƴan group ɗinmu kowa na tura kuɗinsa ya sa a cikin kuɗin da nake da shi dubu bakwai da wani abu na je p.o.s ba tare da sanin Abban Sultan ba na ba da aka tura mini, sauran da ya rage kuma duk na ƙarar da shi a siyan data, don wuni nake a Instagram ina kalle-kalle, hakan ya sa wayata ta ƙara rakwaɓewa, rashin riƙon chajinta ya ƙaru saboda yawan caji, da ya ƙare zan jona idan akwai NEPA, idan babu kuma sai na miƙa ta gurin masu chaji. Yanke shawara na yi zan tuntuɓi Abban Sultan yau da batun, taron yana ƙara matsowa kar na je lokaci ƙure don a tsayar da date ƙarshen watan da muke ciki. Ni kuma na ƙudurce wa raina duk runtsi duk wuya sai na yi ankon na kuma je taron, saboda har wanda ba ƴan Kano ba ma za su zo, bare ni da nake cikinsa, a tsarina har waya nake son canzawa kafin lokacin, gudun kar na je da ta hannuna a raina ni. Bayan ya dawo mun gama komai yara sun yi bacci na tunkare shi da maganar kaina tsaye na ce. "Abban Sufyan bikin ƙawar nan tawa fa Naja za a yi." Na san in na ce masa taron group ne ba zai taɓa bari na, na je ba. Da fara'a ya ce. "Masha Allah, Naja lokaci ya yi kenan? Allah ya sanya alkhairi, yaushe ne?" Na ce. "Ƙarshen watan nan ne, shi ya sa ma na ce bari na sanar maka, don an fitar da anko tuntuni, kuma mai ɗan tsada ce atamfar." Murmushi ya yi ya ce. "Ubangiji zai kawo yadda za a yi, ba za ta gagara ba in sha Allahu, ai Naja mutum ce mai zumunci kuma mai yi, don haka dole mu rama wa kura aniyarta." Na ce. "Haka ne kam." Ya ce. "Nawa ce atamfar?" Gyara zama na yi na fara yi masa lissafi. "Atamfar 12k ce, sai kuɗin ɗinki don mai kyau nake so a mun 5k, sai mayafi da jaka da takalmi, sabbi nake son sakawa kuma masu ɗan kyau, na tambaya kowane six-six thousand ne, sai casual make up da zan yi, amma ita ban san kuɗinta ba sai na tambayo. Sannan kuma ina son ka canza mini waya kafin ranar bikin, tawa duk ta rakwaɓe ta zama jagwal." Wani irin kallo na ga ya bi ni da shi da na kasa tantance ko na mene ne, wajen 2 minutes kafin ya numfasa ya ce. "Hafsah! Kin san lissafin da kika mun kuwa? Kusan 100k fa tunda yanzu wayoyi tsada suke yi, ko kin manta waye ni da sana'ar da nake?" Ɓata fuska na yi na ce. "Na sani, kuma na san ba ka rasa kuɗin da za ka yi mini duk abubuwan da na ce ba." Ya ce. "Haka ne, tabbas ban rasa ba, amma na rasa wadda zan ɗauko na ba ki, ki yi wannan buƙatun, domin wadatata ba ta kai haka ba, ke ma kin sani. Na yi mamakin wannan lissafin naki matuƙa da gaske, domin ba ki taɓa zuwar mini da buƙata mai girman wannan ba." Na ce. "Kamawa ta yi yanzun ma na zo maka da itan, ka san wace Naja a gurina da irin abubuwan da ta yi mini, lokacin bikinmu wacce hidima ce ba ta yi da jikinta da aljihunta ba?" Girgiza kai ya yi ya ce. "Na sani, ita ma kuma in sha Allah ba za mu ƙi yi mata ba, amma daidai ƙarfinmu, zan siya miki atamfa na ba ki kuɗin ɗinki dubu uku, takalmi da jaka da mayafi kuma ki yi amfani da naki na da." Cikin takaici na dube shi na ce. "Yanzu kana da kuɗin amma ba za ka siya mini ba?" Ya ce. "Eh, kuɗina na siyan abincin da za mu ci ne da sauran buƙatu, ga Sallah ta kusa, term ya zo ƙarshe zan biya kuɗin makarantar su Sultan, both boko da islamiyya. Ban san ki da kafiya da naci ba, kar ki koya a yanzu please." Girgiza kai na yi na ce. "Taɓ!" Tare da tashi na fice daga ɗakin. Parlour na je na kwanta akan kujerara zuciyata cike da baƙinciki, kusan matan group ɗinmu duka sun gama siyan komai na fitar taron, kuma kowacce cewa take mijinta ne ya siya mata, amma ni nawa mijin kamar a kansa aka ƙare fatara da tsiya ya ce ba zai iya ba. Tsaki na ja tare da ayyana irin kalolin rashin mutuncin da zan fara shuka masa, matuƙar ya dage da gaske ba zai ba ni kuɗaɗen nan ba. A parlour na kwana, abin da ba mu taɓa yi ba kenan wato raba shimfiɗa don mun samu saɓani, na kuma san ba ya son hakan shi ya sa na yi da gayya. Bayan Sallar Asuba ya same ni a inda na yi Sallah ya ce. "Yanzu dan na ce ba zan yi miki abin da ban da halin yi ba, shi ne kika kwana a nan? Mun samu saɓani kala-kala wanda suka fi wannan amma ba ki taɓa haka ba sai yau, me ya sa Hafsah? Me ya sa kike ɗauko wasu halaye da ban san ki da su kike yi? A Kwanakin nan gabaɗaya na daina gane kanki, duk kin canza, hatta kula da yaranki ma duk kin rage, mene matsalar ne?" Banza na yi da shi na ƙara haɗe raina kamar ban taɓa dariya ba, ina jin takaicin yadda a kodayaushe yake nuna ya damu da damuwata, amma kuma ba zai iya fitar da ni kunya ba. "Magana fa nake miki." "Babu komai." Na ba shi amsa ciki-ciki. "Amma kin san ba na san magana a dunƙule ko? Ina tambayar ki kina cewa babu komai, alhalin kuma da akwai." Yadda ya yi maganar na gane ya fara fusata, hakan bai sa na sakko ba, don da ma abin da nake so kenan na ɓata masa rai. Bai ƙara magana ba ya fice ya bar mini parlour'n. Na bi shi da harara tare da taɓe baki, don na san ba iya dogon fushi zai yi da ni ba, har inda nake zai zo ya same ni ya rarrashe ni......✍️ *Zeey Kumurya* [3/8, 1:36 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 5. *BRIGHT PENS...* _suna mara ba da masu buƙatar a tallata musu kasuwancinsu, masu siyar da turarruka, kayan sawa, magani komai da komai, cikin sauƙi za a tallata musu a cikin duka littafan guda uku🤙🏼 *CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI*_ Tsari👯🏻‍♀️ Duk page ɗaya 200 Duka littafin kuma 600 Shafi biyar a littafi ɗaya 1000 A littafai uku kuma 3000 Domin ƙarfin bayani sai a yi wa wannan number magana 08164069385🤙🏼👯🏻‍♀️🫶🫶🏼 Shi ya tafasa ruwan zafi suka sha tea da bread, ko tsinke ban ɗauke ba har ya dawo daga kai su Sultan school ya karya ya ɗauraye cups ɗin da suka ɓata ya gyara gurin. 300 ya ajiye mini ya ce idan mai kifi ya kawo na siya na saka a miya, ga kayan miya can ya taho da shi ya ajiye a kitchen. Motsi ban yi ba balle na tanka masa har ya fice daga gidan. Ranar haka muka ƙara kwana kowa zuciyarsa babu daɗi, don da ya dawo ko sannu da zuwa ban yi masa ba, na dai yi girki saboda cikina da ƴaƴana. A haka kwanaki uku suka shuɗe babu wata jituwa a tsakaninmu, duk yadda ya so mu sulhunta ni kuma na ƙi, magana dubu in zai yi ba zan tanka ba, yara ma idan yana nan ba na sakar musu fuska, idan suka ishe ni da magana na daka musu tsawa na hantare su. Hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yake yi ba, kuma ina yi ne duk dan na takale shi amma ba ya kula ni. Makwanci kuma tuni na raba mana da ma, tun ranar a parlour nake kwana ko a ɗakin su Sultan. Yau ya siyo mana kayan abinci da sabulun wanka da na wanki, ya haɗo da wani turare da ya san ina so, ya kawo mini har gabana ya ajiye, amma na ƙi ko ɗaga kai na kalle shi bare na ce na gode. Kasancewar Friday ce su Sultan suna gida, shi kuma da ma idan ya dawo daga masallaci ba ya kuma fita, zai zauna mu yi karatu ko hira ko mu fita unguwa tare. Ina ɗakin su Sultan a kwance ina kallon haɗaɗɗun girke-girken da aka turo a group ɗinmu, da yake Juma'a ce majority abinciccikan gargajiya suka yi, ban da haɗiyar yawu babu abin da nake yi, saboda kusan kowanne da zuƙu-zuƙun nama a kansa. "Garin daɗi na nesa." Na faɗa kamar zan fashe da kuka, dafadukar da na yi yau ce ta faɗo mini a rai, wadda ba ta da maraba da ta gidan bikin ƙauye a gurina. Tsaki na ja na tashi zaune tare da ajiye wayar hannuna. Duk wani abun gayu da abinci da ake turawa ni ban taɓa turawa ba, ina tsoron kar hakan ya sa su

Chapter 2 of 24