calls dina ko?
Banza yayi dashi yaje ya karbe handout din da yake hannun jalal "Allah sai ka gayamin ina kaje"
Dan tsaki yayi ya kawar da kanshi "sai fa ka gayamin"
"Mubarak wai meyasa kake jin dadin fitina ne? Toh gayamin ina kaje?
Ba inda naje kawai naje waje dan banason fitina,,, meyasa baka daga wayana ba?
Murmushi jalal yayi "mubarak dan Allah ka barni haka banason wannan surutun"
Tsaki mubarak yayi ya janyo chinchin ya faraci
Wai abincin kuma fa? Bazanci ba
Jalala be qara magana ba ya karbi handout dinshi ya ci gaba da karatunshi
"Jalal wai bros abdul bazai dawo bane? Eh ya bashi amsa
Kaji dashi cen ya tashi yaje ya kwanta
Jalal ya gama karatunshi yaje ya dauro alwala yayi addua ya kwanta
Kai tashi kayi addua,,, jalal Allah nayi fa
Dariya jalal yayi ya gyara kwanciyarshi
Washe gari cool AJ yayi musu sammako saboda a wurinsu ma yayi break
Kallon jalal yayi "Allah jiya akan hanya azumin magana nayi saboda na hadu da parrot a gidansu juwairiya" murmushi yayi
"Wa yafi surutu itada mubarak" wani kallo mubarak ya aiko mishi wanda ya sanya su dariya
"Bros jalal bani a zancen nan gaskiya" yayi kwanciyarshi
Haka sukaci gaba da rayuwa har su cool AJ suka kammala suka bar jalal da mubarak
**********************************
********************** ? **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************? **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ? **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ? **************************
Mubarak ne yake driving jalal yana gefenshi yana aiki da system dinshi har suka qarasa cikin yayi parking
Kallonshi yayi "jalal meye mafita kasan dai ni da kai ba wanda yake da wacce yakeso kuma kasan wannan kallon da baffa yake mana da alama shawara ne shida mai martaba da abba Sadiq"
"Mubarak kaje ka nema kawai amma ni idan sun gaji su nemamin dan bazan iya neman aure ba gaskiya dan bansan me zan gayawa mace ba"
Dariya mubarak yayi dan shi kawai be samu wacce yakeso bane shiyasa
Cikin suka shiga kowa ya zube kayan hannunshi
Mamin mubarak ce zaune tana zuba musu fada "jalal auren ne bakuso ko me?
Mami bafa haka bane,, kai na tambaya?
Allah ya baki haquri
Murmushi jalal yayi
Duk yanda jalal yaso mami ta fahinceshi abu ya faskara dole ya haqura yayi shuru sai faman masifa take mishi
Haka suka tashi suka fice
Result juwairiya tazo karba sosai AJ yake cikin farin ciki zaiga juwairiya
Part din mami suka nufa shida juwairiya da jawahir sai faman surutu take zuba mishi yana murmushi
Sosai mami tayi farin cikin ganinsu suka gaidata
"Bros AJ qawata fa? Harara juwairiya tayi mata ta rama ta mayar da kallonta ga cool AJ
Murmushi mami tayi ta nemi daya dagacin kuyanci ta tura ta kira mata jalilah
Cikin fushi ta shigo "mami gani" nuna mata jawahir tayi
Murmushi tayi "shine ba ko sanarwa? Dariya jawahir tayi
Jalilah ta zauna kusa da ita
Sai ga mubarak ya shigo yana dariya aiko jalilah ta hade face "mami kin ganshi ko? Allah zan hadaka da abba sadiq"
Kusa da AJ ya zauna "bros shine yau naga kayi sammakon fita ashe yau ba wasa
Murmushi kawai sukayi
"Waike meye na hararana? Cool jalal ne ya bata miki kayan fa"
Ai kai kace zaka biyani ko? Toh ai zan biya "pls ya mubarak dan Allah ka biyani"
Dariya jawahir tayi "bros AJ wannan fa? Sosa kanshi yayi dan yasan shida jalilah kawai ya gaya mata
"He is my friend" qarya ba kyau ya abdul jawahir muje wurin ummi
Taja hannunta suka fice
Cike da mamaki take kallonshi "sis wannan fa? Ya jalal ne mana twins brother din ya abdul"
Sam jalal be daga kai ba bale ya kallesu suka shiga ciki
"Sis amma kinsan be gayamin ba kawai yace ku biyu ne" hhhhhhhh bikinsansu bane ai ya mubarak ne kawai yake magana acikinsu kuma fa gara ya abdul da ya jalal
Okay mubarak din shima yayanki ne? Dariya tayi kinga manta da ya abdul surutun ne bayaso shiyasa
Haka sukaci gaba da fira na tsawon lokaci
"Sis jawa muje mu zaga gari"
Da sauri ta tashi jalilah ta sanja kaya suka fito
Kusa da jalal taje ta zauna "ya jalal zamu fita" kai ya girgiza mata
Kwantar da kanta tayi kan jikinshi "ya jalal Allah bazamu dade ba" I said no and I mean it,,,
Kuka tasa mishi "ya jalal jawahir bazataji dadi ba fa"
Ko kulata beyi ba aiko ta qara sa mishi kuka
Kallonta yayi "ya jalal pls"
Kai ya gyada mata tayi dariya tayi mishi peck ta tashi da sauri taja hannun jawahir
Part din mami suka nufa ta zauna da mubarak "ya mubarak muje ka zaga gari damu"
Bacci zanyi gaskiya, kukan shagwaba ta fara yimishi
Tsaki yayi "bros sai mun dawo" ya tashi suka fice
Sosai rayuwarsu take burge jawahir da sunada namiji a gidansu itama haka Zara riqa yi musu
"Ya mubarak tsaya tsaya" kallonta yayi menene "ice cream zamu sha mana
Wuri ya nema yayi parking suka nufi wurin
Zama sukayi ya karbo musu yaje kusa da jalilah ya zauna
Jefar da ice cream din tayi ta tashi da gudu taje ta tareshi ya fado jikinta suka fadi qasa
Da sauri jalilah ta nufeta ta tadasu
Sannu menene halam? Bata bata amsa ba kasancewar taji ciyo
Zama sukayi sai a lokacin mubarak ya kalleta dan bega yanda face dinta ba tunda sukazo be kalleta ba
Sis menene? Xikin yanayin jin zafi ta fara magna
"Kinga yaron ya hau kan gini ne shine yake qoqarin sauka naga zai fadi shine naje na tareshi kasa yaji ciyo"
Eyya sannu bari na karbo miki wani ice cream din ta tashi
Kallonshi tayi ahankali ya furta "good Samaritan" yana murmushi
Murmushin tayi tare da Ciro wayanta daga cikin jaka
"Hello mummy ina wuni? Jawahir juwairiya fa? Mummy bana tare da ita mun fita ni da qawata" katse wayan mummy tayi
Ice cream din ta bata ta karba taxi gaba dashi sai faman satar kallonta mubarak yake
Ya mubarak muje gida jawahir fa da alama wurin yana mata zafi
Tashi yayi suka nufi wurin da sukayi parking direct suka wuce gida
Kallonta yake har suka shiga part din ummi
Ahankali ya furta "my angel".............
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
121-125
Murmushi yayi yabi bayansu dan ganin halin da suke ciki dan yau yayi gamo da angel
Zaune ya samesu jalilah sai faman yi mata sannu take
"Karbo mata pain reliever a wurin mami tasha"
Da sauri jalilah ta tashi dama so yake ya koreta
Kallon da yake mata ne ya sanyata jin kunya ta sunkuyar da kanta
Gabanta yaje ya sunkuya yana kallonta
Ahankali ta dago suna hada ido da sauri mubarak yace "I love you angel"
Ido ta zare ya sauke mata lallausan murmushi tayi saurin sunkuyar da kanta
Ga baki daya mubarak ta qara birkitashi "pls say you love me"
Jalal da yake zaune ga baki daya mamaki ya cikashi ganin yanda ake fadan ina sonki kai tsaye
Jin motsin jalilah ne ya sanyashi tashi yana murmushi ya juya
Saida ya danji zuciyanshi ta buga dan be san jalal yana ciki ba a tunaninshi ya fita
Harara ya aika mishi shi kam jalal badan jawahir ba da yayi dariya
"Dama akan gulma zaka qare ya fice jalal yabi bayanshi
Be kula jalal ba har suka qarasa part din mami
Zama yayi kusa da mubarak yana dariya
Kallonsu mami tayi "lafia?
Mami wallahi jalal ya fiye gulma
Murmushi tayi bata qara kulasu ba
"Allah zamu bata idan baka daina ba"
"Sorry angel" sai a lokacin mubarak yayi dariya
"Cool jalal kai ka fiye gulma Allah kawai ka batamin tsari"
Murmushi yayi yana kallonshi "muje school pls"
Kaima kasan anan zan tare
Ido jalal ya zare "saboda angel? Yes, any problem?
Kai ya girgiza yana murmushi "ka gayama ummi na tafi sai Wednesday zan shigo" har Wednesday? Next week kenan fa?
Eh akwai abinda yake gabana
Toh nidai ka dora daga inda na tsaya
Wai dan Allah research nawa nakeyi ne? 2 ya bashi amsa ba tare da ya kalleshi ba
Kallon mami yayi ta aiko mishi da hararan wasa ya wani bata rai ya fice
Zaune yake cikin hostel sai faman typing din research din mubarak yake
Call din mami ne ya shigo wayanshi ya daga
"Jalal bakaji na kiraka bane dazu? Aa
Saboda kayi fushi shine na kiraka ka kyaleni?
"Mami toh me nake miki ne dan Allah, bakya yiwa abdul hakan mubarak ma bakya yimishi hakan toh ni me nake miki kika tsaneni?
Shuru tayi tana saurarenshi har ya gama qorafinshi "jalal wa yake da gatan da kake da acikinsu? Kai kadai kake da iyaye har uku
Sam abdul bazaiyi bugun gaba da ummin jalal ba mamin mubarak ma kai kadai kake da gata a wurinta toh meye na fitina aciki? Shuru yayi "bazakayi magana ba? Toh mami ni me nake miki ne?
"Baasan magajin sarki da shagwaba fa da jarumta aka sanshi" mami dan Allah ki daina Allah banason sunan
Murmushi tayi "toh yaron ummi baya shagwaba da jarumta aka sanshi"
Murmushi yayi suka dan taba fira daga bisani sukayi sallama
Pic dinta ya bude a system din mubarak ya zubata manyan idanunshi akanta cike da nazari
Murmushi yake lokacin da yake kallon pic din ummi
"My mum My world My life My soul" ya furta yana murmushi
Washe gari su juwairiya sunyi shirin tafia sosai suka sha tsaraba
Kallon jawahir mubarak yayi duk ya wani kalan tausayi "my angel sai yaushe kenan?
Kallon mamaki juwairiya da cool AJ sukayi mishi
Murmushi tayi mishi "sai kazo gaida abbana"
"Inzo gobe? Dariya "you are welcome" wani sanyi yaji aranshi ya juyo yana kallon su cool AJ
"Malam lafia? Gulma kawai kun wani tsareni da ido ya juya tare da daga mata hannu
"My angel naga abba Sadiq bari naje Neman izinin tafia kafin ya tafi" dariya tayi wacce ta qara fito da sak kamaninta da juwairiya
"Jawa me kikeyi ne? Aunty juwai abinda kukeyi ne fa
Dariya cool AJ yayi
"Jawah Juwai" dariya sukayi ga baki dayansu
"Habibi bari muje kada muyi rana a hanya" kai ya gyada mata
"Am going to miss you habibi" murmushi yayi dan gani yake nata wasa ne
Dariya jawahir tayi "bazaka iya magana ba kenan saboda naka yayi yawa" dariya sukayi juwairiya taja mota suka fice
************************************
Bayan dawowar mubarak daga katsina mai martaba ya tura akayi Neman izinin aurensu tare da sanya musu rana aurensu
Zaune yake a gaban mai martaba da mamin mubarak alhaji Sadiq da kuma ummi da baffa
Mami ce ta shigo ta nemi wuri ta zauna
Baffa ne ya fara magna "abdul jalal meye matsalanka da ka gagara fitar da wacce zaka aura?
Shuru yayi dan began wacce zai iya aura ba
"Jalal baza kayi magana ba?
"Ummi Allah ni bazan iya kallonsu ba bale nace ina son wata"
Ga baki dayansu ba wanda jalal be bawa dariya ba
"A haka zaka zauna kenan?
"Dan Allah ummi ki fahinceni Allah ni bazan iya kallonsu ba"
"Jalal tashi kaje" cewar baffa
Sosai yaji sanyi aranshi ya fito yana murmushi ganin kallon da mami tayi mishi
Duk wani shirin biki da akeyi an kammala sam mai martaba yace ba wani bidia da zaayi aka shirya akaje aka daura aure katsina
ABDUL JABBAR MAHMUD
&
JUWAIRIYA HAMEED
MUBARAK MUSTAPHA AZARE
&
JAWAHIR HAMEED
Ana kammala wa suka dauko hanya sai sharra gudu suke
Cike fadar mai martaba sarki Mahmud take abin baa magana
Fatiha sukaji ana karantowa
Sai faman tsokanar mubarak jalal yake da mijin angel
"Alhamdulillah an daura auren
ABDUL JALAL IBRAHIM da JALILAH IBRAHIM..........
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
126-130
Kallon juna sukayi da mubarak zuciyanshi sai bugawa yakeyi, lokaci daya suka juya suka nufi wurin da su baffa suke
Alhaji Sadiq ne ya tareshi "jalal zo ganinan" cikin rawar murya ya fara magana "Ab.. Abba daurin auren wa akayi?
Alaman yayi shuru yayi mishi yaja hannunshi ya shiga dashi cikin gidan har zufa yake suka shiga parlour ya nemi wuri ya zaunar dashi "jirani anan"
Ga baki daya jalal ya fita hayyacinshi sai zufa yake
Da sallama mai martaba ya shigo shida baffa da alhaji Sadiq suka nemi wuri suka zauna
Gyaran murya alhaji sadiq yayi "abdul jalal ni na daura aurenka da 'yar uwarka jalilah wanda na samu goyon baya daga wurin baffanka na biya sadaki kamar yanda addini ya tanadar ina fatan zaka riqeta amana"
Daqyar jalal ya samu qarfin daga kanshi alaman eh,,,
Tashi kaje Allah yayi maka albarka
Tashi yayi ya fito ya rasa ina zaije kawai ya nufi part din mami
Zaune take tare da hadimanta tana ganinshi tayi musu umurni dasu fita
Sai a lokacin jalal ya samu damar yin kuka
"Mami dan Allah ki tausayawa rayuwata ki fahintar dasu abba sadiq bazan iya rayuwar aure da jalilah ba"
"Jalal kasan me kake fada ko? "Mami jalilah fa? Haba mami kada ki goyi bayan wannan auren dan Allah ki tausayawa rayuwata"
"Jalal tun aranar da na fara ganinka kafin nasan cewa nice na haifeka nake alfahari da rayuwanka, tun daga lokacin da nasan kai dana ne nake qara yiwa Allah godiya, kasan cewarka dan halat yasa ko yaushe idan na tuna dakai nakajin wasu abubuwa da suka gabata sun wanke a zuciyana,
Jalal anya kasan babbancin alkhairi da sharri ko? Shuru yayi yana mai jin zafi a zuciyanshi
Jalal ya kake tunanin baffanka da ummin jalal za suji idan sukaga ka guji gudan jininsu? Jalal kayi tunanin rayuwarka ta baya da abinda kake shirin aikatawa yanzu,,, nikam sam banyi tunanin jalal zai guji hada zuria da jalilah ba"
Mami dan Allah kada ki fassarani wallahi ba butulci nake shirin aikatawa ba kawai bansan ta yanda zan kalli jalilah a matsayin matana ba
Murmushi tayi "jalal kana tunanin akwai wanda zai ci gaba da bawa jalilah tarbiya da kulawa sama dakai ne? Kaine komi na jalilah fa kuma ba ko wane namiji ne zai riqa yiwa jalilah wadan nan abubuwan ba
Jalal kanaso jalilah tasha wahalan rayuwa ne? Kai ya girgiza
Toh kaje ka ci gaba da riqonta bisa da amana nasan kaine mutum na farko da za muyi alfahari a aurar dashi a zuriar nan
Kai ya gyada ya tashi ta kirashi ya dawo ya zauna "haka zakaje wurin ummin naka cike da damuwa?
Murmushi yayi ya dauki ruwan da yake gabanta yasha badan yaji sanyi a zuciyanshi ba saidan bushewar da throat dinshi yayi
Dakin ummi ya nufa tana zaune sai faman rarrashin jalilah take tana sauke ajiyan zuciya
Ganin jalal ne ya sanyata tashi ta shige ciki
Kallon ummi yayi tare da sakar mata murmushi ta mayar mishi
"Uwace kawai zata iya fahintar halin da danta yake ciki"
Kusa da ita yaje ya zauna "sannu da gida ummi"
Ya fada voice dinshi a disashe
"Jalal banso ganin ranar da zan ganka cikin damuwa ba amma sai gashi kana cikin damuwa banida abinda zanyi maka maganinta,, jalal kayi haquri da hukuncin iyayenka a wurinka ni......... Saurin dakatar da ita yayi
"Ummi su waye iyayen nawa? Murmushi tayi "jalal bansan da wannan auren baffanka da alhaji sadiq suka qullah ba sai bayan an daura auren
Ajiyan zuciya ya sauke "ummi sam bana tare da damuwa akan hukuncinsu akaina tausayin jalilah ne kawai a tare dani bansan wane irin hali zuciyanta take ciki ba"
Murmushi tayi ya kwantar da kanshi a lap dinta shi kadai yasan yanda yakejin zuciyanshi
Baffane ya shigo sosai yaji tausayin jalal din
Ahankali jalal yayi mishi sannu da zuwa ya amsa mishi
"Jalal mubarak yana waje yana nemanka kasan cewar be samu wayanka ba"
Tashi yayi jiki a sanyaye "ummi sai na dawo" murmushi kawai tayi mishi
Tsaye ya sami mubarak da cool AJ
Murmushi ya sakar musu "angel ta qaraso ne? Murmushi kawai mubarak yayi yasan jalal yanaso ne kawai ya boye damuwanshi
Kallonshi cool AJ yayi "bros muje ciki ko? Ba musu ya bisu suka shiga ciki
Zaune suke a part din da juwairiya zata zauna an zagayeshi an gyarashi sosai
Kallonshi suke ya nemi wuri ya zauna "abdul kaida juwairiya wa yafi wani son abunda yake purple? Murmushi kawai yayi dan yasan zancen da yakeso yayi ne jalal yakeso ya kawar
"Bros jalal dan Allah ka qara bawa zuciyanka haquri ka zauna da jalilah a matsayin mata" murmushi yayi kawai danshi ko zancen bayaso
Kallon mubarak yayi "zan fita akwai wanda nakeson gani sai na dawo sai muyi magana ko? Kai ya gyada mishi
Ga baki dayansu tausayin jalal din sukeji
School ya nufa yaci gaba da gudanar da shirye shiryen seminar presentation da yake gabanshi a wannan satin
Ba irin nemanshi da baayi ba amma shuru ba labari
Haka suka haqura sunsan duk inda yaje zai dawo
Washe gari cool AJ da juwairiya sukaje gaida ummi bayan sun dawo daga wurin mami
Kwance suka sameta ta rufe idanunta amma ba bacci take ba tanajin su ta tashi tare da sakar musu murmushi "morning my sis" murmushi tayi "ya abdul barka da safia"
Komi nata a sanyaye yake
"Jalilah kin tashi lafia? Kawar da kanta tayi tana murmushi "bari na kira ummi tana ciki
Tausayinta yaji ya fito da wayanshi ya turawa jalal text ya maida
Tsawon kwana hudu ba wanda yaga jalal haka ba wanda ya nemeshi mubarak ne kawai suke haduwa a school din
Gobene ranar da jalal zeyi presentation ya shirya ya nufi gida
Ahankali yayi sallama kamar mai rada
Kallonta yake ta zabga tagumi tana tunani ga Baku daya sai yaga tayi rama
Sallama ya qarayi sai a lokacin ta juyo
Kallonshi tayi ta sunkuyar da kanta "ina wuni? Lafia qalau ya amsa tare da shigewa ciki
"Ummi ina wuni? Murmushi tayi ta tashi "jalal duk karatu ne haka? Murmushi yayi ya zauna kusa da ita
Ummi yunwa nakeji
Jalilah ta kira "ummi gani" kawoma jalal abinci
Ta juya ta fice
Bayan ya kammala cin abinci ya kalli ummi "ummi gobe zanyi presentation dan Allah ki tayani da addua"
Jalal Allah yasa ayi akan nasara
Shuru ba wanda yake magana acikinsu "jalal kaje ka gaida mamin abdul tana fama da mura
Tashi yayi ya nufi part din mami
Harara ta aiko mishi tare da kawar da kanta...........
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
136-140
Kallonta yayi na wani dan lokaci ya kawar da kanshi suna saurarenta har ta gama waya da amira ta ajiye wayan taci gaba da sha fruit dinta
"Jalilah bikiga yayanki bane?
"Ai na gaidashi" ta fada a takaice taci gaba da sha fruit dinta ba tare da ta kallesu ba
Mamaki ne kome ya cika jalal ganin jalilah tayi qarya karo na farko kenan kuma ga wani basarwa da take
Tana kammalawa ta tashi zata fita "ina zaki haka? Cewar ummi
"Gum mami" ta fada ta fice kawai
Murmushi ummi tayi tasan duk wannan jalal ake yiwa sai kuma abin ya bata dariya
Kallon ta mami tayi cike da murmushi ga qanshin nan ga baki daya ya cika dakin mami "jalilah yau ba school ko?
Murmushi tayi "eh shine nakeso anjima zan tafi wurin kunshi" au jalal din kuma fa?
Turo baki tayi "ni banason nashi" murmushi mami tayi "toh ai sai kije ayi miki wanda kikeso" tayi dariya
Fira suka dan taba ta koma wurin ummi ta sameshi shi kadai a parlour ta wuce ba tare da tayi mishi magana
Sanye da wani lace ta fito pitch yayi kyau sosai da jikinta ta shiga wurin ummi ta gaya mata ta tafi wurin kunshi kai kawai ta gyada mata ta fito
Ko kallon arziqi jalal be samu daga gareta ba ta fice yana jiyo fitanta da mota ya sauke ajiyan zuciya
Gidansu amirah taje sukaje wurin mai kunshi sosai akayiwa jalilah kunshi aka gyara mata kanta ta fito fes da ita
"Amirah Allah duk da ya jalal be kyauta ba abinda yayimin amma fa banason yaga nayi mishi rashin kunya kinga harda qarya nayi mishi a gabanshi kuma nasan yayi mamakin hakan kar ya shiga damuwa"
Damuwar nakeso ya shiga ai
Ido jalila ta zare "Allah ni banaso" idan be shiga damuwa ba ai bakikai mace ba kenan kinga zo ki tafi banason qorafi kuma kada ki daga mishi qafa ta juya kawai dariya jalilah tayi taja mota tayi gida
Mubarak ne tsaye shida cool AJ da jalal taje nesa dasu tayi parking
Qafarta daya ta fara fitarwa wacce tasha zane abu ga farar fata tayi kyau sosai
Tsawon lokaci suna jiran ta fito ita kuma bada wani nufin ba kawai ta tsaya wayane da jawahir
"Kinga yanzu nake dawowa kinaso ki kasheni da dariya zan bawa ya mubarak zam zam din ya kawo miki" ta kashe wayan ta janyo jakanta ta fito
Kallon mamaki suke mata ta biyo kusa dasu batayiwa kowa magana ba saida ta wucesu kadan "ya mubakar akwai saqon sis a hannuna kazo ka karba"
Duk yanda sukaso su boye mamakinsu ba wanda ya iya daga cikinsu sosai ta burge cool AJ yasan dole jalal yaji ta burgeshi
Dariya mubarak yayi "bros bari naga mami sai inzo muje ga baki daya ko? Kai ya gyada yana murmushi
Sauri sauri tayi wanka ta fito tayi kwalliya ta shirya ta zuba tularenta ta fito da ice cream daga cikin fride ta nufi part din mami
Sanyayar qamshi ne ya ziyarcesu a lokacin da suke qoqarin ficewa lokaci daya suka juya
Tafia take tanasha ice cream ko kallon batayi kamar batasan suna wurin ba ta wuce abinta
Dariya mubarak yayi "bros wannan fa neman magana jalilah take" ka barshi kawai ai tamin dai dai
Jalal ne ya fito cike da qasaita yana sanye da baqin wando da riga dark blue ya sanya glass dinshi sosai yayi kyau
"Mami nason ganinka fa" kallonshi yayi da mamaki ya juya kawai ya nufi part din mami
"Amma kasan qarya ba kyau ko? Banason yayi missing wannan wanka ne shiyasa na turashi
Murmushi kawai AJ yayi
Sallama yayi cike da girmamawa ta amsa mishi "mami gani"
Kallonshi tayi "lafia? Mubarak ne yace kinason ganina"
Kallonshi tayi cike da zargi sai kuma tayi murmushi "na bawa abdul saqon kaje kawai"
Ko kallonshi jalilah batayi sai faman game takeyi..............
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
131-135
Murmushi yayi ya nemi wuri ya zauna "mami ya mura?
"Sai zakamin ya jiki? Murmushi yayi tare da kawar da kanshi
"Mami kimin addua gobe zanyi seminar presentation"
"Allah yasa ayi akan nasara" ameen ya amsa tare da tashi
Wurin ummi ya koma suka dan taba fira na tsakanin uwa da da ya gaya mata zai koma school
Tun daga wannan lokacin ba wanda yayiwa jalal zancen tarewar jalilah haka shima beyiwa kowa ba kuma ba wanda ya nuna mishi komi har suka kammala karatunsu shida mubarak
Zaune yake jalilah tazo ta sameshi "ya jalal ina wuni? Kai ya gyada ba tare da ya kalleta ba
"Ya jalal dan Allah so nake ka barni nayi karatu koda diploma ne"
Kai ya gyada mata tayi mishi godiya ta fita tana murna direct taje ta shirya tazo ta sameshi
"Ya jalal zanje gidan ya mubarak" kai ya gyada mata tayiwa ummi sallama ta fita
Daya daga cikin motocin gidan aka dauketa da ita kasan cewar mubarak yana gidan da alhaji Sadiq ya bashi mijin mamin munarak kenan
Cike da farin ciki suke zuba fira har mubarak ya shigo
"Mrs jalal ce haka? Bata rai tayi "Allah ya mubarak zamu bata" dariya yayi ya zauna "cool jalal fa?
Na barshi gida mana" dariya yayi
"Ya mubarak ya jalal fa yace inje inyi karatu shine fa nazo wurinka dan ka samomin admission"
Jalal din
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 13