sunanka ne saboda kanamin kama da wani" kallon mubarak yayi aiko mubarak ya shiga dariya dan yasan koda sama zata hade jalal bazai gaya mata sunanshi ba
"Kinga malam sunanshi Abdul jalal ibrahim" ya juya yabi bayan jalal dan har ya fara tafia
Tabbas bazasu rasa alaqa ba
Sanye yake da manya kaya farar shadda yayi kyau sosai aciki akeje aka taryo baqin masarautar sarki mahmud sosai suka yaba da hali irin na abdul jabbar basusan tsoron hukuncin mai martaba ne yasa yayi hakan ba dan yasan kowa sai yaji abinda ya aikata wa masarauta
Cikin girmamawa yq zube gaban sarki ya kwashi gaisuwa "an gaisheka magajin sarki"
Cike da natsuwa ya shiga jera bayani game da baqin da tayasu godiya akan abinda masarauta tayi musu kuma suna tafan alkhairi ga wannan masarauta
Sosai sarki Mahmud yaji dadin abinda abdul jabbar yayi dan ba kadan ya burge ba
Akayiwa baqi rakiya cool A J ya dawo part dinshi ya sami A K zaune yana jiranshi
A K gaskiya dole na dauki mataki "name kenan? Mami zan lallaba ta nemo maganin da zata haihu Allah bazan yarda da wannan aikin sarauta ba kai kaji yanda zuciyana yake kadan ya rage nayi zagi a fada yau" aiko A K yace me zeyi inba dariya ba
Wai meke faruwa ne? Tsaki yayi ya shege toilet yayi wanka ya fito ya sanyawa dakin key ya kashe wayanshi suka shiga shaye shaye har sukayi bacci
Haka rayuwa taci gaba da tafiya har yakai su jalal ana first semester UG 3 dashi da mubakar ko yaushe zaka gansu da kaya iri daya abdul jabbar da juwairiya kuma suna UG 4 sam ba wani abu da yake shiga tsakanin juwairiya da abdul jabbar saboda ta daina ko kallonshi shi kuma ba damuwa yayi da mata ba
Tafiya suke jalal sai faman fushi yake da mubarak wanda ya sanya mubarak dariya saboda ya nuna mishi wata yace sun dace ya aureta shine sanadin fadan har abdul jalal yayi fushi
Suka kawowa kusa da motan cool A J kawai ya bude mota wanda sanadin hakan ya sanya ya buge mubarak kuma yayi hakan da gangan saboda ya hango su suna zuwa ta kusa da motanshi
"Ashhhh" mubarak ya fada tare da sunkuyawa qasa da sauri jalal ya dawo kusa dashi
Mubarak kaji ciyo ne? Kai ya gyada mishi, ya juya yana kallon motan yaga bayada alaman fitowa bale ya bashi haquri kawai ya tashi da sauri juyawa jalal yayi mubarak yayi sauri ya riqeshi "kyaleshi kawai" fisge hannunshi yayi kawai yaje ya janyoshi daga cikin motan ya wankeshi da mari..............
Kallon mamaki cool A J yake mishi wanda sam be hango wannan ba "what's d fillings? Ka buge mutu kuma u can't tell him sorry, who r you and who d you think you are!!!? Ya fada da qarfi
Kallonshi A K cike da mamaki
Sam cool A J beji me yake fada ba saida tsananin mamakin kamarsu da yake gani ansha gaya mishi akwai wani mai kama dashi amma ya nuna bayason zancen saboda ba gaskiya bane sai ganshi ya gani da kanshi
Tureshi jalal yayi ya nufi mubarak ya taimaka mishi ya tashi suka nufi hostel yana riqe da hannun mubarak sai furzar da wani zazzafan iska yake
Kallonshi mubarak yayi "jalal kaga abinda na gani ko? Cire kayanshi kawai yayi ya nufi toilet yayi wanka ya dawo
Ta bangaren A J kuma mamaki ya hanashi yayi magana sai AK ne yayi magana. "Cool AJ kaga abinda na gani ko? Har voice dinku irin daya ne fa? Ga baki daya cool A J ya rasa me zeyi dan gani yake kamar a mafalki ne
"AK r u sure munada kama sosai ko nine nake ganin hakan? Cool AJ Allah bakuda babbanci amma waye wannan?..........
[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
41-45
Waya ya sameshi yanayi da mami "mami I saw what amazing me wlh Allah I was so surprised da na ganshi yana wannan fadan kuma shi sam be kula da yanda sukayi kama ba fa" murmushi tayi "hope dai ba Inda yake maka ciyo yanzu? "Aa mami saidai kawai inajin tsoron kada su tabashi? Baza suyi mishi komi ka kwantar da hankalinka" toh mami sai munzo week end
"Kai kenan komi sai ka fada ko? Bazaka iya shuru da bakinka ba ko? Meyasa kakeson ka zama parrot? Eh na fada ka dakeni idan kaji zafi,,, murmushi kawai yayi sosai masifar mubarak take bashi dariya kamar wani qaramin yaro idan yana magana
Zama yayi kusa dashi ya janyo abinci ya fara zubawa a plate sai da ya gama zubawa mubarak ya dauke ya faraci, be kulashi ba kawai yayi kwanciyarshi har saida mubarak ya kammala ya dauka ya faracin ragowar
************************************
Cike da murmushi take kallonshi "abdul kasan dai bakada yaya ko qani ko? Toh kama ce kawai" mami Allah akwai alaqa dan wannan kamar tayi yawa" hmmm meye sunanshi? Mami nifa kawai ya mareni ne yaci gaba da fadanshi ina kallonshi" mari fa kace? Kai ya gyada mata "toh waye wannan? Dan a iya saninta abdul bayada sauki amma gashi har wani ya mareshi be dauki mataki ba
"Kaje ka binciko asalinshi"
Zaune suke cikin hall suna karatu sai ummi ta kirashi ya daga suka gaisa "jalal meke faruwa dakai ne? Ummi ba komi me mubarak ya gaya miki ne? Aa kawai dai nayi wani mafalki ne dakai,, ba komi Ummi, toh ka yawaita addua kaji? In shaa Allah
Kallon mubarak yayi "wai kai bazakayi aski bane? Eh ya bashi amsa,, murmushi yayi ya janye handout dinda yake gaban mubarak "sai fa kayi" dariya mubarak yayi dan yasan koyonshi ne jalal yake "dan Allah ka bani Allah zanje inyi idan na tashi daga nan" aa tashi muje kayi" tsaki yayi "matsala na dakai kenan wallahi" ya tashi ya fice jalal yabi bayanshi
Cak mubarak ya tsaya yana kallon cool A J cikin shiga ta alfarma ga baki daya haka ya ganshi kamar jalal din
Kallo daya jalal yayi mishi yaji gabanshi ya fadi dan beyi tunanin kamar tasu takai hakan ba amma yayi saurin kawar da kanshi ya qarasa wurin mubarak yaja hannunshi
"Malam muje kada mu bata lokaci" kallonshi mubarak yake shima kallonsu yake yana mamakin jalal
"AK how r we going to do? Mu bisu kawai,,, no banason raini ya shigo tsakanina dasu
Amma kasan da alama ba wanda zai gaya mana komi game dasu saboda duk wanda na tambaya zaice haka ya gansu su biyu kuma basa magana da kowa"
Ajiyan zuciya cool AJ yayi
"Muje kawai zansa a kawominsu" murmushi AK yayi dan yasan yafi komi sauki a wurin cool AJ
Aski aka gamawa mubarak suka fito "cool jalal muje hostel yunwa nakeji" harara yayi mishi "kai kenan da an fara karatu ka fara jin yunwa" eh naji yunwa" dariya yayi
"Bari na samo mana snacks kaci amma bazamu je hostel ba yanzu gaskiya" tsaki mubarak yayi yayi gaba ya barshi yana dariya
Juyawa yayi dan zuwa siyo mishi snacks din
Cike da natsuwa yake tafiya
Parking sukayi kusa dashi kawai suka fito suka turashi cikin motan suka fice
Kallon juna suke da jalal duk yanda yake tunanin zafin jalal yafi hakan dan yana hangoshi ba irin abinda baa yimishi ba amma amma bayada alaman magana ga wayanshi yana ringing amma sun hanashi ya daga kuma yasan mubarak ne
Tunanin halin da mubarak din ze shiga ya sanyashi suke ajiyan zuciya
Ahankali ya furta "Abdul jalal" ido cool AJ ya zare
"From where? Daya daga cikinsu ya tambayeshi,, ahankali ya dago yana kallonsu daya bayan daya "kafancen" mamaki ne ya cika cool AJ ba alaman qarya a tare dashi amma toh shi iya saninshi basuda alaqa da kafancen asaluma basuda kowa acen toh ya haka?
Umurni yayi musu dasu maidashi makaranta
Cike da takaici ya siyo snacks ya nufi hall din be sami mubarak ba ya kirashi a waya "jalal kana ina ne dan Allah? Hall kawai ya bashi amsa ya kashe wayan
Kallonshi yake cike da tashin hankali "jalal meya sameka?
"Mota ta kadeni" ya bashi amsa kawai
Sosai mubarak yaji hankalinshi ya tashi "jalal muje clinic a dibaka " harara yayi mishi kaci abinci ba Inda zani" kallonshi kawai mubarak yake yaci gaba da karatunshi
Zama yayi kusa dashi "jalal wannan guy din ne yasa aka dakeka ko? Harara yayi mishi "amma kasan banason surutu idan ina karatu ko?
Yaci gaba da karatunshi
Zaune yake gaban mami yana mata bayanin yanda sukayi da jalal
Ikon Allah toh yanzu ya zaayi in ganshi? Mami nifa harda tsoro nakeji "tsoron me? Ai gara na ganshi mami zansa a kawo miki shi" kasa kayi haka kyaleshi
Zaune suke a premises na school din "mubarak muje mana bacci fa nakeso nayi"
Kallonshi ya maida wurin da mubarak yake kallo
Tsaye yake yana kallonsu ya jingina da jikin mota
Tsaki jalal yayi wai dama wannan bastard din ne kake kallo? Dariya mubarak yayi jalal yaja hannunshi suka fice
Zaune take a gaban mai martaba tana sanar dashi abinda ke faruwa
Ya sunan yaron? "Abdul jalal" zaune ya tashi cike da tashin hankali "da gaske kike? Kai ta gyada mishi"
Shuru na tsawon lokaci ya shiga tsakaninsu kafin yayi mata izinin tafia
Tsawon lokaci yana tunanin wasu abubuwa
Zaune yake gaban mai martaba yana mishi cikakken bayani game da abdul jalal,,
Umurni yayi da akawo mishi jalal din
Ga baki daya mamaki ya cika mami mai martaba kam ya shiga tashin hankali ta wani bangaren kuma ya cika da farin ciki
Cike da qasaita ya shiga yi mishi tambayoyi
Kamar wanda akayiwa dole duk da hakan ce akayi mishi
"Sunana abdul jalal Ibrahim ina zaune a farin kafancen" yana kaiwa nan yayi shuru tare da Sara hade face
"A wurin iyayenka kake? Wani kallo ya aikowa mai martaba tare da kawar da kanshi "murmushi mai martaba yayi
Aje dashi kafancen nazo da iyayenshi...............
[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
46-50
Kallonsu suna hada ido da mami ya sunkuyar da kanshi tare da ciro wayanshi
Mubarak ya kira ya da cike hanzari yake tambayarshi lafia? " ka kwantar da hankalinka zan dawo amma yanzu kafancen zamu tafi wai zaa zo dasu baffa da ummi" lafia dai? Oho maybe suna ganin ba gaskiya na fada ba kawai dai ka kwantar da hankalinka zan dawo kuma kaci abinci yana nan na girka maka" jalal ko inzo muje ne? Murmushi yayi wanda ya qara tabbatarwa da mai Martaba abinda yake zargi "karka damu zan kiraka back" ya kashe wayan tare da qara hade face dinshi
Tafia suke cike da gudu har suka qarasa kanfance
Jalilah ya hango tana tafia cike da natsuwa murmushi yayi ya nuna musu gida suka shiga baffa na zaune ya tashi da sauri "abdul jalal lafia? Baffa ka kwantar da hankalinka ba komi bane kazo muje ina ummi?
Murmushi ya sakar mata lokacin da take fitowa? "Jalal lafia? Be bata amsa ba jalilah ta qaraso da sauri tayi hugging dinshi "ya jalal lafia? Ba komi je ki sanja kayan zamu tafi zaria ne ana buqatar ganin family nane? Wai wa yake buqatar ganinmu? Baffa a masarautarsu ne ake buqatar ganinku muje kada mu bata lokaci mubarak yanacen hankalinshi baa kwance yake ba
Da ummi har baffa hankalinsu a tashe yake ba wanda baya addua acikinsu har suka qarasa
Parlour'n baqi aka ajiyesu suka zauna
Kallon juna suke shida mai martaba cike da tashin hankali baffa yake kallonshi
"Dan Allah kada ka tarwatsa rayuwar jalal Alhaji ka barshi yaci gaba da rayuwa cikin natsuwa wallahi bamu karya alqawarin da mukayi ba"
Kallonshi jalal yayi "baffa meke faruwa ne?
Mai martaba ne ya bashi amsa "ba komi abdul jalal ku tashi ku tafi a maidasu garinsu" "baffa dan Allah meke faruwa ne kada ka boyemin rashin fadamin shine zai tarwatsa rayuwana ummi dan Allah ki gayamin menene?
Kallonshi ummi tayi "baffan jalal bayada wani amfani boye mishi ahalin yanzu kayi haquri mu rungumi qaddara mu sanar dashi wannan sirrin kodan kwanciyar hankalinshi"
Haba Aisha me kikeso ki gayamin kin karya alqawarin da kika yimishi kenan? Ba haka bane wallahi banason abinda zai sanyashi damuwana ne kwanciyar hankalinshi nake nema
Kallonsu mami tayi "wai meke faruwa ne? Ai gara a fada musan koma menene?
Cike da girmamawa cool A J yake kallon mai martaba "abba dan Allah ka bari a fada ko muma hankalinmu zai kwanta
Tashi jalal yayi "jalal ina zaka? Ummi zan shigo da mubarak ne" ya juya ya fita sai gashi ya shigo tare da mubarak
Kallonshi mai martaba yayi "mubarak mustapha azare" kallon mai martaba yayi cike da mamaki yanda yasan sunanshi
"Tashi ka ficemin daga gida kada na qara ganinka cikin gidan nan kuma ka gayawa maryam ni sarki mahmud nace ba kai ba abdul jalal idan kuma na qara ganinka cikin gidan nan zakayi dana sani"
Kallon mamaki suke mishi mami ce tayi magana "kana nufin yaron maryam ne? Kai ya gyada mata "gaskiya bazai fita ba tunda Allah yasa mun ganeta bazamu bari ta qara bace mana ba"
Mami wai me kuke magana dakai ne dan Allah? Wannan da kake gani dan qanwar mahaifinka ne matsala suka samu akan mubarak din tayi fushi tabar yayanta
Kallon juna suke shida abdul jabbar "mami jalal fa? Shine nakeso nasan meye alaqarshi da gidan
Kallonsu mai martaba yayi
Labari ne mai tsayi hafsa amma ya zama dole na gaya muku kuma na nmi gafararki Duk da inada damar yin haka
*ASALIN LABARN*
Sunana Mahmud Adam ni haifaffen farin zaria ne kuma cikin masarautar zaria iyayenmu Mu biyu kadai suka haifa ni da maryam qanwata wacce nafisonta da komi a rayuwa
Lokaci mai tsayi Allah baci kawowa maryam mijin aure ba kasancewar ta zurfafa cikin karatu Sam bata damu da aure ba
Lokacin aurena ya gabato lokacin mahaifina yana kan karagar mulki
Bayanda mahaifinmu beyi da maryam amma taki amincewa da zancen aurenta da dan gidan sarkin mijittafa haka ya haqura ya kyaleta da yake mutum ne mai saukin kai
Na auro hafsat acikin farin zariya saboda na yaba da natsuwarta sai dai duk lokacin da hafsat zata samu ciki zai zube wanda sanadiyar hakan yasa matan mahaifina suka tsaneta kasan cewar mahaifiyarmu bata raye
Ba irin wahalar da hafsat Natasha a wurinsu ba saboda wannan matsalar
Wata rana hafsat ta samu ciki wanda ya kasan ce shine na bakwai ajikinta sam na hana idanuna bacci ko yaushe ina roqon Allah yasa ta haifa wannan cikin lafia
Wata rana hafsat ta tashi da ciyon na quda na dauketa myka nufi asibiti da ita cikin ikon Allah hafsat ta haifa tagwaye
Na fito zan tafi masjid na hadu da wasu bayin Allah sai faman kuka matar take mijinta yana bata haquri na riqinshi ya sauwaqe mata
Nayi musu sallama suka amsa "bawan Allah lafia?
Sunanan malam Ibrahim sunan matata Aisha muna zaune lafia da ita saidai duk lokacin da zata haihu abin baya zuwa da rai shine mahaifiyata tace mayyace ita ke cinye jikokinta wannan shine na bakwai kuma Allah yayi mishi rasuwa shine Mike tunanin baqincikin da zamu fuskanta har take roqona Dana sauwaqe mata ni kuma inason matana na yarda da qadda
Cike da tausayi nake kallonsu wanda nake hango baqin cikin da yake cikin zuciyansu saboda nima acikin irinshi na fito
Dakin da hafsat take ciki na koma na dauko wanda yake hassan din na fito dashi ba tare da sun ganni ba kasan cewar hafsat tana bacci na fito na samesu
"Zan baku Dana bisa amana kuma Ku bashi tarbiya inaso ka sanyashi yayi ilmi kuma kasa ku taba sanar dashi wannan sirrin ka Santa mishi suna abdul jalal
Cike da farin ciki suke yi mishi godiya
Wannan ba komi bane saidai inaso Ku bani wanda yake naku dan na mayarwa matan dashi saboda Mu sallaceshi a matsayin Santa da ya mutu
Gawar suka bani na sanja mishi zani zuwa cikin na abdul jalal na maidashi wurin hafsat
Tun daga wannan lokaci ban qara San in halinda suke ciki ba saboda taimako nayi kuma dan Allah nayi shiyasa ban taba nemasu ba kuma ban taba bawa kowa wannan labarinba
*matsalata da Maryam*
Abdul jabbar yanada wata Biyar a duniya Maryam ta shigo gidan yayanta
"Yaya ina wuni? Lafia qalau maryama "Yaya dama mijin da zan aura ne na kawo maka" cike fa farin ciki nayi mata umurnin ta shiga dashi muka gaisa sosai na yaba da halinshi akayi shirin aure ba tare da bata lokaci ba aka aurar da maryama
Ranar da maryama ta cika wata goma a gidanta aranar Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa tashin hankalin da maryama ta shiga ya sanyata haihuwa ta haifa da namiji haka mukayi faman zaman taaziya wanda farin Zaria ba wanda beji mutuwar ba ajikinshi
Yaron Maryam yaci suna mubarak
Lokaci kadan aka dauka aka dorani akan karagar mulki
Wata rana maryam tazo tana kuka akan mijinta ya saketa wai ta zagi mahaifiyarshi wanda sam jikina be yarda da hakan ba na tura aka kiraminshi yazo na tambayeshi dalilin sakin
"Wallahi ko gobe na dawo mahaifiyata ta gayamin tayimata rashin kunya bazata zauna gidana ba
Cike da Bacin rai nake kallonshi
Nayi mishi umurni da ya kawomin takardan sakina Maryam
"Yaya ya zaayi da mubarak so kake ya tashi ba uba? Kallon mamaki nayi mata da takaici " toh ki sani ba Inda zaki bazaki koma gidanshi ba
"Yaya gaskiya banson mubarak ya tashi ba tare da mahaifinshi dan bansan wa zai kalla yaji dadi ba "Maryam kuna nufin ban isa ga mubarak din ba? Ka isa Yaya amma ai mahaifi mafine kuma baza samu kamarshi ba
"Hakane gaskiya amma kisa ni muddin kika bishi bani bake"
Tashi tayi ina kallonta tabi mijinta saboda danta mubarak
Run daga wannan lokacin ban qarajin tarihim maryama ba wannan mubarak din da zakuga mahaifinshi zakusan cewa wannan jimin mustapha azarene................
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
51-55
Jalal lafia? Ummi bacci zatayi ajina nasani kuma tafia zakuyi" kallonshi baffa yayi yana murmushi "abdul jalal kuzo ku tafi kuyi karatunku kada jalilah ta bata muku lokaci kuma mu anan zamu kwana mai martaba ne yayi umurnin hakan"
Kallon ummi yayi ta sakar mishi murmushi shima ya mayar mata "mubarak tashi ku tafi ko? Cike da girmamawa ya qarasa gaban mai martaba "abba dan Allah ka yafewa mami tabbas batayi biyayya a gareka ba kuma tayi maka rashin kunya, abba ka yafeta dan Allah nasan mami rayuwa kawai take ba tare dajin dadi ba saboda abinda ta aikata kuma nasan gudun zuciyanka ne yasa bata dawo ba kuma tunda mahaifina ya rasu ka yafe mishi laifinda yayi maka,,, "mubarak kana nufin mahaifinka ya rasu? Abba ni bansanshi ba saboda inada shekara biyu ya rasu daga wannan lokacin mami ta dawo Kaduna da zama"
"Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un" abinda mai martaba ya samu damar furtawa kenan daganan ya tashi ya nufi dakinshi ba wanda ya yiwa magana acikinsu
Kallon mubarak jalal yayi "muje ko? Murmushi mubarak yayi rana ta farko da jalal yaga tsantsar damuwa a tare da mubarak din dan sam baya sanya abu aranshi
Hannunshi mubarak ya riqe sukayiwa su ummi sallama
Sam jalal be kalli inda mami take ba haka be kalli cool A J ba
Kallon jalilah yayi "gobe kafin ki wuce zan saya miki kayan" dariya tayi "ya jalal wannan wayon fa? Ai bazan hanaka tafia ba" murmushi yayi suka juya
"Mami let me drop them" no thanks,,, cewar jalal
Mamakine ya cukasu shida mami yaja hannun mubarak suka fice,, kallonshi jalilah tayi tana daria "Allah ya jalal bayada gwani gara ma kada ka sanya kanka cikinsu kaga ai ko ya mubarak yanda yake fama dashi" sosai cool AJ yaji zafin abinda jalal yayi mishi ko ba komi ai shi twins brother dinshi ne sufa jini daya ne
Tafia suke yana tsokanar mubarak har suka sami a daidaita sahu suka qarasa cikin school
Bayan sunyi wanka mubarak ya kalli jalal "jalal sai dai akwai abinda kayi wanda baka kyauta ba dolene muyi haquri abdul jabbar dan uwanmu ne ba yanda za muyi fa abinda kayi gaskiya baka kyauta ba"
Kallon wulaqanci jalal yayi mishi "Allah kada ka qara yimin irin wannan kallon"
Murmushi yayi ya kawar da kanshi "jalal pls kada ka qara yi mishi haka" mubarak Allah sai ranar da ya karbi kuskurenshi ya baka haquri zan kalleshi a matsayin mutum" ido mubarak ya zare "wai kai wane irin mutum ne mai kafiya? Kwanciya yayi dan ya gaji da surutun da mubarak yake sanyashi
Waya yake da mami yana sanar da ita duk abinda ya faru "mubarak yanzu kana nufin jalal din yaron Yaya mahmud ne? Ikon Allah
"Mami ki shirya kizo ki nemi gafara a wurin yayanki dan Allah" murmushi tayi "mubarak gobe zanyi sammako in shaa Allah
Yauwa mami sai ki taho mana sinasir kinsan jalal yana sonshi sosai
Murmushi tayi aranta tanajin dadin yanda mubarak da jalal din suke son junansu duk da jalal din ba wani magana yake da ba
Washe gari da sassafe mami ta kira jalal tana shaida mishi tana cikin school din
Sauri yayi ya shirya "jalal ina zaka? Be kulashi ba yayi sauri ya fice
Cike da girmamawa ya gaidata "jalal mubarak din fa? Sunkuyar da kanshi yayi "baka gaya mishi nazo bane? Yanajin bacci ne shiyasa bn gaya mishi ba
Murmushi tayi "ai ya fito dan gidan yaya mahmud zamu tafi" kiranshi yayi a waya ya sanar dashi zuwan mami
Gaidata yayi tare da yi mata sannu da zuwa
"Mami ke kikayi driving da Kanki? Eh muje ko? Bata suka shiga ga baki dayansu taja suka tafi
Cike da sallama ta shiga ciki sai faman miqa gaisuwa barorin gidan suke saboda akwai wadan da suka santa acikinsu
Kallon juna suke itada mami "maryama" da sauri ta qarasa wurinta "aunty hafsa ina yaya" hannunta taja suka nufi dakinshi sukayi nocking yayi musu izinin shiga da sauri ta qarasa gabanshi ta fashe da kuka "Yaya dan Allah ka yafeni nasan na saba maka banyi mana biyayya ba"
Zama yayi ta zube a gabanshi "maryama ban riqe ki da komi ba kuma kafin ki roqeni gafara na Riga na yafe miki
Kusa dashi ta matsa "Yaya da gaske ne labarin da mubarak ya bani? Murmushi kawai yayi tasan me hakan yake nufi
Zaune suke cikin parlour din ya kira Ummi ya sanar da ita suna gidan
Zaune suke suna gaisawa dasu ummi
Mai martaba yayi gyaran murya suka qaraso shida mamin mubarak da kuma hajiya hafsa
Gaisawa akayi da juna wanda mai martaba yana Kyle da jalal shi kadaine be gaida kowa ba sam be daga kai ya kallesu ba
Cool AJ ne ya shigo yaje ya kwashi gaisuwa duk wanda yake dakin ba wanda be gaida ba ya nemi wuri ya zauna
"Ikon Allah, aunty hafsa wadan nan tagwayen mazan duk ke suka kwaso
Amma dai voice din kam nawane dan tun a jalal na gane hakan sai kuma ga abdul naji shima duk daya ne
Sallama mai martaba yayi dasu saboda zai shiga fadasukayi mishi fatan alkhairi
"Mami za muje school saboda munada lectures" kai nifa bazani ba,,, kallonshi jalal yayi "lectures din ne baza kayi ba? Eh,,, dariya jalillah tayi "ya mubarak sai kayi tayin abu kamar yaro qarami Allah" kawar da kanshi yayi "mami ni zan tafi" mubarak tashi kuje mana,, Ummi Allah ba wani lectures bane kawai shi idan yana kusa baa missing lectures ne" murmushi baffa yayi "mubarak tashi Ku tafi mana"
Tashi yayi yana qunaquni ya fice kadan jalal yayi dariya wanda ya fito da kamanninshi da mahaifiyarshi yabi bayan mubarak din
Kai mami ta girgiza "mubarak Allah ya shiryeka dan ni bansan irin wannan halin naka ba"
Mami ya jalal ne ya takurashi ai,,, jalilah meye laifin wanda yace kaje Neman ilimi? Dariya kawai tayi
"Mami zan tafi school inada lectures nima" shine ka bari 'yan uwanka suka tafi? Cewar mamin mubarak
Kallon maminshi yayi "mami ya jalal fa bayason tafiya dashi jiyama haka yayi mishi" kamar ya? Ai wannan shashanci ne ta kirasu a waya suka dawo
"Mami gani" meyasa Baja kula dan uwanka? Kallon mubarak yayi ya dawo da kallonshi gun mami
Au bazakayi magana ba? Sunkuyar da kanshi yayi
"Mami Allah
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 13