har yayi bacci jalal be daina ba
Kallon ummi yayi tare da kwantar dashi da kyau "gobe zanje kafancen" Allah ya kaimu, tashi kawai yayi ya fice
Kallo mami tabishi dashi tare da yima Allah godiya........
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
76-80
Tsawon lokaci ya dauka yana bacci kafin ya samu tashi daga bacci
Kallonshi ummi tayi ta sakar mishi murmushi ya tashi ji yake kamar yayi wani aikin gajiya
"Tashi kaje kayi wanka" ba musu ya tashi har mamakin lokaci yayi
Washe gari jalal yasa mubarak yayi mishi rakiya zuwa kafancen sukaje
Kallonshi kawai yake yana yana diba sayyun itatuwa
Wai me zakayi dasu ne? Ummi ta sani nemansu mana
Haka suka gama abinda suke suka dauko hanya suka dawo zariya
Kallonshi mubarak yake yana hada sayun ya gama ya hada man shafawa
Sayyun itatuwa da zaitun da habbatus sauda
Zanje wurin ummi,,, harara yayi mishi ya tashi shima ya sanja kaya zuwa irin na jalal din
Cike da girmamawa suka gaida ummi "jalal ka gama hada maganin? Eh kawai yace "toh muje ko?
Part din mami suka nufa harda mubarak din
Suka sameta kishingide ta tashi zaune suka gaidata
Ummin jalal dazu ko na tura a kiraki akace bacci kike
Ciyon kaine ya sani bacci
Toh da sauki dai ko? Alhamdulillah gaskiya
Abdul din fa? Bari na kirashi yanzu ya bar nan ta daga waya ta kirashi ya shigo da sallama
"Ummi wannan zai riqa shane wannan kuma zai riqa shafawa ne idan ze kwanta"
Toh meye matsalan? Sai bayan kwana uku zan gaya miki
"Bros jalal na menene? Ko kallonshi beyi ba bale ya bashi amsa
Bakaji me yake cewa bane? Kallon mubarak din yayi ya aiko mishi da saqon harara
Murmushin dole yayi tare da kawar da kanshi
Ummi zamu koma school
Ummi kin soya nama? Mubarak jalilah ce ta cinye sauran saidai kazo anjima ko gobe
Wannan yarinyar ta fiye kwadayi wallahi
Kallonshi jalal yayi "toh meye damuwarka? Ba shiri jalal yayi dariya dan yanayin yanda mubarak din yayi magana ba kadan ya bashi dariya ba
"Wai jalal idan ba mubarak ba ba wanda yake sanyaka dariya ne kome? Ummi dan Allah ki daina yanzu zaice saboda nayi mahaukaci dashi ne
Dariya sukayi lokaci daya mubarak da jalal suka tashi har sun kusa fita daga dakin jalal ya juyo yana kallonshi alama yayi mishi da yazo
Wuri ya nema suka zauna mubarak kam tashi yayi ya matsa yana amsa waya
Kallonshi jalal yayi cikin ido
"Ka riqa addua kafin ka kwanta ka daina sauraren waqoqi nan da kake saurare basu da amfani ga rayuwarka" CD plate ya bashi "ka sanyashi acikin motanka ka zubar da wadan nan" kai ya gyada mishi yana murmushi
"Giya illa ce ga rayuwarka ka daina shanta kafin kayi dana sani" nan ma kai kawai ya gyada mishi
Jalal ne ya fara tashi yana kallon mubarak "malam wayan nan ya isa haka mana"
Kashe wayan yayi "jalal Allah yunwa nakeji" dariya yayi tare da kawar da kanshi daga kallon mubarak din
"Toh muje" wai ka dafa wani abune da zakace muje,, part din ummi mubarak ya nufa
Binciken food flacks din ya fara "yauwa ai da sauran naman"
Jalilah ce ta shigo da alama daga school take ko kallon jalal batayi ba shige kawai
Bayanta yabi ya sameta tsaye kusa da mubarak sai shagwaba take zuba mishi
Tana ganin jalal kawai tayi ciki yabi bayanta
Hijab dinta ya cire ya qaraso kusa dashi "jalilah fushi kike dani?
Kyaleshi tayi "bazakimin magana ba? Ya qaraso kusa da ita har suna juyo numfashin juna "gayamin me kike yima fushi? Ba komi
Amma kike fushi? Ya fada a raunane "toh meyasa jiya kazo na hangoka ina sauri kawai ka fice dan kada ka ganni" murmushi yayi "sorry ummi ce ta aikeni shiyasa kikaga ban tsaya ba" juyawa tayi da sauri ya juyo da ita "bazaki daina fushin ba? Toh zaka sayamin ice cream? Dariya yayi cike da qasa ita
Zan saya miki,, dariya tayi ta fada jikinshi rabata yayi da jikinshi bari naga ko mubarak ya gama zamu tafi ne "ya jalal" juyowa yayi yana kallonta "hhhhhh yau kunyi kyau" murmushi kawai yayi ya fice daga dakin
Zaune ta samesu ta zauna kusa dashi "ya jalal na samu qawa tanada kirki sosai" kinsan banason wannan shirmen ko? Maza ki rabu da ita
Kwantar da kanta tayi ajikishi "ya jalal kayi haquri Allah tanada kirki sosai"
Murmushi mubarak yayi ganin yanda suka kafe juna da ido gashi ta wani shigewa jikinshi kamar wata mage
"Ya jalal kayi haquri? Kai ya gyada mata har lokacin tana jikinshi
Ummi ce ta shiga kallonsu tayi ba wanda ya kula da ita cikinsu jalilah hankalinta yanaga chatting din da jalal yakeyi "jalal meye haka?
Ummi menene? Harara tayi musu "ko yaushe sai fadan da nake maka bazai shiga kunneka ba ko? Jalilah Allah na qara ganinki jikin jalal rankin zai baci" kallon juna sukayi
Tsawa ummi ta daka mata da sauri ta tashi ta nufi dakai tana kuka
Tashi yabi bayanta ya sameta kwance tana kuka
Dariya yayi "jalilah tashi kiji" ba musu ta tashi
Share hawayenki kiji,,, Ta share hawayenta "banason kina yawan kuka kinsan banason wannan kukan ko?
Toh me nayi takemin fada? Ya isa banason irin wannan surutun
Jikinshi taje ta kwantar da kanta "yaushe zaka kawomin ice cream din? Tashi yayi "anjima zan kawo miki amma ki tabbatar kinje islamiyya
Kai ta gyada ya fice ya sami mubarak sukayiwa ummi sallama suka fice..............
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
81-85
Sai mami tayi da gaske kafin cool AJ yasha maganin sai yace ba dadi tsawon kwana uku kenan ummi ta kira jalal "jalal ba yaune zakazo ba? Ummi muna hanya ai"
Zaune suke a parlour'n mami ta kira cool AJ yazo suka gaisa
Kallonshi jalal yayi da kyau "zo nan" ba musu yaje amma gaskiya ji yake kamar zuciyanshi zata fashe ga baki daya ji yake ya tsani jalal din
"Mubarak zo ka gani" ba musu ya matsa kusa dashi "riqemin babban yatsanshi" haka ko akayi kallonsu kawai mami da ummi suke
Wani magani ya fitar ya fara shafa mishi acikin kanshi ko ina kafin ya shafa mishi a face dinshi
Hade face yayi yana yiwa jalal mugun kallo "wai me kakeyi ne haka? "Mubarak sakeshi kawai
Karatu jalal ya fara yi ba tare da ya riqeshi ba da sauri ya tashi ya shiga zaga dakin jalal ko kallonshi beyi ba yaci gaba da karanto ayoyin al Quran
Tsawon lokaci yana karanto ayoyin masu ratsa zuciya cool AJ sai faman zaga dakin yake
Cike da razana suke dafe kunnayensu sakamakon qarar da yayi ya fadi
Kusa dashi jalal ya matsa yaci gaba da karatun ahankali bakinshi ya fara motsawa
Shuru jalal yayi yana kallonshi
" 'yata ke sonshi ni kuma ba abinda zata nema na bari ta rasashi"
A iya tunaninki akwai aure tsakaninsu?
Wannan ba damuwata bace
Idan na qonaki nayi laifi?
Kada kayi haka
Meyasa kika bata rayuwanshi?
Bani bace,,, "qarya kike" dan murmushi yayi
"Idan har banyi hakan ba duk mace ta gari zata soshi daga baya na gane hakan ba mafita bace sai na sanya tsanar mata acikin zuciyanshi"
"Abu mai sauki ne na qonaki amma zanyi miki adalci"
Kada kayi tunanin zan rabu dashi dan 'yata ko yaushe tana ganinshi tana kasancewa cikin farin ciki ni kuma bazan rabu dashi ba"
Kinsan a ina 'yarki take yanzu?
"Ka daureta acikin jikinka"
Kinsan dalilin yin hakan?
Aa
Jikina tamkar garwashi yake a wurinta zan azabtar da ita kafin in qonata ne kamar yanda zan qonaki
Amma kasan sauran 'ya'yana bazasu barka ba?
Murmushi jalal yayi "ba abinda zasu iya dani dan ke kanki biki iya aikata komi ba"
Kana ganin idan kayi hakan zaka zauna lafia?
Murmushi yayi ya fara karanto wasu addu'o'i
Nan take ta fara ihu
"Zan barshi basai ka qonani ba" sam jalal be saurara mata yaci gaba da qonata
Tsawon lokaci tana ihu har tazo ta daina ga baki daya
Shuru yayi yana kallon cool AJ
Sanyayar ajiyan zuciya ya sauke
Dafe zuciyanshi yayi "ummi bani ruwa" da sauri mubarak ya miqa mishi yasha
Duk idanunshi sun sanja zuwa ja kallonshi kawai suke
"Jalal lafia? Kai ya girgiza sai faman gumi yake
Lokaci daya kuma ya fara kakkarwa "jalal wai lafia?
Ummi ta riqeshi
"Mubarak tashi ka fita"
Lafia? Tashi nace
Tashi yayi yana tafia yana waige
"Ummi dan Allah ki yafeni ba lallai bane na rayuwa kuma nayi hakan ne saboda abdul jabbar ya samu lafia nasan zasu ilkatani amma nayi miki alqawarin zan qonasu kafin nabar duniya, ummi dan Allah kada ki bari mubarak ya shiga wani hali akan rashina"
Jalal meyasa kayi haka? Cewar mami duk hankalinta ya tashi
"Ummi bani ruwa " karatu ya shigayi yana tofawa a ruwan tsawon lokaci kamar numfashinshi zai dauke
Zubawa yayi ajikinshi wani zafi yaji duk ya fita hayya cinshi
Daqyar yake numfashi
Ahankali har ya fara samun natsuwa mami ga baki daya hankalinta atashe yake sai faman jera addua take
Ahankali ya dago yana kallon ummi "ummi zai dauki tsawon kwana uku yana baccin nan a nemo wadan da zasu sanja mishi wurin kwanciya
"Jalal kai kuma fa? Kallonta yayi
"Ummi jinin da yake jikina kadan ya rage bazai wadaceni na rayu ba" nan take ummi ta gane matsalar saboda ta taba faruwa da baffa
Da sauri ta kira mubarak "muje a kaishi asibiti da wuri a qara mishi jini kafin ya mutu"
Jinin mubarak aka fara gwadawa cikin sauri aka fara qara mishi jinin
Duk wannan abinda da ake mai martaba be sani ba haka baffan jajal
Mami kam hankalinta be kwanta ba ta kira mai martaba ta gaya mishi halinda ake ciki
Da sauri suka nufi hospital din har ya fara bacci mubarak kam har idanunshi sun kumbura saboda kukan da yake
A&E ga baki daya cike take saboda zuwan sarki Mahmud
Kallonshi baffa yayi yayi murmushi "Aisha yaron nan naki bayada jarumta fa" haba baffan jalal na'ima saida aka qara mana jini" toh meye abin roqon gafara?
Murmushi mai martaba yayi
"Allah ya bashi lafia" suka amsa da ameen
Kallon mubarak yayi ya sakar mishi murmushi
Zaune suke tare da baffan jalal "wannan shine na farko da yayi shiyasa kuma bata bayn gida yazo musu ba saboda zuciyanshi ta riga ta kawo kawai ya tunkaresu
Murmushi mai martaba yayi
Zaune suke gaban AJ sai faman bacci yake
Kallon mai martaba baffa yayi "sun cutar da yaron nan ba kadan ba kuma matsalan basu zauna ajikinshi ba bale a gane da wuri" jinjina lamarin mai martaba yayi
Washe gari jalal yana kwance ya juya yana kallon mubarak murmushi sukayi juna
Mamin mubarak ce ta shigo suka gaidata tayi musu ja jiki
Abinci ta zuba musu sai faman hararan jalal mubarak yake "malam lafia? Meye damuwarka dani? Kawar da kanshi yayi yana murmushi
**********************************
Da salati ya bude bakinshi ahankali ya fara bude idanunshi ya qarewa dakin kallo
Sannu mami tayi mishi jin zuciyanshi yake kamar an dake mishi dotse akanta
Kallonta yayi "mami jalal fa? Murmushi tayi mishi
Je kayi wanka kazo ka rama sallar kwana uku
Ido ya zare "mami kwana uku fa? Kai ta gyada mishi
Tashi yayi ya nufi part dinshi yayi wanka ya shiga reja sallolin da make binshi
Ba yanda ummi batayi ba akan jalal yazo su tafi gida yace shi school ze tafi dole mubarak ya haqura yabishi suka tafi............
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
86-90
_Allah ya gafarta miki aunty amina yasa aljannah ce makomarki_ *ameen*
Kwance suke bayan sunyi wanka kowa da abinda yake tunani aranshi, wayan jalal ce tayi ringing ya diba yaga new number ne ya daga tare da kwarara sallama
Ta dayan bangaren kuma cool AK ne ya amsa "bros jalal where r u? Shuru yayi kamar bezeyi magana ba
"Hello" sai a lokacin yayi magana "am in d hostel" okay which room you guys r? "7" okay ya katse wayan
Kallonshi mubarak yayi "waye? Abdul"
Ni dan Allah ka hadamin kunu Allah shi nakeso nasha
"Kai bazaka iya bane? Eh bazan iya ba
Ko kallonshi jalal beyi ba bale ya tashi
Sallama yayi suka amsa mubarak ne kawai ya tashi amma jalal sam bayada alaman tashi suka gaisa
"Bros jalal jikin ne? Kai ya girgiza mishi alaman aa
Murmushi yayi ya zauna kusa da mubarak suka dan fara taba fira
"Jalal amma kasan inajin yunwa ko? Tsaki yayi ya sauko ya dora ruwan zafi ya dama mishi kunu ya zuba a cup saura kuma ya juye a flacks
Qin dauka mubarak yayi "Allah idan yayi sanyi kamin magana zakasha mamaki" toh ka bani ne? Ya fada yana hararan jalal din
Murmushi cool AJ yayi "you guys r very funny"
Kwanciya jalal yayi abinshi mubarak yaqi daukan kunun tsaf jalal yasan mubarak ba dauka zeyi ba ya sauko ya dauka ya bashi "sai ka zubamin ajiki ne? Eh ya bashi amsa
"Bros mubarak wai haka kuke fada? Bakasan waye cool jalal ba ai wallahi hurt jalal yafi dacewa dashi
Aiko jalal saida yayi dariya dan mubarak din ya fiye rikici
Haka mubarak da cool AJ suka sha fira abinda mubarak ya fahinta kusan halinsu daya kawai dai abdul din yafi jalal yawan magana
Lokacin sallah ne yayi mubarak yace ba inda zashi a ciki zeyi sallah
"Allah baka isa ba sai kaje" sai kamin dole "sai fa kaje" tsaki kawai yayi jalal yazo yayi tsaye gabanshi suka shiga kallon juna
Jalal kasan dai baa wasa da sallah ko? Sai fa kaje masjid din
Tsaki yayi ya janyo kaya irin na jalal din ya sanya yayi gaba jalal yabi bayanshi yana dariya
Sosai cool AJ yaji sun burgeshi shida jalal ne a baya mubarak yana gaba suka qarasa cikin masjid din jalal yaje kusa dashi ya tsaya
Sosai ya basu dariya ganin ya sanja wuri
Jalal da AJ ne suka daidaita suka fara yin sallah AJ yan bin jalal har suka kammala
Mubarak ya rigasu fita ya nufi hostel
Lokaci daya suka dago dan satar kallon juna aiko suka hada ido jalal yayi sauri ya kawar da kanshi murmushi AJ yayi
"Amm rakani mana" kallonshi yayi "akwai wanda nakeson gani" juyawa sukayi
Kowa ya gansu baya buqatar tambaya yasan jini daya ne
Wuri ya nema ya zauna yana jiranshi ya gama magana da AK ya juyo yana kallonshi tare da sakar mishi murmushi ya tashi kawai suka fara tafia
Kallonta yake yana nazarin wasu abubuwa kallonshi ya maida ga hannunta ba alaman jin ciyo har ta kawo kusa dasu ba tare da kallesu ba ahankali ya sauke ajiyan zuciya wanda ya sanya jalal ya kalleshi
Hanya jalal ya sanja yaje ya siyo coke guda biyu suka nufi hostel
Kallon coke din mubarak yayi jalal yayi mishi harara ya cire kayan jikinshi
Supergetti da kifi jalal ya dora sosai ya bawa abdul dariya ganin yanda yake girkin kamar mace ya kammala ya juye a food flacks ya tashi ya fita
Be jimaba ya dawo da qanqara a hannunshi ya fasa ya ya zuba a cups ya dauko plate ya ajiye musu kawai ya nufi toilet yayi wanka
AJ tunanin yanda zeci abincin yake dan ganin yake bazaiyi dadi ba haka ya zuba abincin yakai spoon daya a baki
Sosai yayi mamaki test din abincin
Kallon mubarak yyi yaga shi sam hankalinshi baya kanshi ci kawai yake
Ba wanda ya kalla daga cikinsu ya sanja kaya da alama fita zeyi
"Malam ina zaka? Meye damuwarka? Bafa inda zaka
Tsaki kawai yayi ya mayar da kayan ya dauki ragowar abincin mubarak yaci kadan yayi kwanciyarshi
Haka suka wuni a hostel din AJ sai faman dariya yake ganin fadane kawai tsakanin jalal da mubarak kuma ba wanda yake tsallake zancen wani
Sun gama sallah isha cool AJ ya kallesu cike da murmushi "bros zan tafi bacci nakeji" dariya mubarak yayi toh muje muyi maka rakiya ko?
Tafiya suke sai mubarak ne kawai yake zuba surutu
Wurin da yayi parking suka tsaya ya bude motanshi ya shiga ya tada motan "bros abdul ka sayamin ice cream wa jalilah dan Allah" cewar mubarak
Kallonshi yayi yana murmushi tare da gyda mishi kai sukayi sallama dashi suka juya
Kallonsu yake suna tafia da alama jalal magana yake yiwa mubarak kuma serious magana ce
Waya take har ta qaraso ta wurin da cool AJ yake
Kallo daya tayi mishi ta kawar da kanta tayi taci gaba da tafia kamar ya tsayar da ita kuma yaji sam bazai iya yi mata magana ba har ya daina hangota
Gida ya nufa cike da tunani a zuciyanshi
Tsawo sati daya cool AJ ko yaushe a hostel yake wuni idan sunada lectures su tafi su barshi haka shima idan yanada zai tafi ya barsu
Yau ta kama sunday jalal ya kalli mubarak "malam ya dace kayi aski fa" tsaki yayi
Bros abdul muje dan Allah tunda ya fara zancen askin nan sai nayishi gara na tafi kafin ya batamin
Dariya jalal yayi ya sanja kaya suka fito
Duk yanda abdul AJ yaso su tafi a mota sam jalal yaqi haka suka taka da qafa suna tafia
Tafe suke itada salma sai faman dariya salma take mata
Tunda ya hangosu yanayinshi ya sanja tafia kawai yake
Duk yanayin da yake ciki jalal yana kule dashi haka mubarak amma ba wanda ya nuna mishi
Aski akeyiwa mubarak jalal yace acire gashin ga baki daya wani kallo yayiwa jalal "Allah baka isa ba" sai fa an cireshi duka
Tsaki yayi yana kallon mai shagon "malam dan Allah cire duka sauri nake" dariya jalal yayi "kada ka cire duka yi mishi wanda ka saba yi mishi" kallonsu kawai cool AJ yake amma hankalinshi baya wurinsu har suka kammala suka nufi hostel
Kwanciya yayi yana tunanin juwairiya shin dagaskene ya yanka mata hannu ko mafarkin hakan ne yayi? Wa zai amsamin?
Tashi yayi ya dauki wayanshi ba tare da yayi musu magana ba ya fita ba wanda yayi mishi magana daga cikinsu
Duk inda yake tunanin zai ganta ya diba ba alamanta har ya haqura ya nemo wuri ya zauna
Tun kafin su qaraso ya ganeta yayi saurin tashi ya nufesu
Sosai juwairiya taji zuciyanta ta buga dan tasan ba kirki ne da cool AJ ba
Cak ta tsaya suka zubawa juna ido,,, cike da qarfin Hali ta fara yi mishi magana "malam lafia? Salma kam gaba tayi tana murmushi
Tsaki taja tabi gefenshi zata wuce
Cike da mamaki Salma take kallon ikon Allah ganin yanda cool AJ ya janyo juwairiya ya hanata da qirjinshi ahankali ya furta mata "am very sorry pls"
Janye jikinta tayi da sauri tana hararanshi
Da sauri ta nufi wurin salma
Kallonta Salma take taja hannun Salma suka nufi hostel
Kallonta salma take duk tayi wani iri "juwairiya kinga fa guy din nan ya cika da rainin hankali kamata yayi kasan abin yi tun da wuri"
Kwanciya kawai tayi lokaci kadan tayi bacci har mamaki salma take
Hostel ya nufa kallo daya jalal yayi mishi ya fahinci akwai abinda yake damunshi
Sam AJ yace bazaici abinci ba wani kallo jalal yayi mishi
Key dinshi kawai ya dauka ya nufi hanyar fita "abdul" jalal ya kirashi ya juyo yana kallonshi
Something bothering you and your keeping it to yourself, right? Murmushi kawai yayi ya juya ya fice
Kwanciya jalal yayi yaci gaba da aiki da system dinshi
Kallonshi mami take tana nazarinshi "abdul meke damunka ne? Kamar zeyi kuka yake kallonta "mami kamar a mafalki na yake hannunta fa amma fushi nake dani kuma ni sonta nake" kai ta girgiza tana murmumshi
Ya gaji da zaman da yake ya tashi ya fita sai faman fushi yake
"Ya abdul fita zakayi? School zan tafi" jirani dan Allah zan bika
Da sauri ta nufi part din ummi ta sanja kaya suka nufi school din
"Bros jalal suna lecture fa" ba wurinshi zan tafi ba wurin sis juwairiya" da sauri ya juyo yana kallonta "jalillah kinsanta ne? Ya mubarak ne yake sonta " sosai yaji zuciyanshi ta buga wani tashin hankaline ya ziyarceshi...............
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
91-95
Kallon juna suke shida ita ganin tayi duk ya fita hayyacinshi har ya fara zufa "ya abdul lafia? Girgiza kanshi yayi "by 2 zan gama abinda nake sai ki fito"
Sam AJ beyi attending lecture ko daya ba saboda baya cikin hayyacinshi
Kasancewar mubarak yanajin yunwa ya sa jalal ya fito shi kadai yaje sayen kayan da suke buqata
Kallonshi ya tsaya yi sam baya tare da natsuwa
Kusa dashi yaje ya dafashi
Kallon juna suke na tsawo lokaci kafin AJ ya sauke ajiyan zuciya
"Meke damunka? Murmushi ya qaqalo wanda ya sanya jalal qara hade face dinshi
"Gayamin meke damunka? Bros jalal abubuwa sunata zuwanmin kamar a mafalki ne kawai" tsaki yaja
"Wai atunaninka bansan damuwarka bane? Juwairiya right?
"No na haqura da wannan yarinyar kabar zancenta" meyasa? Amma kasan mubarak ne yake sonta ko?
Dariya jalal yayi yana kallonshi "mubarak din ne ya gaya maka hakan? No jalilah ce tare ma mukazo da ita tana wurin juwairiya din"
Sosai yake kallon jalal yana dariya "abdul meye abin dauka acikin zancen jalilah? Toh ba gaskiya bane dan baya soyayya idan kana sonta kaje ka gaya mata kawai
"Bazata saurareni ba" why? Bayanin abinda ya faru yayiwa jalal
Ka bata haquri kuma? Kai ya gyada mishi
Tashi ka rakani
Tafia suke jalal yanajanshi da fira ahankali yake amsa mishi jalal kam mamaki yake yanda soyayya take mayar da mutum haka
Harara mubarak yayi musu "kawai daga zuwa sayen tulare sai kayi zamanka" meyasa bakaje nemana ba?
Kai waramin yarone da zanje nemanka? Tsaki jalal yayi mubarak ya matsa kusa dashi
"Bawan Allah ai yau zaka yi mana dan wake ko? Kakan wake zanyi" sai a lokacin AJ yayi dariya "sai fa kayi mana"
Duk yanda yake cikin damuwa idan jalal da mubarak suka fara rikici dole ne yayi dariya
"Bros jalal nifa zanci" sai ku girka,,, kwanciya AJ yayi tare fito da wayanshi ya bude email dinshi
Zama jalal yayi ya janyo system dinshi ya shiga aikin gabanshi
"Bros jalal wai bazaka yi mana ba? So kake yunwa ta illatamu ne? Tsaki yayi ya kashe system din ya dora ruwa suka shiga dariya
Allah za kuyi girkin nan da kanku
Ba wanda ya qara yin magana daga cikinsu sai faman dariya suke qasa qasa
Zuba musu yayi a plate yaje yayi wanka ya dawo ya sami AJ sai faman sauri yake ya kammala
"Ba kyau fa" jalilah jirana take kada tayi gaba" wallahi yafi komi sauki indai jalilah ce "
Rakiya mubarak yayi mishi "kaga bari na koma banason fitina ka gaida su mami"
Kallonsu yake har suka qarasa kusa dashi sai faman fira suke suna dariya
"Ya abdul sis juwairiya tayimin dan wake" murmushi yayi "muje"
Kallon juwairiya tayi "sai nazo muje wurin ummi ko? Kai ta gyada mata tana murmushi
Ta shiga motan yaja jalilah na daga mata hannu
*9:30pm* duk mubarak yayi bacci jalal ya shirya tsaf ya fita sai zuba qanshi yake ya nufi wurin da yasan zaiga juwairiya
Cikin saa ya ganta ita kadai zaune tana rubutun project dinta yayi mata sallama ta amsa ya nemi wuri ya zauna
Kallonta yayi tayi saurin sunkuyar da kanta "juwairiya right? Kai ta gyada mishi
Murmushi yayi yana kallon system dinta "project kike typing? Zan turawa supervisor dina ne a email dinshi
Karba yayi yana kallo tare da murmushi
"Sorry zan iya yi miki correction? Kai ta gyada
Janyo system din yayi ya shiga typing yana gyara mata cike da mamaki take kallonshi har ya kammala tanada yaqinin da itace ko rabi batayi ba
Kallonta yayi cike da natsuwa "juwairiya nasan kinajin zafin abinda abdul yayi miki wanda nasan hakan ba dadi amma inaso ki fahinci abdul mutum ne mai kirki saidai matsalan rayuwa da ya samu nasan ke kanki kinsan ya sanja yanzu,, cike da natsuwa yayi mata bayanin abinda ya faru da cool AJ ba abinda ya boye mata ,,, "juwairiya abdul yana sonkine bawai da wasa pls ki bawa zuciyanki haquri for God sake" sam juwairiya batayi tunanin abinda jalal yazo mata dashi kenan ba
Kallonta yake yana jiran yaji me zatace "pls say something" ahankali
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13