nayi mishi magana amm biki amsar da ya bani ba? "Jalal d u want us to fight? Kai ya girgiza "toh ka sanja" kai ya gyada mata
"Mami rantsuwa fa yayi akan bazai kalleshi a matsayin mutum ba har sai ya bani haquri akan bigeni da yayi
Fada Ummi ta fara yima jalal "yaushe ka zama haka shi din an gaya mana as on ranshi yayi ne? Dan Allah ummi kiyi haquri,,, naji amma banason wannan fadan kaji na gaya maka? Kai ya gyada kuma Ku tafi tare nan ma amsar daya ce
Kusa ummi cool AJ yaje ummi sai mun dawo
Mubarak da cool AJ ne a gaba jalal yana bata suka qarasa cikin school din
Kallon mubarak yayi tare da sakar mishi murmushi "am very sorry mubarak" kai ya gyada mishi suka fice shida jalal yana hangosu suna dariya saboda tsokanar jalal da mubarak yayi sai abin ya basu dariya
Wani tunani ya zowa mai martaba ya umurci su Ummi dasuyi sati daya a cikin masarautar wanda hakan sam beyiwa jalal dadi ba
Zaune suke shida mubarak suna sanye da kaya iri daya
Da gudu ya shigo da mota yayi parking ya fito ya haye saman motan ya shiga zuqar sigari kallon juna sukayi wanda sam cool AJ be gansu ba
Jalal kaga me abdul yakeyi? Tsaki yayi "toh meye damuwarka? Dariya yayi
Cike da yanga take tafia tana waya har ta qaraso kusa da cool AJ "mummy dan Allah ki bani" cak ta tsaya dan bata kula dashi ba
Tsaki taji yayi ya kawar da kanshi daga kallonta
"Jalal gafa qawarka cen" sam be kallesu ba ya tashi mubarak yabi bayanshi yana dariya
Kusa da cool AJ suka so sam basuyi tunanin zeyi musu magana ba
"Hi bros" "morning,,, Cewar mubarak "hey bros jalal excuse me pls
Juyowa yayi yana kallonshi "ka bude wayanka mana Ummi zatayi magana dakai
Juyawa kawai yayi yaci gaba da tafia............
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
56-60
Kallonsu juwairiya tayi cike da mamaki daman 'yan uwane amma suke haka? Duk yanda akayi tagwayene
Sam cool AJ be qara kallonshi ba yaci gana dashan sigarinshi
************************************
Zaune yake cikin school tare da jalilah da mubarak
Jalilah kije mubarak ya maidaki gidan anjima zamu shiga lecture,,, aa bazani ba
Kallonta mubarak yana dariya "zo muje in badaki ajiya kafin mu qarasa lectures din"
Sallama yayiwa juwairiya suka gaisa "amm nace kinada lectures ne? Aa lafia dai? Dan Allah ga qanwana ajiya zan shiga lecture ne"
Murmushi tayima halillah "zo ki zauna" godiya yayi mata ya juya "ya mubarak" ya juyo yana kallonta "hhhhh karku dade fa kuma kazomin 😉 " aiko ya shiga dariya tare da girgiza kai ya tafi
Kallon ta juwairiya tayi cike da murmushi "ya sunanki? Jalilah? Wow nice name,, amma brothers dinki twins ne? Dariya tayi "ya jalal da abdul ne twins ya mubarak qaninsu ne amma maminshi itace qanwar mai martaba" okay kice ke gimbiyace
Aa fa ni qanwar ya jalal ce,,, kenan ke gimbiyace ni ba 'yar sarki bace fa,,,
Toh ke wacece? Cike da quruciya jalilah ta bawa juwairiya labarin komi har dariya juwairiya take saboda yanda jalilah ke magana
"Muje hostel kici abinci ba yanzu zasu fito ba"
Zaune suke jalilah taci abinci har ta qoshi suka shiga fira da juwairiya
"Bari na danyi bacci kafin su fito ko? Kai ta gyada mata
Sosai ran mubarak ya baci dan ba inda basuje nemanta ba amma basuga juwairiya ba kuma ba jalilah
"Jalal ka dauki abinnan da wasa fa? Tsaki yayi "kafi kowa sanin halin jalilah fa maybe itace ta janyeta sukayi wani gu daban"
Tafe suke sai faman dariya jalilah take daga nesa ta hangosu ta qaraso wurinsu da sauri "ya jalal kun fito?
Tsaki mubarak yayi "ina kika je? Hostel nayi bacci
Meyasa? Meyasa nace!!!! Ke bakida hankali ne? Ko bikisan zamu nemeki ba?
Kallon mamaki juwairiya take mishi "ya mubarak ba budurwarka bace? Shut up pls!!!! Yayi exclaiming da qarfi
"Pls come down" jalal ya fada a cen qasa
"Kallon juwairiya yayi "sannu ko? Kai ta gyada mishi tare da juyawa ta wuce kawai
"Haba mubarak at least ka bari har yariyar nan ta tafi sai kayi fadan mana, gaskiya baka kyauta ba" ita mahaukaciyace da zata tafi da ita? Ya isa haka
Kallonshi kawai jalilah take ya juwa ya tafi
Dariya jalal yayi "muje jalilah" ni bazani ba ta juya ta nemi wuri ta zauna
Sauri yayi ya cimma mubarak "wai kai meye haka? Kai kayi fushi ita tayi fushi Allah zan kyaleku" juyawa yayi ya hangota ta sunkuyar da kanta da alama kuka take
Juyawa yayi yaje wurin da take,, dagowa tayi a tunaninta jalal ne tana ganinshine ta qara kuka
Dariya ta bashi "jalilah kinga yanda kika daga hankalin jalal ko? Kinga bansan yarinyaar ba nayi tunanin ta gudu da qanwanane shiyasa nayi miki fada sorry tashi muje" toh ka bata haquri tanada kirki sosai
Toh naji muje na maidaki kinsan gone zaku tafi " muje mu bata haquri toh
Kallonta kawai yake "muje toh,, dole yabi bayanta ya nemi wuri ya zauna ta shiga ciki ta kirata
"Ya mubarak gata nan ka bata haquri" kallon jalilah yayi "Yaya ka bata haquri sai Mu tafi" ahankali ya furta sorry ba tare da ya kalleta ba
Aa yaya bata haka ake bada haquri ba idan mutum yayi laifi zeyi kalan nadama ne sai ya bada haquri
Kallonshi ya mayar gun juwairiya tare da furta sorry ya wani kwanta da kai gefe daya, dariya ya bata "is okay ta juya kawai tana cikin tafia tajiyo dariyansu
Kallonsu jalal yake har suka qaraso kusa dashi duo ya wani hade face yayi ya juya
Manta dashi muje na maidaki
Kallonsu cool AJ yayi har suka qaraso "hey where to? Zan maidata gidane? Kallonta yayi farace sosai ba laifi "muje" aa kuje kawai
Pls ya mubarak kuzo da wurin anjima kuma ka zomin da ice cream,, kai ya gyada mata tare da yi mata murmushi
***********************************
Juwairiya kada ki fita da Alama akwai hadari fa,, salma Allah bazan dade ba zan dawo
Tafiya take ta qarasa wani store ta ciko leda da kayan zaqi tana tafiya tana waya
Iskane ya fara tasowa duk mai adaidaita sahu ko taxi idan juwairiya ta tsayar dashi bata tsayawa
Sauri take iska ya qara tasowa Duk hankalinta ya tashi aka fara ruwa sosai juwairiya ta jiqe har ta soma kuka ta shiga cikin school
Ruwan ya dake juwairiya na tafia take ahankali duk material dinta ya kwanta ajikinta komi nata a bayyane yake
Kallonta yake har ta qaraso kusa dashi duk kunya ta kamata cike da rashin kuzari ta biyo ta gabanshi ta wuce
Kallonta yake tana tafia duk jikinta a bayyane yake har tausayi ta bashi
Ahankali taji ya kira sunanta ta tsaya cak,,, motanshi ya shiga yaja kusa da ita ya tsaya ya bude mata ahankali ta zaga ta shiga
Driving yake ahankali har ya qarasa bakin hostel da ita
Kallonta yayi duk taji ta tsargu ganin yanda yake kallonta "out" ya furta ba tare da ya kalleta ba ta bude tq fice sum sum ta shiga hostel............
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
61-65
Kallonta salma tayi ta shiga dariya "daman wanda beji bari" harara tayi mata ta nufi room dinsu ta sanja kaya ta nemi wuri ta kwanta sosai ta shiga bacci
Zaune suke a parlour mami da ummi suna fira jalal da mubarak suna sauraren labarin jalilah
"Ya jalal kamin kunshi mana" ido ya zare "ke wai meyasa kike dauko abinda kikasan bazai yuyu ba? Ya jalal kunshin ne bazai yuyu ba? Dan Allah kamin
"Jalilah dan Allah ki ajiye zancen kunshin nan Allah banida lafia juriya ce kawai nake" meke damunka? Headache,,
Hannunta ta dora saman kanshi sosai ko taji da zafi,, kallonshi tayi cike dajin ba dadi "ya jalal kasha magani? Kai ya gyada mata "toh kaje ka kwanta ka huta mana
Murmushi yayi ya tashi yaje kusa da Ummi "Ummi zamu tafi kaina yana ciyo" cike da damuwa take kallonshi "kasha magani? Kai ya gyada mata "toh shikenan Allah ya qara sauki" ya amsa da ameen "amma ummi gobe bazamu hadu ba saboda munada text kuma da alama mubarak ba wani karatu yayi ba zamu tsaya dan ya samu yayi karatun
Kai ta gyada mishi "Allah ya kiyaye hanya" ta amsa da ameen ya tashi ba tare da ya kalli mami ba "mubarak muje ko?
Tashi yayi yayi sallama dasu ummi suka fice
A harabar gidan suka hadu da cool AJ da AK sam jalal be kallesu ba yana riqe da hannun mubarak
Daka ganshi kasan yana cikin damuwa shima be wani kula dasu ba saboda yanayin da yake ciki
AK kaje kawai gobe za muyi magana ya juya ya nufi part dinshi
************************************
Rikici sukeyi sosai acikin class din amma sam bakajin muryan jalal sai na mubarak
"Wallahi a kaduna za muyi hutu gara kawai kasa aranka cen zamu tafi" sam jalal be kulashi ba "tashi muje mu hada kaya" "bafa inda zani na gaya maka a kafancen zanyi hutu" why? Its where I belong" tsaki mubarak yayi "kaci gaba da nacin zance mana Allah wannan nacin naka na yau sai na karyashi
Ya tashi kawai ya nufi hostel
Dariya jalal yayi "kaji dashi cen ba inda zani"
Cike da natsuwa yaje kusa dashi ya zauna, kallo daya jalal yayi mishi ya kawar da kanshi
"Bros jalal bros mubarak fa? Kamar bazeyi magana ba cen qasa ya amsa mishi "he is in d hostel" okay can I ask you something?
Kai kawai ya gyada ba tare da ya kalleshi ba
"Pls did I upset you?
Kallonshi jalal yayi shima din ya tsareshi da idanu kawar da kanshi yayi kafin ya bashi amsa "no" okay to meyasa bakason ganina? Idan akan mubarak ne ai na bashi haquri ko? I'm your twins brother so pls tell me if am did something that make you fell bad and you can't tolerate?
Tsawon lokaci kafin jalal yace mishi "ba komi" no jalal there is something in your mind just tell me"
"I have something to do" ya tashi kawai da sauri cool AJ ya riqo hannunshi "jalal why all this? Saboda kaga na damu dakai? Kallon juna suka tsaya yi "jalal ne ya fara kawar da idanunshi daga kallon da suke yiwa juna
Juyo da face dinshi AJ yayi "did I upset you? Kai ya girgiza,,, then why all this?
Sam jalal besan me zece dashi ba "pls jalal say something I know you have something to say, so pls just say it
"Abdul I don't have anything to say" murmushi yayi AJ yayi
"Me zakayi yanzu? Kallonshi yayi badan yaso ba yayi murmushi "gobe zan tafi kafancen"
Murmushin yayi shima tare da sake mishi hannunshi ya zauna "meyasa baza kayi hutu anan ba?
Ko kallonshi beyi ba dan besan me zai gaya mishi ba
Juwairiya ce ta shigo tare da salma ,, lokaci daya jalal da AJ suka kawar da kansu daga wurin da suke AJ harda Jan tsaki ya tashi kawai ya fice
Kallonshi jalal yake har ya daina hangoshi ya dauki wayanshi ya nufi hostel.........
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
66-70
Kallon juna sukayi itada Salma "juwairiya wannan fadan harda dan uwanshi kike yinshi? Salma dan Allah banason yawan surutu mu jira zuwanshi ki gama abinda kike mu tafi,,,
Tsaki salma tayi "Allah juwairiya banason guy dinnan" toh ya zakiyi? Mahaifinki ya zaba miki fa
Zaman jiran zuwan anas sukayi wanda ze auri salma har yazo sukayi magana da salma ya tafi abinshi
Jalal banda kallon mubarak ba abinda yake har ya kammala ya fito musu da kayan bowel fari "tashi ka shirya zamu fita" banza yayi dashi "amma kaji me nace ko? Tsaki yayi "wai ina zamuje ne? Ka tashi mu tafi
Shiryawa sukayi suka fito sosai sukayi kyau cikin kayan mubarak ya tsayar da taxi ya gaya miahi inda zai kaisu
Takaici ne ya cika jalal lokacin da ya fahinci gidan mai martaba ne zasu tafi
Ko kallonshi mubarak beyi ba yana riqe da hannunshi suka shiga ciki
Sai faman miqa musu gaisuwa ake ba wanda yake amsawa cikinsu har suka qarasa ciki
Zaune take cikin shiga ta alfarma tana karatun al Qur'ani sukayi sallama suka shiga ciki
Saida ta kammala ta dago cike da murmushi tana kallonsu, cike da girmamawa mubarak ya gaidata ta amsa jalal kam kanshi na sunkuye qasa mubarak ne yake magana
"Mami gobe zamu tafi ne shiyasa mukazo mu gaidaku" murmushi tayi ta tashi ta nufi part din mai martaba bata jimaba ta dawo tayi musu umurni da su biyota
Zaune yake cikin parlour yana kallon labarai sukayi sallama ya amsa musu suka shiga ciki
Cike da girmamawa mubarak ya gaidashi amma jalal kanshi yana sunkuye qasa
"Mubarak ya karatu? Alhamdulillah abba,,, dama gobe zamu tafi kaduna ne muyi kwana biyu sai mu tafi kafancen saboda taya baffa aikin gona" murmushi mai martaba yayi sosai kuma zancen na mubarak ya bashi dariya
Zaune suke shuru ba wanda yake magana saiga cool AJ ya shigo da sallama suka amsa ya nemi wuri ya zauna ya kwashi gaisuwa
"Abba mu zamu tafi" oh bros mubarak da wuri haka? Murmushi yayi "jalal yanada wurin da zai tafi ne"
Ahankali jalal ya dago ya kalli mubarak ya sakar mishi harara murmushi yayi tare da kawar da kanshi
Murmushi mami tayi da suka hada ido da mubarak
Basusan ko meye acikin envelope din da mai martaba ya basu ba mubarak ya amsa yayi godiya
"Zaku koma school ne? Matse hannun mubarak jalal yayi suka dago suka kalli juna "bros jalal nafa ganka" murmushi yayi suka fito tare da cool AJ
Tsaye sukayi mubarak ya fara fada "Allah bakada kirki kai kenan komi sai anyi maka gyara Allah baka kyautawa kuma zan gayama ummi Allah" kallonshi yayi ya kawar da kanshi ganin mubarak ya harareshi
qara juyowa yayi suna hada ido yayi dariya badan yaso ba
Sauke labulen mami tayi tana murmushi tare da mamakin halin jalal din sam be taba gaidata ba kuma atunaninta harda mai martaba be taba gaidashi ba
AK ne ya shigo suka gaisa
"Cool jalal muje ko? Kasan fa akwai saqon jalilah" kallon juna sukayi "cool jalal and cool AJ" that is nice,,, cewar AK murmushi mubarak yayi suka juya
Kallonsu AK yake har suka fice yayi murmushi kawai suka nufi dakinsu
Duk yanda mai karatu yake tunanin Bacon ran jala yafi hakan a lokacin da baffanshi yake sanar dashi yanda sukayi da mai martaba "baffa wai meyasa yakeso ya shiga rayuwarmu ne? Gaskiya bazamu koma cikin wannan masarautar da zama ba meye alaqanmu da ita? Kuma zancen masu yi mana aikin gona gaskiya bama so dan ba gazawa mukayi ba"
Murmushi baffan yayi "jalal nima banso hakan ba amma banida zabi saboda wani dalili kuma banaso hakan ya sanyaka damuwa kaji,,, shuru yayi ummi ta karbi wayan taci gaba da kwantar mishi da hankali
Dariya mubarak yayi ya Santa kayan cikin mota suka nufi Kaduna
Sosai mami tayi hidima dasu
Zaune suke a parlour mubarak yana buga game jalal yana aiki da system dinshi
Mami ce ta shiga ta zauna kusa da jalal "dadina ya yoron nan yasan computer" dariya mubarak yayi jalal kam kunya ma yaji
Three days sukayi a Kaduna suka nufi zariya kasancewar su ummi sunzo kuma zuwan ga baki daya ne
Kowa yana farin cikin ganin wani jalal yana zaune kusa da baffa sai faman magana suke qasa qasa ba wanda yake jiyo abinda suke tattaunawa akai
Gyaran murya yayi ya shigo kowa ya shiga miqa gaisuwa ya nemo wuri ya zauna kowa yayi shuru yana saurarenshi
"Malam Ibrahim bana nuna mulki bane akanka said an ganin hakan ba wani abu bane a wurina kuma nasan ka fahinceni,,,, abdul jalal dawowarka anan bayana nufin mune iyayenka ba nasan zakayi wani tunani aranka wanda ba haka bane dan haka inaso kowa ya cire wani kwankwanto acikin zuciyanshi" ya qara da cewa maryama zama ba aure ba naki bane nasan koda ban fada ba kinsman dalilin wannan maganar dan haka inaso ki shirya ranar jumaa zan daura aurenki da alhaji sadiq wafa
Murmushi kawai tayi ga baki daya dariya ta cika mubarak
Mai martaba ya tashi ya fice sukayi mishi fatan alkhairi
Kallonta mubarak yayi "Allah ranka zai baci" aiko ba ahiri yayi dariya " mami me kuma nayi? Cool jalal ne ya sanyani dariya fa" bata qara kulashi ba su ummi suka nufi part din da aka basu "ya jalal ai zakamin kunshi yau ko? Kai ya gyada mata "amma banason black red kawai zaamin" nan ma duk amsar daya ce
Duk wani abu da suke buqata ba wanda babu komi an tanadar musu
*8:30pm* jalal yana zaune yana Yuma jalilah kanshi mamin mubarak ga baki daya mamaki ya cikata ganin yanda jalal ya tsara kunshin kai bazakace namiji ne yayi ba haka mubarak din yake kallon ikon Allah
"Ummin jalal wai dagaske ne abinda nake gani? Hmmm jalal kam yafi hakan indai jalilah zaayiwa
Allah mai iko
Toh yaushe zaa yimin nawa? Dariya mubarak yayi "cool jalal zaka iya na amare ko? Duka taki mishi ya goce yana dariya "mubarak wallahi ka kiyayeni...........
[25/12, 14:04] Hassan Atk: 🤴🤴 JININ SARAUTA 🤴🤴
*Written by Hafsat MN*
IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_
71-75
Ummi ma dariya tayi "mubarak Allah zamu bata idan baka daina ba" mami na daina basai mun bata ba
Zaune yake gaban mai martaba cike da girmamawa "abdul jabbar yanzu ka kusa kammala karatu inaso ka nemi matan da zaka aura kafin kaje service zaayi auren in yaso duk garinda aka turaka sai kaje da iyalinka "
Sosai yakejin zuciyanshi yana bugawa yayi godiya ya tashi har jiri yakeji
Tafiya yake jiri na dibanshi shi sam bayaso mace ta shigo cikin rayuwarshi ya tsani abinda zai hadashi da bace ya fison ya qare rayuwarshi ba tare da yayi aure ba"
Kallonshi jalal yake yana tafiya kamar wanda zai fadi ya matsa kusa dashi kamar bayaso yaji me yake cewa
"Are you sick? Kai ya griza mishi "bros I need your advice but not yet,,, why? Am not in the mood" kallonshi yayi yanayinshi ga baki daya ya sanja kai kawai ya gyada mishi ya juya ya fice
Sosai yasha giya a wannan ranar amma duk da haka be samu yin bacci ba saboda sanin halin mai martaba yasan idan ya fada toh sai ya cika koda be kawo wacce zai auraba toh zai nema mishi da kanshi
Tsawon kwana biyu kenan jalal yana kule da yanayinda abdul jabbar yake ciki amma sam beyi yunqurin tambayarshi ba dan a tunaninshi ba huruminshi bane tunda ba mubarak bane
Su mubarak sun shirya sun koma school kasancewar jalal yace shi sam bazai zauna a gidan ba school zai koma
Zaune yake cikin mota idan yasha sigari ya kurba giya ya dan kwantar da sit dinshi
Kallon mamaki mubarak yake mishi dan beyi tunanin shaye shayen sun kaishi ga shan giya ba
Jalal ne ya qaraso kusa da mubarak yaga hankalin mubarak baya kanshi ya mayar da hankalinshi kan Abdul din
Lokaci daya yanayinshi ya sanja ganin a rubuta gulder
Duk yanda yaso kyaleshi dan bayason shiga harqallarshi amma yaji bazai iya ba cike da zafi ya janyoshi cikin motan ya karbi sigari da giyan ga baki daya ya jefar dashi ya hadashi da mota sai faman huci yake "kai me kake nufi ne? Saboda kanada sai ka riqa sabawa Allah? Toh bari kaji wallahi kana gab da mutuwar qasqanci inhar baka gyara tsakaninka da Allah ba dan zakasha wannan kayan mayen ka dauki mota ka fita kayi mummunan hatsari wanda zai kaika ga mutuwar qasqanci" yana kaiwa nan ya wani tureshi yaja hannun mubarak iyaka qarfinshi yake Jan mubarak har suka qarasa hostel
Kallonshi kawai mubarak yake idanunshi sun kada sunyi jajir sam mubarak beyi yunqurin yi mishi magana ba ganin yanayin da yake ciki
Tunda suka fice yake tsaye ya rasa wane irin tunani zeyi ga baki daya jin jikinshi yake kamar bashi ba ya haqura ya bude motanshi ya shiga ya kwantar da sit ya shiga baccinshi
Tsawon kolaci cool AJ yana bacci cikin mota ba tareda damuwa ba haka yayita faman bacci tsawon 3hrs
Dan tsaki yayi yaja motanshi ya nufi gida direct part dinshi ya nufa ya shiga toilet yayi wanka ya sanja kaya yayi sallah ya nufi part din maminshi
Ahankali take mishi magana "abdul ka sanja rayuwanka wanda ba haka nasanka ba gayamin damuwarka? Shuru yayi kafin ya fara magana
"Mami wallahi koda mafarki nayi da mace a wunin ranar zan wuni zuciyana yanamin zafi wanda dalilin ne banason muaamala da mace
Akwai waya juwairiya mami aranar Dana taimaka mata zuciyana nayi tunanin zata FASA qirji nane kuma ganshi mai martaba yace na fitar da matan da zan aura, mami wallahi ni kadai nasan me nakeji idan naga mace wannan jalilar din ma ita ke hanani gaida su ummi"
Sosai mami taji hankalinta ya tashi amma bata nuna mishi ba
Saboda bakason aure shine ka tsani mace? Kai ya shiga girgizawa
Tashi ka tafi
Tashi tayi ta shiga zaga dakin ahankali tana tunanin ko aljanace ta auremin yaro? "Inna lillahi wa inna ilahin rajiun" haka ta shiga nanatawa tsawon lokaci
Daya daga cikin bayin tasa ta kira mata ummi sai gasu sun shiga a tare
Zama tayi suna fuskantar juna "ummin jalal nasan zakiyi mamakin wannan kiran da nayi miki toh ba wani abu bane face wata matsala da nakeso muyi shawara ni dake saboda yanzu kece 'yar uwata ta kusa"
Kai Ummi ta gyada mata ta shiga bawa ummi labarin halinda cool AJ yake ciki
Kwantar mata da hankali ummi ta farayi daga bata ta nuna mata wannan ba wata matsala bace jalal ma zai iya taimaka mishi basai zancen yakai ga baffan jalal ba
Murmushi tayi "toh taya jalal din zai taimaka mishi? Zan turoshi sai kiyi mishi bayanin komi" murmushi tayi tare da girgiza mata kai
Idan kikayi mishi bayani ma ya wadatar
Murmushi ummi tayi dan ta fahinci da jalal din da ita kowa bayason mu'amala da wani
Waya ta daga ta kira jalal ta gaya mishi idan ya samu time yazo tana nemanshi
"Zanzo yanzo in shaa Allah"
Kalllon mubarak yayi da yake bacci kawai ya yake shawarar ya tafi shi kadai
Part din mami ta nufa dashi "Ummi me za muyi acen din" jalal banason shashanci
Shuru be qara magana ba suka nufi dakinta tare da yi mata sallama
Sanin halin Ummi ne yasa ya gaida ta cen qasa kamar bayaso taji
Murmushi kawai tayi dan ita rana ta farko da ya gaidata kuma tanada yaqinin akan Ummi ne ya gaidata
"Jalal matsala ce ta task wacce ta shafi dan uwanka" cike da tashin hankali yake kallonta "Ummi wallahi be gayamin kinsan halin mubarak ya fiye wasa"
Kallonshi suke ga baki dayansu "Ummi Allah be gayamin ba amma zan tamabayeshi"
Jalal mubarak ne kadai dan uwanka? Shuru yayi ba tare da ya amsa mata ba "ka amsamin? Kai ya girgiza
Tashi ka tafi,,, ummi dan Allah kiyi haquri nayi tunanin mubarak din kike nufi" tashi ka tafi nace
Ummi dan Allah ki yafeni,,, yayi magana a raunane
"Jalal me abdul jabbar din yayi maka ne ka tsaneshi haka? Ummi Allah ban tsaneshi ba kawai dai nashi raayin daban ne da nawa" shine kuma bazaka yi qoqarin ganar dashi ba? Shuru yayi tare da sunkuyar da kanshi qasa
Dan tsaki tayi kafin ta fara yi mishi bayani akan matsalar abdul din
Nasan zaka iya basai baffanku ya Sani ba shiyasa na kiraka ana kasa yazo yaji muna zancen
Kai ya gyada mata "yau zaka dawo? Yana gidane?
Bari abincika aji
Kiranshi mami tayi ya gaya mata gashi nan zuwa
Tunaninshi qara jalal ya kawoshi yanashan giya ya nemi wuri ya zauna
Kallonshi jalal yayi "ummi bani miski "
Tashi tayi taje ta dauko mishi ta kawo
Dawo nan ka zauna
Ba musu yaje kusa dashi
Duk wani joint nashi jalal saida ya sanya mishi miski
Kallonshi kawai suke
Kunnenshi daya jalal yasa yatsanshi ciki sosai ya fara yi mishi karatu acikin daya
Mami kallon ikon Allah kawai take da sauraren qiraa mai shiga zuciya
Tsawon lokaci yana mishi karatu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 13