Reading ALHINI by Zee Mmn khadye Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [10/16, 8:01 PM] www.gidannovels.blogspot.com *_ALHINI_*

®```NWA```

_written by_
*_Zee Mmn khady_*


1to2 ```Page```


kuka take kamar zata cire ranta, idanunta sun kad'a sunyi jawur saboda tsananin
kuka, fuskarta tayi face-face da hawaye, zaune take cikin d'akin kan tabarmar kaba,
jikinta wata atamface Riga da zani, simple da ganin atamfar kasan tad'an kwana biyu
saboda farin data d'an yi Alamar kod'ewa, sai wani madai-daicin hijabi data sanya,
shima dai dagani kasan ba sabo bane, amma kuma wankakke ne, duk kayan jikinta basu
tare da datti.

"Haba laraba kiyi ha'kuri ki daina kukan nan, sabi'u dai yariga ya mutu kuma kinsan
kukannan naki baze dawo dashiba, Addu'a kawai yanzu yake bu'kata daga gareki, ta
dafa kafad'arta kiyi hakuri dan Allah ki daina kukan nan.

Sai lokacin Balaraba ta kalli wacce keta faman rarrashinta tace "Haba indo dole
inyi kuka, kukan nan danike shi kad'ai ze ragemin rad'adi da ba'kin cikin danake
tartare dashi, (tacigaba da kukanta,)

Indo tana matu'kar tausayama halin da 'kawarta take ciki, itama wasu guntayen
hawaye ta zubar sannnan ta'kara matsaowa kusa da 'kawarta ta dafa kafadarta da
hannu guda,
gudan hannun kuma tana goge mata hawayen dake kwarara daga idonta, tace
"Tabbass nasan rabuwa da masoyi akwai ciwo, baranta kuma rabuwa ta har abada,
Amma dole kiyi ha'kuri ki d'auki wannan a matsayin jarabawa ce daga ubangiji.

Laraba ta fashe da wani sabon kuka, tace indo bazaki ta6a gane halin ba'kin cikin
danake cikiba, ki duba kiga irin soyayyar da muka shimfid'a nida Iro acikin
'kauyennan muna burge Kowa, amma lokaci guda ana saura sati d'aya bikinmu yaje
wanki rafi yafad'a ruwa sai dai gawarsa aka fiddo, tafashe da wani sabon kuka, indo
ma kukan take, amma hakan be hanata rarrashin 'kawar tata ba.

Cikin sheshshekar kuka tacigaba da cewa "yanzu kuma :yau an wayi gari sabi'u shima
ya mutu kamar yanda Iro ya mutu, wannan wane irin iftila'i ne yafad'amin.

Assalamu Alaikum, inna ce tashigo da sallama, indo ta amsa mata sannan tashigo
d'akin, ta cire ijabinta ta rataye kan 'kyauren d'akin sannan takai dubanta ga
Balaraba wacce taketa faman kuka indo kuma na rarrashinta wacce itama kallo d'aya
zakayimata Kazan kukan tayi.

Indo takai dubanta ga inna dake shirin zama kan kujera tace "lnna har kun dawo?
"Har na dawo indo ay anriga anrufoshi sai dai muyi mashi addu'ar samun rahamar
ubangiji, sabi'u kam yayi mutuwar ban mamaki, duk da ba mamaki cikin lamarin
ubangiji, amma mutane da dama sunce lafiya lao ya kwanta, kawai aka wayi gari ya
mutu, wasu siraran hawaye suka zubo daga idon inna dan tana tausayama tilon yarta,
wacce tayi rashin masoyi a karo na biyu.

Laraba ta fashe da wani irin kuka, ta taso daga inda take tafad'a jikin inna tana
kuka, "shikenan inna yanzu narasa sabi'u wayyo nashiga ukku, sabi'u miyasa kamin
haka saida kabari na sha'ku dakai sannan zaka tafi ka barni,
innalillahi,wa'inna,ilaihirraji'un, ta fad'a kawai sai ji sukayi tayi shiru ba
Alamar numfashi tattare da ita, duka jikinta ya saki
Nan inna tashiga wani irin rud'ani tana girgizata tana kiran sunanta, "fatima.....
Fatima innnalillahi nashiga ukku,
Indo dake tsaye hankalinta duk ya tashi tarasa inda zata sa kanta da gudu
tafita daga gidan tana neman taimako.

"Dan Allah Hashim ka taima mani kada ta mutu, wanda takira da hashim yace "wacece
zata mutu, bata bashi amsaba tacigaba da kuka tana cewa ka taimakeni, mutuwa
zatayi, dan Allah, da gudu takoma cikin gidan.

Har yanzu laraba na rungume jikin inna ba Alamar numfashi tattare da ita, inna kuma
sai kuka take tana kiran sunanta.

Da gudu hashimu yanufi gidan me gari ya aro baro,
Kofar gida ya ajiye baron, sannan yashigo gidan da taimakon, indo da lnna aka dora
Laraba kan baron, Hashim ne ke tura baron da gudu.

Lnna da indo suna biye dashi hankalinsu tashe suka nufi 'karamar asibitin dake
'kauyen.




Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 8:02 PM] www.gidannovels.blogspot.com *_ALHINI_*


```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*


3to4```Page```



Sannu Laraba sannnu kinji, kallo kawai take bin mutanen dake gurin dashi, idanunta
suka ciko da hawaye, Inna tasa gefen mayafinta tana goge mata.

Sai da musalin 'karfe biyar na yamma aka sallamesu daga asibiti, bayan 'karin ruwan
da aka sanya mata ya 'Kare,
Indo kuwa duk abinnan tana tare dasu sai gab da magrib inna ta umarceta data koma
gida kada anemeta,
haka ta wuce tana me tausayama halin da 'kawarta ta tsinci kanta.

Hashim kuwa tinda akaje asibitin yaketa hidima da Laraba dan kusan duk kud'in da
aka kashe shine yabiya, yana mutu'kar tausaya ma Laraba,

Shima sai lokacin yabar gidan yanama Laraba fatan samun lafiya, inna kuwa godiya
kawai take mashi dan ya taimakesu ba kad'anba, dan in baccin shi da batasan inda
zata samu kud'in da zata biya na magani da 'karin ruwan da akayima Laraba ba.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*_BAYAN SATI BIYU_*
Zaune take kan guntuwar tabarmar da aka shimfid'a kan shararren gidansu na 'kasa,
ta tasa kwanon abinci gabanta, ita bata ciba kuma bata maida ta rufe ba, ta zubama
abincin ido tana kallo, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, tasa hannu ta
goge.

"Yanzu Laraba bazaki cire damuwarnan daga cikin ranki ba, kiyi ha'kuri ki d'auki
kaddara, kin riga kinsan dukkan me rai mamacine, muma nan mutuwa jiranta muke ko
yau ko gobe ko jibi koma yanzu,
Dan Allah kisama ranki ruwan sanyi.

Wasu siraran hawaye suka zubo daga idanunta tace na ha'kura inna.... Na
ha'kura..... Ki tayani da addu'a Allah yayemin damuwar dake tattare dani.

Inna ta tausayama Laraba har cikin ranta, tace "Allah yaye maki Laraba, Allah sa
maki 'ha'kuri da dangana.

Tace Ameen tare da share hawayen dasuka zubo daga idanunta.

Da 'kyar inna ta rarrasheta taci abincin, Wanda taci be wuce loma hud'uba, dan ma
lnna ta matsa mata ta d'ora da fura rabin cup, sannan taji d'an 'karfi-'karfi.

Da sallama ya shigo gidan, ya dur'kusa har 'kasa ya gaida inna, cikin far'a ta Amsa
"Hashim kaine sannu da zuwa, ta d'auko wata guntuwar tabarma ta shimfid'a mashi ya
zauna, tunda ya shigo idanunshi na 'kan Laraba wacce duk tabi ta rame ta fita
hayyacinta,

Saida ta lura da yanda yake kallonta sannan tace mashi "ina wuni, ya amsa da
"Lafiya lao Laraba ya jikin naki?
"Da sauki, "Allah 'kara sauki, tace "Ameen.

Sannan ta tashi tanufi randa ta ebi ruwa cikin wani madai-daicin bokiti tashiga
kewaye dan tawatsama jikinta taji sanyi.

Tunda ta tashi yake binta da kallo, cikin zuciyarshi yana cewa
_"Na dad'e ina son Laraba dan dai wasu sun rigani ne yasa na ha'kura, amma yanzu
bazanyi sake da wannan damar ta wuceniba, 'kila dama rabonace shiyasa Allah ya
kashe lro da Sabi'u_.

Inna ce ta katse mashi tunani "Hashim ya mutanen gidan naku?, yayi saurin dawowa
daga dogon tunanin dayake yace "suna lafiya sunce agaisheku, daga gurin aike nake
nace bari in biyo inga jikin Laraba, inna taji dad'i har cikin ranta yanda Hashim
ke nuna kulawa ga 'yarta, tace "jiki Alhmdlh, yace "Allah 'kara sau'ki tace Ameen.

Nan dai suka 'dan ta6a fira kafin yayi mata sallama, ya ajiye wata ba'kar leda yace
"ga wannan aba Laraba, inna tace "a'a Hashim hada hidima kuma, yace "ba kome inna
Allah sauwa'ke nina wuce, tace to Angode Allah bada lada, yace Ameen.

Bayan fitarsa ne, Indo tashigo, lokacin Laraba tagama wanka tana shafa mai, inna na
Nuna mata abinda Hashim ya kawo mata, balangu ne lafiyayye hanta tafi yawa aciki,
sai 'kananan robar yourghut guda ukku,.

Bayan inna tafita waje, Indo ta kalli Laraba tace, "gsky Laraba Hashim yanada wata
manufa acikin ransa dangane dake, dan ni nasan ba a banza yake maki wannan hidimar
ba,
Laraba ta kalleta cike da nuna rashin sanin inda maganarta ta dosa, tace "Ban
ganeba wace manufa kuma? Indo tayi murmushi tace "gani nake kamar 'Hashim sonki
yake.. .
Wani mummuman Fad'uwar gaba Laraba taji, dan yanzu ko kad'an bataso taji an anbaci
kalmar wani na sonta.

Tace Dan Allah indo mubar wannan maganar Hashim ba sona yakeba, inajin kawai dai
yana tausayi na ne, amma babu wata soyayya dayakemin, murmushi kawai indo tayi, dan
bata so suna kace-nace da 'kawar tata.

Ranar dai indo ta d'ebema Laraba kewa dan fira suka sha sosai, har fita sukayi suka
d'an zaga gari,

Tinda suka fita mutane ketayima Laraba ta'axiyya, indo ce ke amsawa dan bata son
abinda ze daga hankalin 'kawar ta.

Sai bayan la'asar indo taraka Laraba har 'kofar gidansu saida taga shigewarta
sannan itama ta wuce gidansu.




Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [20/08 12:47 pm] 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*😘



5⃣6⃣
5⃣to6⃣```Page```



🖊Kwanaki sun ja lokaci na tafiya, yau an wayi gari sabi,u nada wata ukku da sati
biyu da rasuwa,
Alhmdulillahi Laraba ta saki jikinta, ba kamar da ba, kuma jikinta ya goge yayi
sumut,

6angaren Hashim kuwa kullum soyayyar Laraba 'kara ha66aka take acikin zuciyarsa,
har yakai da yakasa sukuni, hakan yasa ya yanke shawarar zuwa gidan yayarsa, ya
fad'a mata halin dayake ciki, kuma ya ro'keta taje gidansu Laraba ta gabatar dashi
amatsayin me neman Laraba da Aure.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Laraba ce tafito cikin shirinta, atamfa ce jikinta d'inkin doguwar riga, kalar
ruwan 'kasa duk da atamfar ba sabuwa bace amma ta masifar yimata kyau, abinka ga
farar mace, kowane kaya tasa kyau yakeyimata, wani 'karamin hijab ta sanya shima
'kalar ruwan 'kasa tayi kyau abinta, duk da ta taso 'kauye bazaka kalleta ka kirata
'yar 'kauyeba, saboda bata irin shigar nan da 'yan 'kauye keyi na zani daban riga
daban, ita tanasa kayanta complete, sannan kuma bata fiye sa gyale ba, yawanci
kullum zaka ganta da hijab d'inta, gata da nutsuwa da kamun kai, shiyasa duk
mutanen 'kauyen take burgesu.
Kitchen ta iske mahaifiyarta tana faman girka masu abincin rana, tace "Inna zan
d'an fita,
Inna ta kalleta tace "ina kuma zaki Laraba,?
"Inna inaso zanje gidansu indo ne naji kwana biyu ban gantaba,
To shikenan Laraba kije Allah kiyaye hanya, tace "Ameen, sannan ta fice daga
gidan.

Inna kuwa har cikin ranta taji dad'in yanda d'iyarta ta saki jiki, dan rabon datace
zata fita tun da rasuwar masoyinta sabi'u.

Cikin nutsuwa take tafiyarta, kanta sadde dan batason yawan kallon da mutane suke
mata.

Dai-dai santar dazata sadata da gidan su indo ne taji kamar ana kiranta, waigowa
tayi dan ganin me kiranta,

Cikin nutsuwa ya iso inda take fuskarsa d'auke da murmushi, yace "Laraba kina
lafiya, tace "Lafiya lao Haruna,
ya'kara fad'ad'a murmushinsa yace "Laraba ashe kina ganuwa, itama mumushin tayi
tace wace ni ince bani ganuwa,
yace ay naga tun rasuwar sabi'u rabon da inganki sai yau tace kaidai bari Haruna,
wallhi fitar ce yanzu kwata-kwata tayimin wahala yauma dan naga kwana biyu banga
mutumniyarba shiyasa nace bari inzo inga ko lafiya, Haruna yayi murmushi yace
"gaskiya ne 'kara da kika fito, nikau wallahi 'kawancenku yana birgeni keda lndo,
duk 'kauyennan ba Wanda besanku tare ba.

Murmushi kawai tayi tace "Haruna kenan, yace "Allah kuwa, duk 'kauyennan kuna burge
mutane da dama kuma gashi kunsha bam-bam da 'yan matan 'kauyen, gurin nutsuwa da
kamun kai.

Tace "to mungode da wannan yabo damuka samu daga gareku, ni zan wuce kaga rana na
'karayi baniso in wuce azahar ban koma gida ba,
Yace "to Amma idan bazaki damuba inaso zamuyi wata magana dake, tace "ina
sauraronka Amma Allah sa bazata d'auki lokaci ba.

Yace "inshaAllahu bazata d'auki lokaciba duk da bansan yanda zaki ji ba indan
kikaji maganar dazan fad'a,
bejira tafad'i wani abuba ya'kara gyara tsayuwarsa yace "watako Laraba a gaskiya
na dad'e ina Sonki cikin zuciyata, ganin sabi'u yarigani ne kuma gashi har
maganarsa takai ga iyaye yasa na ha'kura ban bayyana kainaba, amma yanzu tunda ta
Allah ta kasance shine nace bari nazo da 'ko'kon barata ko Allah zesa a ki 'kar6eni
in maye gurbin sabi'u a cikin zuciyarki.

Tunda ya furta kalmar so, Laraba taji gabanta yayi wani mummunan fad'uwa, da kyar
ta tattaro nutsuwarta, batare da ta kallesa ba tace "naji duka bayaninka amma inso
kabani likaci inyi shawara.

Yace "nabaki kwana biyu ko wace shawara kika Yanke zanji, tace "Allah kaimu yace
"Ameen.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Da sallama tashiga gidansu lndo, innar indo ta iske tsakar gida tana wanke-wanke,
ta dur'kusa har 'kasa ta gaisheta, "inna ina wuni, cikin fara'a ta amsa "lafiya lao
Laraba yau kece a gidan namu, tayi murmushi tace "nice inna, indo nanan kuwa?
"Tananan da yanzu ma take cemin zata gidanku, ki isa mana.

Cike da murna indo ta tarbeta, 'kawata sannu da zuwa, wlh shirinnan da kika ga
inayi gidanku zani, Laraba tace "sai kuma gani nazo, lndo tayi dariya tace "ay naji
dad'in zuwanki, dama jiya Hashim yazo gidannan yabani sa'ko gurinki, Laraba cikin
halin rashin damuwa da maganar da lndo zata fad'a mata tace sa'ko kuma, lndo tace
kwarai ko, dan abinda na dad'e ina gaya maki ne ya tabbata, Hashim dai yace inmi'ka
'ko'kon bararsa gareki, yace wlh ba wasa yakeba sonki yake, kuma baza'a d'auki
lokaciba yakeso ayi aurenku.

Laraba tayi murmushi tace "yanzu ma kan hanya Haruna yatsareni da surutu waishi a
dole yana sona, lndo tayi murmushi tace "inkon Allah, to yanzu yazamuyi kenan?
Laraba tace "yafa zamuyi addu'a zamuyi Allah za6amin abinda yafi Alkhairi, indo
tace hakane Allah shige mana gaba, Laraba ta amsa da "Ameen.

Ranar gidansu indo Laraba ta wuni, sai bayan la'asar takoma gida.

Zaune ta iske innarta cikin inuwar bedi tana hutawa, d'aki tawuce tacire hijabinta
sannan tadawo ta zauna kusa da innar, tace inna sannu da hutawa, tace "yauwa har
kin dawo, tace nadawo innna.

Inna ta kallata tace bayan tafiyarki, saratu yayar Hashim tazo gidannan, wai Hashim
ya turota yana sonki idan anbashi dama kuma kin amice Aurenki zeyi, cike da kunya
Laraba ta sadda kanta 'kasa ta gayama inna yanda sukayi da lndo, sannan kuma ta
gayamata shima Haruna yana sonta, inna tace "to dukansu dai basuda makusa amma ni
aganina Hashim kamar zefi, kuma idan kikayi la'akari da hidimar daya dad'e
yanayimaki idan kika gujeshi yanzu kamar munyi butulci ne.

Laraba tace "inna nidai duk Wanda kika za6amin shine za6ina, fatana kawai kitayani
addu'a Allah za6amin abinda yafi Alkhairi.
Inna tace "Ameen.




🖊Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [20/08 6:36 pm] 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*😘


7⃣8⃣
7⃣to8⃣```Page```



🖊 Soyayya me 'karfi ta 'kulle tsakanin Laraba da Hashim duk 'kauyen mutane sun gama
sanin Hashim ne ze Auri Laraba.

Haruna kuwa hakuri Laraba tabashi akan soyayyar daya nema daga gareta, bata za6e
Shiba,
A ranshi yaji ba dad'i amma sai ya nuna bedamuba, yayi mata fatan Alkhairi.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Inna na zaune gidin bedi tana tsintar wake wanda zasuyi sanwar rana, tajiyo
sallamar mal Lawal, Wanda ya kasance 'kanine ga mahaifin Laraba, da fara'a inna ta
amsa sallamar "a'a mal Lawal ne sannu da zuwa, jiki na 'kyarma taje ta d'auko
tabarma ta shimfid'a mashi.

Mal Lawal mutum ne d'an bala'i bayada mutunci ko kad'an shiyasa lnna ke binsa
ahankali dan tasan duk garin Laraba batada mahaifin daya wuceshi,
Yayinda shikuma yake amfani da wannan damar yanayimasu yanda yaga dama.

Laraba ma masifar tsoronsa takeyi, hakan yasa tanajin shigowarsa gabanta yayi
mummunan fad'uwa dan tasan akwai abinda yakawo shi,
Zuwa tayi har gabansa ta dur'kusa ta gaisheshi, cike da gadara da nuna isa ya
amsa, sannan ta mi'ke taje ta d'auki tukunyar 'kasar data kasance ta ebar ruwansu,
ta yafo gyalenta tazo gaban inna tace "inna zanje d'ibar ruwa, inna ta kalleta,
tariga tasan dalilinta na son tafita, saboda haka bata hanataba, tace to Allah bada
sa'a tace "Ameen sannan tafice.

Kamar jiran fitarta yakeyi, ya maida hankalinsa ga inna yafara magana cikin bala'i
da d'aga murya,

"Hinde dama gurinki nazo, watako banida daraja a idonku dan baku d'aukeni bakin
komeba keda d'iyarki, shine har yarinyar nan tana soyayya da wani ba'a sanar daniba
dan an d'aukeni mahaukaci Wanda besan abinda yakeyiba.
Tunda yafara masifarsa lnna bata d'aga kai ta kalleshiba, saida yagama,
sannan tace "Allah baka ha'kuri, dama wallahi yau nayi niyyar inzo dakaina har gida
ingaya maka.

Ya tari numfashinta cikin masifa, yace "sai kuma gani nazo, to duk da bakison
sanyani cikin Al'amarinki baki isa ki rabani da Laraba ba, saboda Laraba batada
Uban da ya wuceni duk fad'in 'kauyennan.

"To duk da baki tura shi Hashimun gurinaba yaje ya sameni munyi magana, kuma yatura
magabatanshi mun tsaida maganar aurenshi da Laraba nan da sati ukku idan Allah ya
kaimu.

Inna tace "Allah kaimu Allah sa muna raye, ta tashi tashige d'aki tana matsar
kwalla, kusan duk randa mal Lawal yazo gidan sai inna ta zubar da hawaye.

Nan yagama zamanshi yanata zazzaga masifa marar dalili, ta inda yake shiga ba tanan
yake fitaba, lnna kuwa tana d'aki tana jinshi har yagaji ya'karama rigarsa iska.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Zaune suke kan wani dutse 'kafafunsu na cikin ruwa, da Alama sunajin dad'in yanayin
gurin, Hashim ya kalli Laraba yace "Am Laraba na manta ban sanar dakeba, jiya
baffanki yasameni yace intura magabata na, yanzu haka kafin infito nabaro su baba
bala sun tafi,
Wata irin kunya takamata tasa hannu tarufe fuskarta, tace "kace munkusa zama miji
da mata, Hashim yayi dariya yace "Allah dai yacika mana burinmu, wlh Laraba dan
bakisan yanda nake sonkiba, ina maki 'kaunar da duk cikin masoyanki babu wanda
yata6a yimaki makamanciyarta,
Wani lokaci nakan zauna inta tainani, inga kamar baffanki baze bani keba, sai
inji gabana yayi wani mummunan fad'i.

Laraba ta kalleshi cike da tausayawa, dan ko ita tagama yadda da son da Hashim yake
mata bana wasa bane tace "ka kwantar da hankalinka masoyina indai muna raye
inshaAllahu bakada wata mata bayan ni.

Cike da jin dad'in kalamanta Hashim yace "Allah sa tace "Ameen.

Haka ta Ebi ruwan Hashim d'in ya d'aukar mata suka kama hanyar gida suna tafiya
suna tad'i cike dajin dad'i.

Saida suka kawo gab da gidansu Laraba sannan yami'ka mata tukunyar ya tsaya nan
saida yaga shigarta sannan ya wuce.

Da sllama tashiga gidan, inna tayi saurin 'kar6ar ruwan dake kanta, tace "Laraba
kindawo,

Kallo d'aya tayima innar tata tasan tana cikin 6acin rai, tasan arina _(wai ansaci
zanin mahaukaciya)_ muddin ldan baffa Lawal yazo gidan to dole sai inna ta zubar da
hawaye.

Bata ko tambayi inna dalilin 6acin ranta ba, tashiga rarraahinta tana bata ha'kuri.

Inna ta kalleta cike da tausayawa tace "Laraba 'kanin mahaifinki yazo, ko ban
fad'aba kin riga kinsan halinsa, yace ya sanya bikinki da Hashim nan da sati ukku,
ina ro'konki da dan Allah kada ki d'aga hankalinki ki zamo me biyayya sai kiga an
zauna lafiya.

Laraba bataji komeba dangane da abinda mahaifiyarta ta fad'a mata sai cewa tayi
"inna kitayani Addu'a Allah za6a min abinda yafi zama Alkhairi a rayuwata, inna ta
share wasu guntayen hawaye tace, tashi kiyi wanka ga abincinki can gindin bushiya,
cikin langa, ba musu ta ebi ruwa cikin bokiti tafad'a kewaye, inna kuma tacigaba da
matsar kwallar tausayin yarta.




🖊Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [21/08 8:18 am] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*😘


to```Page```
9⃣



🖊Ranaku suna wucewa lokaci na tafiya, yau saura kwana hud'u d'aurin Auren Laraba da
masoyinta Hashim
Hidima sosai 6angarorin guda biyu sukeyi, lnnar Laraba kuwa bata wani damu ba
game da abubuwan da ake bu'kata gurin biki, saboda dama tanada kome ta tanada, sai
d'an abinda ba'a rasaba,

6angaren Laraba kuwa yau sun fita gayya itada 'kawarta indo, sun gayyato 'kawayensu
da dama wad'anda mafi yawansu sunada aure, marassa auren basuda yawa, wasu ma harda
'ya'yansu.

A gajiye suka dawo, gidansu indo suka sauka, lnnar indo tayi masu sannu,
Sannnan suka wuce d'aki suka cire mayafansu suka fito suka d'aura alwala suka
gabatar da sallar la'asar sannan lndo ta d'auko masu abinci suka fara ci, dambun
masara ne yaji zogale, sai 'kamshin man gyad'a ke tashi,
Sun kammala indo ta d'ebo masu ruwa me sanyi a tulu suka sha, sannan suka cigaba da
tattauna yanda shirin bikin ze kasance, sun shirya taron 'kawayen amarya ana gobe
d'aurin Aure.

Sai gab da magrib suka fito indo zatayima Laraba rakiya ta tafi gida, suka gamu da
ilu saurayin lndo,

Laraba ce tafara gaidashi, ya amsa cike da fara'a,
Sannan lndo ta gaidashi cike da jin kunyarsa, ya amsa sannan ya maida dubansa ga
Laraba cikin tsokana yake magana "Amarya baki laifi,.... Laraba tayi saurin
tarbarsa "kada dai ka ida wannan magana dan ba yanda za'ayi mutum yakashe d'an masu
gida ace beyi laifi ba, kai ko kazar masu gida marya takashe sai tayi laifi
barantana d'a.

Suduka sukasa dariya, ilu yace yanzufa nan da kwana hud'u kinzama marya, tayi
dariya tace kai kuma nan da wata d'aya kazama ango, yace "inshaAllah ga kuma
amaryata, ya nuna indo ya wani kashe mata ido, cike da jin kunya indo taja hannun
Laraba tace zomuje dan Allah yamma na'karayi, haka suka wuce suka barshi cike daso
da 'kaunar indon sa.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Yau Yakama Alhamis, kuma daren d'aurin auren indo,
Yau ne kuma suke taro da 'kawayenta, sun taru gidan wata mata nan makwabciyarsu,
anata shewa, Kowa kagani cikin farin ciki, abin Alhamdulillah.
Indo ce tafito cikin shigar sabuwar atamfa riga da zani d'inkin yayimata kyau,
duk da simple ne d'inkin amma ya'kara fito da kyawunta,
Kafarta tasha 'kunshin Jan lalli, tayi kyau tafito amarya sak _(amma a 'kauyensu)_😜

Sun zauna Kowa na yaba kyawu irinna Laraba, wata daga cikin 'kawayensu me suna
hansai tace "gaskiya Laraba kinada kyau, inama ace yayana ne ze aureki ki ri'ka
haifo masa kyawawan 'ya'ya masu Kama dake.

Murmushi kawai Laraba tayi mata dan tasaba jin haka 'kawayenta da dama sunaso ta
auri yayyensu.

Hansai ta matso kusa da Laraba ta rad'a mata a kunne, wallahi yaya habu ya d'ad'e
yana sonki, abinda yasa be furta maki ba dan yaga lokacin bashida 'kud'i, tun bayan
rasuwar masoyinki na farko, yanzu kuma yadawo daga birni yayi kud'i, amma sai
yadawo da rashin sa'a ya iske saura sati d'aurin aurenki.

Wani mummunan fad'uwar gaba Laraba taji lokacin da hansai ta tuna mata da rasuwar
saurayinta, sai lokacin ta tuna da samari biyu nefa aka saka masu rana sai ana gab
da d'aura masu aure suka mutu.

Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta tasa gefen mayafinta ta goge, cikin ranta
tace _(Ya Allah kada ka kashe Hashim Allah sa muna da rabon kasancewa inuwa d'aya
nida shi)_
Ganin Laraba na hawaye yasa hansai tayi shiru da maganar datake tace "dan Allah
kiyi ha'kuri idan maganata ta 6ata maki rai, bata jira jin abinda Laraba zatace ba
ta tashi ta koma cikin 'kawaye aka cigaba da labari, amma tana yawan satar kallon
Laraba dan ganin yanda lokaci d'aya hankalinta ya tashi.

Indo tafito da biskit da cingam wanda suka kulla cikin ba'kar leda tashiga
rarrabawa, saida ta tabbatar da Kowa ya samu sannan takoma kusa da Laraba ta zauna,
tin tana cikin rabon kaya ta lura da 'yanda 'kawar tata take cikin wani irin
yanayi.

Sai gab da magrib 'kawayen amarya Kowa ya watse, lokacin lndo da Laraba suka wuce
gidan su Laraba.

Gidan cike yake da 'yan'uwa da abokan arzi'ki, anata hidima, nan suka gaisheda
mutanen dake tsakar gidan sannan, suka wuce d'aki.

Suna shiga Laraba ta cire mayafinta ta zauna da6as kan tabarmar dake shimfid'e
tsakar d'akin jikinta ba 'karfi ko kad'an,
Indo ta kalleta tace "Laraba na lura dake tun d'azu baki cikin nutsuwarki, wai me
ke damunki?

Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta tace, "lndo jikina duk ya mutu,
hankalina yakai 'kololuwa gurin tashi, gani nake Hashim mutuwa zeyi kamar yanda,
lro da sabi'u suka mutu... ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi.

Indo tace ki daina wannan tinanin acikin ranki, dan Allah ki daina kuka inshaAllah
Hashim baze mutuba, ay mutum baya mutuwa sai kwananshi sun 'kare, suma da suka mutu
dama Allah ya 'kaddaro hakan ne garesu.

Nan lndo tarin'ka rarrashinta, sai bayan isha'i sannan tabar gidan cike da tausayin
halin da 'kawarta take ciki.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Rana bata 'karya sai dai uwar d'iya taji kunya```

'Daruruwan mutane sun taru 'kofar gidansu Laraba domin halartar d'aurin Aurenta.

Yayinda itakuma a ranar ta tashi sukuku, jikinta ba 'karfi ko kad'an, matar 'kanin
babanta ce mal Lawal ta matsa mata tayi wanka ta shirya cikin wata koriyar atamfa,
riga da zani sannan tayi mayafi da kalar zanin atamfar,

A 'kofar gida kuma yan'daurin aure sungama taruwa dangin ango kawai ake jira a
d'aura aure, amma shuru basu ba labarinsu,

Mal Lawal yagama 'kulewa shiru kawai yayi, jira yake dangin angon suzo sai ya sauke
masu ta cikinsa snnan a d'aura auren.

Bayan kamar minti talatin mal Lawal yanata cika yana batsewa, sai ya hango ml bala
tare da wasu mutane guda biyu suna tinkaro su.

Cike da bala'i mal Lawal ya mi'ke dan ya saukema mal bala ta cikinsa, sai mal bala
yafad'a mashi wata magana wacce ni kaina bansan meya fad'a ba, sai ji nayi ya rafka
uban salati, nan mutane suka taso suna tambayarsa "meya faru?.

Cikin gida kuwa mata sunata tsegumin an'ki d'aura aure an shanyasu, jira suke a
d'aura atafi da amarya gidan mal Lawal daga can za'a d'auketa akaita gidan miji.

Baba salame ce wata makwabciyarsu tashigo gidan hankali tashe, bako sallama, da
sauri mutane sukayo kanta ana tambayarta "meya faru? Sai ta fashe da wani irin
kuka, wata magana tafad'a masu bansan me tafad'aba saboda cikin muryar kuka tayi
maganar sai jinayi suduka sun d'auki salati.



*To fah 🤔 nifa ansani aduhu😱 miye ake fad'a wanda yake tada hankalin mutane 😭🙆🏻*



_ku biyo zee mmn khady dan jin cigaban labari_

_08166169254_




🖊Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [21/08 12:15 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*😘


1⃣1⃣1⃣2⃣
1⃣1⃣to1⃣2⃣



🖊 zaune take d'aki tasha lulli6in zanin atamfa, wani mummunan fad'uwar gaba taji,
kawai sai jitayi hawaye suna gangarowa daga idonta, suna diga bisa jikinta.

Hayaniya tajiyo a tsakar gidan, a tunaninta an d'aura auren ne amma koda ta 'kara
saurarawa sai taji sa6anin haka *_Dukkan me

Please Login or Register in order to submit comment