Reading ALHINI by Zee Mmn khadye Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda
take, tin tana kallonsa nesa da ita har yazo gab da ita,
Wani irin matsanancin tsoro ya'kara kamata,
Wata irin 'kara ta fasa sannan ta ranta a na kare๐Ÿƒ๐Ÿป

ยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐ

Inna na kwance d'aki, kan guntuwar tabarmarta sai juyi take bacci ya gagari idonta,
ba abinda take sai tinanin kowane hali 'yarta take ciki,
Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, tasa hannu ta goge,
Lokacin kuma taji Uciyarta tayimata nauyi kamar an d'ora mata wani katon dutse,
lokaci guda taji yun'kurin amai, aiko tatashi zaune tafara amai, babban tashin
hankalin da inna tagani duk yun'kurin datayi maimakon taga aman abida taci, jini ne
take amayowa hadda gundarinsa,

Cikin 'kan-kanin lokaci ta galaibaita tafita hayyacinta,

Da gudu Laraba tashigo gidan, wata irin 'kara tasaki dan ganin halin da inna take
ciki, sauri ta 'karaso gareta, takamata tana kuka tana kiran sunanata,
inna....inna...inna... Da 'kyar inna ta iya d'aga ido ta kalleta tace "Laraba nasan
tawa ta 'kare amma bazan gusheba inamaki addu'ar Allah fiddaki daga mawuyacin halin
da kike ciki.

Fad'uwa tayi rai yayi halinsa, ```Allahu akbar inna tarigamu gidan gaskiya```

Wata uwar 'kara Laraba tasaki, dan ganin inna ba Alamar numfashi tattare da ita,

Wani irin duhu taga ya gufta mata, kokacin kuma kanta yayi wata irin sarawa, jiri
ya ibeta ta fad'i kasa sumammiya,....




๐Ÿ–ŠZee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [24/08 7:45 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


2โƒฃ3โƒฃ2โƒฃ4โƒฃ
2โƒฃ3โƒฃto2โƒฃ4โƒฃ
2โƒฃ3โƒฃ2โƒฃ4โƒฃ


๐Ÿ–Šwashe gari tunda asuba Habu yanufi gidan iyayenshi, yana isa innarshi taganshi da
uban rauni a kai, ga jikinshi jage-jage da jini, dan be canja kayaba haka ya kwana,
wani uban salati ta buga tace "Habu lafiya meya faru dakai, ina Larabar,? Lokaci
d'aya ta jero mashi wad'annan tambayoyin, Habu bayaso ya fad'i gaskiyar Al'amarin
abinda yafaru dashi saboda besan wani halin fad'in ze jefa laraba ba, saboda haka
shiru yayima innar tashi.

Innar taga bayada niyyar bata amsar tambayoyin datayi mashi, kawai saita d'ora
hannu a kai tafashe da kuka, wanda yin hakan ya jawo da hankalin mutanen gidan
garesu, duk akayo d'akinta ana tambayarta lafiya meya faru, dayake gidan irin
gidan yawa ne,
Ganin habu dasukayi zaune ga jini duk ya 6ata jikinsa yasa suka ba kansu amsa,
tabbass koba tambaya sun san larabace ta tasarma kasheshi Allah beyiba dayake
yanada sauran shan ruwa.

Wata mata cikin mutanen dake tsai-tsaye Bakin 'kofar d'akin tace "ina kabaro
amaryar angon Laraba?
cike da takaici habu ya kallesu yace "Laraba na gidansu na saketa,

Wani uban salati matan suka d'auka lokaci guda, sukace "yo habu ya akayi haka
tafaru?
Be basu amsaba illah fita dayayi yabar gidan dan bayaso ana can-cana maganar.

Wata tsohuwar mata ta kalli innar Habu tace "Wallahi atika kinyi ta barka, dan
wannan maganin da 'yar me ganye tabada tace ki binne a gidan, amma da badan haka ba
da yanzu habu sai dai wani bashiba.

Innar habu tayi murmushin takaici tace "Hmmm Wanda beji bari ba ay yaji hoho, cikin
gidanan waye be ba Habu shawarar kada ya auri Laraba ba amma yakafe, ay dama me
rabon shan duka bayajin kwa6a, bata jiran me sauran matan zasu fad'aba tashige
d'aki tana matsar kwalla.

Ganin haka yasa kowace takama gabanta, suna fad'in albarkacin bakinsu,
Abinka ga matan 'kauye kad'an suke jira su 'kara, kafin kace me labari ya bud'e
gari.

Mutanen gari anata yayatawa, Laraba takusa kashe Habu Allah ya taimakeshi ya
saketa.

Aiko labari yakaima mal Lawal, a fusace yanufi gidansu Laraba da niyyar yaci masu
mutunci itada uwarta wacce ke d'aure mata gindi tana kashe mutane.

Bako sallama ya bankad'a 'kyauren gidan yashiga,
Laraba yagani ta had'a kai da gwiwa tana kuka, gefe kuma ga innarta kwance cikin
jini.

"Ke.....ya daka mata tsawa, da sauri ta d'ago da fuskarta ta kalleshi, saitaji wata
dama-dama a ranta, tunda tariga tasan inna tamutu, kuma batasan wa zata gaya
mawaba, tunda mutane yanzu da sun ganta guduwa suke.

Da sauri ta taso tazo gabanshi ta dur'kusa, yanzu kam idonta ba hawaye ko kad'an
dan tayi kuka har hawayenta sun 'kafe, tace "dan Allah baffa Lawal ka taimakeni
inna ta mutu, tun jiya da dare, ban san yazanyiba, shiyasa ban fitaba dan nasan duk
inda na nufa ba wanda ze saurareni,

Wata irin dariya mal Lawal yayi sannan ya kalli Laraba yace, "watako maitar taki
har takai ga uwar data haifeki, to wallahi ki shiga hankalinki, danni idan kikace
zaki cinyeni sai inci ubanki, 'yar iska kawai, yakai mata wani hauri har saida ta
fad'i, sannan yafita yabar gidan.

Zuwa yayi yasanar da mutane, innar Laraba ta mutu, amma kowa sai yace Allah
ji'kanta, da ance suzo ayimata sutura akaita makwancinta sai kaga mutum yafara
zame-zame Alamar dai baya zuwa.

Haka akayita fama da muatanen Gari, karshe dai saida me gari yasa Baki, yasa liman
da wasu tsirarun mutane akaje akayima innar
Laraba wanka akayimata sutura aka kaita makwancinta,
Kuka kau Laraba yanzu ta daina na hawaye, sai dai na zuci, dan zuciyarta tariga
tagama soyewa, tasaba da ba'kin ciki da takaici.

*_BAYAN KWANA BAKWAI_*

Yanzu Laraba ita kad'ai ke kwana gidansu babu me ra6arta, ga yunwa dan ba wanda
kebata koda sauran abinci, idan kuma tafita dan tasiyo abinda zataci dataje shago
sai muatane sukama gudu, haka zata dawo gida takama kuka, abin dai gwanin ban
tausayi, duk ta rame ta kod'e idanun nan sun kara fitowa sunyi zuru-zuru, ga wani
ciwon ciki datake fama dashi sakamakon yunwar datake fama da ita,

Ruwa kawai take banka ma cikinta koda yaushe, to yanzu ma idan tasha ruwan sai ya
'kulle mata ciki tayita amai,

Yau dai tagaji da bala'in datake ciki, saboda haka tayi niyyar zuwa gidan baffa
Lawal dan ya taimaka mata.




๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [25/08 7:08 am] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


2โƒฃ5โƒฃ2โƒฃ6โƒฃ
2โƒฃ5โƒฃto2โƒฃ6โƒฃ
2โƒฃ5โƒฃ2โƒฃ6โƒฃ



๐Ÿ–Š Baffa Lawal ne cikin gonarshi yanata noma, yanayi yana 'yar wa'ka irin ta mutanen
'kauye, abin yayi masa dad'i har gyad'a kai yakeyi, zuwa can kuma sai yatashi
yanufi inda ya ajiye kayansa ya fiddo da wata 'yar madai-daiciyar radio, yasanya
sabbin batura ya 'kunna, ya kuwa yi sa'a gidan redio an sanyo wa'kar d'an kwairo,
aiko sai ya rataye redion jikin bedi yana ji yana aikinsa,

Befi minti shidda da kunna red'ion ba sai yaji d'if redion ta d'auke, ya d'ago
kansa ya duba bega kowaba, yaje ya ta6a redion sai yaji kashe take, nan ya sake
kunnawa ya maida yarataye ya juya ze cigaba da aykinsa sai yaji an 'kara kashewa,
yana juyowa wa ze gani,

Laraba ce tsaye jikin bedin tana yimashi wani mugun kallo,
Cike da masifa da bala'i baffa Lawal ya tunkarota na niyyar ya wanka mata mari,
amma kafin yayi wani Abu sai jin saukar mari yayi, a fuskar shi.

Cike da tsoro yakai dubansa ga Laraba, wacce tana dai tsaye inda take ko motsi
batayiba, wani wawan mari aka 'kara d'aukeshi dashi, lokaci guda kuma aka rufeshi
da duka ta ko'ina, Laraba dai na tsaye har yanzu bata motsa ba,
Haka akayita jibgar mal Lawal saida ya daku sannan aka 'kyaleshi, wata irin
mahaukaciyar dariya Laraba ta she'ke da it'a sannan ta 6ace, mal Lawal yashiga
rud'ani, hankalinsa yayi matu'kar tashi, jikinsa yakama 6ari, aiko da sauri ya
tattare 'yan kayanshi yanufi gida,

Ganin ya shigo hajaran-majaran yasa matarshi tamabyarshi, "mal lafiya, meya faru
naga ka dawo tun 'yanzu gashi ko azahar batayiba,
Mal Lawal bayaso yafad'i gaskiyar Al'amari dan kada mutane suyi Mashi dariya, sai
cewa yayi "gajiya nayi kuma jikina ba dad'i d'an dafamin ruwan d'umi inyi wanka,
cike da mamaki matar tace "ruwan dumi kuma malam ๐Ÿค”, kaida idan kadawo daga gona
kake son ka watsa ruwan sanyi amma yau ruwan d'umi kake nema,

Aiko nan yarufeta da bala'i "keni banison shashanci, Idan zaki dafamin ki dafamin,
idan kuma bazaki dafaba ni in tashi in dafa da kai.........

Be ida rufe bakiba, Laraba tashigo gidan da sallama, mal Lawal naganinta jikinsa
yafara kyarma, yace "la......la....la...raba miya kawoki nan? Ba yanzu kikaje gona
kika sameni,

Cike da ladabi Laraba ta dur'kusa har 'kasa tace "wallahi baffa banje gonarkaba, ni
yanzuma daga gida nake, dan Allah baffa ka taimakamin da abinci yunwa nakeji,

Cike da tsoro baffa Lawal yace "bamu dafa ba, ki koma idan mun dafa zan kawo maki
har gida, jiki ba 'kwari Laraba tanufi hanyar fita daga gidan, matar baffa Lawal ce
taji wani irin tausayinta yakamata, ta kirata taje d'akinta ta d'auko mata wata
tsantsamar fura tace anshi kisha ko wannan ce kafin ayi abincin akawo maki, jiki na
'kyarma Laraba ta kar6a ta kafa kai ta shanye sannan ta ajiye kwaryar tace "nagode,
sannan tabar gidan zuciyarta cunkushe da ba'kin ciki da takaici.

Laraba kuwa daga gidan baffa lawal maimakin tayi hanyar gida saita yanki hanya
tayita tafiya cikin daji, saida tayi nisa da Gari, wani wawakeken rami ta iske
gabanta, nan ta tsaya tana kallon fad'in ramin da zurfinsa, take wasu zafafan
hawaye suka wankemata fuska, a fili ta furta "'kara in mutu da rayuwar ba'kin cikin
danake ciki, lokacin kuma taji kanta ya sara,idanunta sun rufe, bata ganin kome,
nan ta fad'i war-was gata gab da ramin, dan motsi kad"an zatayi ta ida afkawa ciki.

ยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐ
Tafiya yake cikin had'ad'd'iyar motarshi 'kirar Camry mai ruwan sumunti, tu'ki yake
cikin kwanciyar hankali, cikin motar kuwa ba abunda ke tashi sai sanyin a,c daya
had'e da kamshin freshener, sai kuma 'kirar'ar sheik Abdurrahama sudais dake tashi,

Tafiya yake amma zuciyarshi na raya mashi abubuwa da dama, game da 'kauyen kwata-
kwata babu titi ko d'aya sai dai mutum yayita bi cikin jar 'kasa da burji,

Kamar ance yakai dubansa gurin, lnnalillahi yafad'a yayin da ya hango mutum kwance
'kasa, gab da wani wawakeken rami, da sauri yayi fakin din motarshi yafito, addu'a
yafarayi kafin yakai hannunshi gareta, saida ya tabbatar da sauran numfashi jikinta
sannan ya kinkimeta ya sata bayan motar shi,

Juya akalar motar yayi yakama hanyar komawa cikin gari, tafiyar awa ukku ta dadashi
da garinshi, asibiti ya wuce kai tsaye, da sauri aka amshi Laraba aka shiga wani
d'aki da ita domin duba lafiyarta.

Awon farko aka gano yunwace ke neman halaka ta, nan aka d'aura mata drip, sannan
akayimata Allaurai, bata farka ba amma likitan ya tabbatar mashi da lafiya lau babu
wata matsala zata iya tashi koda wane lokaci, saboda haka asamo mata abinda zataci,
dan tana tattare da yunwa kuma tana bu'katar abinci mai kyau.
๐Ÿ–ŠZee Elkaseem
Mmn khady๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [25/08 8:21 am] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜



2โƒฃ7โƒฃ2โƒฃ8โƒฃ
2โƒฃ7โƒฃto2โƒฃ8โƒฃ
2โƒฃ7โƒฃ2โƒฃ8โƒฃ


๐Ÿ–ŠMotarshi yanufa a zuciyarshi yana tausayama halin da yarinyar take ciki, mintina
da basu wuce sha ukku ba suka sadashi da gidan iyayenshi, wani 'katon gida ne
had'adden gaske, bakin get yayi horn me gadi ya bud'e mashi get yashiga da
motarshi, gurin ajiye motoci ya ajiye motarshi, motocine gurin kusan guda shidda,
sai lokacin nagane ashe wacce naganshi ciki batada kyau, dan manya- manyan moticine
masu tsadar gaake ajiye gurin, wannan yafita da itane dan yasan yanayin garin da
zaya.

Hanyar da zata sadashi da ainafin cikin gidan yanufa, kai tsaye falon hajiyarsa
yanufa.

Wata dattijuwar mata ce zaune cikin falon, cikin shiga ta Alfarma, idonta sanye
cikin wani siririn farin glass, wanda da alama medical ne, hannunta ru'ke da Al
Qur'anic, tana nazari, gefe kuma wata 'kya'kyawar yarinyace wacce bata wuce shekara
sha biyarba, ita kuma ta maida hankalinta gun kallon TV, tashar sunnah tv take
kallo.

Sallamar yayan nata yasa tayi saurin kai dubanta gareshi tare da amsa sallamar,
tace "lah Yaya Mukhtar, ya akayi ka dawo yanzu, ko baka kai da tafiya bane, yace
"naje mana, amma ban kai ga isaba wata 'yar matsala ta maidoni, tace matsala kuma
Yaya, Tame?

"To tambai, wannan tamaboyoyi haka, kamar wata 'yar jarida, tace "hm Yaya Mukhtar
ai ko banzama 'yar jaridaba kasan abinda nake burin zama,
Yasan kullum burinta be wuce na tazama lawyer ba, murmushi yayi yace "Allah
taimaka, inaso ki shiga kitchen keda Uwani me aiki ku dafamin abinci, jallouf d'in
wake da shinkafa zakiyi, ayi amfani da hanta gurin girkin, dan bani bu'katar wani
kalan nama, sannan a dafamin ruwan zafi ahad'a kayan tea,

zatayi magana yayi saurin tarbarata "banison tambaya kiyi sauri ina jiranki yanzu,
haka Jidda tanufi kitchen a zuciyarta tana tinanin me Yaya zayayi da abinci yanzu
kuma harda kayan tea.

Sai da yagama da Jidda sannan yanufi inda mahaifiyarsa take, wacce duk abinda suke
shida Jidda tana jinsu, itama zuciyarta cike take da tambayoyi da dama gareshi.
Cike da ladabi ya isa gurin hajiyar tashi, yasamu guri ya zaune kusa da 'kafafunta,
yace "Hajiya barka da hutawa, cike da fara'a ta kalleshi tare da rufe Qur'anic dake
hannunta tace "yauwa, kafin tayi wata magana yace "nasan zakiyi mamakin ganina
yanzu, wata yar matsalace ta maidoni, nan ya kwashe yanda ya tsinci Laraba ya gaya
mata, take tausayin yarinyar yakamata, kuma tayi alwashin taimakamata.

Saida sukayi sallar magrib sannan suka nufi asibiti, Mukhtar ne ke driving, sai
Jidda dake zaune gefensa duk ta isheshi da surutu, sai Uwani me aike dake bayan
motar,

Jidda ta kalli yayan nata tace, wallahi yaya har na 'kagara inga yarinyar nan,
wallahi ta matu'kar bani tausayi, ko ina iyayenta suka barta, har yunwa na neman
halakata, kai wallahi mutanen 'kauye basuda hankali, wai sai mutum yayi zaune da
yunwa har sai tayi mashi lahani,

Mukhtar dai jinta kawai yake tanata zuba, be cemata uffan ba har suka iso asibitin,
Parking d'in motarsa yayi inda aka tanada dan ajiye motoci sannan suka nufi cikin
asibitin uwani na d'auke da kwandon da aka jero kayan abincin ciki.

Sun shiga d'akin da Laraba take, zaune suka isketa, tayi zuru da alama tafad'a
kogin tinani, saida sukayi mata sallama sannan ta dawo hayyacinta, binsu kawai tayi
da kallo dan su duka ba wanda tasani, jidda ce tafara magana, tace "Yaya wannan
itace yarinyar daka tsinta d'in, kai Amma ky'k'kyawa da ita, amma gaskiya mutanen
'kauye basuda wayo da har sukayi sakaci da wannan 'kya'k'kyawar yarinyar... Wata
uwar harara yayan nata ya daka mata, hakan yasa tayi saurin jan bakinta tayi shuru,

Sannan ya maida kallonshi ga uwani yace "Uwani gatanan ki bata abincin, Uwani da
tunda suka shigo take kallon Laraba, tana yaba irin kyawun da Allah ya zuba mata,
tace "to amma yakamata ta d'an watsa ruwa taji dad'i kafin taci wani abu, sai dai
kuma babu kayan da zata canja idan tayi wanakan, jidda tayi saurin cewa "yaya muje
gida in d'auko mata cikin kayana, Mukhtar ya gyad'a kai yace barshi kawai bari inje
in siyo mata, ya kalli uwani yace a taimaka mata tayi wankan kafin indawo, sannan
yafice daga d'akin.

Bayan fitarshi uwani tahad'ama Laraba ruwan d'umi ta kaita kewaye, ta gwada mata
yanda zatayi, dayake Laraba yarinyace mai nutsuwa batayi wani karanbani ba, yanda
aka gwada mata haka tayi, ta dade tana wanke jikinta da sabulu mai 'kamshi, wanda
rabon datayi wanka da ruwa ma har ta manta, sai da ta tabbatar da tayi fess sannan
tafito daga kewayen.

Bata dade da fitowaba mukhatar yashigo da wata 'katuwar Leda a hannunsa, ya mi'kama
Uwani, sannan yafita daga d'akin yabasu guri dan suji dad'in aiwatar da kome.

Jidda ce tayi saurin zazzage kayan tana dubawa, kayane kusan kala takwas duk na
kanti, wasu riga da siket wasu kuma dogayen riguna,
Wata doguwar riga jidda ta d'auko, kalar sararin samaniya daga gaban rigar anyi
mata kwalliya da duwatsu dark blue tace wannan zaki sanya, Laraba dai binsu kawai
take da ido, dan ita har yanzu batasan a ina take ba, ba musu ta 'kar6i rigar ta
sanya sannan jidda ta d'aura mata d'an kwalin rigar, wani irin kyau tayi duk da ba
wata kwalliya bace a fuskarta, jidda kasa yin shiru tayi tace "kinga yanda kikayi
kyau, wai miye ma sunanki, sai lokacin karaba ta iya bud'a Bak tace "sunana Laraba,
jidda tayi murmushi tace wallahi na d'auka larabci zanji kinyi, dan kwata-kwata
kinfi kama da jinsin larabawa, to amma miye asalin sunanki dan Laraba ba suna
bane...

Mukhatar ne yashigo da sallama, yakai dubansa ga Laraba, wani dum yaji gabansa ya
fad'i dan bacin yasan uwani da jidda suna d'akin da sai yace wannan ba yarinyar
daya tsinta bace, saboda wani masifaffen kyau datayi mashi.
Tambaya yayi taci abincin kuwa, Uwani tace "jira nake agama shirin sai in zuba mata
abincin, wata harara yayima jidda dan yasan kicifin tane, mutumin da beda lafiya
har wani shiri za'ayimashi.

Da kanshi ya had'a tea mai kauri Wanda yaji madara da Milo ya mi'ka mata.
Ba musu ta 'kar6a ta kafa kai ta shanye, dayake tanada bu'kata dama, sannan aka
zuba mata jallouf d'in wake da shinkafa wanda yaji kayan lambu da hanta, nan ma
taci amma kad'an kasancewar tean data sha yacika mata ciki.




๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [26/08 12:13 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜



2โƒฃ9โƒฃ3โƒฃ0โƒฃ
2โƒฃ9โƒฃto3โƒฃ0โƒฃ
2โƒฃ9โƒฃ3โƒฃ0โƒฃ



๐Ÿ–Šsai bayan sallar isha'i sukayi niyyar barin asibitin bayan sun yanke cewa Uwani
zata zauna gurin Laraba, aiko itama jidda kafewa tayi dole sai an barta ta kwana
gurin Laraba, saida mukhtar yayimata fad'a sannan suka tafi, ranta yayi matau'kar
6aci dan an hanata kwana gurin Laraba,

Haka suka tafi tanata zum6ura baki ita a dole fushi take, dan ko surutun data
sabayima yayan nata yau batayiba tunda ya 6ata ranta,
Yana lura da ita yanda taketa cika tana batsewa, amma sai yayi kamar besan
tanayiba,
A haka suka iso gida, bakin get sukayi horn me gadi ya bud'e masu get suka Shiga,
gurin ajiye motoci yayi parking d'in motarsa, kafin ya gama gyara parking tafito
daga mortar tanufi cikin gida da gudu, tana zuwa falo bata taradda Hajiya ba,
saboda haka bedroom d'inta ta wuce kai tsaye, zaune ta isketa kan abin sallah tana
tasbihi, fad'awa tayi jikinta tana kuka,

Cike da mamaki Hajiya ke tambayarta "lafiya jidda meya faru, meya saki kuka ina
yayan naki,? Kafin ta bata amsa sai gashi yashigo, cikin ladabi yake gaisheda
hajiyarsa, sannan yace "Hajiya bafa wani abune yafaruba, kawai dan nace bazata
kwana asibiti bane shine take fushi,

Murmushi Hajiya tayi tace "haba Jidda yaza'a barki ki kwana, asibiti ayba gurin
zaman yaro bane, kibari idan Allah ya kaimu gobe tunda ba school sai mu tafi tare
nima zanje in gano yarinyar,

Haka Hajiya tayita rarrashinta har tasamu ta saki ranta, tayi murmushi tace "Hajiya
bakiga yarinyar ba wlh kya'k'kyawa da ita, ni naji dad'i nasamu 'kawa, Hajiya tayi
murnushi tace daga ganin sarkin fawa sai miya tayi za'ki, daga ganin yarinya sai
kice kinyi 'kawa,
Mudai iyakarmu taimako, kuma data samu lafiya ta warware zamu maidata ga iyayenta,
nasan yanzu duk inda iyayenta suke suna can hankalinsu ba kwance ba,

Jidda tayi saurin tashi daga kwancen datake kan cinyar Hajiya tace "dan Allah
Hajiya kada a maidata, inasonta inaso tazama 'kawata,
Hajiya bata cemata komeba sai murmushi kawai tayi, *(Yaro man kaza)* sai
lokacin Mukhtar yayi magana yace "kedai baki gajiya da shirme, ke yanzu kinaso
arabaki da Hajiya wasu su ri'keki,
ta turo baki tace to ayni hajiyata na sona bazata barni da yunwa ba,har in
kusa mutuwa wasu su tsinceni, harara yayi mata sannan yafita yabar d'akin.


'Dakinsa yanufa kai tsaye zuciyarshi cike da tausayin Laraba, shi kanshi yanda
jidda tafad'a hakane bayason rabuwa da Laraba, dan tsakanin wannan d'an lokacin
wani irin abu yakeji dangane da ita,

Da wannan tinanin yafad'a toilet ya she'ka wanka, sannan yafito ya canja kaya,
jallabiya yasa me gajeren hannu sannan yanufi babban falo, can ya iske Hajiya da
jidda kan dining suna niyyar cin abinci, shima kujera d'aya yajawo ya zauna kusa da
hajiyarsa, jidda ce ta zuba mashi tuwon shinkafa da miyar Alayyahu, sai 'kamshin
curry ke tashi,
Haka suka ci abincin kowanensu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bayan sun
'karasa suka kora da kunun aya me sanyi, sannan suka ta6a fira

Sai gurin 'karfe goma sannan, sukayi bankwana, mukhtar ya wuce d'akinsa, jidda kuwa
d'akin Hajiya tanufa, Hajiya ta kalleta tace "kika biyoni nan d'akin naki kuma fa?
Cikin shagwa6a tace "Hajiya ki barni in kwana anan idan aka sallamo Laraba ta dawo
nan gidan sai mu koma d'akin nida ita kinga nasamu abokiyar fira, murmushi Hajiya
tayimata sannan ta canja kaya zuwa kayan bacci, itama jidda kayan baccin ta sanya
sannan suka haye katafaren gadon wanda yasha wani lallausan bedsheed, sukayi addu'a
suka shafe jikinsu.

Mukhtar kuwa koda ya koma d'aki tinanin Laraba ya zauna a kwa'kwalwarsa, cikin
zuciyarshi yari'ka ro'kon Allah sa iyayenta su yarda ta zauna tare dasu, dan shima
har ga Allah baya son rabuwa da ita, yarinya 'kya'k'kyawa amma dayake 'kauye ta
taso sukayi sakaci da rayuwarta har tana neman halaka.

Da wannan tinanin bacci yayi awon gaba dashi bayan yayi addu'a Ayatul kursiyyu da
qula'uzzai ya shafe jikinsa.

_```Waye Mukhtar```_?

Mukhtar Abass shine asalin sunanshi, haifaffen d'an garin katsina ne, a wata unguwa
me suna 'yan,shuni.

Mahaifinshi Alh Abass, mutum ne mai ilimin addini, kuma yana aiki dashi, dan duk
wani abu daya shafi addini yana fidda dukiyarshi yayi hidima da ita, shiyasa kullum
Allah ke 'kara bud'a mashi, kuma dama yana dukiya me yawa ga kuma taimakon na 'kasa
dashi da miskinai, ga fidda zakka duk shekara kamar yanda Allah ya hukuta.

sunyi auren saurayi da budurwa da matarshi wato Hajiya Zainab, bayan aurensu da
shekara ukku Allah yabasu haihuwa inda suka haifi namiji aka sanya mashi suna
Aliyu, har Aliyu ya shekara bakwai Hajiya Zainab bata kuma haihuwa ba, wata rana an
taso su Aliyu makaranta yafito bakin titi yana jiran driver yazo d'aukarsu wata
mota ta bankeshi, kafin akaishi asibiti rai yayi halinsa, Hajiya Zainab da Alh
Abass sunyi kukan rashin d'ansu, 'karshe suka ha'kura suka fawwalama Allah
lamuransu, kuma daga lokacin Hajiya Zainab bata kuma samun cikiba sai bayan shekara
biyu tasamu cikin mukhtar, bayan an haifeshi ne da shekara bakwai aka haifi jidda,
wanda daga ita hajiya Zainab bata kuma haihuwaba.

Jidda nada shekara ukku Allah yayima mahaifinsu Alh abass rasuwa bayan yayi fama da
gajeruwar rashin lafiya,

Bayan rasuwar Alh Abass da shekara d'aya 'yan'uwan Hajiya zainab sunso takoma
garesu amma sai tace sam bazata komaba zata zauna ta ri'ke yaranta dan bataso ta
dorama wani nauyinsu.

Haka Hajiya Zainab tacigaba da kula da karatun yaranta da tarbiyarsu, amma haka be
hana 'yan,uwan Alh Abass taimakonsuba, dayake mahaufinsu mutum ne mai taimakon
'yan,uwa.

lokacin da muke yanzu, mukhatar yazama cikakken d'an kasuwa, dan sana'ar babansa
kenan kafin ya rasu, hakan yasa mukhtar karantar business, ga kuma kiyo da suke a
gidan gonarsu da mahaifinsu ya bar masu gado, lokcin da mukhatar ya tsinci laraba
gidan gonar tasu yanufa, sai Allah ya had'ashi da ita.

Jidda kuwa yanzu take junior secondary, j.s.s 3 bana zasu zana jarabawa.

*_WANNAN SHINE TAKAITACCEN TARIHIN MUKHTAR_*




๐Ÿ–ŠZee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [26/08 9:30 pm] ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


3โƒฃ1โƒฃ3โƒฃ2โƒฃ
3โƒฃ1โƒฃto3โƒฃ2โƒฃ
3โƒฃ1โƒฃ3โƒฃ2โƒฃ


๐Ÿ–Š Haka Uwani tacigaba da kula da Laraba, yayinda mukhatar kullum sai yayi zuwa
yakai shidda asibitin, dan bayaso anemi wani abu baya nan, hajiyar Mukhtar kuwa sau
ukku tana zuwa ganin Laraba, jidda kuwa 'yar rigimar kullum nan take yini, kuma sai
anyi daga da ita gun komawa gida, dan kullum kafewa take sai ta kwana,

Satin Laraba d'aya asibitin taji sauki sosai, ta'kara fari tayi wani fresh, dan har
'yar 'kiba tayi, tana samun kulawa sosai daga malaman asibitin zuwa ga mukhtar sai
kuma Uwani me aiki itama tana bakin 'ko'karinta.

Yau Likitan dake dubata yazo round nan ya duba jikin uwani ya tabbatar da kome
normal, sannan yarubuta masu sallama.

Mukhtar ne ya d'aukesu a mota, jidda ce gaban mota kusa da yayanta, yau dai farin
ciki fal a zuciyarta, dama kullum addu'a take a sallamo Laraba 'kawarta ta dawo
gidansu da zama,
uwani da Laraba kuwa bayan motar suke sunata sauraren jidda da keta zuba uban
surutu.

Dai-dai get d'in gidan sukayi horn me gadi ya bud'e masu get suka shiga,
Tunda sukazo Laraba kebin gidan da kallo, saboda tsananin 'kyawunsa, cikin
zuciyarta tace _"Anya ba mafarki nake ba, dan bani tinanin akwai irin wad'annan
gidajen nan duniyar da muke_

Niko nace *Hmm Laraba kenan sai ma kin shiga gidan zaki tabbatar da ba irin duniyar
da kk sani bace, (wani hanin ga Allah baiwa ne)*

Jidda ce takama hannun Laraba sukayi cikin gida, wani irin tsoro yakama Laraba dan
ganin 'kawatuwar falon, kai lallai dama ashe akwai masu irin wannan jin dad'in a
duniya, haka kawai take fad'a a zuciyarta.

Cike da murna da sakin fuska Hajiya ta tarbesu tanayimasu sannu da zuwa, jidda kuwa
murna yau gurinta bakin har ya'ki rufewa, da kanta ta zaunar da Laraba kan kujera
tace "Zauna 'kawata ki huta kafin anjima kiyi wanka,
Laraba dai kallon mutanen kawai take, duk abinda sukace shi take yi, tazama tamkar
ra'kumi da akala,

Bayan sallar azahar suka zauna kan dining suna cin abinci, jidda ce ta matsama
Laraba ta zauna suci, amma ita duk d'arare take ba kamar idan da mukhtar gurinta
dan wani irin kwarjini yake mata.



Bayan sun kammala ne jidda ta kama hannun Laraba tace 'kawata zo muje ciki kiyi
wanka ki canja kaya, ba musu Laraba tabita zuwa d'akinta,
Toilet taje ta had'a mata ruwan wanka, tare da zuba mata turarurrukan wanka masu
'kamshi gaske, sannan tazo ta kama hanunta ta kaita har toilet ta gwada mata yanda
zatayi, sannan ta jawo mata 'kyauren tafito tana jiran ta.

Laraba ta dad'e tana dirje jikinta a kewaye, kafin tafito d'aure da zanin atamafa
jikinta, dan 'kin yarda tayi da d'aura tawul, dan bata ma san yanda zata d'aura
shiba.

Jidda tace "harkin fito, ta kamo hannunta zo inyimaki kwalliya irinna larabawa,
laraba tayi murmushi tace " Hmm jidda kenan'har wata kwalliyar larabawa akeyi,
jidda tayi dariya tace kedai bari kigani idan nayimaki ke kanki sai kin kasa gane
kanki, murmushi kawai Laraba tayimata, dan abun jidda har mamaki yake bata yanda
take nan-nan da ita,

Please Login or Register in order to submit comment