Reading ALHINI by Zee Mmn khadye Chapter 7 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

arzi'ki fatima ta tara gun sunan ba, saboda 'yan'uwan mukhtar
sunyi mata kara sosai, a ranar ma saida jidda ta zubar da hawayen *_ALHININ_*
tunowa da mahaifiyarta, da kuma ganin duk taronnan da kuma abin arzikin data tara
babu 'yan'uwanta ko d'aya.

Yanzu gashi tayi aure har Allah ya azurtata da samun d'a amma ba rabon innarta taga
wannan ranar, *(Allah sarki laraba haka Allah ya 'kaddara)*

Haka akagama hidimar suna Kowa ya koma gidansa cike da farin ciki, washe garin suna
hajiya tace Mukhtar ya maido fatima gida dan tayi wanka anan, haka Mukhtar ya
maidota badan ranshi yasoba, yaso ace anbarta gidanta tayi wanka acan kullum yana
kusa dasu itada babynsa, ya d'auko matar dazata ri'ka kula dasu amma Hajiya ta'ki
amincewa da hakan, saboda haka dole ya tattarasu ya kaisu can badan ranshi yasoba
sai dan bin umarnin mahaifiyarsa.

Jidda kuwa dama Usman tunda aka gayamashi ya amince da tafiyarta gida wanka, saboda
haka itama washe garin suna Usman da kanshi ya tattaro ya kawota gidan da kanshi.

Haka Hajiya tacigaba da kula da 'ya'yanta da jikokinta, tare da taimakon jummai me
aiki.
_*BAYAN WATA BIYU*_

Hajiya na zaune falo ta tasa 'yan jikokinta gaba zuciyarta cike da farin ciki,
yaran sai wutsil-wutsil suke da 'kafafunsu da hannuwa alamar suna cikin 'koshin
lafiya.

Jidda kuwa da fatima suna zaune gefe sunsha kwalliya kamar wasu sabbin amare, dan
bazaka kallesu kace sun ta6a haihuwaba, kome nasu cif,

jidda kwalliyar tata ta taron me gidanta ce dan yayimata waya yana zuwa, itakuma
fatima dama tunda suka dawo gidan shima mukhtar ya dawo nan dan kwana kad'ai ke
beyi anan.

Da misalin 'karfe hud'u na yamma Usman ya iso gidansu jidda,
Bayan yayimata waya ya sanar da ita zuwanshi tayimashi masauki a a falon ba'ki,
bayan ta cikashi da kayan ciye-ciye da lashe-lashe, komawa tayi cikin gida ta
d'auko rahama, a kafad'a ta sa6ota, tana taku Ahankali cikin nutsuwa harta iso
gurinsa tasamu guri ta zauna gab dashi, 'kamshin turarensu ya gauraya dana juna,
sannan ta gaidashi, bayan ya amsa suka cigaba da firarsu.

Acikin firar nasu ne Usman yake cema jidda "A gaskiya jidda nayi rashinki kusa dani
yaufa tsawon wata biyu kenan yakamata ace kin koma hakanan, jidda tayi murmushi
tace nima nayi missing d'inka, usman yace "ban yarda da zancenkiba, jidda tayi
saurin kai dubanta gareshi "baka yardaba fa kace, yace "kwarai ko dakinyi missing
d'ina dakincema hajiya kinaso ki koma haka, domin ni gaskiya inajin kunyar
fad'amata, jidda tayi murmushi tace "indai wannan ne kada ka damu kabani kwana biyu
inshaAllah zan dawo cike da jin dad'i usman ya rungume jidda yana sumbatar ta, wani
irin feeling sukaji suduka sakamakon rashin jin d'umin junansu dasukayi na tsawon
lokaci.

Baby rahama kuwa kwantar da ita jidda tayi kan kujera tanata sharar baccinta,

Haka suka rin'ka romancing junansu, lokaci guda Usman ya rikice yafita hayyacinsa,
idanunshi sun rufe yama manta da gidan surukai yake, sai da jidda taji yana
'ko'karin wuce gona da iri sannan tayi 'ko'karin saita nutsuwarta dan itama ta
shiga wani irin yanayi, ta tureshi daga jikinta sannan ta tashi daga kujerar dayake
ta koma nesa kad'an dashi tana maida numfashi,

Shima kallonta kawai yake yakasa ta6uka kome idanunnan nashi sun kad'a sunyi ja,
kusan mintuna ishirin suna haka sannan suka dawo hayyacinsu, ya kalli jidda cikin
wata wahalalliyar murya yace "jidda zan tafi kinga magrib ta gabato amma zan shiga
mu gaisa da hajiya tukun, tace "ba damuwa amma kasa ran dawowata nan da 2 days,
yace "danafi kowa farin cikin hakan, tayi wani 'kawataccen murmushi tace kada ka
damu abban rahama, wani irin dad'i yaji dan jin sunan data kirashi dashi, sannan
yakai dubanshi ga 'kya'k'kywar babynsa rahama wacce ke baccinta cike da jin dad'i,
yace "je kiyimin iso gun hajiyar.

Haka ya shiga suka gaisa da hajiya, fatima da kanta tazo suka gaisa sannan ya
d'auki sultan yana mashi wasa, jin anata kiraye-kirayen sallar magrib yasa ya mi'ke
tare dayimasu sallama sannan ya wuce, jidda tarakashi har gurin motarshi saida taga
tafiyarshi tana d'aga mashi hannu sannan tadawo cikin gida cike da tsananin so da
'kaunar mijinta.
🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:13 PM] www.gidannovels.blogspot.com [17/09 7:30 pm] 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘


6⃣5⃣6⃣6⃣
6⃣5⃣to6⃣6⃣
6⃣5⃣6⃣6⃣


🖊 Bayan sallar isha'i mukhatar ya shigo gidan a falo ya iskesu zazzaune suna shirin
cin abinci,
Shima zama yayi fatimace tayi serve kowa ta ajiye a gabanshi, bayan sun kammala cin
abincinne Hajiya ta kalli mukhatar tace "d'azu mijin jidda yazo kuma ya nuna yana
bu'katar matarshi saboda haka bazan tauye masu hakki ba na yanke shawara jibi zata
koma gidanta kamar yanda itada mijin nata suka yanke, sannan ta maida dubanta ga
fatima wacce keta faman rirriga sultan shikuma yanamata 'yar rigima tace "kema
fatima sai ki shirya jibin kibi mijinki.

Wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyar mukhatar dan jin Hajiya tabashi izinin
tafiya da fatimarsa,

Fatima kuwa gyara zama tayi lokacin tasamu sultan yayi bacci ta kwantar dashi,
sannan ta kalli Hajiya tace "Hajiya Kafin inkoma ina Neman wata Alfarma, Hajiya ta
maida dubanta gareta tace ina jinki

Wasu irin hawaye masu zafi suka zubo kan kumatunta, tasa hannu ta goge sannan tace
inaso dan Allah kafin inkoma inje 'kauyenmu.....

Hajiya ta numfasa tace "to Alhamdulillahi naji dad'i da ya kasance yau da bakinki
kika furta kinason zuwa, amma bazance komeba akan tafiyar ga mijinki nan kuyi
shawara.

Mukhtar yayi murmushi mai d'auke da damuwa dan ganin fatimarsa na zubar da hawaye,
yace "Ba kome hajiya nima naji dad'i da hakan, amma tunda jibi ne aka sanya ranar
komawar tasu sai ta shirya gobe muje garin nasu.

Cike da jin dad'i laraba ta kalli mijinta tayi mashi wani 'kyawataccen murmushi,
shima murmushin ya mayar mata.

Jidda dake zaune tanajin duk abinda aka tattauna, bata tanka ba tashi tayi kawai
tanufi bedroom wayarta ta d'auko tashiga laluben sunan Usman sannan ta danna mashi
kira yana d'agawa tace "dan Allah abban rahama inaso gobe zamuje garinsu Fatima,
Usman yace "me akeyi ne?
Tace "zamuje mu gaidasu ne.
Yace "ba damuwa, ki kularmin da kanku keda baby rahama Allah kiyaye hanya
Tace "Ameen"
Sannan ta tsinke kiran ta ajiye wayar ta dawo falo.
Yanda tabarsu zaune haka ta tarar dasu gurin datake ta koma ta zauna sannan ta
kalli Fatima tace "sister goben sai muje tare ingano garin naku nima.

Wata irin harara Hajiya tayimata tace "da izinin wah zaki tafi?
Ta kalli Hajiya tayi murmushi tace abban rahama ne yace inje, Hajiya tace "yaushe
kukayi maganar ?
Tace "yanzu fa nakiraahi a waya.
Hajiya tace "to Allah kaimu goben kuma Allah kaiku lafiya ya maidoku lafiya.

Sai lokacin mukhtar yayi magana yace "Amma gaskiya Hajiya abinda jidda keyi bata
kyautawa yanzu dagajin tafiya harta sanar da mijinta zataje da son yawon tsiya
kamar taci 'kafar kare.

Jidda ta turo baki tace "ay dama tuni nake cema sister duk ranar dazata garinsu
tare zamu tafi.

Hajiya najinsu bata tanka masuba, tasan dai duk abin mukhtar tunda jidda ta
'kwallafa rai a tafiyar nan saitaje sai dai idan Allah ne be 'kaddara ba.


_```WASHE GARI```_

misalin 'karfe tara na safe na hango fatima cikin wata shiga ta Alfarma wacce
shigar tafi kama data 'ya'yan sarakuna.

Dan wani tsadadden material ne purple jikinta me Ado da wasu kalan duwatsu masu
haske, sai zanen farin flowar jikinsa, sannan wasu tsadaddun takalmi dake 'kafarta,
material d'in d'inkin riga da zani pieces hakan ba 'karamin 'karamata girma yayiba,
da kyau da kwarjini, wani babban farin mayafi ta yafa shikuma farine anyimashi ado
da flower's purple sai adon duwatsu farare.

Sultan na sa6e a kafad'arta shima anyimashi shiga ta Alfarma kayan jikinshi shima
farine da purple sai fararen kyawawan takalmashi masu tsada.

Jidda ma kwalliya tayi tagani ta fad'a dan itama ba daga bayaba gurin kyau, itakuma
material d'in nata golden colour ne haka takalmi da mayafinta da jakar data rataya,
baby rahama ma shigar golden d'in akayimata.

Sai oga mukhatar shima yayi shiga ta Alfarma dan wata tsadaddiyar wagambari ya
sanya ash colour sai hula itama kalar ruwan toka sai ba'kin takalmi, sai 'kamshin
daddad'an turarensa dake tashi.

Haka suka Shiga mota kirar Camry kalar ruwan toka me duhu, Hajiya na tsaye
tanayimasu addu'ar zuwa lafiya da dawowa lafiya,

Megadi ya bud'e masu get suka d'auki hanya, tafiya suke cikin nutsuwa da kwanciyar
hankali dan mukhatar mutumne me nutsuwa saboda haka kome nashi cikin tsari
yakeyinshi saboda haka tafiyar da bata wuce tsakanin awa ukku da rabi zuwa awa
hud'uba ya sadasu da garin su laraba.




🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:13 PM] www.gidannovels.blogspot.com [18/09 6:58 am] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘


6⃣6⃣6⃣7⃣
6⃣6⃣to6⃣7⃣
6⃣6⃣6⃣7⃣



🖊 Suna isa 'kofar gidan baffa Lawal suka sauka bayan sunyi parking d'in motor
d'insu suduka suka fito daga motar, Fatima ta kalli gabas da yamma kudu da arewa na
garin, batasan lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta ba, tasa
gefen hankchief ta goge *Lallai wani hanin ga Allah baiwa ne*
Fitowarsu daga mota yasa hankalin mutanen dake gurin yadawo garesu, Kowa kallonsu
yake kamar basu ta6a ganin mutaneba.

Dan yan yara wanda basuda hankali sosai har zuwa suke suna ta6a kayan jikinsu, tare
da tatta6a motar dasukazo da ita.

Gidan baffa Lawal suka shiga kai tsaye da sallama matar ta tarbesu tayi masu
shimfid'ar sabuwar tabarma suka zazzauna amma bata gane ko mutum d'aya daga cikinsu
ba.

Baffa Lawal yana gonarsa yanata faman aiki labari ya iskeshi wai anga wata
had'addiyar mota taxo gidanshi tare da wasu mata masu kyau, da wani namiji kuma
anga sunshiga gidanshi.

Aiko yanajin haka yayi saurin tattara yanashi-yanashi yanufi hanyar gida, da sauri
yake tafiya kamar ze tashi sama, yana Isa 'kofar gidanshi yaga mota aiko stayawa
yayi yana kallo cike da mamaki.

Sannan ya 'karasa cikin gidan, laraba na ganinshi gabanta yayi mummunar fad'uwa,
har gabansu yazo ya dur'kusa yana gaishesu, sukuma sai abin yabasu kunya cike da
ladababi suka gaisheshi ya amsa sannan yace "bayin Allah ai ba nan bane gidan
megari yanacan saman layi, amma tunda kunzo nan muje in rakaku aiba damuwa, yana
magana jiki na 'kyarma sai wannan 6a6are yake yana washe ha'kora.

Fatima tace ba gidan me gari zamuba nan mukazo, yanzu baffa Lawal baka ganeniba,
Sai lokacin ya 'kuramata idanu kamar yana neman sanin wani abu tattare da ita, yace
"kai yarinya banganekiba har yanzu, inaji ba nan bane gidan da kuke nema saboda ni
banida 'yan'uwa birni.

Kad'an yarage jidda tayi dariya dan ganin yanda baffa Lawal ya ha'kikance be gane
laraba ba,
Laraba kuwa goge hawayen dake idanunta tayi sannan tace *"baffa 'yarka ce laraba*
😳 mamaki yakamashi kuma tana fad'in itace laraba sai yaganeta, yace Laraba ina kika
shiga shekara da shekaru mun d'auka kin mutu, matar baffa lawal ma tasowa tayi
cikin mamaki tace "Laraba da kina raye Allah me iko,
Baffa Lawal ya kalli su jidda da mukhtar yace wad'annan fa su waye?
Fatima tace wannan shine mutumin daya taimakeni, ta nuna mukhtar kuma yanzu haka
shine mijina, ga kuma d'an da Allah ya azurtamu dashi,
ta mi'kama baffa lawal sultan, sannan ta nuna jidda wannan kuma 'kanwarsace lokaci
d'aya akayi bikinmu itama ga d'iyarta, ta amshi rahama daga hannun jidda tami'kama
matar baffa lawal.


Cike da mamaki baffa Lawal ke kallon fatima yace "laraba haka kika koma, ikon
Allah,
Allah kenan me d'aukaka bawansa ta kowace hanya.
Laraba dai in banda zubar da Hawaye ba abinda takeyi,
Kusan awarsu guda gidan baffa Lawal laraba nabashi labarin irin taimakon da Hajiya
da mukhtar yayimata, da kuma irin yanda suka ri'keta kamar 'yar cikinsu.

Sannan mukhtar yaje but d'in motarshi yasa aka shigo da tsarabar da sukayomasu,
buhun shinkafa katon d'in taliya dana makaroni da sabulun wanka dana wanki da
sauran kayan abinci,
Ahaka aka ri'ka shigowa da kayan baffa lawal kuwa banda godiya ba abinda yakeyi,
saboda tsananin farin ciki besan lokacin da wasu hawaye suka zubo daga idonshiba,
ya kalli laraba yace "Ashe dama akwai ranar dazanga aurenki har inga d'anki Allah
Sarki Allah maki Albarka kinji laraba, Ashe hakanan mutane suke zarginki akan
*maita* ashe Sharrin iska ne Allah dai ya'kara tsareki laraba, tana zubar da hawaye
tace ameen baba.

Bayan sun gama danan ne suka tashi, laraba tace "baffa zamu d'an shiga gari mu
gaisa da jama'a.

Cike da jin dad'i yace to laraba amma kafin kuje ko'ina ianso kuzo muje gidan me
gari ki gaisheshi, mukhtar yace ba damuwa muje, haka suka d'unguma suka nufi gidan
me gari kasancewar ba nisa tsakaninsu da gidan baffa lawal d'in shiyasa suka tafi a
'kafa, duk inda suka gifta kallonsu kawai ake kamar wasu taurari, baffa Lawal kuwa
daya gaisa da mutane a hanya sai ya nuna masu laraba da mijinta da d'anta, haka
shikuma Mukhtar ze fiddo dubu ya mi'kama wanda aka nunama larabar.

Da haka suka isa gidan megari, baffa lawal yakwashe labarin da tafad'amashi duka
yagayamasu sannan ya gwadamasu mukhtar a matsayin mijinta da kuma d'ansu sultan,
sun d'an jima suna gaisawa da jama'a kafin suyi sallama tare da cika me gari da
abin arzi'ki kafin kace me labarin zuwan laraba ya bud'e gari mutane sai zuwa ake
ganinta duk wanda yazo sai mukhtar yabashi 'kud'i wani dubu wani d'ari biyar, yara
kuwa me dari me d'ari biyu ranar garin duk wanda kagani bakinsa washe saboda murna.

Baffa lawal kuwa daga nan gida yakoma yasa aka yanka zabbi akayima su laraba soye
lafiyayye sannan aka dama masu fura wacce taji nono.

Gidan indo 'kawar laraba suka nufa, kan hanyarsu ta zuwane suka gamu da habu yadawo
daga gona yayo uwar ciyawa ya d'ora akai ga kuma hauya rataye akafad'arsa sai uban
gumi yake had'awa, Fatima ta kalleahi tace habu, cike da mamaki ya d'ago ya kalleta
dan jin wata 'yar gayu wacce batayi kama da 'yar 'kauyensuba ta ambaci sunashi,
sauke ciyawar dake kanshi yayi ya'karema fatima kallo yace baiwar Allah daga ina
kuma ina kika sanni?

Fatima tayi murnyshi tace "habu nice laraba baka ganeniba, cike da mamaki habu yace
laraba kece kika koma haka, dama wallahi abinda yasa nabaro Gona kenan inacan
labari ya iskeni wai kindawo wanda ada mun dad'e da d'auka kin mutu.

Laraba tayi murmushi tace "ina raye habu harma nayi aure, ta nuna mashi mukhtar
wannan shine mijina, ga kuma kyautar da Allah yayimamu bayan Aurenmu ta nuna mashi
sultan, sannan ta kalli Mukhtar tace wannan shine habu, mukhtar ya mi'kamashi hannu
suka gaisa sannan ya d'auko 20k sannan sukayi sallama suka wuce, habu ya tsaya yana
juya kud'in kafin daga bisani yanufi gida cike da farin ciki dan kobi takan
ciyawarsa beyiba.
🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:13 PM] www.gidannovels.blogspot.com [18/09 6:33 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘


6⃣8⃣7⃣0⃣
6⃣8⃣to7⃣0⃣
6⃣8⃣7⃣0⃣




🖊 Sun isa gidan indo, da sallama suka shiga gidan sun isketa tana sharar tsakar
gida da yaronta goye, d'agowa tayi daga duken datake takai dubanta ga fatima, kallo
d'aya tayimata tace "laraba kece, cike da mamaki ta rungumeta tana zubar da hawaye,
laraba tace nice indo,
Indo tace Ku shigo, haka suka shiga d'akin indo tayimasu shimfid'ar tabarma suka
zauna, nan suka gaisa, laraba taba indo labarinta kaf bayan barinta 'kauyen, lndo
cike da mamaki tace "Allah kenan shike yanda yaso da bawansa, kinga kuwa yanda kika
koma laraba, wallahi baccin sanin danamaki ba kad'an bane da bazan shedakiba, yanzu
d'inma ba namijin 'ko'kari nayiba, dan yanzu kinfi kama da irin turawan damuke gani
a talabijin, jidda tayi dariya,

Haka sukasha firarsu sannan sukayima indo sallama bayan laraba tayimata 'kyautar
kud'i me yawa sannan tace zata aiko da katon-katon d'in sabulun wanka dana wanki
duk wata 'kawarsu dake garin abata sabulun wanka sin'ki guda saina wanki dozin,
indo tashiga godiya,
Suna gaf da fitowane ilu yayi sallama bayan indo ta amsa tanunamashi laraba, cike
da mamaki yake kallonta, sannan yace "tabbas naji ana labari a gari laraba tazo da
mijinta ance yanata rabon kud'i, indo tace kwarai dan nima ga abinda larabar tabani
ta nunamashi dubu goma sha biyar, ilu ya zare ido dan tunda yake beta6a tinanin
rike kud'i irin hakaba amma yau larabace ke bayar dasu kyauta.

Tare sukayoma su laraba rakiya, a 'kofar gidan indo ta gaisa da Mukhtar shima ilu
sun gaisa, Mukhtar yabashi kyautar dubu goma, wayyo dad'i kashe ilu ai fad'uwa yayi
yana zuba uwar godiya.

Daga nan asalin gidansu laraba suka wuce, sun shiga gidan ba abinda ya canja ga
yanda tabarshi, d'aki tanufa duk kayanta Dana innarta sunanan, wani irin kuka
tafashe dashi, jidda tashiga rarraahinta da 'kyar tasamu tayi shiru, kusan mintuna
sha biyar suna cikin gidan sannan suka fita.

Daga nan gidan baffa Lawal suka koma sun iske soyayyun zabbin da baffa Lawal yasa
aka soyamasu da fura me rai da lafiya, sunsha sosai sannan suka ci naman, bayan sun
kammala ne suka 'kara ta6a fira, saida sukayi sallar la'asar sannan saukayi haramar
tafiya gida, har mota baffa Lawal yarakosu, kafin subar garin said a suka 'kara
biyawa gidan indo suka sauke katon-katon din sabulu na wanka dana wanki wanda za'a
rabama 'kawayenta.


***********************************
Bayan sallar magrib suka iso gida,bayan sunyi horn megadi ya bud'e masu get,
mukhtar yayi parking inda aka tanada dan ajiye motoci, su duka suka shige gida cike
da gajiya tattare dasu, falo suka iske Hajiya ta tarbesu tana masu sannu da zuwa.

.
Washe gari da misalin 'karfe goma na safe Hauwa me 'kunshi tazo tayima jidda da
fatima, kunshi, itace me 'kumshin Ameeno yanzuma itace ta turota tayimasu, kunshin
ya zanu kamar wasu sabbin amare, bayan sallar azahar kuma sukaje gyaran kai, gyara
sosai saukayima jikinsu Hajiya ma ta had'amasu duk wani abu datasan ze taimaka masu
gurin gyara,

Washe gari kafin la'asar sun gama kammala kome nasu, bayan sallar magrib Mukhtar
yazo yatafi da fatimarsa, basu dad'e da tafiyaba Usman yazo ya d'auki jidda,

To Alhamdulillahi kowace takoma d'akin mijinta, suncigaba da rayuwar soyayya da
bawa junansu 'kyakkyawar kulawa.




🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:13 PM] www.gidannovels.blogspot.com [18/09 9:00 pm] . 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘



_```THE END```_


7⃣1⃣8⃣0⃣
7⃣1⃣to8⃣0⃣
7⃣1⃣8⃣0⃣


🖊 Bayan wata biyu, yau yakama week end saboda haka Mukhtar baije ko inaba, dama duk
weekend baya fita zama yakeyi tare da fatimarsa su ri'ka debema juna kewa,

Yauma kamar kullum zaune yake kan kujera 3 seater sultan rungume ajikinsa yana
bacci, fatima ce tafito daga bedroom d'auke da wata lallusar katifa me had'e da net
ta yara ta ajiye sannan ta lalla6a ta kar6esa ta kwantar dashi, mukhtar na fad'in
"kifabi ahankali kada kuma ki tasheshi kinsan dai rigimar dayayi kafin yayi baccin.

Koda ta kwantar dashi beko motsaba dan dama rigimar ta baccin ce yayi,
Koda tasamu ya kwanta tashi tayi tadawo inda Mukhtar yake zaune kan three seater ta
kwanta tayi filo da cinyarsa shikuma yasa hannunsa kanta yana wasa da lallausan
gashinta.

Cikin nutsuwa da tausasa murya tafara magana "Abban sultan dama inaso muyi shawara
dakai, ya tattara nutsuwarshi sannan ya maida duk wani hankalinshi gurinta yace
inajinki, tace "inaso duk kud'in dake gareni zanyi amfani dasu a roshe gidanmu na
'kauye amaidashi ialamiyya wacce za'a ri'ka koyarda addini acikinta, shine nace
bari insanar dakai hakan danayi yayi kuwa?

Mukhtar ya numfasa har cikin ransa yaji dad'in wannan tunani na fatima dan d'an
zuwan dasukayi 'kauyen ya fahimci yanda jahilci ke d'awainiya da mutanen garin.

Yace kada ki damu indan wannan ne ni zan d'auki nauyin kome, kuma zanyi 'ko'kari
insayi wani fili kusa da gidan sai ayi masallaci, kuma zamuyine da niyyar Allah kai
ladar ga iayayenki,

Wani irin farin ciki taji ya ziyarci zuciyarta batasan lokacin da wasu irin hawaye
sukayo ambaliya daga idanuntaba, tace "nagode Abban sultan Allah sakama da gidan
Aljanna.


Haka kuwa akayi cikin satin Mukhtar yaje 'kauyensu laraba yasanarda baffa lawal
shawarar dasuka yanke shida laraba, baffa Lawal yaji dad'i sosai sannan aka sanar
dame gari, wani tsohon gida li'ke da gidansu laraba mukhtar yasiya aka had'e aka
roshesu baki da'aya kasancewar gidajen manyane ansamu wadataccen fili.

Ayki ya kakankama kasancewar nera ke magana, cikin wata d'aya aka kammala ginin
islamiyya da 'katon masallaci me kyau duk 'kauyen babu kamarsa.

Bayan ankammala da sati d'aya akayi walimar bud'e islamiyyar, Wanda laraba da kanta
ta kaddamar da ita, su hajiya da jidda suma sun halarci walimar, laraba kuwa a
ranar tayi kukan *ALHINI*Allah ya d'aukakata, ba rabon innarta taga wannan lokaci.
, mutanen 'kauyen sunyi matu'kar farin ciki,
Taro yatashi lafiya kowa yakoma gida duk garin bakajin maganar Kowa sai ta laraba.

Cikin satin mutanen 'kauyen suka fara karatu a islamiyyar da suke kira _*LARABA
ISLAMIYA*_




```Alhamdulillahi``` 👏🏻

_*Anan nakawo 'karshen wannan littafi nawa me suna ALHINI, ina fatan me karatu ya
nishad'antu kuma ya d'auki darussa dake cikin wannan littafi nawa*_


💞 _*Kyakkyawar gaisuwa ga masoyana a duk inda suke*_ 💞

_*JINJINA GA GROUP'S*_

Nagarta writer's association.
Wisdom Hausa writer's.
Sahaf's novel.
Deejer taheer group.
Matan kwarai group.
Presidential villa group.
Mesha Luv fan's
S.A.Azeez group.

_*MY SpECIAL GROUP'S*_

💞 *Zee Mmn khady fan's & nvl*
👉🏻👩🏻 *Ciwon ya mace group*


_*Ina gaisuwa ga duk masu bin littafina, sai kunjini a sabon buk d'ina me suna*_
👇🏻
💃🏻 *_YARINYAR BABA_* 💃🏻


*Litattafan marubuciyar*

💞 *Siyasa ko soyayya*
🌍 *Duniya juyi*
👍🏻 *Halin girma*
🏤 *Gidan ASALI*
🕊 *Autar Hajiya*
🐇 *Alhini*




Love u all my fan's 💋💃🏻




🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment