Reading ALHINI by Zee Mmn khadye Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun batayi mata magana har tad'an fara sakin jiki tana maida
mata amsa idan tayimata.

Haka jidda ta zaunar da Laraba gaban mirror tafara d'and'asa mata kwalliya, make-up
tayi mata sosai, fuskar nan tafito ta larabawan sak yanda jidda ke fad'a, dan ba
'karamin kyau Laraba tayiba, dan koda ta kalli fuskarta a madubi kasa sheda kanta
tayi, in baccin ma jikinka jikinka ne da Laraba tace ba fuskarta bace a madubin.

Jidda kanta tsayawa tayi tana kallon kyawun da Allah yayima Laraba, kasa yin shuru
tayi tace _"tsarki ya tabbata ga ubanjin daya halitta wannan 'kya'k'kyawar sura_,
juwowa Laraba tayi dan ganin wace kya'k'kyawar sura ce jidda ke fad'i amma bataga
kowaba sai jiddar hakan yasa ta tabbatar da ita jidda take.

Murmushi tayi tace, kai jidda wallahi baki gajiya da zaualaya, yanzu nice kikema
wannan zuzutawar, bayan nasan kin fini kyau nesa ba kusa b....... Jidda tayi saurin
sa hannu ta rufe bakin Laraba tace, bari kada kiyi sa6o, inani ina had'a kaina
dake,

Wadrope d'inta tanufa ta d'auko ma Laraba wasu riga da zani na less cikin kayanta,
tace "amshi ki saka wannan nasan zeyi maki 'kyau.

Laraba ta gyad'a kai tace "jidda da kinbar kayanki na sanya cikin wanda Yaya
Mukhtar ya siyomin, tunda akwai ma wanda ban sanyaba har yanzu,

Jidda ta harareta cikin wasa tace banison haka, ay nice nace ki sanya idan kuma
bazaki sanyaba to ki gayamin, bata jira me Laraba zata fad'aba tashige toilet domin
itama ta watsa ruwa.

Haka laraba ta rin'ka juya less d'in a hannunta tana yaba kyawunsa, dan ko a
mafarki bata ta6a tunanin zata sa irin wannan kayanba, Allah mai yi yanda yaso da
bawanshi, wasu siraran hawaye suka zubo daga idonta dan tunowa datayi da Innarta,
tasa hannu tayi saurin gogewa dan kada jidda tafito taga tana kuka ta isheta da
tambaya, dan tagama karantar halin jidda ahegen surutu gareta, ga kuma tambayar
tsiya kamar tamabai......




๐Ÿ–ŠZee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [27/08 8:02 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


3โƒฃ3โƒฃ3โƒฃ4โƒฃ
3โƒฃ3โƒฃto3โƒฃ4โƒฃ
3โƒฃ3โƒฃ3โƒฃ4โƒฃ


๐Ÿ–ŠBayan sun kammala shirinsu tsaf, Laraba ta sanya less d'in da jidda tabata ta
Sanya, aiko less d'in yayi masifar yimata kyau ya zauna d'as ajikinta, itama jidda
less ta sanya tayi kyau sosai, ta kalli Laraba tace kin san wani abu,? Laraba ta
gyad'a kai Alamar a'a, Jidda tace wannan kwalliyar gurin Yaya kawai yakamata muje
yaga yanda kikayi kyau, 'kilama idan ya ganki baze ganekiba,
Laraba tayi murmushi tace, "sai dai idan wata fuska na canja, to sannan na yarda
baze ganeniba, amma fuskar da yayi kusan sati biyu yana tare da ita yaushe dan yau
d'aya kinyi min kwlliya kice baze ganeniba.

Jidda ta kyal'kyale da dariya tace "lnda ba 'kasa nan ake gardamar kokowa, inaji ai
yayan yana gidan ba inda yaje saboda haka muje araba gardama,

Laraba ta zaro ido tayi dariya tace "kefa dad'ina dake jidda baki gajiya da shirme,
to idan munje muce masa me?

Jidda tayi dariya tace kedai kibar komi a hannuna, yau zaki tabbatar ma kanki
tsananin kyawun da kikayi idan ni baki yarda da maganata ba,
bata jira me laraba zata fad'a ba ta kama hannunta tace "zo muje, laraba ba yanda
zatayi da jidda haka yasa tabita kawai, cike da mamakin shirme irinna jidda..

A falo suka iske Hajiya tana hutawa, suduka suka iso gareta suka rissana sukace
"barka da hutawa, ta kai dubanta garesu, wani irin fad'uwar gaba Hajiya taji dan
ganin wani irin kyau da Laraba tayi mata, cikin zuciyarta tace *Allah sarkin
halitta lallai Allah ya ajiye kyau tattare da Laraba ga nutsuwa da sanin ya kamata*

Cikin fara'a Hajiya ta amsa "yauwa 'yan matana, wannan kwalliya haka, kamar 'ya'yan
saraki, murmushi laraba tayi cike da jin kunya, Jidda kuwa dariya tayi tace "Allah
Hajiya laraba tafi 'ya'yan sarki kyau, murmushi kawai Hajiya tayi masu,

Jidda takama hannun Laraba, suka nufi hanyar fita daga falon, Hajiya tace "ina zaku
haka,? Jidda tace zamu gurin Yaya ne, Hajiya tace to 'yan gidan Yaya, idan kunje
kuce ina nemansa yanzu, kutaho tare, tare suka had'a baki suka amsa da "to.

A lambun gidan suka tarar dashi, yana zaune kan wasu fararen kujeru, gabanshi kuma
wani 'karamin table ne d'auke da laptop d'insa yana danne-danne, gefe kuma fresh
milk ne da cup d'in glass, besan isowarsu ba saboda haka jidda tace ma Laraba
"kawata ki tsaya bayan wannan flower so nike inba Yaya mamaki, laraba tace "wane
irin mamaki zaki bashi kuma? Jidda tayi saurin rufe mata baki tare da jan hannunta
ta turata bayan wata flower, sannan ta isa ga yayanta wanda hankalinshi na kan
computer shi, bema san sun zo gurin ba.

Sallama jidda tayi mashi, d'ago kanshi yayi yakai dubanshi gareta sannan ya amsa
sallamar, murmushi yaga tanayi, saboda haka yasan akwai magana tattare da ita,
hakan yasa ya tambayeta "ya dai 'kanwata? Ta 'kara fad'ad'a murmushin dake fuskarta
tace Hajiya ce ta aikoni gurinka, amma kafin in gaya maka sa'kon inaso in baka
*surprise* yayi murmushi yace mamakin me za'a bani kuma? Tace kaidai ko miye
zakagani amma ka rufe idonka tukun.

Yasaba da shirmen 'kanwarsa saboda haka beyi musuba yasa hannu ya rufe idonsa, yana
jiran yaga yau kuma da wane shirman tazo mashi.

Tana ganin yarufe idonshi tayi saurin zuwa inda ta 6oye Laraba ta kamo hannunta
suka nufi inda Mukhtar yake zaune.

Laraba nagani haka tarin'ka bin jidda kamar ra'kumi da akala, saida sukaje gaban
mukhtar sannan tace "Yaya bude idonka,

Ahankali ya sauke hannuwanshi daga idonshi ya saukesu kan laraba, kallonta yacigaba
dayi, cikin zuciyarshi yace *tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan
'kya'k'kyawar yarinya, lallai Allah ya ajiye kyau a nan* .

Laraba ta kula da yanda mukhtar ya tsareta da ido hakan yasa taji duk ta tsargu,
takama hannun jidda tana janta Alamar tazo su tafi, dariya jidda tayi, wacce ta
dawo da mukhtar daga dogon tinanin dayake, tace "Yaya dama hajiyace tace kazo yanzu
tana nemanka.

Basu jiran amsarshiba suka wuce cikin gida, Jidda na dariyar yanda yayanta ya tsare
Laraba da ido, Ita kuwa Laraba bata ji da'din hakan ba amma bata nuna ma jidda taji
haushi ba ko kadan.




3โƒฃ5โƒฃto3โƒฃ6โƒฃ very 3โƒฃ5โƒฃ3โƒฃ6โƒฃ
3โƒฃ5โƒฃ3โƒฃ6โƒฃ
_*Kuyi ha'kuri da wannan ๐Ÿ‘†๐Ÿป yau ina busy be*_
3โƒฃ5โƒฃ3โƒฃ6โƒฃ
3โƒฃ5โƒฃ3โƒฃ6โƒฃ
๐Ÿ–ŠZee Elkaseem
Mmn Khady๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [28/08 12:50 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


3โƒฃ5โƒฃ3โƒฃ6โƒฃ
3โƒฃ5โƒฃto3โƒฃ6โƒฃ
3โƒฃ5โƒฃ3โƒฃ6โƒฃ



๐Ÿ–Š Laraba na ri'ke da hannun jidda suka shigo falon, suka samu guri suka zauna,
basufi minti biyar da zama ba sai ga yayan su yashigo, cike da ladabi ya zauna kan
kujerar dake facing d'in Laraba ya zuba mata idanunshi masu tsananin kwarjini yana
kallonta, itako ta lura da yanda yake kallonta hakan yasa duk ta daburce.

Hajiyace tayi gyaran murya tare da 'kara gyara zamanta tace "am mukhtar abinda yasa
nace akira mani kai shine kan maganar Laraba,
Wata irin fad'uwar gaba laraba taji dan jin maganar da Hajiya tayi, a zuciyarta
tace _"shikenan nasan lokacin barina gidannan yayi, dan nasan muddin suka San
Matsala ta bazasu kuma zama daniba_.

Hajiyace ta maidota daga dogon tinanin datake, tace "Laraba, laraba ta d'ago
fuskarta ta kalli Hajiya, sannan t sadda kanta 'kasa tana kallon kafet d'in dake
malale tsakiyar falon.

Hajiya tacigaba da magana "kamar yanda kika Sani mun taimakeki kuma Alhmdulillahi
kin samu lafiya kin warware, kuma nasan bazaki rasa sanin inda 'yan,uwanki da
iyayenki sukeba, saboda haka inaso ki sanar damu ke wacece? Kuma miye ya jefaki
cikin mawuyacin halin da shi mukhtar ya tsinceki a ciki?
Saboda munaso mu maidake gurin iyayenki.


Shiru Laraba tayi takasa ko motsi dan jin tambayoyin da hajiyar ta jero mata lokaci
guda, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta, batada niyyar d'ago fuskarta,
saida Hajiya tayi mata magana karo na biyu tace "laraba ke muke sauraro.

Laraba ta d'ago da fuskarta wacce tayi sharkaf da hawaye, ganin haka yasa
hankulansu tashi su duka, cike da damuwa jidda ke rarrashin Laraba tasa hannu tana
goge mata hawaye "kiyi ha'kuri 'kawata ki gayama Hajiya abinda ta tambayeki, ni
nasan hajiyata mai tausayice zata taimaka maki a kan abinda kike Neman taimako,
inshaAllahu.

Haka jidda tayita rarrashinta da kalamai masu taushi, hartayi shuru sannan ta goge
hawayenta tafara basu Labarinta, kamar haka:



_*Sunana Fatima amma amfi kirana da laraba kamar yanda kuka Sani, mahaifiyata yar
Asalin 'kasar camaron ce, sun h'ad'u da babana ne lokacin yana zuwa fatauci can
'kasar.*_

_*Mahaifina kuma d'an nan cikin garin karsina ne a wani 'kauye dake 'karamar
hukumar malumfashi me suna 'kurungafa' Allah yayima mahaifina rasuwa tin ina 'yar
shekara ukku a duniya, kamar yanda naji mahaifiyata tana fad'a,*_

_*Haka yasa muka taso cikin wahala nida mahaifiyata, kasancewar batada kowa a nan
'kasar shikuma babana su biyu ne gurin iyayensu daga shi sai 'kaninsa baffa Lawal,
baffa Lawal mutum ne wanda bashida taisayi ko kad'an hakan yasa baya taimaka mamu
da koda ruwan sha,*_

_*Haka mukacigaba da rayuwa nida mahaifiyata, yau da dad'i gobe babu har nakai
shekara shidda lokacin kuma mahaifiyata tasakani makarantar bokon dake 'kauyenmu,
bayan na kammala aji shidda ne samarin 'kauyen sukayo ca Kowa nason Neman aurena,
lokacin inada shekaru sha ukku a duniya*_

_*An tsaida wani saurayi matsayin wanda baffa lawal ya amince dashi, dan baffa
Lawal Isa da ta'kama ba wanda bayayi mamu amma kuma idan neman taimakone sai ya
nuna be sanmu ba, ana gab da bikinane Allah yayima mahaifiyata rasuwa, Al'amarin
daya sakani cikin mayuwacin hali, dan bayan rasuwarta da sati biyu saurayin dazan
aura ya aiko a maida mashi duk wani abu daya kawo gidanmu yafasa aurena, nan fa
tashin hankalina ya 'karu.*_

_*Baffa Lawal da kanshi yazo har gida yacimani mutunci, yana cewa ai nasan abinda
nayimashi yace yafasa aurena, saboda haka tsinke baze barmin ba cikin kayan da
yaron ya kawo, inaji ina gani ya tattare kome yasa kai yabar gidan, haka na zauna
na had'e kai da gwiwa ina kuka ni 'kad'ai cikin gida babu me rarrashina, dan dama
tunda mahaifiyata ta mutu yazamana ni d'aya ke kwana gidan, tun ina jin tsoro har
zuciyata ta saba*_

*_Ban fuskanci babbar matsalaba sai da na wayi gari banida abinda zanci, yunwa
tayimani mugun kamu wanda har wani matsanancin ciwon ciki ya kamani, hakan yasa na
lalla6a naje gidan baffa Lawal ko ze taimakamin amma sai yayimin korar kare,
lokacinne na 'kudiri niyyar kashe kaina ta hanyar fad'awa wani 'katon rami dake
nesa kad'an da 'kauyenmu, dan lokacin na 'kwammace mutuwa da halin da nike ciki, ga
ba'kin cikin rayuwa ga ALHININ rabo da iyayena....._*

Wannna shine labarina, laraba ta fad'a tana goge hawaye,

Jidda ma kuka take saboda tusayin larabar, "Lallai laraba kinsha gwagwarmaya, Allah
Sarki, ta fad'a tana sharar kwalla.




3โƒฃ7โƒฃto3โƒฃ8โƒฃ very 3โƒฃ7โƒฃ3โƒฃ8โƒฃ
3โƒฃ7โƒฃ3โƒฃ8โƒฃ
3โƒฃ7โƒฃ3โƒฃ8โƒฃ
3โƒฃ7โƒฃ3โƒฃ8โƒฃ




๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [28/08 5:07 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


3โƒฃ7โƒฃ3โƒฃ8โƒฃ
3โƒฃ7โƒฃto3โƒฃ8โƒฃ
3โƒฃ7โƒฃ3โƒฃ8โƒฃ


๐Ÿ–Š Haka jidda takama hannun Laraba suka wuce d'aki, tashiga rarrashinta "kiyi
ha'kuri Laraba ki d'auki rayuwar da kikayi a baya amtsayin jarabawa, kuma kiri'ka
yima iyayenki Addu'a Allah kai haske kabarinsu, kuma ina me tabbatar maki bazamu
gujekiba, zaki zauna damu har 'karshen rayuwarki inshaAllah, Laraba tasa hannu ta
goge hawayen dasuka zubo a kumatunta tace "ko yanzu nabar gidannan nasan kunyi min
hallacin da 'kanin mahaifina yakasa yimin wanda shi kad'ai yarage a dangina, nagode
Allah saka maku da Alkhairi.

Jidda tace ba kome laraba ki d'aukeni a matsayin 'yar'uwarki Hajiya kuma a matsayin
mahaifiyarki Yaya mukhtar kuma a matsayin yayanki, inshaAllah bazaki 'kara
fuskantar Matsala a rayuwarki ba.

Haka jidda tayita rarrashin Laraba har zuciyarta tayi sanyi, ta goge hawayenta,
Nan jidda tacigaba da bata labarai kala-kala tun tana jinta kawai harta biye mata
ta saki jiki tana dariya kamar ba itaba.

A falo kuwa Hajiya ta kalli mukhtar jiki a sanyaye tace "kaji abinda yarinyar nan
tafad'a ya ka gani, Mukhtar Wanda shima duk illahirin jikinsa yayi sanyi dan jin
labarin Laraba, yace Hajiya kawai abinda ya kamata shine mu ri'keta ta zauna
gurinmu muga abinda Allah zeyi.

Hajiya tace hakane, zatacigaba da zama gurinmu kuma zaka samo mata form a
islamiyyar su jidda suri'ka zuwa tare.

Sannan idan su jidda zasuyi Exam ayi 'ko'kari asakata ciki, tafara daga s.s.1 tunda
kaga yanzu takai kimanin shekaru sha hud'u baze yiyu asata j.s one ba tayi girma,
sai asamo Wanda zeri'ka mata lesson a gida kafin sufara karatun.

Cike da jin dad'i mukhtar ya amsa ma Hajiya, zuciyarshi cike da farin ciki, dan ko
kad'an dama bayaso ayi maganar maida Laraba garinsu.

Jidda Kuwa dataji hukuncin da Hajiya ta yanke na zaman Laraba gidansu murna
tashigayi hada tsalle.

Laraba kuwa cikin ranta tana tsoron ranar da zasu gane gaskiyar labarinta data 6oye
masu, dan tasan muddin suka gane to zasuyimata korar kare.


_```BAYAN SHEKARA UKKU```_

Wasu kyawawan yan mata na hango su biyu tsaye bakin titi kusa da school d'insu
sanye suke cikin uniform d'insu rigar chek pink, sai wando brown, sai 'yar karamar
abayar da bata ko rufe hannuwansu ba, kafafunsu sanye cikin brown sandals sai farar
safa computer, sunyi kyau sosai kamar 'ya'yan larabawa.

Wata ba'kar mota 'kirar 4matic tayi parking gabansu, sannan matashin dake cikin
motar ya sauke glass d'in motar yakai dubansa ga 'yan matan, da gudu 'yan matan
wad'anda basu wuce shekara sha bakwai ba suka nufi motar suka shige, kowace baki
ya'ki rufewa saboda farin ciki.
Sun fara tafiya a motar jidda dake gaba, kusa da yayan nata ta juyo ta kalli
Laraba ta kashe mata ido, murmushi kawai Laraba tayi mata dan tasan jidda da
surutun tsiya, yanzu haka akwai abida takeson fad'a...

Bata gama tunanin datakeba, ta tsinkayi muryar jidda tana cewa "Yaya bakayi mana
congratution ba yau munyi graduated, ya juyo ya kalleta yace tun nan a mota zanmiki
congrat d'in, to ke bari inyimaki amma Fatimana sai munje gida zan mata, yafad'a
yana kallon Laraba yakashe mata ido, itako wata irin kunya ke kamata idan yakirata
fatimarsa, jidda kuwa cewa tayi eh na yarda ayimin anan, ya juyo ya kalleta yace
"lna tayaki murna 'kanwata, yanzu saura musha biki keda Usman, cike da jin kunya
jidda tarufe idonta, daga lokacin bata 'kara magana ba, dan wata irin kunyace
takamata, Usman shine saurayin datake masifar so kuma shine Wanda zata aura, dan
maganar harta kai ga iyaye, dama makaranta kawai ake jira ta kammala.

Laraba kuwa na kula da ita, saboda haka tari'ka kallonta ta madubin motar tana mata
dariya ๐Ÿ˜œ itakuma girgiza kai tayi, Alamar zasu had'e........


Haka suka Isa gida cike da farin ciki, bakin get sukayi horn megadi yabud'e masu
get suka shige, sukayi parking, da gudu suka nufi cikin gida suna kiran Hajiya,

Hajiya na bedroom tajiyo haniyarsu da sauri tafito tana masu sannu da zuwa, nan
suka zauna anata labarin makaranta, Hajiya tayimasu congrat, sukaji dad'i har cikin
ransu.

Sai lokacin mukhtar yashigo fuskarshi d'auke da fara'a yasamu guri ya zauna,
lokacin kuma Hajiya takoma d'akinta dan cigaba da aikin datake,

Tasowa yayi yazo gaban laraba, ya du'ko inda take zaune har numfashinsu na gauraya
dana juna, hannu yasa aljihu yaciro wata had'ad'iyar waya mai kyan gaske, kirar
tecno Hยณ yami'ka mata, tare da cewa *"Congratulation on your graduation Fatima na*
cike da jin kunya ta amsa tace *Thank you very much, My Brother*.

Duk abinnan jidda na zaune tana kallonsu, a zuciyarta tagama yarda yayanta son
laraba yakeyi.

juyawa yayi yanufi hanyar barin falon, da sauri jidda dake zaune tana jiran ami'ko
mata tata wayar tayi saurin kamo hannunshi, cikin shagwa6a tace "Yaya nifa, cike da
zaulaya yace "kikace iyimaki murna tun a mota, kuma nayi maki.

Cikin shagwa6a tace ay ba cewa nayi kada kabani phone ba, dariya yayi sannan ya
fiddo wayar itama ya mi'ka mata iri d'aya data Laraba.

Da gudu tanufi inda laraba take tana tsalle,......




3โƒฃ9โƒฃto4โƒฃ0โƒฃ Very 3โƒฃ9โƒฃ4โƒฃ0โƒฃ
3โƒฃ9โƒฃ4โƒฃ0โƒฃ




๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [29/08 7:32 am] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


3โƒฃ9โƒฃ4โƒฃ0โƒฃ
3โƒฃ9โƒฃto4โƒฃ0โƒฃ
3โƒฃ9โƒฃ4โƒฃ0โƒฃ


๐Ÿ–Šmaganar Auren jidda da Usman d'inta ta kankama, dan har ansa ranar biki wata
hud'u, jidda kuwa dad'i har cikin zuciyarta, amma takaicinta d'aya yanda Laraba
bata kula maza ko kad'an, dan akwai wani abokin Usman daya nuna yana sonta kamar
zeyi zauci amma ta bad'e ido toka ta nuna ita bata soyayya, tome hakan ke nufi?
Amma ko badad'e ay dole tayi aure tunda tsarin gidansu ne mace bata wucewa gaba da
karatu daga secondry, barantana tace karatun tasa gaba.

_```Bayan kwana biyu```_

Yaune Hajiya ta tara 'ya'yan nata tana masu magana, kamar haka "Alhmdlh ke jidda
banda ke cikin wannan fad'an da zanyi, ta maida kallonta ga Laraba tace "Fatima
saboda me bakison ki fidda miji kiyi aure? Bata jira abinda laraba zata fad'aba
tacigaba da magana "ita mace duk yanda take jin dad'i gidan iyayenta to gidan
mijinta yafishi, kome duk Kyan mace da dukiyarta ko mulkinta darajarta shine d'akin
mijinta.

Haka Hajiya taketayi masu nasiha, suduka sunyi kasa'ke suna sauraronta, shikuwa
mukhtar tsoro yake acikin zuciyarshi kada Fatimarsa tafad'i wani namiji tace shine
wanda ta tsaida a matsayin miji, bayan shekarun daya d'auka yana fama da dakon
soyaryyarta a zuciyarsa.

Hajiya tayi gyaran murya tacigaba da cewa "kodayake ga yayanku nan shima tun yaushe
nake fama dashi akan ya fiddo mata yayi aure amma yayi biris da maganar, amma 'kila
so yake insamo wata koda 'yar Almajirace in had'ashi da ita, jidda ta kyalkyale da
dariya, tace "kai Hajiya Yaya yafi 'karfin Almajira, itama hajiyar dariya take tace
to kada ya fiddo matar kusha mamaki daga ke har shi,

Sai lokacin mukhatar ya d'ago da idonshi wanda suka kad'a zuwa ja, ya kalli
hajiyarshi cike da jin kunya yace "Hajiya ayni na dad'e da samun matar da zan aura,
sai kuma ya sadda kanshi 'kasa yana shafa kanshi da Alamar kunya tattare dashi,
Hajiya tace "uhum ina saurarenka wace mai sa'ar ce wannan, shiru yayi yakasa furta
kome.

Jidda tace Allah Hajiya nasan ko wacece, Hajiya ta harareta "ke banison shirme ina
sauraronka, "dama...hm..dama ba wata bace sai Fatima, cike da jin kunya yake
maganar.

Jidda tace dama nasan wlh Hajiya Yaya ya dad'e yana son Laraba, Hajiya tace "to
uwar surutu wai waya sanyo bakinki cikin maganar nan, tayi saurin sa hannu tarufe
bakinta ๐Ÿ™Š.

Cike da farin ciki fuskarta kuma d'auke da fara'a tace kai amma naji dad'in wannan
abu, ta kalli laraba wacce tunda mukhatar ya furta Kalmar so gareta duk illahirin
jikinta kyarma yake.

Haka Hajiya tagama dasu ta sallamesu, tawuce d'akinta, Shima Mukhtar d'akinsa ya
wuce zuciyarshi cike da farin ciki.
6angaren laraba kuwa tun lokacin da Mukhtar ya furta Kalmar so gareta tayi sukuku,
kamar marar lafiya, jidda na kula da halin datake ciki takan tambayeta ko lafiya,
sai ta 'ka'karo murmushin 'karfin hali tace mata ba kome, itakuma jidda sai
tacigaba da tsokanarta tana cewa amaryar yayanmu, Laraba sai dai tayimata murmushi
amma ita kad'ai tasan abinda takeji a zuciyarta, dama ranar data dad'e tana gudun
zuwanta kenan, dan dama ta dad'e da lura da take-taken mukhtar na sonta, amma ba
kome dole ta samarma kanta mafita, bawai son mukhtar ne batayiba, dan ko itace ta
d'aurema butulci gindi a duniya bekamata tace bata son mukhtar ba, matsalarta d'aya
shine abinda yabarota daga 'kauyensu, mutum nawa suka mutu dalilin aurenta, tabbas
tasan idan mukhtar yadage akan aurenta shima 'karshen rayuwarsa yazo, wasu irin
hawaye masu rad'd'i suka zubo daga idonta tasa hannu ta goge, duk abinnan bata
yarda ta nuna damuwarta fili dan kada mutanen gidan su gane.

_```Bayan wata d'aya```_

Soyayya me 'karfi ta 'kulle tsakanin mukhatar da Laraba, wacce a yanzu ta canja
suna takoma sunanta na Asali wato *Fatima*

Ranar ne kuma Hajiya takira Laraba tace mata, yakamata ki bada address d'in baffa
Lawal saboda za'a tura magabatan mukhatar suje neman aure.

Laraba cike da damuwa da far gaba tace "Hajiya kibari da safe zan bada yanzu kaina
yana min ciwo, Hajiya ta tausaya mata tace "eyyah Allah sauwa'ke to kisha magani
kafin ki kwanta kinji, tace "to, sannan tanufi d'akinsu zuciyarta cike da tunani
kala-kala, *gaskiya bekamata ta sakama mutanen nan da sharri ba, yanda suka
d'auketa amatsayin 'ya suka ri'keta suka nema mata gata wanda ko a mafarki batayi
tunanin samun irinsaba, gaskiya dole tasamoma kanta mafita*

Haka ta isa d'akin ta iske jidda tana chat da Usman d'inta tana dariya ita kad'ai
kamar mahaukaciya, laraba ta kalleta batayimata magana ba ta haye gadon tayi
kwanciyarta.

Jidda ta kaimata duka, "ke yau baki chat da yayana, nasan yana online yana jiran
zuwanki, Fatima tayi wani d'an guntun tsaki ta 'kara gyara kwanciyarta tace "kaina
ne yakemin ciwo nasha magani bacci zanyi, cike da tausayawa jidda ta dafa kanta
tace "Allah sauwa'ke, itama sai taji chat d'in yafita ranta haka sukayi sallama da
Usman yanata magiyar kada ta tafi ta barshi, tace "kayi ha'kuri sister d'inace ba
lafiya bazanji dad'in yin chat d'ina, yace "Allah sauwake sukayi sallama.

Itama jidda kwanciya tayi bayan tayi addu'a tashafe jikinta, sannan tayima Fatima
addu'ar dan ta lura da lokacin data kwanta batayi addu'ar ba.

Duk abinnan Laraba na jinta dan ba bacci tayiba, tunanine kala-kala cikin
zuciyarta.

Jidda bata dad'e da kwanciyaba bacci yayi awon gaba da ita, haka laraba tayita juyi
kan gado bacci ya gagari idanunta, wayarta ta d'auko ta duba 'karfe 1:58 am na
dare, a zuciyarta tace yanzu ne yakamata in samoma kaina mafita, dan muddin nasan
idan nabari mutanen nan sukaje 'kauyenmu sunan dana 6oye masu nawa na *mayya* zai
bayyana.

Saboda haka ahnakali ta tashi cikin sand'a ta d'auko site bag d'inta ta bud'e
wadrope ta d'auki kaya kala 2 sannan ta cire rigar baccin jikinta ta Sanya wata
doguwar riga ta atamfa sannan tasa wando legis daga ciki, sannan ta Sanya wata 'yar
'karamar hijab, ta d'au takalminta a hannu, ta lalla6a tayi sa'ar barin gidan
batare da Kowa ya gantaba kokuma yaji motsinta.
Bakin titi ta tsaya ta 'karema unguwar kallo bakajin kome sai kukan maguna da
karnuka, da tsintsaye, haka ta yanki hanya tacigaba ta tafiya, zuciyarta cike da
tsoro.......




4โƒฃ1โƒฃto4โƒฃ2โƒฃ Very 4โƒฃ1โƒฃ4โƒฃ2โƒฃ
4โƒฃ1โƒฃ4โƒฃ2โƒฃ




๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [31/08 8:21 am] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


4โƒฃ1โƒฃ4โƒฃ2โƒฃ
4โƒฃ1โƒฃto4โƒฃ2โƒฃ
4โƒฃ1โƒฃ4โƒฃ2โƒฃ



๐Ÿ–Š Tafiya take batare da tasan inda zata dosa ba, ta d'anyi nisa kad'an da gidan
zuciyarta cike da tsoro, sai tajiyo Alamar tafiyar mutane bayanta suna tafiya suna
magan-ganu wanda bata iya jiyo abinda suke cewa, saboda suna d'an nesa kad'an da
ita, hakan yasa zuciyarta kara tsorata, tayi maza ta 'kara sauri cikin sa'a tayi
karo da wani gida da aka fara ginawa amma ba'a karasaba, aiko tayi saurin shigewa
ciki dan ta 6uya, da sauri ta shige wani guri a cikin gidan wanda da Alama d'aki ne
amma ba'a karasaba dan ko rufi ba'ayiba, gidan dai kamar kango ne dan duk illahirin
gidan ba 'kofar da aka sanyama 'kyaure, sai uwayen karikitai da Shara a cikinsa.

Tana cikin kangon gidan data 6uya 'kirjinta na dukan taraยฒ, sai ji tayi wad'annan
mutanen data 6uya dominsu sun iso gurin, jitayi sun tsaya bakin 'kofar kangon gidan
data 6uya suna magana, muryar guda taji yace "gaskiya nifa na gaji da abinda
mutuminnan yake samu muna aykatawa, kawai hakanan yasa muri'ka kawo mashi 'ya'yan
mutane yana 6ata Masu rayuwa.

Gudan yayi dariya, cikin wata muguwar murya marar dad'in sauraro yace "nikam bazan
ta6a barin wannan sana'ar danikeba, dan in baccin ita ina zamu ri'ka samun 'kudin
da muma zamuji dad'in rayuwarmu, haba baba, kazo muje kawai mucigaba da neman
abinda ya fiddo mu, gudan yace to yanzu ina zamu nufa? Kasan dai yanzu duk wata
d'iya mace indai tanada mutunci to tana gidan iyayenta, gudan ya gagga6e da wata
irin dariya yace "yo dama duk wacce muka kama yanzu ay bata mutunci bace, dama mu
irin 'yan iskan nan muke nema masu yawon dare, idan sunsha sun bugu mukuma sai muyi
awon gaba dasu, suduka sukasa dariya marar dad'in sauraoro.

Duk abinda suke Fatima na La6e cikin wannan gidan tana jinsu in banda kyarma ba
abinda take, lokaci guda ta had'a wani uban gumi, dan tariga ta fahimci inda
zancensu ya dosa,
A gida kuwa da misalin 'karfe ukku da minti sha shidda na dare jidda ta farka zata
shiga toilet sai taga bataga Fatima ba, hakan yasa tayi tunanain ko tana toilet
d'in ta dad'e tana jiran fitowarta amma kusan minti goma shiru saboda haka saukowa
tayi daga kan gadon da niyyar ta duba toilet d'in.

Abinda idanunta yafara karo dashi shine ya d'aga mata hankali, kayan baccin Fatima
yadde a 'kasa, bata tsaya d'auka ba ta tura 'kofar kewayen, nan ma ba Laraba, cikin
tashin hankali tayo baya sai tayi karo da wadrop bud'e tayi sauri dubawa cikin
wadrop d'in saitaga kaya yamutse da Alama an d'auki wani abu aciki, nan tashiga
matsanancin tashin hankali lokacin data ta6a kofar fita daga d'akin tajita bud'e.

Cikin tsananin tashin hankali tanufi d'akin hajiyarta ta sanar da'ita abinda ke
faruwa,

Mukhtar ma an tasoshi an fad'a mashi halin da ake ciki, cikin tashin hankali
yafito, haka suka shiga duba ko'ina na gidan Amma ba Alamar Fatima, an tambayi me
gadi yace shikam bega fitar Kowa a gidan ba.

Lokacin idan hankalinsu yayi dubu tashe yake, mukhtar d'akinsa yanufa ya d'auko
key d'in motarsa yacema Hajiya "Zan fita in duba ko Allah zesa in ganta.

Lokacin itakuma jidda ta d'auko wayarta dan ta lura duk inda Fatima take ta tafi da
waya dan ta duba bata gantaba, lokacin ta lalubo sunan sister Fatima, sunan data
sanyama Laraba kenan ta danna mata kira.


Dadai lokacin da wad'annan mutanen guda biyu suka tashi daga 'kofar kangon gidan da
Fatima ke la6e a ciki guda na cewa "baba yakamata fa mu'kara gaba ko mun samu, ya
duba agogon hannunshi yace 'karfe ukku da rabi kada gari ya waye mamu anan, kasan
oga mayen mata ne duk ranar dabamu samo mashiba bamuda jin dad'i, d'ayan wanda tun
farko yace yagaji da sana'ar yace "waallahi ni abin na oga yana bani mamaki, ga yan
mata nan karuwai masu Neman mazan da kansu meyasa baya ri'ka d'aukosu yabiya
bukatarsa yabiyasu 'kud'insu hankalinshi kwance suma hankalinsu kwance, gudan yace
"kai dai banzane baka

Please Login or Register in order to submit comment