Reading NAUSHIN WUTA by AMEERA ADAM Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi.

Washegari

Tun da Jafar ya yi sallar Asuba bai koma ba, gari yana yin haske ya shiga cikin
kitchen ya ɗauke tukunyar cilinder gas ya fice da ita. Da yake Maman Nana ba ta
tashi da wuri ba, saboda a daren bacci bai ɗauke ta da wuri ba ko kaɗan ba ta san
wainar da ake toyawa ba. Sai da ta ji alamun buɗe gate ta tashi ta fito, a
tsammaninta Jafar fita ya yi kasuwa.
Banɗaki ta shiga bayan ta fito ta shiga kitchen za ta shirya wa su Nana abin
breakfast da na makatanta. Amma sai ta ga wayam babu clinder, ba ta kawo komai a
kanta ba; sai ta yi tsammanin ko ƙaro musu gas zai yi saboda idan ya ga ya kusa
ƙarewa yana ɗauka ya ƙaro mata.
Tana daga ƙofar kitchen ta hango shi yana kokawar shigowa da ƙaton buhun gawayi,
sai da ya ƙarasa ya jingine shi sannan ya sake fita gate ya sauke mirgino buhu na
biyu. Maman Nana tana tsaye ya gama dire buhunnan gawayin har guda biyar, sannan ya
ɗauko kurfoti ya dire a gabanta. Fuska a haɗe ya ce, "Daga yau ga abin da za ki
dinga girki da shi, gas ya sake tsada ba zan iya sayensa ba. Cilnder ma na sayar wa
mai shagon da nake sako mana gas, sai a ci gaba da malejin rayuwa tun da komai
tsada yake sake yi." Jafar yana gama faɗar haka ya shige ɗaki.

Kabir kwance ya yi a kan gado, yana jin haushin kansa a kan abin da ya aikata.
Fushin Fauziya ya fi komai ɗaga masa hankali, don Fauziya mace ce mai haƙuri da
sauƙin kai. Amma idan ta yi fushi ba ta iya zuciya ba, juye-juye ya fara yi yana
hangen ta da take kwance idonta biyu tana hawaye. A hankali ya tashi zaune ya
tsugunna a gefenta murya a sanyaye ya ce.

"Fauziya! Don Allah ki tashi mu yi magana, ba na son ki saka kanki a cikin wani
hali saboda yanayin da kike ciki."

Ɗagowa ta yi ta dube shi, tana jin sautin muryar martanin batsar da yake mayarwa
da Hafse a cikin kunnuwanta. Zuciyarta ta shiga zafi, wani abu ya tokare ƙirjinta.
A hankali ta fara jin mararta tana tsira mata, ta cije bakinsa tana girgiza kai.

"Don Allah ki yafe mini..."

"Idan ka sake yi mini magana zan fice daga gidan nan na ba ka wuri."
Ta katse shi da wani irin sauti, kamar sabon munafiki haka Kabir ya ja jiki yana
sunne kai ƙasa ya koma kan gadon ya zauna.
A cikin wannan daren daga shi har Fauziya bacci rabi da rabi suka yi, sai bayan
Asuba ta samu bacci mai hauyi ya yi awon gaba da ita.
Tun da Kabir ya tashi bai koma ba, saboda ya san ya yi wa Fauziya laifi a hankali
ya dinga aiki don kada ya tashe ta. Shi ya dafa wa yara abinci, ya shirya su suka
tafi makaranta. Sannan ya shiga ɗakin ya share mata, kwanukan wanke-wanken kuma ya
ajiye a bakin rariya zai wanke mata. Lawisa tana sanye da hijabi tana girki a bakin
ƙofarta ta hango shi ya tsugunna zai yi wanke-wanke, miƙewa ta yi ta ƙarasa wurin
ta ce, "Baban Na'ima ka bari zan wanke mata, ko jikin Maman Na'iman ne." Kabiru ya
ɗan sosa kai ya ce, "Eh ta tashi ba ta jin daɗi ne, shi ne ta ɗan kwanta zan rage
mata aikin."

"Subhanallah! Allah Ya raba lafiya, bari na ƙarasa girki sai na haɗa na wanke da
nawa."
Godiya ya yi mata sannan ya koma ɗakin, tun da ya shiga yana son ya tambaye ta abin
da za zai girka musu da rana yana shakkar tashinta da ɓacin ranta. Tukunyarta ya
buɗe ya ga akwai sauran miya, sai kawai ya ɗora taliya ya dafa musu. Kafin Fauziya
ta tashi tuni Kabir ya gama komai, hatta turaren wutar da take sakawa ya saka musu.
Ya shiga ɗakin ya same ta a bakin gado a zaune ta tashi, fuskarta ta sauya sosai
daga jiya zuwa yau duk ta rame.

"Ga ruwan wanka zan sirka miki sai ki yi wanka."

Kabir ya furta yana satar kallonta, ko kallonsa ba ta yi ba har ya sake maimaita
mata.
"Don Allah ka matsa daga gabana Kabir." Da sauri ya fice daga ɗakin, ya shiga
banɗaki ya yi wanka. A inda ya bar ta a nan ya same ta, bayan ya shirya ya tambaye
ta abin da take buƙata a wannan karon ma banza ta yi da shi. Don haka ya zaro dubu
ɗaya ya ajiye mata, bayan ya fita ta bi bayansa da kallon tsana.

Miƙewa ta yi ta ɗauki wata 'yar babbar leda ta ɗebo kaya a drowerta, sai da ta yi
wanka ta ɗauki kular abincin su ta zuba, sannan ta saka wata doguwar rigar atamfa
ko man kirki ba ta shafa ba. Bakin ƙofar Lawisa ta ƙarasa ta ce.

"Lawisa ga abincin yaran nan da kayan makarantarsu, idan sun dawo don Allah su
wuce makaranta."

Lawisa ta karɓa tana faɗin, "Ai na leƙa kina bacci, wai ko abar ce ta zo."
Fauziya ta girgiza mata kai ta ce, "Ga wannan mukullin kuma koda babansu zai dawo."

Da mamaki Lawisa ta bi Fauziya da kallo, don ba ta taɓa tafiya unguwa ta ajiye
mukulli ta ce a ba wa Kabir ba, amma sai ta haɗiye abin a ranta don tun daren jiya
ta fahimci akwai abin da yake damunta saɓanin maganar da ta faɗa mata.
Sallama Fauziya ta yi mata ta fice daga gidan, tana fatan wannan fitar da ta yi
daga cikinbaƙin gida ya zame mata ita ce fita ta ƙarshe da za ta yi masa.


+2347062062624

[14/02, 17:27] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da
ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da
mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA TAKWAS

UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳

Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda
habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta
ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai
musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan
kyauta tana kara soyayya

Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya
qualitatives via +234 816 916 8731

***
Kabir tun da ya fita daga gidan ba a nutsuwarsa yake ba, kwata-kwata ya rasa me
yake yi masa daɗi. Zuciyarsa ce ta shiga wassafa masa laifin abin da ya aikata, har
yake jin kamar ya rabu da su Hafsee ya rungumi matarsa ita kaɗai. Ɗaya tsagin na
zuciyarsa kuma, ya shiga kwaɗaita masa haɗe da harsaso masa surorin jikin Surayya
da Hafsat. Nan take ya ji sam ba zai iya rabuwa da su ba, koda a ce bai auri su
duka ba. To tabbas dole zai auri ɗaya, domin zuciyarsa ta jima tana kaɗayin
dandalar ni'imar da Allah ya yassare musu. Rashin walwala da sukunun da yake ciki,
ya sa mutanen cikin shagon suka lura da shi. Har suke tambaayarsa ko ba shi da
lafiya, saboda Kabir mutum ne mai faram-faram yana da sakin fuska sosai. Ganin ya
gagara gudanar da aikin da yake yi, yamma liƙs ya yi wa Ogansu sallama ya ce zai
koma gida saboda ba ya jin daɗin jikinsa. Lokacin da ya tunkaro gida, kamar ya kira
Fauziya a waya ya tambaye ta ko akwai abin da take buƙata ya sayo mata. Sai kawaa
ya haƙura, saboda ko sunanta ya tuna gabansa faɗuwa yake yi.

Lokacin da ya ƙarasa gida kusan shida saura, su Na'ima suna jin sallamarsa suka
fito daga ɗakin Lawisa da sauri suka rungume shi. Mukulli ta ba wa Fatima ta ce ta
kai masa. Kabir turus ya yi a bakin ƙofar ganinta rufe da kwaɗo, kamar yaran sun
san tambayar da take cikin zuciyarsa Hidaya ta ce.

"Mami ta je unguwa!"

Gabansa ne ya faɗi, ƙafafuwansa har rawa suke yi saboda tashin hankali. Da ƙyar ya
iya saita nutsuwarsa hannunsa yana karkarwa ya buɗe ƙofar ɗakin suka shiga, yana
shiga ɗakin ya fara kiran layin Fauziya sai dai tashin farko ya ji an ce masa a
kashe take. Kamar zai yi hauka, haka ya fara zagaye ɗakin da sauri-sauri. Wani
tunani ya faɗo masa cikin sauri ya sake riƙo hannun yaran, ya kai su ƙofar ɗakin
Lawisa ya ce su shiga zai je ya dawo. Rufe ɗakin ya yi ya sake ba wa Lawisa
mukullin sannan ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama.

"Ina Fauziya ta tafi? Ko dai ta tafi gidansu ne? Fauziya ba ta taɓa yin yaji ba,
ko ƙarata ta kai gidansu? Yanzu haka za su dinga yi mini kallon mutumin banza? Kai
Fauziya ba za ta yi mini haka ba, ina da tabbacin ba za ta bankaɗa labulen sirrina
ba."

Haka Kabir ya dinga tafiya yana surutai kamar sabon taɓin hankali, domin kafin ya
ƙarasa bakin titi gani ya yi hanyar ta ƙara yi masa nisa. A gurguje ya tari
adaidaita sahu ya nufi uguwarsu Fauziya, yana zuwa ya samu mahaifinta a ƙofar gida
yana sallar magriba. A hargitse ya zube a gabansa yana faɗin, "Baba barka da
yamma."

"Baba ya yi masa kallon tsaf ganin ƙafafuwansa duk sun yi butu-butu, da mamaki ya
ce. "Barka dai Kabiru, kai ne da doshin magriba haka? Ya Fauziya da yaran?"

Turus! Kabir ya yi ya ɗan sosa kansa, gabansa ya cigaba da faɗuwa saboda fargaba.
Amma gudun kada Baba ya gano shi sai ya ce, "Duk lafiyarsu ƙalau, dama wucewa zan
yi na ce bari na biyo mu gaisa."

Baba ya saki murmushi ya ce, "To Ma Shaa Allahu, ai jiya mun ga abin alheri. Allah
dai ya raya zuri'a." Jiki a sanyaye Kabir ya amsa sannan ya cewa Baba zai wuce.
Haka Kabir ya cigaba da tafiya yana kiran layin Fauziya har lokacin a kashe,
gidan ƙawarta Jamila ya je suka gaisa. Ita ma ta wurga masa tambayar Fauziya, don
ta yi mamakin ganinsa a ƙofar gidanta. Saboda rabon shi da gidanta, tun tana amarya
da suka zo mata shi da Fauziya kusan shekara biyar kenan.

"Kabir ko ƙawar tawa ce ta haihu?"

Jamila ta jefe masa tambaya tana gyara mayafinta.
"Amm dama na ɗauka ta ƙaraso nan ne, da yake ta fita ɗazu ta ce mini idan ba ta
yi yamma ba za ta biyo ta nan. To mukullin yana hannunta, kuma akwai ɗinki wata Mai
jego da aka zo karɓa daga nesa, ga ɗakin ta rufe shi. Na kuma kira wayarta a
kashe." Ita ma Kabir ya zabga mata ƙarya, Jamila ta ce.

"Ai kuwa ba ta biyo ba, ina jin ko kun yi saɓani a hanya tun da magriba ta yi."
Amsa mata Kabir ya yi suka yi sallama.

Tunanin duniya ya shiga yi a kan inda zai je ya lalubo Fauziya, saboda tun da
suke duk faɗan da za su yi ba ta taɓa yi masa irin haka ba. Wayarsa ce ya ji ta
fara ƙara, da sauri ya ciro ta a tsammaninsa ita ce sai ya ci karo da lambar
Surayya. Guntun tsaki ya saki ya ƙi ɗauka, amma sai ta cigaba da kira. A ƙufule
Kabir ya ɗauka yana faɗin, "Wai Surayya me ya sa kin fiye naci ne? Idan kika ga ban
ɗauka ba ai kin san ina uzuri."
Daga can ɓangaren Surayya ta kwantar da murya ta ce. "Haba sweet..."

"Babu wani sweet, Surayya ba na cikin nutsuwata yanzu haka duniyar ta yi mini
zafi."

"Me yake damunka baby? Ko za ka zo na rage maka damuwa?"
Kamad Kabir ya buɗe baki ya faɗa mata abin da ya faru, sai kuma ya tuna idan ya
yi haka kamar ya rusa soyayarsa ne, idan Surayya ta ji labarin hotunan tsiraicin da
hafsa ta tura wa Fauziya ne ya sa ta fita daga gidan.

"Wannan ba damuwarki ba ce, family issuesne."

Daga haka ya katse wayar, sai ya sake lalubar layin Fauziya amma a kashe. Gida ya
ƙarasa ya laɓe a soro, don kada mutanen gidan su fahimci akwai matsala tsakaninsa
da ita.
Ganin har lokacin ba ta dawo ba ya sa Kabir ya nufi gidan Inna domin ya sanar da
ita halin da ake ciki, a lokacin da ya shiga gidan har an fara kiraye-kirayen
sallar Isha'i.
Yana shiga ɗakin Inna ya nemi wuri ya zauna haɗe da haɗa kai da gwiwa. Inna da
ta gama alwala ta shiga ɗakin ta ce.
"Kabiru nake gani da daren nan?"

Kabiru ya share ƙwallar idonsa ya ce, "Inna ni ne."

"To ashe Fauziyan ta isar maka da saƙona, amma ba ka samu zuwa ba sai yau. Yau
kuma me ka kawo mini, saboda dama garin tuwona ya ƙare."
Inna tana yin gama magana ta ji Kabir yana shasshekar kuka, a ɗan kaikaice ta
leƙa fuskarsa ta ce.

"Wai kuka kake yi Kabiru? A cikin yaranka wata ce ta mutu?"

Kabir ya girgiza mata kai, Inna ta sake cewa.
"To Fauziyan ce ta mutu?" A nan ma ya sake girgiza mata kai.
"To uban me ya sa ka kuka tun a farkon daren nan? Ni dai na san rabon da na ga
kukanka tun ranar da mahaifinku ya mutu."

"Inna gida na koma na ga Fauziya ba ta nan, na je gidansu da niyyar tambayarsu sai
mahaifinta ya tambaye ni ya take, kin ga kenan ba ta je can ba. Ga shi dama ba ta
tambaye ni ba, ban san inda ta tafi ba."
Kabir ya ƙarasa maganar yana zubar da ƙwallah. Wani takaici ne ya maƙure ziciyar
Inna, ta dube shi a wulaƙance tana sakin dogon tsaki ta ce. "Mttssswww amma dai
Kabiru ka yi asara wallahi, yanzu a kan mace kake zubar da ƙwalla? Ashe abin da ake
faɗa gaskiya ne, yarinyar nan ta gama wanke hannu a kanka."

Inna ta koma bakin gado ta zauna ta cigaba da cewa, "Yo wai ma Fauziyar yarinya
ce? Da za ta fice har ka dinga neman saboda ta ka ganɗma lalacewa"
Cikin damuwa Kabir ya ce, "Wallahi Inna ni ne da laifi, ni na ɓa ta mata rai, duk
macen da ta ga abin da na yi fiye da haka ma za ta iya aikatawa."
"To ai sai ka yi ta yi tun da wahala ta aure ka, yanzu kuma a ina ta bar yaran?"
Kabir ya ce, "Suna ɗakin matar gidanmu."

"Amma wannan yarinya an yi baƙar munafika, haka kawai ina zaune ƙalau ta ɗaga
mini hankali. Sai ka fita ka kai cigiyarta gidan radiyo, tun da lalacewarka ta kai
haka." Daga haka ta saka hijabinta ta tayar da sallah. Kabir da ya lura zamansa a
wurin Inna ba mafita zai kawo masa ba, sai ya miƙe ya fice. Kasancewar Sadiya ta ji
duk abin da yake faɗa, sai ta tsayar da Kabir tana tambayarsa. A nan ya zayyane
mata duk abin da ya faru, duk da bai fito ya faɗa mata laifin da ya aikata ba.
Shiru ta yi tana nazari, amma har cikin ranta take ji Kabir ne bai kyautawa Fauziya
ba, domin ta san tana da haƙurin gaske. Saboda damuwa Kabir haka ya dinga takawa a
ƙafa, yana tafe yana jimamin halin da take ciki da tsohon ciki a wannan lokacin. A
haka har ya ƙarasa gida.

Tun lokacin da Fauziya ta tashi daga bacci ta ji mararta da bayanta suna ciwo,
don haka ta yanke shawarar zuwa asibiti. A ranta tana fatan koda haihuwar ce ta zo
mata, tana fatan ta kasance silar tafiyarta lahira. Duk haihuwa ukun da ta yi Kabir
ne yake kai ta asibiti, daga baya kuma sai ya kira matar mahaifinta ya sanar da ita
idan sun je. Amma da yake zuciyarta a cunkushe take da haushin Kabir, ya sa ta
ɗauki duk wani kaya da za a buƙata a asibiti. Ta ƙi sanar da Lawisa ne, saboda ta
san idan suka tafi ita da Lawisa asibiti babu a inda su Na'ima za su zauna
ballantana su ci abinci.
Sai da ta fara biyawa ta gidan Dillaliya ta roƙe ta, da ta ba wani abin daga
cikin cikon kuɗin firji, bayan ta karɓi kuɗin ta fice daga gidan.
Fauziya ba ta damu da kallon da mutane suke yi mata ba, tana tafe tana hawaye
haka ta dinga tafiyar ƙafa domin ya taimaka mata wurin samun saurin naƙuda. Ta yi
tafiya mai nisa sannan ta samu adaidaita sahu ya kai ta asibiti, a lokacin da ta je
asibiti ana duba ta aka ga tana 5cm. Wayarta ta ciro ta fara kiran ƙanwarta da suke
uba ɗaya ba ta same ta ba, ta kira ta matar babanta ita ma a kashe. Na'ima ba ita
ta haihu ba sai bayan sallar magriba, ta haifo jaririyar 'yarta mace kyakkayawa mai
kama sak da Kabir.
Ido ta ƙurawa jaririyar tana kallo, saboda tsananin kamar da suke yi da
mahaifinta. Wani irin takaici ya kamata sai kawai ta fashe da gunjin kuka, Midwife
ɗin da ke gefe ta dafa ta ta ce.

"Maman baby kukan kuma na mene ne? Ai farinciki ya kamata ki yi, tun da Allah Ya
raba ku lafiya." Murmunshin yaƙe Fauziya ta yi, sannan ta ciro wayarta ta sake
kiran lambar ƙanwarta Shukura. A wannan karon ta ci sa'a an ɗauka, a nan ta sanar
da ita asibitin da take. Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba Shukura ta ƙarasa asibitin,
bayan an gama duba ta da jaririyarta aka sallame ta suka wuce gida.

Lokacin da Fauziya ta yi sallama da gudu yaranta suka fito daga ɗakin Lawisa suna
faɗin.
"Mami oyoyo."
Turus! Lawisa ta yi ganin Shukra tana rungume da jaririyar Fauziya, tsalle Lawisa
ta buga ta ƙarasa gabanta ta ce.

"Wai dama matar nan abin da kika fita kenan? A gaskiya kin shammace ni Maman
Na'ima, shi ma kuma Abban Na'ima abin ka da namiji bai ce mini haihuwa kika fita
ba.
Barka-barka uwar 'yan'mata, In Shaa Allahu matar gwamna kika haifo mana." Fauziya
ta saki murmushi, tana shirin shiga ɗaki su A'ilo suka fito suka yi mata barka
sama-sama kowacce tana yamutsa fuska.
Sai da Shukura ta yi mata ɗan abin da ba a rasa ba, sannan ta wuce gida. Kafin
wani lokaci tuni Lawisa ta ɗora mata ruwan wanka, sai da ta surka mata sannan ta
karɓi jaririyar ita kuma Fauziya ta shiga wanka. Bayan Fauziya ta gama Lawisa ta
haɗa mata ruwan shayi ruwan bunu. Karamcin da Lawisa ta yi mata ya sa ta dinga
zabga mata godiya, har sai da Lawisan ta nuna ɓacin ranta. Sai da ta yi wa su
Na'ima shimfiɗa, ta tambayi Fauziya ko akwai abin da za a yi mata ta ce a'a, sannan
Lawisa ta yi mata sallama ta tafi ɗakinta.

Lokacin da Kabir ya shiga gidan hango ɗakin ta ya yi a kunne da fitila, wanda
hakan ne ya ba shi tabbacin ta dawo gidan. Ƙafarsa har harɗewa take saboda sauri, a
haka ya faɗa ɗakin. A zaune ya same ta jingine da gado, yanayin fuskarta babu yabo
babu fallasa. A fili Kabir ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, saboda farinciki
kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha.
Fauziya yi ta yi kamar ba ta gan shi ba, sai dai kallo ɗayan da ta yi masa ta
fahimci duk ya fita a kamanninsa. Ƙafafuwansa sun yi futu-futu kamar wanda aka tuno
daga rami, a gefenta ya zaune murya a raunane ya ce.

"Fauziya!"

Ido ta zuba masa tana kallo sai dai ba ta amsa masa ba, ya riƙo hannunta a sanyaye
ya ce.
"Hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba da na dawo na ga ba kya gidan nan, don
girman Allah ki yi haƙuri ki saurare ni. Na san na yi kuskure amma don Allah ki
yafe mini."
Ajiyar zuciya Fauziya ta sauke tana janye hannunta daga cikin nasa ta ce, "Da a
ce ban yafe maka ba, da fitar da na yi ba zan sake tsoma ƙafata a cikin gidan nan
ba."

Lumshe ido ya yi cikin farinciki ya ce, "Wallahi wannan yarinyar da kika ga
maganarmu ban jima da haɗuwa da ita ba, kuma kin san akwai shaiɗanun mata da suke
jan hankali maza. Wannan ne nan farko da ƙarshe, In Shaa Allahu haka ba za ta sake
faruwa ba..."

"Wannan ba damuwa ta ba ce Kabiru! Amma ka sani, ka zabtare kaso casa'in da tara
na daga cikin yarda, ƙauna da amincin da na damƙa maka. Ka shayar da ni ruwan
mamaki Kabir, mamakin da har zuwa numfashina na ƙarshe ba zan daina yin sa ba. A
kullum ina son ka dinga tunawa, kai ma uba ne. Uban 'ya'ya matan da kake yunƙurin
ɓa ta tarbiyyar 'yar mutane."
Shiru Kabir ya yi yana jin kalamanta suna ratsa shi, ko babu komai ya ji daɗi da
ta furzo abin da yake cikin zuciyarta. Ya sake marairaicewa ya ce, "Duk abin da
kika faɗa haka ne, In Shaa Allahu zan kiyaye. Amma don Allah ki daina fushi da ni,
wallahi fushinki shi ne abin da ya fi komai ɗaga mini hankali."

Kabir ya faɗa yana jiran amsarta, kukan jaririya ya ji a bayanta. Fauziya ta juya
ta ɗauko ta tana yunƙurin ba ta mama, wani irin abu ne ya tsarga masa kamar wanda
aka yi wa shocking. Da wata irin murya cike da ruɗewa ya ce, "Wai dama kin haihu
Fauzina?" Fauzina da ta ji ya faɗa ya sa kalmar ta ƙara ba ta mata rai, ta tuno
boyis ɗin da ta saurara wanda ya yi wa Hafsa da ta ji yana cewa, duk duniya bai
taɓa yi wa kowacce mace soyayyar da yake yi mata ba. Ganin ba ta za ta ba shi amsa
ba, ya sa shi saurin karɓar jaririyar ya rungume a ƙirjinsa.

Kamar mutum-mutumi haka Maman Nana ta daskare a tsaye tana kallon Jafar har ya
shige ɗaki, ita abin ma mamaki ya ba ta. Domin tun da suka yi aure ba ta taɓa
amfani da gawayi ba, duk da a shekarun baya ƙarfin Jafar bai kai na yanzu ba. Rufa
masa baya ta yi cikin ɗakin, yana ganin haka ya sake haɗe fuska.

"Abban Nana wai me yake faruwa? Me ya sa kake son cusguna mini? Me na yi maka duk
ka canza kake ƙaƙalo abin da za ka cusguna mini?"
Maman Nana ta yi maganar muryarta tana rawa.

"Me kuma na yi miki?"
"Amma clinder fa ka ɗauke mini ka kawo buhunhunan gawayi ka ajiye mini."
Sai da ya ɗaura towel ɗin wankansa sannan ya ce.

"Su waɗanda suke amfani da gawayin mutuwa suka yi? Ko kuma taɓo ya yi musu a
goshi? Am sorry to say na ga ke gidanku ma da itace suka amfani." Saukar kalaman
Jafar a kunnenta ji ta yi tamkar an buga mata guduma. Maman Nana ta haɗiyi wani
irin abu mai ɗaci a zuciyarta, idonta ya ciko da ƙwalla.

"Gori za ka yi mini Abban Nana? Ko dai ka daina ƙaunata ne? Wane ne yake zuga ka
a kan iyalinka ne?"

Jafar ya matsi toothpaste kamar ba zai tanka mata ba, sai da ya je bakin ƙofa ya
waiga ya ce.
"Babu ɗaya daga ciki, kawai ke kika yi zargin haka. Yanzun ba ni da ƙarfin saka
gas ne..."

"Wallahi kana da shi Jafar, sai dai idan wani ne yake zuga ka kuma wallahi ba zan
yi amfani da gawayi ba."
Maman Nana ta furta cikin kuka, jin hayaniyarsu ya sa Abdul ya rarrafa ya riƙe
ƙafarta ya saka kuka shi ma. Ɗaukarsa ta yi tana hawaye ta ji ya ce, "Ke dai
Sumayya wallahi ba matar rufin asiri ba ce, ban da haka saboda na kawo miki gawayi,
za ki yi mini hayaniya har maƙota su ji."

Wani irin sak Maman Nana ta yi, tana jin wata irin juwa tana yunƙurin taɗe
ƙafafuwanta. Hawaye ya shiga kwarara daga kwarmin idonta, cikin ƙunan zuciya da
sarewa ta ce.
"Yau ni kake kira da ba matar rufin asiri ba Jafar?" Cikin halin ko inkula
Jafar ya ce.
"Mata nawa ne a nan unguwar suka amfani da gawayi? Su sun yi wa mazajensu irin
abin da kika yi mini? Idan kina

Please Login or Register in order to submit comment