Reading NAUSHIN WUTA by AMEERA ADAM Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da su Asiya suka ci abinci suka wuce Islamiya sannan Maimuna ta sake
lalubar wayarta. Kamar ya san wayar tana hannunta nan take ta ga alert na dubu
ashirin, wani irin tsalle ta buga tana riƙe baki. Jikinta har rawa yake ta shiga
ɗaki ta ɗauko ƙaramar wayarta ta saka batirin ta kunna ta, a gaggauce ta shiga
kiransa sai dai bai ɗauka ba don dama ta san ba lallai ya ɗauka ba sai dai ya kira
ta.
"Baby yanzu na ga kuɗin ya shigo."

Maimuna ta furta muryarta har rawa take yi, jin sautin murmushin da yake yi har
cikin zuciyarta ta yi. Ta mayar masa da martanin murmushin sai ta ji ya ce, "Yanzu
saboda dubu ashirin kika kira? Haba my Moon, don Allah kada ki sake yi mini haka."
Maimuna ta saki murmushi, tana shirin magana ta ji ya shagwaɓe murya ya ce.

"Ni fa na gagara haƙuri gaskiya, na biya ta kasuwar waya na saya miki sabuwar
babbar waya wacce za mu dinga ganin hotuna da bidiyon juna."
Maimuna ta ji daɗi sosai, amma tana tsoron kada asirinta ya tonu Nazir ya gano
ta.
"To ya za a yi ta zo hannuna? Kuma ni ina jin tsoron kada Nazir..."

"Idan muna magana ba na son ki dinga ce mini kina tsoron Naziru, wai wanne irin
zama yake yi da ke da kike mugun jin tsoronsa."
Jafar ya katse ta cikin sauri, shiru Maimuna ta yi sai ya cigaba da cewa.
"A gaskiya alamu sun nuna ba kya jin daɗin zama da shi, a haka ka gan shi kamar
na gari yana sunkuyar da kai ƙasa. Amma ya zo a jiye kyakkyawar mace, yana azabtar
da ita." Sai kuma Jafar ya ɗan kwantar da murya ya ce.

"Haba my Moon, ki duba irin kulle da takunkumin da yake yi miki? Wai a haka kika
iya zama da shi har tsawon shekara goma? A gaskiya an ci amanar kyau wallahi."

Jin maganganun Jafar sai suka soso mata mikin da yake ɗamfare cikin zuciyarta,
kalamansa suka yamutsa zuciyarta tana jin ɗacin yaudarar da Naziri ya yi mata a
shakarun baya.

"Hmmm ai Nazir ya dasa mini mikin da zai jima a zuciyata bai goge ba, lokaci
kawai nake jira my baby."

"Kada ki jira lokaci Moon, kamata ya yi lokaci ya jira ki. Saboda yara uku rak ba
za su hana ki rawar gaban hantsi ba. Wai ma kina kallon kanki a mudubi kuwa?"

Tambayar da Jafar ya yi mata, ya sa Maimuna ta yi saurin matsawa gaban mudubinta
tana ƙarewa kanta kallo.
"Ni fa tun ranar da na fara ganinki na san Allah Ya zuba halitta, kuma wallahi
duk wanda ya ganki ba zai ce kin taɓa haihuwa ba. Ba kamar waccan sakaran da ta yi
shaɓar da jiki ba, dubi ƙirjinta ba kyan gani duk ya saki ya tamushe kamar an tsoma
leda a ruwa."
Dariya Maimuna ta shiga ƙyaƙyatawa har da riƙe ciki, sai da ta yi mai isarta ta
ce.
"An ya ba faɗa kake ba Baby don na ji daɗi, ka san fa babu laifi ƙawar tawa tana
mayar da hankali wurin gyara."

Jafar Ya saki tsaki ya ce, "Hmm ke dai a yi sha'ani kawai, yanzu dai wayarki zan
ba wa Maman Nana ta kawo miki gobe..."
Tun bai gama magana ba ta katse shi, "Maman Nana fa? Ka san me kake faɗa kuwa
Jafar?"

Dariya ya yi a fili ya ce, "Saboda zan ba wa Maman Nana waya ta kawo miki har shi
ne ya sa kike kiran sunana gatsal? Zan ba ta ta kawo miki kamar yadda na faɗa, zan
ce mata mijinki ne ya ba ni sautin waya daga kasuwa. Sai na ce ta miƙo miki, amma
sai na kintaci lokacin da Naziru ba ya gida don kada a samu matsala. Idan kuma na
samu wata mafitar shi kenan, ko kina da wata shawarar?"
Kamar Jafar yana ganinta ta girgiza kai ta ce, "A'a babu." Sun ɗan ɗauki lokaci
suna waya sannan suka yi sallama cike da kewar juna.

Fauziya tana nan zaune a gefen gado tana hawaye ta fara jin sautin munsharinsa,
wanda hakan ne yake tabbatar mata da tuni bacci ya yi awon gaba da shi. Haska shi
ta yi da wayar hannunta, tana ƙare masa kallo. Ta kawar da kai gefe cikin sanyin
murya ta ce.

"Ya Allah Ya Ubangiji ba don ni ba, ba don halina ba. Allah ka shirya mini
mijina."
A inda yake ta bar shi, ita kuma ta haye gado ta kwanta zuciyarta a cunkushe da
ɓacin rai, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da asuba ta yi cikin bacci ta
ji Kabir yana tashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune. Sai ta ga ya yi mata
kalar tausayi ya zauna a gefenta, ya saka hannunsa ta bayanta ya riƙo ƙugunta.
"Don Allah ki yi haƙuri Fauzina!"
Kabir ya furzo kalamansa ƙasa-ƙasa.

"Zuwa yanzu ya ci ace na haddace waɗannan kalaman naka, ka sake ni Abban Na'ima
zan je na yi sallah."
Ta ba shi amsa rai a ɓace, Kabir ya riƙo ta a jikinsa tsam ya ce.

"Wallahi ba laifina ba ne, su Abbati ne suka ingiza ni amma In Shaa Allahu wannan
ne ƙarshe."

"Ashe idan su Abbati suka ce ka shiga wuta sai ka bi su ko? A yanzu babu wata
magana da za ka faɗa mini na yarda da kai a kan shaye-shaye. Su Abbati sun isa su
yi maka dole idan kai ma ba ka so ba?"

Kabir ya yi shiru har sai da Fauziya ta gama sannan ya shiga lallashinta. Alwala
ya fita ya yi, ya wuce masallaci. Bayan ya dawo cike da daɗin baki ya ce.

"Ni kuwa ya maganar Dillaliya? Allah Ya sa ta taya kayan da mutumci."

Da yake a lokacin Fauziya ta ɗan sauko ta ce, "Ta taya shi dubu saba'in har ta
bada rabin kuɗin." Fauziya ta miƙe ta buɗe drower kayanta, jakar ratayarwa ta ɗauko
ta zura hannu ta zaro kuɗin ciki ta miƙa masa.

"Ragowar ta ce sai bayan kwana uku za ta bayar, an jima idan gari ya waye ta ce
za ta zo da wanda zai ɗauka."
Kabir ya janye hannunsa daga jikin kuɗin ya ce, "A'a ki ajiye a wurinki ko jari
sai ki ja da su" Girgiza kanta ta yi ta ce, "A'a ka cika ka sayi wani abin na aikin
gidan can, ka ga an rage wani abu. Idan ta kawo cikon kuɗin, kafin nan kai ma ka
samu wasu sai ka haɗa da na wurinka kafin dai ranar tashinmu an rage abin da za a
rage." Fauziya ta ɗan kalli ɗakinsu da shinfiɗar su Na'ima cikin damuwa ta ce.
"Na gaji da zaman da muke yi ɗaki ɗaya Abban Na'ima. Yaranmu sun fara wayo kwana
da su a ɗaki ɗaya zai iya haifarwa tarbiyyarsu matsala." Kabir ya sauke ajiyar
zuciya ya ce.

"Haka ne Fauzina, amma kuɗaɗen da kike ba ni a ginin nan ina gudun wani abu a nan
gaba."
Yanayin yadda ya yi mata maganar cikin sanyin murya ya sa jikinta ya yi sanyi, ta
dube shi a sanyaye ta ce.
"Me kake gudu Abban Na'ima?"

"Ina gudun kada watarana wani abu ya haɗo mu ki yi mini gori, sannan tarin
kuɗaɗen da kika ba ni lissafinsu nake yi. Idan Allah Ya buɗa mana nan gaba zan biya
ki kuɗinki." Maganar Kabir ba ƙaramin ɓa ta ranta ta yi ba, domin duk abin da take
yi wa Kabir tana yin sa tsakani da Allah ne. Tun da a ganinta rufin asirinsa tamkar
rufin asirinta ne. A irin kalubalen rayuwar da ta fuskanta a kaf faɗin duniya, gida
biyu ne ya zame mata gata kuma madogararta. Daga gidan mahaifinta sai gidan
mijinta, gidan mijin da take fatan sai dai mutuwa ta ɓamɓare ta daga ginin
turɓayarsa. Gidan mahaifinta kuwa a yanzu ba ta fata ko burin kawo wata ƙaddarar,
da za ta kwashe ta daga gidan mijinta kuma aljannar duniyarta zuwa ƙangin bautar
gidan mahaifinta. Amma sai ta ji Kabir yana faɗar kamalan da take jin, tamkar bai
ba ta matsayin da ta ba shi a cikin zuciyarta ba. Don haka a ɗan ƙufule ta ce.

"Shi kenan tun da kai abin da ka ɗauka kenan sai ka lissafa abin da nake bin ka,
tun da ai da na ba ka cewa na yi na ba ka aro."

Murmushi ya yi don ya fahimci ta ji haushi, sai ya gyara zama ya ce.
"Tuba na ke uwargida kuma amarya a gidan Kb babban tela. Haba Fauzin Kb fushin
na mene ne?"
Fauziya ta ɗan kwaɓe murya a shagwaɓe ta ce, "To ai kai ne da wata irin magana."

Hira suka ɓarke da ita har gari ya ƙarasa wayewa, gabanin Kabir zai fita ta ce
masa za ta je gida ta gaida mahaifinsa. Amma sai ta fara biyawa ta wurin Inna ta
gaida. Fita ya yi ya sayo mata ɗan omo, sabulu da magi ƙulli bibbiyu. Ƙulli ɗaya ya
ce ta miƙa wa mahaifiyarsa, ƙulli ɗaya kuma ta kai wa mahaifinta. Godiya ta zuba
masa sosai, ta sake ba wa Kabir wani matsayi a zuciyarta. Domin kusan duk ranar fa
za ta je gaida mahaifinta sai ya sayo wani abin ya ce ta kai masa, har turare sayo
mata yake ya ce ta kai masa. Kyautatawar da yake wa mahaifinta ya sa Kabir ya sake
samun fada a zuciyarta da zuciyar mahaifinta har ma da matan babanta. Don ba ta
taɓa zuwa gida haka, idan ya saya wa mahaifinta abu. Ita kuma da ɗan canjin
hannunta na kuɗin kitso, ko na ɗan gyare-gyaren kayan da take yi sai da saya wa
matan babanta ɗan magi ko tsintsiya. Wani lokacin kuma ƙannenta take sayawa alewa
ta tafi musu da shi, haka idan za ta leƙa gidan mahaifiyarsa Inna ko bai ba ta
komai ba da kuɗinta take saya mata omo da ɗan abin da ba a rasa ba.

Shirya su Na'ima ta yi tsaf cikin ankon atamfa dogayen riguna, sannan ita ma ta
shirya cikin doguwar rigar abaya ta ɗora babban mayafi ta yane kanta. Lokacin da za
ta fita Lawisa kawai ta yi wa sallama, saboda magana mai daɗi ba ta taɓa haɗa ta da
su A'ilo. Koda ita ta yi musu mai daɗi, sai sun san yadda suka yi suka mayar mata
da martanin baƙar magana.
Duk wanda ya ga Fauziya da 'yan'matanta uku sai sun birge shi, saboda kusan
gabaɗaya kansu ɗaya tazararsu babu yawa. Daga gidan su Fauziya zuwa gidan Inna babu
nisa sosai, don a adaidaita sahu bai fi naira ɗari ba. Idan mutun bai sa ƙyuya ba
ma zai iya zuwa da ƙafa.

A lokacin da Fauziya ta yi sallama a gidan Inna, Sadiya tana tsakar gida tana
wanki. Inna kuma tana zaune tana ɗaurin tsintsiya. Sadiya ce ta faɗaɗa fara'arta ta
ce, "Yanzu uwar biyu ba ki rufe fita ba sai kin haife mana ɗa a titi?"

Murmushi Fauziya ta yi mata, ta ƙarasa gaban Inna ta tsugunna ta ce.
"Barka da hutawa Inna."
Inna ta ɗan taɓe baki ta ce, "Wane hutu Fauziya ana fama da rayuwa." Fauziya ta
sake yin murmushi saboda idan da sabo ta saba da halin Inna, domin irin matan nan
ne da ba su da godiyar Allah. Saboda bakin ƙoƙari 'ya'yanta suna kyautata mata,
amma duk lokacin da suka haɗu sai ta yi jajen tana cikin wani hali. A cikin yaran
Inna mijin Sadiya da Kabir ne marasa ƙarfi sosai, don haka ta fi ji da matan 'yan
uwan Kabir. Kuma a haka ma tana nannan da Fauziya saboda kyautatawar da take yi
mata, amma Sadiya da yaranta da suke zaune a gida ɗaya kullum cikin tsangwama da
kyara suke. Su Na'ima suka zube ƙasa suka gaida Inna, Inna ta taɓe baki ta ce.

"Ai dama ku ba na ganinku sai idan uwarku za ta zo, ko ban isa a turo mini ku ba
ne oho." Sadiya da Fauziya suka haɗa ido suka saki murmushi a fakaice, Inna ta sake
leƙen hannun Fauziya ta ga ba ta ga komai ba sai kuwa ta sake cewa.
"Kabirun ma kusan sati guda kenan ban gan shi ba, tun ranar da ya kawo mini
garin tuwo da taliya. To dai nan ɗin da ba kwa son zuwa, nan ne dai gidanku tun da
ubanku ma a nan ya tashi. Kuma ni na haifi Kabiru babu yadda kuka isa ku yi da ni."
Shiru su Na'ima suka yi, saboda dama babban dalilin da ya sa ba sa son zuwa wurin
Inna yawan faɗanta. Sau tari Fauziya za ta shirya su musamman ranar Juma'a ta ce su
zo su gaida Inna, amma suna zuwa ko zaman minti talatain ba sa yi suke tafiya. Wani
lokacin ne ma suke zama su yi wasa da yaran Sadiya.

"Kai Salim ku zo ku ɗauki tsintsiyoyin nan, ke kuma Zainabu ga mafitai ki ɗauka.
Yau idan kika sake ki yar mun da kuɗi wallahi sai ubanki ya biya ni kuɗina."
Inna ta furta wa 'ya'yan Sadiya tana tura musu farantan da aka jera tsintsiya da
mafici. Sadiya ko kaɗan ba ta jin daɗin tallan da Inna take ɗora musu, don dai babu
yadda za ta yi ne amma ba ta son tallar musamman ga Zainab da ta kasance 'ya mace.

"Inna ga wannan a yi wanki da shi babu yawa."
Fauziya ta zaro ledar daga kan cinyarta. Ina sai da ta ɗora wa su Salim farantin
tsintsiya, sannan ta waiga wurin Fauziya riƙe da baki ta ce, "Oh ke dai Fauziya ba
kya gajiya, to an gode madalla. Ai kuwa kin ce na sha wanki, dama kayan sawata duka
sun ƙare sai masu datti. Ai ka ga masu abin kirki, amma wasu kuwa ko ƙullin gishiri
ba su san su ba ni ba. Ke dai Allah Ya yi miki albarka, wannan ciki da kike ɗauke
da shi Allah ya sauke ki lafiya ya sa ki haifo wa Kabiru magaji." Fauziya ba ta
amsa ba, suna nan zaune suka ɗan taɓa hira. Fauziya tana son su keɓe da Sadiya amma
tana tsoron fassarar da Inna za ta yi musu. Sun ɗan jima suna hira Inna ta ce.

"To yanzu ni dai ragowar Taliya ɗaya gare ni ballantana na dafa mana abinci, ko da
wuri za ku wuce ne Fauziya?"
Girgiza kai Fauziya ta yi tana mamakin rayuwar Inna, Fauziya ta miƙe ta ce.
"Yanzu za mu wuce Inna, da ma zan je gaida Baba ne na ce bari na zo na gaishe ki."
Nan take kuwa Inna ta hau washe baki ta ce, "To shi kenan ku gaida gida, shi kuma
Kabiru ki ce masa ina son ganinsa." Fauziya ta amsa sannan ta nufi hanyar fita, da
sauri Sadiya ta bi ta tana faɗin.
"Wai har za ku tafi, bari mu fita tare dama zan miƙa wa Mariya kayan wankin da na
yi mata."

Da biyu Sadiya ta bi Fauziya suka fita, suna fita Fauziya ta ce. "Wai dama har
yanzu su Salim ba su daina tallar muhucin nan ba?"
Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai na kusa barin gidan nan Fauziya,
wallahi na gaji haƙurina ya kusa ƙarewa."

"Idan kin tafi yaran kuma fa Sadiya?"
Cikin halin ko'inkula ta ce, "Allah zai raya su, wasu ma suna tasowa babu iyayen
kuma su yi rayuwa kamar kowa."
Fauziya ta tsaya tana bin Sadiya da kallo, duk ta lalace saboda rashin kwanciyar
hankali.
"Don Allah ki daina wannan maganar, addu'a za ki cigaba da yi har Allah Ya hore
muku ku bar wa Inna gidanta. Kin san zama wuri ɗaya dama yana kawo haka, ki cigaba
da addu'a sai ki ga watarana sai labari."

"Hmmm ba za ki gane ba Fauziya, ni na san takaici da baƙincikin da nake ci a
gidan."
Cikin ƙarfafa gwiwa Fauziya ta ce, "Babu abin da ya fi ƙarfin addu'a."

Fauziya da Sadiya sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama, Fauziya ta
wuce ta tari adaidaita sahu suka wuce gidan mahaifinta. A tsakar gida ta samu
mahaifinta yana ta bambamin faɗa, a kan 'yan nefa sun zo karɓar kuɗin wuta. Har
ƙasa ta tsugunna ta gaida shi, sannan ta miƙa masa saƙonsa, nan take Baba ya shiga
washe baki yana saka mata albarka. Ɗakin Inna Sakina ta shiga da yake a nan ɗakin
aka raini Fauziya, bayan sun gaisa ta fara bin ƙannenta da alawoyi tana danƙa musu.
Su Nai'ima kuwa dama tun a tsakar gida suka fara wasa da ƙannen mahaifiyarsu.


Kabir yana fita daga gida kai tsaye wurin masu sayar da ƙofa ya nufa, ƙofofin ba
ƙaramin tsada ya ji sun yi masa ba. Ya cika da ragowar kuɗin wurinsa ya sayi guda
ƙofofin guda uku, ƙofar farko ta ƙofar gida. Sai ɗakin da yake a tsakar gida, da
kuma ƙofar falon gidan. Daga nan wurin can gidan nasa ya nufa, ya kira masu saka
ƙofofi suka fara aiki. Ba su suka gama ba sai yamma liƙi, gabanin zai fito daga
gidan kiran Hafsa ya shigo masa, zama ya yi a bakin dandamalin rijiyar sannan ya
ɗauka.

"Gimbiyar mata!"

Ya furta cike da kashe murya, daga can ɓangaren Hafsa ta ce.
"An ya kana jin abin da nake ji na soyayyarka kuwa?" Kabir ya sake kwantar da
murya ya ce, "Haba Hafsyna, don Allah ki daina faɗin haka."
Hafsa ta ce, "Ka duba whatsapp ɗinka na turo maka da hotuna."

Jikin Kabir har rawa yake ya katse wayar, sannan ya yi saurin buɗe datarsa. Yana
shiga whatsapp ya fara cin karo da saƙonninta, buɗe hotunan ya yi ya ga ta ɗauko
masa hoton ƙirjinta da ƙasanta kamar yadda ya buƙata. Cikin wani irin yanayi ya
sake kiranta, a kunyace Hafsa ta ɗauka sai ta ji duk muryarsa ta sauya.

"Baby kin yi kyau sosai, amma don Allah ki yo mini bidiyo mana."
Hafsa da duk ta ji nauyinsa ya kama ta ta ce, "Baby gaskiya ka yi haƙuri, wallahi
wannan ma da ƙyar na iya turo maka."

"Guda ɗai-ɗai fa kawai za ki yi mini, kuma kin san ai aurenki zan yi ko ba ki
yarda ba?"

Shiru ya ji Hafsa ta yi, ya ɗora da cewa. "Akwai kuɗin da nake saka ran za su
shigo mini nan da kwana uku. In Shaa Allah a satin nan za a kawo kuɗin aurenmu."
Daɗi ya lulluɓe Hafsa, jikin yana rawa ta ce.

"Zan turo maka amma don Allah kana gani ka goge."

Cikin sauri Kabir ya ce, "Wallahi ina gani zan goge." Kashe wayar Hafsa ta yi ta
shige ɗakinta ta yi masa bidiyo ta tura masa. Kabir yana ganin bidiyon a ruɗe ya
shiga yi mata replay da kalaman batsa, tun tana jin nauyinsa har ta fara biye shi.

Yamma liƙis Fauziya ta koma gida ta ɗora musu girki, a wannan karon ma ana yin
magriba ta kira Kabir ta sake tuna masa maganar da suka yi, game da alƙawarin da ya
ɗaukar mata ba zai sake shan komai ba. Sannan ya ce ta tsala masa kwalliyar domin a
cike yake da kewarta. Zuciyar Fauziya fes ta tsala wanka cikin wata doguwar riga
marar nauyi, ta raba gashinta gida biyu kamar wata 'yar baby ba ƙaramin kyau ta yi
ba. Suna nan zaune ita da yara kimanin ƙarfe tara suka ji sallamarsa. Kusan lokaci
ɗaya ita da yaran suka rungume shi har ita suna faɗin.

"Abi oyoyo."

Rungume su ya yi gabaɗaya, sai Fauziya ta saci kallon yadda suke nishaɗi ita da
yaran, saboda dawowarsa da wuri kuma a cikin nutsuwarsa, sai ta ji ƙwalla tana
shirin zubo mata. Ɗaya bayan ɗaya ya tsugunna yana sumbatar yaran a goshi, sai ya
ɗago ya dube ta suka haɗa ido. Rungumo ta ya yi a jikinsa yana kashe mata ido ɗaya,
irin kallon da take bin sa da shi ya sa shi hura mata iska a fuska.

"Wannan kwalliyar zan biya tukwicinta an jima."

Ya furta mata a hankali, ta sakar masa murmushi ta ce.
"Na fa tsufa da yawa."
Kafaɗa ya maƙale mata cikin kwaikwayon muryarta ya ce, "Ni ban yarda ba." Duk da
yaran ba su fahimci me suka tattaunawa ba, jin yadda mahaifinsu ya maƙale murya ya
sa suka fara ɗariya.

Hula, agogo da wayarsa ya ajiye a gefen gado ya ɗauki bokiti ya zuba ruwa ya tafi
yin wanka. Kabir ya manta shaf da abin da Hafsa ta turo masa bai goge ba, har ya
iya ajiye wayarsa. Kuma ya bar hotunan ne saboda idan ya keɓe ya dinga kalla yana
jindaɗi.

Fatima ce ta ɗauki wayar ta shi, da yake wani lokacin idan yana gida ya kan kunna
musu game ko cartoon su kalla. Shige-shige suka fara yi masa har suka shiga cikin
gallery ɗinsa, Na'ima ta zura kanta ta danna ɗaya daga cikin bidiyon da Hafsa ta
tura masa. Fauziya da ke tsugunne tana jera masa kayan abinci ta ji muryar mace
raɗau a kunnenta tana faɗin.

"Baby kana gani, wannan bidiyon..."

A gigice Fauziya ta fisge wayar daga hannunsu jikinta yana karkarwa, sakamakon ji
irin bayanin batsar da buduwar take yi. Domin a bidiyon hafsa tana yi masa tana
bayanin komai dalla-dalla.

"Lah Mami mene ne wannan?"

Na'ima da ta fi su wayo ta tambaya, sai da Fauziya ta saita nutsuwarta ta ce,
"Bidiyon wata marar lafiya ne da take neman taimako, za a haɗa mata kuɗi a yi mata
magani. Na sha faɗa muku idan mutum ya ajiye abu, sai an tambaye shi ake taɓawa
ko?"
Gabaɗaya suka gyaɗa mata kai, Fauziya da take jin wani abu yana taso mata a ƙirji
ta yi ƙarfin halin faɗin.

"To daga yau, ko da wasa ka da na sake na ƙara ganin ku taɓa wa mutum wayarsa.
Idan ba haka ba ranku zai ɓaci." Su Fatima suka amsa mata.

Ear pices ta ɗauko ta saka a kunne, ta shiga bidiyan ta kunna shi. Jikinta ya
ɗauki karkarwa gabanta yana wani irin bugu da ƙarfi, lokaci ɗaya hawaye ya wanke
fuskarta domin bidiyon ya matuƙar ƙazanta. Da sauri ta shiga whatsapp ɗinsa, ta ga
yawanci masu saƙon duk maza ne, don haka take mamaki a inda Kabir ya samu wannan
bidiyon. Har za ta fita ta ga an saka costomer Hafsa lace bubu, tana shiga ta ci
karo da emojin heart ta turowa Kabir. Can sama ta haura ta fara cin karo da
saƙonnin batsar da suka tattauna, a nan ta gano wannan bidiyon na Hafsa ne tun da
ga muryar ta nan ta kunna voice ɗinta ta ji."
Jikinta yana rawa ta kifa wayar, sai ta jingina da bango tana jim wata irin
tsanar Kabir ta mamaye ta.



Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[13/02, 21:15] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da
ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da
mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA SHIDA

UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳
Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda
habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta
ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai
musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan
kyauta tana kara soyayya

Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya
qualitatives via +234 816 916 8731

***

Tun tana zubar da hawayen zuci don kada yaranta da ke zaune su fahimci halin da
take ciki har ta gagara sarrafa zuciyarta saboda wani irin zafi da ɗacin da take yi
mata. Hawaye taka sosai tana shassheka tamkar za ta shiɗe, saboda wani irin
kakkarwa da jikinta yake yi ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri-sauri. Ganin halin da
mahaifiyarsu take ciki ya sa suka ƙarasa wurinta suna tambayarsu, ba ta iya tanka
musu ba sai ma wani irin kallo da ta dinga bin su da shi kamar ta ga sababbin
hallita. A ranta ta ayyana ƙila yarinyar da suke musayar munanan kalamai da Kabir
ko kaɗan iyayenta ba su san abin da take aikatawa ba. Sai kawai ta rungumo su
jikinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, ganin haka ya sa su
Fatima su ma suka rairai kukan

Please Login or Register in order to submit comment