Reading NAUSHIN WUTA by AMEERA ADAM Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [12/02, 21:41] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
TSOKACI: Labarin ya faru a gaske, sai kwaskwarima da na yi masa.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da
ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da
mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA ÆŠAYA

Gumi ne yake keto mata ta ko ina, saboda yanayin tsananin zafin garin da ake
busawa. Sai dai zafin da take ji bai kai rabin wanda yake É—amfare a birnin
zuciyarta ba, duba da zafi, zugi da raÉ—aÉ—in da ke kwance kane-kane a cikin ranta.
Wanda a kullum cigaban da yake samu, shi yake kuma dakusar da ƙwarin gwiwarta.

"Fauziya! Ke Fauziya, ki fito ki rufe mana gida. Kin san dai gidan matan aure ne,
za ki bar mu a yashe salon wani ƙaton ya faɗo mana."

Kiran mafarautar da A'ilo take yi mata, ya katse igiyar tunanin da ta zabarto ta
ba tare da ta sani ba. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita tsakar gida, tana shirin
magana A'ilo ta sake katse ta.
"Allah dai ya kusan raba yari da ɓarawo, don masifa a ce kullum sai ka kwanta a
ishe ka da bige-bigen ƙofa. Haƙƙi dai na zaman maƙotaka, wallahi ana shiga
haƙƙinmu. Baban Walid ya shigo tun ɗazu ki je ki rufe mana ƙofa. Idan mijin naki ya
dawo, ki riƙe hannunsa ki kai shi har ɗaki. Don wallahi idan ƙaton mashayi ya sake
faÉ—o mini É—aki sai mun sheme shi."

Ko kaÉ—an ba ta ji zafin maganganun A'ilo ba, domin kusan duk maganganunta a hanya
suke. Don haka ta gagara furta koda kalma ɗaya, ta ƙarasa soron mai cike da duhu ta
haska da 'yar ƙaramar wayarta ta rufe ƙofar. Sai da ta haska yaranta da ke kwance a
ƙofar ɗaki, ta gyara musu kwanciya sannan ta koma ciki. Domin zafin da ake yi ne ya
sa ta yi musu shimfiÉ—a a waje, kamar yadda ragowar matan gidan kowacce take yi wa
'ya'yanta shinfiɗa a ƙofar ɗaki. Idan dare ya tsala gari ya ɗan saki, sai kowacce
ta mayar da yaranta É—aki.

A hankali ta zauna, bayan ta kashe fitilar wayarta ta latsa lambar mijinta Kabir.
Sai dai tashin farko aka tabbatar mata wayar a kashe take, ta mayar da kallonta
wurin agogon wayar ya nuna mata ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare.
GyangyaÉ—i take yi daga zauna, don haka ta kishingiÉ—a da gefen gadon. Don kada
ta kwanta nannauyan bacci ya ɗauke ta, daga baya Kabir ya zo ya yi ta bugun ƙofa da
ƙarfi yana ja mata zagi a wurin matan gida. Da yake baccin yana kanta, nan taka ya
yi awon gaba da ita.

"Wayyo Allah ƙafata! Mami ƙafata cinnaka ya cije ni."

Kururwar Fatima ta katse mata daddaÉ—an baccin da ya yi awon gaba da ita, a gigice
ta fita tsakar gidan ta shiga kiciniyar haskewa da hasken fitilar wayarta. Inun
Fatima ya cika gidan, saboda azabar harbin kunamar da yake ratsa ta.

"Mene ne Fatima? Me ya samu ƙafar ki?"
Fauziya ta shiga jera mata tambayoyi tana haska ƙafar tata. Ba ta ga komai ba, sai
dai wurin da Fatima ta riƙe ya yi wani irin ja. Da hannu ta janye ta gefe, sai kuwa
ta ci karo da wata ƙatuwar baƙar kunama za ta gangara wurin da Na'ima take kwance.
Da sauri ta suri wani takalmi da yake gefenta ta buga mata, nan take kunamar ta
mutu. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, sai ta rasa taimakon da ake yi na gaggawa
idan kunama ta harbi mutum. Ga Fatima da ke sakin kuka kamar za ta shiÉ—e, duk ta
gama gigita ta. Hijabinta ta É—auko, ta É—auki Fatima mai kimanin shekara uku ta
goya. Wani irin nauyi ta ji, saboda tsohon cikin jikinta da kuma goyon Fatima da ta
yi. Kan mudubi ta fara dubawa saboda a nan take ajiyar kuÉ—i, amma ita kanta ba ta
da tabbacin za ta samu kuÉ—i masu yawa.

Naira É—ari biyu taci karo da ita, da sauri ta É—auka ta fita tsakar gida, ta
ƙarasa ƙofar ɗakin Lawisa tana yin sallama.
"Salamu alaikum. Lawisa! Lawisa."

Cikin bacci Lawisa ta amsa mata, Fauziya ta gyaya goyon Fatima ta ce. "Don Allah
ko zan samu aron dubu ɗaya a wurinki? Zan leƙa na miƙa Fatima kemis, kunama ce ta
harbe ta."

"Subhanallah kunama fa? To bari na dubo miki, amma dai ba za a samu dubu É—aya ba."
Lawisa ta furta tana daga É—aki. Fauziya tana nan tsaye, Lawisa ta É—aga labule ta
miƙe mata kuɗin hannunta, "Fauziya wallahi ɗari da hamsin kawai aka samu ga ta."
Fauziya ta karɓa tana faɗin.

"Don Allah zan tura ƙofar gida idan na fita, koda na dawo idan an rufe Lawisa. An
ce ba a son barin harbin kunama da sai na bari zuwa safiya."
Lawisa ta furta, "Shi kenan sai kin dawo, Allah dai ya tsare mu. Wallahi shi ya sa
kullum na kwantar da su Siyama hankalina yana wurinsu, wannan zafi Allah Ya sa mu
ga wucewarsa lafiya."
Fauziya ta amsa sannan fita. Kemis É—in da ke bayan layinsu ta zagaya, tun ba ta
ƙarasa ba ta hango shagon a rufe. Ta kalli yagulallun canjin hannunta ɗari.

'Bayan kemis É—in Bala ina zan kai Fatima?''

Fauziya ta raya a ranta, sai wani tunani ya faÉ—o mata. Da sauri ta sake É—aga waya
ta kira lambar Kabir, amma har lokacin a kashe take. Don haka ta yanke shawarar
zuwa shagonsu, don ta fi tunanin ba shi da caji ne ya sa wayarsa take kashe. Bakin
titi ta nufa, a lokacin babu mutane sosai sai tsirari da suke kai-komo. Zuciyarta
a cunkushe take tafiya, saboda kukan da Fatima take rairawa ga ciwon ƙafafuwa da
bayanta suke yi.

Ta É—an jima a bakin titi babu adaidaita sahu, har ta yanke shawarar fara tafiya
da ƙafa. Saboda shagon su Kabir ana iya zuwa da ƙafa, sai dai akwai 'yar tafiya
sosai. Tana tafe tana saƙa da warwara a cikin ranta, ga shi duk lallashin da take
yi wa Fatima ta ƙi yin shiru. Wani mai adaidaita sahu ta hango, da sauri shiga ɗaga
masa hannu. Har ya wuce ta, ganin goyon da yake bayanta ya sa ya dawo.

"Baiwar Allah wannan yarinyar da take kuka daga ina?"

Mai É—an sahun ya tirke ta da tambaya, yana wurga mata kallon tuhuma.
"Yata ce, shagon Babanta zan je kunama ce ta harbe ta zan kai ta kemis."
Fauziya ta furta a gajiya, kallon da yake yi mata na rashin yarda ya sa ta É—an
waiga ta ce.
"Fatima ki faɗa masa me ya samu ƙafarki."

Fatima ta sake sakin ihu cikin kuka ta ce, "Cinnaka mai allura ne ya harbe ni,
wayyo Mami ƙafata. Don Allah ki cire mini allurar cinnaka."
Sai da mutumin ya haska Fatima, sannan ya ga zallar kamar da suke yi da
mahaifiyarta. Ya ce Fauziya ta shiga, bayan ta zauna ya wuce da su.
Ba su yi wata tafiya mai mugun nisa ba suka ƙarasa, ta miƙa wa mai adaidaita sahu
É—ari biyun don ya É—auki kuÉ—insa. Ya ce mata ta je kawai, bayan ta yi masa godiya ta
nufi layin da shagon ɗinkin su Kabir yake. Tana gab da ƙarasawa shagon, ta ga wani
ya fito daga ciki da mukulli yana shirin rifewa.

"Assalamu alaikum."

Fauziya ta yi masa sallama, mutumin ya amsa mata yana saka mukullin ƙofar.
"Don Allah Kabir fa?"
Kallon tsaf ya yi mata, yanayinta ya ga ba ta yi kama da masu karɓar ɗinki ba. Kuma
koda ɗinkin za ta karɓa, tana mace har sha biyu saura yana ganin dare ya yi.
"Hajiya lafiya?"

Fauziya ta dafa bango a gajiye ta ce, "Matarsa ce."
Sai a lokacin mutumin ya É—an faÉ—aÉ—a fara'arsa.

"Ah Allah sarki, ai ban gane ki ba. Wallahi Kabir ya fita tun bayan sallar isha'i,
ni kaÉ—ai na rage a shagon ni ma yanzu zan tashi."
Wani abu ya tsaya a zuciyar Fauziya, amma don kar ya fahimci wani abu sai ta saki
fuska ta ce, "To shi kenan na gode."

Kamar ta karɓi aron kuɗi a wurin mutumin, sai kuma ta haƙura. Don ba ta san duk
wani abu da zai taɓa mutumci, da martabar Kabir. Kemis ɗin da ta hango a farkon
shigowarta layin ta nufa, ta sake zaro ƙaramar wayarta ta latsa lambar Kabir ko
Allah zai sa ta shiga.
Bugun farko ta ji an É—auka, don haka ta yi saurin faÉ—in. "Hello."

Ita ma sai ta ji an ce hello da muryar mace, amma sai ta yi tunanin ko network ne
ya maimaita abin da ta faÉ—a.
"Abban Na'ima kana jina?"
Daga can ɓangaren ta ji an ja dogon tsaki an kashe. Dam! Gabanta ya yi wani
mummunan bugawa, wanda ya sa juya ta fara zabarin ƙafafuwanta har take yunƙurin
wurgar da ita.
Da sauri ta sake latsa lambar amma sai ta ji ta a kashe, haka kawai ta ji
zuciyarta tana yi mata wasu-wasin ko kuskuren lamba ta kira. Kamar wacce take bitar
hadda, haka ta fara karanta lambar Kabir a fili tana saka wa a cikin wayarta. Ta
sake latsa lambar ta kira saboda ta fita daga kokonton da take yi, amma sai ta ga
duk lamba É—aya ce da wacce ta kira da farko.
Wani irin abu ta ji ya tokare mata maƙoshi da ƙirji, ta haɗiyi yawu mai ɗaci har
ta ƙarasa shagon mai Kemis ɗin da yake ƙoƙarin rufewa. Da sauri ta ƙarasa ƙofar
shagon tana faÉ—in.

"Don Allah ka taimaka ka duba yarinyata kafin ka rufe, wallahi kunama ce ta harbe
ta."

Tausayinta ne ya kama shi, ya zare kwaɗon ƙofar ya koma ciki. Saboda tsabar
gajiya, da ƙyar ta iya sauko Fatima ta miƙa masa. Bayanin abin da ya faru ta yi
masa, sannan ya yi wa Fatima allurai. Ya É—ebo magunguna ya yi mata bayanin yadda za
a ta dinga ba ta, jiki a sanyaye Fauziya ta ce.

"To nawa ne kuÉ—in?"

Sai da ya sake duba magungunan ya ce, "Hajiya gabaÉ—aya kuÉ—inki dubu huÉ—u da É—ari
biyar." Kirjin Fauziya ya buga, ta dubi wayarta da ko dubu huÉ—u ba za a saye ta ba
ta ce.

"Don girman Allah ka yi mini wata alfarma, don Allah ka yi mini haƙuri zuwa gobe
da safe. Yanzu haka shagon mahaifinta na zo ba ya nan, wallahi É—ari biyu ce kawai a
hannuna."
Cike da takaici yake wurga mata wani kallo, ya furta.
"Haba Hajiya, yanzu ni kin yi mini adalci kenan? Tun farko ai da sai ki ce mini
ba ki da kuÉ—i, ni ma fa ba shagona ba ne. Yanzu idan Oga ya zo me zan ce masa? Kin
san dai gari ba gaskiya, magana ta Allah ba zan iya ba ki kayan dubu huÉ—u da wani
abu ki tafi da su ba."
Wayar hannunta ta miƙa masa ta ce, "Na san ban kyauta ba, amma don Allah ka yi
haƙuri. Ga wayata ka riƙe, zuwa gobe In Shaa Allahu zan kawo maka cikon kuɗin..."

"A'a gaskiya, ba zan karɓi wayarki ba. Zan dai karɓi magungunan, ki je gobe da
safen sai ki kawo kuÉ—in. Idan ma ba ki dawo ba, ni a aljihuna na biya kuÉ—in allurar
da na yi mata."
Mai kemis ɗin ya katse ta yana kwashe magungunansa, sannan ya miƙe mata wayarta
ya ƙoƙarin fitowa daga ciki. Duk yadda Fauziya ta kai ga roƙonsa fir ya ƙi
amincewa, saboda ya jaddada mata shi ma ba shagonsa ba ne. Idan aka samu matsala a
aljihunsa yake ciko.

A wannan karon ma haka ta dinga tafiya a ƙafa, sai dai wannan lokacin har ta
ƙarasa gida ba ta samu adaidaita sahu ba. Sai tsirarun motocin gida da suke kai
kawo a titi. Ta ci sa'a kamar yadda ta janyo ƙofar haka ta same ta, ta yi mamaki
sosai da har sha biyu da kusan rabi amma Kabir bai dawo ba. Ba yau Kabir ya saba
kai dare da sunan yana shago ba, amma bai taɓa haure sha biyun da rabi na dare a
waje ba. Wannan ne ya sake tabbatar mata da zarginta.

"An ya Kabir É—ina zai iya zuwa wurin wata mace a tsohon daren nan?" Ta furta
tana sake tuna muryar wacce ta É—auki wayar.
"Kabir É—ina babu macen da take gabansa."
Fauziya ta faɗa tana girgiza kanta. Da haka ta miƙe ta sake yi wa su Na'ima
shimfiÉ—a a tsakar É—aki, ta kwantar da su don ta samu Fatima ta tsagaita da kukan.

Bugun ƙofarsa ta ji, ta ji wani ɓacin rai ya lulluɓe ta. Kamar ba za ta tashi
ba, tuna gidan ba su kaɗai ba ne ya sa ta yunƙura ta fita ta buɗe masa. Saboda
haushinsa da take ji, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce ciki.
Suna shiga É—aki ta É—ebo kayan abincinsa ta ajiye ba tare da ta tanka masa ba.
"Ummu banat lafiya kuwa? Na ga kamar ba yadda na saba ganinki ba."

Kamar tana jira a ƙule ta ce, "Ta ya za ga gan ni dama? Bayan kana can wurin
'yanmatanka, yanzu Abban Na'ima cin mutumcin da wulaƙancin har ya kai ka tafi wurin
wata har na kira ka ba ta waya." Idanunta suka ciko da hawaye tana jin wani maƙaƙi
a cikin zuciyarta.
"Ai duk wulaƙancin da za ka yi mini ban cancanci haka daga gare ka ba, amma babu
komai akwai Allah." Ta ƙarasa maganar cikin shasshekar kuka.

"Innalillah wa inna'ilaihir raji'un! Yanzu ni kike zargi Fauziya? Ni Kabir É—inki
kike zargi da yawon gidan 'yanmata? Yanzu ko wani ne ya jefe ni da waÉ—annan
kalaman, ashe ba za ki iya wanke ni ta hanyar shaidata ba?"
Shiru Fauziya ta yi tana mamakin kalamansa, tana kallon rainin hankalin da yake
shirin yi mata. Ita kanta da wani ne ya sanar da ita abin da ta ji a lokacin, ba za
ta taɓa yarda ba.

"Kana nufin wacce ta yi mini tsaki É—azu ba ka santa ba? Ko kana nufin ba wayarka
ba ce? Don Allah Abban Na'ima kada ka mayar da ni wacce ba ta san me take yi ba."

Kabir ya sake marairaice murya ya ce, "Haba Fauziya, mene ne nawa ba ki sani ba?
Kina tsammanin akwai wata mace da zan ɓata lokacina a kanta? Wallahi abin da kike
faɗa ban san shi ba. Haba Fauzeena, yau fa da farinciki na ƙaraso gida saboda 'yan
canjin da na samo."
Ya yi maganar yana sakin murmushi ya cigaba da cewa.
"Wallahi yau aiki ne ya sha mini kai, mun jima ba mu yi É—inki irin na yau ba."

Girgiza kai Fauziya ta yi tana jin ɗaci a ranta, a ɓangare ɗaya tsoron Kabir ya
fara kama ta saboda ita da Kabir ba sa ɓoyewa junansu komai.
"Abban Na'ima yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki? Yaushe ka fara yi
mini ƙarya?"

Ƙirjin Kabir ya buga da ƙarfi yana shirin yin magana ta katse shi.
"Ko minti talatin ban yi da baro shagonku ba, kuma an tabbatar mini da tun bayan
sallar Isha'i ka bar shagon. Ashe kullum ninke ni kake yi? Ina nan yashe da baki
ban sani ba."

"To ai fitar da na yi daga shagon gidan Alhaji Musa na je, kaya na kai wa
iyalinsa kin san duk cikin shagonmu ya fi yarda da ƙwarewa ta. To lokacin da na je
ƙofar gidan na kira wayarsa a kashe. Da na ce a yi mini sallama da shi, sai yaran
gidan suka ce yana ganawa da wasu abokan kasuwancinsa, sai dai da na jira su
kammala. Ganin zaman ya yi yawa ya sa na bayar da wayata aka jona mini caji a
gidan, lokacin da Alhaji ya sallame ni har na kusa zuwa gida, na tuna na bar wayata
a gidan shi ya sa na koma na karɓo." Kabir ya janyo ledojin da ya shiga da su ya
ce.

"Ki dubi wannan sayayyar da na yi, duk da kuÉ—in da Alhaji ya biya ni ne. Wannan
shinkafar kwano É—aya ce, ga taliya da makaroni guda bibbiyu sai wake kwata da na
ƙaro mana." Ya sake buɗe ɗayar ledar ya ce.

"Wanna kuma fulawa ce kwano É—aya, ga sabulun wanka da omo dama na ji kin ce za ki
yi wanki. Sai biskit da alawar yara." Sai ya sakar mata murmushi ya miƙa mata wata
ledar ya ce, "Ga shi har tsire na sayo mana mu da yara, kin ga da safe sai mu sha
da shayi tun da har madara na sayo."
Har a ranta ta ji daÉ—i, domin duk halin Kabir mutum ne da ya tsayu a kan ciyar da
iyalinsa. Shi ba mai ƙarfi ba ne, amma indai a ɓangaren ciyarwa ne ko wani mai
kuÉ—in ba zai nuna masa komai ba. Amma haka kawai ta ji zuciyarta ba ta aminta da
abin da ya faÉ—a mata ba, duk da ta ji kaso mafi yawa na daga damuwarta ta yaye.

"Ina jin a cikin gidan Alhaji ne aka É—auki wayar da kika kira, amma kin san babu
wata mace da zan ɓa ta lokacina a kanta. Haba Fauzeen KB, har kya kawo wani abu ki
sa a ranki don Allah?"
Jin sunan da ya faÉ—a mata ya sa ta saki murmushi, nan take ta aminta da shi.
Ganin ya shawo kanta sai ya miƙe ya sauya kaya, ya zura jallabiyarsa ya ɗauki
ƙatuwar butar da ke cike da ruwa ya ce.
"Bari na watsa ruwa wannan zafin ya yi yawa."
Har zai fita ta katse shi.

"Yau fa kunama ce ta harbi Fatima a ƙafa."

Da sauri ya juyo ya ce, "Garin ya ya?" Ya ƙarasa tambayar yana duba ƙafar da
Fauziya ta haska masa. A nan ta sanar da shi duk yadda suka yi da mai Kemis, ya É—an
yi jim ya ce.

"Wallahi ciki da waje dubu ashirin ne suka rage mini, nake son na adana ta na
samu cikon dubu goma sha biyar na haɗa. Domin na sayi ƙofar da za a saka mana a
ginin can. Ko ba mu samu ta ɗakuna ba sai mu yi haƙuri zuwa wani lokaci."
Sai ya É—an yi jim ya ce, "Amma daga wurinki babu wani abu da za a samu?"

"Wallahi babu Abban Na'ima, sai dai zuwa gobe Dillaliya za ta zo mu ji nawa za ta
yi wa firjin nan kuÉ—i, ni babban tashin hankalina wa'adin kwanakin nan da suke
ƙaratowa. Tun da yau saura wata guda cif, kuma na tabbata Alhaji Mudi ba zai taɓa
ɗaga mana ƙafa ba. Da ya zo ya yi mana korar kare gara na sayar da firjin, a yi
abin da ba ya rage mu koma. Tun da ba wutar nepa muke samu ba, ka ga yafi ajiyar da
ake yi da shi."
Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce, "Allah zai kawo mana É—auki, amma gaskiya ba
na son ki sayar da firjinki Fauziya. Ki bari dai mu ga yadda Allah zai yi da mu,
idan muka koma can wataƙila a dinga samun wuta sai ki yi sana'a da shi." Fauziya ta
gurgiza kai, "Kai fa ka ce mana ya ce ranar da notice ɗinmu ya ƙare duk wanda bai
tashi ba zai fitar masa da kayansa titi, tun da har muna da abin da za a É—aga a
sayar ɗin ya fi zaman wulaƙanci Abban Na'ima. Na gaji da gidan nan, na gaji da
zaman takurar da nake yi ni da 'ya'yana a ciki." Fauziya ta ƙarasa maganar tana jin
É—aci a ranta.

"To shi kenan Fauzina, amma dai aro zan karɓa idan Allah Ya hore na ba ki kuɗinki
ko jari kya ja."
Daga haka ya saka kai ya fice, ta bi bayansa da hararar wasa ta ce.
"Ko ba aro ba? Lallai Abban Na'ima."

Da yake hanyar banÉ—akin, da hanyar fita duka kusan hanya É—aya ce. Da sauri Kabir
ya yi soron gidan, ya latsa lambar Surry don tun bayan da ya baro wurinta ya saka
wayar a blacklist ta yadda ko ta kira shi ba za ta yi ringing ba idan ba shi ya
duba ya gani ba. Murya ciki-ciki ya ji ta É—auka tana faÉ—in.

"Na gode Kb har ni za ka yi blocking saboda ka koma gida, ai na gwada kiranka da
wani layin na ji ya shiga."
Kabir ya yi ƙasa da murya ya ce, "Kin san bala'in da kika kusa ɓallo mini kuwa?
Wai Sury dama bayan kin shiga gida da wayata matata ta kira kin É—auka? Gaskiya ban
ji daÉ—i ba kada ki sake yi mini haka."
Ganin ran Kabir ya ɓaci sai ta kwantar da murya cikin kissa ta shiga ba shi
haƙuri, da yake duk ba a nutsuwarsa yake ba sai ta fahimci haka.

"My Kb wai lafiya na ji muryarka haka? Kamar a tsorace kake?"

Kabir sai da ya ɗan leƙa don kar ataho bai ji ba ya ce, "Ke ina soron gidanmu fa,
yanzu haka wankan da kika jaza mini zan yi shi ne na raɓe a soro. Kin ga yanzu dai
sai da safe, kada ta ji ni shiru ta biyo bayana."

Har zai kashe ta shagwaɓe murya ta ce, "Baby don Allah kada ka fasa zuwa kai ni
ganin ginin da kake yi mini, ka san yadda na gama ba wa ƙawayena labarin gidan
kuwa? Gaskiya dole na yi bidiyo na nuna musu."
Kabir ya saki murmushi ya ce, "Haba love, ai tun da na yi miki alƙawari kin san ba
zan saɓa miki ba, yanzu dai ki yi bacci da tunanina..."
Motsin da ya ji a bayansa ya sa shi saurin waigawa, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi
sakamakon tozalin da ya yi da Fauziya.


07062062624
Ummou Aslam Bint Adam
[12/02, 21:42] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da
ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da
mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA BIYU

Irin kallon da take wurga masa, ya shi saurin sauke wayar daga kunne gabansa
yana faÉ—uwa. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, tana bin sa da kallon tuhuma. Duk da
ba ta ji wayar da yake yi ba, amma tana da tabbacin da mace yake yin wayar.
"Abban Na'ima wankan kenan?"
Fauziya ta furta murya babu walwala. Kallo É—aya za ka yi wa Kabir ka fahimci ba shi
da gaskiya, a É—an diririce ya ce.

"Wallahi wata amarya ce ta dame ni da kira, wai gobe É—aurin aure ban gama mata
É—inki ba."
A wannan karon ita kanta Fauziya ba ta aminta da shi ba, duk da a cikin duhu ne
amma hasken fitilar wayar ta fallasa sirrin zuciyarsa.
"Abban Na'ima!"
Ta furta kamar za ta yi kuka, saboda sauye-sauyen halayensa a kullum ƙara ba ta
tsoro suke yi.

"Abban Na'ima, yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki?"
Kabir da har lokacin ƙirjinsa yake bugawa, ya ɗago wayar da yake har lokacin bai
kashe ba ya ce.
"Ga ta ai ban kashe ba, kina iya yi mata magana Fauziya."
Kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta karɓi wayar. Saboda ta fahimci kamar akwai
abin da yake ɓoye mata.

"Hello!"

Fauziya ta furta cikin sanyin murya, daga can ɓangaren Sury ta amsa.
"Uwar gida sarautar mata!"

Kusan lokaci ɗaya zuciyoyin Kabir da na Fauziya suka buga da wani irin ƙarfi.

"Ban da abinki uwar gida, Oga ai ba na ki ba ne ke kaÉ—ai."
Maganar Sury ta katse su, nan take jikin Kabir ya É—auki karkarwa saboda ya yi
tsammanin Sury za ta rufa masa asiri. Fauziya tana shirin yin magana Sury ta cigaba
da magana.
"Idan kika riƙe Oga ke kaɗai mu costomers ina muka kama? Kin ga gobe ɗaurin
aurena, a haka ma sai magiya nake kada ya jirga ni, shi ya sa na kasa haƙuri na
kira yanzu na yi masa tuni."
A fili Fauziya ta sauka ajiyar zuciya ta ce, "Shi kenan, Allah Ya sanya alheri."

Sury ta amsa da Amin, sannan ta katse wayar. Butar ya É—auka ya wuce banÉ—aki, ita
kuma Fauziya ta wuce É—aki duk sai ta

Please Login or Register in order to submit comment