Reading NAUSHIN WUTA by AMEERA ADAM Chapter 10 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya isa ban yafe maka ba, kuma wallahi indai ni ce ba zan taɓa komawa
yadda nake a baya ba."

Nazir bai kula ta ba ya fita, kai tsaye cikin store ɗin ta ya shiga. Ya ɗauko
wani ƙaramin mukulli ya rufe shi, sannan ya ɗauke ƙaramar wayar Maimuna da ke falo
ya koma ɗakin.
Duk abin da yake yi tana jin sa, don ba sabon abu ba ne idan sun yi faɗa ya rife
store ɗinta na kayan abinci. Sai dai kullum idan zai fita ya ɗebo mata wanda za ta
dafa. Fulo ta ga ya ɗauka ya tafi falo, ta taɓe baki tana nuna ko a jikinta. Don ta
sake ɓa ta masa rai sai ta furta.
"Ko a jikina, wai an tsikari kakkaura."
Ta gyara kwanciyarta, tana ayyana irin abin da za ta yi wa Nazir don ta huce
takaicin marin da ya yi mata.

GIDAN INNA
Tun bayan fitar Sadiya gidan Inna ya kacame da iface-ifacen kukan yaranta,
Inna ban da kyara da hantararsu ba abin da take yi. Fauziya ce ta janyo su ta
rarrashe su, da ƙyar Zainabu ta ta yi shiru. Zazzaɓi ne ya rufe Fauziya, saboda duk
cikin matan 'yan'uwan Kabiru Sadiya ce ta hannun damanta, suna ba wa junansu
shawara musamman da ya kasance Sadiya ba ta da kowa a garin. Sai su rufe su binne
ba tare da wani ya ji labari ba, domin dama Kabir da Yaya Nura sune masu ƙaramin
ƙarfi. Gudun raini ne ya sa su Fauziya suka kama kansu, don haka ma ya sa matan su
Yaya Tasi'u ko gidansu ba sa zuwa.
Abincin kari Fauziya ta haɗa gabaɗaya har yaran Sadiya, bayan ta gama ta zuba wa
yaran. Suka fara ci, sai dai ta lura har lokacin sun gagara sakin jikinsu.
Kabir kafin ya tafi sai da ya kira Mai adaidaita sahu ya fita da keken ɗinkin
Fauziya, kai tsaye shagonsu ya wuce da shi. Ya yi sa'a Ogansu yana nan, yana
ganinsa ya washe baki ya ce.

"Allah Ya taimaki Oga"

Oga ya faɗaɗa fara'arsa ya ce, "Kb namu."

Janyo keken ɗinki ya fara yi har ya samu ya shigar da shi cikin shagon, sai ya ce,
"Oga ya ka ga keken? Ay na faɗa maka sabo ne bai ji jiki ba."
Tasowa ya yi daga mazauninsa ya sake leƙa keken ya ce, "Gaskiya ne kuma na ga
butterfly ne. A ajiye shi a gefe, zan sa a yi masa service sai ku cigaba da amfani
da shi."
Kabir ya matsar da keken ciki, sai kuma ya saki murmushi ya ce.
"To Oga cittar fa?"

"Idan za ka tafi an jima ka yi mini magana, zan ba ka rabin, rabin kuɗin kuma sai
zuwa nan da rana ita uku."
Ba haka Kabir ya so ba, ya so ace duka kuɗin ya samu. Amma duk da haka ya san
idan ya karɓi kuɗin, za su cika a haɗa a kai gidansu Surayya.

Tun daga wannan ranar zaman Fauziya da Inna ya fara ɗaukan sabon salo, sai dai
Fauziya tana bakin ƙoƙarinta don ganin wani abu bai haɗo su ba. Duk safiya idan ta
yi abinci tana bakin ƙoƙarinta, don ta ga ta ba wa su Zainabu abinci ko yaya ne duk
da ciyarwarsu ta koma hannun Inna kacokam.
Kwana biyu da tafiyar Sadiya, har gida Yaya Tas'u ya zo ya ƙarewa Yaya Nura faɗa
a kan sakin da ya yi wa Sadiya. Don wani lokacin idan suka yi faɗa tana zuwa ta kai
ƙararsa wurinsa, shi kuma sai ya je ya yi masa faɗa. Idan aka yi haka sai Sadiya ta
samu sassaucin rashin mutumcinsa, bayan kwana biyu kuma ya ɗora daga inda ya tsaya.

Duk aikin da Sadiya take yi wa Inno sannu a hankali ya dinga dawowa kan Fauziya,
lokaci ɗaya ta yi wani irin duhu ga rashin hutu daga wannan sai wannan. Murmurewar
jegon da ta yi duk sai ta zuge, a ɓangare ɗaya ga tunanin halin da gininsu yake
ciki. Saboda halayen Kabir sun dawo mata sababbi, don tana yi masa magana yake rufe
ta da faɗa. Idan Inna ta jiyo sai ta ƙarasa bakin ƙofa ita ma ta cigaba da tofa
albarkacin bakinta.
Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali, bai wuce yadda ta lura da take-taken
Inna tana son fara ɗora wa su Na'ima talla ba. Duk da ba ta fito ta faɗa ba, amma
ta lura da yanayin shaguɓen da take yi. Hakan ne ya sa ta shiga takura wa Kabir a
kan ya saka su a makaranta, amma sai dai ya ce mata ba shi da kuɗi. Kuma ta rasa
wurin da yake zuwa, a kullum ya dawo gida da wuri haka zai buga wankan ƙananan kaya
ko manya ya fice daga gidan. Wani lokacin ma sai ta yi bacci yake dawowa, saboda
gajiya ta sa ana yin sallar Isha'i take yin bacci.
Watarana suna zaune bayan magriba yana tsaka da shiri ta ce.

"Abban Na'ima!"

"Ina jin ki."

Ya amsa mata yana saka belt ɗin wandonsa.

"Wai kasuwar ɗinkin ce yanzu ba a samu ko yaya? Zaman yaran nan babu makaranta
baya zai mayar da su, don Allah ko Islamiya ce ka saka su."
Sai da ya ƙarasa komai sannan ya ce, "Islamiyyar ma ai ba kyauta ake zuwa ba, ki
bari idan na samu kuɗi zan saka su. Kin san dai yadda abubuwa suke ƙara tsada."
Saboda takaici ba ta tanka masa ba, ya gama shiryawa yana fesa turare, a daidai
lokacin wayarsa ta kawo haske da yake a silent take. Da sauri ya ɗauke wayar ya
saka a aljihu har zai fita Fauziya ta ce, "Abban Na'ima ni fa ban gane wannan shige
da ficen nan da kake yi ba. Ina za ka je ne da daren nan?"

"Haifata kika yi da za ki tsare ni da tambaya, ina ruwanki da wurin da za ni? Kin
san dai yanzu na daina shaye-shaye ballanta ki kafa mini zargi."
Sai kawai ya saka kai ya fice daga ɗakin, shiru Fauziya ta yi tana nazari.
"Tabbas ruwa ba ya tsami banza, wallahi akwai abin da Abban Na'ima yake
ƙullawa." Ta faɗa a sanyaye, tana jin nadamar ba shi kekenta. Saboda ta san da ko
da kuɗin gyaran da take yi ne za ta iya samu ta biya musu kuɗin makaranta, a nan
take tunani ya faɗo mata a kan ta fara yin wankau tun da yanzu Sadiya ba ta nan.
Sai kuma ta ga sam ba za ta iya wankau ba, don wani lokacin ko wankin yaranta ta yi
wuni take bayanta yana ciwo. Sai kuma dabara ta faɗo mata a kan ta fara yin kitso,
da wannan shawarar ta bar wa zuciyarta a kan idan gari ya waye za ta shiga maƙota
duk ta faɗa musu.

Kabir yana fita daga gidan ya ciro wayarsa ya latsa lambar Surayya yana faɗin,
"Na fito fa baby."
Surayya ta akashe murya ta ce, "Tun ɗazu fa nake ciki da muradin son ganinka
gwarzona."
Amsa mata ya yi sannan ya kashe wayar. Adaidaita sahu ya tara kai tsaye ya wuce
unguwarsu Surry, waya ya ciro ya kira ta sannan ta fito. Kamar kullum idan za su yi
zance a soron gidan suke yi, hakan ce ta sa yanzu ma ta shimfiɗa musu dadduma a
soro.
Rungumo Surayya ya yi, ita kuma ta kamo bakinsa ta fara sakar masa kiss. Nan take
Kabir ya fara birkice mata, ya shiga kai hannunsa cikin sassan jikinta. Jingina
suka yi da bango, ita ma Surry ta fara sarrafa shi da hannunta tamkar ƙwararriyar
matar aure.

"Baby na gaji fa!"
Kabir ya furta cikin wani irin yanayi.
"Kamar yau ne fa, ba yanzu saura wata goma ba. Ni fa ba don 'yan gidanmu ba, da
ko ba lefe tsaf za a sha biki. Don tun lokacin da aka tsayar da rana na so a saka
wata shida."

Janye kansa ya yi daga cikin ƙirjinta ya ɗago yana kai hannunsa ciki jikinta
sannan ya ce, "Amma kafin lokacin me ya sa ba za ki ɗan dinga rage mini zafi ba
dear?"

Surry don ta zolaye shi sai ta ce, "Ba kana da mata ba, ya kake abu kamar wanda
bai taɓa aure ba."

"Mtswww."
Ta ji Kabir ya ja dogon tsaki sannan ya ce, "Ana maganar matan da suka cika
cikakkun mata, kina sako mini zancan waccan abar. Don Allah ki taimaka mu dinga
zuwa gidan can kina yi mini dabaru." Wani irin daɗi Surry ta ji, saboda ta jima da
fahimtar matarsa ba komai ba ce a wurinsa. Ta sake maƙale shi ta ce.
"Shi kenan my love, zan yi ƙoƙari na dinga yi wa su Yaya dabarar fita, kasan tun
da aka saka ranarmu yake saka mini ido sosai."
Sake haɗe bakinsu Kabir ya yi sai da suka ji alamar motsin za a fito, da sauri ya
sake ta yana sauke numfashi, Surry ta wayance da cewa.

"Hasko nan mu ga ko can azurfar taka ta yi."

Wayarsa ya zaro ya fara haska mata, kamar masu neman azurfar gaske. Suna cikin
haka Yaya Umar ya yi musu sallama ya fita daga gidan. Ya so sake yamutsa Surry ta
nuna masa ya yi haƙuri za ta dinga zuwa can gidan, saboda tana tsoron kada yayanta
ya sake dawowa ya kama su.

Cike da kewar Surry Kabir ya fito daga soron gidan, yana fitowa babu jimawa ya
zaro wayarsa. Misscall ɗin Farha ya gani har sau uku, ya latsa layin nata yana
karawa a kunne ya ce.
"Ina fatan sarauniya ba ta yi fushi da ni da."

"Idan na yi ma ai ka saba kanainaye zuciyata har ta yi maka afuwa."
Farha ta furta cikin shagwaɓa. Murmushi ya yi yana jinjina baiwar da yake da ita.
Kabir irin mazan nan ne masu iya tsara zance da kanainaye zuciyar 'yanmata. Ya
ƙwarai sosai wurin iya yaudara da kife mace, kuma yana ɗaya daga cikin maza masu
kule-kule da ƙoƙarin dandanlar arzikin jikin budurwa.

"To yanzu dai ayi mini afuwa cajina ya ƙare, zan kira ki da asuba. Ina fatan za
ki yi bacci da ni a zuciyarki."
Kafin su yi sallama sai da suka yi musayar kalaman soyayya sannan ya katse.
Lokacin da ya ƙarasa gida tuni Fauziya ta yi bacci, don haka ya ɗauki buta ya
faɗa banɗaki ya tsarkake jikinsa sannan ya koma ɗaki.

Sannu a hankali haka rayuwa ta cigaba da tafiya watanni suna shuɗewa, Fauziya ta
fara kitso babu laifi tana samun ɗan kuɗin kashewa. Da kanta ta saka yaran a wata
makaranta da ake yi boko da Islamiyya, sai dai duk da hakan ba su tsira ba sai da
Inna ta fara ɗora musu tallar barkono ranar Alhamis da Juma'a. Tun Fauziya tana
kara har ta gagara haƙuri ta yi wa Inna magana, a lokacin faɗa ta rife ta da shi
amma da shi ma Kabir ya nuna yaransa ba za su yi talla ba sai ta kawo ido ta saka
masa. Fauziya da karanbami har magana ta yi a kan su Salim, a nan ne Inna ta ce
daga Kabir har ita ba su isa ba matuƙar ba mahaifinsu ne ya hana ba. Wannan dalilin
ne ya ja wa Fauziya da yaranta baƙin jini a wurin Inna, ko fita suka yi tsakar gida
wasa ta dinga zaginsu tana hantarasu wani lokacin har da duka.
Daga ɓangaren Kabir shi ma zamansa da ita tuni ya sauya salo, don babu abin da
za ta yi masa haka kawai zai ɗauki fushi da ita. Ko kuma magana kaɗan za ta yi masa
sai ya rufe ta da faɗa, daga haka ma sai ya ƙaurace mata. Domin a zaman da suke yi
sun tafi kusan wata biyu ba tare da wani abu ya gifta a tsakaninsu ba.

Ana cikin haka watarana Kabir ya dawo da daddare a lokacin sha ɗaya saura, a zaune
ya samu Fauziya ta yi shiru tana nazari. Tsakin da ya ja ne ya sa ta ɗago tana
kallonsa, karaf idonta ya sauka a kan damɓareren jambakin da ke gaban rigarsa har
zuwa leɓensa. Ta haɗiyi wani irin yawun takaici, amma ba ta tanka masa. Kamar yadda
ta yi tsammani, buta ta ga ya ɗauka ya tafi banɗaki. Ba tun ranar ba, dama ta lura
da shi kusan kullum idan ya dawo ya yi wanka ya fita, to bayan ya sake dawowa daga
yawonsa sai ta ji ya ɗebi ruwa yana wanka. Ya tafi banɗaki ba jimawa ta ji kira ya
shigo wayarsa, a kan windo ta hango wayar jikinta har rawa yake ta saka hannu ta
ɗauka. Wannan ce rana ta farko da zuciya ta ingizata a kan ta ɗauki wayarsa,
ƙirjinta yana bugu ta ɗauki kiran da ta ga an ributa 'Sec wf' Ɗauka ta yi sai ta yi
shiru daga can ɓangaren ta ji an ce.

"Baby don Allah idan za ka yi wanka ka turo mini hoton lovely ɗina, ni ma na turo
maka ina wanka ka duba whatsapp ɗinka."
Da sauri Fauziya ta katse, ta ci sa'a wayar babu key tana duba whtaspp ta ga
sakon lambar da aka kira.
Ƙazantaccan hotun surorin jikin Surry ne, sai ta yi sama a nan ta ci karo da
hotunan al'aurar Kabir ya tura mata hotuna. Sai kuma wasu hotuna da ta gansu
rungume da juna hannun Kabir yana saman ƙirjin Surry. A yadda ta gani babu riga a
jikinsa, ta ga kuma ita ma Surayyan ko ɗankwali babu a kanta. Amma sai ta lura
wurin da suke kamar ba gida ba ne.

"Innalilla wa Inna ilahir raji'un."

Fauziya ta furta tana jin kanta yana sarawa, idabunta suka fara ganin dishi-dashi.
Ɗakin da take ciki ta ga ya fara juya mata.

GIDANSU MAIMUNA
Saboda fushin da Nazir yake yi da Maimuna ya sa koda gari ya waye bai bi ta
kanta ba, wanka kawai ya yi ya ɗebo shinkafa kofi huɗu ya tsiyayo mai wata 'yar
roba ya ajiye mata sannan ya fice kasuwa. Maimuna tana kallonsa duk abin da yake yi
har ya fita, da yake a lokacin tuni yaranta sun tafi makaranta, wanka ita ma ta
shiga ta tsala a banɗaki. Bayan ta fito ta zaro wayarta ta ga misscall ɗin Jafar,
goge hannunta ta yi za ta kira ta ga wani kiran ya sake shigowa. Tana ɗauka cikin
zumuɗi ya ce.

"Baby ke fa nake jira."

Murmushi Maimuna ta yi ta ce, "Na gama komai kayana zan saka." Katse kiran ya yi.
Maimuna ta jima a gaban drower kayanta, sai ta ɗauko wasu figaggun ƙananan kaya ta
saka, ta zaro zumbulelen hijabinta ta zura. Ƙaramar wayarta ta gani Nazir ya
mantata a falo, don ta tabbatar da ya yi nisa da gida sai ta kira shi. Har ta kusa
katsewa sannan ya ɗauka.

"Ina jinki."

"Na ga ka ajiye mana shinkafa, har dare ko iya rana."
Ta furta tana sauraron yanayin wurin da yake. Daga cikin wayar ta ji alamar yana
cikin kasuwa, don ta ji ana tambayarsa hula lamba ashirin (Size 20).

"Har dare za ku dafa."

Ya ba ta amsa a zafafe yana katse wayar. Tsalle ta buga sannan ta ɗauko mukulli ta
rufe gidanta, kamar yadda Jafar ya ce zai bar mata gidan a buɗe haka ta same shi.
Duk da ta san Maman Nana ba ta nan, haka kawai ta ji gabanta yana faɗuwa. Tana
shiga ciki ta hango shi daga shi sai gajeren wando, da sauri ya ƙarasa ya rungume
ta yana zame hijabin jikinta. Wata irin kunyarsa Maimuna ta ji ta sunne kanta ƙasa,
shi kuwa ya shiga laluben jikinta kamar waɗanda suka jima da sanin juna. A kan
gadon Maman Nana suka yada zango, Jafar ya shiga rage mata kayan jikinta har ya
raba ta da su gabaɗaya, ya shiga gwaɗa mata zafaffiyar soyayya. Abin da ya birge
ta, ya kuma ba ta mamaki yadda ta ga Jafar ba ƙyamar komai na jikinta. Abin da
Nazir bai taɓa yi mata ba, don shi ko kiss bai damu da ya yi wa mace ba. Sai da
Maimuna da Jafar suka gigita juna sannan komai ya wakana a tsakaninsu, cike da so
ya rungumo ta a jikinsa ya ce.
"Don Allah ki cigaba da ni haɗin kai zumata." Gyaɗa masa kai ta yi har lokacin
hannun Jafar yana cikin jikinta.

Bayan gari ya waye sai da Maman Nana suka ci abinci sannan ta yi musu wanka, ta
nufo hanyar gidanta. Mahaifinta ya yi mata nasiha sosai, ya sake tabbatar mata da
zai kira Jafar ya yi masa faɗa. Da yake ita ma tana da mukulli a hannunta, tana
zuwa bakin gate ta saka key ta buɗe jamlock ɗin. Ta yi mamaki da ta ga motarsa a
gida har lokacin, amma sai ta yi tsammanin ko lalacewa ta yi bai fita da ita. Don
haka ba ta yi wata-wata ba ta nausa kanta ciki, tun daga tsakar gida ta fara jiyo
sautin dariya da wasannin da suke yi a cikin banɗaki da ruwa suna wanka.


AlhamduLIllah a nan ƙarshen free pages ya ƙare, ba sai na tsaya bayanin irin
cakwakiyar da za a riska a gaba ba. Mai son cigaba zai biya kuɗin karatu 500 ta Acc
Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624
In Shaa Allah Jibi Asabar zan cigaba da posting a paid group

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment