Reading NAUSHIN WUTA by AMEERA ADAM Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kashe take,
amma riƙe ki yi blocking ɗinta da kanki. Dama ni ban taɓa kiranta ba, ita take
kirana amma tun da an yi haka babu ni babu ita. Munafuka haka kawai za ta haɗa ni
faɗa da iyalina ina zaman lafiya da ita."

Har a ranta ta ji daɗi, don haka ma ta ɗan saki fuskarta. Ta karɓi wayar ta saka
ta a blacklist, sannan ta ce.
"Abban Nana wallahi wannan ita ce ta farko ta ƙarshe, kada ka mata kwanaki ma
haka na yi yaƙi da kai a kan Fati wacce ka ce wai ƙanwar abokinka ce. Wa ya sani ma
ko ita ce wannan, wai yanzu duk irin kulawar da nake ba ka amma sai ka kula
'yanmata."
Maman Nana ta ƙarasa maganar cikin ɗacin rai.
"Don Allah ki daina dawo da bara bana, waccan ta wuce kuma wannan ma In Shaa Allahu
ta wuce ba zan sake ba." Ruwan wanka ta juye masa ta dawo ta ce, "Lokacin fitarka
yana tafiya ga ruwan wanka can na juye maka."

Yanayin da yake ciki na tunanin Maimuna ya sa shi janyo hannunta ya ce, "Wai kwana
biyu ba ki da lafiya na ga ko gayyatata ba kya yi!"
Murmushi ta yi masa ta ce, "Ai na ga ba ka dawowa da wuri ga gajiya shi ya sa."
Da yake ta kwantar da Abdul ya yi bacci, sai bayan da komai ya gifta a tsakaninsu
sannan suka faɗa toilet lokaci ɗaya. A gurguje ya shirya ya tafi kasuwa ganin har
sha biyu saura, Maman Nana ta cigaba da aiki cikin sauri tana alla-alla ta gama ta
leƙa gidan Maimuna.

Tun lokacin da Maman Nana ta fara magana, Maimuna ta yi shiru tana sauraronta.
Lokacin da ta ji Jafar ya ce zai kira layin Maman Nana ta zage ta, sai ta yi sauri
ta kashe wayar gabaɗaya. Haka kawai ta ji wani irin kishi ya rufe, ta shiga hango
irin rarrashin da Jafar zai mata. Domin Maman Nana ta sha ba wa Maimuna labarin
idan Jafar ya yi mata laifi, matuƙar shi ne ba shi da gaskiya har kusan tsugunna
mata yake yi.
Sai da Jafar ya shiga mota yana driving sannan ya kira Maimuna amma sai ya ji
ta a kashe, guntun tsaki ya saki ya ajiye wayar sannan ya cigaba da driving. Sai da
ya shiga cikin shagonsu yana duba wayarsa ya ga misscall ɗinta. Hannunsa har rawa
yake ya kira ta ya ce, "Wallahi Sumayya ta yi bala'in ba ni haushi, ina tsaka da
jin muryarki ta zo ta yi mini tsaye a ka." Ya yi maganar yana sakin tsaki.

"Hmmm bayan da ka gama ba ta haƙuri kenan, ai na san yadda kake bala'in jin
tsoronta."
Jafar ya saki dariya ya ce, "Kamar wani matsoraci, idan muka haɗu ai za ki gane ni
jarumin gaske ne "
Maimuna ta yi murmushi za ta yi magana ya katse ta.
"Yanzu dai ba wannan ba, na lura haɗuwa za ta yi mana wahala. Amma me zai hana na
saya miki babbar waya sai mu dinga chatting da ita, na fi so na dinga ganinki ina
jin daɗi ko na samu nutsuwa."

Shiru Maimuna ta yi ta ce, "Kana ganin ba za a samu matsala ba?"

"Matsalar me Moon? Ai kin ga wannan layin da muke waya babu wanda ya sanki da shi,
kuma ke ba kowa za ki yi wa magana ba sai ni. Ba sai mu dinga magana ba."

'Maimuna me kike shirin aikatawa ne? Wai ko kin manta kina da aure?'
Wata zuciyar ta raya mata a rai, sai ta ji sam zuciyarta ta mata babu daɗi.

"A gaskiya sai na yi nazari, sai an jima zan dafa wa yara abinci."

Jin sauyin muryarta ya sa shi saurin faɗin, "Lafiya My Moon, ko kina da wata
damuwar ne? Turon lambar asusunki sai na turo miki dubu ashirin ko kati ki saka."
Da sauri Maimuna ta ce, "Dubu ashirin fa?"

Jafar ya yi murmushi ganin kamar tarkonsa ya kama ta ya ce, "My moon, na rantse da
Allah, zan iya ɓatar da ko nawa ne a kan samun farincikinki. Idan ba za su ishe ki
ba, ki faɗa mini sai na ƙara miki."
Bugun ƙofar da Maimuna ta ji ana yi mata ya sa ta ce, "Ana buga ƙofa, zan turo
maka account number ina zuwa." Daga haka ta katse, tana zuwa gate da ta buɗe ta ga
Maman Nana ta shigo da alama ranta a ɓace yake.

Kabir yana idar da sallar magriba, bai tsayana ko ina ba sai ƙofar gidansu Sury.
Waya ya zaro ya kira ta, tana ɗauka ya ji muryarta a can ƙasa tana faɗin.

"Mu haɗu a bayan layinmu ta ɓangaren hannunka na dama, idan ka zagaya ka same ni
a bakin layin ƙarshe."

Kabir yana jin haka ya amsa mata sannan ya katse wayar, kwatancan da ta yi masa ya
bi. Yana zuwa a daidai wurin ya shiga waige-waige, daga bayansa ya ji ta ce.
"Lah bai gane matarsa ba."
Da sauri ya waiga, cikin mamaki yake bin ta da kallo.

"Wai baby ke ce?"
Sury ta saki murmushi ta ce, "To ya za a yi, ai idan hagu ta ƙi sai a koma dama.
Ƙarya na yi zan je dubiya, shi ya sa na ɓoye niƙab ina zuwa bayan layi na saka.
Yanzu dai mu yi sauri kada a ga na daɗe."

Kabir ya kanne mata ido ɗaya ya ce, "To shi kenan amaryar Kb, amma daga jiya zuwa
yau na yi kewarki."
Bakin titi suka ƙarasa ya tsayar musu adaidaita sahu, shi kansa ya ji daɗin yadda
Surayya ta ɓatar da kamanni. Domin har a cikin ransa yake fargabar wani ya gan shi,
kuma a yanzu kowaye ya gansu yana iya ce masa ƙanwarsa ce.
Tafiyar kusan minti ashirin suka yi, da yake sabuwar unguwa ce gidajen tsilli-
tsilli haka suke. Tun daga farkon layin Kabir ya ce mata.

"Ki jira a nan zan je na buɗe ƙofa na shiga, bayan wani lokaci zan taɓo ki a waya
sai ki biyo bayana. Kin san mutane da munafunci, ba za a rasa 'yan tsurku ba. Kina
miƙe layin nan da zan bi idan kika yi kwana gida na farko za ki ga ba fulasta
ƙofarsa ta langa-langa ce."
Sury ta amsa masa shi kuma ya yi gaba. Lokacin da Kabir ya shiga layin gidan babu
kowa a waje, don haka jikinsa har rawa yake ya latsa lambar Surayya ya ce mata ta
ƙaraso.

Yana nan tsaye ta ƙarasa ciki, kunna fitilar wayarta ta yi saboda duhu ta shiga
haske cikin gidan.
Ciki da falo ne guda ɗaya, sai fallan ɗaki da banɗaki a ciki. A gefe banɗaki ne
da kitchen sai ɗan ƙaramin tsakar gida. Kusan an gama komai, sai daɓe, fulasta,
fenti, ƙofafi da winduna su suka yi saura. Farinciki ya sa Sury ta rungume shi
tsam, tana faɗin.
"Gaskiya gida ya yi masoyina, amma kana ganin wannan ƙarashen zai iya kai wata
nawa ba a gama ba?"
Tun da ta rungume shi ya ji duk yanayin jikinsa ya canza, jikinsa a mace ya shiga
yawo da hannunsa a jikinta. Da wata irin murya ya ce, "Kin san samun namu lokaci-
lokaci ne, amma dai ina fatan har aurenmu ba zai haure shekara ba."
Ganin saƙon da take aika masa ya fara tasiri a jikinsa ya sa Sury ta cigaba shi
ma yana mayar mata da martani. Dogon hijabin jikinta ya zame mata, dama Surayya
kafin ta fito sai da ta faki idon mahaifiyarta ta zuro dogon wando da ƙaramar riga
a ciki, sannan ta zura zumbulelen hijabinta har ƙasa.

Duk zuwan da Kabir yake yi wurin Sury wani abu bai taɓa shiga tsakaninsu ba,
bayan rungume-rungume da shafe-shafen da suke yi wa juna. Don haka da ya ji Sury za
ta zo ganin gidansa, ya ci alwashin saninta a wannan ranar. Yana tsaka da yawo da
hannunsa a jikinsa, ya ci karo da abin da bai yi tsammani ba.
"Mene ne wannan?"

Kabir ya faɗa ransa a ɗan ɓace.

"Gabannin magriba period ɗina ya zo!"
Ta furta masa, don dama ta ƙi faɗa masa ne saboda kada ya fasa kawo ta. Domin ta
san matuƙar suka zo gidan ta san sai ya nemi koda taɓa wannan ɓangaren ne. Cikin
wata irin murya ya raɗa mata a kunne, "Yanzu ya za ki yi da ni?"
Murmushi ta sakar masa ta ce, "Dabarun mu na mata mana, ko ba ka san idan macen
aure tana wannan halin akwai dabarin da take yi ba?" Ya sani sarai, domin Fauziya
duk a halin da take ciki tana ƙoƙarin faranta masa. Amma shi sam ba haka ya so ba,
ita ma Sury ta fahimci haka amma ta basar. Babu kunya Surayya ta shiga sarrafa shi,
tamkar yadda macen aure take yi wa mijinta. Suna cikin wannan yanayin kiran Fauziya
ya shigo cikin wayarsa, kamar ba zai ɗauka ba tuna matsalar da aka samu a daren
jiya da ta je shagonsu aka ce ya fita da wuri, ya sa ya ɗauka don ya ji abin da za
ta faɗa masa.

"Hello!"

Daga can ɓangaren Fauziya ta ce, "Abi barka da yamma!"
Ya ɗan yi gyaran murya don ka da ta fahimci sauyinsa ya ce, "Barka dai Ummu
Banat, ya jikin?"
Ta amsa masa tana wurga masa tambaya.
"Amma ba ka shago ko? Na ji ban ji ƙarar ɗinki ba?"
Duk da ya san zai yi wuya Fauziya ta gane a inda yake, amma sai da ya ji gabansa
ya faɗi.
Ya janye jikinsa daga jikin Surayya yana faɗin, "Na'am eh na je karɓo wa oga
kayan ɗinki ne, ina zuwa an zo kaina za a sallame ni."
Daga haka ya katse, tun da ya fara waya Surayya take wurga masa harara tana
shirin yin magana ya ce.
"Ayi mini afuwa."
Juyar da kai gefe ta yi cikin fushi, ya shiga lallashinta sannan Surayya ta cigaba
da sarrafa shi. Sai da suka ɗauki lokaci a haka sannan Kabir ya samu nutsuwa, da
yake gidan akwai rijiya sai kawai ya ja ruwa da guga ya yi wanka da ita sannan suka
fito daga gida.


Ummou Aslam Bint Adam🌚
+2347062062624

[12/02, 22:24] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da
ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da
mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA HUƊU

Fauziya tana gama waya da Kabir ta tashi da sauri ta faɗa banɗaki ta sheƙa
wanka, bayan ta fito ta ciro wata doguwar riga ta saka. Jikin rigar roba ce, ba ta
da tsayi har ƙasa. Daga iya gwiwarta ta tsaya, ta ɗauko kum ta fara gyara gashinta.
Fauziya irin dogayen matan nan ne, sai dai tana da ɗan kauri. Tana da ƙira sosai
sai dai ba fara bace tas, tana dai da haske da kuma yalwar gashi. Faka gashinta ta
yi jelar ta sauka har gadon bayanta, ta ɗebi turarruka masu ɗaɗin ƙamshi ta feshe
jikinta da su. A gaban mudubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, su Na'ima sai
zagaye ta suke yi suna cewa ta yi kyau. Ita kanta ta san ta yi kyau, don haka take
ta ɗokin Kabir ya dawo ya ga kwalliyarta. Dafa tsohon cikin jikinta ta yi ta saki
murmushi, domin ta san Kabir mutum ne mai san ƙananan kaya. Jin kiran sallar Isha'i
ya sa ta saka zumbulelen hijabinta har ƙasa, ta tasa su Na'ima suka gudanar da
sallar Isha'i. Bayan sun idar sai da ta yi wa yaran tilawar Alƙur'ani, sannan ta
zuba musu abinci suka ci. Da suka gama suka ɗan yi wasa sannan ta yi musu shimfiɗa
a tsakar ɗaki, don ta ci alwashin duk zafi ta daina fitar da su waje.

Kabir da Sury tare suka tafi har unguwar su Surayya. Ita ta sauka ta wuce gida,
shi kuma ya wuce shagonsu. A lokacin da ya koma Ogansu ba ya nan, don haka shi ma
bai zauna ba ya fice daga shagon. A madadin ya wuce gida yana fitowa sai kiran
abokinsa Abbati ya shigo masa.
"Ya Abbati kana iya?"
Kabir ya furta bayan ya ɗauki wayar, daga can ɓangaren cikin muryar maye Abbati ya
ce, "Ga mu a majalisa, kai fa muke jira kwana biyu nan ba ma gane maka sai wani eh
yane kake yi wa mutane."

"Don Allah mijina ka daina wannan shaye-shayen, a yanzu matsayinka na uba ne.
Idan za ka yi sara, ka dinga lura da bakin gatari kana wasa shi. A yanzu da muke
rayuwa, kamata ya yi ka duƙufa a neman ciyar da mu halali ba shaye-shaye ba. Allah
Ya yi mana arzikin 'ya'ya mata, ina gudun kada watarana idan suka girma a dinga
goranta musu. Ka yi mini alƙawarin ba za ka sake shan komai ba Kbna."

Kabir ya tuna kalaman da Fauziya ta yi masa, bayan ya dawo hayyacinsa a ranar da
ya faɗa ɗakin A'ilo yana cikin maye. Murya a can ƙasa ya ce. "Ku sha kawai Abbati,
Fauziya ba ta san shaye-shayen da nake yi."

"Ɗan abin rage zafin shi ne za ka ce Fauziya ba ta so? Kai yanzu kana namiji
mace ce za ta zauna tana yi maka ƙabali da ba'adi? Haba bros kada ka bayar da maza
mana, don Allah ka taho muna jiranka."
Daga haka Abbati ya kashe, har zuciya ta ce masa ya yi tafiyarsa gida, sai kuma
wata ta ce ya je ya sha ko kaɗan ce. Saboda shi kansa kwana biyun da ya yi bai sha
ba, har jin sa yake yi wani iri. Don haka daga nan bakin ƙofar shagon ɗinkinsu ya
wuce bayan wata makarantar firamare, wacce iren-irensa suka laɓewa a lungunta suke
shaye-shaye. Kabir yana zama T-boy ya miƙa masa wata 'yar roba haɗe da da wata
baƙar leda, nan take Kabir ya fara shaƙa yana ɗaɗɗakar ruwan robar kafin wani
lokaci tuni ya yi wa kansa caji.

Jin shiru har ƙarfe goma da rabi Kabir bai shigo ya sa Fauziya ta ɗauki wayarta
ta latsa lambarsa. Sai dai wayar ta ƙari ringing har ta katse bai ɗauka ba, haka
kawai ta ji gabanta ya faɗi. Zuciya ta shiga raya mata ko dai Kabir yana wurin
shaye-shayen da ta hana shi, girgiza kanta ta yi cike da ƙwarin gwiwa ta ce.
"In Shaa Allah a wannan karon ba zai sake ba..."

Maganarta ce ta katse sakamakon jin mummunan bugun ƙofar da ake yi, wanda ya
gigitata saboda tsoro, firgici da tashin hankali.
"Fauziyataaaaaa! Fauzeeeee, zooo ga ni na zo."

Kalaman Kabir cikin maye suka doka sallama cikin dodon kunnenta, ba yau ta saba jin
haka daga gare shi ba. Amma a wannan ranar sai ta ji wani irin ɗaci, ɓacin rai da
baƙinciki ya mamaye ta. Ta kalli su Na'ima da ke kwance a ƙasa, haka kawai ta ji
tausayinsu a ya kamata. Hawaye ne bibbiyu suka fara zuba daga kwarmin idonta, tana
nan zaune ta sake jin ya buga ƙofar da ƙarfi yana cewa.

"Don Allah... kar ki min faɗa... ni babu abin da na shaaaa..."

Sanin halin mutanen gidansu ya sa ta yunƙura da ƙyar ta fita, inuwa ta gani a
bakin ƙofar Maman Sabir da alama a tsaye take tana leƙen ganin abin da zai faru.

"Ni fa... ba na shan... komai, Fauziyaaaaaa ko kin sha kin bugu ne... kika yi
bacci... ki zo ki buɗeeee."

Ta sake jin muryarsa a daidai lokacin da ta tura ƙofar gidan, tana buɗewa ya faɗo
jikinta da yake ya saki jikinsa a kan ƙofar. Hannu ta saka ta kare cikinta, tana
shaƙar ƙamshinsa ta ji yana wani irin warin hayaƙi.

"Fauzinaaaa."

Ya furta yana shafa fuskarta, takaici ne ya gama maƙure ta. Ta haɗiyi yawu mai
ɗaci ta dube shi tana jin kamar ta rufe shi da duka, a wannan ranar ji ta yi da ace
su kaɗai ne a gidan tana buɗe masa za ta bar shi a wurin. Idan ya ga dama ya shiga
ko ya kwana a nan, amma gudun kada ya shiga ɗakin matan aure ya sa ta kamo shi.
Suna tafe yana layi tana dafa bango, tana shiga tsakar gida ta hangi A'ilo da Maman
Sabir suna magana ƙasa-ƙasa. Duk da ba ta ji me suka faɗa ba, amma jikinta ya ba ta
maganarta da Kabir suke yi. Ta girgiza kanta cike da tausayin irin rayuwar da take
ciki, sannan suka shiga ɗaki. Suna ganin Fauziya ta shiga ɗaki suka saki shewa haɗe
da tafi A'ilo ta ce.

"Ke dai Maman Sabir a kullum maraɗinki ba ya kunya, wato yau kuma da haka kika
shigo. Sabon salo kiran salla da usur, ai gara haka da ki faɗa ɗakin da ba na ki
ba."
Maman Sabir da tuni ta fahimci zancan ta ce, "Ke kuwa ai dukan da kuka yi mini
ban ji da daɗi ba. Abin dariyar ma, baban Sabir tunkur yake zama bai yi bacci ba
yana jirana."
Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya.
Lawisa da take ɗaki take jin su kamar ba za ta tamka musu ba, sai kuma ta yi
zaraf ta leƙo ya ce.

"Sai ki yi takatsantsan kuwa, domin babu ruwan Ubangiji. Ba abin mamaki ba ne ki
ga Sabir ya gado ki. Ni ina fata da roƙon Ubangiji, tun da har fatan da kike yi wa
kanki kenan Ubangiji Ya sa Sabir ya gaji abin da kike yi wa izigili."
Tana faɗar haka ta koma ɗaki.

"Wallahi sai dai ki gani a kanki, aniyarki ta biki mai mugun baki."
Maman Sabir ta furta cike da tsoro.

Fauziya suna shiga ɗaki, bayan ta saka shi ya tsallake su Na'ima da ke kwance sai
kuwa ta sake shi rai a ɓaci. Daga gefen gadon ya faɗi, kansa ya bugu da katakon
gado. Cikin azaba ya runtse ido yana shafa wurin, takaici ya sa Fauziya ta zauna a
gefen gadon sai kawai ta fashe da kuka.

Sai da Maimuna ta tura ƙofar ta rufe sannan ta waigo tana bin bayan Maman Nana da
harara, ganin za ta waigo ya sa ta saki fuska cikin wayancewa ta ce.
"Uwar gida kuma amarya a gidan Baban Nana, ke kaɗai ki sha kurumki daga ke babu
ƙari."

Maman Nana ta saki guntun tsaki ta zauna a kan kujera, sai kuma Maimuna ta sha
jinin jikinta duk da Jafar ya tabbatar mata da ba ta gane da wacce yake wayar ba.
Amma sai ta ce, "Uwar Nana ko dai kin samo wa Abdul abokin wasa ne? Na gan ki duk a
sanyaye."

Maman Nana ta zaunar da Abdul da bai wuce shekara ɗaya ba ta ce, "Ni da wannan ne
ai da sauƙi, sai na saka shi ya ɗauko mini mai aiki ta dinga komai kamar lokacin da
na yi cikinsa."
Cikin bugar ciki Maimuna ta ce, "To! Me yake damunki?"

"Wallahi ban tabbatar namiji munafiki maci amana ba ne ba sai yau, wai har ni
Abban Nana zai munfurta?"
A razane Maimuna ta dube ta, tana shirin yin magana ta cigaba.

"Wai har ni zai dinga yin waya da budurwa a ɗaki? Tsabar wulaƙanci ya saka ni
aiki, ina can ina haƙilo ko yaro ya ƙi riƙe mini ashe soyayya zai sha. Wallahi ta
ci sa'a ban same ta a waya ba, da sai na ƙare wa kaf danginta zagin rashin mutumci.
Sai da na raini mijina yanzu kuma 'yan'iskan mata za su fara kawo mini hari,
wallahi duk yarinyar da ta yi gangancin auren mijina sai na lahantata." Ras! Ƙirjin
Maimuna ya buga, don ta san halin Maman Nana akwai ta da baƙin kishi. Amma duk
baƙin kishinta ba ta ji ko ɗar ɗin za ta iya rabuwa da Jafar ba. Dalilin haka ya sa
ta dafa ta ta ce.

"Gaskiya ni Abban Nana ma ya ba ni mamaki, saboda Allah duka shekararku nawa da
zai dinga wani kule-kulen 'yan'mata?" Maman Nana ta wara hannu tana taɓe baki
alamun kema dai taya ni gani, don Maminuna ta sake zuga ta sai ta ce.

"To ai ko ni me shekara goma da aure Nazir ba shi da budurwa, ina laifin ma ya
bari ku shekara ko sha biyar ne kin ga lokacin ke da yaranki kun samu jindadin da
kuka samu bakin gwargwado. Amma kina zaman zamanki a kwaso miki gayyar tsiya, gara
dai tun wuri ki san abin yi."

Ai kuwa nan take Maman Nana ta sake cika, rai a ɓace ta ce.
"Ai wallahi bari ya dawo, dama ai na faɗa masa sai ya kira mini budurwar idan ba
haka ba zai ga ɓacin raina."

Wani irin farinciki ya mamaye zuciyar Maimuna, saboda a yanzu babu abin da yake
damunta sama da ta ji Maman Nana ta ce suna cikin daɗi ita da Jafar. Ta sake taɓe
baki ta ce, "To ni ban da ma abin namiji, mace har mace kamar ki me zai yi da wata
kuma. Dirin nan bakin gwargwado kina da shi, gashin nan kina da na zaman falo. Ke
dai a fuska ba za ce miki mummuna ba, to don Allah me namiji yake so da ba ki da
shi."
Maman Nana ta yi caraf ta ce, "Jaraba fa irin ta namiji, ki duba ki ga irin
magungunan da ke ɗurawa cikina Maman Dija, ke kanki shaida ce saboda Abban Nana na
fara shafe-shafen man bilicin, tun da na lura yana leƙe-leƙen fararen 'yanmata."

'Ba dai leƙe ba, sai da faɗawa. Jafar ai ya yi nisan kiwo a kan alkyabbar mata.'
Maimuna ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce.

"A toh ga shi kina ƙoƙari a turaka ma na ji kin ce ba kya sanya, to wai da ba kin
ce har zauce miki yake ba?"

Maman Nana ta yi ƙwafa ta ce, "Yaushe rabo? Ni yanzu rabona ma da shi ai mun kusa
sati, Abban Nana da yake da jaraba wai shi ne har yake sha mini ƙamshi jiya. Ƙiri-
ƙiri mutumin nan ya ce mini ba shi da lafiya..."
"Sati fa Maman Nana? Ke kuwa kina me? A gaskiya ki dawo nutsuwarki, ni fa ba don
kar na faɗa ki ji haushi ba da na ce wani abu."
A zabure Maman Nana ta dafa Maimuna ta ce, "Faɗi mana, ni da ke ai kin san ba ma
haka."

"Astagafirullah ba wai zargi nake ba, sai na ga ko dai budurwar tashi ce ta
ɗauke masa hankali? Kin san fa 'yan'matan yanzu wallahi idonsu a buɗe yake, ba abin
da ba sa yi wa sauraye ke kina can yashe a baki suna harkarsu."

"Bantan uba! Ai kuwa sai yanzu kika kamo mini bakin zaren."
Maman Nana ta furta jikinta yana karkarwa, sannan ta cigaba.
"Ai kuwa zan saka ido a kansa, wallahi idan na gano wani abu a tsakaninsu sai an
maimaita yaƙin dunuya na biyu."
Maimuna ta cigaba da zuga ta, sai ta gama yi mata famfo sannan ta yi mata sallama
ta tafi. Tana fita Maimuna ta saki shewa, cike da ƙeta ta ce. "Sakarya wawiya marar
lissafi, in dai ni ce wallahi baƙinciki yanzu kika fara ƙunsa. Sai na raba ki da
jin daɗin, da kike hura wa 'yan unguwa hanci kina faɗar ke mowar miji ce."

Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[12/02, 23:08] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da
ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da
mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA BIYAR


UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳

Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda
habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta
ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai
musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan
kyauta tana kara soyayya

Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya
qualitatives via +234 816 916 8731


***

Maman Nana ta fita babu jimawa yaran Maimuna suka dawo daga makaranta,
hankalinta yana kan wayarta saboda so take Jafar ya turo mata kuɗin ta goge alert
ɗin. Sai

Please Login or Register in order to submit comment