Reading NAUSHIN WUTA by AMEERA ADAM Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji ba ta ji daɗin abin da ta yi masa ba.
Fauziya tana da kishi sosai a kan Kabir, sau tari sai ta yi wani abin sai kuma ta
ji ba ta kyauta ba.

"Allah ka rage mini raɗaɗi da zafin kishin bawan Allahn nan, ina tsoron kada
zuciya ta sa na fara zargin mijina." Ta furta a raunane.

Washegari tun da gari ya waye, Fauziya ta fito ƙofar ɗaki ta fara haɗa musu kayan
karin safe. Da yake kowacce abin girkinta yana ƙofar ɗakinta, kasancewar babu
kitchen a gidan.

Gidan da su Fauziya suke zaune, gidan haya ne mai ɗauke da ɗaukunan mata biyar.
Kowacce daga mai yara biyu sai zuwa uku, kuma dukkansu ɗakunansu falle ɗai-ɗai ne
sai banɗaki ƙwaya ɗaya da suke amfani da shi. Dalilin da ya sa su A'ilo suka kafa
wa Fazuiya ƙahon zuƙa saboda, duk cikinsu mijinta ya fi nasu rufin asiri. Domin ta
fi su yawan sauyin tukunya, don Kabir idan da 'yan kuɗi a hannunsa haka zai sayo
musu nama ko kifi ko ba can mai yawa ba ta sarrafa. Kuma indai Fauziya ta yi sauyin
girki duka sai ta zuba a 'yan robobi ta aika masu, saboda fita haƙƙin maƙotaka. Duk
cikin gida Lawisa ce kawai ta su ta zo ɗaya, ba ta yi mata irin cin kashin da su
A'ilo suke yi mata. Don haka Fauziya da Lawisa suka haɗa kai, su kuma su A'ilo suma
su uku suka haɗe kansu. Da yake ita Lawisa ba ta da haƙuri, sai ya zama suna
shakkarta don suna yi mata kan kara take yi musu na itace. Saɓanin Fauziya da ta
kasance mace ce mai sanyi, tsananin haƙuri da kawaici. Duk abin da za su yi mata ko
su yi wa yaranta, sai dai ta yi shiru idan kuma yara aka yi wa sai dai ta zaunar
da su a ɗaki.
Babu damar yaranta su fita wasa tsakar gida, sai yaran su A'ilo su doke su da
yake kusan duk sun girme su. Ita kuma Fauziya ƙiris suke jira ta yi wani kuskuren,
ko ta taɓa kayan wani daga cikinsu sai su hau ta da faɗa. Don haka gidan suke
zaune kara zube babu haɗin kai, hatta shara kowacce sai dai ta share iya ƙofar
ɗakinta. Banɗaki ma kuwa sai dai kowacce idan mijinta zai yi wanka, ta ɗauki buta
ta je ta wanke masa. Shara ce kawai idan ta cika suke haɗawa, idan ta cika wannan
ce za ta biya idan wani karon ta sake cika sai wata ma ta bayar da kuɗi a kwashe.

Maman Sabir tun da ta fito tsakar gida take leƙen abin da Fauziya take dafawa,
ana cikin haka Kabir ya fita ya sayo musu ƙwai guda huɗu. Nan take gidan ya cika da
ƙamshin suyar ƙwai, baƙinciki da hassada suka ƙara cika zuciyoyin su. Bayan ta gama
sai da ta gutsiri kaɗan-kaɗan ta saka a leda kowacce ta miƙa mata, sannan suka
shige ɗaki ita da iyalanta suka karya. Da yake ranar Lahadi ce babu makarantar boko
ya sa bayan sun gama ta yi wa yaranta wanka. Kabir ya ɗauki Fatima ya mayar da ita
kemis, ya karɓo mata magunguna sannan ya wuce shagonsu na ɗinki.

Su Fatima ne suka fita tsakar gida wasa, abin ka da yaro duk kyarar da yaran su
A'ilo suke yi musu da sun ga suna wasa haka za su je su shiga cikinsu. Zaman su a
wurin babu wuya kenan sai Nabila ta fisge abin wasanta a hannun Na'ima ta ce, "Umma
ta ce na daina wasa da ku, babanku ɗan shaye-shaye ne." Duk da ba su san me kalmar
take nufi ba, amma tun da suka ji suna yawan faɗa musu cikin tsangwama sai suka
ƙyamace ta, Na'ima ta ɓa ta fuska ta ce.
"Ba dai babanmu ba, sai dai babanku. Abi yana siyo mana alewa da biskit, ba ɗan
shaye-shaye ba ne."

Duk cikinsu Sabir yayan Nabila ya girme su, don kusan shekararsa goma. Ya fi su
wayo don haka ya ce, "Ke mu babanmu ba ya shaye-shaye, Ummanmu ta ce mu daina wasa
da ku kada mu zama 'yan'iska. Wai babanku har shiga ɗakin matan aure yake yi."Yaron
ya ƙarasa magana yana dariyar tsokana. Abin sai ya yi wa su Na'ima ciwo, don haka
suka shiga mayar da martani abin har ya zame musu faɗa. Suna cikin kokawa su Nabila
suka tararwa Na'ima da duka, da ta ji zafi ita kuma sai ta ciji Hafsa a hannu. Nan
take iyayensu suka fito, dama kamar jira suke yi.

Cikin masifa Maman Sabir ta fisge Fatima tana ƙwalawa Fauziya kira, Fauziya da ke
ɗaki ta yi saurin fitowa tana shirin yin magana Maman Sabir ta katse ta.

"Wallahi wannan shi ne na farko na ƙarshe, ko da wasa idan Fatima ta sake cizar
mini 'ya'ya sai na ɗauki hannunta na tura musu a baki sun rama. Ƙarya aka yi uban
na su ba mashayi ba ne? Na ga rannan da ya yi mankas ɗakin A'ilo ya faɗa."
Fauziya ta yi shiru ta rasa bakin magana, Lawisa ta ɗaga labule tana faɗin.
"Haba ku kuwa kamar ba ku san faɗan yara ba har za ku shiga? Wallahi indai yara
ne kuna zaune za su ba ku kunya..."
A zafafe Abu ta katse ta. "Sai ki bari idan an ciji naki 'ya'yan sai ki faɗi haka,
za ki fito ki yi wa mutane gwalangwaso. Don sun ce ubansu ɗan maye ne shi ne za ta
cije su. Shekaran jiya waccan, ina ce butata ya ɗauka ya yi mini wurgi da ita ta
fashe." Lawisa za ta sake magana Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta girgiza mata
kai sannan ta ce.

"Don Allah ku yi haƙuri, In Shaa Allahu ba za su sake cizonsu ba."

Kusan lokaci ɗaya suka taɓe baki, Fauziya ta yi wa su Na'ima magana suka wuce
ɗaki. Jiki a sanyaye ita ma ta wuce ɗaki, tana jin su A'ilo suna ci gaba da yadda
mata magana da habaici haɗe da yin dariya.

"Mami wai mene ne shaye-shaye? Me ya sa kullum su Sabir suke ce mana Abi yana
shaye-shaye?"

Tambayar Na'ima ta katse dogon tunanin da Fauziya ta faɗa. Ras! Ta ji gabanta ya
faɗi, da sauri ta kamo hannunta fuska ɗauke da alamun tsoro ta ce.

"Kul Na'ima yara ba sa faɗan irin wannan maganar kin ji! Babu kyau kada na sake
jin kun faɗi haka."

Lokaci ɗaya suka gyaɗa mata kai, sai Hidaya ta ce. "Mami to ki faɗa wa su Hafsa su
daina faɗa kada Allah Ya ƙona su a wuta."
Fazuiya ta yi murmushi ta ce, "Su ma mamansu za ta faɗa mu, sannan don Allah
Hidaya ku daina zuwa cikinsu kuna wasa. Ba ga kayan wasanku nan ba, ku dinga zama a
ɗaki kuna yi kun ji."
Lokaci ɗaya suka amsa mata, tana nan zaune ta ji sallamar Sadiya facalarta.
Daga wurin da take zaune ta amsa mata, Sadiya ta shiga tana faɗin.

"Uwar huɗu, wai har yanzu ba za ki kotse ba ne?"

Fauziya ta miƙa mata fulo ta ce, "Zauna uwar 'yan sa ido, ni kaina kullum jiranta
nake yi."

Sai da suka gaisa Fauziya ta ce, "Ina zuwa haka da tsakar rana?"
Sadiya ta yi dogon tsaki tana kallon su Na'ima da ke wasa ta ce, "Ai tun da akwai
radiyo mai jini dole na gyara zancan. Wallahi Fauziya komai ya yi mini zafi, kin
san dai halin wancananka. Yau haka ya ƙare mini zagin cin mutumci, saboda kawai na
ce ya biya ni kuɗaɗen da nake bin sa bashi. Ke dai shaida ce kin san ba yau ya fara
zagin iyayena ba, ni ma yau na gaji na rama. Ke faɗa har sai da ya kaimu tsakara
gida, shi ne fa o'o (Inna) ta shigarwa ɗanta suka yi mini zagin ƙare dangi. Abin da
ya sake ɓata mini rai kwanana uku kenan ina zazzaɓi, kullum nace ya ban kuɗin
magani sai ya ce mini yake ba shi da kuɗi. Amma ina duba wayarsa a chart ɗin da
suke da budurwarsa, na ga ya tura mata dubu shida kuɗin ɗinki wai bikin yayarta ake
yi."

Sadiya ta furzar da iska mai zafi, tana tuna ɗacin abin da mijinta ya yi mata ta
cigaba.
"Kin san fa shi indai a kan 'yanmata ne duk arzikinsa a nan yake tafiya, ni kuwa
ina gida ko oho wani lokacin na omon wanki ma gagarata yake yi."
Fauziya ta girgiza kai cikin damuwa ta ce, "Ke ma Sadiya tun tuni kin san
halinsa, da kin sani ba ki biye masa ba kun yi ba daɗi a gaban yara ba. Ita kuwa
dama kin san yaranta ba sa laifi, kwanaki fa a gabanta ya mare ki amma sai cewa ta
yi ai ɓata masa rai kika yi."

Kamar Sadiya za ta yi kuka ta ce, "Idan ban biye masa ba Fauziya ya zan yi? Kina
ga fa haka zai tsallake ya bar mu indai akwai tsaba babu ruwansa da kuɗin kayan
mahaɗi, duk ni nake fafutukarsu. Ga shegen kule-kulen mata har da na hauka, don
wallahi da kuɗin da yake kashe musu ba gara mu ya kashe mana ba."

"Eh to haka ne, lamarin ne sai haƙuri kawai. Ni dai ta nan fanin sai dai na ɗaga
hannu na gode wa Allah, domin gaskiya babu macen da ta sha gaban Kb da har zai
tsaya ɓa ta lokaci a kanta..."
Murmushin da Sadiya ta yi ya katse furucin Fauziya.

"Ban ga laifinki ba, da kika faɗi haka. Domin ruwan da ya dake ka shi ne ruwa.
Amma ni dai a wannan gaɓar da zamantakewata da Ali, ta koma irin da zaman cin
kunamar ƙadangare. Na rantse da Allah ko me aka ce mini ya yi ba zan musa ba, ki
bar cin alwashin namiji saboda ko yaya basa rasa 'yanmatansu ke dai ki ga rijalu
kawai."

Fauziya ta yi dariya ta ce, "A'a Sadiya, dole na bigi ƙirji wallahi ko a gaban
mutanen duniya Kb ɗaya a cikin dubu, ya zamo mini tamkar zara a cikin taurari. Ni
shaida ce wallahi-wallahi tun daga ranar da ya muka fara soyayya, har kawo yanzu
babu macen da yake kulawa."
Sadiya ta miƙe tana gyara hijabinta ta ce, "To ni bari na zo na wuce, ko ba komai
mun ɗan tattauna na rage zafin da nake ciki. Kada na daɗe uwar masu gida ta fahimci
na fita, na ƙara wani laifin."
Har soro Fauziya ta raka ta, Sadiya ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Wai mutanen gidanku har yanzu zaman naku sai a hankali ne? Na ga da na yi
sallama A'ilo ba ta amsa mini ba."
Fauziya ta furta, "Hmmm ke dai bari, wallahi shi ya sa zaman gidan duk ya gundure
ni."
Fauziya da Sadiya sun jima suna hira sannan suka yi sallama.

Sai da ta tabbatar da yaran sun tafi makaranta, shi ma Nazir ya tafi kasuwa.
Sannan ta shige uwar ɗaki, ta buɗe drower kayanta. Daga can ƙasa ta zura hannu ta
ciro 'yar ƙarama wayarta, ta koma gefen gado ta zauna sannan ta kunna ta. Ba a
ɗauki lokaci ba wayar ta kunnu, nan take ta latsa wata lamba ta kira, daga can
ɓangara aka ɗauka.

"Barka da safiya sarauniyata!"

Maimuna ta saki murmushi cike da kissa ta ce, "Barka dai jarumin jarumai."

"Wai sai yanzu ya matsa ya ba mu wuri ne? Wallahi tun safe nake jin ƙishirwar
muryarki."
Jafar ya furta cike da sha'awa.
"Hmmm to ya za a yi? Ka san abin ka da mai iyali ko ya fita ai dole sai na
sallami yara."
Jafar ya yi murmushi ya ce, "Me zan samu? Don wallahi yau kwana biyu kenan, na kasa
kataɓus da waccan sakaryar." Dariya sosai Maimuna ta yi ta ce, "Wallahi babu
ruwana, kai da Maman Nana."

Jafar ya sake kwantar da murya cikin wani irin yanayi ya ce. "Moon!"

Yadda ta ji ya ambaci sunanta ya sa har sai da ta ji tsikar jikinta tana tashi, ta
janyo filo ta rungume cikin wata irin murya ta amsa.
"Na'am Abban Nana!"

Ajiyar zuciyarsa ta ji har a fili, ya sake narke murya ya ce.
"Ba na son ki dinga kirana da wannan sunan, tun da ita ma waccen haka take faɗa.
Don Allah ki saka mini sunan da zai dinga faranta mini rai."
Maimuna ta lumshe ido, ta ɗan shagwaɓe murya ta ce.
"Baby ya yi?"

Shi ma sai ya yi irin muryarta ya ce, "To ya zan yi? A dinga faɗa mini hakan, amma
dai har yanzu kin ƙi ki ba ni dama na nuna miki zallar soyayyar da nake yi miki a
cikin zuciyata."

Jafar ya sake kwantar da murya cike da shauƙi, kamar wanda yake waya da matarsa
ya ce.
"Moon! A gaskiya Naziru ba ƙaramin dace da sa'a ya yi ba. Wallahi da ace ke na
fara gani kafin Sumayya, da babu abin da zai hana ban aure ki ba. Don Allah ki ba
ni dama koda sau ɗaya na nuna miki salon tawa kulawar."

Wani farinciki ne ya lulluɓe Maimuna, tabbas ko bai faɗa mata ba. Ta sha ji a
bakin Maman Nana, cewar Jafar gwani ne a fagen kulawa da soyayya. Don da bakinta
take ba ta labarin Jafar irin maza nan ne masu buɗaɗɗan ido, don cewa ta yi wani
lokacin wayewarsa har tsoro take ba ta. A duk lokacin da Maman Nana take ba wa
Maimuna labarin mijinta, sai dai ta yi ta sha'awa tana jin ina ma ita ce ta yi
dacen samun miji wayayye mai rifin asiri kamar ita. Kafin daga baya kuma su
tsunduma kogin soyayyar da suka yi nisan kiwo ba tare da sun ankare ba.

"Moon! Ba ki ce komai ba."

Jafar ya katse mata tunani, Maimuna ta yi murmushi sannan ta ce.
"Ina tsoron kada Maman Nana ta gano mu, ka ga a cikin unguwa ɗaya muka."

"Haba My Moon, ai dama ko don magulmata ba za mu haɗu a unguwa ba. Wallahi ko
hotel zan iya kama mana..."

Cikin razani Maimuna ta ce, "Hotel!"

Kafin Jafar ya yi magana daga can falo ta ji motsi, da sauri ta katse wayar ta
zare batirinta. Jikinta har karkarwa yake, ta tura wayar cikin drowerta.
Tana waigowa ta ga Naziru yana tsaye a bakin ƙofa ya harɗe hannuwa a ƙirjinsa.
"Maimuna da wa kike magana?"
Ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi, cikin firgici bakinta yana rawa ta ce.
"Ni... ni... kuma?"
Fuska ta ga ya ƙara haɗewa, bai tanka mata ba sai gyaɗa mata kai da ya yi.

Kabir yana fita daga gida tun bai ƙarasa titi ba, ya kira Sury. Cikin muryarta
mai fisgar hankalinsa ta ce, "Matsoracina! Wato sai yanzu ka samu damar fita daga
gida?" Kabir ya saki murmushi ya ce, "Kin gan ki ko?"
Sury ta ɗan haɗe fuska kamar tana gabansa ta ce, "Kb ni fa jiya abin da ya faru
ka sa na fara jin tsoron ko yadarata kake yi. Ka duba fa ka gani tambaya ɗaya
matarka ta yi maka amma duk ka birkice, yanzu a haka za mu yi auren har ka kai ni
gidan da kake gini?"

Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Haba baby, me ya sa kike kawo wasu-wasi a cikin
soyayyarmu ne? Kin san dai ina sonki ina ƙaunarki. Ko soyayyar da na nuna miki jiya
ya ci ki fahimci irin soyayyar da nake yi miki. Ki ajiye maganar aure, wannan wani
lissafi nake yi a kansa kin san ke ba kalar zaman gidan haya ba ce."

Sury ji ta yi kanta ya sake girma, ta lumshe ido cike da jin soyayyar Kabir tana
sake nuƙurƙusarta. Domin Kabir irin mazan nan da suka iya nuna zallar soyayya, duk
cikin samarin da ta yi babu wanda take yi wa mutuwar so kamar Kabir.
Sun jima suna hira sannan suka yi sallama, suka tsayar da magana a zuwa bayan
la'asar zai kai Sury gidan da yake gini ta gani.

Har zai saka wayar a aljihu sai ya ha wata lambar ta shigo, guntun tsaki ya saki
kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka. Yana ɗauka ya ji ta fashe masa da kuka,
shiru ya yi yana jin kukanta har cikin jikinsa.

"Kukan na mene ne?"
Kabir ya furta cikin tattausan lafazi.

"Na gagara jure rashinka ne, na gagara jure horon da ke raunatar da zuciyata.
Kabir! Ka san na saba da hutawa a lambun ƙaunarka, sai da ka bari zuciyata ta yi
nisan kiwo a ƙaunarka sannan kake ƙoƙarin fincike ta da ƙarfin tsiya. Me ya sa kake
azabtar da ni Kabir?"

Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Hafsa kenan! A kullum haka kike faɗa a fatar
baki, amma kin gagara nuna mini zallar soyayyar da kike faɗa. Hotuna biyu kawai na
ce ki ɗauka ki turo mini, amma kin ƙi yarda ko ba ki yarda da ni ba ne?"
Jim Hafsat ta yi tana nazari zuwa can ta ce, "Shi kenan, zuwa dare zan turo maka
matuƙar za ka sauka daga dokin zuciyar da ka hau."

Kabir ya cije baki yana murmushin samun nasara ya ce, "Haba ko ke fa Hafsyna, da
sai nake ganin kamar ni nake wahalar da kaina a kanki."
Hafsa ta ce, "Hmmm ba za ka gane halin da nake ciki ba, yanzu dai yaushe za ka
zo."

Shiru ya yi yana nazari, don Sury ta kwaɗaitar da shi irin salon tata soyayyar.
Kuma ko babu komai ya san idan ya kai ta kangon da yake gini, zai iya samun fiye da
abin da ta yi masa a soron gidansu a daren jiya. Don haka ya ce, "Ammm yau dai
gaskiya ɗinki ya yi mini yawa, saboda akwai kayan amaren da ban kammala ba. Bayan
haka ma, Oga yana raba mana ɗinki saboda gobe za a tafi da su Abuja. Ina jin sai
zuwa gobe za ki gan ni."
Hafsa ta narke murya ta ce, "Wallahi na yi kewarka, kwana ukun da ka daina ɗaukar
wayata ji nake kamar mun shekara ɗari uku."
Kabir ya yi murmushi sannan suka cigaba da hira, bayan sun gama ya wuce shago.


Bayin Allah wasa farin girki kenan, me kuka fahimta a game da rayuwar Kabir?
Kabir yana da 'yanmata amma ya aka yi Fauziya ba ta sani ba? Kuma me kuke tunanin
ya sa ta ba shi yarda 100% a kan babu budurwar da yake kulawa. Ga dai Maimuna tana
soyayya da mijin maƙociyarta, shin wacce amsa za ta ba wa mijinta Naziru? Sai na ji
daga gare ku.😄


Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[12/02, 22:13] Ameerah Adam🌚: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da
ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da
mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA UKU

Tun da yamma ta kawo kai Sury ta fara doka wa Kabir kira, saboda zumuɗi tun bayan
Azahar ta gama shiryawa. Kasancewar akwai ɗinkunan da Ogansu ya tara na 'yan wunin
biki ya sa shi tsayar da ragowar yaran shagon ya raba musu ɗinkunan domin su yi
saurin gamawa. Wannan dalilin ne ya sa da Sury ta kira shi ya sanar da ita, a zuwan
ya ɗaga mata ƙafa ko zuwa gobe ne. Ko kaɗan ba ta ji daɗi ba don haka ta nuna masa
ɓacin ranta.

"Kb shi ya sa nake tsoron soyayyarmu, wallahi sai na ga kamar yaudarata kake yi.
Na kai kwana nawa ina son ka kai ni na gano ginin nan, amma yanzu ka zo kana tsara
ni."

Kabir ya miƙe ya fita zuwa ƙofar shagon ya ce, "Kin gane Sury, wallahi da gaske
nake yi miki. Amma tun da haka ne ki ba ni zuwa nan da bayan Sallar magriba, duk
yadda zan yi na san yadda zan ɓullowa Oga koda ban gama aikina ba."
Sury ta ɗan yi jim sannan ta ce, "Amma ka san bayan magriba Yaya Umar ba ya
barinmu fita, sai dai na san dabarar da zan yi masa."
Kabir ya yi saurin faɗin, "Yawwa Suryna, kamar ba mace ba. Don Allah ki shawo
mana kansa ba za mu daɗe ba, muna gama gani za mu wuce."
Sai a lokacin Sury ta ji daɗi, ganin ya lallaɓa ta ya sa shi yin sallama da ita ya
koma cikin shagon. Ɗinkin kusan mutum uku ne a gabansa, don haka ya ci gaba da
ɗinkin cikin sauri don ba ya son abin da zai sake ɓa ta ranta.

Girgiza kai Maimuna ta yi, don har cikin ranta gani take kamar Nazir ya ji
kalaman da suke tattaunawa. Amma gudun ta yi saurin bada kai bori ya hau, ya sa ta
ce.
"Gaskiya sai dai idan kunnenka ne."

Shiru ya yi yana kallonta kamar mai nazari, har sai da ta sake tsarguwa. Domin a
lokacin da ya shiga ji ya yi kamar waya take duk da bai ji abin da take faɗa ba,
amma da yake ya ga wayarta tun a falo sai ya basar. Yana shirin yin magana ta ce,
"Ko dai waƙar da ka ji ina yi ce?" Cikin halin ko inkula ya ce, "Wataƙila! Ina
wayarki take?"

Ya tambaye ta don Nazir mutum ne mai bin diddigi da tsanani a kan iyalinsa.
"Tana falo!"
Ta ba shi amsa a taƙaice.

Falo ya koma ya ɗauki wayarta, sai da ya yi shige-shige sannan ya saki muryarsa ya
ce.
"Wallahi mantuwa na yi, na manta hulunan mutane ɗauko mini suna drowerta."

Sai a lokacin hankalin Maimuna ya kwanta, ta shiga ciki ta buɗe drowersa ta ɗebo
masa hulunan ta ba shi, sannan ya sake fita. Ajiyar zuciya ta sauke a fili, sannan
ta furta.
"Dole na sauya taku, tun da mutumin nan yana da key da yake buɗe ƙofa. Ya zama
dole na yi takatsantsan, idan ba haka ba a samu matsala."

Gate ɗin ta sake komawa ta saka sakata a gidan, sannan ta koma ta zaro ɓoyayyiyar
wayarta. Mayar da batirin ta yi bayan ta kunnata ta sake kiran Jafar.

"Hello!"
Ta furta cikin kashe murya. Daga can ɓangaren Jafar ya ɗauka murya a can ƙasa, sai
kuma ta ji muryar Abdul yana kuka.
"Wai kana nufin ba ka fita kasuwa ba? Na ji kamar muryar Abdul ko?"

Murmushi Jafar ya yi ya sake jan bargo ya ƙudundune, wani shauƙi yana fisgarsa a
kan Maimuna ya ce.
"Ya za a yi na iya fita? Bayan ina lulluɓe da bargon bege da kewarki. Don Allah
Moon ki nemar mana mafita mana, ki tausaya mini wallahi muryarki ba ƙaramin gigita
nutsuwata take yi ba."

Shiru Maimuna ta yi, tana nazarin hanyar da za ta ɓullo musu domin ita kanta ta
kwaɗaitu ta ga irin soyayya da Maman Nana take faɗa mata.
"Ka san dai halin Nazir mutum ne mai shegen kishi, ga shi da zargi da bin
diddigin duk abin da nake yi. Kana ga hatta unguwa ba ya iya barina na je ni kaɗai,
shi yake kai ni duk inda za ni. Wallahi kaina ya kulle ban san ya zan yi ba."
Nazir ya kwaɓe murya kamar wani mace ya ce, "Wallahi ni sai na ga kamar ma ba kya
yi mini irin soyayyar da nake yi miki. An ya kin san yadda zuciyata ta kamu da
mutuwar sonki kuwa..."

Salatin da Maman Nana ta saki ya sa Jafar ya yi sauri ɗagowa, nan take gabansa ya
faɗi. Maman Nana da kishi ya gama tirniƙe ta ta ce, "Na gode Abban Nana, yanzu
wulaƙanci da tozarcin naka ya kai har ka haye mini kan gado ka kira wata shegiya
kuna waya da ita? Yanzu ka yi mini adalci kenan? Ashe duk alƙawarurrukan da kake
ɗaukar mini na ƙarya ne." Sai kuwa ta fashe da kuka. Hamdala ya yi a ransa da ya
fahimci Sumayya ba ta gane da wacce yake waya ba.

"Don Allah ki yi haƙuri My love, wallahi duk wani abu da kika ji na faɗa wa
yarinyar nan a fatar ba ki ce. Wata yarinya ce ta nace mini, ni kuma ba na son yi
mata rashin mutumci kin san wulaƙanci babu kyau shi ya sa nake son mu rabu lafiya."

Wani irin mugun kallo take jifansa da shi, rai a ɓace ta ce. "Idan kai ba za ka
iya yi mata rashin mutumci ba ni zan iya, ka kira mini ita in zazzage ta ko
wacece."

Kamar gaske Jafar ya ɗago wayar ya kira ta amma sai suka ji a kashe, ya saki
murmushi a cikin ransa. Ya rungumo Maman Nana ya ce, "Kin ji wayar

Please Login or Register in order to submit comment