Reading MAR ADAMS BOOK 3 BY AYSHA BAGUDU Chapter 27 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana illata zuciyar dan adam ta kallesa a tsanake tana sauke numfashi ".



"banason ki illata zuciyarki ko babu komai kina da qarancin shekarun ,kinyi kankatar da zaki jefa rayuwarki cikin over thinking haka .ta sake kallonsa taga har lokacin ita yake kallo  sai dai fuskar nan tashi  a hade take "nasan daga yau zaki daina ko? ya fad'a yana matse yatsun hannunta cikin nashi sai dai ta girgiza  masa kanta ,alamun bazata iya ba, sai ya sake langwabe mata ya dawo  kamar wani abun tausayi  yana murza tafin hannunta cikin nashi .tayi qoqarin zare hannuta ya damke sosai  yace "Please maryama wai mai yasa bakya tausayin kanki ne  ?"
yayi mata tambayar yana mata tafiyar tsutsa a tsakiyar hannunta tayi saurin zare hannuna daga nasa tana yarfarwa kamar wadda wuta ta kona saboda wani yanayi da taji ya taso daga hannun nashi  zuwa  cikin nata, cikin kankanin lokaci ya zagaye dukkanin ilahirin jikinta ,cikin sarkewar murya tace "no sir I can't bazan ta'ba dainawa ba yaya sadam fa jinina ne ko babu aure atsananinmu babban yaya ne a wajena .“ina tabbatar maka idan babu baba gali a raye da yaya sadam yana raye shine ma daurin aurena .da mahaifina da mahaifinsa uwa daya uba daya ta yaya kake tunanin  zan iya mantawa da  wannan dangantar?"



ahankali  ya lumshe mata tsumammun idanunsa yace "shikenan ba’a bukatar ki daina tunaninsa ki cigaba da tunaninsa idan kina só ma kema kije ki haqa rami ki shiga ki binne kanki “kai a ruwa miko min  kwalin sigari "sigari kuma ?"ta furta a razane baqar maganar daya fad’a bai mata ciwo ba kamar abinda yake qoqarin aikatawa yanxu .a ruwa ya miko masa tare layter ja ya kar’ba  ya bude ya ciro Karan sigari daya ya rike batare daya kai bakinsa ba  duk tana kallonsa yayinda idanunta suka sake ciccikowa da ruwan hawaye ya janyo hannuta mara ciwo ya saka layter ciki "kunna min !"ya fad'a yana miko mata sigarin , zaro idanu tayi  waje tana dubansa cike da matsanancin mamaki .hankalinsa kwnace yayi  mata wannna banzar maganar aiko sai ganin hawaye yayi sharr suna gangaro mata ." numfashi ya sauke sannan ya sake kamo hannunta ya cire layter sa ya kunna sigari  ya fara zuka ahankali ahankali hannu ta kai ta toshe hancinta tana tunanin abun yi ita kam tayi data sanin shiga motarsa mutun kamar mai ajanu sam shi baya son zaman lafiya yanzu daga magana me ya kawo batun ta kunna masa sigari ko shan sigari saboda Allah?"yayinda shi kuma ya kai hannu yana shafa goshinsa zuwa keyarsa .”



ahankali ta juyo garesa still hannunta na rufe da hancinta "sir !” ya kalle a d’age da gefen idanunshi “warin abar nan yana damuna "gara ki saba."gara ta saba kuma ?"wannan wace irin banzar magana ce " tayi maganar aranta “zuwa yanzu yaci ace kin fara sabawa da warin sigari "inna ilaihi "ta furta a fili"ita kam ta rasa gane inda maganganunsa suka dosa me yake nufi da hakan kuma?”  tunda ya soma zugar sigarinsa bai kalleta ba sai yanzu da ya wani tsareta da tsumammun idanunshi da suka fara canza kala tare da dage mata  girarsa d'aya yace "tsoro kike ji ne ?" cike da jin haushi ta fixge sigarin a hannunsa ta manna a gefen hannunta mai ciwo "kina hauka ne ?"
yayi mgnr a firgice yana cigaba da kallon hannun "kasan illar abinda kake yi kuwa ?muna cikin mota kana sha mana wannan qazantar "ka kuwa ma san yadda nake ji idan naga kana shan wannan abar ?"ta qarasa maganar tana juya masa baya sakamakon kukan daya kwace mata ."



ahankali ya kwanto jikinta tare da juyo daita garesa ya sake makale mata ya janyo  hannunta ya tsura ma hannun ido "kalli illar da kika yiwa kanki "?gara wannan rad'ad'in akan zafin sigarin da kake sha a gabana "bai san sanda murmushi ya bayyana akan fuskarsa ba sai dai ya gintse yace "marayam kina da rigima "ai kai ne rigimam me ."tayi maganr a kasan ranta tana zabga masa harara."ni kikewa wannan kallon ?tayi shiru tana qoqarin janye jikinta daga nashi “kince na  kuwa  san yadda kike ji idan ina shan sigari ?kawar da kanta tayi gefe dan bata ma son kallon fuskarsa sai dai ji tayi ya fixgota jikinsa gbdy ta kwanto jikinsa wani irin bugawa zuciyarta tayi ta sauke numfashi tare da tsuke qaramin bakinta tana kallonsa muryarsa can qasan makoshi yace “fada min me kike ji ?"zuciyata na zafi "tayi maganar kmr zatai kuka “amm da ni ina son ki saba daita "akan wani dalili kenan zan saba ?” ni wallahi  bana son warinta yana mugun d'aga min hankali bama warinta ba ni d'an sigari ma banason shi a kusa dani "to ya zakiyi dani  kenan ?"ya fad'a yana hura hucin numfashi da iskar bakinsa ya qarasa maganar adaidai lokacin da a ruwa yayi magana “yalla’bai mun shigo agege “nan yayi directing dinsa inda zasu sannan ya sake janyo hannuta yana kallo inda ta kona kanta .”



“Karki sake min abinda kikayi min yanzu kalli kiga har kin kona hannunki mutun sam baya abu da tunani yana magana yana hura mata gurin nan take taji ta daina jin rad’ad’i a wajen batare da ‘bata lokaci ba suka iso unguwarsu maryama a ruwa na gama parking maryama ta dauki jakarta tace masa "goodbye sir " yayi murmushi yace "till we meet tomorrow ".da sauri ta bud’e motar ta fita daga motar tana harhada hanya, but she felt as gangar jikina ce ta fito ta bar zuciyata a cikin motar tayi kokarin calming down din zuciyarta kafin ta karasa gida ahankali ta shigo gidansu kai tsye kamar yadda ta saba da part din umma ta fara tayi knowking har sau biyu taji shiru ta kai hannunta da zumar sake knowking taji kofar ta bude "a she ma kofar a bude take ta fad'a tana tura kofar shiga parlour'n babu kowa sai umma ita kadai zaune tayi shiru tana tunanin “lafiya umma ta zauna shiru haka?” tayi mgnr a kasan ranta kana ta tsaya tana kallon hannuta dake nade da bandage tana tunanin ta fad'a mata abinda ya faru yau a office ko tayi shiru kai bai kamata ba hankalinta zai tashi matuka bayan yanzu hankalinta a kwance yake bari mr ata ya gama bincikesa sai na fada mata idan da bukatar haka ta qaraso ta dafata tana kiran sunanta "umma nah ! .”



Umma tayi firgigib ta dawo haiyacinta yace "a'a yaushe kka dawo ban sani ba ?zo ki zauna ki huta kinji diyata ta zagayo daita gabanta ta zaunar daita akan dogon table din dake gabanta tana murmushi "me Ke faruwa ne umma tun jiya na lura bakya cikin farinciki?"meke damunki babu abinda ke damuna kawai dai kaina ke d'an min ciwo umma wannna ba ciwon kai kawai bane akwia abunda ke damunki baki saba boye min komai ba idan kika boye min zanji babu dadi umma dan allah ki fada meke damunki ?nace babu komai  bari na kawo miki abinci kici nasan kin gaji dayawa ".umma karki min karya yanzu Kenan bazaki iya fada min damuwarki ba ?Umma ashe zaki iya boyewa diyarki abinda ke damunki ?dan allah ki fada min meke damunki tayi mgnr Kmr zatai kuka "tabbas akwai abinda ke damuna maryama ,mutane basa da amana maryama .”



dana dawo daga ijesha na biya kamfaninmu bread in takaice miki wai dan zaman danayi agida saboda rasuwar sadam ban samu na leka ba idan kika ga barna da gali yayi sai kinyi mamaki nan ta zayyane mata komai da irin matakin data dauka akanshi "tabbas baba yayi kuskure umma daman kuma haka mutane suke kullum cikin Kuskure muke amman kiyi hakuri umma ki bashi wani dama "da wannan damar mutane suke sake kashe mutun kullum ana yi maka ana baka hakuri amman ya zakiyi umma yanuwa ne ki yafe masa umma yanzu wannan matakin da kika dauka akansa idan kika dawo dashi bana tunani zai sake aikata laifin kuma dai kice Kike koyar da na tare dake ,idan mutun yayi maka laifi ka hukunta shi sai kuma ka dawo ka yafe masa “.shike nan na hakura amman saboda ke” maryama ta kwanto jikinta tana murmushin jin dadi tace "na gode sosai umma ina qaunrki .”umma ta shafa gefen fuskata "nima ina sonki maryama "kamar ance ta kalli hannun maryama tace “menene haka a hannunki ?”


Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 31


Zaune ya’yan ummi suke a bangaren hagu da damanta a babban parlour’nta har maryam, inda aunty shahida ta dubi mami tace “mami kince zaki fad’a mana abinda ya faru jiya tsakanin baba qarami da adamcy amman munji shiru gashi har muna shirin tafiya” ke dai shahida bari ,alamarin adamcy sai addua nan mami ta shiga rat ta’bo masu abinda ya faru a yammacin jiya ,murmushin farinciki ne ya bayyana akan fuskar maryam kasancewar tana mugun qaunar halaiyarsa” she really miss his face “a halin da take ciki zaune babu abinda take muradi da kwadayin gani kamar ta d’aura kwayar idanunta akanshi dan tayi mugun kewar fuskarsa da komai nashi ita fa tana ji aranta dan shi kawai take numfashi acikin duniyar nan ,ita fa duk abinda yake mata bai ta’ba rage digo d’aya acikin soyayyr da take masa ba, hassalima sai qaruwa da soyayyarsa take acikin zuciyarta ,haka kuma duk yanayinsa da abubu wansa da yake ma mutane da wanda yake mata bai ta’ba ‘bata mata ran da taji wai zata iya daina son shi ba. duk abinda yayi ma burgeta yake shiyasa tana jin rashin dadi aranta da ba namiji zata haifa masa ba .
dan zata so ta haifa masa yaro mai kama dashi sak da irin halaiyarsa idan ma da hali ya zartashi akomai
mami tana gama qarasa mganrta ta mike tsaye tace dasu tana zuwa ta nufi parlour’nta na biyu ta barsu zaune inda nana hauwa’u ta soma nata bayani daki daki“.“nifa ba hayaniyar da’aka yi jiya tafi komai damuna ba kamar fuskar yarinyar nan da’aka yi presentation daita .”



“Wallahi idan Kunga yadda yaya ya rungume yarinyar nan ajikinsa cike da tsananin kulawa da soyayya sai abun ya firgitaku .jin haka yasa maryam ta d’ago kanta da sauri gabanta na wani irin fad’uwa da matsanancin qarfi ta tsurawa nana hauwa’u eye’s dinta “runguma kuma !”ta tambayi kanta zuciyarta na wani irin tsinkewa da zafi yayinda har lokacin idanunta kyam akan nana hauwa’u gabad’ayansu suka natsu suna sauraron bayanin nana hauwa’u “wallahi aunty shahida wannan yarinyar da wahala ba yarinyar mafarkin yaya bace, kunsan ni na ta’ba ganin zanen hotonta akan table a parlour’nsa amman sau d’aya ne“.ko yanzu kuka gan yarinyar nan ,matukar kun ta’ba ganin zanenta zaku tabbatar da cewar itace yarinyar mafarkinsa ”na shiga ukuna !maryam ta fad’a acikin ranta hankalinta na tashi “tabbas nima na ta’ba ganin zanen hotonta a tsarka wuyansa amman a yanzu gaskiya na manta yadda kamanin fuskar yarinyar take dan cikin tsananin fushi naga hoton alokacin “maryam ta waiga ta kalli aunty shahida qirjinta na bugawa “kallo d’aya zaka wa maryam ka fahimci hankalinta yayi matuqar tashi da jin wannan mummunar labari gabad’aya annurin fuskarta ya d’auke “kada fa maganar sister ta zamo gaskiya yarinyar mafarkinsa ce ?”ai kuwa idan ya tabbatar itace da tata rayuwarta taza qarshe ina zata saka kanta ?”dame zataji ?”tasan shikenan har abada bazata sake rayuwa dashi ba .”babu ita azahiri ma yaki amsarta amatsayin matarsa ina ga ta bayyana ?.”duk tunaninta a yanzu da hope dinta akan cikin jikinta ne jira kawai take ta haifa masa babyn jikinta taga yadda zai yi raact ,zai cigaba da nuna mata qiyayya ne da babynsa ko kuwa zuciyarsa zata saduda ya kar’bi abinda ta haifa masa sai ga wani sabon tashin hankali ya kunno kai .”



“yanzu tunda yarinyar maakaciyarsa ce kamata
yayi mu nemeta muganta a zahiri domin tabbatar da gaskiyar da muke nema kafin musan matakin da zamu d’auka akai ai yadda bai bar maryam ta samu natsuwa da kwanciyar hankali ba wallahil azim shima babu shegiyar yarinyar da zai ji dadin zama daita .”suna cikin tautaunawa suka jiyo sallamarsa wanda yayi aciki kuma itace ta katse masu maganar da suke nan take kowacce ta had’eye maganarta cike da tsoro mai tsanani , ahankali ya qaraso cikin parlour’n ya tsaya ,cike da natsuwa yake dubansu fuskarsa a matukar had’e kamar koda yaushe yayinda maryam take dubansa hankalinta na sake tashi “ kawai tunanin yadda zata ga yarinyar take ji take sam ba abu bane mai yuwu ace mafarkinsa ta bayana ,dan bata ta’ba ganin yadda mafarki irin nasa ya zama gaske ba .”yana tsaye yana dubansu cike da zarginsu kira ya shigo cikin daya daga cikin wayoyinsa.ya d’aga yana amsa kiran mami ta dawo parlour’n ta zauna a inda ta tashi tana dubansa a tsanake "Eh muna bada wa !okay zaku iya had’uwa da ahmed zai yi maku qarin bayani akai alright zan maka text din numbersa “. yana gama fadar haka ya katse kiran "ahankali ya motsa lip’s dinsa mami kawai ya gaisar batare daya sake duban sha shin inda yanuwansa suke zaune suna kallonsa ba bare yayi ma har yayi tunanin gaishesu .” zabiba da nana hauwa’u ne suka gaishesa cike da tsoro ,suma kuma bai amsa ba sai faman cin magani yake dan jikinsa ya bashi maganrsa suke abinda suka kasa fahimta ne kenan shi bazai hanasu suyi magana akanshi ba amman ya tsani yaga suna maganrsa agaban wannan yarinyar maryam dan ganinsa wannan raini ne .”



Kallonsa kawai suka cigaba da yi fuskarshi babu annuri, kullum fuska kamar wanda yake cin fushi aunty Khadija tayi maganar a qasan makoshinta
d’an qaramin tsaki yaja kana ya juya a natse ya nufi step yana taku cike da jin kai da isa suka bisa da kallo kamar su saka kuka dan ‘bacin ran da suka gani a saman fuskarshi yayi mugun d’aga masu hankali “mami ta kallesu d’aya bayan d’aya tace "ya naga duk kunyi wani iri haka ?”wallahi mami bama jin dadin yadda adamcy yake nuna mana ki duba fa kigani mu yayyensa ko kallo bamu ishesa ba ,kannensa kuma sun gaishesa yaki amsawa “inji cewar aunty shahida “bai kyauta ba amman ai wannan ba komai bane acikin halinsa da kuka sani me zai hana ku manta da wannan damuwar ku cigaba tsabgoginku tunda kunsan halinsa dan tunda akayi hatsaniyar nan jiya kafin ya dawo daidai sai an d’an kwana biyu ni kaina akwai magana mai mahimanci da nake son mu tautauna dashi amman na barshi har zuwa nan da kwana biyu ,aunty khadija ta soma magana rai a bace “yanzu mami kina ganin wannan wulakanci nashi ba komai bane ?”gsky mami ke kike ganin ba komai bane amman mu agurimu komai ne danuwan mu ne fa “?kuma shi kad’ai Allah ya bamu namiji amman ace bai d’aukemu abakin komai ba .”



"Khadija ki daina cewa haka ya d’aukeku abakin komai mana adamcy fa yana matukar qaunarku duk sanda kuka ga yayi maku haka kuyi masa uzuri ni wacece a wajensa ?”ta tambayesu tana dubansu “nifa na kawosa duniya amman a duk sanda halinsa ya motsa nima yi min yake yanzu ku duba bayan gaisuwa mai ya had’ani dashi ?”amman kuma ya zan masa baa canzawa mutun d’abiarsa da nayi dan haka duk kuyi hakuri idan da sabo mun rigada mun saba da halinsa fatan mu Allah ya canza mana shi inji cewar mami "nima shine abinda na gani tunda halinsa ne mai zai sa mu damu kanmu ni dai idan ba tautaunawarmu yaji ba ai da sauki zabiba ta fad’a tana kallonsu shiru sukayi babu wacce ta sake cewa uffan "maryam kam tunda ta d’aura goshinta akan hannu kujera bata sake d’agowa ba hatta maganar da suke akan ata ta daina fahimtar komai sai hawaye ne ke fito daga cikin kwarnin idanunta suna bin gefen idonta har sanda aunty shahida tai mata magana “maryam tashi mu wuce gida lokaci na tafiya da kyar maryam ta yunkura ta mike tsaye mami da sauran jama’ar dake wajen sukai ta mata sannu “to mami mu zamu wuce gida sai an kwana biyu kuma “to shikenan allah ya tsare haka ma aunty khadija da zabiba sukai mike tare da yiwa mami sallama suka kama gabansu gidan ya saura daga mami sai auta.”


********

Mr ata yana shiga bangarensa takalman qafafunsa kawai ya cire da safa ya fad’a bathroom yayi alwal ya fito ya gabatar da sallahr magarib da isha’i bayan ya idar ya d’aga hannuwansa sama ya soma addua yana mai kaskantar da kanshi a wajen Allah ,allahumma as aluka bi anna lakal hamda laila ailla anta wahdaka lasharika laka ,al mannan ya badi’us-samawati wal ardi, ya hayyu ya qayyum ya zal jalalu wal ikram inni as alukal janna wa auzubika minan nar, Allahu
al wahid ,al ahad ,Allahu assamad, wa ilahukum ilahun wahid ,laila a illahuwar rahmanur rahim “. a qarshe ya fad’i bukatarsa a wajen Allah wadan nan sunayen sune sirrin sunayen allah matukar mutun ya iya fadanci da wadan nan sunayen babu abinda zaka roki allah dasu bai baka ba in dai alkhairi ne . dan a yanzu ya gane yayi sakaci sosai arayuwarsa ta baya shiyasa yayita samun matsala .”bayan ya gama adduar ya mike tsaye ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka ya dan jima ya fito ya goge jikinsa sannan yabi jikinsa da turaraku masu sanyi kamshi sannan ya sanya vest da boxer ya zauna a tsakiyar katifarsa ahankali ya janyo system dinsa da hannu d’aya ya kunna kai tsaye inda na’urorin sadarwar camerorin saman office dinsa suke ya shiga yayi rewarning ya soma duba abinda ya faru a tsakanin nadia da maryama ba komai yasa yayi haka ba sai dan yana son ya gano wani abu .”




Ahankali ya natsu tare da tsurawa screen din laptop din ido ,abinda ya d’aga masa hankali shine mutumin nan mai spray control daya gani tare da nadiya tsaye suna musayar magana har a qarshe ya mika mata wayarta ya fita da sauri ita kuma jin motsinsa yasa ta buya a qarqashin kujera “waye shi din ?”ya tambayi kanshi “yana sake zoomin din fuskarsa mutumin duk yadda yaso yaga fuskarsa ya kasa sakamakon babu inda ya bari a bude dan gabad’aya ilahirin jikinsa a rufe suke haka fuskarsa hatta kwayar idanunshi wani katon glass ne d’an tsiririn hancinsa ne a waje shima bai gama bayyana ba amman dai yasan babu wanda zai kawo masa wannan mutumin sai nadiya lallai shima yana son yasan ko waye shi .kwakwaluwarsa na cikin wannan tunanin mami ta turo kofar bedroom dinsa ta shigo kai tsaye zama tayi a gefensa tare da tsura masa ido “barka da dare sweetheart “barkanmu adamcy ya kake fatan kana lafiya?”lafiya sweetheart"!ya fad’a yana sauke numfashi tare da kashe laptop din gabansa ya rufe ya tsura mata tsumammun idanunshi, sai da mami ta gama nazarinsa tsab sannan tace “mai yasa kake yiwa yan’uwanka haka bayan kasan duk duniya baka da kamarsu suma haka .”



“Mai sukace nayi masu sweetheart ?”basu ce ba amman kai a ganinka abinda kayi masu daka shigo daidai ne ?”kallon arziki baka masu bare ka gaishesu kannenka kuma sun gaisheka suna ka wulakantan su .numfashi ya sauke yana shafa sumar kanshi “mami shigowa nayi naji suna zagina “.zagi kuma adamcy ?”ya d’age mata girarsa daya “alamun “eh !”taya zasu zageka adamcy ?”sweetheart ki tambayesu idan ma zagina zasuyi sai su zauna sunayi dani a gaban wannan yarinyar haba sweet heart “mami ta girgiza kai tana cewa “adamcy rigimar duniya ni dai wannan qiyayya taka da maryam allah ya kusan kawo min qarahenta ,aranshi yace “in sha allahu allah bazai kawo qarshensa ba .ta kamo hannunsa cikin nashi kana ta cigaba da magana “yaushe zaka kawo min yarinyar maryama ?”ya kalli mami yana nazarin maganarta kafin ahankali ya motsa lip’s dinsa yace “maryama kuma ?”ta lumshe masa ido ina son ganinta ka kawo min ita “okay !”ya fad’a atakaice “when zaka kawo min ita “sweetheart may be zuwa next week Insha Allah"Toh Allah ya kaimu next week din sannan sai abu na gaba “ka dinga hakuri da komai adamcy yanzu girma kake yi gashi zaka zama uba "Allah yayi wa rayuwa albarka
"Ameen" ya amsa mata yana tsuke fuska baya son tana masa batun cikin yarinyar, mami ta mike tare da shafa sumar kanshi “akawo maka coffe ko tea ?”kowanne ya samu sweetheart “abinci fa ?”dan qaramin tsaki yaja kana ya girgiza mata kai alamun baya bukata , ta fice tana fita ya dawo parlour’n tare da danna wayar yaronsa ahmed ya kira ya kai sau uku bai dauka ba .”ahankali cike da natsuwa mr ata ya ajiye wayar ya kwanta flat akan kujera tare da rungume hannuwansa ya soma tunani maryama .”



Dare yayi dare amman maryam ta kasa runtsawa juyi kawai take akan gado a qarshe dai ta yunkura ta tashi ta zauan tare da ruqunqume hannuwanta duka a qirji tana tunani ,sosai tayi zurfi cikin tunani mai zai faru idan har yarinyar ta tabbata gaskiya ne ?”maryam !" taji sautin muryar aunty shahida ta kiran sunanta,da sauri maryam ta maida hankalita zuwa bakin kofar shigowa tana amsawa da raunanniyar murya "meke damunki?”tayi shiru kawai zuciyarta na wani irin harbawa da sauri, aunty shahida tayi taku zuwa inda take zaune ta zauan a gefenta tare da dafata tace fad’a min damuwarki maryam “Allah aunty shahida na kasa bacci labarin d’azu da sister ta gaya mana ya hana zuciyata sukuni daren yayi min tsawo sai nake ganin kamar gari bazai wayewa ba ,zuciyata zafi take haka kwakwaluwata ,na rasa natsuwar komai aunty “kada ki damu kanki da maganar yarinyar nan kinji,sannna ki rabu da adamcy zamuyi miki maganinsa da izinin allah yadda ya dasawa zuciyarki ciwo ya hanaki sukuni da kwanciyar hankali muma zamu dasawa zuciyarsa ciwo domin kuwa ciwon 'ya mace na 'ya maca ne, kina wannan halin na yau lafiya gobe babu amman ya hana zuciyarki hutawa wanda a daidai wannan gabar zaki iya rasa rayuwarki .”



Maryam numsafa kawai tana jin wani irin zafi a zuciyarta tare da kai idanunta sama tana kallon dakin d’akin tana sake zurfafa tunaninta “ki daina tunanin maryama ki jajurce da addua domin baki da mataimaki sai Allah “ina addau aunty addua nake amman kullum alamarin sake tsamari yake ni har nagaji da addaur aunty , na rasa me zanyi zuciyata kullum muradinsa take ni bama kaina nake ji ba a halin yanzu abinda ke cikina nake tunanin halin da zata shiga idan tazo duniya “ ta qarasa maganar hawaye na gangaro mata akan kuncinta .”wannan kuma ki qyaleshi ko yaki ko yaso abinda yake cikinki nashi ne kuma jininsa ne idan ya ga dama karya amsa mu dai mun amsa kuma muna so .”sannan duk fushi da zai yi na banza ne zai ma sauko ne ni nasan bazai iya cigaba da fushi da abinda ke cikinki ba sai dai idan bata zo duniya ba

Please Login or Register in order to submit comment