Reading MAR ADAMS BOOK 3 BY AYSHA BAGUDU Chapter 14 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakuri akan ya tsaya ya saurareta” yau ta wuce na zuwa aiki amman gobe idan kaje office ka nemeta ka bata hakurin tozarcin da kayi mata” tana gama fadar haka ta bar dakin dan ya d’an ya samu ya huta tana fita ya mike tsaye yana tafiya yana tunanin maryama yana tunani maganr mami shi gabadaya yanzu ba rasa aikin bane damuwarsa yadda zuciyarta ta mace akan matacce shine babban tashin hankali sa washegari da sanyi jiki ya tashi ya shiga bathroom ya jima a bathtub cikin ruwa kafin ya fito ya goge jikinsa ya feshe ilahirin jikinsa da turarensa REED Kmr koda yaushe ya shirya cikin suit black and milk colour bai daura yar saman suit dinsa ba ya qarasa gaban mirrow ya dauki curm yana taje sumar kansa ya ajiye curm ya dauki agogon ya daura atsintsiyar hannunsa duk jikinsa ya sanyaye yake komai ya manne medical glas dinsa duk abinda yake tana makale aransa ya rasa wani irin zazzafan so yake mata .”


“ina maseefar sonki maryama” ya furta a fili bayan ya gama shirinsa ya tsaya cak yana kallon kansa ta cikin mirrow maryama ya gani tsaye ta cikin mirrow sanye da doguwar riga ja tayi rolling kanta da bakin mayafi fuskarta babu alamun annuri haka zalika babu alamun murmushin nan nata , yayi shiru yana kallonta tayi masa kyau sosai bai san lokacin daya kai hannunsa yana shafa fuskarta ta cikin mirrow zuwa lip’s dinta ba .”nan take ta sakar masa laulausan murmushinta .kokuwa ya shiga yi da numfashinsa ya juya da sauri zuciyarsa na rawa byn Kmr second ya juyo yaga wayam yaga babu ita babu alamunta ya lumshe tsumammun idanunshi “it was imagenation .”ya furta yana sakin numfashi da qarfi “zatazo aiki yau dan jiya an tabbatar masa bata je ba amman yau kam yana ji ajikinsa zataje “? Idan kuma taki fa ? ya tmbyi kanshi “to karita mana kace mata taje aiki kai ma kasan irin haukan daakayi mata zataji tsoron zuwa .”should I called her or not ?ya sake tmbyr zuciyarsa “a’a bazan kirata ba ya furta yana lumshe idanunshi yayi shiru yana zagaye dakin.”



bangaren maryama itama shirin zuwa aiki take saboda umma tun daren jiya ta matsamata lallai taje aiki tunda itace tayi masa laifi bugu da qari ba korarta yayi ba .ta shirya tsab cikin daguwar riga kamar koda yaushe exactly yadda ya ganta a tunaninsa haka shirin nata ya kasance cikin doguwar Riga ja mayafi baki haka baby shoes din da take sanye dashi baki ne agogon hannunta baki ne ta qarasa ta dauki takardan zanenta ta rufe ta saka cikin jakar aikinta ta rataya sai dai ta tsaya shiru tana jin tsoron fuskartasa “ko ya zamu qare yau da mr ATA ? Kinsan irin asarar da kikasani wai Ke dame kike takama ya tsaidaita Kinsan yadda kasuwancina yake da matukar mahimanci agurina gabaday na daura raina akan designs dinki na saka raina nayiwa wanda zaizo yagani alkwari amman sai kika ki zuwa kuma idan na kiraki sai Kiyi rijecting din kirana me ma kike yi anan ki bani amsa .” ?maganarsa ta shiga dawo mata kamar alokacin abun ya faru ta dan ciza harshenta tana jin wani iri ajikinta kamar karta tafi “wannan mutumin yana ban tsoro ta furta a fili .”


“Hakika baka kyauta ba abinda kayi ka kirata ka bata hakuri tun kafin kaje office,no!!akan me kenan zaka bata hakuri bayan itace tayi maka laifi ,aa adam kai ma ka fada mata abubuwa dayawa tô na bata hakuri nace ma me ?kawai sai nace maryama kiyi hakuri akan …”no impossible I can’t gbdy ya rasa yadda zai fuskanceta da wannan kalmar dan tunda yake bai ta’ba bawa wani mutun hakuri ba sai mahaifinsa da mahaifiyarsa saboda me ita zai bata capital NO no !dan haka yayi cilli da wayar akan gado yana duban wayar ai itace tayi min laifi to dan me zan kirata?Kyakkyawar zuciyarsa tace sai me ai ba wani abu bane karka tsaya girman kai akanta ka dai san irin wahalar daka sha tsawon shekaru kana nemanta alhalin tana raye kuma a kusa da kai ma dan ina gra apapa ina agege is not far kai ya kamata ace ka fahimci kayi kuskure dan haka ka kirata nan take wata zuciyar tace “saboda me zaka kirata ai tama fika laifi ita data hada maka Zafi biyu ,ita yakamata ta nemi yafiyarka .”


“Idan mai hankali ce kuma tana bukatar aiki dani ai ya kamata ace ta kirani since tayi apologize abinda tayi amman taki saboda tana tunanin bata aikata kuskure ba. dan haka she’s the one who wil apologize she must apologize” ya furta a fili kuma idan ma taki zan sata dole tayi apologize da wannan shawarar zuciyarsa ta samu natsuwa .”yana tsaye mami ta shigo tana kiran sunansa “Adamcy Nah !kallonta yayi tare da cewa “good morning sweetheart morning my dear fatan ka tashi lafiya lumshe tsumammun idanuwansa yayi ya zagayo ya tsaya kusa daita ta dauki yar saman suit dinsa ta saka masa tana cewa “ kayi aure da ban huta ba ,shima yanzu ban huta ba har sai yashe zaka bar mahaifiyarka ta huta ?sai randa mafarkina ta bayyana ya bata amsa da haka yana kallonta .”



Murmushin mami tayi “wannan mafarki da gskiya ne da zanji dadi kadan “idan ta tabbata gsky ce sweetheart zaki sota kamar yadda kike sona ?” ya fad’a yana cigaba da kallonta yana son yaji amsar da zata bashi “ zan sota mana amman kadan tunda kai ma baka so zabina ba ,son 50 50 zan mata mur mushi ya bayyana akan labbansa “sai abu na gaba “karka manta idan kaje office ka kira yarinyar nan ka bata hakuri ka nuna mata shima Adam mai kuskure ne ka nemi yafiyarta yace “uhm alamun yaji idan ka gama ka sauko kasa abincinka yayi ready .shiru yayi kawai yana tunanin ta ina hakan zai faru “kabi umarnin mahaifitarka zai zame maka alkhairi ki rata tun kana gida kyakkyawar zuciyarsa ta bashi kwarin gwiwa , jiki a sanyaye ya dauki wayarsa ya soma neman layinta tare da tsurawa sunanta idanunshi .”




Mmn sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


             Page 16

Fuskar wayar yake kallo tare da raya abubuwa da dama acikin zuciyarsa ,wani irin abu yake ji yana tsarga masa a gbdy  sansar jikinsa,  sai wayar ta kusan shiga sai ya katse ,yayi haka ya kai sau uku yana katsewa cike da fargaba ya rike wayar a hannunsa yana tafiya acikin d'akin  yana tunani ." maganar mahaifiyarsa ta shiga dawo masa "zuciyarta na tattare da damuwa mai tsanani ,da ciwo a zuciya ba kowa bane zai iya dauriyar abinda ya faru daita .
“Dan hk ka dinga mata hakuri  kana tausaya mata mutuwar miji fa baqaramin ciwo bane ," runtse idanuwanshi yayi sosai yana kiran sunan Allah a lokacin da ya tuna yadda hawayenta ya dinga  zuba akan wani matacce  .”wani dogon tsaki yaja  ya sake cilla wayar akan gado yana sake  jan tsaki  tare da kai hannu ya dafe goshinsa ahankali ya bud'e idanunshi wad'an da suka kad'a sukayi jajur saboda tuno abinda ya faru jiya. kukanta da damuwarta  akan wani namiji wanda bashi ba ."wannan abu yayi matuqar masa ciwo ,qirjinsa na wani quna ya juya wa wayar baya kamar itace tayi masa laifi ."




Ya kamo lip's dinsa na qasa gabad'aya ya dinga taunewa da karfi gashi dai zafi yake ji amman zafin kishin maryama ya zarta zafin da yake ji acikin zuciyarsa ,byn kmr second goma ya sake juyowa  da sauri yana kallon wayar kmr zaiyi kuka ,"bazan ta'ba bayyana miki soyayyata a yanzu ba dan nasan ko na bayyana miki a acikin wannan halin bazaki ta'ba sona  ba amman zan san abunyi ," ya furta a fili yana  sauke wani naunayen ajiyar zuciya ya sake d'aukar wayar stil numberta ya shiga kira yana tunanin  mgnr da zai  fad'a mata da zai sa tazo aiki dan yayi imani tunda bata zo jiya ba tabbas yau din ma bazata zo ba "to idan ina kirata ta d’aga me zance mata ?” ya sake tambayar kanshi yana sake danne lip's dinsa da hakori "idan ta d'auka kace mata tazo   aiki amman karta zo maka  da past dinta , ta  bar komai a gida baka buqata that's all ."



sai dai wayar na daf da shiga ya sake ya katse wa yana sauke zazzafan numfashi ."maryama ta tsaya shiru acikin haraban ma'aikatan tana tunanin hawa sama ,kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana cikin tsananin  fargaba, ita ba wai tsoronsa take ji haka  nan ba kamar yadda sauran ma'aikatan suke rawar jiki idan sun gashi disgi da  tozarcinsa ne bata so kuma shi babu ruwansa ko gaban uban waye shuka rashin mutuncinsa yake kuma kamar bai d'auki hakan a wani abu ba ."da kyar ta tattare jarumta ta sanya ajikinta ta nufi kofar shiga lift byn ta shiga ta shiga, mutane da dama  sun shiga a natse ta danna number inda zata sauka sannan ta ra'be jikinta waje d'aya tana jin mummunar fad’uwar gaba ,kofar na gama rufewa wani sabon fargaba yayi mata diran makiya  gabanta ya dinga luguden bugu har sanda kofar ta  bud'e , sai da kowa ya fita ya barta kamar ta koma kasa amman wata zuciyar ta dinga karfafa mata gwiwa.”


Ahankali ta fito zuciyarta na bata kwarin gwiwa "haba maryam kowa tsoronsa yake ,ya kamata ki zama zaka acikinsu ba wai ki masa taurin kai ba aa ki zama jaruma ."kai tsaye ki shiga office dinsa ko kuma ki kirasa “ta zaro  wayarta ta rike tana tunanin abinda zata ce masa idan ta kirasa   "sir kayi hakuri nayi realize din mistakes dina bazan sake aikata wannan kuskure ba shikenan kina yin hk zai yafe miki ."tana cikin tunanin kawai taji wayarta ta d'auki qara a matukar tsorace ta duba sunanshi ta gani yana yawo a scren din wayar nan take bugawar da zuciyarta take ta qaru yayinda sansar jikinta ya kama kyarma ,amman tayi karfin halin ta daidaita natsuwarta ta d'aga kiran cikin sanyayyar muryarta mai sanyi da bugar da zuciya duk wanda ya saurara  "assalamu alaikum " !.



shiru taji bai amsa ba ,dan a can  bangarensa bai san kiran ya shiga har ta d'aga  ba yana can yana  tunaninsa sai jin sautin muryarta yaji "assalamu alaikum .""hello ta sake maimaitawa duk da yana jinta amman yayi mata  shiru yaki yin magan yana shan kamshi kamar tana gabansa .  ji tayi  kamar ta saki fitsari ajikinta tsabar yadda gabanta yake dukan tara tara ."jin shirun yana son yayi yawa ta sake motsa labbanta cike da girmamawa tace "good morning sir" morning !ya fad'a atakaice yana ciccin magani sannan ya juya ya cigaba da tafiya acikin d'akin batare da ya sake cewa  komai ba." itama shiru tayi .”har kusan second talatin bai ce komai ba ga mutane sai faman wuceta suke suna kallonta dan Allah yayi mata baiwar kyau mai d’aukar hankali da tafiyar da ruhi ,dole ne idan ka kalleta ka sake kallonta sannan ka yaba da irin zallar kyawun da Allah tabaraka wata ala yayi mata .”



ta sauke naunayen ajiyar tana sake duba screen din wayar ta gani ko kiran ya katse ne yasa taji shiru gani tayi still yana kan layi can dai tace "sir ko akwai abinda zakace ne ?"no...sai kuma yace "yes !"what !?
“what do you want to say sir ?ta furta a dan kid'ime shiru yayi yana sauke mata numfashinsa a kunne wanda hakan ke sake haddasawa zuciyarta mummu nar kidima da shiga tashin hankali muryata a matuqar raunane ta sake tambayarsa ” me kake son kace sir ? "abinda zance kizo office akan lokaci "okay  sir ..!kafin tace wani abu ya katse kiran murna da farinciki suka taru suka  lullu’beta ,kafin ahankali tayi shiru tsaye  tana nazarinsa " ko me yake son fad'a mata? kamar ba wannan maganar yaso fad'a mata ba" kai koma dai  menene  matsalarsa ce wannan tunda har ya furta tazo tana  da hujja kare  kanta idan zai tozartata  .""wayyo allah dadi "ta furta a fili cikin tsananin farinciki bai ma san na kusan shiga office ba, allah na gode maka da kasa ya furta nazo  da bakinsa .”



Cike da kuzari ta soma tafiya cike ta shiga office dinsu lokacin kowa ya hallarar "sautin muryarta suka jiyo daga sama "good morning !good morning!!ta furta gbdy suka mike sakamakon ganinta sectary tace "me yasa shekaranjiya da jiya baki zo aiki ba ?”gsky baki kyautawa mr ATA ba kin kunyata shi tunda nake aiki dashi ban ta'ba ganin abokan kasuwamcinsa sun masa haka ba yusura  da surayya duk suka matsota suma dai tmbyarta dalilin rashin zuwa kwana biyu  suke "nima ba haka naso ba  na .."
“ba haka kika só din  wa ba ?”daman dayawa ya'yan talakawa basu iya samun guri ba sannan basu iya d'aukar aikinsu da mahimmanci ba "inji cewar sultana dake zaune tana watsawa maryama wani mugun kallo ajiyar zuciya maryama ta sauke sannan tace "haba sultana gsky banji dadin kalmarki ba rayuwar nan fa da mai arziki da talaka duk daya né a wurin allah babu bambamci sai wanda yafi wani jin tsoron allah ."



Maryama tana cikin wannan bayanin mr ata ya taho a hankali hannunsa daya cikin aljihun wondonsa tun kafin ya qaraso kamshin daddaren  turarensa ya kawo masu ziyara, bai tsaya a koina ba sai a bayan maryama  yana kallonta” tayi kmr zata juyo ya bar gurin kad'an still dai yana bayanta kuma idanunshi na kanta numfashinta kawai take janyowa da kyar tana fesarwa dan gbdy acikinsu babu wanda bai firgita da ganinsa ba kafin a hankali suka shiga gaishesa daya byn daya da girmamawa ."itama maryama ta bude baki da kyar ta gaishesa  dan zuwa alokacin ya dawo gabanta  ya tsaya kyam  yana kallonta sai dai bai amsa gaisuwarta ba illa tsura mata tsumammun idanunshi da yayi ta cikin medical glas  dinsa yana kallonta itama shi din take kallo sai dai ita a dan rikice take ."



“sosai ya tsareta da idanunshi duk tayi masa laifi mai girma amman  kallonta a yanzu ya d’an rage masa kashi hamsin na cikin damuwar data haifar masa sakamakon wani zazzafan kyau datai masa domin sosai kayan dake sanye a  jikinta suka mata masifar kyau gashi dai bata  bayyanar da surarta afili, amman kowani kaya ta saka sai ya zauna ajikinta kuma suyi mata kyau “princess kinyi masifar kyau yau..."ya furta a can qasan ranshi  yayinda ita kuwa tashiga tsananin damuwa dan a zahiri yake iya kallon yadda take hadiyar zuciya
irin kallon da yake mata yasa numfashinta ya soma qoqari d'aukewa "sir ..!tana furta hakan ya juya ya wuceta da sauri ya shige office dinsa .”aiko nan take wani sabon fargaba da tsorone sukayima maryama  dirar mikiya, jitake kamar tasaki fitsari mai wasali a wando tsabar yanda gabanta yake bugawa .”




Yayinda duka wata gaba da Allah subhanahu wata'ala ya halitta ajikinta rawa takeyi,kallo daya zaka mata kagane hankalinta amatukar tashe yaje . qafafuwanta  dake karkarwa ta shiga motsawa ta juya da zumar   zata bi bayansa gbdy sukayo kanta har sectary "karki kuskura ki shiga office dinsa yanzu “ki barshi zuwa wani lokacin sai ki gansa "cikin tsananin tashin hankali tace "karku  damu  ku barni  na gansa yanzu domin  a yanzu ya kamata naje na nemi yafiyarsa ba sai an dauki lokaci ba , idan naki zuwa yanzu  zai dauka cewar da gangan nayi , ko ya d'auka girman kai zan masa ,ku dai kuyi min addaur da fatan nasara tana gama fad’ar haka ta wuce su "uhmm ba dai ya Adam ba sai kin gwamace baki je ba sultana ta fad'a a kasan ranta tana  murmushin mugunta sannan  ta gyara zamanta zuwa kallon office din mr ata tana jiran taga irin korar wulakancin da zai mata."




Ahankali maryama tayi knowking tare da cewa" ko zan iya shigowa sir "abun mamaki sai ji tayi yace "comming "! zazzafan numfashi da ajiyar zuciya ta sauke tana mai  tura kofar glass din ta shiga idanunta kyam  akanshi  tare da maida kofar ta rufe ahankali batare data juya ba, yana tsaye yana waya  ahankali cikin yin kasa da murya  "okay kuna bukatar qarafe kimanin adadi nawa ?okay okay !!
"shikenan zan hadaka da ahmed zan tura masa komai yanzu zai nemeka amman fa bazan qarfi wannan farashin ba zaa sauke komai akan tsare no gsky bazan bada a wannan farshin ba gbdy mun qara  farashin komai namu saboda ingancin abubuwan da muke amfani dasu dan haka ka tura kudi sai tura maka kaya."


Cike da sanyi muryar maryama  ta bude baki "sir ! ya dakatar daita da yatsan hannunsa yana cigaba da magana "ka tsaya ka fahimceni wannan matsalar ba daga gareni bane ,Okay idan yayi maka shin kenan sai najika idan kuma bai maka  ba babu matsala ma hadu zuwa gaba".shayayyun idanunta ta tsura masa tana kallon yadda yake magana a natse cikin harshen tsadadden turancinsa bakinsa ma da kyar yake motsawa har sanda  ya ajiya wayar office yana kallonta tare da qara  girman idanunshi akanta tunda daga kasanta  ya dauki kallonta har zuwa samanta yadda bai ce mata komai ba  haka itama bata ce masa ba saboda gudun wulakancinsa.”



ta lumshe idanunta ta sake rungume littafin dake hannunta "dan kawai ki tsareni da wadan nan idanuwan naki kika shigo min office? "no sir ammm actually actually ..!!sai kuma tayi shiru ta kasa cigaba da magana  "actually what ?"ya tambyeta yana sake tsareta da tsumammun idanunshi ."idan baki da abun cewa kina iya wucewa  ki bar min office dina "no sir  ina dashi daman nazo maka design din shejaranjiya ne  na qarasa shi ajiya gashi nazo dashi ta ajiye agabansa ."tana mai sunkuyar da kanta kasa tare da jin wani sabon fad'uwar gaba mai tsanani ."
"this is totally nonsense maryama  “me zanyi dashi?ya tamvayeta cikin zafin zuciya yana tsareta da kwayar idanunshi .”



ahankali ta dago kanta ta zuba masa idanunta " ki dauke min wannan shirmen daga gabana dan basu da wani amfani a wajena yanzu dan takalmin kafarki ma  ya fishi daraja a wajena  dan hk ki daukeshi banason ganinsa .”tana kallonsa jikinta na rawa dan azahiri ake iya ganin yadda  jikinta  yake rawa  Matsowa tayi kusa dashi kad'an still tana kallonsa tana jin kamar ta kamo  hannuwansa gabadaya cikin nata ta rike ta rarrashesa dan tabbas ta aikata masa ba daidai ba.” manzon Allah sallallahu alaihi wasalam yace “idan aka ‘bata maka ka nuna fushinka dan kai ba jaki bane ." haka zalika idan aka baka hakuri ka hakura dan kai ba sheidan bane sai dai tasan duk abinda zatayi a yanzu bazai sauko ya karbi aikin ba sakamakon mugun taurin kan dake garesa uwa uba zuciya " kin wani  tsaya kina kallona ?”
ta marairaice masa fuska kamar zatai kuka .”



"maryama leave my office right now I don’t want to see your face ." ya fad'a yana nuna mata kofar fita ."
"Dan girman  Allah sir ka sake bani wata dama .”
"babu wata dama da zaa baki domin ke kullum cikin matsala kike sannan  rayuwarki kullum acikin second chance take ko wace dama zaa baki sai wannan mataccen yasa kinyi loose "ya fad'a yana jan tsaki tai shiru tana nazarinsa da mamakinsa ta rasa dalilinsa na daukar zafi har haka akan mijinta "bata gama tunaninta ba ta sake jiyo muryarsa "there's no second chance maryama go back to your  work ."
"am  so sorry sir ..."I said go back to your  work ya fad'a a tsawace "go! ya sake furtawa yana nuna mata kofa da bakinsa jikinta a sanyaye ta kallesa sai dai hankalinta a tashe yake, ta juya da sauri tun kafin ya rufeta da duka dan taga alamun zai iya aikatawa yabi bayanta da kallo kafin a hankali ya zauna akan kujera ya sauke numfashi ya dauki wayarsa dake ringing "yes sweetheart daga can bangaren tace "fatan ka isa office lafiya ?lafiya sweetheart “yarinyar tazo office ne ."?



"yes sweetheart !" fatan kayi abinda nace kayi "? ya juya ya kalli kofar da maryama ta fita  yanzu "ai nasan bazakayi ba ,wacece ni da zance kayi abu kayi min alokacin da nace ? tana gama  fadar hk ta katse yayi shiru kawai yana tuna maganar daya gama fada mata tanzu  "I said go back to your  work yana cikin wannan halin ya sake jiyo  muryarta tana neman izinin , itama  kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali tayi koda ta koma office dinsu bata iya aikata komai ba ,zuciyarta ce  ta dinga azalzatar ta dawo garesa ko zai kasheta gara ya kasheta ta huta."
ya tsura mata ido kawai ganin irin kallon da yake mata ya sake kidima ta tana qoqarin sake juyawa ta fice idanunta suka sauka akan takardar zanen data ajiye masa da hannu ta nuna masa saman table dinsa "sir na manta file dina .”


ya nuna mata da hannunsa alamun ta d’auka tasa hannu ta d’auka "madadin ta wuce sai tayi tunanin ta sake bashi hakuri "kayiwa girman allah da girman iyayenka kayi hakuri akan laifina bazan sake aikata wannan Kuskuren ba idan nayi ka d’auki kowani irin hukunci akaina “ ta qarasa maganar cike da raunin zuciya   wanda adaidai lokacin ya juyar da kanshi gefe ganin hk yasa  itama ta juya cikin sanyin jiki ."
Har  tayi taku biyu  taji sautin muryarsa ta doki dodon kunnenta "am sorry  too for yesterday ."da wani irin mugun sauri ta juyo ta tsura masa ido.”



Mmn Sudais
[8/31, 11:25 AM] Safwan Libiya 2: 💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 17


Tunda mr ata ya furta mata kalmar “am sorry too for yesterday bai sake juyowa ya kalleta ba illa zuciyarsa dake mugun bugawa da sauri sauri, kallonsa take tana mamaki me zai faru ?wannan wani sabo alamari ne ?mr ATA da kanshi ya furta hakuri gareta .?”anya kuwa abinda kunnuwanta suka jiyo mata kenan ?”shine mana to idan shine anya kuwa wannan kalmar daga bakinsa ta fito ?”ta yiwa kanta tambayar ajere tana jifansa da wani sanyayyen kallo zuciyarta na bugun tara tara.kusan suman tsaye maryama tayi a wajen dan tsananin farincikin data tsinci kanta ciki .”ta kasa d’auke kwayar idanunta akanshi ta cigaba da kallonsa rungume da file aqirjinsa”office din yayi shiru tamkar babu wata halitta tsaye agabansa wanda hakan yasa zuciyarta ta fara wasi wasi “kai bana tunanin shi yayi wannan maganar. wannan maganar ba daga bakinsa ta fito ba “.



shi kuwa tunda ya furta maganar ya kasa kwakwaran motsi tamkar wanda aka dasashi zaune kunya da tsananin fargaba tasa shi ya kasa juyowa ya kalleta duk da ta gefen idanushi yana tsinkayo mamakinta "sir did you say anything? ya juyo ahankali yana kallonta qirjinsa na dokawa da kafin gaske sannan ya sake kawar da kanshi gefe muryarsa a kasalance yace "nothing!ko kinji nace wani abu ne ?”idan ma bakace wani abu ba sir ni ina son nace wani abu ko zan iya ce…”?kafin ta kai qarshen maganarta ya jefa mata wani mugun kallo zuciyarsa na bugawa da karfi wanda ya sanyaya maryama gaggawar yanke maganarta babu shiri .”murmushi yayi a ciki yana cewa “ga tsoro ga tsoratar da mutane kalleta kamar wata ta kirki “.



“ganin irin kallon da yake binta dashi yasa ta sunkuyar da kanta

Please Login or Register in order to submit comment