Reading INAAYA (Riba Biyu) by queen meenali Chapter 19 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

anbata danta Abdulsamad Wanda tasaka a makarantar kudi anan lagos Yana karatu cikin kwanciyar hankali da wadata,

Yan uwan salisu da dama yanzu zumunci da hulda sukeyi da ita sosai Dan kuwa Babu qyashi a zuciyarta tana musu Alkhairi,

Yaya Umar da Yaya kabiru sune tsundum aduk Dan abinda ke gareta sbd mj ba mai Zama bane shiyasa daga ita har uwar gidansa uwar yayansa dukiya yake musu sosai.

Ahaka rayuwarta ta sauya Babu wani labari ko bayanin ganin Ayshatouh da Abdul majeed.

Shekaru sunja sosai manyanci yazo akan dole ta dangana ta cire ran ganin Ayshatouh har abada a qarshema ta sanyata cikin adduar datakewa salisu dasu mama na Allah yayi musu rahama.

Abdul baitaba sanin yanada 'yar uwaba sbd zancen da aka rufe gabaki dayansa aka barsa amatsayin qaddarar data wuce.

Dr iklimat tazama uwa kuma 'yar uwa gareta Dan haka bayan mj yayi retire tadawo abuja da Zama Amma sai zaman lfy na Neman gagararta da uwar gidanta Dole aka rabasu ita Takoma Adamawa nata gidan sbd ta nuna Masa tafi ra'ayin Zama acan sbd Kota koma Lagos din tunda yabar Lagos yakoma Abuja ba wani amfani Dan haka tafison Adamawa.

Da wannan ta tattara tadawo adamwa qaton gidanta da MJ yasiya Mata Mai girma daga ita sai Inna da masu aiki sai Dr Abdul idan yazo sbd aiki dayake a asibitin Dr iklimat dake Abuja.

Yaya Umar da Yaya kabiru ma tuni suka zama cikakkun masu rufin asiri da Yar wadata ta sanadin mijin Hadizan daya sakasu cikin wasu Yan haurkokinsa na business Kuma suna samu sosai aciki Dan haka suka sake tsayawa sosai akan duk wata hidimar Hadiza da iyalinta duk da Bata sake haihuwaba tun tsawon shekarun Wanda Dr iklimat tayi Mata bayanin tasamu matsala tun wancan lokacin data samu matsalar gaba ba lallai takuma haihuwaba shiyasa ta dauki tsananin son duniya ta dorawa Dr Abdulsamad sbd ga dukkan alamu shikadaine Dan dazata samu a duniya.

WANNAN SHINE ASALIN ABINDA YAFARU.


***************************
Tsit kowa yayi Banda kukan Haj umma Dana Hadiza saina umma yaganah Babu abinda yake tashi.

Alhaji babbah da cm dama sauran duka mazan gurin duk jarumtarsu jikinsu saidaya yayi tsananin sanyi.

Cm da umma yaganah ne suka Dora da irin gwagwarmayar wahalar rayuwar dayaSha iya wadda suka sani gurin kulawa da Inayah da sauran wahalhalun har arzikinsa.

Duk Wanda yake gurin ya jinjinawa AA MAJEED da irin karfin zuciyarsa.

Ita kanta hadiza jikinta sanyi yayi tareda sabuwar danasani ga girmansa daya cika Ido da zuciyarta sbd duk Wanda ya riqe 'Yar dabai hada komai da itaba irin hakan Basu taba tunanin zaa samu Mai wannan zuciyarba.

Tun farko nutsuwar da zuciyarta tayi dashi a ganin farko yasata guduwa tabar Masa 'yarta batareda tunanin komaiba Amma bataba dauka kyan zuciyarsa da karfin zuciyarsa yakai hakan ba.

Hawayen kunya da damuwar abinda tayi dama na tausayin kanta dana majeed take tsayayowa tana sunkuyar dakanta qasa sbd Babu Kuma wani abun fada daya ragewa kowa.

Hajiya umma tafi kowa shiga baqin ciki da Dana sani sbd ko a bayan da hadiza tadawo neman yarta tafada musu gaskiyar su juwairiyyah Basu Bari hajiyar ta yarda da duk abinda Hadiza ta fadaba shiyasa suka hanata bayyanarda damuwarta akan rashin majeed dinta da karfi da yaji Amma tun daga wancan lokacin Bata Kuma isashiyar lafiya ba sbd ciwone da qunci a dunkule ranta na 'danta datafi so fiyeda komai da kowa.

Su Yaya Umar kusan sunfi kowa kunya da baqin cikin abinda suka aikata dan kuwa kusan sune sanadin komai Dan tun farko dasun rungumi qaddarar Yar uwarsu da duka baa cutatar da wanda baijiba Bai ganiba aka tarwatsa Masa rayuwa aka rabasa da iyayensa.

Alhaji babbah yaji tausayin MAJEED da Hadiza fiyeda kowa sbd kusan kowa mafita take nema a halin matsuwar dasuka shiga Amma tunda kusan komai yazo qarshe Kuma kowa wahalarsa ta wuce tazama tarihi sai kawai a rungumi qaddara sbd duk wannan Al'amarin idan anduba rabon aurene dake tsakanin majeed da Inayah yasa komai yashigo ta hanyar tsanani.

Anty juwairiyyah kunya da takaicin Hadiza harma Dana 'yarta ya hanata cewa komai har zaman ya tashi kowa ya watse aka bar Yan gidan kawai sai Haj umma da Babu Inda Zata sai 'danta yadawo Dan bazata iya sake tafiya tabar majeed dintaba sanyin idanuwanta dayaSha gwagwarmaya da wahalar rayuwar duk tarin arzikinsu.

Ta bangare daya jin tayi zuciyarta na Dan qonuwa da Inayah sbd akanta 'danta ya zabi ya barta,

Ya bar mahaifiyarsa sbd ita,
Ya fifita kaunarta Mai tsanani da duk duniya tasan da Babu abinda yake kauna sbd ita duk da tayi imanin da kaunarta na qasan ran majeed dinta sbd bazai taba daga so da kaunar wani akantaba.

Amma Kuma duk da hakan ya fifita Inayah akanta qarshe yanzu karshen rashin rabuwa ya aureta Wanda ita Sam batajin danta ya cancanta wannan auren sbd tako Ina danta ya cancanta rayuwar Jin Dadi da farin cikin daya rasa shekaru.
##MAMUH#
#HOT LOVE/ROMANCE
#MAJEED/INAYAH





_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107[11/7, 11:34 AM] +234 805 800 0496: *_44_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Inayah da kafafuwanta suka kasa riqeta sbd kukan datake Mai tsanani Mara sauti ahankali ta juya tana dafa bango ta nufi dakinta...

Daqyar ta iya Kai kanta daki sbd ko ganin gabanta batayi sbd kuka hannuwanta na toshe da bakinta.

Tana Isa bakin gafo ta silale Wasa ta zauna tana sake sabon kuka.

Abbinta kawai zuciyarta kewa wannan kukan sbd sam ita batajin tanada wani abun tausayi tun jarinta har yanzu sbd Abbinta bai taba Bari ta Zama abar tausayawaba tun tana cikin zanin goyan da uwarta ta yarda ita ta tafiyarta.

Taji tausayi da kaunar mahaifiyarta saidai Kuma har lokacin kaunar kaunar Abbinta daban take a ranta Musamman yanzu datake qaunar tasa na qara nauyi da cikin ranta Dan kuwa har abada Batajin Zata karbi mahaifiyarta matuqar ba abbin ne ya yafe Mata ba ya hadata da ita.

Neesah ce ta fito toilet taga yanda Inayah din ke kuka ta qaraso tana kallonta cikin mamaki da firgici tace"

Lafiya?
Wani abin yakuma faruwa ne?
Haryanzu Baki samu abbin bane a waya?

Kasa magana tayi ajiyar zuciya datake jerowa idanuwanta sunyi jajir.

Umma yaganah ce tashigo dakin fuskarta jajir da alamar kukan datasha sbd tausayin MAJEED datake Jin itama kaunarsa da girmansa  sun ninku a ranta sbd ya tabbata Mai tautasayi da kyakkyawar zuciya duba da yanda itama ya riqeta da Maigidanta kafin ya rasu har zuwa rayuwarta daya Gama ingantawa yazama gatanta Mai kare mutuncinta da martabarsu yabasu suna da mutunci a idon duniya.

Tabbas har abada daga ita har Inayah basuda tamkarsa Kuma zasuci gaba da Zama a qarqashin ikonsa da sunan Daya Basu,
Yazama ubansu gatansu Kuma zaici gaba ra zama hakan har abada da yardar Allah.

Inayah na ganin umma yaganah ta sake fashewa da kuka tana fadawa jikinta tana cewa"

Umma yaganah Abbina nakeson gani kawai yanzu,.bana samun wayarsa Dan Allah ki kirasa yadawo gida na Dena duk wani rashin jin magana,,,
Ni har aurenma na karba zanyi auren dashi Dan Allah kice ya Dena fushi Dani yadawo.

Umma yaganah data kasa cewa komai bayanta kawai take Dan bubbugawa tanajin kaunarsu su dukan duk da Inayah tako ina bata Zama abar tausayiba Dan kuwa rayuwarta tagama samun haske tunda MAJEED ya tsaya Mata.

Umma yaganah Bata sake Jin tsananin kaunar auren MAJEED da Inayah dinba sai yanzu Da komai ya bayyana.

A duniya Babu Wanda ya cancanta da Inayah dai Abbinta majeed Wanda shi wannan auren ya zamarwa dukkaninsu RIBA BIYU.

Rarrashinta umma yaganah tayi tareda Neesah wadda take sauraran maimaicin zancen komai abakin umman wadda ke fadawa Inayah komai batareda tasan taji komai ba.

Sun jima a daki suna rarrashin juna kafin a dakin Inayah din dayafi kowane daki girma da tsaruwa a gidan Banda na Abbinta daya banbanta da nata ta hanyar tsarararren palonsa dake hadeda master bedroom dinsa Wanda shima komai na cikinsa milk ne sbd tsananin tsaftarsa yafison komai me haske bazai bayyanar Masa da komai qaqantar datti Dan ya rabu da ita.

Gidan tsit kaman ba kowa saisu zubbi da Salimat dake aikin kaida kawon abinci da maimaicin tsaftace gidan,

Haj umma da Anty juwairiyyah na daki
Anty juwairiyyah sai kame kame takeyi sbd kunyar kanta data mahaifiyarsu saidai Kuma tana maimaitawa Haj umma girman lefin MAJEED dayaqi waiwayo gida ya zabi 'yar tsintuwa akan mahaifiyarsa.

Itadai Haj umma Bata tankataba sbd yanzu Babu wani Hadi dazai sake rabata da 'danta ciki kuwa harda Inayah wadda ta tsaya Mata arai sbd kaunar da aketa maimaita majeed dinta nai Mata.

Sai dare kowa ya fito cin abinci suka hade a dining kowa na kallon dan uwansa Banda Inayah wadda kafin ta fito sai yawon zuwa kiranta tazo taci abinci kowa keyi daga umma yaganah har masu aikin da Neesah.

Saida suka fara cin abincin ta fito sanyeda Gucci Riga da wando gajere Wanda ya bayyanarda fararen qafafunta masu kyau da lafiyar fata.

Rigar batada Fadi sosai Kuma Bata saka bra ba sbd kusan Shirin baccine tayi.

Slippers ne a qafarta da wayarta a hannu tana sake saka Kiran Abbinta Wanda duk yakira bai shigaba sai idonta yacika da hawaye.

Qamshinta kawai yasa Anty juwairiyyah sake Baki tana kallonta sbd tasan Qamshin Turaren da tsadarsa tunda tana yawon qasashe.

Haj umma kuwa kayan jikin Inayah din da yanda take wani irin Bata fuska kaman zata fasa kuka take kalla cikeda mamaki,

Lallai yarinyar tasamu sake fiyeda yanda suke tunani.

Zama Inayah tayi Kai tsaye batareda ta kalli anty juwairiyyah ba ta gaida haj umma da cewa"

Haj umma Ina wuni?

Ita kadai ta gaida Dan haka kowa yayi tsit,

A natse hajiyar ta amsa itama batareda takuma kallontaba.

Cikin daure fuska umma yaganah tai Mata nuni da juwairiyyah wadda ke juran Inayah din tawi gaidata Tai mata fada tatas ba ruwanta da gatan dataga yayiwa yarinyar yawa.

A hankali ta gaida anty wadda ta haifeta nesa ba kusaba Dan kuwa yarta ta fari ta girma Inayah din sosai.

Wannan auren datakeyi yanzu yayanta biyu Dan haka yayanta uku
Auren ne irin na yayan masu kudi bawani Zama takeyiba kusan koyaushe taso tana gidansu kokuma yawon wata qasar dauko kayan business,

Anty safiyyah ce kawai take Dan Zama gidanta itama sbd aikinta datakeyi Dan haka Bata wani yawo ko tafiya sai wadda ta danganci aiki
Itama yayanta uku bayansu Bata qaraba ko yanzu da Alhaji babbah dakansa ya aiko nemansu Bata samu biyosu Haj umma ba sbd aikinta da Bata Wasa dashi shiyasa sukazo su kadai.

A taqaice anty juwairiyyah ta amsa gaisuwar tana zuba abincin dazataci.

Zubbi Inayah tafara zubawa tuwon semo da vegetables soup dataji Naman rago da ganda da kifi.

Tana Gama zuba Mata ta kawo Mata ruwa Mara sanyi dan ita batashan ruwa Mai sanyi
Yana daya daga cikin koyarwar Abbinta tun tana qarama baya barinta da sanyi kowane iri ne sbd sanyin dayaso shigarta tun tana jaririya.

Da spoon takecin tuwon Dan haka hankalinta ya rabu akan abincin da wayar hannunta.

Dungurar da wayar tayi da qarfi akan dining tana sakin qaramin tsokin rashin samun Abbinta Dan zuwa yanzu hankalinta yafara tashi da rashin jinsa.

Sudai su Haj umma mamakin duniya yagama cikasu da kallon Inayah wadda shagwabar da ita da akayi take a fili...

Budurwar yarinya likita guda Amma duka halayyarta da dabi'unta kaman wata qaramar baby.

Bata Gama cin abincinba ta miqe zatabar gurin umma yaganah ta dakatar da ita cikin kulawa tace"

Inayah Ina zaki bakici komaibafa a abincin?
Meyasa kike Wasa da cin abinci yanzu?

Shi abbin naki idan yaji bakya cin abinci aikinsan fadan dazaiyi.

Ba dazu kika Gama cewa afadawa Abbinki kin daina rashin jiba?

Dawo zauna kici abinci.

Zubbi da sauri tasake matsowa cikin kulawa tana kokarin zuba Mata wani abincin sbd wannan ya huce
Inayah din tace"

Barshi zubbi zanci wannan din ahaka.

Dawowa tayi badan tasoba ta zauna tana tura abincin.

Kasa riqe mamaki anty juwairiyyah tayi tana Satan kallon Haj umma cikin ranta tana cewa"

Akwai matsala kuwa babba Dan haj umma tazo qarshen kishin 'danta kila Dan wannan yariyar da alama tagama nisa a tabara Mai lasisi gurin MAJEED.

Koda aka gama cin abincin Saida umma yaganah tasa aka hada fruit salad takaiwa Haj umma daki da kanta harya zauna sukai Dan fira duk da bawani fuska sosai gurin Haj umma din.

Danta MAJEED kawai take buqatan yadawo ta rungumi abinta tashafa kansa ta tsiyayar da hawayenta na shakarun rashinsa dake qasan zuciyarta.

Inayah kuwa hankalinta tashi yayi sosai Dan hakan Bata taba faruwa da itaba na rashin Jin Abbi Kuma Bai sanar da itaba Ina yatafi Dan haka hankalinta yayi masifan tashi daqyar taga safiya.

Duk Wanda yake gidan tun qarfe 6 na safe ta tadasu bacci da tashin hankali harsuma duk saitasa hankalin kowa yatashi sbd kowa yakira wayarsa baya samu

Kosu Haj umma dake basuda numbernsa anbasu kowa yayita Kira baa samu.

Kuka da tashin hankali Babu wanda Inayah bata shigaba ba shiri aka nema CM suka Samar dashi.

Baiso sanar musu tafiya AA din yayiba Saida yaga yanda Inayah ta dagawa kowa hankali tukuna ya kwantar musu da hankalin tafiya majeed din yayi Kuma wayarsa da basa samu sbd layin baya Aiki acan ne.

Hankalinsu ya Dan kwanta anty juwairiyyah Saida tayita fadan yanda Inayah ta dagawa mutane hankali Batasan Haj umma nada hawan jini bane Zata kashe musu ita tunda batada asara.

Itadai Inayah batace komaiba sai Haj umman dataje tabawa hakurin daga Mata hankali datai taqara da cewa bazata sake ba.

Har dare ma still abbin bai kirasu ba haka jiki amace Inayah ta kwana,

Washe gari neesah Zata wuce Dan haka itace da kanta takaita airport tareda Safnah suka rakata ta wuce.

Daga airport gidan anty Hafsat suka wuce.

Acanma anty Hafsat rarrashinta tayi tareda Bata qwarin gwiwa akan auren a fakaici Dan kuwa suma basusan yaushe wannan auren zai Zama cikakke ga ma'auratanba Amma dai kam Zata dage gurin ganin ta ingiza Inayah tako Ina tunda baruwan Inayah din ba doguwar Noke Noke ta iyaba
Babbar matsalar da fargaban na gurin AA MAJEED Wanda kwata kwata matan ne basa gabansa bare Inayah dayakewa kallon 'yar cikinsa.

Sai yamma tadawo gida bayan umma yaganah tayita kiranta tadawo gidan hakanan.

Koda ta dawo anyi sallar magriba Dan haka daki ta wuce Kai tsaye tayi alwawala tayi sallar magriba ta zauna tana sake gwada kiransa Dana Neesah Amm duka Bata samesuba.

Ajiye wayar tayi ta nufi dakin Haj umma ta gaidata kafin ta fito ta wuce dakin umm yaganah ta taddata tana waya da Yan uwanta dake maiduguri.

Zama tayi gefenta tan saurarenta harta Gama tukuna tace"

Umma yaganah ke kisake gwada Kiran Abbi ko zaa samesa.

Bara mugani to"
Nemo numbernsa tayi tasaka Kira Amma Bata shigaba Dole suka hakura.

Fira umman kewa Inayah Mai Kama da nasiha saiga Kiran Hadiza yashigo wayat umman ta kalli Inayah tace"

Ga mahaifiyarki Nan nakirana.

Dauka tayi da sallama suka gaisa Hadizan ta tambaya ko AA MAJEED din yadawo daga tafiya umma ta sanar Mata Bai dawoba.

Inayah ta tambaya cikin sanyin murya da jiki.

Kallon Inayah umma tayi kafin tace"

Lafiyanta kalau gatanan zaune Bata nabata ki gaisa.....

Aa,aa kyaleta tunda naji lafiyartama ya Isa zanci gaba da jira har AA din yadawo kaman yanda nayi alqawari Inshallah Zan jira sai ranarda ya yafemun ya hadani da ita Dan kansa Zan tunkareta.

Tausayin Hadizan yasa umma Dan rintse Ido tana cewa"

MAJEED baida matsala Inshallah idan Anbi komai a hankali zakiga da kansa zai hadaku.

Godiya Hadiza tayi kafin sukai sallama suka aje wayar.

Inayah shiru tayi batace komaiba
Itama umman tana aje wayar batacewa Inayahn komaiba.

Tashi sukai Sakai sallar ishai suna gamawa Inayah tayi dakinta jikinta a mace tanajin wata irin damuwa da tashin hankalin rashin ji daga Abbinta.

Wanka tayi tana fitowa ta sanya D&D off-white Riga da wando masu Dan kauri Amma guntaye Dan wandon Bai Gama kaiwa gwiwarta ba Amma yanda Fadi sosai
Rigar kuwa daidai jikinta ce saidai yau tasaka condom bra.
Kanta farar qaramar wulace akanta data bayyanarda kusan Rabin gashinta dayake sauran gyaran aurenta har lokacin.

Slippersta ziro ta fito qamshinta Mai dadi Yana tashi daga jikinta ahankali.

Tun kan ta iso palon anty juwairiyyah tajiyo Dan qamshinta Dan haka ta waiwayo tana tallon hanyar kofar dakin Inayah din.

Dukkaninsu me zaune a palon har Haj umma da umma yaganah sun Dan zatawa sama sama.

Zuwansa yasa Haj umma kallonta ta dan dauke kai sbd kayan Inayah din kullum Babu na arziki tasaba da rayuwar turai da sakewa a gida ba ruwanta.

Umma yaganah data lura da yanayin haj umma da Anty juwairiyyah dakewa Inayah kallon mamaki
Saita miqe a Dan fuske ta kalli Inayah zatai Mata magana aka bude kofar palon Kai tsaye Wanda yasasu juyawa duk su dukan sbd Babu mai shigowa Kai tsaye batareda Danna doorbell ba idanba Mai gidanba dakansa.

Cikin nutsuwa kuwa yashigo sanyeda black Armani's fuskarsa fes tana daukan idon kwarjini Mai tsanani,
Take qamshinsa ya doke Wanda Inayah tacikasu dashi.

Cak kowa ya miqe suna kallonsa dukkaninsu shima cak din ya tsaya yana kallonsu.......

Inayah data Gama kallonsa cikin tsananin farin cikin ganinsa da Murna taje a guje ta fada jikinsa ta maqalqalesa da wata irin kyakkyawar rungumar datasashi dafa kofa.
##MAMUH#



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/7, 11:34 AM] +234 805 800 0496: *_45_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Kofa ya dafa da kyau sbd ba zato yaji ta jikin nasa....

Yaune Karo na farko data rungumesa tunda tayi girma tazama budurwa sosai,
Kuma yau shine Karo na farko da mace ta taba rungumarsa har kirjinsa dana mace ya hadu.

Saurin janyeta yayi daga jikinsa Yana kallonta cikin yanayi na Dan kame yanayin da dan fada kadan yace"

Ki nutsu mana,
Bakya girma ne haryanzu Inayah.

Bata fuska tayi idanuwanta nacikowa da hawayen dabatasan Kona menenba ta sake riqo hannunsa tana riqewa sosai tace"

Abbi kasan yanda hankalina yatashi da tafiyar Nan taka?
Kowa anan yadamu Amma nafisu damuwa sbd baka taba fushi Dani irin hakaba...

Tafin hannunta ta sake sakawa cikin nasa tafin hannun ta riqe tana cewa"

Dan Allah kayi hkr Abbi bazan sakeba.

Dagowa yayi Yana kokarin janye hannunsa duk da tasaba riqe hannunsa sosai ko bayan girman nata Amma yau din akwai mutane.

Kasa amsa Inayah din yayi idanuwansa nakan matarda yake son tabbarda idan mahaifiyarsa ce daya rasa shekaru masu yawa,

Ummansa da Babu lakacinda zaizo qasar baije ya bincika lafiyartaba yaji yanda take agurin Mai gadin gidan Wanda ya tabbatar Masa da Karya taba fadawa kowa zuwan nasa.

Anty juwairiyyah da ita mamaki da takaicin duniya yayi Mata yawa na Inayah ya kalla ya tabbatarda itace take ya yarda da ummansa ce agabansa cikin gidansa Yaka gani.

Sukuwa dukkaninsu mamaki rashin kunyar Inayah sukeyi Mai girma Banda umma yaganah datasan halin kayarta tasaba da hakan Amman yau abin yayi wani irine sbd agaban hajiyar MAJEED dinne da yayarsa Wanda data kusada Inayah yashigo riqeta zatayi bazata Bari tajeba koba komai ga kayan dake jikinta dasuka Santa su hajiyar mamaki tun farko Dan su komai Inayah tayi haryanzu a mazaunin rashin kunya da da'a suke sanyashi duk da sunada wayewa suma sunyi yawon qasashen Amma dai na Inayah ciwo yakewa Haj sbd kishin kusanci da gata Mai tsanani da MAJEED yayiwa Inayah.

A hankali cikin nutsuwa da yanayin na mamaki da bayyanarda rauni sosai Wanda su Inayah Basu taba ganinsa dashiba ya tako ya nufi gurin hajiya umma Yana sake danne zuciyarsa ga raunin dayake bayyanarwa sbd baisan dalilinsu na Neman Inda sukeba sukazo...ko haryanzu fushi ummansa keyi dashi.

Haj umma data fara hawayen ganin 'danta daya rabu da ita Yana matashinsa yazama tamkar babban mutum,
Yazamar Mata wani kamilallan Alhaji komai nasa ya rikida Yakoma tamkar mahaifinsa lokacinda yake daidai shekarunsa.

Kasa jiran ya Isa gabanta tayi sbd sanyin jikin daya nuna na shakkar fushinta akansa
ta tako ta qaraso gurinsa itama da sauri ta rungume abinta tana fashewa da kukan farin cikin ganinsa da jinsa.

Akaro na farko tun Bayan barinsa gida Yana dan matashinsa daya zubarda hawaye daga idanuwansa.

Mahaifiyarsa dayake tsananin kauna a duniyarsa ta yafe masa,
Ta sauka daga fushinta na shekaru,
Yau itace agabansa tana kukan farin cikin ganinsa.

Daqyar hajiyar ta sakesa ta dago tana kallon fuskarsa da shima ita yake kalla muryarsa a sanyaye yace"

Umma..kin yafemun?

Gyada Kai tayi da sauri tana hawaye tana murmushi duka alokaci daya tace"

Na yafe maka MAJEED,
Na yafe maka,
Nice nayi kuskuren bakaiba..

'dana yadawo gareni ya Allah nagode maka.

Ahankali ya Dan sunkuyar dakai Yana hadiye hawayensa cikin nutsuwa da farin ciki Mai yalwa shima yake yiwa Allah godia,.

Kuma dagowa yayi ya kalli anty juwairiyyah dake tsaye itama tana kallonsa duk tunanin duniya ya ninku akanta sbd ganinsa ya tabbatar Mata da arzikin dasuka gani ma kenan Wasa ne,

Majeed din yakoma wani hakimtaccen namiji Mai zallar kwarjini da cika ido,

Ita kanta datake yayarsa Jin tayi tana Neman kasa hada Ido dashi Saida tayi da gaske Bata Ankara ba taji bakinta na furta"

Sannu da dawowa MAJEED.

Qayataccen murmushinsa yasake cikin nuna farin cikin ganinta itama ya miqa mata hannunsa daya Yana cewa"

Ina farin cikin dawowarku rayuwata kema anty juwairiyyah.

Dayake sun saba da shaking hannuwa tun suna Dan kaunar juna Dan haka ta miqa hannu takama nasa tana bayyanarda farin cikinta na ganinsa itama.

Hannunsa cikin na hajiya da Anty juwairiyyah ya juyo ya kalli umma yaganah da Inayah dake tsaye tana kallonsa da idanuwanta dasuka Dan sauya da yanayi Dan Jin wani iri Abbinta zai Zama ba nata Ida kadaiba yanzu tunda family dinsa zunzo Bayan tasaba da Baya hadata da kowa bare komai.

Kasa sakinsa hajiyarsa tayi Dole anan suka zauna duk da gajiyar tafiyarsa ta sakesa take sbd farin cikin ganin mahaifiyarsa.

Cikin nutsuwa da sanyinsa yace"

Umma yaushe kukazo?
Waye yakawo?
Ya kukasan Nan?

Cikin farin ciki tace"

Majeed bazan taba iya rabuwa dakaiba yanzu sbd haryanzu Bayan ganinka ciwon da zuciyata take na rashinka Bai dainaba..

Alhaji babbah da kansa yayi aikin mutum har gida aka taho damu Bayan Kiran waya dayayita yimun..

Banda zabi Bayan zuwa din sbd Nima Ina Neman 'dana Ido rufe,

Meyasa katafi baka dawo gareniba MAJEED?
Meyasa baka taba waiwayataba majeed?

Kuka ta fashe dashi tana bayyanarda tsananin radadin da zuciyarta tashiga na rashinsa duk tsawon lokacin.

Anty juwairiyyah ce dashi suka ringa rarrashinta Yana sake Bata hakuri akan kuskuren rashin komawa dakuma kuskuren zaban tafiya yabarta,

Bai tsaya Jan tado zancenba ya yarda da suka shine mai lefin yabata hakuri tareda alqawarin insha hakan bazata Kuma faruwaba.

Umma yaganah ma ta Dan saka baki tasake bawa hajiyan hakuri da adduar Allah ya tsare gaba.

Inayah data matsu sugama tayi magana da Abbin ta matso tareda Zama gefensa daya tana kallonsa cikin yanayin son magana zatai magana ya Dan saci kallon hajiyarsa Dan yasan idan ba yanzu ta sauyaba zataji damuwar shigewar da Inayah Tai Masa Dan haka cikin Dan kulawa da nutsuwa ya kalli Inayah din yace"

Inayah kina gaida hajiya yanda yakamata tunda tazo kuwa?

Kallon hajiyar tayi tace"

Eh Abbi kullum safe da yamma har dare ma wani lokacin.
Kuma tare muke cin abinci a dining.

Dan murmushi yayi Yana cewa"

Kin kyauta to.
Jeki ki saka kayan sanyi
Ana wannan sanyin Zaki fito haka?

Umma yaganah ya kalla yace"

Da mutane a gida shine take yawo hakan?

Kallon Inayah tayi tace"

Kasan Inayah ba Jin maganata takeyi sosaiba.

Abbi banajin sanyi fa,
Nidai Zan sauya Kaya Amma saika yafemun kadaina fushi Dani,
Abbi Dan Allah kayi hakuri ka daina fushi Dani wlh nafadawa umma yaganah nayi alqawari ko sunan Heart bazan Kuma ambataba,

Ni har aurenmu ma na karba zanyi
Amma Dan Allah Abbi ka yafemun.....

Hawaye tafara tana riqeda hannunsa cikin yanayi da dana sanin lefin data aikatadin duk da batasan takamaimai akwan wanne daga cikin lefin take fushi da itaba.

Nauyin mahaifiyarsa mai tsanani yakeji Musamman ganin duk sunyi zuru suna kallon ikon Allah Dan Inayah dinnan tafara wuce tunaninsu
Gashi kaman majeed din biye Mata yake da alama shiyasa tabarar tata take yawa.

Zame hannunsa yayi Yana kallon umma yaganah yace"

Kuje ciki zamuyi magana gobe idan na nutsu.

Gangarowa hawayen Inayah sukayi tace"

Abbi gobe?
Nidai bazan iya bacci ba idan baka dena fushi daniba ka yafemun.

A natse ya juyo ya kalli fuskarta cikin kulawa yace"

Bana Hana wannan kukan ba?
Kije ki saka kayan sanyi
Anjima zamuyi mgn.

Ok Abbi" tace muryarta a sanyaye.

Tashi tayi ta wuce umma yaganah tabita suka Basu guri yabisu da kallo kadan sbd yasan Inayah saitayi kukan idan suka Isa daki.

Baki sake Haj umma suke kallonsa
Ya dawo da kallonsa kanta Yana sake Jin farin ciki.

Bata Bari Inayah tashiga damuwarta akan danta ba sbd tasan Babu Wanda zai taba samun matsayi irin nata a zuciya da rayuwar 'danta.

Anty juwairiyyah Kuma mamaki da tunanin zaman da Haj tace zatai a gurin 'danta takeyi Dan kuwa akwai matsala.

Haj na kishin 'danta
Inayah ma da alama batason kowa ya rabi Abbinta sbd ta taso da kaunarsa da kulawarsa akanta ita kadai Bai taba hada kaunarta da kulawarta da komaiba Dan haka a take tagano Inayah ma zatai kishin wani ya rabi Abbin nata Wanda yake mijinta yanzu duk

Please Login or Register in order to submit comment