da ko daya. To don haka ruſawa kanki asiri, ki iya
da rigimar da ke gabanki, kar ki kara janyowa kanki wata. Da
wannan tunanin na shafawa kainalafiya, na kuma dauka a raina
ccwa wani abu ma bai faru ba. To amma yayin da gari ya karc
wayewa, sai na ji ina son zuwa na kara ganawa da mutumin.
Ba tare da na yi wani kokonto ba, sai na sanar a mahafiyata
cewa za ni unguwa, ce mata na yi wajen Nusaibah za ni, ba ta
nemi hana ni ba, domin ita kanta ta kan so na fita, a fadinta da
yin haka zan hadu da mijin aurc.
Ban dakata a ko'ina ba, sai cibiyar bincike, ofishin
mutumin na nifa kai tsayc. Ina zuwa na kwankwasa, aka yi
min izni da na shiga shigartawa ta jefa ni wani rudanin
dabam. Ba shi nc a ofishin ba, wani mutumin nc da ya fi shi
karancin shekaru. Na dafa bango zuciyata cike da damuwa.
Mutumin na fara gayarwa, daga bisani na nemi wanda na zo
don shi. Kame-Kame na yi ta yi, sakamakon rashin sanin suna.
Ilujjar da na kafa ita ce bayar da kamanni, sun taimaka kwarai
wajcn sawa mutumin ya amince da ni. Abin da ya sanya shi
shaida min cewa ya yi 'yar tafiya zuwa Abuja. Da na tambaye
shi sababin tafiyar yace bai sani ba. Yaushe zai dawo? Nan ma
babu amsa. Da haka na bar cibiyar a cikin takaicin rashin cin
nasarar abin da ya kai ni. Tun da na tun karo gida na yi arba da
wala jibgegiyar Jeep. Ko tantama ba na yi abokin Abbah ne ya
zo. Ban yi mamaki ba, domin kuwa mulum ne na mutane. Na
yi yunkurin shiga gida sa'arda zuciyata ke ta sake-sake, ko
shakka babu mutumin nan yaudara ta ya yi, da na yi azarbabin
ba da labarin da na kare da kunyata.
"Yawwa! Da ma ke zan je na kirawo" Ilabib kenan da
muka hadu a sorо.
'Me ya faru zaka tafi kirana?""
"Bako kika yi, yana sitting room yana jiranki
Na yi tsaki gami da karawa gaba, "Kai ni babu wajen wani
bako da za ni, na gaji da bata lokaci a banza"
"Yaya! Ya kira ni
Na waiwayo a fusace" Me nene?"
Ya yi murmushi baki san kowayc bakon ba, shi ya sa ki
ka fadi hakan'"
Na sake yin tsaki "koma wanenc ya yi tafiyarsa, ni ba ni
da lokacin ganawa da shi"
Sai na kara kada kai na yi gaba. A guje Habib ya zo ya sha
gabana "Yaya Abdul ne fa"
Kirjina ya buga da karfi, sakamakon jin abin da ban
shirya jinsa ba. Ban san sa'arda na gigice ba, ji kike kau! Na
kwadawa Habib mari 'kai ina wasa da kai nc?"
Ya dafe kunci, a kuma lokaci guda da ya ke shirin kuka
'"yaya ba tsokanarki na ke ba, wallahi Abdul ne'"
Ban ko sake komawa ta batun Ilabib ba, a gujc na bazama
waje na nufi sitting room, ko sallama ban yi ba na ban kada
labule. Yana zaune akan kujera, sanye da bakar jacket da
wando, farar coller shirt da bakin takalmi, ya kuma tamke
wuyansa da neck tie baki.
"Abdul !" na kira sunansa sa'arda na tafi da gudu da
niyyar rungume shi, na manta da cewa a halin yanzu haramun
ne mu taba juna.
"Wait karimah! Wait!" Abdul kenan ya ke dakatar da ni,
amuma ina! Aikin gama ya gama. l'uni na fada kirjinsa ina
kuka, maimakon ya banbaare ni shi ma sai ya rufe da ni, mu
ka ci gaba da kukan tare. Ba mu tashi ankara ba, sai da aka
dauki dogon lokaci.
Abdul ne ya ankara Karimah haram fa mu ke aikatawa"
Na yi gaggawar barin jikinsa da sauri, tuni hawayc ya cika
ko;ina a fuskata. Hankici ya sa yana goge min amma a banza,
wani ne ya ke kara fitowa.
Ul ina ka tafi ka bar ni?'" Ina maganar ne cikin shasshcka. Ya sharc nasa hawaycn"Karimah ina nan kusa da ku"
"Shi ne ka bar ni na yi ta shan wuya, kuma ka sani ina da bukatarka"
"Dole ce tasa haka Karimah na barki a lokacin da bukata
ta dake tafi taki sosai, kuma na azabtu da rashin ki"
Ya matso kusa da ni "Karimah na wahalar da ke, na je fa rayuwarki cikin garari, ba don Allah ya so ni ba, ta dalilinki
ina iya shiga wuta"
Na girgiza kai" Abdul bari fadin haka, duk abinda Allah
ya hukunta babu makawa sai ya faru" "Duk da haka Karimah dubi fa yanda duk ki ka lalace, kin
koma kamar ba ke ba, don Allah ki yafe ni, na tuba"
Na share hawaye 'Abdul babu komai da ma haka Allah ya
so, fatana dai ace dawowa garc ni ka yi"
Ya gyada kai "Na dawo Karimah, babu sauran abin da zai
Kara raba ni da ke, na ji irin rayuwar ha'ula'in da kika shiga,
na tausaya miki kuma na tsani kai na. Yanzu da a ce mutuwa
na yi shikenan sai ki karashe rayuwarki cikin tagayyara da
rashin mijin aure"
Na dubc shi "A ina ka sami labari?'"
Ya gyara tsayuwa 'duk abinda yafaru nakaji agida wajan
zuwana uku"
"Amma Abdul ka ki zuwa wajena?"
Dole cc tasa Karimah, a lokacin ba zan so ki ganni ba, na
san in har kika ganni ba za ki bar ni na tafi ba. Ni kuma a
lokacin duk ina kan zaton cewa ina dauke da cutar, yanzu ma
ba don mutumin yaje ya tawo dani, ba gami da fallasamin
gaskiya da bazan dawo ba zan dawo ba, harma sai da aka sake
saban awo na kuma tabbatar'"
"Kana nufin a Abuja kakc da zama?"
ya gyada kai "kwarai kuwa, ina wajcn Mubarak abokina
mai gidan da muka yi gudun hijira dan kwangila ne acan, nima
ya daga min naci har na tara kudade"
Na dube shi "wane mataki kadauka akan mutumin da uwar
Sakina?'
67
Ya yi murmushi zancen yaushe, a ofishin 'yan sanda na
sauke shi banbar wajen ba sai da aka kamota ita ma,
kwamishina ya yi min al'kawarin turamu kotu nan da dan
lokaci'
"To yaushe za a mayar da auren Abdul?""
"Yau din nan Karimah, da Abba ya dawo za a mayar da
shi, kuma a yau zan daukc ki mu tafi can mu lashc abin da na
tara mana'"
Dadi ya cika zuciyata, na ji kamar na rungume shi.
'"Karimah ''ya kira sunana
Nadaga kai a hankali
"za ki ga abin da ake kira gata, zan yi miki abin da ya
shallake tunani, zaman da za mu yi yanzu sai kin ce zaman mu
na baya irin na auren kiyayya nc, zan nu na miki kauna
zanzurutunta, na shagwabaki, amma fa sai kin yi hakuri da ni,
kin dai san yanda na ke, ga shi kuma daga ke babu wata, na
daddara na yi hankali"
Na kalle shi irin kallon da ke zauta masoyi, a lokacin da
yayyafin kaunar sa ya ke jika ni "zan jure"
Ya yi murmushi'to nagode, za kuma ki ga sakamako.
Rayuwar duniya sai da kudi, kuma a halin yanzu ina da su"
BAYAN WUYA
A
wa biyu ba mu kara a Kano ba bayan mayar da auren mu,
Lakan sadaki Naira dubu dari. Gidan da mu ka isa katafare
ne, ya wadata da duk wasu kayan kyalc-kyale, irin gidan
nan ne da idan kana ciki sai ka manta da batun ajali.
Ina kwance shame-shame akan gado, Abdul yana yi min tausa.
Ya dakata a lokacin da ya ke son shaida min wani abu. A hankali
ya kishingida a kusa da ni 'Karimah ina yiwa Allah godiya da ya
maido minke,shakka babu a tarc da ke Allah ya adana farin cikina,
Isawon lokaci da na yi ba tare da ke ba na yi shi ne a cikin kuncі,
amma haduwarmu ta yau sai ta kore min duk wata damuwa,
tamkar ma wani abu bai taba faruwa ba."
Na juyo gareshi muka fuskanci juna "Abdul nima haka kake a
raina, kainc sirrin farin cikina, rashinka lare dani shi ne rashin
komai a rayuwata."
68
Zancen nawa ya faranta masa rai, cikin azama ya rufeni ruf I
LOVE YOU DARLING, I LOVE YOU TOO. Sai muka ci gaba da
tunatar da junanmu rayuwar farin cikin da ta shude a baya....
Na farka sa'ar da rana ta dade da hudowa.
"Sannu da tashi." Muryar Abdul ce ta ratsa kunnena, a kuma
lokaci guda da yake kokarin zama a kusa dani, ya kama
hannaycna, gami da tashina zaune daga bisani ya dafa kafaduna.
'Tashin mu je bandaki na cika miki baho da ruwan dumi, idan
mun yi wankan kuma sai mu je mu karya. Abin karinmu yana kan
table." Na bude idona gami da kallonsa "Abdul muna da 'yar aiki
ne?" Ya gyada kai "Kwarai kuwa, ke ma ai kin ganta da idonki."
"A ina na ganta?"
"A kan gadonki mana, yanzu ma ga ta tanan tare da ke."
“Ban gane ba." Na bayyana da sauri.
Ya yi murmushi "Karimah ni ne dan aikin ki, zan hidimta
miki ba tare da kosawa ba."
Na girgiza kai "Gaskiya ban yarda ba, mata ita aka sani da
hidimtawa miji, amma ba miji ya hidimtawa mata ba."
Ya yi dariya "To ban da tsakanin Abdul da Karimah su za su
kasance akasin haka ne."
Na girgiza kai "Suma ba za su canza ba."
"To na amince, amma za a yi canji, daga yau ni ne matar ke
ce mijin, kin ga sai na ci gaba da hidimta miki ko?" ya kara jan
hannuna "Tashi mu je dakin wanka."
Na fara kokarin mikewa da kyar, saboda mutuwa da jikina ya
yi "Ok. Ba za ki iya tashi ba Karimah, bari ki ga yanda za a yi."
Ban yi aune ba na ji ya ciccibeni, bai ajiyeni a ko ina ba sai a
gindin bahon wanka. Shi ya shirya ni tsaf, daga bisani ya shirya
kansa, sai muka tsunduma tare.
本
Ina zaune akan kujera, cikin wasu furanni zuciyata fal farin
ciki da nishadi. 'Yan kwanaki biyu sun mantar da ni kuncin
shekara biyu, a lokacin ne Abdul ya dawo. Bayan da ya sanar dani
cewa na yi jiransa awa hudu. Na tsallake kujcrar gami da rugawa
wajen mijina, ina zuwa na rungumeshi, cikin halin farin cikin
Allah ya dawo da shi kalau. Ya kama hannuna "Zo mu je waje ki
ga wani abu Karimah." Sai ya fara jana. Kasancewar ya fini sauri
ya sanya ni da dan gudu-gudu na ke hadawa. A haka muka fito
69
waje, ya ja ni har zuwa inda aka yi fakin da wasu motoci guda uku
ne sababbi, sai walkiya suke. Ya fara bude min 'yar karamar kirar
Ilonda Brama, daga bisani ya bude min Bus-bus din guda biyu.
Na yaba masa motocin gami da fatan Allah ya kiyaye.
"Ba nawa bane." Ya fada yana mai kafa min idanu.
"To na wanenen? Ko na Mubarak ne?"
4.
Ya girgiza kai "Bana sa bane, zo na fada miki mai su."
Na karaso a hankali, jawoni yayi gami da kara bakinsa a
kunnena, ya fara rada min cikin tsanaki. "Ki yi hakuri da 'yar
karamar, kin rinka gurgurawa, domin gaida 'yan uwa da kawaye,
bus-bus din kuwa ki yi maleji da abinda za su ajiye kullum, ina ga
ba zai fi dubu uku ba."
Na juyo gareshi, da sauri "Abdul ban gane nufinka ba."
Ya yi murmushi "Duk na ki ne Karimah, somin tabin
sakamakon wahalarki saboda ni."
Ban san sa'ar da na fashe da kuka ba, ya jawo ni ya rungume
"Karimah bari kuka, kyautar ba ta kai yarda za a yi mata kuka
ba."
ni."
"Haba Abdul, so kake ka zauta ni?"
Ba zan iya zautaki ba Karimah, ke ce dai kaunarki ta zauna
Na kwanta a kirjinsa sosai "Abdul ban san kalmar da zan yi
amfani da ita wajen yi maka godiya ba."
Ya girgiza kai "Ba kya bukatar gode min Karimah ni da ke
mun zama abu daya, babu mai bukatar godewa wani."
Na ciro kaina dga kirjinsa gami da kura masa idanu, shi kuma
sai ya yi murmushi "Akwai kari Karimah ga caki na Naira Miliyan
Biyu, ki sayi duk abinda ranki yake kwadayi."
Ban san sa'ar da kukan ya dawo ba "Abdul ya yi min yawa sai
ka sa na tabu."
"Ba za ki tabu ba Karimah dan abin bai kai yadda za atabu
ba."
Ya cireni daga jikinsa gami da jan hannuna zuwa cikin gida, a
lokacin da na ke kwatanta abubuwan da ke faruwa da mafarki. Ya
dafa kafadata "Je ki ki shirya za mu je sayayya wani kanti THE
REAL INDIAN JEWELLARY ki zabi duk wani kyalkyalin mata
da kike sha'awa, tun daga Naira daya har miliyan daya." Sai na
tsaya turus, rikicewar da na yi ta sanya ni fadin abinda ban shirya
ba "Abdul ba ka isa ka kaini ko ina ba, haba sai ka ce hauka." Ya
70
yi murmushi a kuma lokaci guda da ya dafa kafadata "Karimah na isa, na sani ba kya saba umarnina, ko za ki fara yau?" na girgiza kai "AaNba zan saba maka ba." Ya yi murmushi gami da bude
hannaye "Come on my dear, you're the best I habe in life." A guje
na taho na shige kirjin mijina, ya rufe da ni yana mai dan jujjuyawa. ウ
"Ni da ke mutu ka raba Karimah." ba Na kara lafewa "Abadan ba zan barka mijina."
KARSНЕ
Zabgegen jirgi mai makale da daruruwan targon farin ciki ya shude.
Shudewarda ta zamemana bankada da tonon asiri gareni da mijina, aka
fahimci bama zaman lafiya da dare, bayanda na sullubo tagwaye, abune
mai wuya gane wanda yafi farinciki tsakanina da Abdul, ana iya takaitawa
ace kowa yayi daidai iyawa, sunayen 'ya'ya ya zamo Na'ima'da Na'i'm,
'yan uwa da abokan arziki suka taru dankam.
Awani yammaci sa'arda na shagala kallon yaran. Abdul ya shigo sulalewa
yayi gamida zama a kusa dani. Ya dora hannu a kafadata garmida umarta
ta da na juyo, juyawar nayi muka fauskanci juna sosai. Ya fara magana a
hankali; bayanda ya matso da fuskarsa kusa da tawa, ta yanda muke iya jin
hucin numfashin juna.
"karimah ki kula mana da 'ya'yanmu, ki gane hakuri da rashin hamidah ne
yasa yanzu aka bamu biyu kitattala mana har suyi girman da zamuyi
alfahari dasu, babu sauran hawa acaba, kinji ko?"
nagyada kai "naji na kuma bi, nima bani da burin da ya wuce wannann"
ya lumshe ido. "Thank you, biyayyar ki gareni ita take karamin kaunarki
araina, akullum na kan kalli abinda ya afku abaya amatsayin wani jan
kunne daga mahalicci, kuma na yi masa godiya da bai kwace ki ya bawa
waniba, da ace wani ya aureki kuma na fahimci lafiyata kalau da anga
rigima, da tsiya sai an sakar min ke'
nayi nazarin fuskarsa, domin gane matsayin abinda ya fada. Shin wasane
ko kuma gaske? Banga alamun wasanba.
11
Ya sassauta murya. "Kece abin alfaharina karimah, ako wanne lokaci na
kanso kasancewa tare dake, abinda nake nema yanzu a wajenki, yimin
alkawarin ci gaba da mallaka min kanki tsahon rayuwa'
Na mayar da idanuna ga kallon kasa a kuma lokacinda hannuna ke wasa da
maballan rigar da ya ke sanye. "abdul na yimaka alkawari akan duk binda
ka ke nema'
Murmushi ya cika fuskarsa cikin sauri ya rungumeni hannayensa suka
cigaba da yawo a bayana. "na gode abar kaunata, da sannu ni kuma zan
cika miki alkawarin da na daukarwa kaina, mallam miki duk wani abu da
na mallaka, dama wanda zan mallaka agaba, babu sauran hango wata
awaje, ke kika iya kuma ke zaki ci gaba".
Bege da kaunar mijina suka cika zuciyata ban san sanda na fara hawaye ba.
Ya kara matseni. "karimah babu mai rabamu, ko mutuwa zango tayi mana
alfarmar tafiya lokaci guda, kin goyi da bayana?"
Na gyada kai "nima haka nake fata mijina"
"Thank you my dear" sai ya jona bakinsa ga tsotsar nawa.
***
farin cikina ya yawaita yayinda 'ya'yana suka fara ta ta ta, aduk lokacin da
zani unguwa nakan zubasu abayan móta na ran kaya. Mutane kanta kallona
cikin sha'awa da birgewa, musamman ma 'yan uwa mata. Inda ko wacce
ke kwadayin ina ma zata wayi gari a rabin matsayina.
Na girgiza tunanin jama'a yayinda nakai ziyara gida, suka rinka bina da
kallo baki bude, bayanda suka ganni da tsaleliyar mota, da suturun da suka
zarce tunani, suturunda suka dace da yanayina na wannan lokaci,
kosashishiyar mace da ni'ima ta sanyata komawa jazur. Da kallona zaki
san ina sakata ina walalwa, yaya ba zan bararrajeba! Alhali ni kadai ke
kwankwadar kauna daga mijina, bayanda ya watsar da halayyar
Kwashe-kwashe!
ALHAMDU LILLAHI. RUFAIDA M. UMAR
Na gode sai wani lokaci.
72
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels