hannu " to a dawo lafiya ko"
13
Ya yi murmushi "Allah ya sa hakan nan"
Sai ya tashi motar, ya kura min ido tsahon lokaci kafin daga
bisani ya fara Kokarin dagawa.
Na Kara karkada masa hannu " a dawo lafiya"
Ya dago min nasa hannun shi ma "Allah ya kaddara haka"
Sai ya tafi ya bar ni a wajen a tsaye, na bi motar da kallo,
zuciyata cike da kaunar mijina, ban iya barin wajen ba har sai da
idanuna suka gaza hango sha cin motar, a sannan ne na juya cikin
gida, raina tas.
***
Agogon bango ya buga sha biyun rana abin da ya tabbatar
min da cewa Abdul kasuwa ya zarce kenan, sai na fara shiryeshiryen dora girkin rana. A lokacin ne na ji sallama, ba muryar
kowa ba ce illa ta kanina. Na amsa ina mai yi masa maraba.
Ya durkusa ya gaida ni, sannan ya fara karanto sako
Karimah ki zo Abba yana kiranki"
"Abba yana kirana?" na nemi tabbaci
Gyada kai ya yi.
"To lafiya Abba ya ke kirana?"
"Lafiya kalau, ina zaton Ummah za ki raka unguwa"
"To! Kuna gashi Abdul baya nan, ka ga kuma ba na fita
babu saninsa ba"
Yayi murmushi " Karimah ke ma kin san babu yanda za a yi
Abba yace ki fita babu sanin mijinki, ina ga sun gana da shi ta
na'urar sadarwa"
Na kada kai " ai ho! To ka ce gani nan zuwa"
"Tare aka ce mu tafi da ke, ko wanka cewa a ka yi kar ki
Isaya yi"
"Kar na tsaya yin wanka! Habib ko dai babu lafiya ka ke
boye min?"
Ya girgiza kai " ba haka ba ne yaya, da babu lafiya ai za ki
iya fuskanta a yanayina. Ina ga dai shi Abban ne ya ke sauri
ya koma kasuwa"
14
Sai na shiga daki, na bude sif domin debo kayana. To amma
sai na ga abinda ya ba ni mamaki, banga kayan Abdul ba. Na tsaya
anan a daskare, cikin rashin sanin abinda hakan ke nufi. Habib ya shigo falon bayan da ya ji shiru. A gindin kwabar ya
same ni a tsaye. Ya dube ni " Yaya aka yi yaya?"
"Eh! abin mamaki na gani, na nemi a
kayan Abdul na rasa
kwabar nan, kuma ni nawa duk suna nan, ballantana na yi zaton
sata aka yi"
"To kuma ba kya zaton wanki ya kai?"
"A wanke suke fa a goge, ka ga kuwa batun ace ya kai wanki
ma ba ta taso ba"
Ya yi shiru dan lokaci, daga bisani ya nisa " To bari za ki yi
ya dawo, sai ki ji koma me ake ciki"
Na amince da shawararsa, na kuma shirya cikin tsanaki. Mu
ka fito tare da Habib, na kulle gidan, sannan muka kama hanyar
gida.
Mahaifina ya dube ni, bayan da suka tasa ni a daki, shi da
mahaifiyata " Karimah yau she rabon Abdul da gida?"
Tambayar ta zo min a bazata, na kuma fara tunanin dalilin
yenta, fuskata na mai bayyana mamakina a fili.
"Yaushe rabon Abdul da gida?" Ya sake maimaitawa
Na sunkuyar da kai " da safen nan ma ai muna tare, mun
rabu akan za shi daurin aure "
Mahaifina ya yi shiru, daga bisani ya dora" amma lamarin akwai daure kai, to me ne ne fa'idar takardun da ya aiko? Me ya hana shi fada miki sakon baki da baki?"
Na daga kai da sauri " sako kuma Abba? Wane irin sako kuma?"
"Eh takardu aka kawo guda biyu, daya sunan ki daya nawa,
tawan na bude na karanta gaisuwa na gani a ciki, gami da sakon na
tura a yi kiranki yanzu-yanzu, kuma na baki taki takardar ki
karanta a gabana"
15
Ya miko min wata takarda " gashi dai ki duba ki gani"
Na karbi takardar hannuna rawa, na kuma fara warwareta, a
lokacin da duk jikina ya dauki tsuma, sakamakon rashin sanin
abinda takardar ta kunsa. Da gama warware ta na fara karantawa.
Karimah!
Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala. Na kaşance cikin tashin
hankali yayin rubuta wannan takarda. Idanuna sun zubar da
hawaye, zuciyata ta kasance tamkar ta kama da wuta, ba don
komai ba, sai don dumbin bakin cikin da ke tattare da ita,
sakamakon rubuta abinda hannuna bai taba rubuta abin da ya kai
shi muni ba.
Karimah! ba sai na fada ba, ke kan ki kin san yanda kike a
raina, ke ce komai a rayuwata, babu abinda raina ke so illa
kasancewa tare da ke, sakamakon dumbin kaunarki gare ni da
kuma yanda ki ke tarairayata, wanda hakan ya sanya ni fatan
kasancewa tare da ke tsahon rayuwata. Sai dai kash! Babu wani
hali da ya ke madawwami, komai sabintar abu zai tsufa, mai kyau
ya lalace, haduwa kuma ta zama rabuwa.
Karimah! na sani zaki kasance cikin tashin hankalin abin
da zai faru, sai dai ina mai tabbatar miki cewa tashin hankalin da
na ke ciki ya fi wanda za ki shiga, rokona da ke ki dauki hakuri, ki
kuma yi addu'ar duk Allah ya ba mu dacewa.
A zahirin gaskiya boye miki na yi, ke ce Allah ya
tsallakar, amma ni na dauki kwayoyin cutar, abin da ya tilasta min
kawo zaman mu karshe, ba don komai ba sai don gudun kar na
cutar da ke, ga kuma hangen abinda zai je ya zo, in har aka san
cewa ina dauke da cutar, to ke ma za a rinka kirgawa har ke,
sakamako kuma ya zama ki rasa miji bayan mutuwa ta, abinda ba
zan taba fatan ya faru ba.
Na sani Karimah ba za ki taba amincewa na sake ki ba, bisa
take-takenki dana gani wannan shi ya sanya ni daukar wannan
mataki. Zan bar garina kuma mahaifata na tafi can wata duniyar
daban, inda a can zan sude dan abin da ya ragu na
rayuwata, wanda hakan shi zai zame miki kwanciyar hankali, ki
16
auri duk wanda ki ke son aura ba tarc da wani abu ya kawo cikashi ba. To ina mai nunka godiyata gareki bisa kauna da biyayyar da ki ka yi min yayin zaman mu tare, Allah ya yi miki babban sakamako. Ki mika godiyata ga su Abba ma sun rike ni kamar dan da suka Haifa. Kuma ki duba cikin kwabarki akwai takardun gidana, na mallaka miki shi har abada. Mahaifiyata kuma na bar mata rumfata ta kasuwa tare da duk abubuwan da ke ciki. Ita ma
zan aika mata takarda, zan kuma sanar da ita komai. A nan na ke
cewa ki dau hakuri, ki kuma yi min afuwa bisa abinda zan rubuta,
da kin ji yanda kirjina ya ke yayin rubuta shi da kin tausaya min. NA SAWWAKE MIKI Allah ya maye miki da wanda ya fi ni komai. Na gode, sai wata ran.
Tsohon mijinki
Abdul Hussien
Na jefar da takardar gami da fasa kara, a kuma lokaci guda da
na mike tsaye. Nufina na bazama waje da gudu, mahaifiyata ta yi gaggawar rikeni.
"sakar ni Ummah! sakar ni! Abdul zai tafi ya bar ni, tafiya zai yi" Mahaifina ma ya agaza, na yi iya yina domin na kwace amma ina! Ruko ne da ake kira sai dubu ta taru. Na yi ta mutsu-mutsu na har na gaji, numfashina ya fara ja baya, sakamakon galabaitar da na yi. Radadin da ke cin kirjina ya ci gaba. Abinda ya sanya numfashina dakatawa gaba daya. Sai jikina ya saki, na langabe shakaf!
Ina jin sa'ada mahaifina ke umartar Habib da ya kira masa likitansa, daga nan kuma ban san abinda ya faru ba.
Na jini lubus a cikin katifa, na gyara kwanciyata gami da mika hannu domin lalubo mijina, to amma ina! Ban iya jin na taba komai ba, sai na bude ido da sauri, ga mamakina ba dakina ba ne, wani dakin ne dabam a gidan iyayena. Na tashi zaune, zuciyata cike da firgici akan abinda na gani. Kwakwalwata ta fara aiki nan da nan tamkar a majigi, ta fara haska min abubuwan da suka faru
11
da rana. Na ganni rike da zungureriyar takarda ina karantawa. Da
tuna haka sai na fasa Kara. Shirun da ke gari sakamakon tsalawar
dare ya yada ta da nisa.
Sai na ji ana kokarin bude kofar ta waje, ba da jimawa ba
mahaifina ya shigo. Tsugunawa ya yi a gaba na " kwanta Karimah
dare ya yi sosai"
"Abba ina Abdul? ni wajensa zan tafi"
"Eh za ki je, amma bari sai da safe, mai yiwuwa ma ya zo shi
da kansa"
"Cewa yayi fa zai bar garin"
"Da gangan ya ke yi miki daurin aure ya tafi, kuma ma ya dawo, kwanta sai da safe"
Da jin haka sai na koma na kwanta, shi kuma sai ya tafi daga
dakin, ya kara kullewa ta waje"
Hawaye ya ci gaba da tararowa daga idona, anya kuwa Abdul
ya dawo? ba dabara mahaifina ya yi min ba, domin na sami
nutsuwa? Da alama dai haka din ne, sai zuciyata ta kara rikicewa.
Na tashi zaune gami da sa sabon kuka, kwakwalwata na mai tariyo
min abinda ya wakana, tsakani na da mijina, tun daga jiya har
zuwa yau da safe. Na tuno sa'adda ya zaunar da ni a cinyarsa,
sa'arda muka yiwa juna belt muna masu neman afuwar juna, na
kuma tuna yanda muka farantawa juna rai tsahon lokaci, kafin
tunanin nawa ya juyo kan abinda ya faru a yau da safe. Kura min
ido da ya yi a falo kamar bai taba gani na ba, zancensa mai
sarkakiya da ya yi ta nanatawa, har ya zuwa inda na raka shi mota,
da kuma 'yar muhawarar da mu ka yi anan. A sannan ne na gano
manufar maganarsa " ba lallai ne na dawo ba, mai yiwuwa na zarce
daga can"
Babu shakka mutuwa ya ke nufi, ba wai kasuwa ba. Sai dai in
har haka ne sai in ce ni ma gain nan tafe, ina dai shakkar ace zan
iya jure rashinsa. Na shaku da shi matukar shakuwa. Gwani ne
wajen iya tarairaya da faranta rai, sannan kuma kwararre ne wajen
iya debe kewa, ashe kuwa in har na rasa shi ba karamin rashi na yi
ba. Da na san tafiya zai yi ya bar ni to da ban yi sake ba, zan
18
manne masa ne matukar mannewa, na rinka bin diddiginsa duk inda zai nufa, sai dai kash! Na makaro mai afkuwa ta afku.
Sai na dafe kai cikin jin jiri, jijiyoyin idanuna suka daddaure, damuwar da ke zuciyata kuma ta dadu. Ban iya komawa na kwanta ba, maimakon haka sai na jingina da bango na ci gaba da ganawa da bakin cikin da ya kawo min ziyarar bazata, a haka har asubahi ta yi.
ANA WATA GA WATA
ana ta yi zirga-zirga daga gabas zuwa yamma sau tulin R
adadi, a kullum sakon da na ke bata shi ne ta dawo min da
mijina. Sai dai kash! ba ta iyar da sakon ba. Tun ina kallon
abin almara-almara har na gaskata shi, na kuma amincewa raina
Abdul ya tafi, shi kenan ni da shi.
Shakka babu guguwar bakin ciki ta yi awon gaba da farin cikina, ta kuma tule min sharar damuwa da takaici. Nishadi da
walwala suka guje ni, kuka kuma ya zama sabon mijina, a
kowanne lokaci ina tare da shi dare da rana, a zaune a kwance.
Ba zan manta da ranar wata talata ba, 'yan mintuna kadan bayan da na idar da sallar azahar, mahaifina ya shigo rike da takarda. Da kallon fuskarsa nasan baya cikin walwala.
Ina lura da shi sa'adda ya kara nazarin takardar, bayan da ya jingina da bango. Ya girgiza kai cikin takaici, ya kuma kirawo mahaifiyata, ta iso gare shi nan da nan. Takardar ya mika mata gami da fadin " duba ki ga ni"
Ta karba ta fara nazari, ina lura da yanda fuskarta ke canzawa.
Mahaifina yace da ni " zo ki gani kema"
Sai na ta so domin ni ma na gani. Tun kafin takardar ta shiga
hannuna na gane cewa ta kotu ce, suna na ne a rubuce a jiki. Na kalli mahaifina cikin kaduwa " Abba wannan fa?"
Yajanye takardar gami da dubana kai tsay" uwar mijinki ce
ta shigar da fara"
Mamaki ya kamani " To akan me kuma?"
"Ina zaton zai zama akan maganar gida"
Na girgiza kai cikin takaici " To Abba gidan me? ni dama ba
ya gaba na, a ba ta takardun mana"
"Eh! ni ma haka na gani, yanzu zan je na same ta a gida, zan
ba su damar mu jc a ba su takardun, ala kulli halin dai ba zamu hau
kotu da su ha"
Bai Kara komai akan wannan ba, sai ya kama hanyar fita. Na
koma kofar daki na zauna cikin tagumi, tunanin al'amarin har ya
kai ni ga zuhar da hawayс.
Mintuna da dama sun shude, wadanda su suka ishi
mahaifina dawowa, ban ga alamun nasara a fuskarsa ba.
kenan
"Yaya aka yi?" Tambayar da mahaifiyata ta fara yi masa
Ya jingina da bango, a kuma lokaci guda da ya ciji lebensa"
babu makawa mu shiga kotu da su, ba maganar gida ce kawai a
gabanta ba, mummunan zargi ne na abin Allah wadai, wanda ba
shi da tushe ballantana makama"
Ya dan sassauta, da alama zancen ne ya ke cin ransa. Bayan
wani lokaci ya ci gaba" Inji ta asiri Karimah ta yiwa dunta, domin
ya bar garin ta mallake abin da ya ke da shi"
Mahaifiyata ta dafe kirji, yayin da ni kuma na dora hannu
aka, sai na fashe da kuka.
"kin ga ba batun kuka ba ne, abu ne da za a yi nazarin ta
inda ya kamata a bullo"
" Me nene abin yi kenan?" Mahailiyata kenan ta ke son jin
mafita
Mahaifina ya nisa "abin yi kenan mu shiga kotun, ita ce
hanya mafi ısari da kyau, wadda za a magance ko wane irin
gunaguni nan gaba"
"Na sani akwai illoli ga yin hakan, na farko duk zaman
mutuncin da aka yi a baya yana iya tarwatsewa. Abu na biýu
bankada da fallasa, wato yayatawa duniya halin da ake ciki, ba
zan yi farin ciki ba a ce duniya ta san abin-da ya sanya Abdul barin gari. Cin zarafi ne a gare shi da kuma to zarta shi, haka zalika ga Karimah hanya ce ta kore mata samun mijin aure"
Na sako baki " Abba ni a bar batuna, na yafe maganar kara
aure"
Ya girgiza kai" bari ma wannan zance da miji ya samu za ki
kara aure, musulmin kwarai ba zai bar 'yarsa a gidansa ba, alhali
kuma babu larurar da ta hana ta yin aure. Da kuma ace duk wadda
ta rabu da mijinta shikenan, to da ina shakkar ace muma akwai mu
yanzu"
Na yi shiru ban ce komai ba, duk kuwa da cewa batun kara
auren baya raina.
Da an siffanta maka gini ma'abocin tsayi da fadi, da kuma
bencina a shirye daki-daki, za ka kira shi ajin makaranta. Sai dai
in har aka ce ba shi ba, kotu za ta fado ranka. Babu shakka kotu ce,
in da anan muke a zaune ni da iyayena, a gefe guda kuma
kawayena ne Asma'u da Nusaibah, sai kuma saurayin Nusaibah
Barista Mukhtar wanda shi ne lauya mai kare ni. A daya bangaren
kuma mahaifiyar Abdul ce da 'yan tawagarta. Adadin 'yankallo
kuwa ba zan iya kiyasce shi ba. Wadanda har suka hada da
wakilan kafafen yada labarai, kasancewar ta kotu da ke samun
shari'u masu sarkakiya.
Allah ne kadai ya san radadin da ke cin zuciyata, ba don
komai ba sai don kasancewar yau mai yiwuwa ranar da duniya za
ta san halin da mijina ya ke ciki. Ban iya jurewa ba, dai na Kunshe
kai na a mayafi na ci gaba da zubar da hawaye.
Ba a jima ba alkali ya shigo, kowa ya tashi tsaye domin girmama shi, aka zauna bayan da ya zauna. Bayan 'yan bude-bude
da rubuce-rubuce, sai mai gabatar da kara ya fara gabatarwa. Wata shari'a ce aka karashe, ta wasu ma'aurata da ke rigima akan rikon
da. Ana kammalawa da ita sai ta mu kuma. Mai gabatar da kara ya
21
gabatar, inda ake tuhumata da laifin yiwa miji asiri, domin ya bar
garin na mallake abinda ya ke da shi. Da gama gabatarwa jama'a
suka shiga girgiza kai cikin jimami. Ni kuwa da na ke a tsaye a
mahallin wanda ake tuhuma sai na ji kamar na fashe da kuka.
" Ke zaki yi magana ko kuma kina da lauya mai kare ki?"
Tambayar da aka yi min kenan
"Ina da lauya" Na fada kamar zan yi kuka.
Sai aka nemi da ya fito. Barista Mukhtar ya tashi tsaye, ya
gaishe da alkali gami da gabartar da kansa. Sannan ya fara da
musunta abinda ake zargina da shi.
"Lamarin ba gaskiya ne ba, mijinta ya tafi ne bisa radin
kansa, sakamakon wayar gari da aka yi yana dauke da kwayoyin
cutar II.I.V, bayan da ya auri wata matar da aka yi masa rufa-rufa,
aka aura masa ita ba tare da an shaida masa halin da ta ke ciki ba.
Akwai takarda da ya bari mai dauke da bayanin komai"
Sai ya fitar da takarda, ya kuma nemi izini da a ba shi
dama ya karanta. Aka ba shi dama, ya karanta, sannan ya gabatar
da ita ga kotu. Sai aka nemi mahaifiyar Abdul da tace wani abu.
Lauyanta ne ya mike tsaye, shi ma ya gabatar da kansa, sannan ya
fara bayani kamar hakа
"Ya mai girma takardar kirkirarriya ce da aka kwaikwayi
hannun mutumin, kuma ina roko kotu za ta yi watsi da ita, domin
kuwa ba ta isa shaida ba"
Sai aka nemi wata shaidar daga bangarenmu. Takardun
sakamakon cibiyar binciken cutar kanjamau, lauya na ya gabatar,
ya kuma kara danganta su da abinda ke cikin takardar farko. Babu
shakka shaidu ne da babu damar a musanta, sai dai abinda kotu
zata nema shine ta tabbatar da sahihancin takardun, wanda da an
tabbatar nasara ta fara zuwa gare mu kenan. A haka aka tashi,
kowa ya watse. Mu ma mu ka tafi gida, zuciyata cike da bakin ciki
marar iyaka.
Ban Kara shiga wani hali ba, sai da na ji an kawo rahoton
shari'ar ta mu a taskar labarai (Radio Kano), Inda ranka ma sun
.
وو
sanya (Freedom F.M) Shi kenan kuma tafiya ta tafi, duniya ta
gama sanin abinda ke faruwa da ni.
***
A zaman mu na biyu aka tabbatar da ingancin takardu, abin da
ya karawa shari'ar ta mu tsaho inda alkali ya nemi Jimmai da
yayarta Uwani, bayan da ya zama wajibi su ma su shigo ciki.
Kwana daya da yin zaman, mahaifiyar Abdul da yayarsa
suka tarar da mahafina a gida, roka suka zo da shi akan ya bayar
da hadin kai a janye shari'ar. Sai dai ina! Sun makaro, babu
mahalukin da ya isa ya janye shari'ar a wannan lokacin dole ne su
bari a kai karshe.
Zama na uku shi ne ya fi tara jama'a fiye da kowanne zama,
da alama wadansu ma a redio suka ji, son ganin yanda za a karke
ya sanya su takowa.
"ke matar Abdul Hussien ce a 'yan watannin da suka gabata?"
Tambaya ta farko kenan da aka yiwa Jimmai, bayan gurfanar da ita
"Babu shakka" Ta amsa tambayar kai tsaye
"kuma kina dauke da kwayoyin cutar H.I.V"
"Haka ne"
Na yi mamakin yanda ta amsa tambayar kai tsaye, to amma
ina zaton tana son saukakewa kanta shari'a ne.
Mai tambaya ya ci gaba " Yaya aka yi ki ka aure shi ba tare da
kin sanar da shi halin da kike ciki ba?"
Ta girgiza kai " ba zan iya tabbatarwa ba ko an shaida masa
ko ba a shaida masa ba, domin tsayuwar mu biyu da shi, kafin
kuma mu tsaya din sai da suka tattauna da yayata"
Akwai hikima cikin zancen da Jimmai ta gabatar, da alama
sun tsaro komai ne tun daga gida.
Aka gurfanar da Uwani itama.
"Ke ce yayar Jimmai, kuma wadda aka nemi aurenta a wajenki?"
"Haka ne Allah ya gafarta"
23
4
To amma kin san tana dauke da kwayar cutar H.I.V.
Ya ya aka yi baki sanar da mai neman auren ba gashi kuma an
wayi gari shima ya kaти?"
Ta gyara tsayuwa "Eh, to ba zan ce ban sani ba, sai dai ina da ja
akan cewa Abdul ya dauka, domin kanwata tana shan magani, kuma
bai daina tasiri a jikinta ba, in har kuma an ce ya dauka din, to sai dai a
sakė gwadashi a karkashin kulawar kotu, in ya so kome aka ce sai na
yarda."
"A ajiye wannan batun, tunda ba a san inda yake ba, amma da
wacce hujja za ki kare kanki akan aura masan da kika yi babu
sanarwa?"
"Ina da hujja kwakkwara."Ta labbatar da wuri. Ta ci gaba "Kuma
hujjata zata zama bankada da fallasa, sunan wannan rana, ranar tonetone, ba zan rufi asirin wanda ya tona nawa ba."
Galibin jama'ar dake kotun kura mata idanu suka yi domin jin
abinda take shirin fada.
Ta dora "A 'yan watanni da suka gabata aka turo min kanwata
daga Legas, inda a can iyayenmu suke da zama, bayan da ta dauko
kwayoyin cutar a 'yan yawace-yawacensu na 'yan mata. Manufar
turowar shi nc ta rinka smaun magani cikin sauki, domin a Legas yana
da wuya, sakamakon masu cutar da suka yawaita a can. Kwananta
bakwai a garin nan, suka hadu da Abdul a wata rana da na aiketa wajen
Kawata Zuwairah aka yi sa'a shima va je.
Ku kalli yarinyar, ni kaina na san1 koce ga duk mutumin da yake
da maita akan mace, to Abdul ma bai ..ira ba, tuni ya ſada tarkonta.
Tuni ya bayyana soyayyarsa garcta, amma fa da manufar aurc, ya
kuma daukota a motarsa har gida. Ta shigo min da kudade, ta kuma
bayyana min abinda ya faru. Na kasance cikin tunanin wacce za a yi,
shin na fada masa ne ko kuwa na yi shiru abina? Ban kai ga yanke
shawara ba, ya sake dawowa.
Anan ma abinda ya ſada ya jaddada, sai dai na amince wa raina
bayyanamasa zai fi sauki, musmaman da ya ce auren zai dauki lokaci,
a kalla watani takwas a gaba. Watannin da nake ganin kafin su iso,
cutar na iya cin karfin kanwata. Ina shirin shaida masa ne Zuwairah ta
zo gidana gab da za a yi bikin wata kanwarsu Maimunat, roko ta zo
min dashi, akan wala mummunar bukatarta. Bukatar ita ce: tana so na
taimaka mata gudanar da wani aiki, a yunkurinta na raba Kaninta da
wata karfen kafa, wada ta tsare gabas da yamma, kudu a arewa.
24
AN GUDU BA A TSIRA BA
hari'armu da aka gudanar ta bar min wani katon bakin allo S
mai dauke da dankareriyar alamar tambaya. Tambayar da a
kullum na ke ga ża amsata, shin wai gaba aka ci ko baya?
A bangare daya dai na wanku fes daga mummunan sharrin da
aka yi min na sata, duniya ta ji cewa ni ban zamo barauniya ba,
kuma matar da ada ta tsane ni yanzu ta dawo tana ganin girma na,
bayan da ta gane cewa 'yar tace ummul aba'sin komai, har gida ta
zo da kukanta ta bani hakuri.'Ni kuma na dauki takardun gidan na
ba ta, na shaida mata cewa ni ba gida ne a gabana ba, shi kansa
hakan ba karamin girgiza ta ya yi ba.
A daya bangaren kuwa yayata mu aka yi gami da tona mana
asiri ni da mijina. An sanar da duniya cewa ga halin da ya ke ciki,
na kuma tabbata har ni mutane su ke lissafawa, a bin nan da ake
kira JA GAME
Munanan bakaken kwanaki suka ci gaba da shaide min, irin
shudewar da dare ke yiwa mai fama da ciwon hannu. Ban tsira da
komai a cikinsu ba, illa bakin ciki da kunar zuciya. Zullumi da
fargaba gami da takaicin rabuwa da mijina suka busar da ni, farar
fata ta mai walwali ta dusashe, da dama daga kasusuwan jikina
kuma suka bayayyana a fili. Abin da ya sanya masu kokonto
dainawa. Kowa ya amince akan cewa cutar AIDS ce da ni. Ba tare
da la'akari da cewa ita kanta mai yada cutar ba ta bushe din ba.
Wannan takara da na shiga ta darewa kujerar sarautar
kanjamammu ta tilasta min kasancewa a cikin gida kowane lokaci,
domin kuwa bana jure kallon da mutane suke yi min idan na fita
waje, a haka na share tulin watanni ba tare da na ga mota ko babur
ba.
A wannan hali wata 'yar yayar mahaifiyata ta haihu, Ummah
kuwa ta matsamin akan sai na je suna. Babu yanda na iya haka na
shirya na tafi. Sanda na isa gidan tuni ya dinke da mutane, ai kuwa
25
A fadinta asirceshi ta yi, shi yasa babu wani mai fada a ji sai ita.
Taimakon da yake yiwa 'yan uwansa duk ya daina, komai ya samu sai
dai ita, ta kara da cewa, tana tunanin yanda lamarin zai zama a gaba.
Ba kowa take nufi ba illa matar Kanin nata Karimah.
Kirjina ya buga da karfi da na ji an shigar dani zancen, na kara
gyara zama domin jin karashen maganarta.
Ta ci gaba "Ta zayyana min duk abinda take so za a yi, ni kuwa
ban musa mata ba, baya da na ga cewa nima ai riba ta ce, in har shirinn
ya yiwu Abdul zai gaggauta aurensa da kanwata.
To kowa dai ya san abinda ya faru da Karimah a gidan biki, inda
muka zuba mata kaya a jaka, ta tashi a matsayin barauniya.
Koda yake rayuka sun 6aci, amma bukata bata biya ba, domin
Abdul din bai saketa ba, amma dai ni tawa bukatar ta biya, sabanin da
ya shiga tsakaninsa da ita sakamakon mutuwar 'yarsa ya sanya shi
gaggauta auren kanwata, a wani mataki na turá haushi da huce takaici,
to wannan shi ne gaskiyar lamari."
Karc zancen nata ya sanya fuskokin mutane nuna takaici, alkali da
masu taimaka masa suka shiga girgiza kan jimamá. Lauyoyi kuwa suka
ji da share gumi, yayin da Zuwairah ke raba idanu, IHajiya kuma ke ta
shirgar kuka.
A nawa bangaren daskarewa na yi, sakamakon mamakin da ya
cikani, bayan da na ji cewa yayar mijina ita ta kulla min sharri, a bisa
wani zargi da bashi da