Ciki kuwa har da aminiyata, wadda take fama da zazaabi
mai mugun zafi. Abin da ya tilasta min zuwa na dubata. Ina
gidansu hadari mai karfi ya taso, abin da ya sanya ni dakatawa. An
tafka ruwa kuwa mara misaltuwa, kasa ta sha iya shan ta har ta
gaji, ta kuma rage saura a sama, abin babu ko dadin takawa.
Tsayuwar ruwan ita ce ta sanya ni fitowa domin tafiya gida, na
kalli irin jagwalgwalewar da kasa ta yi, da da hali sai in koma, sai
dai ina babu hali dole na nemi gidanmu ni ma. Na kama hanyata
cikin taka tsantsan, ina yi ina lura da inda zan saka kafata, a haka
har na ci tafiya mai nisa.
Gab da zan tsallake wani tarin ruwa mai kama da
kududddufi wata mota ta kawo jiki, kafin na ankara mai motar ya
turata ciki. Ji ka ke facal! Duk ya wanke ni da cakwali. Na dubi kai
na cikin jin haushi, sannan na bi motar da kallo, kallon da ke
bayyana irin takaici na.
Ganin irin ta'adin da mai motar ya yi ya sanya shi yin fakin
a gabana, shakka babu akwai takaici 6ata 'yar kyakkyawa irina, a
kuma wannan lokaci da na yi kwalliya. Yana yin fakin ya nufo
inda na ke da sauri. Matashi ne fari dogo, yana sanye da hartin da
wando na koren boyel, agogon hannunsa na matukar walkiya.
" don Allah ki gafarce ni Hajiya, wallahi ina kokirin kunna
C.D ne na bata ki ban ga ni ba"
Na sunkuyar da kai " jeka babu k i, Allah ya kiyaye gaba"
Ya yi murmushi " amma na gode fa ban yi tsammanin za ki
yi saukin kai haka ba, zato na ina fitowa za ki zage ni gaba da
baya"
Na fara tafiya "haba dai, waye baya kuskure"
Ya yi tsaki "amma ban ji dadi ba, ina ga abinda ya fi kamata
ayi ki zo mu je na kai ki gida, bai kamata ki bi tsahon hanya a
wannan yanayin ba"
"Ka ga bar shi kawai, yi tafiyarka"
"A'a ba za a yi haka ba, in dai har da gaske kin hakura to ki
za na kai ki, idan kuma ta ciki na ciki ne shike nan"
Fadin haka da ya yi ya sanya ni murmushi, domin ganar da
shi cewa babu wata a ciki " kar ka damu kanka, wallahi babu wani
abu a raina" Sai na ci gaba da tafiya ta.
Ya biyo ni a baya " To tsaya ki ji"
Na dakata gami da waiwayowa
"Idan ba za ki amince na kai ki gidan ku ba, ki yi min
alfarma na kai ki gidan yayata, ni ma dama yanzu can na nufa, sai
ki yi wanka acan ki canza kaya"
Na girgiza kai " A'a ni......."
Ya daga min hannu " dakata, da Allah fa na ke hada ki, sai
kace dai ba musulma ba?"
Babu yanda na iya, sai na kaďa kai "Shikenan, mu je ka
kai ni gidan namu"
Yayi murmushi " na gode fa"
Muka nufi gidin motarsa, wadda da ganin ta ka san gayen
ya hadu, ni ya fara budewa sannan shi ma ya kewaya daya
bangaren. Kamar ba zan shiga ba, sai dai na yi shahada na shiga.
Da zamana na tabbatar da cewa motar ta hadu, illahirin cikinta ya
wadatu da kamshin Air Freshner, wanda hakan shi ya dace da
kujerunta masu wadatar laushi. Ya tashe ta gami da turawa gaba,
ba mu dade da fara tafiya ba, ya tashi wani sauti a hankali, abin da
ya tabbatar min da cewa irin matasan nan ne masu son hutu.
Ya dan waiwaye ni " Ina zamu nufa?"
Na fada masa.
Ya sake maida hankalinsa ga kallon hanya sosai.
"don Allah idan babu damuwa na yi miki wata tambaya mana"
" ka iya tambaya in har ka tabbatarwa kan ka abinda ya
kamata ka tambaya din ne
"Eh ina zaton haka, dama makarantarki na ke so na ji"
" Makaranta? Na dade da jingine karatu"
"me yasa haka?"
"Aure mana"
Ya kalle ni da sauri "yanzu nan kina da aure?"
Na yi dariya bayan da na ga alamun tsoro a fuskarsa.
"Haba dai, ina da aure zan shigo motar ka?"
"Ai ho! Ya mutu kenan?"
da alama"
" Allah sarki, ni ma da kin ga ina da aure, amma yanzu ni ma
haka na ke gayana. Banbanci na dai da ke ni matar mutuwa ta yi, ta
zo haihuwa, yau kusan shekara biyu kenan, har yanzu na kasa
sakewa, domin ban gama jin radadin mutuwar ba"
Na langabe kai " Allah ya jikanta, ya kuma canza maka da ta
gari"
Ya amsa da sauri " Amin, amma fa na ji dadin addu'arki"
A cikin hirar muka karasa gida, ya yi fakin ni kuma na dube
shi " To na gode fa"
Sai na kama hannun kofar da nufin na bude na fita.
"dakata hajiya" ya tatsayar da ni
Sai na tsaya gami da kallon fuskarsa.
mana"
Yayi murmushi " idan babu damuwa fada min sunanki
Na kauda kai na ga kallonsa " suna na Karimah"
Sai na kara kama kofar zan bude
"Tsaya mana, saurin me ki ke yi alhali mun zo gida? Ni ma ai
ya kamata ki ji nawa sunan, ko ba kya ra'ayi?"
"Yaya zance bana ra'ayi, zan so ji mana in har zaka fada"
"To sunana Anas, a gidan mu kuma A a ake kira na"
Na kada kai "Ummm ya yi kyau" "To idan babu matsala zan so na zo mu gaisa da dare"
Da jin haka walwala ta kaura daga fuska ta, na kalle shi irin
kallon da zai sanya shi zargin wani abu, daga bisani na fara karkada yatsa " Sam! Kar ma ka soma"
Ya kalle ni cikin rashin fahimta "amma na yi mamaki fa
yanda da fadin zan zo mu gaisa ki ka hade rai nan da nan, ko kina
zargina da wani abu ne?"
41
"Ba na zarginka da komai, akwai dai dalilin da ya sanya ni
dakatar da kai, kuma kamata ya yi ka hakura din"
"To ba na ki ba, amma in da hali zan so jin ko wane dalili ne"
"Ba zaka ji dalilin ba, ka dai yi hakurin kawai"
Ya kura min ido tsahon lokaci, ni kuma sai na bude motar "
ka ga sai an jima" sai na nufi cikin gida.
***
Ina karatun Alkur'ani mai tsarki aka tayar da sallar Ishah,
abin da ya sanya ni rufewa, na bi jam'i daga masallaci. Bayan da
aka kammala sai na shiga addu'o'i.
Aka daga labulen dakina, Habib ne ya leko " Karimah wani
mai mota yana magana da ke"
nan.
Na hada rai gami da karkada masa yatsa, alamar yace bana
Bai gane nufi na ba sai ya yi ta kokarin canka " ba ke ya ke
kira ba? Ba za ki jc ba? Ba ki da lokaci?"
Bai sami cankar abinda na ke nufi ba, har mahaifiyar mu ta ji
ta zo " wai me ne ne?"
"Eh! wani mai mota ne ya ke sallama da ita"
A daidai lokacin na shafa addu'ata "cewa na yi ka ce masa
bana nan"
Sai ya juya. Mahaifiya ta ta dube ni "me isa ba za ki je ba?"
Na sunkuyar da kai " Ummah ni na tsinke da lamarin ne,
lokuta na zan ta Gatawa a banza, daga karshe kuma lamarin ya kare
da bakanta min rai da shiga damuwa"
Ta girgiza kai " kar ki fadi haka, baki san lamarin Allah ba, a
ko wane lokaci Allah na iya yin abin da ya fi karfin tunani"
A daidai lokacin Habib ya dawo " Yaya yace don Allah don
Annabi ki daure ki fito"
"Jeka ka ce tana zuwa" Mahaifiyata kenan ta mayar da shi. Ta
juyo gare ni " Tashi ki shirya " da fadin haka ta tafi.
Ba ni da zabin da wuce na fita din, dole na kimtsa na fita.
Yana tsaye a jikin mota, fara ce mai matukar tsari, daban da
wadda na gan shi da ita dazu da rana.
Na karasa cikin alamun mutuwar jiki, a lokacin da shi kuma
ya ke aikin murmushi. "Ya hakuri Karimah na san ba ki so fitowa
ba, amma ina neman afuwa"
Na jingina da motar ni ma " Ina yini?"
"Lafiya kalau, yaya gida?"
"Lafiya lau"
"To madalla, ina ga zai fi kyau mu dan shiga daga mota, domin waje ta yi sanyi sosai"
Da gama fadin haka sai ya bude motar, ya zauna gami da bude min daya bangaren ni ma. Na shiga na zauna ba tare da na
kulle kofar ba. Ya ci gaba " to kafin na bayyana miki abinda ke
raina, zan so don Allah ki fada min abinda ya sa ba kya son fitowa, shin wai ba ki amince da ni ba ne?"
"idan ban amince da kai ba har na shiga motar ka dazu?"
"Ni ma haka na gani, shi yasa ma har na sami karfin guiwar
zuwa, amma don Allah me ne ne matsala? Ki fada min iya gaskiya
ba na so ki boye min komai"
Na shiru gami da kurawa dash board din motar idanu, ba da jimawa ba hawaye ya gangaro kan kumatuna.
Ya girgiza kai " la! Me ne ne na bata rai kuma? Ко
tambayar ta wace ta ba ta yi miki dadi ba? Idan haka ne ki yafe ni,
zan kuma kiyayewa kara yin makamanciyarta"
Na sa hannu na share " ba tambayarka c 6ata min rai ba,
wani dai abin na tuna da ya ke da nasaba da labarin da na ke shirin
ba ka"
Na dan dakata kafin daga bisani na dora" idan baka manta ba
dazu na shaida maka cewa na yi aure a baya mijina Abdul wanda
mu ke matukar son juna, har Allah ya ba mu haihuwa daya da shi,
amma 'yar ta rasu"
Ya girgiza kai cikin tausayi " Allah sarki"
Na ci gaba " tsautsayi ne ya sanya shi auren wata yarinya,
ashe cutar kanjamau ce da ita aka boye, sai daga baya aka gano.
43
Bisa wannan dalili ne ya dauke ni muka je wajen gwaji, cikin
rashin sa'a shi ya dauki cutar nice dai Allah ya kiyaye. Amma bai
fada min haka ba, boyewa ya yi, yace shima lafiyarsa kalau,
sakamakon sanar da shi da na yi cewar ni fa babu abin da zai raba
mu. Kwana daya da karbo sakamakon ya yi min dabara, yace
daurin aure za shi, ashe garin zai bari, sai dai na ga takardar sa, a
ciki ya fada min halin da ake ciki, ya kuma sanar da ni cewa ya bar
garin ne domin na hakura da shi na kuma samu mijin aure. Sai dai
ni ban so haka ba, a ra'ayina babu abinda zai raba ni da mijina.
Faruwar haka ta sanya mutane daukar cewa ni ma ina da cutar,
kuma suke rade-radin haka a gari.Wanda shi ne ya sa har na kawo
yanzu ban yi aure ba"
Ya girgiza kai cikin jimami " Amma na tausaya miki, dama
haka take faruwa, duk wadda cutar ta kama mijinta ita ma ba ta
samun mijin aure, ko da kuwa ita ba ta kamu ba. Sai dai jahilci ne
ya kawo haka, yanzu lokaci ne na wayewa, idan kana shakka sai ka
je a gwada ta, ba shikenan ba? To Karimah ni wannan dalilin ba
zai sanya ni janyewa ba, na yaba da ke dari bisa dari. Tunda na
rasa mata ta na rasa wadda za ta maye min gurbinta. Wayayyiya ce
mai matukar saukin kai, abinda ya bambanta ta da wayayyun
yanzu, wadanda girman kai ke matukar damunsu. Amma daga
haduwa da ke dazu na gane cewa yanayin ku daya, saboda haka na
yi mata, me ne ne ra'ayinki dangane da ni?"
Na yi jim tsahon lokaci ina mai tattauna lamarin a raina, daga
bisani na dube shi "To ka bari na yi shawara"
Ya girgiza kai " So baya bukatar shawara Karimah, in har
kana son abu da ganinsa zai shiga ranka, idan kinsa ka ke yi ma
haka"
"Haka ne, to ka bari mu je a gwada ni tukunna"
"Ma'ana kin amince da ni, kina so na?"
Na rufe ido cikin kunya " Ina sonkaan sbiede an
Ya yi murmushi " Alhamdu lillahi, to ni bana bukatar a
gwada ki, soyayyata a gareki tasa na yarda da abinda ki ka fada"g
Na girgiza kai" ban yarda ba, akwai bukatar kore ko wane irin kokonto daga ranka"
"Ba na kokonton komai Karimah, wallahi na amince dari bisa dari"
"To iyaye fa, da me za ka kafa musu hujja? Ka dai san sai
zancen abin da ya faru da ni ya je kunnensu, kuma suna iya hanawa"
Ya yi murmushi "kar wannan ya dame ki, Allah ya bani iyaye
wayyayyu. Mahaifiyata ma'aikaciyar banki ce, mahaifina kuma darakta ne a matatar man fetur ta Port Harcout, kin ga kuwa sun
san ko me ne ne rayuwa, Karshen boren da za su yi shi ne su ce sai
an gwada wannan kuwa ba damuwa"
Na kada kai " Shikenan Allah ya tabbatar mana da alherinsa"
Ya amsa " Amin, amma fa tsaya ki ji ba wąni lokaci mai tsaho na ke so a diba ba, zan yi wata tafiya kwanan nan zuwa Dubai harkar kasuwanci ce za ta kaini can, kwana biyar zan yi a
can, da na dawo na ke so a yi biki, domin zan sake komawa. Idan
na koma kuwa zan yi kamar wata uku a can, tare na ke so mu tafi"
"To zan fada a gida, abinda suka ce shi kenan"
"To zan dawo gobe na ji"
Ya bude aljihun mota, a hankali ya zaro rafar 'yan dari biyu jimlar Naira dubu ashirin " ga shi kin sayi jan baki"
Na kalli kudin sannan fuskarsa " ka ga kar ma ka wahalar da
kan ka, ba zan karbi ko sisi ba"
"don Allah don Annabi ki karба"
Na zura kafafuwana waje " wallahi ba zan karba ba, ka ga ma tafiya ta sai da safe"
"Karimah "ya kwalla min kira
Ban waiwayo ba.
don Allah dawo, wallahi wata maganar ce"
Da na ji ya rantse sai na dawo, na dan sunkuyo domin jin abinda zai fada
"don Allah ki rike alkawari fa, kar na zo ki ce kin canza
ra'ayi, ki taimaka ki yi min muhalli a inda Abdul ya bari"
Na girgiza kai " Gaskiya zan fada maka, ba zaka sami
muhallin Abdul ba, kai ma dai na yi maka na ka dabam"
"To nagodc a hankali zan shiga na Abdul din ma"
Na karkada yatsa "Abdul babu mahalukin da zai sami shiga
muhallin Abdul, yayin min abubuwan da waninsa ba zai iya ba"
"wadanne abubuwa ne? fade su na ji, ni kuma na yi
alkawarin yi miki su, in nuna miki cewa bai fini kaunar ki ba"
Da na ji yana neman wuce gona da iri sai na juya, domin
kadan ya rage ya fara ba ni haushi. Na shige gida bayan da nace
masa "sai da safe"
Kwanaki masu auki suka shude min cikin warwarewar
matsaloli. Mu ka shaku da Anas sosai, bayan da ya zo wajena sau
da dama. A halin yanzu yana so na je na gayar da iyayensa ne,
daga nan kuma sai a shiga maganar biki.
Ranar Lahadi da karfe ukun yamma ya zo domin mu tafi. Na
shirya kwalliya tsaf, sannan na shaidawa mahaifiyata cewa za mu
tafi. Ta yi min a dawo lafiya, na nufo waje.
Yana cikin mota a zaune, shimfidediyar mota ce kirar
Macedes E class da ganin na taho ya bude min kofa, ina zuwa na
shiga, na ja na rufe.
Ya kura min ido ba tare da ya yi kokarin tashin motar ba,
daga bisani ya jinjina kai " Tabarakallah!"
Na dube shi " me ne ne ya faru?"
Ya yi murmushi "Karimah kin keru, wallahi ba zan boye
gaskiya ba, kin fi mata ta kyau nesa ba kusa ba. Gaskiya na
tausayawa Abdul, ba karamin rashi ya yi ba. Ni kuma na taya
kaina murna, domin na yi babban samu, godiya ta tabbata ga
wanda ya yi shekara ta zamo mai fasali-fasali, cikin fasalolin ya
fifita na damuna, wanda a cikinsa ruwa ya ke sauka, kasa ta tsotsa
Harta koshi tabar ragowa a sama, mota kuma ta shiga ciki ta fantsalawa mutane"
Nayi 'yar dariya "dama duk kewaye kaweyen nan naka tsokana ka ke son yi?"
Dariya yayi shima, sannan ya tashi motar bayamda ya wadata kasancewar tamu da shan suti daga wani faifan CD na baamiriken mawaki Joc awata waka wai ita “I wanna know"
Cikin natsuwa da kuma alfahari da lokacin da ya sami
kansa ya ja motar muka tafi. Tafiya ta dogayen mintuna ta iso damu wani kantin sayarda kayan masrufi na zamani: nadubi
Anas. “saurara zan danyi sayayya anan".
"me zaki saya?"
"Zan dan siyi abinda zanyi tsaraba ne, kasan ba naje hannų biyuba"
Ya gyada kai "hakane" sai yanemi waje ya tsayar da motarsa.
Muka fito tare gamida Jerawa zuwa cikin kantin,
alokacinda na tabbatar da cewa yana alfahari da ni fiye da yanda nakeyi dashi.
"me ya kamata na siya?" nanemi ra'ayinsa. Hannayensa ya juya “oho"
“Nuna min kantar da ake ajiyeshi?
"Me kenan?" Ya nenami ji.
"Shi oho din" Dariya ta kamashi. “kai karimah baki da dama, amma zo muje na nuna miki abinda zaki siya"
na bishi har zuwa gindin wasu kantoci, dubana yayi gamida nuna minsu da hannu "kin gansunan Daddy da Mummy basa girmama wata kyauta sama da wannan, agaresu wanda ya basu wannan yagama komai.'
Na fara nazarin kantar, turarurruka ne Iri-Iri akanta,
masu saukin kudi da kuma masu tsada, nidai ba zan wuce masu
saukin kudinba, su na diba harguda biyar, sannan mukaje wajen kashiya (cashier) na biya kudi muka sake dawowa mota tare.
47
Bayan mun dan jima da barin kofar kantin ya waiwaye
ni "karimah akwai abinda ya kamata nayi wanda kuma ban yi
shinba"
"meпene shi?"
"kamata yayi ace ni na biya kudin, to amma naki biya ne
domin farantawa zuciyata, da kinji farin cikin dake lullube da
ita ahalin yanzu dakika kashe kudinki domin faranta ran
iyayena kin yi mamaki,kinyi min komai karimah."
Nadanyi murmushi "haba anas, ina abin yake anan?
turarene da bai wuce afesashi abaundakiba"
kallona yayi da sauri “kin san kuwa abinda kika ce?"
na gyakda kai na sani mana"
"menene hujjarki na fadin haka"
Nadan daga idona kadan “Anas zolayar kaina nayi in har
nayi zaton cewa iyayen mu da zumuje gayarwa zasu fesa
wannan turaren, matakin rayuwarsau ya wuceshi"
Ya yi 'yardariya " karimah kenen, kina da gakiya baki
da gaskiya, gaskiyarki itace; hakika in har zasu sayi türare da
kansu ba wannan zasu sayaba, rashin gaskiyar kuwa zasu fesa
turaren saboda hanyar da yazo daga ita. Karimah iyayenmu
suna sona ni kuma ina sonki. Kinga kuwa zasu martaba abinda
kika kai.
Na kuma ji dadi matuka yanda kika danganta iyayena da
kanki, na kara amincewa raina cewa kece matar da ya kamata
na aura, matarda take kallon iyayena amatsayin nata, wanda
hakan shi zai sanya ta girmamasu"
A wannan lokaci ya karkata linzamin motar nahiyar
wasu kayatattun gidaje, bayan yar karamar tafiya ya sanya
signal, kokarinsa kai hari nahiyar wani katafaren gida,
tsantsarere kerarre da fulawoyi suka baibayenshi, cikin sauri
maigadi ya bude mana kofa, yadan rusuna gamida yi mana
maraba, shi kuma sai ya tura kan motar ciki a-gindin wata yar
matattakala yayi fakin. Sannan ya gayyaceni zuwa ciki. Duk
inda muka saka kafafunmu babu komai illa kukan na'urorin
sanyaya dakuna gefe kuwa shuke shukene acikin kwatarniyoyi,
haka muka yi ta tafiya har zuwa wani rukuni-inda anan muka
tararda wata katuwar kofa ta gilas na tabbata ba ko ina banc illa falon shakatawa.
Anas ne yadan janye kofar sannan ya tura kai gamida gayyatata. Dakin wadace yake da mugun sanyi, sanyinda na tabbata na'urorin sanyaya dakine suke haddasa shi, akwai carpet (kilishi) mai kyau dalaushi kewaye dashi, duma duman kujeru na alfarma, rukuni guda mai tattare da kayan wuta, wanda acikinsu ne wata dingimemiyar talabijin ke aikin nuna Hoto, wadda garetane mutanen biyu suka mayar da hankali.
Bazan iya kiyasce wanda yafi nuna murnar ganina
tsakanin mutane biyunba, suntareni kyakikyawar tarba, sun kuma nuna farincikinsu da ganina amatsayin wadda dansu ya zabo.
Wajen awa biyu nayi agidan cikin karamci da girmamawa.
Anas ya mayar dani gida bayanda nasha goma ta arziki, shi kansa saida yayi min yan sayc saye awani kanti
Yadube ni saʼarda na ke shirin fita daga mota. Karimakh kifada agida jibi zamu kawo kaya kuma awajen za'a fadi ranar daurin aure"
Na gyada kai “shikenan"
"dubbanni nan” naji muryarsa na umartata.
Na kalleshi a hankali murmushi naga yanayi "Kinyi farin ciki da cewa zan zamo mijinki?"
sun kuyr da kai nayi cikin jin nauyi.
Yakara yin wata tamanayar "amma yanzu na shiga mahallin Abdul ko?
Nadaga kaina da sauri, kura masa ido nayi cikin yanayin dake nuna a kwai shakkuga abinda ya fada, Ya ci gaba. Ki shaida min gaskiya karimah na kama kafar Abdul aranki". Girgiza kai nayi “Anas agaskiya baka kamaba, ba kuma na zaton zaka iya kamawa azahirin gaskiya ka fishi kudi, kyau kuma akwai alamar tambaya amma Abdul nesa ba kusaba ya zartaka iya mallake zuciya"
"Wace hanya yake bi?"
49
Nagirgiza kai "ba naceba, saidai na amincewa raina а
jininsane.
Yayi murmushi raidai! da sannu saina fatattaki
tunaninsa daga zuciyarki.Allah ya kawomin ke zaki shaida"
Na fice daga motar cikin musanta abinda ya fada araina.
Karfe daya na rana gidanmu ya cika da yan uwa da
abokan arziki, an shirya kaya iri- iri daga abinci zuwa kayan
shaye-shayc awani mataki na kar bar baki masu kawo kaya.
A yanzu ba kamar wancan karonba, ina murna
dawannan auren da zanyi, ko ba komai Anas matashine, bansa
ran samun cikakken farin ciki awajensa kamar yanda- na samu
a wajen Abdulba, amma dai na san zan samu daidai
gwargwado. Cikin sanda da jan rai rana tayi ta matsawa har
lokaci ya kai karfe hudu, an zarta lokacin da su Anas sukace
zasu zo da wajen awa guda, saidai ba adin damuwa bane, duk
wanda yasan harkar mata yasan ta gaji haka, musammun akan
abinda ya shafi aure.
Muna nan zaman jira biyarma tayi ta wuce, shida kuma
ta kawo jiki asannan ne abin ya fara damu na, muaiman da
naji an fara taraddadi awaje anya zasu zo kuwa?.
Na fara ji ariana tamkar na lulluba mayafi na tafi gidan
su Anas domin shaida musa ana jiransu ba zanso a watse babu
biyan bukata ba, ko ba komai hakamma zai haifar da wasu yan
rade radi a gari,
Ina cikin wannan tunani Habib ya shigo, shaida min ya yi
Anas na magana a waje, sai na fita da sauri. domin jin wace ake
ciki, abinda nake rayawa a raina cewa zaiyi anan dage zuwan sai
da dare.
Jingine na sameshi ajikin mota, yanayin daa na same shi
a ciki ya nemi tayar min da hankali.
50
Babu wani abu makamancin walwala a fuskarsa. Ban kuma jiyo
kamshin turaren da na saba jiyowa a tare da shi ba. IHakan ya na nufin ba cıkin shiri ya yo tafiyar ba.
Na karasa gare shi cikin sanyin guiwa. Gaishe shi na fara yi
cikin halin shan jinin jikina. Karewaz, gaisuwar sai ta katse kowacce irin kalma daga bakunanmu, shuru ya aboce mumu ka yi jigum kamar masu jimamin wani abu. Tsawaitar lokaci cikin wannan hali ya sanya Anas yin karfin hali, ya kalle ni kamar zai zubar da kwalla " ki gafarce ni Karimah, sako na ke dauke da shi mai hargitsa zuciya"
Da fadin haka sai ya yi shiru, ni kuma tsoro ya kara cika zuciyata, ko raba daya biyu ba na yi abin da na guda tun asali ne ya afku.
Na dubi Anas cikin takaici " ka ga kar ka tsaya kewaye-kewaye, na
san sakon na ka bai wuce ka ce auren mu ba zai yiwu ba"
Shiru ya yi bai ce komai ba, wanda wannan ma amsa ce ga
zance na. Gano haka ya sanya ni fuskantar gida "shikenan Anas, haka Allah ya yi"
Karimah " ya kirawo ni da sauri
Ban amsa kiran nasa ba, ban kuma ko waiwaya domin
dubansa ba, a lokacin tuni zuciyata ta fara tafasa, hawaye kuma
ya dade da cika kumatuna, juwa ta fara dibana. A lokacin daidai na ke da na kamu da hauhawar jini.
Karimah" ya kara kira na, bayan da ya biyo ni
" ka ga ka rabu da ni, ka yi tafiyarka kawai tun da ba ka ra'ayina"
"kar kiyi min haka" ya fara fada cikin rawar murya, a kuma lokaci guda da ya rike min mayafi, na waiwayo cikin fushi, niyata
itace na kwada masa mari, to amma abin da na gani a fuskarsa sai
ya karya min zuciya, tamkar tawa fuskar hawaye ne cike da ita.
Ya ci gaba da magana " Karimah don Allah kafin ki dauki
mataki a kai na ina so ki tsaya ki ji abin da zan fada"
"To me ne ne fadi na jin abin da zaka fada Anas? Zancen dai guda daya ne, baya wuce kace auren mu bazai yiwu ba, to na kuma
51
ji, ba sai ka kyale ni na tafi ba. Tun farko sai da na nuna maka
shakku akan lamarin, amma son ka wahalar da ni ya sanya ka
kawowasu Kabli da ba'adi, to ga shi ba su amfana ba"
Ya ci ji lebe gami da girgiza kai " haba Karimah ke kan ki
kin san ni mai kaunarki ne, kuma na so aurenki kamar yanda ke ma
ki ka shaida, to amma matsala 'yan 'uwa sun dami iayena, vi
akwai hadari cikin matar da mijinta ya ke da cutar. Na yi kokarin
ganar da su akan cewa lafiyar ki kalau amma sun gaza ganewa, har
Éarya na yi cewa mun je an auna ki amma su ka ce ina! Matakin
suna Karshe ma wai ba zan auri bazawara ba. Karimah na rasa inda
zan saka kaina, ni kaina na san cewa 6ata miki lokaci na yi amma
don Allah ki yafe ni"
" to sakar min mayafi, ba mutunci ba ne mutane su wuce su
gan ka rike da mayafina. Ka je kuma Allah ya yafe mu gaba daya"
Ya saki mayafin cikin mutuwar jiki "To don Allah don
Annabi tsaya ina zuwa"
Jin girman magiyar da ya yi ya sanya ni dakatawa. Ya isa
motarsa da