Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
makama. Na sani Abdul yana yi min abubu a, sai dai babu maganar mallaka ko asircewa, kaunarsa gareni ita ta kawo haka, sakamakon biyayya da kyautatawar da nakc yi kullum. Bayan rubuce-rubuce, alkali ya fara yanke hukunci, mallakamin gida ya fara yi, ya kuma yankewa kowa hukunci daidai laifin da ya yi, wanda diyyar bata min suna duk tana ciki. Sai dai na kudure a raina, daga gidan har diyyar bana son ko daya, duk zan tarkata na mayarwa Hajiya, tun da basa gabana, ba kuma su isa tsone min ido ba. Bayan tashi daga kotu 'yan jaridu suka yi caa a kan mu, ban yarda na yi magana da kowa ba, amma Hajiya tayi, inda take neman gafarata gami da Allah wadai ga abinda 'yarta ta yi. Zuwairah da Uwani ma sun nuna nadamarsu, hirar da kafafen yada labarai suka yi ta sawa, duk duniya kuma ta ji. 26 duk inda na yi sai idanu su bi ni da kallo. Na ji ina ma ban zo ba, to amma tun da mai afkuwa ta afku dole sai hakuri. Na shige dakin mai jego domin samawa kai na sa'ida. Mu ka yi ta hira da ita, har ya zuwa lokacin da zama ya gagare ta, sakamakon masu son ganinta da suka yawaita ako'ina. Na kasance anan tare da wasu mata su biyar, hirar su suke yi, yayin da ni kuma na ke fama da tunane-tunane. A haka aka shafe dogon lokaci har zuwa sanda aka fara raba abinci. Faranti guda aka shigo mana da shi dakin. Kwata-kwata abincin baya gaba na, to amma sai na amincewa a raina akan na ci don gudun kar a yi min wani zato daban. Na dubi matan " Ku zo mu ci abinci ko?" Suka yi musayar kallo, sannan daya daga cikinsu ta yi murmushi " ai mu nan mun koshi" Ban taba jin irin haka a gidan sabga ba, kuma hakika ina da ja akan abin da ta fada, to amma ba ni da ta cewa ni ma sai na zurawa abincin idanu. Wata 'yar yaye da uwarta ke zaune a dakin ta gaza jurewa, hakan ya sanya ta tasowa da sauri, tana zuwa ta fara kokarin duma hannu. Zafin abincin ya sanya ni rike hannunta, na kuma sa hannuna na debo inda babu zafi na kuma fara kokarin kaаi mata,baki. Tuni yarinyar ta bude bakinta. "Kai! kai!! " uwarta take dakatar da ni, amma ina! aikin gama ya gama, tuni na juye mata a baki. Da sauri ta taso ta janye yarinyar, ta matsa bakinta gami da zura yatsa da kwakulo abincin. Sai na tsaya cikin mamaki, ina mai tunannin abin da ya sanya uwar hana a baiwa 'yar ta abinci, alhali kuma yarinyar tana bukatarsa. Da wurwuri na gano dalilin, wato suna dari-dari da ni ne bisa zaton cewa ina da cutar kanjamau, abin da ya sanya su cewa da ni kenan sun koshi. Da tuna haka sai na fashe da kuka, na mike tsaye gami da daukar jakata, ban tsaya wata-wata ba na saka takalmana na nufi waje. Kukana ya sanya hankulan jama'a kawowa gare ni, abinda ya sanya galibinsu tambayar abin da ya faru, ban tsaya baiwa kowa amsa ba, maimakon haka sai na nufi gida. Har biyo bayana mai jegon ta yi tana ba ni baki na ki kulata, dole ta hakura ta koma. Da isa ta gida mahaifiyata ta dube ni a firgice " me zan gani haks 'yar nan ?" " Ummah abinda na ke gudu ne ya faru, an tozarta ni a cikin taro, wai ba za a ci abinci tare da ni ba" Zancen nawa ya sanya jikin mahaifiyata sanyi, ludayin miyar da ke hannunta ya sullube, ita ma sai ta fara taya ni kuka. Shi kenan aka rasa mai lallashin wani. *.. Al'amarin da ya faru da ni a gidan suna ya Kara tilasta min zama ko yaushe a gida, bana sha'awar zuwa ko ina, mahaifiyarta ma bata kokarin tura ni. Daidai da kawayena sai dai su zo su tarar da ni a wannan hali, na share wata tara cur. Ranar wata juma'a da safe mahaifina ya kirawo ni dakinsa, ya zaunar da ni tare da mahaifiyata. Ya dube ni "Karimalı dama na kirawo ki ne domin har yanzu ban ji an ce da ni komai ba" Mahaifiyata ta saka baki " Alhaji ba wai aure ta ki yi ba, abin tambaya anan shin ina mijin? da ace wani ya zo ai tilas ne ta canza shawara, matsalar kenan babu wanda yazo, kuma babu alamun za a zo din" Mahaifina ya yi shiru tsahon lokaci, daga bisani ya cira kai. Dogon numfashi ya fara ajiyewa, sannan ya fara da cewa "in har rashin miji shi ne matsala, to zan kawo mata miji, amma fa sai dai ta yi hakuri, ta san ba zan iya samo matashi ba" Kirjina ya buga da karfi sau da dama. Ba zan so ace wai zuwa aka yi aka samo min miji ba, ko babu komai zai fi kyau mutum ya kawo kansa, wanda hakan ma kyau a bari nace yayi min, amma ba wai a turo min wani ba, kuma dattijo kamar yanda ya fada. Kuma in har ya turo din ba ni da damar cewa a'a domin yin haka zubarwa mahaifina daraja ne. "Ke!" Mahaifiyata ta kira ni Na amsa cikin shasshekar kuka. "To kin ji abinda mahaifinki yace, me kika gani?" Ban iya ba da amsa ba, sai dai na ci gaba da kukana. Mahaifina ya dora "To shi kenan da alama ranki ba zai so haka ba, ni kuma ba zan tilasta ki abinda ba kya so ba, gara na jure kunan ran da na ke fama da shi sakamakon ganinki a cikin gidan. Tashi ki tafi shikenan" Na fashe da wani sabon kukan, ba zan taba so ran iyayena ya rinka kuna ba, dan haka gara ni na rungumi kaddara, na bi abin da ran iyayena ke so, na jure duk wani matsi da kunan zuciya. Na fara magana cikin shehsekar kuka " Babu komai Abba ka turo shi ko wane ne" "A'a Karimah kar na yi abinda ba haka ba, na takurawa rayuwarki haka kawai, gara na hakura na zubawa sarautar Allah ido, duk abin da ya zartar shi ne daidai" Na share hawaye " ka turo din nace Abba, Allah ya zaba min na gari" Ya yi shiru tsahon lokaci, daga bisani ya kada kai " to shikenan tashi ki je Allah ya yi miki albarka" Na tashi na nufi dakina, a can na kafa wata sabuwar majalisar ta kuka. Mahaifiyata ta shigo ta same ni " Karimah kin ce kin amince kuma kina kuka, kina ganin ran Alhaji zai so haka? Idan kin san da matsala ki fada tunda wuri" dacewa" Na share hawaye "babu komai Ummah Allah ya ba mu Sai na mike tsaye na nufo tsakar gida, ina zuwa na hada wanke-wanke, na shiga yi kamar yanda na saba kullum, amma fa ta ciki na cikai, don bakin ciki ji na ke yi kamar jijiyoyin da ke rike da zuciyata za su tsintsinke. *** A safiyar wata lahadi mahaifiyata ta sanar da ni cewa zan yi bako, saboda haka na zama cikin shiri. Da yamma kuwa sai ga Habib a cikin gida. "Karimah ana magana a waje" 99 A Na mike tsaye, jikina babu ko wani cikakken karfi A ina bakon ya ke yanzu?" Yana cikin sitting room " Sai na nufi dakina, har yanzu bana jin karfi a jikana, sakamakon rashin sha'awata da kara aure. Gashi kuma ban san ko yaya zan tarar da bakon ba. Na shirya tsaf na nufo waje. Farar mota Toyota Carina na fara gani wanda ko tantama ba na yi ta bakon ce. Na yi sallama a kofar Sitting room din, na jira jin amsawa daga ciki, sannan na saka kafata. Kamshin turare mai karfi na fara karo da shi, daga bisani idanuna suka tsinto min mutumin zaune akan kujera. Kakkaura ne iya kacin kauri, mai duhun fata gami da kananan idanu. Fafladan hanci gami da katon baki, ni dai a raina banga abinda zan yaba a tare da mutumin ba. Na durkusa har kasa na gaida shi, ko ba komai dai ya yi sa'an mahaifina. Ya amsa min da muryarsa ma'abociyar kauri. Ya yi gyaran murya bayan da muka gama gaisawa " suna na Alhaji Sadi, kuma ni abokin mahaifinki ne, shi ya yi min izini da na zo. Ina kuma da kowane irin sani akan abinda ya faru da ke, na kuma san abinda ya faru ya sanya jama'a gudunki, ba zan 6oye gaskiya ba, ke kyakkyawar mace ce mai cike da kuruciya, na kuma sani in har ba wannan dalilin ba, kin wuce aurena, ina shakkar ki zabe ni alhali ga sankacecen saurayi ma'abocin kyau kuruciya kamar ki ko ba gaskiya ba? Na yi 'yar dariya ban kuma ce da shi omai ba. Ya ci gaba" To amma ratsawar rabo ta sanya su yin bayabaya, bisa wani zato na banza da wofi, sai takamar cewa an yi ilimin zamani amma ilmin yana shirin ficewa tare da hayaki. A gani na babu sauran duhun kai a wannan lokaci, zamani na kwararru da wadatar na'urori, babu shakka sai akan abinda mutum ya sa kan sa, to amma duk an manta da wannan an ci gaba da rayuwa irin ta zamanin da can. Karimah kar ki ji ina maganar kwararru da na'urori ki yi zaton cewa ina nufin za a auna ki, ko kusa babu shakku a raina, na yarda da abinda Alhaji ya fada. 30 3 Mutum ne shi mai gaskiya, mun dade tare da shi, kar ki yi mamaki idan nace ba ki wuce 'yar yaye ba" Zancen na sa ya ba ni dariya. Ya dora " Ai gaskiya ne, ni ba na yau ba ne ba, na sha miya gaskiya, to amma abinda na ke so na ji daga gare ki shi ne shin na yi miki ko yaya? Amma fa kafin ki amsa ga karin bayani, matana uku, ta hudu ce ke, 'ya'yana kuwa ashirin da hudu, yaya ki ka gani?" Tafdijan! Rututu kenan, anya kuwa zan iya zaman gidan yawa da mutum sa'an mahaifina mai mata sa'annin uwata? Shin yaya sunan zama tare da su? Kishiyoyi ne ko kuwa iyaye? A nan fa ake yenta, wace amsa zan ba shi kenan? "Ba ki ba ni amsa ba " ya tuntube ni Na yi ajiyar zuciya, babu zato kuma na ji hawaye na shirin fitowa daga idanuna, ba zan so ya ga haka ba, sai na kunshe kai na a cikin mayafi, anan na goge kwallata. Ba tare da na fiddo kan bana ba shi amsa, bayan da na tuna cewa mahaifina ne ya turo shi, na kuma yiwa Abba alkawarin karbar duk wanda ya turo. "babu komai Allah ya ba mu zaman lafiya" Ina jin sa'arda ya yi dariya, alama murna ce ta kama shi, sai dai da ya san yanda zuciyata ke tafarfasa kamar ta kama da wuta da ya shafa min lafiya, da kuma zai ga hawayen da idanuna ke zubarwa da murnarsa ta koma ciki, to amma ban bari ya gani din ba. Ya ci gaba " kin san ni dai ba yaro ba ne, saboda haka ba dogon lokaci zan diba ba, sati mai zuwa na ke so a daura aure" *** Gayyar motoci da babura suka cunkushe kofar gidan mu, sai dai ba su ne abin la'akari ba, jama'ar da suka debo sun yi matukar nunkasu. Wadanda ke ta nuna murna da farin ciki, haka abin ya ke ga iyayena, sai dai a nawa bangaren ba haka ba ne ba. Don tsabar bakin ciki ji na ke tamkar kirjina zai dare biyu. 31 A daren ranar ta Lahadi kwana na yi ina kuka a dakina, a yinin na ta ma haka ce ke shirin faruwa, domin na shiga ban daki ya kai sau bakwai, ba kuma komai ne ya ke kai ni ba illa cin kuka. Idan na tuna wasu abubuwa na kan sami kai na ina mai fatan Allah ya dauki raina. Na kan tuna rayuwata ta farin ciki tare da kyakkyawan matashin tsohon mijina, rayuwar da bakin Karen bakin ciki ya dauke ta, ya yi kuma wata nahiya dabam da ita, ban san sa'ar da ya ke shirin dawo min da ita ba, mai yiwuwa ma ya cinye. Abu na biyu kuma da na ke tunawa shi ne sabuwar rayuwar da na ke shirin shiga tare da sabon mijin da ake shirin daura mana aure. Mutumin da na tabbata cewa ya kai sa'an mahaifina, ko tantama kuma ba na yi matan sa sun kai sa'o'in uwata. Shi kuma yaya rayuwa za ta zama tare da shi? Ban dai ce zan wahala a gidan sa ba, sai dai na san ba zan sami gata da tarairaya irin wadda na samu ni kuka. a wajen Abdul ba. Wadannan abubuwa su suke sanya Muryar wani maroki ta keto cikin gidan mu sa'arda na ke cikin halin tagumi "E! yanzu ma ango na iya kama hannun amaryarsa su tafi, ciniki ya rigaya ya shiga, sai kuma mun zo taron suna" Da jin haka na barke da kuka, shi kenan na mutu kawai, abin da na ke ganinsa mafarki-mafarki, almara-almara, ya tabbata, ba ni da sauran wani goce-goce. Mahaifiyata ta iso gare ni, hannu.a ta kama ta nufi dakin mahaifina da ni, muna shiga ta zaunar da ni. " Karimah yanzu kyautawa kenan ki tayarwa Alhaji hankali? Ki fa tuna bai aiwatar da komai ba sai bayan da ki ka ce kin amince, to amma yanzu ga shi kina kuka, a kuma lokacin da ki ka tabbatar da cewa zai shigo da baki, har cikin gidan, salon su tafi da tunanin tilas aka yi miki kenan?" Na sa hannu na rufe bakina, abinda ya tilastawa kukan tsayawa iya zuci, shi kuwa na tabbata ba zan iya tsayar da shi ba, sakamakon bakin cikin da na ke ciki, wanda na ke ganin cewa 32 3 yayi min yawa ni kadai da da halin rabawa da na raba biyu, in ji da rabi in ya so rabin kuma ya san inda ya nufa. 南市 Tun da rana, a ranar litinin Asma'u da Nusaibah suka iso, su ne kawayena da za su rakani gidan mijina da dare, haka muka zauna a dakina cikin zama mai kwaikwayon na makoki, babu mai cewa da wani komai, su kansu al'amarin bai yi musu dadi ba. Ni kuwa a lokacin zuciyata cike ta ke da tunane-tunane. Yau zan tare, kuma shakka babu yau mijin zai halarci dakina, wani dabam ba Abdul ba. Wannan tunani ya yi matukar karya min zuciya, wadda har ya tilasta min kuka. Karfe biyar din yamma daidai Habib ya shigo kira na wai Alhaji Sadi ne ya zo. Na tashi babu karfin jiki na nufi waje salalaf-salalaf, bayan da na gama kintsa fuskata, ta yanda ba zai fahimci halin da na ke ciki ba. A cikin motarsa na tarar da shi a zaune, wai irin abin nan an mallaka masa ni, saboda haka ni ma sai na shiga kenan, mu tattauna abin da za mu tattauna anan. Na sa hannu na bude daya bangaren, sannan na sulale ga zama akan kujera. Gaida shi na fara yi, sannan na tsaya sauraron abin da ke tafe da shi. "Karimah am ......." Sai ya yi shiru bai fadi abin da ya ke son fada ba. Na dube shi fuskata da alamar tambaya, shin me ya ke son fada ne da ya kasa? Can jimawa sai ya dora " Karimah wata magana ce ke tafe da ni, kin ga dai 'yan awoyi suka rage a kai ki dakinki amma ina tsammanin sai dai hakuri" Ya dan yi shiru kafin ya dora " abin da ke faruwa, illahirin matana iyayen 'ya'yana sun hade kansu, sakamakon kururuwar shaidan da ta shigar musu kunne, wai cutar kanjamau ce da ke" Kirjina ya yi wani irin duka, hankalina kuma ya tashi gaba daya. Ya ci gaba " wani mataki suka shirya dauka, ko wacce ta daure kayanta, wai kina saka kafarki za su jeho na su kafafun waje, su da gidan kuma sai dai su zo ganin 'ya'yansu. A fadin su da lafiyarsu ba za a kawo musu jallijoga ba. Kin dai san halinku na mata, saboda haka ina ga hakuri shi ya fi, ki je na bar miki duk abinda na kawo, zan sa a kwaso miki kayanki gobe, na saukake miki" Da gama maganarsa na fashe da kuka, ba wai ina kukan an sake ni ba ne ba, a'a ina kuka ne bisa ganin yanda mutane ke gudu na, na koma sai ka ce mutuwa, wadda na tabbata in ma har tana da masoya to ba su fi biyu a cikin ko wacce dubu ba. Alhaji Sadi ya ci gaba da ba ni baki. Haka na fito daga motar na nufi gida. Kukana mutan cikin gidan su ka jiyo suka fito tsakar gida, suka tambay a abin da ya faru. Na fada jikin mahaifiyata " Ummah wai har an sake ni, matansa ne suka bar gidan wai cutar kanjamau ce da ni" Labarin ya sanya kowa hawaye, tun ma ba mahaifiyata ba, wadda ta rungume ni tana kuka. *** Saki na da kuma kwaso kayana tun ban tare ba, ya zama abin yayatawa a gari. Ko wane gidan biki da na suna zancen da ake tattaunawa kenan, hatta da dalibai mata idan ki ka ga sun tsaya hira akan hanya, bayan an taso to zancen ske nanatawa. Don tsabar kage da iya kulla sharri, sai ake cewa v zuwa a ka yi aka auna ni shi ne aka ga ina dauke da cutar, ab. da ya sanya shi saki na kenan, kuma akan haka kowa ya yarda. Sai duniya ta kara yi min kunci, na rasa inda zan saka kaina, kullum ba ni da abokin hira sai kuka. Da abin ya kai ya kawo sai na yanke wata shawara,. Shawarar ita ce na bar garin, na koma can gidan wata yayar mahaifiyata. A wani kauye da ake kira Faruruwa cikin karamar hukumar Shanono. Hakan aka yi, na shaidawa iyayena shawarata, ba su nemi hana ni ba, domin su kan su zantuttukan na damun su. Suka yi min addu'a da fatan alheri, har ma da kyautata zaton cewa zan sami mijin aure a can. Na shirya kayana a akwati, Ranina Habib ya daukar min domin raka ni tasha, na yi sallama da iyayena muka fito daga gidan tare da shi. Na damu matuka da ganin yanda jama'a ke bina da kallo, sai dai babu yanda zan yi, gab da zamu isa titi, mu ka hadu da wasu 'yan mata guda biyu. Sai da suka gifa mu dayar ta ke cewa da daya "Larai kin ga jaraba za a bar gari" Dayar ta amsa da " Sai ta gaishe su" Wani abu ya kulle min zuciya, wai ni ake kira jaraba, ban shiga rayuwar kowa ba, an shiga tawa an yi kane-kane, don dai kawai Allah ya kaddara wani al'amari akan mijina Haka muka isa tasha ina wannan hali. Habib bai tafi ba sai da ya ga motarmu ta tashi, sannan ya juya ya nufi gida. RANA ZAFI INUWAKUNA waggo Gambo mace ce mai fara'a da son mutane, wannan G shi ne abin da ya sanya ni zabar komawa wajenta da zama. Ta yi matukar farin ciki da gani na, a kuma kwana daya kacal da na yi a gidan har hankalina ya fara kwanciya. Ga jama'ar kauye zama kawai ba shi yiwuwa. Da wuya ki sami mace ba ta da sana'ar kanta, baya ga kiwo wanda shi dama tamkar kwata ce a birni, gidan kowa akwai. Gwaggo Gambo ma tana da sana'arta da ta shahara akanta. Sana'ar kuwa ita ce sai da waina, inda za ki ga ana cuncurundon yo sammako domin sayen wainar ta mai dadi, tsafta, da kuma arha. Zuwa na ya kara taimaka mata, inda na ke yin wasu abubuwan daga aiyukanta. Kuma tana jin dadin haka nan. Kwana tashi, kwanaki suka jujjuya aikin ya ragu a gun Gwaggo, sai dai abin mamaki cinikinta ma ya fara raguwa. A sanda na zo na tarar tana yin wainar kwano uku, ba a jima ba ta १९ koma kwano biyu da rabi, haka-haka har ta koma ta kwano daya, ta kwano dayan ma sai ta nemi gaza saidawa. Ganin haka ya sanya ni zare hannuna daga aikin waina, bisa zaton cewa ko rashin fwarewata ne ya sanya wainar ta canza dandano, amma hakan bai maganta ba. Abu dai ya ci gaba da baya-baya. Shawarar da na baiwa Gwaggo ita ce ta sami wani daga cikin masu sayen wainar ta na kullum da yanzu ya daina zuwa ta tambaye shi dalili. Ta kuma karbi shawarar tawa. Wani yaro ta aika aka a kirawo mata wai shi Dan Ali, a fadinta tun da ta fara waina bai taba fashin zuwa ba. Yaron ya zo, shekarunsa ba su fi goma zuwa sha biyu ba. Ta dafa kafadarsa "Dan Ali me yasa yanzu baka zuwa sayen waina?" Ya yi shiru bai amsa mata ba, maimakon haka sai yasa yatsa a baki. " bari cin yatsa" Ta hana shi, sannan ta kara nanata tambayarta. Ya sunkuyar da kai " Inna ce tace mu bar zuwa nan, wai kabari salamu alaikum ce a gidan" Wani zogi mai kama da na babbar hanyar wutar lantarki ya bi jikina, sakamakon ji da na yi ni ce ummul aba'isin tsayawar cinikin waina. Bisa dukkan alamu labarina ya riga ni isowa kauyen kenan. Na baro birni saboda takura, ga kauyen ma ba ta canza zani ba. Sai na dafe kai na na kuma he da kuka. Gwaggo kuwa ta ma rasa abinda ya kamata ta yi, sai ta tsaya kawai kikam. Ni kuwa tuni na shiga daki na fara hada kaya, sai dai gani na ta yi na kinkimo akwati. Ta tare ni " Ina zaki je Karimah?" Na share hawaye"Gwaggo gida zan koma" " ba za ki koma gida ba, ai ba lallai ne sai na yi sana'a ba, zan ma hakura da ita gaba daya" Na girgiza kai " ba zai yiwu ba, ni kuma hankalina bai zai kwanta ba, gashi yanda za a tsangwame ni anan ba za a tsangwame ni a birni ba" Ta yi shiru cikin tunani da alama tana tattauna lamarin ne, bayan wani lokaci ta dube ni " To na ji amma ki bari zan raka kí har gida gobe" Na dage akan lallai yanzu zan tafi, tayi-tayi da ni na ki sakkowa, dole ta rabu da ni. Ta kawo Naira dari biyar ta ba ni, ni kuma na kama hanyar tashar kauyen, zuciyata cike da tsananin radadi. 中市市 Yayin da na iso gida magariba ta kawo jiki, na tarar da mahaifiyata tana kwashe tuwo, gani na ya sanyata dakatawa "me ya dawo da ke da wuri haka Karimah?" Na saka kuka " Ummah har gara nan da can, an daina sayen wainar Gwaggo saboda ni" Jimami da takaicin lamarin ya sanyata fasa kuka ita ma, " wannan lamari ! wannan lamari !! yaya za mu yi da shi ?! Allah ka dai gani, ka ji kan mu ka yaye mana shi" Na nufi dakina na bar Ummah anan, ina ajiye akwatin na fada kan gado, anan na ci gaba da kukana. Tsahon lokaci ban sassauta ba, har ya zuwa lokacin da aka yi kiran sallar magariba, sannan ne na yi karfin halin mikewa, domin nayo sallah. A wannan ranar dai ko abincin dare ban ci ba, haka na zauna a gefen gado, ina ta sake-sake, tunani na ke yi akan abin da ya fi dacewa da ni. A sake-sakena na sako abinda na ke ganin shi ne daidai. Na tashi na nufi dakin Ummah, cikin sa na tarar ba ta cikin me yiwuwa ta tafi kaiwa Abba abinci. Na fara dube-dube, kama daga kan taga har zuwa kwaba, na kuwa yi nasarar ganin abin da na ke son gani. Ina dauka na dawo dakina, karkashin filo na jefa shi, na tsaya sauraren dare ya kara rabawa. Awoyi suka yi ta canzawa, har ya zuwa lokacin da karfe dayan dare ta yi, a sannan sawu ya gama daukewa. 37 Na züra kafsfuna daga kan gado, kwano na dauka na zuba ruwa a ciki, sannan na daga filo na dauko ajiyata, irin maganin nan ne me kashe 6era nan da nan. Na farke ledar sannan na zazzzage shi a cikin ruwan, na sa hannu na dama sosai, abinda ya rage kawai na kwankwada, wanda da zarar na yi haka ko minti talatin ba na zaton zan kara yi ina numfashi. Na dauki kwanon da niyyar kafa kai. Na saba komai zan ci ko zan sha na kan ambaci Allah, wannan din ma ban manta ba, to amma yayin da na ambaci Allah sai hannuna ya fara kyarma, ban san sa'ar da kwanon ya kufce ba, tuni gubar ta kife a kas. Na kalli kwanon cike da tsoro, a lokacin na ji wata boyayyiyar murya na zance da zuciyata " Karimah kina fushi da abin da Allah ya kaddara, ba ki yarda da cewa shi ne mai ikon komai ba, mai canza abu a duk lokacin da ya so can za shi, sai ki ka zabi ki kashe kan ki, a zaton ki ita ce hanyar hutu. Sai dai abin da ba ki sani ba, za ki bari duniya mutane na wadai da ke, ki je.can kuma ki tarar da azabar mahallici" Da jin haka na fashe da kuka " ka gafarce ni ya Allah, ka yi min afuwa bisa abinda zuciya mai horo da mummuna ta kawata min aikata shi. Na yi imani, na kuma yarda kai ne mai yaye komai, Allah ka yaye min ni ma, ba don halin na ba sai don rahamarka da kuma tausayawarka ga bayi" Na tashi na fita waje, alwalla na yo, sannan na dawo daki, anan na yi ta nafilfili. Ina mai rokon Allah gafara bisa mummunar aniyata da na yi. Da na kammalla sai na bude alk'urni mai tsarki na yi ta karantawa ina mai zubar da hawaye, zuciyata tana mai nadama bisa abin da ta yi niyyar aikatawa. Tana kuma mai kwadayi da kaunar samun rahamar ubangijinta. Haka na kasance har hudowar alfijir. Na ji zuciyata wasai, tamkar wata damuwa ba ta taba shigar ta ba. TA LEKOО ТА КОМА uyawar yanayi daga zafi zuwa damina, ya kai jama'a da yawa J kas.

Chapter 3 of 6