Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
sauri, ya bude ya dauko wani dan akwati, a hankali ya nufo inda na ke a tsaye. "Ga wannan Karimah, kyauta ce ta musamman saboda matsayinki a zuciyata" Na yi masa wani kakkaifan kallo "Anas kamar yanda 'yan 'uwanka basa ra'ayina ni ma bana ra'ayin kayanka, ka ma mayar da mota domin hutar da kanka, ka ga ma tafiyata" Na nufi gida da sauri, ya yi kira, iya kira amma na ki na ko waiwayo, anan ba bar shi rike da akwatin a hannu. Ina shiga gida na zarce dakina. Zama na yi agefen gado na yi tagumi. Shakka babu nagama tabbatar dacewa ni da aure kuma fan!fan!!fan!!!. Shikenan na bi sahun mutan da, idan mazajensu suka mutu sakamakon mummunar cuta, babu batun aure sai dai ragaita a gari. Tausayin kai na ya kama ni, yanzu haka zan kare kenan har tsufa na? ga shi kuma ko dan dan da zai rika debe min kewa ba ni da shi. Mafarkin da na dade ina yi na haifar yarinya kyakkyawa ya 52 Bi hadarin kaka kenan, saina sami kaina ina mai fadin abinda da ahayyacina nake ba zan fadiba. Allah me isa ko yar Hamidan baka hariminba, gashi yanza yaya saidai na gani awajen wasu" Na fashe da kuka, wannan shi ya karkato hankulan jama'a ga dakina, xai gasu gungu guda. "Me ya faru karimah?" kanwar mahailiyata ke tanbayata ban bata amsaba. Kai na dafe ina kiran wayyo Allah na! Mahailiyata tashigo da sauri, zama tayi kusa dan igamida kwantar da kaina acinyarta "me kuma ya faru karimah? Cikin shashshckuar kuka na bada hayani. "Ummah dama na fada miki sauraran Anas ba zai haifar min da komaiba illa bakin ciki kika ce a'a ba hakaba, ga abinda nake gudu ya faru, yan uwansa sun zuge iyayen sa suncc ba zai aurcniba" Jin zancen nawa ya sanya mahaifiyata tafashe da kuka sauran yan uwa na kusama hakace tafaru, wandan da babu alaka ta jini kuwa suka kama sallallami.tsahon lokaci babu mai lallashin wani, haka mukayi ta fama, harzuwa lokacinda magariha ta kawo jiki, sannan ne kowa ya watse cikin halin mutuwar jki. Alokacin da mahaifina ya dawo yadawo ne da jinkarfin gwiwar an kawo kaya, amma sai ya tarar da abinda yatarar duk karfin zuciya da juriya irin ta mazaje saida yayi hawayc, yazo ya sameni a daki sa'arda na hada kai da gwiwa “karimah" na dago kai. Fuskata jike da hawaye yacigaba. "kar ki tashi hankalinki karimah, kidauka cowa wadannan abubuwa jarrabar ubangijice. Shi Allah dama haka yake, yakan jarraba bayinsa da Alheri da kuma sharri, yin hakuri da komawa garcshi sai su zama magani. To ina horonki da yin hakuri ki kuma kara komawa gareshi ki luzumci karańta wannan Adduah: INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UNA, ALLAHUMMA AJIRNI MIN MUSIBATI HAZIHI WA AKIBNI KIHAIRAN MINHA" kin ji ko, da yardar Allah komai zai ware" Na gyada kai "to Abhah nagode" Ya muke tsaye ahankali ya fice daga dakin yabarini cikin halin kurawa sili ido bayanda na zurfafa aduniyar tunani. 53 kwanakin juyayi taraddadi, da bakin cki suka kewayeni, kwanakinda acikinsu ne nake kwana kuka na wuni kuka badon komaiba sai don ganin abinda na fi karfin sa ada yanzu yana lallasani. Idan na tuna yan matancina lamirin kan kara firgitani, hakika sanda ina budurwa anyi budurwarda aduk sashin mu ba'ayi mai farin jinintaba, naga samari dabam dabam, na mota, na babur da na kasa duk sunso amincewawata lamarin ya zama kamar layi, lokacinda nake wajen wannan wancan na jirana, wanda hakan shi ya sanya Abba tsawatarmin ya kuma tilastani fidda guda daya, Abdul na zabo, domin aduk taronsu ya fi shiga raina. To amma yau gani ncman mijin nake ido rufe abin yaci tura. Allah sarki jiya bayauba. Ina ma gaba zata koma baya saidai kash! ba zata koma dinba. Lamarin janycwar Anas ya kara jefani wani kangin dabam, wata sabuwar jita jita ta kunno kai, kuma taci gaba da ruruwa, ba acikin mata kawaiba harda mazajen da basu san ciwon kansuba. Koda yake ada farkon tafiyar Abdul ina cewa nagama aurc, to amma yanzu sai na fashimci kurena, hakika aore ya wajaba akaina, musamman in har ina son ganina da yar diyar da zata rinka debemin kewa, diyarda na dade inagani a mafarki, ma'a bociyar kyawun jiki da yalwar gashi wadda zan tsaya tsayin daka domin ganin ta sami ilimi. Wannan buri nawa sai ya sanya a lokacin jinake ko tsoho na samu zan aura, koda kuwa zaice sai na biyashi kudi, saidai inal! tsofafinma basa sona domin gudun kar na kaisu kabari, kaico! Hakika nashiga tsaka mai wuya, abinda da nake gani ga wasu gashi yau akaina nabi sahun matayenda mazajensu ke yafa musu bargon tsiya, na fachimci cewa komai runtsi illar cutar ga mata take komawa, sauda dama su akę gogawa fiye da yadda su suke gogawa, kuma hakika gab ake da shiga zamaninda za'a nisanci, auren bazawara, ko wace iri ce ita, da wadda mijinta ke da cutar dama wadda ba hakaba domin koke koke sunyi yawa cewa da dama sun dauki cutar ajikin zawarawan da suka aura, idan kuwa hakane ashe za'a daidaita sahu, rigimar omo ko sabulun wanki zata daina kashe aure, ko don gudun kar ki bar lafiyayye ki auri alakakai, ko kuma ka saki lafiyayya ka auro jalli joga. saidai kuma akwai gyara, maimakon yan guje guje da akeyi kamata yayi idan mutum yaga yanaso aje a auna acibiyar bincike, hakan shi zaifi za makai wayc, kuma da hakan akeyi da dadama ba su shiga halin da suka sami kawunansu acikiba, saidai kuma yaushene zamuwaye? Yaushe zamu ga cewa yinhakan ba nuna kin yarda bane kuru-kuru? amsar itace babu rana, Ashe kenan duhun kai da karancin aiki da limi zaici gaba da ruguza mana rayuwa. acikin wadannan kwanaki da nake halin bakin ciki da tshin hankali, na farinciki da kwanciyar hankali suka iso ga aminiyata, shi kansa hakan ba karamar cuzgaunawa bace ga rayuwata, ita kadai dama ta rage min, ita take dan dehemin kewa, take kwantar min da hankali to gashi itama zata tafi abin takaici kuma ba agarin zasu zaunaba Kaduna zasu koma. ranar yinin bikin anga abin mamaki, ana farin ciki ina kuka, nusaibah ma bata sami sakewaba ta jani wani daki zaunar dani tavi domin ganaw a dani. "karimah wata shawara na yanke da nake ganin zata kawo mana mafita, kinga dai yanda Abubuwa ke faruwa anan garin. Na sani muddin kina nan babu ke ba kwanciyar hankali, kizo mutafi can tare, tunda gidansane, kuma shi kadaine a ciki na fada masa haka kuma ya bada goyon baya” halin bakin cikin da nake ciki bai hanani murmushiba. "Nusaibah kenan, kinzo da batunda zuciya ta ba zata taba lamuntaba, ko kusa babu dacewa nabiki wani gari alhali da minjinki' ta daga min hannu. “dakata kar kisa raina ya baci, karimah a zatona kawancemu ya dade da canza kama maimakon kawaye zaifi kyau a kiramu yan uwa. Inkuwa hakane menene don kin bini wani gari?" na girgiza kai "duk ba wannan ne matsala ba nusaibah, da acе ke babbace da akalla kika haifeni kuma shi kansa mukhtar yakai sa'an Mahaifina sai na biki, amma a wannan shckaru bazai yiwuba, musamman afarkon angwancinku, abinda baki saniba, ango da amarya basa bukatar kasancewar kowa kusa dasu, suna da bukatar kadaita domin su mori soyayyarsu, kinga kuwa zuwana zai zame muku cikashi ba haka nayi amarcinaba ba kuma zanso -kiyi naki hakaba" Da gama fadin haka na mike tsaye. Tashi tayi ita ma tarike min hannu "kar kiyimin haka karimah nazo da roko ki watsamin kasa a idanu, Idan kina zaton Abbahne ba zai amineeba naje na rokeshi' girgiza kai nayi "karma ki soma, wallahi babu inda zani, nadai gode da har kika yiminvannan karamcin, Allah ya bar zaumunci da kaunar juna" Haka ta rabu dani ba a son rantaba. Washe gari nabi tawagar da suka raka amarya Kaduna, gidane mai kyau a jerin gidajen masu hannu da shuni, wanda ya dace da matasa sabon aure kamar nusaibah da angonta, sunso na kwana biyu acan amma na kekashe kasa, dole suka rabu dani haka na dawo gida zuciyata cike da radadin rabuwata da aminyata. ALLAH MAGANI Sha shida ga watan uku ta zamo wata muhimmiyar rana ga jama'a musamman ma mata, ba don komai da sai don gagarumin taron wayar da kai akan cutar kanjamau (Aids) wanda kungiyar mata manoma, (WOFAN) tashirya Akwai wadatattun kujeru shirye a dakin taron, wadanda aka kasasu bangare biyu, bangaren hagu domin maza bangaren dama kuma mata, kamar yanda aka raba su kansu kofafi, na shige da ficen mata dabam na maza ma dabam. tsarin ya kayartar sosai ya dace da Addini da kuma al'adarmu. Sanin ccwa za'ayi haka shi ya karfafamin zuwa nima bayanda na hakkake cewa zan karu da wani abu. Bayan bude taro da addu'ah, sai shugabar kungiyar ta karanto tarihin kafuwar. kungiyar a takaice, aiyukan da ta saka agaba da kuma gudunmawar da ta ke nema daga Jama'ar gari da hukumomi. Sannan tayi karin haske akan. manufar taron da kuma dalilin shirya shi. Daga nan aka ci gaba da gabatar da kwararru daya bayan daya. Sun yi bayanai wadanda su ke masu gamsarwa, tun daga asalin samuwar cutar da kuma yanda ta rinka yafuwa, illolinta da kuma hanyoyin kamuwa da ita,yanda ya kamata mutum ya yi domin gujewa kamuwar da kuma yanda wanda ya kamu ya kamata ya rayu. Bayan wani lokaci sai aka fara gabatar da masu ba da shawarwari, musamman ma daga wadanda suka sami kansu a wani matsayi ta dalilin cutar. Wata mata ce ma'abociyar tsayi da dan kauri ta fara fitowa, ta fuskanci jama'a bayan da ta tsaya a gaban abin magana, to amma maimakon ta yi magana sai ta buge da share hawaye. Abin da ya ja hankalin kowa ga sauraron abin da za ta fada. Ta fara magana bayan da ta natsu " na rayu cikin taka tsantsan da kame kai, sakamakon kyakkyawar kulawa da iayena ke bayarwa yayin tarbiyantar da 'ya'yan da suka haifa, wannan ys s mijina shi ne farkon wanda na baiwa amincewata, bayan shi kuma babu sauran wani. Sai dai kash! Shi mijin nawa yana da matan bayan fage ban da ni, a can ya kwaso cutar, kuma aka wayi gari har da ni ake kirgawa a sahun masu ita, ban ji ba, ban gani ba ya cutar da ni" Wata matar ta bayyana " nawa mijin baya neman mata, sai dai kuma an yi ba a yi ba, ya auro mai cutar ba tare da ya sani ba, sakamakon rashin bin diddigin lokacin aure, daga ni har shi duk mun kamu" Wata matashiyar yarinya ta fito "Iyayena ba su binciki halayyar mijina ba, yayin da ya ke neman aurena, da suka ga yana da abin duniya sai suka ba shi ni, ga shi yau kwadayin irin na kwadayin kuda, a yau ko gobe cutar na iya kai ni kabari" Wani matashi ya gabatar da kansa "Kyawun yarinyar da na aura shi ya ja ni ga auren na ta, ban damu da bincika halayyar rayuwarta ba, a yau kyawun ya zama na dan maciji, domin kuwa ta yafa min bargon tsiya" 57 Ilahirin jama'ar da ke wajen sun girgiza da suka ga wata mata mai yawan shekaru ta fito, kowa ya fara tunanin cewa na ta labarin zai kasance ne akan jikanta, amma akasin haka ce ta afku "ku dube ni nan a yawan shekaru na, to duk rabinsu na karar da su ne ba tare da miji ba, tun bayan da cutar ta kashe mijina na farko, an auna ni ba na dauke da ita amma hakan bai gamsar da mutane ba, tun da ya mutu ko kare bai zo yace yana so na ba, ga shi ma har na tsufa" Jawabin da matar ta yi ya yi matukar tayar min da hankali da alama matsalata iri daya ce da tata, bambancina da ita daya. Ita babu wanda yace yana sonta, ni kuwa har mutum biyu sun fito, sai dai fa a banza tun da kuwa ba su aure ni ba. Ban san sanda hawaye ya zubo min ba da na kara duban matar, yanzu matashiya da ni 'yar shekara ashirin da daya a ce haka zan kari rayuwata babu aure? Shakka babu in haka ta afku a kai na na yi mutuwar tsaye, me yiwuwa ma bakin ciki ya kashe ni, yanda na san dadin zama da miji ba zan jure rashin sa ba. Kowa ya Kara natsuwa sa'ar da wata karmasashshiyar yarinya ta fito, ko balka tambaya ba za ka san cutar ce ta tsotseta, ta fara isar da jawabinta. "Shekarata biyar ina holewa na kan bada hadin kai ga duk wanda zai ba ni kudi, a gani na wannan babbar sana'a ce, sai dai a yau na tsani kai na, sakamakon kamuwa da cutar da na yi. Abin da na samu a baya bai tsinana min komai ba, zancen da ake rabona da samun kwandala yau sama da wata hudu, dangina sun tsane ni, Kawaye da abokan holewa ta ma har ba sa so su hadu da ni, na amincewa kai na, ni kalubale ce ga sauran 'yan mata, su gane cewa a cikin yawo babu komai illa tulin bakin ciki buhu-buhu, a karshen yawon kuwa akwai da na sani kwando-kwando. Yawo ba sana'a ba ce ba, kunshi da kitso sun fi yawon banza" Wani matashi ya mike " ba ni ne da cutar ba, ba kuma da ni lamarin ya faru ba, yaya na ne ya daukota a wajen yawon dare, yau shekara daya da cutar ta kashe shi, ba mutuwar tasa ce tafi damummu ba, gorantawa iyayen mu da kuma kannansa da ake yi 58 da cutar da ta kashe shi. Irin wannan gorin kan sanya iyayen mu kuka, na yi imanin cewa da yaya zai dawo duniya, ya ga halin da ya bar iyayenmu a ciki da ya gwammace ina ma Allah bai halicce shi ba. Ya mutu ya bar musu bakin cikin da mutuwa ce kadai za ta iya yaye shi" Haka jama'a dabam-dabam su ka yi ta gabatar da kawunansu, kuma jawabin kowa ya kan bambanta da na wani. Lamarin da na tabbatar zai zame wa al'umma karin ilimi. Lallai na amince kanjamau shirgegiyar annoba ce da ta addabi al'ummar duniya, gwana wajen iya kai harin sari ka noke da sumame. Kuma kwararriya wajen iya kisan kare dangi ga al'uımar da ta tasa a gaba. *** "Hajiya minti daya mana" zancen wani mutum kenan da ke bi na a baya, bayan da taro ya tashi, a kokarina na iso bakin titi domin hawa mota na koma gida. Sai na waiwaya domin jin abin da mutumin zai fada, da ganin fuskar na tuna cewa na san ta a wani waje, sai dai ba na iya tuna ko ina ne ba. Ina wuni ?" ya fada bayan da ya karaso lafiya kalau" na amsa kin gane'ni kuwa?" " ban gane ka ba" Ya yi murmushi " ma'aikaci a cibiyar bincike ta northern road, kin tuno yanzu?" " Oh! Yes na tuno, yaya aiki?" "aiki Alhamdu lillahi, yaya mai gidan na ki?" Wani kunci ya cika zuciyata, amma duk da haka sai na yi karfin hali "yana nan lafiya kalau" " To madalla don Allah yaya za a yi na sami haduwa da shi kuwa'?" "wani abu ne?" Ya gyada kai " muhimmi ma kuwa" 59 a gaskiya ya yi wata 'yar tafiya" "Kash! Yau she ki ke sa ran zai dawo?" Na girgiza kai " ba na ce ba, na san dai zai dade sosai" Ya yi jim, tsahon lokaci daga bisani ya dago kan sa, ya zuwa dubana " to dan Allah idan babu damuwa na ganki mana a madadinsa, tunda ke da shi ai daya ne ko?" " Eh! Babu matsala" " To mu dan koma daga can mana, tun da nan ina ganin kamar kan hanya ne" Ban yi musu ba, mu ka koma inda ya nuna min din, ya sake dubana"am, hajiya kun sake zuwa wata cibiyar ne bayan ta mu da kuka zo?" Na girgiza kai " ba mu je ko ina ba" mijinki yana ci gaba da shan magani?" "Eh! Yana sha" "To ki ce ya bari haka, kar ya kara wahalar da kansa" "Me yasa ?" na tambaya cikin zakuwa saboda lafiyarsa kalau" saboda lafiyarsa kalau!" "saboda lafiyarsa Kalau!!" Amsar tasa kenan ta yi ta amsa kuwwa a kwakwalwata, kirjina ya buga da karfi kafafuna kuma suka gaza daukata, sai na durkusa cikin sauri. "Lafiya dai?" "ba lafiya ba" na amsa nan da nan Ya dora hannu aka " a'uzu billahi, me ke faruwa?" " Me nene ma bai faru ba" Sai ya kara rikicewa. Na dube shi cikin damuwa " ka се mijina lafiyarsa kalau?" " babu shakka haka lamarin ya ke Hajiya" "Kuma haka ka fada masa shi ma?" Yagirgiza kai " ba haka na fada masa ba" Zumbur na mike tsaye, ban san sa'ar da na ci kwalarsa ba " bisa wane dalili ka 6oye gaskiya ?" Vy "relax it Hajiya, mu warware matsalar a hankali" Na sakar masa kwala ina huci kamar wata macijiya, sannan na tsare shi da idanu cikin halin kin jini da tsana. A lokacin ji na ke tamkar na yi ihu barawo ya ci dukan tsiya. "ka fada min dalilinka na boye gaskiya ko kuma na kirawo maka 'yansanda" Ya daga min hannu " Afuwa Hajiya, ki tsaya na bayyana miki komai a nutse" Da alama mutumin ya gama tsorata sosai, na tsattsare shi da idanu " to fadi ina jinka" Ya ci gaba " ni ma dole ce ta sanya ni yin hakan Hajiya, amma na yi iya yina domin kaucewa hakan lamarin ya gagara. Matar da kuka tarar awajena ita ta tilastani yin haka, kuma ya zama ba ni da damar kaucewa bukatarwa" "wace ce ita matar ?" na nemi ji da gaggawa "Hajiya magajiya tace ita surukar mijinki ce, ta taba aura masa 'ya Sakinah" Kirjina ya buga da karfi, bayan da na ji tsinanniyar matar na neman dagula min lissafi a karo na biyu, na kara dubansa cikin bacin rai" To kai me ne ne naka na amsa bukatarta?" "dole ce Hajiya, tana nema ne ta kulla min sharri, shi yasa dole na amince" " Wane irin sharri ża ta kulla maka da har ka kwammace ka ci amanar aiki?" Ya yi shiru bai ce komai ba "Wallahi idan ba ka fada ba sai na kira maka 'yansanda, kuma ka sani in har asirinka ya tonu kai da aiki famfamfam" Ya marairaice, " ba na so kina shigo da 'yan sanda cikin batun" " in har ba ka son haka sai ka fada min idan na ga ya cancanci yi maka afuwa shi kenan, sai na barka ka yi tafiyarka salun'alun" Ya sunkuyar da kai " To zan fada miki, amma sai kin yi alkawarin rufa min asiri" zan rufa maka" "Rantse" "bazan rantse ba, bu ka isa ka sani rantsuwa ba, idan ba za ka fada din ba, ka yi tafiyarka in ya so 'yansanda sun san a inda za su zakuloka, tunda ba 6oyewa za ka yi ba" " manta da wannan Hajiya zan fada miki yanzu yanzu" "To ina jinka" Ya fara "a daren wata Talata ne matar ta same ni a gida, tare da wata 'yar bakar yariya gajera. Yarinyar cikin shege ta yi, kuma su ke so a zubar da shi. Ba shi ne karo na farko da matar ta zo min da harkar ba, ta jagoranci wasu a baya ya kai sau biyar. Na caje su abinda za a biya ni, tun da aiki ne na bayan fage, ban yi musu cajin wasa ba. Suka ajjiye min kudi a kas ni kuma na dukufa aiki. Tsautsayi garin neman kiba aka samo rama, yarinyar mutuwa ta yi. Ita kuma matar ta tashi kayar baya, akan lallai sai ta fallasa. Na san abin da hakan zai jawo, hukuma ba za ta yi la'akari d cewa mugun iri aka rage ba, matsalarsu kawai na kashe rai, na san kuma zan fuskanci hukunci mai tsanani. Dole na ne nemi shawo kan matar ta hanyar rufe mata baki da kudi, hakan kuwa aka yi, bayan da ta caje ni kudin da a ga baki daya mu'amalar ban karu da ita su ba, yashe ni ta yi tas! Kuma duk da haka ban gama biya ba. A ranar da ku ka zo ma bayan ragowar kudin ta biyo, ni kuma ba ni da su tana cikin barazanar tona asirina ne Allah ya kawo ku, shi ne ta tashi ta fita, bayan tafiyarku kuma ta dawo neman jin abin da ya kawo ku ta yi. Jin zancen ya farnanta mata rai, lafazinta na farko Allah yasa kuna da ita. Na nuna mata shakku akan haka, musamman da mijinki yace matar tana shan magani, kuma maganin bai daina tasiri a jikinta ba, domin a wannan halin babu yanda za a yi a kamu. Sai ta canza akalar zancen. "Abin da za a yi dora masa cutar za ka yi, koda kuwa ba shi da ita, sai na raba tsakaninsu kamar yanda ya rabu da 'yata, in sa ya kaskanta kamar yanda ya nemi kaskanta ni, wannan ne kadai garkuwarka da police, kuma fansa ga ragowar kudina" To kin ji Hajiya, a ranar da za a karbi sakamakon ma zuwa ta yi ta kasa ta tsare, wai gudun kar na yi mata coge, haka na ba shi takardun, amma a raina ina da aniyar binciko inda ya ke na wayar da shi, kuma na yi iya yina na rasa, shi yasa yau da na hadu da ke na ga ya kamata na yi amfani da damar" Na kara kallonsa cikin fushi, a kuma lokacin da tsanarsa ta kara keta zuciyata na fara magana cikin kakkausan lafazi " Saboda wannan dan dalilin kayan ke mana rayuwar jin dadi ni da mijina? Ka san ya ya tsallake ya bar ni a lokacin da na ke matukar bukatarsa? To albishirinka, ka gudu baka tsira ba, ka kaddara cewa kwamishinan 'yan sanda ka gama baiwa labari ba farar hula ba, sai ka dandani dacin zama a gidan maza, kamar yanda na dandani dacin zama babu miji, ka kuma nisanta da 'yan uwanka kamar yanda karyarka ta nisanta mijina da danginsa" Na nuna shi da yatsa " ka zama cikin shirin amsa tambayoyin 'yansanda" Sai na juya a fusace. Ya sha gabana da sauri " dakata Hajiya tsaya ki ji yanda za a yi" " Ba na bukatar jin komai daga gare ka tunda dai ba iya dawo min da mijina zaka yi ba" " ki yi min rai Hajiya, ki fada min inda ya tafi na yi alkawarin dawo da shi" Na yi masa wani kakkaifan kallo "mutumin da ya bar garin ba shiri ne, za a san inda ya tafi? Kai dai ba ka firgita shi ba, to ai ya yi kyau, za ka girbi abin da ka shuka" Sai na ci gaba da tafiya, shi kuma ya biyo ni" Hajiya wallahi zan iya gano shi duk inda ya ke a kankanin lokaci, tsaya ki ji hanyar da za a bi" Jin haka ya sanya ni tsayawa na waiwayo gare shi" fadi hanyar taka na ji, idan kuma ba ta gamsar da ni ba na yi tafiyata" Ya fara cikin sarkewar murya "mijinki mutum ne mai wadatar wayewa, a duk inda ya ke zai nemi magani, maganin kuwa ana samunsa ne kadai a asibitoci da cibiyoyin bincike, kuma akwai list din sunayen masu karbar maganin a ko wace cibiya, kin g Kin gu kuwa zan iya gano mijinki,n tun da a dan iya lokaci zan iya tuntubar ko wace cibiyn ta duniyar gizo (Internet)" "Idan ya canza sunа Ги?" Ya girgiza kai "Ina shakkar haka nan.n" ""To tsaya ka ji, awa ashirın da hufu na ba ka, ka yi duk yadda za ka yi ka maido min mmpima a cikinsu, idan ba haka ba kuwa.......ba sai na karashe ba." "Awa ashirin da hudu ya yı kadan lajiya, saba'in da biyu za ki bani, kwanaki uku kenan." Na girgiza kai "Sam! Ba zan iya ba ka kwana uku ba." "To biyu don Allah, ki taimaka ki duba yawan aikin, ki kuma tuna bayan an gano cibiyar sai an je garin, saukin sanunsa zai danganta da adireshi ko lambar waya idan ya bayar." N anuna shi da yatsa "To kar ka tsallake, in har ka kara daidai da awa daya komai zai iya faruwa." Ya gyada kai "Na amince." Sai na kara gaba na bar shi nan, da alama na hada masa zafi mara misali, ni kuwa Allah-Allah nakc na isa gida na kai labari. *** Duk wasu awoyi da suka shude a gareni, bayan haduwa da mutumin sun shude min ne cikin rudani, zuciyata ta gaza tsayar min da matsayi daya, ta kan kiyasta abin a matsayin gaske, kuma ta kan zaceshi almara, bisa wannan dalili na kowayc wa yin azarbabin shaidawa wani hatta da mahailiyata. Nayi tagumi a daki cikin kara tattauna lamarin, hakika yaudara ce zalla ace wai Abdul lafiyarsa kalau. Kuma in ma har na yarda haka to na zolayi kaina. Wani tunani ya yo shigar sauri, ke Karimah hakan zata yiwu, to na ji za ta yiwu amma ai da mamaki har mutumin ya tareni akan titi ya shaida min, bai kuma tsaya anan ba har ya hada da shaida min wata aika'aika daya aikata. Wannan ma zai yiwu karimah kifa tuna Addu'a ki ke yi a kowanne lokaci ko kina shakkar karbuwar addu'oinki nc? A'n ko kusa bana shakka na kuma amince addu'a tana maganin komai, sai dai inhar biyun sun yiwu akwai shakku acikin faruwar na Karshe, ko kusa zuciyata ha ta zolaye ni cowa mutumin zai iya gano 64 Abdul ba, ina yiwa Abdul kiyasi ne irin na mutumin da ya riga ya mutu, matacce baya dawowa, Abdul ma kuma ba zai dawo ba. Karfafa min hakan da zuciyata ta yi sai ya sanya na dauki lamarin na yi masa kallo irin na abinda ya faru a mafarki, na kuma fada sabgogina gadan-gadan, sai dai duk da haka akwai tunanin a zuciyata. Rana ta fito ta kuma fadi har sau hudи, adadinkwanakin da na dibawa mutumin suka wuce, amma shiru babu wani abu da ya nuna zai aſku. Tuni wata zuciyar ta fara shawarta ta da na shaidawa 'yan sanda. Wata kuma sai tacc "Kul! Me za ki ce musu idan kin jc? Kina tsammanin abinda mutumin ya labarta miki zai iya zama gaskiya? In har ba gaskiyar banc kin jcfa kanki cikin wani rudani kenan, domin idan ya karyata wacce hujja kika rika da za ki kafa? Amsar baki

Chapter 5 of 6