Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Nwasne Kwasnen RUFAIDA M. UMAR a mike tsaye da sauri tamkar wani spring ne ya harba ni a Nkujerar da na ke a zaune, kirjina ya buga da karfi kamar yana shirin buſewa, alamun tsoro da fargaba suka bayyana kuru-kuru a fuskata Na dubi Asma'u da niyyar neman tabbaci akan abinda ta fada, to amma sai harshena ya gaza furta komai, sakamakon yawun bakina da ya kafe gaba daya. Sai da nayi fama na tsahon lokąci kafin na kai ga samun damar yin tambayar. " Wai gaskiya ki ke fada min ko kuma almara?" Ta girgiza kai cikin takaici " Karimah kin sani ko da ina yi miki wasa ba zan yi miki irin wannan ba" Tana gama tabbbatar min na dora hannu aka na fashe da kuka, ina mai yin kururuwa a kan lamarin mai hargitsa zuciya. Ganin haka ya sanya Asma'u mikewa tsaye, hannuna ta kama gami da kokarin zaunar da ni " zauna ki ji Karimah wannan ba shi ne mataki abin dauka ba" Na yi karfin halin zama tare da ita, duk kuwa da cewa har yanzu ban daina kukan ba. Kokarin tana fara magana ya zo daidai da lokacin da kofar dakin ta yi duhu, dalilin da ya sanya mu waiwayawa gaba daya. Abdul ne a tsaye yana kallonmu, fuskarsa na mai nuni da bukatarsa akan abin da ke faruwa. "Yauwa! Shi kenan ma shigo ka ji" Asma'u kenan ta ke gayyatarsa. Ya sulalo zuwa cikin dakin a hankali, sannan ya nemi waje a gefena ya zauna. " Abdul wani babban al'amari ne ya ke tasowa, matar ka Jimmai me ka sani dangane da ita?" Fuskarsa ta yi nuni ga rashin ga ne inda tambayar ta nufa, bai tsaya iya haka ba har sai da ya kai ga furtawa " Asma'u ban ga ne tambayarki ba" "Ma'ana an yi maka wani bayani dangane da wani abu da ya shafi lafiyarta?" Ya girgiza kai " babu wani bayani da aka yi min irin wannan" ト 3 "Ai kuwa an ha'ince ka, ha'inci ba dan karami ba, watskila kuma sakayya sai dai ta Allah. Jimmai tana da kwayoyin H.I.V. me haddasa kanjamau" Da sauri ya mike irin mikewar da na yi dazu, ya zazzzare idanu gami da sunkuyowa " What? H.I.V ?" Ta gyada kai " Kwarai kuwa, ni tabbatau ce ba zatau ba" Ko kalma daya bai kara furtawa ba, ficewa ya yi da duk iya gaggawar da zai iya. Asma'u ta yi kira, tayi kira ina! Lamarin ya zama tamkar ana kiran kurma. Ta juyo gare ni a lokacin da na ke kalace ragowar kukana. " Karimah sai dai ace Allah ya kiyaye, domin kuwa ku duka kuna iya kamuwa. Na tabbata Abdul ya yi zirga-zirga a tsakaninku sau da dama, wanda hakan daya ne daga hanyoyin da ke yada ta" Na yi shiru gami da yin tagumi, hawaye kuma ya ci gaba da sululu a kumatuna. Asma'u ta mike tsaye " Karimah ni ya kamata na tafi, na san yanzu mai gidana ya kusa dawowa, amma ki shaidawa Abdul ku gaggauta zuwa a aunaku. Ina dai zaton yanzu can wajen Jimman ya nufa, zai kuma samu abinda na fada din haka ya ke, ke ma kin ga sai ki kara tabbatarwa" Ban iya cewa komai ba, ta ci gaba " Kin ga fa ta'aziyya na zo yi miki, amma wannan tashin hankalin ya shagaltar da ni, to Allah ya jikan Hamidah, ya kuma maye mu ku da wadansu" tafi Da kyar na iya cewa " Amin" Ita kuma sai ta nufi waje, takalminta ta sa gami da fadin "na Na bita da "ki gaida gida" 本 Abdul ya shigo har falo ba tare da sallama ba, da kallonsa na tabbatar da cewa mai afkuwa ta afku. Ya cusa hannayensa biyu cikin aljihun wando, yayin da fararen idanunsa suka kada su ka yi ja. Da kallona ya kawar da kansa, ya fada kan kujera kamar wanda ya bugu. Na yi karfin halin tasowa na dawo kusa da shi, na fara tambayarsa abin da na san amsarsa. Abdul ya ya aka yi?" Ya dan waiwaye ni daga bisani ya kawar da kansa " rabu da ni Karimah, ni nan na tsani kai na, a halin yanzu mutuwa ita ce mafi cancanta da ni, ban ga amfanin rayuwar mutum iri na ba, shashashan da bai damu da kiyaye kansa ba, ballantana ya kiyaye wani, ba zan yi musu ba in har likita yace kwakwalwata iri daya ce da ta jaki" Na fashe da kuka " Abdul ka dai na fadin haka, ka amince cewa Allah ne me kaddara komai" " Dakata Karimah! Tinkaho da cewa Allah ne mai kaddara komai ba zai hana mutum yin taka tsantsan ba, dubi fa yanda na kwaso Sakinah a baya, don dakikanci da rashin tunani na kuma kwaso Jimmai, ba kuma komai ne matsala ba illa rashin nazari. Da ina nazari da haka duk ba ta faru ba. Ko da yake Jimmai ina ganin kamar gida ne, ashe a gidan ma aka yi rufa-rufa" Na sa gefen zani na na share-hawaye " babu komai Abdul haka Allah ya hukunta, koma me ya faru haka ya so, bari na kawo maka ruwa ka sha" Ya kura min ido tsahon lokaci " wai ke Karimah ba za ki yi min tawaye ba? ba ki lura da irin hadarin da na dora rayuwarki akai ba? Ai ya kamata ace na ba ki haushi" Na girgiza kai " ni babu wani haushi da ka ba ni, ban kuma ga abın da za ka yi ka ba nì haushi ba. Idan ma na dauki cutar a Yawon banza na dauko tan e ? ai ina ce a zaman aure ne?" Ya jinjina kai " Eh! lallai Karimah ba zan sa ran a sami

Chapter 1 of 6