Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
ji a jiki na rayuwata ta kare rayuwata tazo karshe." Cikin kuka Amira ta ƙara matse hannun Rabi'a ta ce " A duk lokacin da Allah ya ƘADDARA wanzuwar halitar ɗan adam a doron kasa to kuwa tabbas, ko yaƙi ko ya so akwai wasu tarin ƘADDARORIN da suke yin jerin gwano a gangar jiki da kuma ruhin ko wani bawa, inuwa wata abace da Ubangiji ƘADDARA wanzuwarta manne a jikin ko wani abu walau mai rai ko akasin haka..... A koda yaushe ta na bibiye damu ne matukar bawa zai zuba maganan sa zai rula da hakan..... Kalmar ƘADDARA kalma ce mai dauke da rassa biyu walau mai kyau, ko kishiyar ta, ƘADDARA abokiyar tagwaitar inuwa ce, domin bawa baya taɓa iya shallake ma tari ƘADDARURINSA, duk iya gudunka, duk iya saurinka,baka isa guje ma tarin ƘADDARA da Ubangijin sammai ya ƘADDARA maka ba, sanin hakan yasa na fahimci maganar malam bahaushe ta, Tun ran gini tun ran zane ta zauna daram kwatankwacin yanda ake dura ƙwarya a gurbinta." Ƙuri Rabi'a ta sakar ma Amira ido kukan da take ya tsaya sai hawaye kawai dake ambaliyar zuba Rabi'a ta yi wani murmushin da ya fi kuka ciwo ta ce " mai yasa? duk cikin tarin KADDARORINA babu mai kyau." Amira ta daura hannun ta a bakin Rabi'a ta na girgiza kai ta ce " Kada kice komai, saboda indan ki kayi wata magana tamkar kin butul ce ma Allah ne." Rabi'a ta ce " shi ke nan, ki kira min Fatima akwai maganar da nike so muyi." *Bashir* Hankalinsa ya kasa kwanciya yana jin wani abu akan Rabi'a anya ma kuwa ya kyutata ma ta wani abu mai kama da SO a tare da shi kuma ba SON kowa ba sai na Rabi'a SON da ya yi masa dirar mikiya *Fatima* Da wani kalar ciwon kai mai zafin gaske ta ta shi saboda rashin bacci da kuma damuwa Kuma tunda ta tashi jikin ta ya yi ma ta wani kalar sanyi Ji take kamar zata rasa wani na jikin ta saboda raban da taji wannan sanyin tun rasuwar mahaifinta Kuma haka dai tai ta daurewa tayi su na yin ƴan aikace aikace ida da Mima babbar ɗiyar Alhaji Abdullahi Bayan sun gama komai ta shiga tolet wanka ta yi ta zo ta kwanta ko zata samu sauƙi, babu yanda Alhaji Abdullahi bai yi ta ita akan suje asibiti ba amma taki Har bacci ya fara daukar ta wayar ta ta fara ƙara Alhaji Abdullahi ne ya dauko ma ta wayar dake jikin chaji ya miƙa ma ta Ganin kiran Amira ne ya sa gaban ta ya yi wani mummunan faɗi a fili ta ce " Shi ke nan komai ya riga da ya faru." Har wayar ta yank ta kasa ɗagawa saboda ta na tunanin abinda za'a faɗa ma ta a cikin marubuta wayar Wani kiran ne ya sake shigowa jiki a sanyaye ta ɗaga kiran Ajiyar zuciya ta sauke jin Amira lafiyar ta lau amma a maganar ta ta fahimci kamar ta na cikin damuwa Ta bangaren Amira ma shuru ta yi sai da Fatiam ta magantu dan kanta ta ce " dan Allah kada kice min wani abu ne ya faru da Rabi'a." Amira ta girgiza kai ta ce " Yaya Rabi'a bata da lafiya, ta na asibiti yanzu haka ta ce ta na son ganin ki." Ai tana jin Amira ta ce haka ta tashi ta faɗa ma Alhaji Abdullahi suka fita *Gidan su Rabi'a* Mama cikin tashin hankali ta fito itama ta je ta fara faɗa ma umma itama hankalin ta a mugun tashe ta fito Mama na faɗa ma umma ta nufa ɗakin Baba shima ta faɗa masa Baba ya ce " hatsari sukayi ne?" Mama ta ce " nima ban sa ni ba amira aka kira." Kafin Baba ya ce wani abu umma ta ce " ba wannan ya kama ta, ace an tsaya ba mu tafi asibitin kawa." *Asibiti* Fatima da mugun guda ta nufa ɗakin da Rabi'a ta ke tun da ta hango ta zuba ma ta idanu kamar yanda Rabi'ar ma ke kallon ta Fatima ta ƙara sa wajan ta ta kama hannun ta ta ce " mai ya same ki faɗa min." Haka Fatima ta yi maganar kamar wata uwarta ta na bata umarni Ita kam Rabi'a kamar jiran umarni Fatima ta ke ta fash fa kuka ta ce " bana faɗa maku Bashir ba mutumin kirki bane, bana faɗa maku bana son Bashir ba." Amira ta kalle Fatima itama Fatima ta kalle ta Fatima ta ce "Eh mai ya faru." Rabi'a kanta tsaye ta ce "Bashir ya lalata min rayuwa Bashir ya yi min fyɗe." Tsakanin Amira da Fatima ba'a san wanda ya riga wani mikewa tsaye ba suna kallon Rabi'a Kafin kuma su duka suka fashe da kuka Dr Hauwa ma da shigowar ta ke nan itama sai kawai ta fashe da nata kukan tana juya wa Dr Hauwa a hanya ta haɗu dasu Baba zasu shiga ɗakin ta dakar da su ta ce "su bari ba yanzu ba idan lokacin shiga ya yi zata kira su." Waje suka koma suka zauna kowa da tunanin da yake cikin ransa Dr Hauwa dalilin da yasa ta hana su mama shiga shine ahalin da Rabi'a ta ke ciki akwai buƙatar ta faɗa ma wani damuwarta idanba haka ba kam komai na iya faruwa Rabi'a su duka kuka suke Fatima ta kasa zama ta zuna ta tashi kwata kwata bata haiyacinta sai kuma taje ta kama Rabi'a da wani mugun ƙarfe ta tallabo fuskarta tana kallo sai kuma ta yi shuru Amira ce ta ce " Inalilllahi waina ilaihi ra'ji unm, Inalilllahi waina ilaihi ra'ji unm, Inalilllahi waina ilaihi ra'ji unm." " Fatima ki ambaci Allah, ki ambaci Allah Fatima." Da karfe kamar an fisgi maganar ta ce " lahauwa wala ƙuwata ilabibah,lailahailala Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam' in Sha Allah wannan mutumin." sai kuma ta fashe da kuka Rabi'a ta yi wani kalar murmushi ta ce "kullum ku ke nasiha akan yardda da ƘADDARA amma mai yasa yanzu kuka manta wannan? Mai yasa kuke son zuciyata ta kare." Shuru su duka sukayi su ka daina kukan sai hawaye Rabi'a ta ci gaba da cewa " ƘADDARA wata abace mai tsanani kuma mai sauƙi, sannan wata abace da ba'a iya ganin launinta da ido, hakan yasa ba'a iya sauyata da mummuna zuwa kyakkyawa, a cikin ko wani rayuwar ɗan adam akwai salon tarin ƘADDAROTURI masu tarin yawa a kowace duniya, a kuma koda yaushe ƘADDARA tana tafiya ne daidai da rayuwa, sannan kuma babu wani bawa wanda ka iya kuje ma tarin KADDARORINSA, haka kuma ana haifar ko wani bawa ne da salon tashi ƘADDARAR, ku dauka cewa haka ƘADDARAR Rabi'atu Musa take." Tunda ta fara maganar suke kallon ta Dr Hauwa ce ta shigo ganin kamar abin yayi sauƙi yasa ta ce "ga iyayen ki nan sun shigo kinsan dole zasu san abin da ya faru." Rabi'a ta yi murmushi tace " bana fargabar komai akan ƙaddarata." Itama Dr Hauwa murmushi ta mayar ma ta Bayan fitar Dr Hauwa sai ga su mama sun shigo harda baba Mama Kam wani kalar faɗuwa gabanta ya yi ganin yanda Rabi'a ta koma Rabi'a tunda suka shigo ta yi ƙasa da kanta ta kasa cewa komai kuma ta kasa daga kai ta kalla ko Sunata magana amma ta yi shuru har Baba ya fara harziƙa Ɗagowa tayi fuskar ta duk hawaye Umma ta ce "Subhanallah mai ya faru." Kuka ka wai take Amira da Fatima ma kuka suka saka Dr Hauwa ce ta shigo suka maida akalar tambayar su gare ta Dr Hauwa tace " zai fi kyau a ce a gida za'ayi wannan maganar." Baba ya ce " ban gane ba? wace magana ce da baza' ayi ta a nan ba?" Dr Hauwa ta ce " dan Allah.'" Baba ya ce "shi ke nan." Su duka harda Rabi'a suka dunguma zuwa gida Bayan sun zauna a falon mama sai da Dr Hauwa ta fara yi masu nasiha sannan ta faɗa masu abinda ya faru Sakan ɗaya biyu uku Baba wa wani mugun bala'i ya tashi tsaye ya na nuna Rabi'a ya ce "nikan nayi baƙar haihuwa anya ke ɗiyata ce." Mama ta ce "haba mana ya zaka ce haka dan Allah kada ka samu damuwa bayan war da muke ciki." Da mugun karfin masifa ya daka ma mama wata shigiya tsawa Umma kam sanƙarewa ta yi tama kasa magana Maganar babace tayi mugun girgiza tunanin su cikin tashin hankali suka zuba mashi ido "Na tsane ki Rabi'a nayi ɓakar haihuwa a kanki, Allah ya isa tsakanin na da ke ki fita ki barmin gida tsina.... Maganar ta yanke saka makon faɗuwar da Rabi'a ta yi Da gudu suka yi kan ta amma ina Sai dai ina Rabi'a rai yayi halinsa rabbi ya amsa abarsa wanda yafi kowa santa da ƙaunar ta Rabi'a ta koma gare shi RABI'A TA RASU😭😭😭TA RASU TA KOMA GA ALLAH WANDA MUMA ZAMU KOMA GARE SHI INALILLLAHI WAINNA ILAIHI RA'JI UN , INALILLLAHI WAINNA ILAIHI RA'JI UN KULU NAFSIN ZA'IKATUL MUT, A YAU RABI'A TA KOMA GA MAHALINCINMU 08:48Am Fir,dec 2025 JARABTATA writing by Fatima Bintu hussain https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ems_copy_t 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*💪✍️ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️ *"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"*💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) *✋𝙒𝘼𝙎𝙄𝙔𝙔𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙉𝙆𝙒𝘼𝙉𝘼🤚* *Ba ko wane labari ne ake gaggawar bayar dashi ba. Ba kowace nasara ce ake wallafa ta nan take ba. Wasu abubuwan sun fi dacewa su zauna a cikin zuciyar ka domin dama nan ne mahallin da yafi dacewa dasu.* _*Nasara, asara, rauni, karfi... Duk wadannan sirrin ka ne, saboda haka kakai makura wajan kare su.*_ Chaptar 12 end Fatima ganin dai kamar babu Rabi'a da ƙarfin tsiya cikin rawar murya ta ce " Ra...bi'..a.. ki..ta.. ta.. s..hh..i.. ni...ni...zan... ts...a..ya..m..m..a..kk..i." Inalilllahi Fatima fa bata cikin haiyacinta Alhaji Abdullahi ne ya ce " asibiti ya kamata aje." Dr Hauwa dama ta ruɗe kwata kwata ta ma manta da cewa ita likita ce Baba wani kalar tsuma jikin shi ya dauka komai na jikin shi ya yi masa nauyi Cikin tsaya mama ta ce "Wallahi Azim wani abu yasamu ɗiyata ta dalilin ka ko hummm." Tayi maganar ta na girgiza kai a motar Alhaji Abdullahi aka saka Rabi'a tunda suka fito mutanan unguwa fa aka fara yaɗawa an ga an dauka Rabi'a kamar babu rai wasu dan gulama haka suka bisu asibitin *Asibiti* A mugun ga je likito ci suka yi ɗakin da Rabi'a take Sai dai ina RABI'A fa babu ita rabbi samawati ya daɗe da amsar abarsa Dr Hauwa ganin dai da gaske babu Rabi'a ta saki wani kalar kuka Wani likita ne ya nemi magana da Alhaji Abdullahi office nashi suka ta fi bayan sun shiga likitan ya ce " wani abu ya faru da ita wanda ya yi sanadiyar bugawar zuciyar ta sai dai ayi haƙuri ka dauka matan nan ku tafi gida za'a kawo gawar a motar asibiti." . "Inalilllahi waina ilaihi ra'ji unm, Inalilllahi waina ilaihi ra'ji unm, Inalilllahi waina ilaihi ra'ji unm, shi ke nan ta rasu."da Da sauri ya fita ya lallaɓa su mama suka shiga mota sauran mutanan unguwama haka suka koma kowa jiki a sanyaye Sai da ya tabbatar da sun shiga gida ya zauna ya yi masu nasiha kafin ya ce "kuyi haƙuri Rabi'a ta tafi, tayi tafiya mai nisa, tafiyar da babu dawowa, tafiyar da muma zamu je." Yana gama fadar haka ya share hawayen da ya zo ma shi Amira tun faɗa farko da akayi a gida nan ta faɗi a sume da yake kowa hankalinsa baya jikin shi sai kowa bai rula da ita ba Fatima kam dama ba'aje asibiti da ita ba tunda Alhaji Abdullahi ya fara magana ta yi suman zaune a wajan Baba Ismail ne da Baba Abubakar suka shiga a mugun tashin hankali domin suna kasuwa wani ɗan unguwar ya kirasu Baba Ismail ya na shigowa kan baba ya yi ka kai ma shi wasu gigitataun maruka a duka fuskokin sa kafin ya zauna dabass a ƙasa Unguwa ta rikece da maganar mutuwar Rabi'a hankalin mutanen unguwar a tashe ya ke Jiniyar motar gawace ta sanar masu da isowar gawar Rabi'a inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm tashin hankali da ba'a saka masa rana Mama da gudu ta fita waje daidai lokacin an fitar da gawar Rabi'a ta gudu ta isa ta kama Rabi'a tana buɗe firin ƙalen da aka rufe mata fuska Dr Hauwa ce da sauri ta jan ye ta kafin ka ce wani abu tuni rasuwar Rabi'a ta zagaye garin Katsina baki ɗaya Yaya Ahmad Tun a jiya yake jin faɗuwar gaba dan saida ya yi zazzaɓi kuma hankalinsa ya kasa kwanciya hakan yasa yana Sallahr asuba ya kamo hanyar Katsina daga Kaduna kuma ko gidan sa bai jeba kai tsaye ya yi gidan su Kuma ya yi mummunar ganin mutuwar Rabi'a abinda tunanin shi bai taɓa tunanoshi ba zuciya bata taɓa raya masa ba hankali bai taɓa hasaso masa ba Duk dauriyar sa duk haƙurinsa ya kasa a wannan lokacin raunin sa ya baiyana muraran kuka ya saki kamar wata mace Fatima kukan da ta ji ya na tashi ne ya sa ta dawo haiyacin ta kuma tana buɗe idon ta ta yi kyakywan gani da gawar Rabi'a Ihu ya saki ta yi kan Rabi'a t buɗe gwar ta kana fuskar ta ta ba kuka cikin kuka ta ke cewa " haba Rabi'a kada ki karyamin alƙawari, kin manta tun muna yara muke yin komai tare dan Allah ki da shi daga wannan baccin bana san kalar wannan wasan bana sooooo." Yaya Ahmad ne ya lura da halin da amira ta ke ciki ruwa ya samu ya shafa ma ta a fuska ta sauke a jiyar zuciya sai kuma ta saki kuka mai karfi ta ce "ai dai bata mutu ba ko?" Kai kawai yaya Ahmad ya girgiza ya na goge hawayen da suka zuba masa Rarafawa ta yi ta shiga ɗaki amma abinda ta gani ne ya yi sanadiyar ƙara sumewarta a wajan Mutane sun cika ko ina a unguwar unguwar ta cika kamar ta fashe yara da manya Mutane da yawa suna ta dana sanin a binda sukai ma Rabi'a dan basu san abinda ya faru ba Ammi kam mahaifiyar Fatima tundata shigo gidan babu abinda ta ke faɗa sai alkairi Rabi'a bama ita kaɗai ba mutane da ya wa suna faɗa alkairinta har ƴan yarama san sau da yawa zata ga suna faɗa ta raba su faɗan ta saya masu wani abu Fatima fa hankalin ta na neman barin jikin ta gwara ma Amira ita a sume ta ke Dr Hauwa gaini halin da Fatima ta shiga ya sa ta samu allurar bacci akai ma ta domin a samu a shirya Rabi'a a kaita gidan ta na gaskiya Haka aka haɗa Rabi'a aka fita za'a sallaci gawarta Babu wanda ya ga tashin Fatima balle ma fitar ta kamar walƙiya haka aka ganta gaban gawar ana shirin fara sallah Nan hankalin mutane ya ƙara tashi tausayin Fatima ya cika masu zuciya dole Fatima zata yi kuka idan da abinda ya fi kukan ma yi zata yi Alhaji Abdullahi ne ya kamata zai shiga da ita ciki a daidai lokacin ne A'isha da Aunty Hadiza suka iso ba'a faɗa masu abinda ke faruwa ba a dai ce kawai su zo gida babu lafiya Nan wani sabo tashin hankalin ya barke bayan sunyi katarida gawar Rabi'a Yaya Ahmad ne ya zo ya Kamasu ya kai su cikin gidan ya ce kada a barsu su ƙara fita subari ayi ma baiwar Allah sallah cikin salama a miƙata gidan ta na gaskiya Zuwa lokacin duk wasu yaran gidan dake aure sun zo Baba ya rasa mai zaiyi a rayuwar sa kamar baya a hankalin sa Cikin tsantsar nadama da danasani ya je zai kama gawar Rabi'a amma Abba Isma'il ya hana ya na ji ya na gani aka tafi da gawar Rabi'a *Bashir* Har ya kusa isa Kano ya juyu ya dawo hanyar Katsina ya shirya auren Rabi'a Bayan ya iso Katsina kai tsaye gidan su Rabi'a ya nufa amma kuma tun daga shigar sa unguwar ya ga unguwar a cike da mutane sosai hankalin sa ya tashi Babban tashin hankali shine yanda ya ga ansa rumfa a ƙofar gidan su Rabi'a Shi tunanin sa wani ne ya mutu a unguwar amma me ganin yanda mutane ke fitowa a kofar gidan su Rabi'a suna kuka ya sa hankalinsa ya ƙara tashi Wata magana ce ta dauka hankalin sa warda ta girgiza tunanin sa ta kusa tsarwatsa mai zuciya Allah sarki Rabi'a mutumniyar kirki Allah ya jiƙan ki halin ki na kirki ya bike Sakan ɗaya biyu uku A mugun tashin hankali ya yi kam mutane da suke wannan mummunar maganar ya ke tambayar su dan Allah da gaske ne Nan suka tabbatar masa da rasuwar Rabi'a da mugun gudu ya koma motarsa a 360 ya fiske motar toƙi yake na rashin hankali Wata babbar motace t tahu mai motar ya yi ƙoƙarin kauce ma Bashir amma ina Bashir nufar sa yake haka ya bige wannan babbar motar *Gidan su Rabi'a* An kai Rabi'a gidan ta na gaskiya babban abinda ya basu mamaki bai yanda kusan kabari uku ana tunawa amma kuma duk ruwa ana ukun ne aka samu mai danshin ruwa da wani kalar sanyi Kowa sai da jikin sa ya yi sanyi haka aka sakata kamar kai ma ta magana ta amsa Bayan an fito daga maƙabarta limamin ya kalla mutane ya ce "haƙiƙa wannan baiwar Allah ce, na daɗe banga kamar wannan abin ba yanda ake zafen nan ake rana amma an samu kabarinta da sanyi Tabbas wannan baiwar Allah ce, bai kamata a yi ma ta kuka ba addu'a ya kamata a ƙara ma ta ko ƙara mai ma ma ta rahamar Allah ." Sosai yaya Ahmad ya ji daɗi har ya saki wani murmushi Bayan sun dawo gida aka ci gaba da amsar gaisuwa abinda ke damun baba bai wuce yan da kowa ya share shi ba dayan yaran sa, matansa, ƴan uwansa, Duniya ta yi masa zafi sosai kalar zafin nan mara musaltuwa Fatima dole tasa akai mata allura mai karfi amira kam bayan ta farfaɗo ta kasa cewa komai sai zaburar da takeyi tana kiran Rabi'a Baba bayan kowa na kusa da shi sun taru a falonsa ya basu hakuri kuma ya nuna da na sanin sa akan abinda ya yi kuma ya janye maganar da ya yi akan Rabi'a ya nema ma ta gafarar Allah amma sam mama taƙi ta saurare shi ta ce ita sai ya sake ta ta gama zama da shi An kasa gane kan mama sai da aka dauko mahaifinta zuwa lokacin Fatima ta tashi haka ya haɗa su ya yi masu nasiha mai ratsa zuciya Bayan ya gama dasu mama ya haɗa Amira da Fatima ya yi masu nasu daban sosai jikin su ya yi sanyi sukayi masa alkawarin basu ƙara yi ma Rabi'a kuka ba Sosai baban mama ya ji daɗi maganar su Haka dai akai zaman kwana bakwai na makokin Rabi'a aka watsa sosai mutuwar Rabi'a ta zamar ma mutane da waya wa'azi a rayuwar su Yaya Ahmad yayi ma Rabi'a babban gata ta hanyar bada maƙudan kudi a gina ma ta masalaci babba da kuma bohul bohul na ruwa *Bashir* Bashir tun ranar da ya yi hatsari bai farfaɗo ba sai jiya Bayan ya farka ne ya ba numbern ƴan uwansa aka kira aka faɗa masu daga Kano aka zo aka dauke shi duk wanda ya gansa sai ya shiga tashin hankali domin an yanke masa ƙafa Koda iyayen sa suka tambaye shi garin ya hakan ta faru bai ɓoye komai ba hakan ya faɗa masu Sosai hankalin su ya tashi sukayi masa faɗa sosai suka ce dole sai sunje garin Katsina sun mai me yafiyar iyayen Rabi'a Haka kam akayi bayan suje suka tai basu hakuri inda suka faɗa abinda ya samu Bashir sai aka kamo Bashir ɗin aka shigo dashi gidan sosai hankalin su mama ya tashi suka ce babu komai Baba yanzu ya zama wani shuru dashi ya chanza ya gyara rayuwarsa domin har makaranta ma ya koma Amira kullum cikin addu'a take ma ƴar uwar ta da naima ma ta rahamar Allah ana ta shirye shiryen bikin Amira ta bangaren Fatima ma ta rungume rashen Rabi'a inda take ta rainon cikin ta Bayan shikara biyar abubuwa da dama sun faru samu daɗi da akasin haka aciki harda rasuwar Bashir rasuwarsa ma girgiza mutane Amira tana da ƴar ta mai suna Rabi'a Sosai yarinyar ke samun kulawa Fatima na da yara uku babbar itace mai sunan Rabi'a sai ƴan biyu Kwance take tana baccin ta cikin kwanciyar hankali cikin mafarkinta sufar Rabi'a ta baiyana tana sakar ma Fatima murmushi Fatima hannu tai na miƙawa tana san ta kamo Rabi'a amma ta kasa Alhaji Abdullahi dake zaune ya na aiki a system ya zuma ma saurutar Allah ido dan ba tun yanzu Fatima take wannan mafarkin ba Cikin mafarkin Rabi'a ta yi murmushi ta ce "ai bazakiya iya taɓa ni ba Fatima, na gode da komai na gode ina mai maki albishir da ina cikin rahamar Ubangiji ki gaida min da mama da amira da yaya Ahmad da mijinki kuma ki ce ma Baba na yafe mashi." Tana gama faɗar haka ta ɗaga ma Fatima hannu ta ɓace bat Fatima wani kalar murmushi ta sake a fili tace "Alhamdulilah Alhamdulilah." Sai kuma ta tashi ta rungume Alhaji Abdullahi_______________________________ Tammat bi hamdillah Alhamdulilah Alhamdulilahi Alhamdulilah Allah na gode maka da ka bani damamaki da yawa na fara littafin nan lafiya na gama lafiya babu abinda yafi wannan daɗi Kuskuren dake ciki Allah ya yafe min ya Allah ka Bama iyayena ladar rubutun nan da nayi _______________________________godiya ta musamman ga makarantan litafina Allah ya saka da alheri Allah ya bar kauna ______________________________bazan manta da JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION Kuma kunbani gudunmuwa ta musamman na gode Allah ya ƙara basira da hazaƙa_________________________ sai mun haɗu a sabon littafi wanda zai zo maku 1/12026 in Sha Allah Sunan wannan littafi KURMAR RAYUWA Fatima Bintu hugssain🥰 Ina son ki masoyana An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Chapter 6 of 7