Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
kamata su zamar maki bango, kuma najingina sune, suka zamar maki damuwa haba dan Allah mai ya sa a wasu lokutan iyayen mu kan komawa kamar wasu mara sa...." Rabi'a ce ta rufe ma ta baki ta na girgiza ma ta kai ta ce "Dan Allah kada kice komai Amira bai kamata kiyi wata mummunar magana akan iyayen mu ba." Fatima ta ce "ƙaddara wata aba ce wadda bawa baya iya tsallaketa, kowa da kalar nasa salon kaddarar, haka kuma kowa da kalar tasa salon kaddarar Haka ba'a iya guje ma ta domin ita ta kasance rubutacciyar aba ce tam kar zanan dutse." Rabi'a ta ce " Tabbas maganar ki haka ta ke babu wata makusa akan ta, Allah ya iya mana Allah ya shige ma na gaba." Da Amin suka amsar Rabi'a ta ce " Amira ta shi mu je gida dare na yi." *JARBATATA* Writing by Fatima Bintu hussain {06:46am) (Wednesday, November 2025) https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://www.arewabooks.com/chapter?id=68f9f2ac0b67675ed115f6c9 https://www.wattpad.com/user/hiameera43?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*💪✍️ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️ *"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"*💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) *اَللّٰهُمَّ صَلِّ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَّعَلَىٰ اٰلِ مُحَمَّدٍ ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَىٰ إِبْرَاهِيْمَ وَعَلَىٰ اٰلِ إِبْرَاهِيْمَ ، إِنَّكَ حَمِيْدٌ مَّجِيْدٌ ، اَللّٰهُمَّ بَارِكْ عَلَىٰ مُحَمَّدٍ وَّعَلَىٰ اٰلِ مُحَمَّدٍ ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَىٰ إِبْرَاهِيْمَ وَعَلَىٰ اٰلِ إِبْرَاهِيْمَ ، إِنَّكَ حَمِيْدٌ مَّجِيْدٌ.*✨ Chapter 8 *Rabi'a* Sai da Fatima ta rakosu har ƙofar gida san nan ta ko na suna tafiya suna fira har suka shiga gida kai tsaye ɗakin su suka nufa Nan ma firar suka dasa kuma suna cikin firar ne wayar Rabi'a ta yi Ringing kallon wayar suka yi su duka domin ganin mai kiran Baƙuwar numbern ce amma duk da haka bai hana Rabi'a gane numbern Bashir ba ne Allah ya yi ma ta wata kalar baiwa kallo ɗaya zata yi ma abu ta haddace shi a kan ta Kuma zama ɗaya zata yi ta mutum zata karan shi duka idan Rabi'a ta yi wani abun sai ka rantse da Allah Computer ce domin Allah ya bata ƙwaƙwalwa mai aiki kamar inji Amira ta ce "To kuma waye ke kiran ki da dare hak." Rabi'a ta ce "Wannan mutumin ne." Sai da ya yi kira huɗu kafin ta ɗaga da sallama A maimakon ya amsa sallamar sai ya kama mata wata maganar Hakan ya sa Rabi'a ta yi shuru ba ta ce komai ba Da ha can kuma ya na ta surutun shi kamar wani wanda aka saka ma batur "Assalamu alaikum." Rabi'a ta ƙara cewa Jin ta ƙara mai sallama a maimakon amasar maganar shi ya sa ya amsa sallamar kafin ta bashi amsar maganar da yake mata Sai kuma duk su ka yi shuru jin shurun ya yi ya wa ya sa ka Rabi'a ta ce "Zan ajiye waya." Murmushi ya yi ya ce "Baki iya yi ma mutum fira ba." Ita dai Rabi'a bata ce komai ba Tana jin shi sama sama ya gama firar shi ya yi mata sallama Amira ta ce "Naga alama wannan mutumin yana da surutu." Rabi'a ta ce "ke ma dai kya faɗa." Amira ta ce "kai yau bamu kwanta da wure ba, ya kamata mu kwanta kusan karfe 12:00 fa." *Yaya Ahmad* Ɗazo da ya zo gidan bayan fitar su Rabi'a Umma ke faɗa mashi zuwan wannan mutumin A ganta ya yi nuna farin ciki sosai Amma Allah kaɗai yasan abinda yake ji a zuciyar shi anya kuwa mutanan nan sun san ƙaddara kuwa saboda ƙaddara ta samu yarinya daga zuwan mutum babu binciken komai a kai mu Aminta da shi Mahaifin shi ya kira domin su yi magana a kain Rabi'a Bayan Baba Abubakar ya ɗaga kiran sun gaisa Ahmad ya faɗa mashi abinda Umma ta faɗa mashi da yaje gidan Baba Abubakar ya ce "To ni banma san anyi hakan ba kuma nasan Usman bai sa ni ba, da ya sa ni sa ya faɗa min." Ahmad ya ce " Yanzu Baba babu wani abun da zaku iya yi akai?" murmushi Baba Abubakar ya yi ya ce "Kasan muna iya bakin ƙoƙarin mu akan mu inganta rayuwar yarinyar nan amma mahaifinta ya hana kada ka manta wulƙancin da ya yi ma na, ya ce mu fita harkar yarinyar shi." Yaya Ahmad ya ce " Allah to ya zaɓa mata mafi alkairi amma wallahi Kawu Musa sai a hankali kamar ba shine mahaifin ta ba." Daga bangaren Baba Abubakar ya ce "Mahaifinta ne mana idan ba shi bane to waye?" Yaya Ahmad ya ce "Wallahi ta na bani tausayi Baba." Baba ya ce "ai da kana jin tausayin ta da auren ta ka yi amma ka zauna kai kana tsoron matar ka matar da ba ta san mutumcin dangin ka ba." Yaya Ahmad ya ɓata fuska ya ce "Ni dai yanzu nayi alƙawarin indai wannan mutumin ba auren ta zai yi ba ni zan aure ta, na nuna mata kulawa na mantar da ita, duk wata damuwa." Baba Abubakar ya ce " Allah dai bai nufa zaka aure ta ba ne amma ni, Tun tuni nike maka sha'awar auren ta, Yarinya ga hakuri ga tarbiya duk a gidan daga ita sai Amira ne suka fita Zakka." Ahmad ya ce " Shi ke nan yan zu dai komai ke nan sai na shigo gidan." sallama su kayi ya a jiye waya *Alhaji Abdullahi* Murmushi ya yi jin Fatima ta kashe wayar mai kenan, mai hakan ke nufi hankan na nufin ta amince ne ko kuwa, Murmushi ya kuma yi da ya tuna binciken da ya sa ayi ma shi a kan ta tunda ga kan auren da ta yi har zuwa dalilin fituwar ta daga gidan auren da rasuwar mahaifinta har labarin ta da Rabi'a aka bashi tabbas ya tausaya ma Rabi'a, sosai kuma ya yi mamakin halin iyayen ta A fili ya ce " In Sha Allah Fatima tawace ni da kaina zanje gidan su gobe." *Fatima* Bayan tafiyar su ya Rabi'a sai ta kwanta da nufin bacci, amma baccin ya ƙi zuwa sai ma tunanin wannan mutumin da ya faɗo mata a rai, badan ta so ba ta afka duniyar tunani a kan shi ita baza ta ce tana jin komai a kan wannan mutumin ba kuma ita bata ga wata makusa a ta re da shi ba ita kanta tasan ba wuce aure ba tasan tana buƙatar aure wata zuciyar ta ce ya kamata ki amince da shi indai da gaske yake kodan ki inganta rayuwar ki da da mahaifiyar ki, tana cikin wannan tunanin bacci ya dauke ta *Bashir* Murmushi ya yi bayan sunyi sallma da Rabi'a a fili ya ce "yaro man kaza." Wai ke a tunanin ki son ki ni ke yi da har ki ke tunanin ki jamin aji (Misssu wallahi wannan mutumin yana bani haushe😠😠😠kufa) *Rabi'a* Kamar yanda ta saba bata iya bacci ba haka tayo alwala ta zo ta fara nafila Sai da ta gama nafilar wani tunani ya zo ma ta ya kama ta ta yi istihara akan wannan al'amarin wannan mutumin Taji daɗi da wannan tunanin ya zo mata haka ta tashi ta yi sallar istihara Kamar dai yanda ta sa ba kamar yanda abin yabi ma ta ji sai da ta yi shi wato kuka ita fa ta rasa meye tsakanin ta da kuka Kuma ba san san da ta fashe da kuka ba kuka Sosai kuka harda shasheƙa Ita dai tana jin ta kamar ba'a dai-dai ba Zuciyarta ta dafe cikin kuka take cewa " komai na rayuwar ɗan adam yana tafiya ne bisa tsari da kuma kudurar Ubangiji,komai kaga yafaru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin rubutun kunɗin rabutun ƘADDARAR shi ne walau walau KADDARA mai kyau ko akasin haka, sai dai masu iya magana sukan ce ita ƘADDARA aba ce mara tabbas, nan take takan iya chanzawa, ita kuma yarda da ƘADDARA kanta mai kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin cikaken imanin ko wani bawa Wani kalar kuka Mama ta fashe da shi mai cin rai kuka na tausayin wani wanda ya rasa komai a rayuwa kuka na tausayin mutumin da ƙaddara ta raba shi da duk wani jin daɗi Da gudu ta far ƙofar ɗakin dan kada wani ya jita ma, ko a ganta Ɗakin ta ta shiga ta ɗurƙushe a ƙasa ta na ƙara sakin kukan Ita kaiɗai tasan abinda take ji a zuciyar ta ita kaɗai tasan kalar zafin da zuciyar ta ke ma ta Mai yasa ta biye ma mutane ne mai yasa ta bari maganar mutane ta yi tasire a kanta wai ina ilimin ta ya tafi ne Dalilin ta zuwa ɗakin ta je ne zuyi magana da Rabi'a akan mutumin ɗazo domin a yanzu da shirya tsaya ma ƴarta ta shirya faɗa da kowa akan ɗiyar ta *Rabi'a* Bayan ta gama addu'ar ta wani bacci ne ya dauke ta bacci mai nauyi Ita kanta ta yi mamakin baccin da ta yi Washe gari Kamar yanda ta saba aikin ta haka ta tashi ta yi abinda zata yi Ta kai yara makaranta Ganin kuma bata da wani aiki da zatayi yasa ta fara karatun littafi da Amira ta tura mata wai ta dinga karan tittafai zata dinga rage damuwa Ko yanzu ma wani take karantawa mai suna FUSKAR ƁOYE wanda Fatima Bintu hussain ta rubuta Tana karantawa tana murmushi domin yanda jarumin littafin ya maida jami'an tsaro wasu shahasu kuma abin dariyar ma a wajan cikin su yake aiki amma sun kasa gane shi Yana ta tura su a rame A fili ta ce "tabbas karatun littafi nasa deɓe kewa kuma yana saka nishaɗi Allah ya saka ma marubuta da alkairi (Nikam na ce Amin Rabi'ar mu🤣🤣🤣) JARABTATA Writing by Fatima Bintu hussain Sunday, November 2025 {11:17pm} https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://www.arewabooks.com/chapter?id=68f9f2ac0b67675ed115f6c9 https://www.wattpad.com/user/hiameera43?utm_source=android&utm_medium=link&utm _campaign=invitefriends 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*💪✍️ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️ *"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"*💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) *✋𝙒𝘼𝙎𝙄𝙔𝙔𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙉𝙆𝙒𝘼𝙉𝘼🤚* *Yakai Dan uwana ka sani, abin da ke cikin zuciyarka shi ne yake bayyana a wajenka. Ba muhimmanci yaushe ko ta yaya? Wannan aikin Ubangijinka ne. Kai dai ka yi imani, ka gaskata.* _*Saboda haka ka gyara niyyarka da ɓoyayyiyar zuciyarka, ka yi zato mai kyau ga Ubangijinka, ka yi aiki da gaskiya, ka dogara gare shi, cikin yaƙini da falalarsa – za ka yi farin ciki a duniya da lahira.*_ Chaptar 9 *Rabi'a* Tana cikin karatun littafin ta cike da nishaɗi da jin daɗi wayar ta ta fara neman agaji, tsaki ta yi ta na jin haushin mai kiran da ita wallahi bata so wani abu ya tsaida ta ba sai ta gama karanta littafin nan duk Wannan kiran shine zai kaita ga wani mataki na wata ƙalar mumunanar ƙaddara, ƙaddara da babu wani haske a cikin ta, ƙaddarar da zata ƙara jefa a cikin wani duhun bayan wanda take ciki, ƙaddarar da bata isa ta guje ma ta ba Da sallama a bakin ta ta ɗaga wayar daga ɗayan bangaren aka amsa mata gaishe shi ta yi, sai kuma ta yi shuru ta na sauraran abun da ya ke cewa Gabanta ne ya yi wani kalar faɗuwa bata ma san ta kashe wayar ta yi wurgi da ita ba, gaskiya ne kuwa abun da aka faɗa ma ta? "Nooooo ya za'a ce Baba ya bada aurena ga mutumin da bai sa ni ba babu binciken komai ba ka san halin mutum ba amma ka bashi, Nikam mai na aikata ma Baba ne zai min haka Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm, Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm , Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm, shi ke nan tawa ta ƙare, Wace kalar ƙaddara ce Allah ya jarabta ni da ita haka, ya Allah, ni kuma haka tawa ƙaddarar ta take bani da wani jin daɗi a rayuwa, wata ƙila naji daɗin rayuwa ta nan gaba, wata ƙila haka rayuwata take, ina fatan idan banji daɗi a duniya ba rahirata ta yi kyau." Duk wannan maganar da take yi a fili take yin ta cikin fitar haiyaci ta fara buga kanta a bango *Baba* Tun sanda ya amsa numbern wayar bashi yake ta tunani ya kira ko kuma ya ɗan bada lokaci haka ya haƙura bai kira ba har zuwa safiya, dalilin kiran Bashir ɗin kuma su yaya Abubakar da Usman ne suka zo suna bashi shawara akan kada ya kai ga amincewa da mutumin da ba'a san shi ba ya bari ayi bancike sosai kafin a amince da shi Ai kam mai Baba zai yi in ba masifa ba cikin faɗa yake cewa "Naga dai Rabi'a ɗiyata ce, kuma ni na haifeta, dan haka babu wanda zai zo ya ce ga yanda zan yi da iyalai na ba." Ya na kaiwa nan ya dauka wayar sa ya kira numbern Bashir ya ce ya zo ya na son ganin shi kuma zai bashi auren Rabi'a Cikin ɓacin rai Yaya Abubakar ya ce "duk abun da ka yi banyi mamaki ba kuma bazan yi ba saboda jahincin da ke dawainiya dakai." Usman ya ce "wallahi yaya ka bani kunya mai yasa ka kasa yarda da ƙaddarar yarinyar nan? Anya kuwa ba kayi ma Allah shishigi akan al'amuran sa ba? Dan Allah yaya kabar Rabi'a ta huta, mata nawane suka mutu basuyi aure ba,dan Allah yaya kada ka yi ma Rabi'a auren dole." "Usmanu." "Na'am yaya." "Usmanu." "Na'am yaya." Usmanu." "Na'am yaya." "Sau nawa na kira sunanka?" "Sau uku ne yaya." "Wallahil Azim na ƙara jin bakin ka a a harkar iyali na sai na ci uban ka." Cikin ɓacin rai! Abba Usman ya ta shi ya ce " indai na haihu bazan ƙara shigar maka hidima ba kuma zan dauka Rabi'a zata koma waje na na ga wanda zai ta kura ma ta." Yaya Abubakar sanƙarewa ya yi a wajan domin ya ma rasa mai zai ce Ganin Abba Usman ya fita shi kuma Baba ya bishi ya na sababi ya dawo da shi haiyacin shi ya sa ya tashi ya bi bayan su Abba Usman kai tsaye yana fitowa ɗakin Rabi'a ya yi abun da ya gani ne ya yi mugun ta da ma shi hankali Rabi'a ce kwance a ƙasa ga kanta sai zubar jini yake kamar a buga ma ta wani abu akan cikin tashi hankali ya ƙarasa ina da ta ke Amma me bata motse da al'ama dai suma ta yi haka ya dauke ta bai damu da jinin da zai ɓata mai kaya ba Ya na fitowa da ita kuma a daidai nan su Baba su ka iso ganin halin da take cike ne ya sa ya haɗiye masifar shi Yaya Abubakar ya ce "Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm, mai yasa me ta haka?" Abba Usman ya ce "wallahi ban sa ni ba ina shiga na ganta a kwance kanta duk jini." Amira ce ta shigo da sallama ganin Rabi'a a hannun Abba Usman ka kuma jini a kan ta ya sa ta fasa ƙara ta ce "Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm, mai ya same ta Yaya Rabi'aaaa." Ta ja sunan cikin yanayi na tashin hankali Wannan ihun Amira ne ya ja hankulan mutanan gidan duk suka fito suga abun da ke faruwa Mama ce ƙashen fitowa domin damuwa ta yi ma ta yawa tun bayan da taje ɗakin su Rabi'a jiya Cikin tashin hankali ta ce "Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm, Iailahailala Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam." Cikin rawar murya ta ce " M....mai y...a...sa...me....ta...?" Kuma kafin wani ya ce ma ta wani abu ta yanke jiki itama ta faɗi da gudu Amira ta yi kan ta Tana girgiza ta kuma a daidai lokacin Fatima ta shigo ganin abun da ke faruwa ya sa ta yanke jiki ta faɗi Sakan ɗaya biyu uku Asibiti cikin ikon Allah da yardar sa Rabi'a ta farfaɗo dama Mama da Fatima tun a gida da aka saka masu ruwa suka farfaɗo *Bashir* Kwance yake da al'ama ma bacci ya ke kuma cikin baccin ne ya ji wayarsa na neman ajaji Cikin magagin bacci ya ɗaga wayar bayan sun gaisa da mai kiran ya ke tambaya waye dan mai gane mai magana ba hassali ma bashi da numbern wayar a cikin wayarshi Jin mutumin ya ce shine Baban Rabi'a kuma ya na son ganin shi zai bashi auren ƴarsa A zuciyar Bashir ya ce anzo wajan da wuri haka kuma, ni ban yi tunani komai zai zo cikin sauri haka ba kace na fara shiri A fili kuma ya ce "Allah sarki Baba na gode sosai, Allah ya saka da alheri, kuma in sha Allah, ina nan zuwa." Bayan sun yi sallama Bashir ya yi wani kalar murmushi kafin ya ce "haba malam ko hakan da ka yi ai ka nuna min ɗiyar ka bata da wata daraja." Yana faɗin hakan ya tashi ya shiga ban ɗaki wanka ya yi ya fito daure da tawul yana goge jikin shi bayan ya yi yan shafeshafen ya shirya cikin ƙana nan kaya ya zari key ɗin motar shi ya yi waje *Fatima* Dalilin zuwanta gidan su Rabi'a a wannan lokacin kuwa Alhaji Abdullahi ne ya kira ta ya ce zaizo gidan su ya na son za su yi wata magana Bayan sun gama wayar taga ya dace a ce Rabi'a ta sa ni shine tazo ta faɗa ma ta ta bata shawara akan zuwan nashi Tana shigowa kuma ta yi wannan mummunan ganin *Yaya Ahmad* Dama ba daɗe wa za su yi ba zai komai kaduna zai bar Fiddausi da yaran a Katsina saboda yanzu ya samu hutu duk bayan sati biyu zai dinga zuwa gida Yanzu ma ya gama shiryawa zai wuce Kaduna suna zaune suna karyawa wayar sa ta yi ƙara alamar ana kiran shi ganin sunan mahaifin shi ya sa ya ɗaga wayar da sallama Sai da ya gaisheshi daga bangaren yaya Abubakar ya amasa yake tambayar shi ya na ina Yaya Abubakar ya ce "Ina gida abbi, fatan dai lafiya." Yaya Abubakar ya ce "kazo muna asibiti." "Asibiti kuma waye baida lafiya." A takaice yaya Abubakar ya faɗa mashi abun da ya ke Cikin kiɗima yaya Ahmad ya ce "WHAT!" "Ganin nan zuwa asibitin wani asibiti ne?" Yaya Abubakar ya faɗa ma shi kai tsaye hanyar fita ya yi bai bi ta kan Fiddausi da ke tambayar shi abun da yake faruwa ba JARBATATA writing by Fatima Bintu hussain Monday, December 2025 {10:12am} https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*💪✍️ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️ *"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"*💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) *HANI GA YIN BUSA A CIKIN RUWAN SHA* *❝Manzon Allah ﷺ ya ce: "Idan ɗayanku zai sha abin sha, to kada yayi nunfashi ko nishi a cikin kofin/ƙwaryar❞* *"Haƙiƙa Manzon Allah ﷺ ya fi kowa ilimi da tarbiyya a cikin hakittun Allah, ya kasance yana koyawa al'ummarsa dukkanin komai da zai amfanesu, yana daga cikin ilimin da ya koyar dasu shi ne, ilimin cin abinci, da abin sha sannan kuma da ilimin biyan buƙata*" "*Kada ka taɓa yin tunanin cewa akwai wata kafa ko ƙofar da Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya bari bai buɗe mana ita ba da ilimi na shiriya, haƙiƙa duk abinda yayi hani daga gareshi to tabbas akwai fa'idar aikatawa, duk abunda yayi umurni dashi to haƙiƙa akwai gwaggwaɓan lada ga wanda ya aikata shi"* Chaptar 10 *Yaya Ahmad* Yaya Ahmad na fita kai tsaye asibitin da Rabi'a take ya nufa Ina isa ya kira Abbi ya zo ya shiga da shi ciki kai tsaye lab suka nufa aka auna jinin shi aka ga kalar na Rabi'a ne dan haka aka ɗebe laida uku Sai da ya ga komai ya yi daidai san nan ya yi masu sallama zai wuce kaduna komai kenan sai sun yi waya Mama bayan ta farka daga baccin da ya dauke ta ta buƙaci ta na son ganin ƴarta, ɗakin da Rabi'a ta ke, ta shiga kwance ta ganta jini na shiga jikin ta ta yi wani kalar haske, kamar ta shikara ta na jinya, Fatima ce a kan kujirar gaban ta ta kama hannun ta ta riƙe gam a haka ita ma bacci ya yi awon gaba da ita, sai kuma Amira da ke zaune kan darduma ta zabga uban tagumi, da alama ta yi nisa cikin tunanin, duk sallamar da Mama ta yi bama ta san ta na yi ba, da yake kowa na fama da tashi damuwar ya sa Mama bata wani kula Amira ba, kai tsaye kan gadon ta hau ta kura ma Rabi'a ido sai kuma ta fashe da wani kuka mai cin rai, wannan kukan nata ne ya yi sanadiyar tashin Fatima, da Amira da ta dawo daga duniyar tunanin da ta faɗa Su duka kallon Mama suke kamar sun samu television domin Mama bata taɓa nuna damuwar ta akan Rabi'a ba shi ya sa koda suka ga tana kuka basu kawo wani abu a ransu ba Amma sai Mama ta girgiza tunanin su ta hanyar rungume Rabi'a ta ƙara sakin wani kukan cikin kuka take cewa "dan Allah Rabi'a ki yafe ni, Rabi'a san zuciya ya kai ni har na banzatar da ke, a matsayina na mahaifiyarki ai kamata ya yi ace na mai da hankali akan ki na baki kulawar da duk wata uwa ya kamata ta bama ƴar ta." Amira basan sanda ta fashe da kuka ba ta ce "Why why why Mana da kika biye ma mutane kika banzatar da Rabi'a haka kamar bake ki ka haifeba ta ba, wallahi da ina tunanin anya ke ki ka haife yaya Rabi'a? Kuwa yanda kina banzatar da rayuwar da babu wanda take raɓa ta ji daɗi daga ni sai Fatima, Fatima itace ta zamar ma ta tamkar uwa, amma dan Allah kiyi haƙuri nasan maganganun da na faɗa maki bai dace ba dan Allah ki yafe ni." Ta ƙarasa maganar tana hada hannuwanta alamar roƙo🙏🏿 Mama ta ce "Amira ba kiyi laifi ba komai ki ka faɗa ya dace a faɗa min, dan ma da abun da yafi haka ki faɗa, min wallahi bazan ga

Chapter 4 of 7