Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
su yaya Abubakar suka sama mashi gida ginan ne saboda lokaci zai ƙure idan akace sai anyi saya fili an yi gini bayan sun sai mashi gida suka daura shi akan harkar kasuwancin kayan hatsin duk wani abun awo shine sana'ar su sai noma da suke yi, Bayan wata biyar A lokacin suna da wata biyu da aure su duka suna zaune cikin kwanciyar hankali matar yaya Isma'il tana da ciki wata biyu, Malam Musa kam lukafa taci gaba domin yana samun ƴanda yake so wajan matar shi Asma'u tana yi mashi biyaibaya Sosai haka yasa son ya ƙara lunkuwa a cikin zuciyar sa kuma ta hana shi abubuwa da yawa da yake yi, Bayan shekara Matar yaya Isma'il ta haihu ƴar ta mace inda taci sunan zainab wato sunan abu a lokacin kuma matar yaya Abubakar da Asma'u sun kusa haihuwa dan cikin su kusan watan su ɗaya, Bayan cikin su yakai watan haihuwa matar yaya Abubakar ce ta fara haihuwar ɗan ta namiji inda yaci sunan Amadu bayan sati biyu Asma'u ta haifi ƴar ta mace kyakyawar gaske inda taci suna Rabi'atu suna kiranta da Rabi'a yarinyar ta taso cikin gata da ƙaunar iyayen ta zaiyi wahala ta naimi abu ta rasa, Ta bangaren su yaya Abubakar ma hake ne suna Bama yaran su kulawa sosai ƴan da addinin musulunci ya nuna mana, Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda haihuwa ta buɗe ma ko wannan su domin su yaya Abubakar sun aurar da wasu daga cikin yaran su, Malam Musa ya hango wata budurwa sa'adatu inda ya haukace a kan ta babu ɓata Lokaci akayi auren su da Asma'u ta nuna tashin hankali amma daga baya sai ta watsar, Amarya sa'adatu da tashigo da niyar rashin mutumci amma ganin Asma'u ta nuna ko kallo bata ishe taba hakan yasa ta zubar da komai nata suka kama zaman lafiya, A lokacin kuma Rabi'a ta maida hankalin ta ga karatu wasa wasa har ta gama karatu bata da wani saurayi tsayaye ga ƴan uwanta duk an masu aure ƙannan ta, Tun da takai shekara ashirin da biyar babu wani tsayayen saurayi fa aka fara magana dun daga wannan lokacin abubuwa suka fara sauyawa a lokacin idan an yi ma iyayen magana sai suce ai Allah ne bai kawo ba haka dai duk akayi ma ƙannan ta aure ƴan zu hakama daga ita sai Amira sune manya a gidan itama Amirar an kusa auren ta, Tunda ta kai shekara talatin nan fa iyayen ta suka saka ta a gaba akan dole ta fitara da miji ta zama abin magana a unguwa ita ko kunya bata ji ana aurar ta ƙannan ta sai dai tai ta zuwa aure amma ita tanan jibge tun iyayen su basu daukar maganar har ta kai ga sun fara dauka Bama kamar mahaifiyar ta Asma'u itace ta fara daukar abin da zafi saboda ana gaya mata magana akan ha ƙatuwar budurwa nan a gaban ta babu aure wannan gorin da habaic habaici sune sukayi nasara a zuciyar Asma'u Wanda ta fara ne da daina shiga lamuranta ko gausheta tayi sama sama take amsawa kuma duk wani abu aiki sai taita sata wasa wasa ta daina yi mata duk wani abinda uwa zatayi ma ɗiyar ta taji daɗi, Haka ƙannan ta suta wuƙantata suna mata rashin kunya amma ba'a hana su da malam yana hanawa amma kuma daga baya sai yayi tunanin idan ana mata gori ta gaji tayi auren dan kan ta hakan yasa duko duk wani aikin gida ita zatayi, Wanke wanke wanki dafa abinci shara wanda da duk masu aiki suke yi, Bayan Amira a wajan mutum ɗaya take samun sauƙi shine yaya Ahmad ɗan ɗan yaya Abubakar ne yake zaune a gidan wajan sa'adatu shima baya jin daɗi abinda iyayen su ke yi mata, Wata rana ma har magana yake yi ma iyayen amma suta zagin shi suna ciwa ya aure ta idan baya son ana mata wulƙanci shi kuma har ga Allah da yana da dama da ya aure ta, Allah ya haɗa shi da mata mai mugun kishin tsiya san nan kuma ma aikin shi bana zama bane na yawo ne soja ne da a nan yake zaune akai mashi taransupar aka mai da Kaduna hakan yasa kusan zaman shi ya koma kaduna sai dai in yazo JARABTATA https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U *🌲 MUSULINCI JIGON RAYUWA 🌲* Shawara: Kada ka bari zumuɗin yin aure ya rinjaye ka, har ka zaɓi wadda ba ta dace da kai ba. Ka nemi zaɓin Allah (istikhara), ka bincika, ka yi haƙuri, kafin sai ka yanke shawara. Yawan gaggawa a cikin zaɓin aure yana jefa mutane da dama cikin nadama mai tsanani. "Ka nemi mace mai addini, hannuwanka su yi albarka." (Hadisin Manzon Allah ﷺ JARABTATA writing by princess Chaptar 3 Hakan yasa bai ce komai ba tunda aka yi mashi maganar auren ta shi dai yana mata addu'a Allah ya bata miji na gari, Tunda ga wannan ranar da ya yi magana bai sake yi ba hakan yasa yake taimaka mata da duk wani abu da take so saboda yaga kowa yana ƙymarta ana gudun ta kamar warda ta aikata babban zunubi, Cigaban labari Wani wahalalen numfashi ta sauke mai haɗe da kuka a firgice amira ta farka cikin damuwa Ta ce "haba Yaya Rabi'a nasan ke musulma ce? kin yarda da Allah kin yarda da manzan Allah mai yasa baki dauki kaddarar ki da hannu biyu ba mai yasa kin manta akwai wainda suka fiki shiga cikin damuwa da mummunar kaddara." Kuka ta ƙara saki mai taɓa zuciya tabbas gaskiya Amira ta faɗa ita musulma ce bai kamata ta shiga damuwa akan kaddarar da ba why ta manta da duk wata baida da Allah ya bada ya bata lafiya ya bata ilimin ya bata duk wani abu da ɗan adam keso yanzu idan tazo a matsayin gurguwa ko makauniya kuma fa? Ita da kanta ta yi ma kanta wannan tambayar sai kawai ta yi wani murmushi da bata san daga ina yake ba. Tunda ta fara wannan tunanin Amira take kallon ta cike da tausaya wa kuma yanayin ta yasa ta gane za'ayi nasara Rabi'a tace " Astagafurillah Astagafurillah Astagafurillah ya Allah Allah na tuba ya Allah ks yafine Ina Hankali na da tunani na suka tafi haka har na manta da abubuwa da yawa da kayi min ba ka yi ma wasu ba Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm Amira na gode da wannan tunin da ki kai main." tana kaiwa nan ta rungume Amira Aisha da take kwance ta buga uban tsaki tana cewa "wannan bala'i har ina kullum sai ki hana mutane bacci da wannan banzan kukan naki." Wasu gigitatun maruka Amira ta sauke mata cikin faɗa! ta ce " maza ki fita ɗakin nan tunkan ranki ya ɓaci." Tana kunƙunai tafita ta bar ɗakin Magana take cikin kuka tana ciwa "ya Allah kaine ka jarbace ni amma na kasa dauka ni kaina ban san mai yasa nikeyi ma Rabi'a haka ba ban san mai yasa ba amma ina son ki sani ni mahaifiyarki Rabi'atu ina son ki amma abin kunya ne na dinga nuna Ina son ki mutane zasu min dariya." (Jan hankali ga iyayenmu bai kamata a matsayin ki na uwa ba ace kina daukar zugar mutane akan ƴar da kika haifa wai dan kada ayi maki dariya ko kada kiji kunya wajan mutane To ita kuma yarinyar fa Allah kaɗai yasa kalar damuwar da suke shiga aduk Lokacin da ko wani yaron kirki yake cikin damuwa mahaifiyace kawai zatasa taji sauƙin damuwar sa amma kuma ya kike tunanin zai ji ace harda ke ake sama shi damuwa dan Allah iyaye ku dinga rungumar yaran ku a duk halin da suke ciki Allah yasa mu cika da imani) Rabi'a yau tayi bacci babu laifi baccin da ta daɗe tana yin shi Bayan Amira ta kora A'isha tasamu tayi nafilar da tasa ba kuma cikin ikon Allah bacci ya dauke ta a kan abin sallar ta Washegari tana gama sallar ta tafita zuwa gaida iyayen ta kamar yanda ta saba ɗakin Umma ta fara shiga ta gaisheta ciki ciki ta amasa mata sannan taje ɗakin Baba da ya dawo daga masallaci ta gaishe shi sama sama ya amsa kamar ba mahaifinta ba Ɗakin Mama ta shiga ta gaishe ta abin da ya bada mamaki jin mama ta amsa gaisuwar ta ta kuma maida mata da ta tashi lafiya Cikin zaƙuwa da farin ciki ta amsa da Alhamdulilah Sai kuma da juya zata tafi sai kuma taji Mama ta kira sunan ta Rabi'atu! Cak ta tsaya da tafiyar da take kamar bishiya sai da tai kunan minti ɗaya kafin ta juyu ta kalle mama Amma ganin mama ta kama harkar gaban ta yasa tace "ki na buƙatar wani abune?" Kai kawai ta girgiza ma ta Ita kuma ta fita cike da farin ciki mai tarin yawa kamar yanda ta saba aikin ta haka tayi takama yara ta kaisu makaranta yau da ka ganta kasan tana cikin farin ciki ko ba'a faɗa maka ba duk maganar da mutane keyi ana nuna ta sai taji bata damuba domin yau rana ce ta farin ciki ta manta rabon da mama ta tambayi lafiyar ta dukan da Mama tayi mata jiyi ta tuna sai kuma zuciyar ta kare JARABTATA https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://www.arewabooks.com/chapter?id=68f9f2ac0b67675ed115f6c9 https://www.wattpad.com/user/hiameera43?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION THE NOVEL WRITER'S TEAM 🌲 MUSULINCI JIGON RAYUWA 🌲 Tsammanin mutane ya na yi wa zukata illa fiye da yadda cin amana ke yi.Ka rage tsammani daga mutane,zaka rage bacin rai🧏🏻‍♂️ Allah ubangiji yasa mudace 👏🏻 Jarabtata Writing by princess Chaptar 4 Haka dai ta wuce gidan su Fatima da sallama ta shiga gidan Ammi mahaifiyar Fatima da tsufa ya fara kamawa ta amsa mata cikin sakin fuska Rabi'a ta duƙa har ƙasa ta gaida ta san nan ta tambaye Fatima Ammi tace "ki shiga tana cikin ɗaki kanta ke mata ciwo." Rabi'a tace "Allah sarki Allah ya bata laifiya Ammi ta amsa da "amin." Ɗakin ta shiga taga Fatima kwance amma ba bacci take ba sallama tayi sai da tayi kusan sau uku san nan Fatima ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi Da murmushin ta tace "a'a yau Rabi'a ce a gidan namu?" Harar ta Rabi'a tayi a maimakon ta bata amsa Tace "lafiya? ina ta sallam baki ji ba tunanin mai ki ke yi?" Fatima tace "babu komai kawai dai kaina ke min ciwo." Amma a gaske ba haka bane kwana biyun nan tausayin Rabi'a yasaka ta a gaba tana tausayin ta sosai Rabi'a tace "sannu Allah ya sawaƙe ki sha magani sai ki kwanta ni zan wuce nakai yara makarantane zan tafi na ƙarasa aiki na tafi gidan Yaya Ahmad." Mamaki ne ya kama Fatima jin Rabi'a tayi magana mai tsayi haka ita ta manta raban da taje Rabi'a tayi magana mai tsawo haka kuma ta lura yau tana cikin farin ciki Ganin ta tashi ne yasa Fatima ta kamo hannun ta ta zaunar da ita a kan gado tana cewa "meye sirrin ne yau?" Nan Rabi'a ta faɗa mata yanda sukayi da Mama sosai Rabi'a tayi farin ciki tana fatan ta daure a haka ita fa dama ta lura da Mama ba da son ranta take ma Rabi'a wani abun ba San nan Fatima tace "ma sha Allah gaskiya nayi farin ciki sosai Allah kasa Mama ta dare a hakan." Rabi'a tayi murmushi kawai tana ji a ranta ba mai daurewa bane Sallama tayi ma Fatima zata wuce Fatima tace "idan kin shirya ki biyo min sai mutafi tare na taya ki aikin." Sosai Rabi'a tayi farin ciki har ta rungume ta Da sallama ta shiga gidan babu kowa a tsakar gidan hakan yasa ta ƙarasa aikin da za ta yi ta yi wanka ta shirya Ɗakin Mama ta fara zuwa tayi mata sallama sama sama ta amsa mata ba kamar ɗazu ba Ɗakin Umma ta shiga ta amsa makulin gidan Yaya Ahmad Harta juya Umma tace "idan taga dama taje Baban su na kira." Sai da gabanta ya faɗi jin wai Baba na kira ita tasan zaiyi wuya wani abun arziƙi zai faɗa mata duk da yana mahaifinta A bakin ƙofa tayi Sallama sai da aka bata izinin shiga san nan tashi ta duƙa har ƙasa tana ƙara gaida shi bayan warda tayi ma shi da safi Amsawa yayi babu yabu babu fallasa san nan yace "ba komai yasa nakira ki ba sai dan na faɗa maki nagaji da ganin ki haka haƙurina yazo ƙar shi a kan ki ko ki fitar da mijin aure ko kuma na haɗa ki da duk wanda yayi min nagaji da magana da akeyi akan ki." Wasu hawaye masu zafi suka sauko daga idanuwan ta ita kam ya za ta yi ina zata saka kanta wannan shi ake kira rana zafi inuwa ƙuna wai yau mahaifinta ne yake buɗe baƙi yace ya gaji da ita ita kam wannan wace kalar jarabtace haka Tsawar! da Baba ya dama mata ce ta dawo da ita cikin hankalin ta "Dan ubanki! da dake nike ba ina maki magana kin tasani a gaba kina hawaye sai kace famfo to wallahi kinji na rante maki idan har baki yi abinda nace ba zan aikata abinda naga dama." Cikin Muryar mai shirin fashewa da kuka tace "in Sha Allah Baba." Tsaki Baba yayi yace " ni kam nayi baƙar haihuwa madiga guda dake amma kina zaune a gidana wasu ma har tunani suke ko ke matata ce." Sai kuma yace Astagafurillah Astagafurillah Astagafurillah Rabi'a har taji sanyi a ranta jin Baba nace wa Astagafurillah tayi tunanin wani abin na hankali ne yazo mashi har tana share hawaye sai kuma taji yace "ta shi ki bani waje." Ai abinda take jira kenan wannan cin mutumci na Baba har Ina haka ita tana jin daɗi Baba baya takura mata amma yanzu gashi nan ya fara bijiro mata da wata sabuwar taƙurar A maimakon fita kai tsaye sai ta koma ɗakin su ta fashe wani irin kuka A'isha ce tafito daga ban ɗaki tace "tofa wai ke dan Allah kuka baya maki wahala? ne kullum cikin kuka kullum cikin kuka sai kace wadda ake yankan naman jikin ta." Idan ta ta ɗaga tana kallon A'isha A'ishar da tayi auren wuri da ta haifi kamar ta koma wardda ta girme ta amma ta zauna tana gaya mata magana haka babu kunya duka shikara A'isha nawa bata wuce shikara sha tara amma take mata wannan abin Bata ce mata komai ba to mai ma zata ce mata sai kawai ta shiga ban ɗakin da A'isha ta fito ta wanke fuskar ta san nan ta fito zuwa gidan su Fatima Da sallamar ta tashiga gidan Fatima na zaune a tsakar gida ta gama shiryawa dama ita take jira sallama sukayi ma Ammi san nan suka fice daga gidan suka kama hanyar gidan yaya Ahmad Suna tafiya suna fira har suka isa gidan Tunda ya hango su yasaki baki da hanci yana kallon ta kamar wani sakarai Har suka zo suka wuce miyau kawai yake haɗiyewa kamar yaron da ya shikara bai baici abinci ba Aminu ganin abokin nashi kamar baya haiyacin shi yasa yace "haba Buhari ya ina ta magana kai kana can kana wani abin na saki baki kamar wani famfo inata magana." Numfashi Buhari ya sauke yace "haba mutumin ya ina kallon kyakyawar halita kamar wannan ka wani katse min jin daɗi ne." Dariya Aminu ya kwashe da ita yace "dana ai nasan ruwa baya tsami banza nasan haka nan bazaka natsu haka ba ashe na canka wace kake nufi haka?" Nuna mashi ita yayi shi kuma Aminu yace "bari kaga indai zaka min biya mai tsoka yanzu zan nemo maka baya nai a kan ta." Buhari yace "kar kar damu mutumina ai ko nawa kake so zan baka." Aminu naji haka ya fita daga motar da suke ciki yai ta bin bayan su har yaga gidan da suka shiga Mai gadin gidan ya gani ya fito zai je masallaci ya tsare shi da tambaya akan Rabi'a nan mai gadi ya faɗa mashi komai akan Rabi'a kuma ya sanar masa da bata taɓa yin aure ba Sosai Aminu yaji daɗi wannan bayanai da ya samu ko ba komai zaije ya samu ƴan na kashe wa Rabi'a suna shiga gidan saida suka ɗan huta san nan suka cigaba da aikin gidan suna yi Rabi'a na faɗa ma Fatima ƴan da sukayi da Baba kafin ta fito Fatima ta kwantar mata da hankali tana bata wasu shawarwari da ya kamata ta bi Kiran Yaya Ahmad ne ya shigo wayar ta bayan sun gaisa yake sanar da ita sun tahu ta daura masu abinci Saida suka gama gyaran wajan baki ɗaya san nan suka daura sanwar abince da mai gadi yayo masu cifane abinci sukayi mai rai da lafiya bayan sun gama Suka ci suka ƙoshi suka zauna suna jiran su Yaya Ahmad su ƙaraso Basu daɗe ba zama ba suka ji hon ɗin mota waje suka fita suka taya su kwaso kaya suna masu Barka da zuwa Yaya Ahmad kallon ƙanwar tashi yake yi cike da tausayi Bayan sun shiga falon sun gabatar masu da abinci matar Yaya Ahamd dama ba shiri suke da Rabi'a ba Sai wani kallo kallo take masu dan koda suka gaishe ta ma bata amsa ba sai da yaya Ahmad yayi mata magana san nan ta amsa a yamitse kamar tana magana da kashi Sallama sukayi masu zasu tafi Yaya Ahmad ya tsayar dasu ya basu kuɗi masu yawa yace suyi na mashing Fiddausi matar Yaya Ahmad tace "tunda naga aikin ki kenan sai dai ki ta bin gidan yaiye da ƙane ke babu aure ke babu sana'a kizo kuyi mana wanki." Wasu gigitataun maruka Yaya Ahmad ya sauke mata cikin faɗa yake ciwa "ke wace kalar banza ce mara tunani ƴar uwata kike faɗa ma haka to wallahi kiyi hankali bata girme ki bane." Cikin tashin hankali Fiddausi tace " honey ni ka mara saboda wata banza can mai baƙin jini?" Wani marin ya ƙara wanke mata fasuka dasu kafin ya kama hannun Rabi'a suka fito waje ya bata haƙuri yayi masu nasiha san nan ya ce su duka su rubuta abin da suke so su tura mashi Dama ya saba masu haka harda Fatima baya ware su haka zai yi masu siyaiya Sallama suka yi ya koma ciki saboda a gajiye yake da shi zai kaisu Rabi'a suna tafiya suna fira tunda suka fara tafiya suka lura da wata mota Prado ash calor na binsu Amma basu kula ba sunyi nisa sosai suka ji ana masu hon *JARABTATA* {Friday, November 21} [10:06 am] https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://www.arewabooks.com/chapter?id=68f9f2ac0b67675ed115f6c9 https://www.wattpad.com/user/hiameera43?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends RANAR JUMA'A Duk ranar juma'a Kayi kokari ka siya fiyo wata (pure water) leda uku kakai masallaci domin iyayen ka guda biyun dayan kuma domin ka ko suna raye ko basa Raye Allah zai baka lada Allah yabamu ikon amin *JARBATATA* writing by princess Chaptar 5 A tunanin su basu ake wa hon ba, sai da suka ji ana yi babu ƙauƙautawa suka juya Ganin sun juyu ne yasa Buhari ya sa ki wani shu'umin murmushi, ya ɗan ƙara gudun motar ya isa gaban su ya na ta murmushi kamar wani zautatace. Da mamaki suke kallonsa, Fatima ce ta yi karafin halin cewa..... "Malam lafiya? Kana ta yi mana hon kamar wanda akai ma sata ko ka ke bi bashi?" Wannan karan kam dariya yayi yace "haba Malama ni ba wani abu nazo wajanku ba face alkairi." Rabi'a tunda su ka yi ido huɗu da wannan mutumin taji bai ma kwanta mata ba kuma yanda yake ta wani abu kamar baida kamin kai Fatima tace "to lafiya?" Murmushi yayi yace "Da za ku zo na sauke ku a gida ai da yafi kunga sai muyi maganar da za mu yi a mota." Sai lokacin Rabi'a ta yi magana tace "mun gode, bama buƙata." Wani munahikin kallo ya bita dashi kafin yace "dan Allah ina son magana da ke." Fatima tace " ai ka san ba'a nan ya kamata ka tare mu." Daga nan kuma ta kama hannun Rabi'a suka yi tafiyar su Kai tsaye gidansu Fatima suka wace. saida suka huta san nan suka shiga firar wannan mutumin da suka haɗa da shi a hanya Rabi'a tace " ni fa wallahi wannan mutumin bai yi min ba baki ga wani kallo da yake min ba?" Fatima tace " na ga kawai kalar ƴan iskan nan ne." Rabi'a tace " Allah kasa kada yaje gidanmu dan na san idan yaje shikenan tafaru ta ƙare wai an yi ma mai dame ɗaya sata." Fatima tace " In sha Allah bai taɓa zuwa gida ba dan nasan a halin da ake yanzu idan ya je babu wani bincike zasu iya amincewa dashi." Kuka Rabi'a ta fashe da shi tace " Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm ni kam wace kalar rayuwa nike ne nagaji Fatima na gaji zan kashe kaina." Fatima ta wanke fuskar ta da mari hakan bai mata ba sai da ƙara mata wani marin cikin kuka take cewa " Ashe ba ki yarda ƙaddara ba? ashe baki yadda da duk wani abu da yake samunki rubuttace ne, komai da kika gani alƙalamin kaddararki ya riga ya zana maki shi koma dole sai ya faru dan Allah ki dai na wannan maganar kin manta mai ya rabani da mijina abin sona rashin haihuwa ne fa rashin haihuwa da aure duk ɗaya ne basu da wata mara ba, Nakan daura komai akan mizani ƙaddara na yarda da dukan abinda yasa me ni ko zai same ni rubuttancan al'amari ne daga wurin mahalacina, wani bai isa ya goge min kamar yanda ban iya yi ma kaina ba, Da zan iya a wannan lokacin da na ba ma kaina haihuwa." Ta idasa maganar tana fashewa da kuka Ita kan ta Rabi'a a wannan lokacin kukan ta ƙara ma fitur Maganganun Fatima sun taɓa ta sun tuna mata abubuwa da dama da ta manta dasu maganar Fatima ta yi mata wani kalar duka duka bana wasa ba tabbas tasan Fatima nada zurfin cikin da ba kowa take faɗa ma damuwar da ba Rabi'a kaɗai take iya faɗa ma damuwar ta kuma ganin itama Rabi'ar na cikin damuwa yasa ta dai na faɗa mata wani abun saboda bata son ta ƙara mata wani damuwar bayan

Chapter 2 of 7