Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
warda take ciki Rungume Fatima Rabi'a tayi cikin kuka tace " kiyi haƙuri na yarda da dukan ƙaddarata zan dauke ta duk yanda tazo min wannan Jarabtata ce da Allah ya ƙaddara min, kiyi haƙuri Fatima Na tada maki da wani ciwo da kika manta." Ƙara rungume ta Fatima tayi tace " nima dan Allah kiyi haƙuri da marin da nayi maki raina ne ya ɓaci, kuma maganar da kikayi bata dace ba dan Allah kada ki ƙara wannan tunanin idan kika mutu ban san yanda zan yi ba ban san yanda rayuwata zata yi ba." *Yaya Ahmad* Bayan ya koma gida faɗa sosai yayi Fiddausi akan abin da ta yi kuna ya nuna mata kan wannan abin zata iya rasa auren ta domin yana son ƴan uwan shi *Fiddausi* Sanin halin mijin ta yasa ta dauka laifin ta ta bashi haƙuri amma badan zata gyara bane ba sai dan a zauna lafiya a wannan lokacin *Buhari* Da wani mayen kallo ya bisu har suka ɓaci ma ganin shi Abinda yasa bai takura ya bisu ba bari yayi sai da daddare sai ya shirya da abokin shi Aminu Hakan yasa ya koma wajan abokin shiya ya faɗa mashi yanda sukayi Aminu yace " ni fa wallahi da ka bar ta kawai." Buhari yace " bazan barta ba Allah da na ɗanɗani zumarta kuma ba zan nuna mata kai tsaye ba sai mun ɗau lokaci kuma bazan nuna mata wani abu ba." Aminu shida kawai hakan nan yaji yana tausayin ta amma kuma yasan halin abokin nashi. *Rabi'a* Bayan sun gama kukan su ta koma gida tana zuwa gidan ta isar masu da tsakon gaisuwar da yaya Ahmad ya bata saƙo Abinda ya ɓata mata rai bai wuce yanda umma ta wulaƙanta ta ta ba a gaban ƙawayen ta ba tana mata rashin mutumci Haka nan sai ta tinci kanta da Addu'ar Allah ya kawo mutumin ɗazo duk yanda halin sa yake zata jure zata yadda da shi ta huta da wannan wulaƙancin da ake mata ( Hummm Rabi'a kenan da kin san abin da wannan mutumin yake tafe dashi da bakiyi wannan tuna nin ba da kin san wata bahaguwar rayuwa da zaki shi haɗuwar ki da wannan mutumin da bakiyi wannan tunanin ba wata bahaguwar ƙaddara ƙaddara da zata sauya tafiyar komai) JARABTATA https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://www.arewabooks.com/chapter?id=68f9f2ac0b67675ed115f6c9 https://www.wattpad.com/user/hiameera43?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*💪✍️ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️ *"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"*💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) *لا إلهَ إلا الله وَحدَهُ لا شَريكَ لَهُ، لَهُ المُلكُ ولَهُ الحَمدُ، وهُوَ عَلى كُلِّ شَيءٍ قَدِيرٌ* JARBATATA writing by princess Chaptar 6 *Rabi'a* Ɗakin Mama ta shiga ta faɗa mata saƙon ita ma, san nan ta koma Ɗakinsu Amira ta gani zaune akan gado hankalinta na kan waya, sai da ta taɓa ta san nan Amira ta ɗago tana kallon Rabi'a ta ce " yaya tun ɗazu na dawo aka ce min baki dawo daga gidan Yaya Ahmad ba." Rabi'a ta yi murmushi tana jin son Amira na ƙara shiga zuciyarta Kafin ta ce " mun ɗan jima da dawo wa muna gidan su Fatima." Amira ta ce " shi ya sa na jiki shuru." Rabi'a ta yi murmushi tana tunanin ko dai ta faɗa ma Amira abin da ya faru *Fatima* Bayan tafiyar Rabi'a kuka ta ƙara fashe wa dashi ita dai tana mugun son Rabi'a kamar ciki daya suka fito shi ya sa ba ta son damuwar Rabi'a ko kaɗan Duk yanda taso ta ɓoye damuwar ta abin ya faskara, sai da Ammi ta fahimci ta na cikin damuwa, koda ta tambayeta abin da ya faro Nisawa Ammi ta yi ta ce " gaskiya Rabi'a tana cikin wani halin, ban san mene matsalar iyayen ta ba, Addu'a kawai zamu tai maka mata.,, Fatima ta ce " wallahi Ammi nima abin yana bani mamaki, kamar a fime ko littafi.,, *Rabi'a* Haka nan ta ji ta na son ta faɗa ma Amira abin da ya faru haɗuwar su da wannan mutumin Amira ganin kamar da magana a bakin Rabi'a ya sa ta ce "yaya naga kamar da magana a bakin ki?,, Rabi'a ita fa tana mamakin kalar fahimtar da Amira ta yi mata ita ta na ganin ko mahaifiyar da ta haife su ba ta kai amira sanin halin ta ba Murmushi ta yi ta ce "tabbas akwai magana amma ke bansan yanda za ki dauke ta ba." Murmushi amira ta yi tace "ina jin ki yaya Allah ya sa alkairi ne." Babu ɓata lokaci ta kwashe komai da ya faru akan hanyar su ta dawo daga gidan yaya Ahmad da kuma abinda ya faru a gidan da kuma abinda Umma ta yi mata a gaban ƙawayenta Numfasawa Amira ta yi ta ce "gaskiya Aunty Fiddausi bata kyutawa akan abin da ta ke yi maki, Allah ya saka ma yaya Ahmad da alkairi da ya nuna mata kina da mahimmanci a wajan shi.,, Rabi'a ta ce "gaskiya ni kuma banji daɗi ba marin da yayi mata saboda ni." Amira ta ce "share ta kawai ai maganin ta kenan." Sannan kuma ta ce "ita kuma Umma abinda ta ke yi bata kyutawa ita tana mantawa da tana da yara a gidan wani san nan kuma ga yara a gabanta.,, Rabi'a tace "Allah dai ya kyuta, ni bani ji haushin ta ba, uwata ma da ta kawoni duniya ta yi min, kin ga bai kamata naji haushin ta ba." Amira a wannan lokacin zuciyar ta ta kare ta ce "ni ina baki shawara akan wannan mutumin, idan har yazo idan da gaske yake kawai ki yarda, saboda ina son ki huta, Kinga yanzu daga ni sai A'isha sai ke, yanzu nida A'isha an kusa bikin mu kinga kawai ki amince sai abi da addu'a Allah ya shiga lamarin ki." Rabi'a ta amsa da amin kafin ta ce "Ni fa wallahi Amira mutumin ne bai min ba, San nan ya cika kallo ni kwata kwata zuciyata bata kwanta da shi ba." Amira tace "a wannan halin da kike ciki bai kamata ki yi kalar wannan maganar, ba addu'a kawai zamuyi, san nan kuma kin san in dai ya zo gidan nan shi ke nan." Rabi'a tace "in sha Allah zan yi koƙari, Amma rayuwata na cikin hatsari." Amira ta dafa ƙafadar ta tace "kada ki tsare yaya Rabi'atu kada ki sare." Dariya Rabi'a ta yi jin sunan da Amira ta Kira ta yau Amira tace "Zan je gidan yaya Hadiza ne, zan gaida ta bata da lafiya kuma na san ke ba zuwa zaki yi ba, tunda ba kwayin shiri." Rabi'a ta ce "Allah ya bata lafiya kin san ko da naje wulaƙanci za su ta yi min." Amira tace "shikenan Zan ce kina gaida ta." Da misalin ƙarfe 05:30pm *Bashir* Wani waje ne mai kama da hotel, da al'ama ma dai hotel ne room 06 Aminu ne zaune a bakin gado ya na kallon yanda Bashir yake ta shirya, wa kamar wani ango Aminu yace " Allah ya shirya ka sai wani shiri kake kamar angon gaske." Hararar shi Bashir yayi ya ce " kaga Malam babu ruwan ka dani, kai dai kawai na baka kuɗi ko, tunda na baka kuɗi ka fita hidi mata, da na samu biyan ɓuƙata ta zan bar garin nan." Aminu yace "Allah dai ya biya, wallahi ina jiye maka wani abu, dan Allah abokin na ka dai na ɓata yaran mutune, kada ka manta wata rana zakayi aure, kuma zaka haihuwa baka tunanin ayi ma yaran ka kalar abin da kake yi ma yaran wasu?" Tsawa Bashir ya daka ma Aminu yace "koma dai meye, babu ruwan ka rayuwa ta ce ba ta taka ba dan Allah tashi ka bani waje, ni bana san wannan wa'azin naka." Aminu kam da yayi zuciya ya fita daga wajan baki ɗaya *Fatima* Tafiya take da ka ganta kasan ta gaji da al'ama daga wani waje take dan ga kaya a hannunta Tazo zata tsallka titi wata mota ta kusa bige ta har sai da ta faɗi Da sauri mutumin da ke cikin mota ya fito yana faɗi "Subuhanal fatan babu abin da ya same ki?" Fatima kai ta ɗaga mashi alamar babu wani abu ta tashi Ganin zata tafi yace "dan Allah hau na kai ki gida." Fatima tace "a'a ka barshi a ba kusa isa." Yace "to dan Allah ki taimaka min da numbern ko." Babu musu ta bashi yace "in Sha Allah zai zo gaida ta, ya duba jikin ta." Murmushi Fatima ta yi tace "babu komai." Ta kama hanyar zuwa gida shi kuma Alhaji Abdullah ya koma motarsa yana murmushi shi har ya Allah kallo ɗaya yayi ma Fatima yaji ta kwanta mashi Lokaci ɗaya yaji ya kamu da son ta indai zata amince zai aure ta bada daɗe wa ba (Tofah🙃waye wannan alhaji Abdullahi su fati ti an samu shiga) *08:15pm* "Assalamu alaikum." Umma dake waje ta amsa da "Wa'alaikum salam, waye?" Wanda yayi sallamar yace "wai ance ana sallama da Rabi'a." Sakan ɗaya biyu uku Mutanan gidan ne suka fito su duka suna mamakin wai Rabi'a ake nema abin da ba'a taɓa ba Mama ce ta yi ƙarfin halin cewa " je kace waje." Bayan fitar yaron sai gashi ya dawo wai Bashir ne Babu binciken ko waye haka suka tasa ta a gaba Ta fita Wannan fitar tata itace sular buɗe mata wani sabon shafin littafin ƙaddarata wata kalar ƙaddara murɗaɗiyar ƙaddara ƙaddarar da babu wanda ya isa ya tsayar da afkuwar ta ƙaddarar da zata kai kowa ga dana sani Dama tana daga cikin ɗakin ta hijab ɗin ta ta dauka har ƙasa ta fita Jingine jikin motarsa ta ganshi kuma tana kallon shi ta gane mutumin ɗazu ne mai shigen kallon nan Da sallama ta ƙarsa wajan amma kuma kallon da yake Bin ta da shi ya hana shi amsa sallamar Sai da ta ƙara yi san nan ya amsa Bayan ya amsa kai tsaye tace "Malam lafiya mai ya kawo ka?" Wani kallo yayi mata kafin ya ce "haka ake tarbar baƙo an kin san babu abinda zai kawo ni wajan ki in ba so ba." Dam dam zuciyar ta ta buga wai so ita fa bata jin akwai wanda zai so ta saboda Allah anya wannan mutumin ba da yaudara ta zo ba amma kuma da take ba ta san gaibu ba yasa ta yi shuru tana kallon shi Ganin tana kallon shi yasa yace "mu shiga daga cikin mota ko." Gaban ta ne yayi wani mungun bugu ta ce "a'a mu yi maganar anan ai ba wani abu bane." Ganin baya son ta gane da wani abu a tare da shi yasa ya bita a hankali har su kayi sallama ya amsa numbern wayarta Ya kama hanya ita kuma ta shiga gida tana shiga Mama ta ce "waye?" Rabi'a ta ce "wani ne wai Bashir yana so na." A haɗe ta yi masu maganar yanda za su gane kuma su fahimta tabbas sun fahimta Kuma a cikin su babu wanda bai yi shuru na kusan mintuna ba Yaya Hadiza da ta zo tare da amira tana jiran mijin ta ya zo ya dauke ta wata kalar buɗe ta fa yi tana cewa " ashe ba ɓakar ƙafa gare ki ba yo ai nayi tunanin baƙin jini gare ki? Kuma na ji ance yazo da wata kafirar mota ko?" Ita dai Rabi'a bata masu komai ba dan ita kaɗai tasan abinda takeji a zuciyar ta Daƙin ta ta shige Amira tabi bayan ta Duk mutanan gidan babu wanda ya tambayeta mutumin banza ne kona kirki duk da dai yau ce haɗuwar su ta farko Amma ai zaka iya fahimtar halin mutum a haɗuwar farko Tana shiga ɗakin su kan katifar ta ta zauna tayi shuru Amira ta matsa kusa ta ita ta ce " ya ku kayi da shi?" Numfashi Rabi'a ta sauke kafin ta faɗa mata yanda su kayi Kuma kafin Rabi'a ta ce wani abu aka aiko kiran ta inji Baba Sai da zuciyar ta ta buga kafin ta dauka hijabin ta da ta cire ta maida A ɗakin shi ta same shi har ƙasa ta duƙa ta gaidashi Ga mamakin ta sai ta ga ya amsa mata fuska a sake Yace "na ji ance kin yi baƙo?" Ƙasa ta yi da kanta kafin tace "eh Baba." Baba na washe hakura yace "to ma sha Allah ki banu numbern wayarsa nasan ya baki." Wayar ta ta Ɗauka ta ba ma Baba numbern Baba yace "tashi kije Allah yayi maki albarka." A mugun sukwane ta juyu tana kallon Baba Shi Kam ba ma ta ita yake ba Albarka wai yau itace mahaifinta yake saka mata albarka anya kuwa ba mafarki take ba kai gaskiya wannan yafi kama da mafarki sai da ta mari fuskar ta ta tabbatar da ba mafarki take ba harda su tunƙuli Wasu zafafan hawaye ne suka zubu mata daga idanuwanta Sai da ta fita daga ɗakin ta zauna a wani ɗan waje da yake kowa yana ɗakin shi Kuka ta fashe da shi tana cewa "yau ni Baba yasa ma Albarka? In dai saboda zuwan wannan mutumin ne na samu albarka daga wagan mahaifina zanyi haƙuri da shi duk yanda yake in dai zai aure ni koda yana yankan naman jiki na nayi alƙawarin zan zauna da shi ashe ni ma inada yance haka ashe ni ma zan samu ƴanci haka?" Ji tai an dafa kafaɗarta ɗagowa tayi dan ganin waye Amira c ta gani ita ma tana hawaye Ita fa ba ta san duk maganar da ta keyi a fili ta ke yin ta ba Hannun ta Amira ta kama zuwa ɗakin su A'isha na ganin sun shigo Rabi'a na kuka ita kuma Amira na hawaye ta tashi tace "nikam naga ikon Allah ka kan na miye? ai na yi tunanin kukan ya kare." *Fatima* Kasuwa ta je yi masu siyaiya a hanyar ta ta dawo wane tana tafiya tana tunani har ba san san da aka kusa bige ta ba Tana zaune shuru tana tunani wayar ta tayi ƙara ganin baƙuwar numbern ne yasaka ta ɗaga Da Sallama daga cikin sanyin Muryar aka amsa mata sallamar ko ba'a faɗa mata ba tasan mutumin ɗazo ne *JARABTATA* writing by princess {16:57pm} Monday, November 2025 https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U .https://www.arewabooks.com/chapter?id=68f9f2ac0b67675ed115f6c9 https://www.wattpad.com/user/hiameera43?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*💪✍️ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.Mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"*💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) *ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA YA CE AKWAI WATA TSOKA A JIKIM MUTUM, IDAN TA GYARU DUKKA JIKI YA GYARU IDAN TA ƁACI KUMA DUKKAN JIKI KI YA ƁACI BA KOMAI BA CE SAI ZUCIYA ZUCIYA, YA ALLAH KA TSARKAKE MANA ZUCIYAR MU* Chaptar 7 *Fatima* Bayan am amsa sallamar ta yi shuru, ta na sauraren abin da za'a ce daga ɗayan bangaren, Ta yi tunanin ko ba'a ji ne ya sa ƙara cewa "Assalamu alaikum." Daga ɗayan bangaren aka amsa da "Wa'alaikum salamu warahamatullahi wabarakatuhu, amincin Allah ya tabbata a gare ki." Fatima a zuciyar ta ta ce, Tofa wa ta sabuwa kuma Amsa wa ta yi da "ta re da kai." Murmushi Alhaji Abdullahi ya yi ya ce "Allah ya sa kin gane mai magana?" Duk da ta dauka muryar shi ta ce "A'a bangane mai magana ba." Da ga ɗaya bangaren ya ce "Kin manta? Ɗazu na kusa bige ki da mota." Fatima ta ce "Oh nage." "To ya kika je gida?" "Alhamdulilah." "Ya sunan ki?" "Fatima." "Ma sha Allah, ka ce mai babban suna ce." Fatima ta ce "Ummm." Ya ce "Abinda za ki ce kenan ma? Ni baki tambaya sunana ba." Fatima ta ce "To ya sunan ka?" Murmushi ya yi wanda har taji shi cikin kunan ta ya ce "Sunana Abdullahi, ni ɗan kasuwane ina da yara uku, amma Allah ya yi ma mahaifiyar su rasuwa." Fatima ta ce "Allah sarki, Allah ya jiƙan ta." Da "Amin." Ya amsa, kafin ya ce " Tunda na ganki na ji na samu matar aure, zaki aure ni?" Sakan ɗaya biyu uku *Rabi'a* Jin abinda A'isha ta ce ya sa ta yi shuru Amira ce ta ce "Kukan ubanki ake yi, wai ke baki da hankali ko A'isha?To wallahi ki bi komai a sannu." Baki A'isha ta turu ta ce "Wai ke Yaya Amira komai ki ce za kiyi ma mutum faɗa to ai gaskiya na faɗa." Murmushi Rabi'a ta yi ta ce "Ta ta ki A'isha ba kukan wani abu ni ke ba, kukan farin ciki ni ke yi." Aisha ta ce "Ai dole za ki yi kukan farin ciki, ni dama can Ina son ki maganar da ƙawaye da mutane kiyi ne a kan ki shi ya sa ni ke ma ki wani abun, amma yanzu na dai na." Murmushi Rabi'a ta yi kawai Amira ta maka ma ta harara ta ce "Dalla Malama fita ki ba mutane waje." Rabi'a bayan A'isha ta fita wanka ta shi ga bayan ta fito ta shafa mai ta kalle Amira ta ce "zo ki raka ni gidan su Fatima." Amira ta ce "Allah sarki Fatima, baiwar Allah wallahi itama ta na bani tausayi." Murmushi Rabi'a ta yi ta ce "Ai Fatima ta na da kirki." Amira ta dauka hijabin ta suka fita zuwa gidan su Fatima *Bashir* Ko da ya shiga motar shi bai ta fi ba sai da yaga Rabi'a ta shiga gida san nan ya yi ma motar shi key ya bar wajan yana tafiya yana murmushi Wayar sa ya dauka ya kira Aminu sai da ya yi kira uku bai ɗaga ba, Ya san Aminu fushe ya yi da shi dole zai je ya bashi haƙuri Kai tsaye gidan Aminu ya wuce, da yake Aminu yana da aure harda ma yara biyu Bayan ya isa gidan mai gadin gidan ya sa ya yi mai sallama da Aminu, Bayan Aminu ya fito ya ce "Lafiya?" Murmushi Bashir ya yi ya ce "kayi haƙuri mutumi na, nasan na ɓata ma ka rai." Fuska Aminu ya ƙara haɗewa ya ce "Ai wallahi ban ji daɗin abin da kai min ba dan bazan ɓoye maka ba." Bashir ya ce " shi ke nan dai komai ya wuce." Aminu ya ce "Ai da bai wuce ba da bazan kula ka ba" Bashir ya ce " Na gode, tunda dai ka hakuri." Aminu ya ce "to ka je wajan tan?" Bashir ya ce "yanzu haka ma daga can nike." Aminu ya ce "to ya ku ka yi?" Bashir ya faɗa ma shi yanda suka yi da Rabi'a Aminu ya ce "To Allah ya kyuta." *Fatima* Wayar kawai ta kashe domin ba ta da amsar da zata bashi to mai ma za ta ce ma shi, Bata san manufar shi akan ta ba, bata sani ba ko shima kamar sauran yake ne tana cikin wannan tunanin su Rabi'a su ka yi sallama Da murmushi Fatima ta amsa sallamar ta yi masu iso zuwa ɗaki Bayan sun gama gaisa Fatima ta ce "Yau kune da daddare?" Amira ta ce "Wallahi kam Yaya ce ta ce na rakota." Rabi'a ta ce "labari ne nazo maki da shi." Fatima ta ce "kice na ƙara kunnunuwa na su zama uku." Su duka suka kwashe da dariya Dama Fatima ta na da barkwananci ta na da wasa da dariya wasu abubuwan ne suka chanza ta ƙaddarar ta ta taka rawar gani wagan sauya ta Rabi'a ta ce "In faɗa maki wannan mutumin ya zo." Idanu Fatima ta zaro ta ce "Wai da gaske?" Rabi'a ta ce "Allah kam." Nan ta kwashe duk abin da ya faru ta faɗa ma Fatima ta ce "Ba wai ƙaddararmu ce kawai a haka ba, rayuwar mu ce wata kila idan mu ka yi hakuri zamu iya cin nasara nan ga ba." Furucin Fatima ba ƙaramin sanya ya masu jiki ya yi ba Nan Fatima ta ke basu labari haduwar su da Alhaji Abdullahi da kuma wayar da suka yi Rabi'a ta ce "In faɗa maki gaskiya Fatima?" Fatima ta ce "Eh ina ji." Rabi'a ta ce "in dai da gaske ya ke, kawa ki amince." Fatima ta kalle Rabi'a ta ce "kina tunanin zan iya yin aure na bar ki." Amira ta ce "Ka da kice haka Sis kowa da kalar tashi ƙaddarar dan Allah kada kiyi wasa da damar da Allah ya baki." Fatima ta yi murmushi kawai Rabi'a ta ce "Dan Allah ba san ni ba in dai da gaske kike ki amince mu sha biki." Amira ta ce "Ni fa yanzu damuwa ta bansan mai Baba zai ce ma wannan mutumin ba." Rabi'a ta ce "Ni wallahi ban ma sa ma kaina damuwa saboda na san komai zai iya faruwa tunda kin ga yanda mutunan gidan suka gaji da ni." Fatima ta ce "Wallahi ko ni wani lokacin idan ina tunanin sai na dinga ganin rashin kyutawar iyayenmu, saboda wannan abin Jarbata ce mai ya sa suka kasa fahimtar jarabtarki ce a haka." Murmushi Rabi'a ta yi ta ce " A wasu lokutan mutanan da muke masu kallon bango, ko majinginar rayuwar mu, suna iya zama sune masu nisantar mu, mutanan da bamu san su ba, sai su iya zamar mana bango kuma majingina" Dan Allah "Amira ki daina wannan tunanin ni wallahi ban taɓa ganin laifin iyayen mu ba." Amira ta share hawayen ta ta ce " Dole zan yi magana mana, mutanan da ya

Chapter 3 of 7