Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
laifin ki ba." Duk wannan abun da suke Rabi'a na jin su domin tun shigowar Mama ta farka daga baccin da take yi Jin abun da Mama ta ke faɗa ya sa Rabi'a ta saki hannun Fatima take hanunta cikin rawar murya ta ce "Ma...ma...k...e.ce..ki...ke maga..na..ha...ka..ke...ce...ki ke ..ku..ka ..a kaina." Ta fisgi maganar da wani mugun karfe *Alhaji Abdullahi* Ta address ɗin da Fatima ta tura ma shi ne har ya yi nasarar zuwa gidan su Fatiam, Koda ya isa gidan a ƙofar gidan ya tsaya ya na kiran wayar ta sai da ya yi kira uku kafin aka ɗaga, a mai makon ya ji muryar sahibar ta shi sai ya ji muryar tsuhuwa tana ma shi sallama amsawa ya yi Kafin ya tambaya ina Fatima Ammi ta ce "ka shigo da ga ciki." Da sallama ya shiga cikin gidan Ammi ta tarbe shi cikin mutumci tai mashi iso zuwa falo Fita ta yi sai gata ta dawo hannunta dauke da ƙaton tire dauke da kuloli guda biyu a kai sai ruwan ruba harda lemun fanta Ta kawo ta ajiye gaban shi bayan sun ƙara gaisawa Ammi ta ce "gashi kazo Fatima kuma ta na asibiti kawarta bata da lafiya." Alhaji Abdullahi ya ce "Subhanallah Allah ya ba ta lafiya." Ammi ta amsa da "amin." Shurune ya biyo baya kafin Ammi ta ce "Fatima ta yi min bayanin haɗuwar ku, kuma ta ce ka kira ta kasan za ku yi magana, ga shi bata nan sai dai ko asibitin zaka je." Murmushi ya yi kafin ya ce " idan babu damuwa Mama Ina son Fatima ne kuma zan aure ta." Ammi wani kalar farin ciki ne ya ziyarce ta tabbas duk inda mutumin kirki ya ke da ka ganshi za ka fahimta shi mutumin kirki ne Ammi ta ce "ma sha Allah, amma ka san Fatima bazawara ce, ta taɓa yin aure saboda batq haihuwa ba ya sa suka rabu da mijin." Alhaji Abdullahi ya ce " Ni babu wa ta matsala indai za ta soni ina da yara guda uku, Allah ya yi ma mahaifiyar su rasuwa wajan haihuwar karamar yarinya ta." Ammi ta ce "Allah ya jiƙan ta ya yi ma ta rahama, ya albarkaci abin da ta bari." Sosai ya ji daɗin Addu'ar Ammi kafin ya amsa da "Amin ya Allah." Ammi ta ce "to kai ɗan ina ne?" Alhaji Abdullahi ya ce " Asalina ni ɗan Malumfashi ne dake jihar Katsina, sunan mahaifina Umar, kuma mahaifina babban Malami ne a jihar ta Katsina kuma babban ɗan katsuwa muna da yawa a wajan iyayenmu, nine na biyun ƙashe, na yi karatun islamiya na yi saukar Alqur'ani, sannan ina da ilimin boka daidai gorgodo, ni babban ɗan kasuwa ne anan jihar Katsina da kewayen ta harma wasu garuruwan amma ina zaune da yarana a nan garin Katsina." Ammi ta ce "ma sha Allah, Allah ya yi albarka." Ya ce "Amin ya Allah." Ya ce "Tom yanzu, wajan wa zanje neman aure ta." Ammi ta ce " akwai yaya mahaifinta, wajan shi za ka je, kafin nan ka fa ra magana da Fatimar, aji ta bakinta." Murmushi ya yi ya ce " in Sha Allah yanzu wani asibiti ne?" Ammi ta faɗa ma shi sunan abibitin ganin baici abincin ba ya sa Ammi ta ce "ya baka ci abincin ba?" Murmushi ya yi ya ce "zanci ne." Ammi ta ce "to ai naga kamar za ka tafine." Zama ya yi ya ci shinka da miyar da ta kawo ma shi, sosai abincin ya yi ma shi daɗi, bayan ya gama ci ya ajiye ma ta kuɗi ma su yawa akan zaije asibin su yi magana da Fatima Sosai Ammi ta ji daɗi tai ta saka ma shi albarka *Asibiti* Umma da shigowar ta kenan ta ji maganar Rabi'a sosai jikin ta ya yi san yi Sosai Su kaita bama Rabi'a hakuri da kuma yi ma ta alƙawarin baza su ƙara ta kura ma ta ba kuma zasu tsaya ma ta tsayin daka akan komai *Bashir* Bayan fitar sa kai tsaye gidan Aminu ya nufa, bayan sun gaisa da Aminu ya ke faɗa ma shi yanda su ka yi da Baban Rabi'a Shi dai Aminu baice komai sai cewa ya yi Allah yasa alkairi Kuma daga nan ya nemi Aminu ya raka shi Aminu ya ce "yana da wani aiki ya samu wani ya raka shi." Aminu ba dan komai ya ƙi raka Bashir ba, bazai iya ba ace ya na ji ya na gani a haɗa kai da shi a yaudara mutane Bashir wani abokinshi ya kira Kabir Amma bai faɗa ma Kabir manufar sa akan Rabi'a ba kai tsaye gidan su Rabi'a suka nufa Sai da suka isa ƙofar gidan san nan ya kira Baba ya faɗa ma shi suna kofar gida Baba ya ce " Ai basa gida suna asibiti Rabi'a ce bata lafiya, ta samu rauni." Cikin tsantsar iya duniyan ce ya ce "Subhanallah mai ya sa me?" Baba ya ce " ta faɗi ne, ta ɗan samu rauni a kai." Bashir ya ce " ayya Allah ya bata lafiya." Baba ya amsa da amin Bashi ya ce "ga shi nan yanzu zai zo asibitin." *Asibiti* Yanzu duk kukan da suke yi ya lafa suna zaune Umma ta je gida ta kawo masu abinci Abba Isma'il ne ya shigo ya kalle Rabi'a cike da tausaya wa ya ce "ya jikin?" Ta ce "da sauki sosai." Abba Isma'il ya ce "Alhamdulilah, Allah ya ƙara lafiya." Da Amin suka amsa Ya ce "zan je gida zuwa anjima zan dawo." Sallama ya yi ya fice *{Assalamu alaikum dan Allah kuyi haƙuri Abba Isma'il zance ba Usman ba dan Allah ayi min uzuri kunsan abun ne sai hankali na gode sosai}* Waya Fatima ce ta yi Ringing ganin mai kiran ya sa ta ma tuna da ya ce zai zo gida Ɗagawa ta yi bayan sun gaida ya ce " ga ni nan a asibitin" Fatima ta yi mamaki amma sai ta ɓoye mamakin ta Fita ta yi can ta hango shi cikin motar sa, ba ta san mai ya sa ta kasa ɗauke idon ta a kansa shi ba Ganin kamar zai kama ta tana kallon shi ya sa ta saurin kawar da kanta gefe Fitowa ya yi yana kulle motar gaisheshi ta yi san nan ya ce "ya mai jikin?" Fatima ta ce " taji sauƙi Alhamdulilah." Alhaji Abdullahi ya ce "ma sha Allah, zamu yi magana ne kafin na shiga na gaida ta ko mu gama maganar." Fatima ta ce "mu shiga ku gaisa." Ledar hannun shi ya bata ya ce "gashi ta bama mara lafiyar." Amsa ta yi tai ma shi godiya ta na gaba ya na baya har suka shiga ɗakin cikin mutumci suka gaisa da Alhaji Abdullahi san nan ya fita Fatima ta kusa fita Rabi'a ta kira ta dawo wa ta yi kusa da ita ta ce "Gani lafiya?" Rabi'a ta ce "dan Allah ki amince ma shi Fatima." Shuru Fatima ta yi Rabi'a ta ce "dan Allah Mama, kisa baki Fatiam ta amince da shi wallahi auren ta zaiyi." Ita ma Mama baki ta sa akan Fatima ta amince JARABTATA writing by Fatima Bintu hussain 12:56pm Wed,dec 3 https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*💪✍️ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️ *"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"*💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) 🌹﷽🌹 🌹🌹 *📿اَللّٰھُمَّ صَــّلِ عَلٰی مُحَمَّدٍ وَّعَلٰٓی اٰلِ مُحَمَّدٍ کَمَا صَلَّیْتَ عَلٰٓی اِبْرَاھِیْمَ وَعَلٰٓی اٰلِ اِبْرَاھِیْمَ اِنَّکَ حَمِیْدٌ مَّجِیْدٌ-*🌹🌹 🌹🌹 *اَللّٰھُمَّ بَارِکْ عَلٰی مُحَمَّدٍ وَّعَلٰٓی اٰلِ مُحَمَّدٍ کَمَا بَارَکْتَ عَلٰٓی اِبْرَاھِیْمَ وَعَلٰٓی اٰلِ اِبْرَاھِیْمَ اِنَّکَ حَمِیْدٌ مَّجِیْدٌ.📿*🌹🌹 Chapter 11 *Fatima* Sanda ta fita lokacin Alhaji Abdullahi har ya kai ba kin motar shi Bayan Fatima ta isa ya ce "Ko za ta shiga cikin mota sai mu yi maganar a ciki." Fatima ta ce " A'a a sai na shiga ba, muyi maganar mu anan." Sosai Fatima ta ƙara shiga ransa kuma hakan da ta yi ya ƙara tabbatar ma sa da tarbiyarta A jikin motar suka tsaya babu ɓata lokaci ya sanar ma ta da abin da ke ransa da kuma yanda su kayi da Ammi Shuru Fatima ta yi tana tunani kafin ta ce " Allah ya zaɓa mana abin da yafi alkairi." Sosai farin ciki ya kama sa ya ce " Alhamdulilah, tunda kin amince, yanzu zanyi magana da magaba ta na su nai ma min auren ki." Ita dai Fatima bata ce komai Sallama ya yi ma ta ya ta fi ya na farin ciki ya na jin ya fi kowa farin ciki a yau ɗin nan *Bashi* Sanda yaje asibiti lokacin su Baba Ismail sun tafi Baba ne ya yi masa iso suka shiga asibitin sai da suka je ɗakin da Rabi'a ta ke lokacin da suka shiga bacci ya dauke ta Bayan sun fito daga ɗakin Baba babu tambayar asalinsa babu komai haka ya ba shi dama akam ya aiko da magabatan shi a yi maganar aure Sosai Bashir ya nuna farin cikinsa a gaban Baba Amma Allah kaɗa ya san abin da ke zuciyar sa *Bayan kwana uku* An sallami Rabi'a daga asibiti in da aka saka ma ta dokoki da yawa Ga kuma hawan jini da take fama da shi amma yanzu Alhamdulilah sosai jikinta ya yi kyau, Ta samu sauƙin aiki sosai kusan duk wani aiki mutanan gidan ke yi, ga wa kulawa da take samu daga wajan Mama ita abin ma har mamaki ya ke ba ta, yanzu damuwarta ɗaya auren da Baba zai mata wanda kai tsaye za'a za ta kira shi da auren dole, amma babu yanda zata Wannan ɗin ya na cikin ƙaddararta da bata isa ta kuce ma ta ba ya na cikin ƙaddarar ta da alƙalimi ya zana ma ta dole dole saita faru babu wanda ya isa ya hana ta faruwa Idan ta tuna yau aka kawo kuɗin aurenta da wannan mutumin ita kaɗai tasan abin da take ji ita kanta baza ta ce ga abin da take ji ba Kuma abin da ya daure ma ta kai bai wuce yanda wasu yan unguwarsu ke magana akan ta ba, wasu na ce wa dana lokacine bai yi ba, wasu kuma na cewa ai ta tsaya ruwan ido ne, Kuma babban abin da ya ƙara jawo maganar bai wuce itama Fatima da aka sa ranar aurenta da Alhaji Abdullahi ba ansaka sati biyu kacal To wannan abin ta sa ake magana *Fatima* A kwanaki ukun da suka wuce ne Alhaji Abdullahi ya aika magabatansa Daga kai kuɗin sa rana suka haɗa harda sadakinta da lefi Sosai abin ya bata mamaki kuma har yanzu baza ta ce ga abin da take ji a kan sa ba *Bashir* Sosai ya ji daɗin jin an saka bikin Fatima dan da wannan damar zai samu ya ci ma burin sa Dan haka tun yanzu ya kamata ya fara shirin sa Idan ya tuna yanda ya samo iyayen ƙarya, ya tura su gidan su Rabi'a sai ya yi murmushi kawai kuma abin na bashi mamaki yanda komai ya tafiyar masa cikin sauƙi Kwanci tashi asarar mai rai yau sauran kwana biyu bikin Fatima wanda na Rabi'a da Amira ya kama sauran wata ɗaya sosai sukeyin shirin biki Babu abinda za suyi walima kawai za suyi washe garin biki akai amarya ɗakin ta Ta bangaren Rabi'a da Bashir kuna ba'a cewa komai domin ita Rabi'a bata shi ta ke ba shi kuma ya takura ma rayuwarta *Yaya Ahmad* Sosai yaji daɗi bikin su Rabi'a da za'a yi ya yi farin ciki sosai inda ya dauka nauyin komai a kan shi Har Fatima ma shi ya dauka ɗawainiyar duk wani abu ya ce ita ma ƙanwarsa ce dan haka dole ya yi ma ta hidima kuma duk abin da yai ma ta bai faɗi ba Fiddausi yanzu duk ta fidda wani haukan kishi dake dawainiya a kanta dan ta tabbatar da Rabi'a baza ta aure ma ta miji ba Rana na bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya a yau asahar aka daura auren Fatima sa Alhaji Abdullahi Aure ne wanda ya tara jama'a abinka da babban mutum Tunda aka daura auren Fatima da Rabi'a ke ta kuka kamar ba gobe kuka irin wanda za'a rabu da juna kuka suke sosai kuwa na jin kamar idan suka rabu baza su sake haduwa ba Washe garin biki Anyi walima anci an sha inda aka kai amarya ɗakin ta gida ne babban gida komai ya ji sai a ce {Allah ya basu zaman lafiya} Sanda Rabi'a zata tafi wani saban shafin kukan suka buɗe suna ganin kamar da wannan rabuwar da za suyi ita ce ta karshe Da kyar aka raba su Rabi'a bayan sun koma gida bacci ya kaurace ma idon ta ta kasa rubtsawa tana tunanin abubuwa da yawa ta na ji a ranta kamar a kwai wani abu mai girma da ƙaddarar ta ta zana ma ta kuma wannan abin ya ba gaf da faruwa Wannan ranar dai bata runtsa ba *Bashir* Ya gama tsara komai yanda zai ta fi daidai Wanka ya shiga bayan wasu ƴan mintoci ya fito ya yi ƴan shafe shafe shi san nan ya shirya cikin wani yadi Black calor sosai ya yi ma shi kyau wayar sa ya dauka ya kira Baba Ya sanar ma sa akan zai zo ya dauka Rabi'a ya kaita ta wajan mahaifiyar sa ya na son zasu gaisa Shi kam Baba bai kawo komai a ransa ba ya amince ma shi ya ce sai ya zo Bayan sun gama wayar cikin farin ciki Bashir ya dauka keyn motar sa ya fita Rabi'a Tunda ta tashi ta rasa mai yake damunta ta ta shi babu walwala a tare da ita wanda hakan ya sa har sai da aka fahimci halin da take ciki Amma sai umma ta ce kewar Fatima ce kawai ke damunta ita ma Rabi'ar kan ta baza ta ce ga abinda ke damunta ba Tana zaune ta yi shuru bayan amira ta ta fi aikin ta wayar ta ce ta yi ƙara ganin Baba ne ke kiran ta ya sa gaban ta ya yi mummunar faɗuwa amma haka ta yi shahada ta ɗaga Bayan sun gaida Baba ya yi ma ta magana cikin umarni ya c ta shirya Bashir zai zo ya dauke ta zasu je gaida mahaifiyar shi Babu yanda zata yi da Baba haka ta amsa shi kan dole jiki a sanyaye ta je ta faɗa ma Mama ita mama sai da ta ji faɗuwar gaba amma ta ce babu komai ta je Haka ta koma ɗakin ta ta shirya cikin wata abaya red calor ta yi ma ta kyau sosai Kuma ba ta daɗe da gama shiryawa ba kiran Bashir ya shigo wayar ta bayan ta ɗaga ya sanar ma ta da yana waje ya na jiran ta Sosai jikin ta ya yi wani kalar sanyi Sallana ta yi ma mana da umma ta fita Wannan fitar tata itace zata jaifata wani hali wannan fitar ta ta itace sular haɗuwarta da wata mummunar ƙaddara wannan fitar ta ta ita ce zata ɓata komai wannan fitar ta ta ita ce zata kai ta ga wani ma ta ki wannan fitar ta ta itace itace itace😭😭😭😭😭 A cikin motar shi ta iske shi Ya na hangota ya buɗe ma ta gidan gaba yana jifarta da wani kalar kallo Gaishesa ta yi bayan ya amsa ya yi ma motar key Wani tamfatsetsen gida ya nufa da ita babu abinda gaban ta keyi sai faɗuwa yanda gaban ta je faɗuwa haka ta ke addu'a Bayan sun isa gidan a falo ya yi ma ta masuki Ya shiga wani waje wanda ya yi kama da kicin lemu ya dau ko ma ta da ruwa ya ce ta sha zai haura sama ya kira maman sa Sama ya hau ita kuma ta ɗauka lemun ta zuba a cup ta sha Bashi dama ba wata mamars da zai kira ganin ta sha lemun ne ya sa wata dariya ta kusa kufce masa ganin abinda ya sa a ciki ya fara aikin sa ya da ya sauko ƙasa ya yi wajan Rabi'a ta ɓata ya yi amma ganin kamar bata numfashi ya sa ya saki wata munahikar dariya A wannan lokacin mai afkuwa ta afku a wannan lokaci komai ya faru a wannan lokacin a wannan lokacin ƙaddarar su ta sauya Bayan wani lokaci Hankalin Bashir a mugun tashe ya fito daga wani ɗaki ya na zufa ya ma rasa mai zai yi Wani tunani ne ya zo ma shi wa ta jaka ya dauka ya kai motar sa san nan ya dauka Rabi'a ya saka ta a motar ya bar gidan da ita *Fatiam* Sunan zaune ita da yaran Alhaji Abdullahi da shi suna cin abinci a wani mugun sauri ta tashi ta na dafe kirginta Su duka da kallo suka bita Alhaji Abdullahi ya ce "lafiya?" Cikin ta shin hankali ta fashe da kuka ta ce"wallahi wani abu yana faruwa da Rabi'a ta wallahi Rabi'a ta na cikin wani hali." Shima Alhaji Abdullahi sosai hankalinsa ya tashi dan da daddare ma haka zai ta mafarkai cikin bacci ta na kiran Rabi'a *Bashir* Bayan ya kai ta asbitin ya bama wata likita kuɗi masu yawa yace ya na zuwa wannan fitar da ya yi ya bar garin baki ɗaya Ya kasa gane kanshi tunda ya keta ma Rabi'a haddi wani abu ya tokare masa zuciya yana ji kamar ya yi kuskure amma zuciyarsa ta hana sa fuskantar haka *Gidan su Rabi'a* Sosai hankalin su ya tashi ganin har kusan ƙarfe tara bata dawo ba gashi ana ta kiran wayar ta baya shiga Har numbern Bashir suka kira shima baya shiga Koda aka yi ma Baba magana sai ya ce ai su ba yara bane ba ɓacewa zasu yi ba Sosai hakan ya ɓata ma Mama rai haka dai suka kwanda amma wasu daga cikin su ba suyi bacci ba Babu abin da take yi sai sallah, sallah kawai ta keyi ta na miƙa ma Allah kukan ta a haka wani bacci ya yi gaba da ita wani mafarki ta yi mai tada hankali wanda ya yi sanadiyar tashin ta babu shiri Amira Kam Babu abinda takeyi sai kuka da addu'a gabanta faɗuwa kawai yake *Fatima* Sosai ta birkice ma Alhaji Abdullahi sai da yai ta ma ta addu'a kafin aka samu sauƙi bacci ya dauke ta Shi kansa jikin sa ya yi wani kalar sanyi ya na addu'ar Allah ya sa ba wani abune ya faru da Rabi'a ba *Asibiti* Sosai Dr hauwa ta shiga tashin hankali ganin kalar barnar da aka yi ma baiwar Allah Sosai ta sha wahala wajan taimaka ma ta zuwa asuba Rabi'a ta farka Sosai Dr hauwa ta yi farin ciki nan take tambayar ta ina mijinta ya nufa wani kalar kuka Rabi'a ta fashe da shi Hakan da ta yi ya nuna ma Dr hauwa cewa akwai matsala kenan Sosai ta bata tausayi ta lalaɓa ta har ta bata labarinta sosai Dr hauwa ta yi kuka ta tausaya ma Rabi'a Ita kuma kalar ta ta ƙaddarar ke nan Sosai Dr hauwa ta yi ma ta nasiha akan yadda da ƙaddara Numbern Amira ta Bama Dr hauwa ta ce ta kira ma ta ita Amira bayan ta gama sallah tana karatun Alqur'ani wayar ta ta yi ƙara dubawa ta yi ganin baƙuwar numbern ya sa ta ɗaga Sallama ta yi bayan an amsa Dr hauwa ta tambaye ta ko ita ce Amira Amira ta amsa da ita ce Dr hauwa ta ce " ki zo asibiti, Rabi'a ce babu lafiya." Hankalin Amira tashe ta nufe ɗakin Mama JARABTATA writing by Fatima Bintu hussain https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ems_copy_t 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*💪✍️ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️ *"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!"*💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) *HIKIMA ZINARIYA* Watarana wani ya je wajan Hassanul Basry yace Ya Abu Abdullah nazo fatawane. Yarinyata ce mutane suke neman auranta, amma wa ya dace na aura ma ta? Hassanul Basry yace: "Wanda yake tsoron Allah! Idan yaƙaunace ta zai mutunta ta, idan ya ƙyamace ta ba zai zalince ta ba". YA ALLAH KABAMU IKON AIKI DA WANNAN NASIHAR Chaptar 11 *Amira* Babu ko sallama ta faɗa ɗakin Mama, Mama na ganin ta hankalin ta yaƙara tashi zuciyar ta tayi wani kalar bugu, da sauri ta kama Amira Mama ta ce " Lafiya? Mai ya faru?" Cikin fitar haiyaci ta ce " wallahi ta na asibiti." Hankalin Mama ya ƙara ta shi ta ce " waye? ki faɗamin." "Yaya Rabi'a, yanzu likita ta kira ni." Cikin tashin hankali Mama ta shiga mai mai ta "Inalilllahi waina ilaihi ra'ji unm, Allahum ajarna fi masibatina, wa'akalif ni kharan minha, Iailahaila anta subuhanaka inni kuntu Minal zalimin." Haka tai ta maimaitawa bama ta san nasa amira ta fita daga ɗakin ba Amira ta na fita ɗakin mama kai tsaye ɗakin su ta koma ta dauka kuɗi ta fita ko gaban ta ma bata kalla, Allah ya taimake ta ta sami mashing ta hau Saboda bata cikin haiyacinta ta ma kasa gane kai asibitin sai ta dauka wayarta ta kira numbern da aka kira ta da ita, ajiyar zuciya ta sauke jin anɗaga kiran, ta sanar ma likitan da iso, likitar ta fito ta shiga da ita Tun daga baƙin ƙofa ta kura ma Rabi'a kallo ganin wata kalar rama da ta yi ta lokaci ɗaya wani tunani ne ya zo mata zuciya ai kam wani wahalalin kuka ta saka wanda ya yai sanadiyar tashin Rabi'a dake bacci Rabi'a na buɗe ido suka yi ido huɗu da Amira wani kalar kuka ta saki mai cin rai Amira da mugun gudu ta isa gare ta ta rungume ta cikin kuka Rabi'a ke cewa "ki gode ma Allah amira rayuwar ki ta yi kyau, nikam a lokacin da nike ganin tawa ƘADDARA ta ƙare, ashe ba haka bane, ashe akwai wata ƘADDARAR da alƙami ya rubutamin ita, wanda dole sai ta faru kamar yanda alƙalami ya zana min, Amira Ina

Chapter 5 of 7