An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
JARABTATA
https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U
https://www.arewabooks.com/chapter?id=68f9f2ac0b67675ed115f6c9
https://www.wattpad.com/user/hiameera43?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
By princess
*A wasu lokutan kaddara na faruwa a yadda ta so ba ayyada ɗan adam yaso ba, a waɗansu lokutan kuma takan farune a yadda muka so, kuma mukan sowa kanmu abu ya kasance ba alkairi bane a garemu, sannan mukan ƙi abu ya kasance shine mafi alkari garemu, kamar de kullum Allah na nasa bawama na nasa, amma na Allah shine gaskiya, kuma hakane zai kasance, uwa ta haifi yarinya amma saboda Allah ya jarabce ta uwa ta guji ɗiyar ta ku biyo ni domin jin me zai faru a wannan littafin jarbtata.*
> Wannan littafin ƙirƙiraran labari ne idan yayi kama da rayuwar wani ayi haƙuri a rashin sani ne.
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai godiya su tabbata ga Annabi mu Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam_
Chaptar 1
Dare ne sosai a lokacin da duk wani mai rai yake hutawa domin samun salama.
Amma a wannan lokacin ita ta hana kanta bacci bama wannan ne karo na farko ba a kusan ko wani dare ba ta iya bacci ƴan da take ganin rana haka take ganin tare,
Kamar ko wani dare wannan ma haka ya kasan ce tana akan darduma tana mai miƙa kukan ta ga Allah,
Kusan tama kasa cewa komai sai nishi da take yi sai kuma kuka da ta keyi da kyar ta samu ta finciko magana daga ji ta fara fita haiyacin ta ne,
“ Ya Allah kaine ka jarrabci ni..... Ya Allah kaba ni ikon cinye jarrabawata..... Ya Allah kasan halin da zuciya ta take ciki.....Ya Allah ina neman gafarar ka idan wani laifi nayi maka ka jarbbcine Ya Allah ka yafe min....ga baiwarka nan da ƙoƙan barar ta ya Allah ka duba ......ina zan saka rayuwa ta iyaye na na tsangwamata.....ƴan uwana na tsangwamata.....mutanan waje na tsangwamata.....babu inda zan sa ka raina naji daɗi rana zafi inuwa ƙuna.” haka take ta Addu'a daga baya kuma ta fashe da kuka mai tsuma rai kuma mai ratsa zuciyar mai sauraro kuka kalar wanda rayuwa tayi ma zafi kuka kalar wanda baka da mai lalashi.
Cikin wa'inda suke a kwance a ɗakin ne wata ta farka da al'ama duk abinda ta ke yi tana jinta cikin tausayin ƴar uwar ta kuma Yayar ta ta sauko daga kan katifar ta ta zo gaban ta ta duƙa ta zuba mata idanu tana kallon ta kallo ne mai cike da abubuwa da yawa..... kallone mai ciki da tausayi.... kallo ne na kalar wanda zuciyar shi ta kare....kallo ne na karya alƙawari.
Ganin kallon da ƙanwar ta kamata wardda a wajan ta ne kawai take samun kulawa....a wajan tane take samun farin ciki.....itace suke raba damuwar ta zata iya rantsawa da Allah tafi iyayen ta da kowa na ta....
Da sauri ta fara share hawayen ta ta ce "ki yi haƙuri ƴar uwata, na kasa tsaida kuka na na rasa ƴanda zanyi da damuwata?"
Murmushi mai cewa Amira ta yi ta ce "amma mai nace maki? A kullum ina son ki cire damuwar kowa a ranki Allah yana tare da ke kuka ki cire damuwar Mama a ranki dan Allah Adda."
Cikin sanyin jiki ta ce "kin sani ina ƙoƙarin sosai wajan ganin na inganta rayuwa ta amma kuma ƙaddara ta riga fata Allah ya daura min jarrabawar da banzan iya gujemata ba ina koƙari Sosai wajan ganin na cire damuwata."
Amira tace "in sha Allah komai zai wuce ɗan Adam baya kauce ma jarbtar shi, mutane na mantawa da aure haihuwa mutuwa duk lokaci gare su idan lokacin su yayi sai dole sai sun faru, ƴan zu idan auren kika yi kika fito aita magana idan kinyi auren baka haihu ba baka tsira ba idan baka yi auren ba ai ta yawo da kai anace kana da baƙin jini, dan Allah Adda kibar wannan damuwar a ƴanzu kina da shikara arba'in babu aure ni banga abin damuwa ba wasu har su mutu Allah bai ƙaddara masu zasuyi aure ba."
Tabbas ta ji sanyi a ranta kuma ta ɗan ji sauƙin damuwar ta murmushi tayi tace "shikenan Amira in Sha Allah zan daina sama kaina damuwa.
Ta nan zaune ta kasa komawa bacci har lokacin sallar asuba tayi kuma tana sallar bata tsaya komai ba tafi ta wajan ta fara aikin gida abin kari ta fara daurawa sanan ta fara share share tana yi tana tunanin da tasa ba yi,
Haka ta gama sharar ta taje ta tada ƴan ƙanan ƙan nan ta tayi masu wanka ta shirya su zuwa makaranta duk wannan aikin da take yi babu wanda zai yi mata sannu sai mutum ɗaya Amira ita ce ke taya ta aiki tun lokacin da Baba ya mai fa komai na gidan kan Amirar ma Baba yace idan ya kara ganin tana taya ta wani abun bai yafe mata ba.
Bayan ta gama shirya yaran ta tasa su gaba zata rakasu makaranta tun da tafito ake nuna ta wasu na kallon ta suna maganganu wasu kuma na zaginta haka ta raka yaran har makaranta ta dawo tana kan hanyar ta ta zuwa gidan ne wasu mata sun taho suna nuna ta wata ke cewa ai naji ana cewa bin maza takeyi shiyasa taƙi aurewa wasu kuma na cewa cikin shige ta yi magan ganu dai da yawa na yawo akan ta mutum ma ya rasa wanne zai dauka.
Wannan maganan tasu ta tada mata hankali wanda ba ta san lokacin da ta fashe da kuka a wajan ba sai kuwa aka maida ta abin kallo yara suka zagaye ta kamar wata mahaukaciya.
Tana cikin kukan nan taji an kama ta cikin faɗa faɗa! take cewa "haba Rabi'a a tunaniny lokacin kuka ya wucey shikara nawa ana yiy maki wannan abin amma kin kasa iya jurewa."
Ba kowa ke wannan maganar ba Fatima ce ƙawar ta bayan Amira ta kaɗai ce mai sauraren damuwar ta,
Shuru ta yi ba ta ce komai Fatima ta kama mata hannu zuwa gida suna tafiya tana tausarh zuciyar ta tare sayi mata nasiha mai ratsa zuciya,
Fatima ƙawar Rabi'a ce tun suna yara Fatima tayi aure tana da yara uku ƙaddara ta faɗa mata suka rabu da mijin ta shine take zaune a gidan su....
Suna shiga gidan suka iske Mama a tsakar gida ganin halin da Rabi'a take ciki bai tada mata hankali ba hassali ma babu al'amun damuwa a tare da ita kalar ta mahaifita,
Maganar Mama ce ta saukar masu a kunne wanda sukan su basu damu ba saboda sun saba jin maganganun ta amma na yau sun tsaya mata a rai,
"Tunda wannan rayuwar kika zaɓar ma kanki....a dole kowa ya tsane ki.... dole kowa ya dinga kyamar ki....mutum niyar banza da wufi haka zaki ƙare shaha kawai duk ƴan uwanki sunyi aure kan nan kima harda masu yara biyar a ciki amma ki kina nan zaune muna haɗa kafaɗa wallahi na baki nan da wata biyar ki fitar da miji idan ba haka ba wallahi zan bar Malam yayi duk hukun cin da yaga dama a akan ki ,
Itama Rabi'a cikin tsanin ɓacin rai tafara magana tana cewa " Haba Mama miye laifi na a ciki?dan banyi aure ba na zama abin ƙyama agun kowa..... Mama banyi tunanin kina cikin masu ƙara min damuwa ba kama ta yayi ace kina kan gaba wajan kawar min da damuwa ta amma kullum kece ma kike ƙara min anya ke kika haifi ne?ina mamaki ace uwa ta dauka cikin wata tara ta raine shi wata ashin da huɗu amma ace ta manta da wannan wahalar ko zafin haihuwa ta da kikaji yakama ta ki tausaya min so kuke na mutu na huta kilan Allah bai ƙaddara min aure a rayuwata ba kilan kuma zanyi lokaci ne baiyi ba dan Allah Mama idan kin gaji da nine ki faɗa min idan kuma ba kice mahaifiyata ba ki faɗa min."
Wai saukar maruka taji wanda saida taga gifcin taurari ba kowa ne yayi mata wannan marin ba sai Mama itace ta mari ta mari Kuma ba ɗaya abin bai tsaya a mari sai da ta samu abin duka ta fara dukan ta....
*Godiya ta musamman ga Yayan mu Yusuf gumal*
*Tare da Minal saeed*
*Bilkisu Garba mai agogo*
*Mrs Auwal*
_Allah Ubangiji ya saka maku da alkairi Allah ya cire ma kowa damuwar shi haƙika da shawarwan ku na fara rubuta wannan littafin Allah ya bamu ladar abin da zan rubuta baki ɗaya ya yafe mana kurakuran dake ciki._
JARABTATA
https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U
https://www.arewabooks.com/chapter?id=68f9f2ac0b67675ed115f6c9
https://www.wattpad.com/user/hiameera43?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
JARBATATA
Writing by princess
*🟢 Waye a online?*
*Allah ya tsare ka da imani da lafiya ya baka farin ciki mara iyaka yacika rayuwarka da Albarka kuma ya haɗaka da Aljanna Firdaus tare da waɗanda Allah ya yi wa ni’ima...🤲🏼*
Chaptar 2
Duk wannan dukan da Mama take mata ku kusa batayi kuka ba bata taɓa tunanin tana da ƙarfin zuciya haka ba,
Mama dan kanta ta gaji da dukan ta ta bar ta,
Amira na shirin fita tayi wanka zata saka kaya taji kamar ƙaran abu kamar ana duka abu cikin sauri ta saka haka hijab tafita waje abin da ta gani ne yayi mugun tada mata hankali,
Rabi'a ce kwance a ƙasa ita ba kuka take ba ita ba bacci take ba idan ba gizo idan ta ke mata ba kamar murmushi taga tana yi kuma ga Fatima zaune kusa ta ita tana ta mata magana amma kamar ma bada ita take ba,
Amira tazu ta ɗurƙusa a gaban ta tana kallon ta kallo na rashin fahimta kallo na mamaki domin idan kaga Rabi'a na wannan murmushin to tabbas tana cikin wani yanayi tana cikin matsananciyar damuwa warda take ɓuƙatar kulawar mahaifiya,
Amira tace ma Fatima "Dan Allah kamata mu shiga ciki."
Babu musu Fatima ta kamata zuwa ɗaki suna zuwa Amira ta kamata ta kwantar da ita kan gado ganin sawon duka jikin ta harda rauni yasa ranta yayi mugun ɓace,
Amira tace "inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm Allahuma Ajirna fi masibati na wa akalafi ni kharan minha ya Allah ga baiwar ka nan yanzu dan Allah Mama ce tayi mata wannan dukan? anya kama Mamace ta haife ta? A ƴanzu Adda ta wuce duka shikara Arba'in amma ace ana dukan ta ya Allah ka kawo ƙarshen komai komai ya wuce."tana cikin Addu'ar wani matsanancin kuka ya ƙuɓuce mata.
Fita tayi ba'a daɗe ta dawo dauke da ruwa a bokiti tahaɗa mata ruwan ta kamata ta rakata bayi tayi wanka ta fito sannan ta gasa mata jikin ta da ruwan zafi ta haɗa mata shayi mai zafi domin tasha amma ta kasa sha haka suka taƙuramata ta sha tana gama sha ta fara ƴin amai dole suka bar ta haka,
Suna cikin jimami da tausayin da kowa ita yake kallo ko ma kowa da abinda yake tunani a ranshi,
Umma ce ta shigo ɗakin Umma kishiyar Mama ce kuma suna zaman lafiya da Mama amma kuma Mama ce ta bada umarnin duk wani aiki na gidan na Rabi'a ne duk kuwa ciwon da takeyi,
Umma na shigowa ta kalle tace "ki tashi ga wanki can kiyi sauri ki gama kuma da kingama zaki zafi gidan Ahmed ki gyara shi dan ya kusa dawo wa."
Wani kallo Fatima da Amira suke binta kallo na rashin imani kallo na rashin tausayi,
Cikin dakiya Amira tace "hada Umma dan Allah ku tausaya mata bakiga halin da take ciki ba dan Allah kiyi haƙuri ta samu sauƙin jikin ta sai tayi duk abinda kuke so."
Wani wawan kallo Umma tayi ma Amira tace "Zaki rufamin baki ko saina ɓata maki rai."
"Ke kuma maza tashi kiyi abinda na saki."
Amira zatayi magana "Rabi'a ta rufe mata baƙi tace "dan Allah kada kiyi magana kada ki damu ni ƴanzu komai ya bimin jiki idan banyi aikin ba bana jin daɗi so kar ki damu."
Umma tace "ai dole zakice haka sha shar banza kawai ƴar iska."
Wasu zafafan hawaye suka zubu ma Fatima tana kallon Rabi'a har ta fita,
Waban wanki ne wanda ko inji yayi shi albarka amma haka ake so tayi shi da hannu kuma akwai washing machine a gidan ba babu ba amma saboda zalinci sai ace da hannu ake so tayi,
Ga famfo a gidan amma kuma da ruwan rijiya ake son ta wanke haka ta fara tara ruwa a rijirar gidan kafin ta fara wankin,
Amira ganin ko ta zauna a gidan ɓakin ciki zai ta kwasa hakan yasa ya shirya ta fita zuwa aikin ta a wani asibiti take aiki likitace,
Rabi'a tana cikin wankin lokacin ɗaura abincin rana yayi ta ajiye wankin ta tafi ta daura abinci tanayin girki tana wanki a haka harta gama abinci ta zuba ma kowa nata ita bama tabi ta kanta ba ta koma ta cigaba da wankin ta,
Ba ita ta gama wankin ba sai bayan sallar la'asar ta gama sannan ta samu taci abinci tayi wanka ta Shira zuwa gidan yaya Ahmad,
Mama ce zaune a ɗakin Baba suna fira cikin firar ne take faɗa mashi lokacin da tasa ma Rabi'a idan bata fidda mijin aure ba zuwa lokacin ya yanke duk hukuncin da yaga dama,
Baba yace "ni kaina wannan abin ya bani mamaki na rasa wani iskanci ne yake damun wannan yarinyar wallahi idan bata fidda miji ba zuwa lokacin zan haɗa ta da duk wanda yayi min ko kuma tabar min gida."
A tunanina Mama zata tada hankalin ta ko ta shiga damuwa ko ta nuna rashin jin daɗi akan abinda za'ayi ma ɗiyar ta amma kuma bata damuba,
Mama tace "ai duk hukuncin da ka yanke dai-dai ne tunda bata jin magana tasa anata zagin mu a gari."
Baba yace "idan ta dawo ki turamin ita naji Sahura tace taji zatayi gyaran gidan Ahmad."
Mama tace "taje zatayi mashi gyran gida ita ko kunya ma bata na rasa wata kalar zuciya gare ta duk wasu samari nata na korar ta tun suna zuwa da arziƙi har suka daina zuwa."
Baba yace "yace ai wallahi Bama kamar ni anya kuwa Rabi'a jini nace?"
{Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm wannan wace kalar rayuwa ce wai uban da ya haife ka yake wannan tunanin a kan ka}
Rabi'a tafiya ce me nisa tsakanin gidan su dana Yaya Ahmad haka take tafiyar cikin gajiya har ta isa gidan gida ne babba tana zuwa babu ɓata lokaci ta fara gyaran gidan har akayi mangari ba ganin isha'i ta taho yasa ta bar aikin akan gobe zata koma ga wani ciwon kai da take fama da shi ga kuma wani zazzaɓi kuma haka ta fito daga gidan tana tafiya tana hutawa har ta iso zuwa gidan su,
A gaye ta iso gidan ga ciwon kai haka ta iso tana zuwa ta shiga ɗaki wanka tayi sannan ta samu magani wajan amira ta sha bata dade da kwanciya ba wani yaro ya shigo babu ko girmamawa cikin rashin tarbiya yace "Rabi'a wai Tace kifito kiyi mana wankin makaranta."
Cikin rashin jin daɗi haka ta tashi ta fito zuwa waje Amira na kallon ta ta rasa mai zatace sai dai kawai ta bita da kallo ta girgiza kai,
Rabi'a na fita ta ga wankin da zatayi wankin babu laifi haka ta haɗa tayi ta shanya sannan ta samu hutu sanda ta koma ɗakin duk sun kwanta sai Amira take jiran ta,
Murmushi Rabi'a tayi tace "Bakiyi bacci ba?"
Amira tace "kin san bazan iya ba sai naga kin shigo ciki."
Wasu kwallane suka cika mata ita kam wace kalar soyayya ke tsakanin ta da amira?
Amira ganin tana kamar kwalla a idon ta ta girgiza mata kai san nan tace" bana son kukan nan Ina son ki zama jaruma ƴanzu da na tafi nasan babu mai tausayin ki sai Allah wallahi ina tausayin ki kece babba a cikin mu mata amma ke Allah ya jarabta."
Share hawayen ta tayi tace "babu ƴanda iya nayi maki alƙawarin zan jure komai har zuwa lokacin da Allah zai bani ikon cinye jarabtata."
Amira tace "shikenan ƴanzu mu kwanta kinga dare nayi."
Babu musu suka kwanta amma ita bacci ya kasa zuwa ta tafi tunanin rayuwar su ta baya tana iran ƴanda suke cike da ƙaunar juna kalar ƴanda suke girmama ta amma ƴanzu komai ya wuce komai ya zama tarihi.
Wacece Rabi'a
Asalin su
Asalin su ƴan garin funtuwa ne dake jihar Katsina,
Sunan mahaifinsu malam Musa Malam Musa su huɗu ne a wajan iyayen su akwai babban su Abubakar sai Isma'il sai shi da yaci suna Musa sai autan su Umar sun taso cikin soyayya da kula iyayen su nada hali babu laifi kuma suna da ilimin addini dai-dai gwargwado,
Sunan mahaifin su Malam Musa Ahmad mutum ne me ilimi da son mutane,
Matan shi biyu da Abu da kuma asabe suna babu ruwan su suna da son mutane kuma basayin faɗa sai kayi tunanin yaya da ƙanwane,
Abu itace Babba ɗan ta na far ko shine Abubakar tun daga shi bata ƙara haihuwa ba dan har sun fidda rai suka fauwala ma ubangiji komai a lokacin da suka fidda rai da ƙara samun haihuwa sun sakan kan ce baza su ƙara haihuwa ba a lokacin ne Allah ya ni'imtasu da ƙara samu ɗa wanda yaci suna Isma'il,
Bayan wasu shikaru Ahmadu ya nuna yana son zai ƙara aure abu bata hana shi ba saboda tasan mijin ta yana son ta,
Wata mata ce da mijin ta ya rasu kuma bata taɓa haihuwa ba ya aure bayan shekara biyu da aure ta samu ciki ta haifi ɗan ta wanda yaci suna Musa sai kuma bayan su shekaru ta ƙara haihuwa idan ta ƙara santalo namiji yaci suna Umar.
A haka suke zaune cikin kwanciyar hankali da salama har yaran suka fara zuwa makaran ta,
Tun malam Musa yanda shekara hudu aka fara zuwa makarantar islamiya da shi a lokacin yana maida hankali sosai abin kwanin ban sha'awa kowa yan son shi saboda ƙoƙarin da yake da shi yana da shi kara bakwai dai-dai aka kai shi makarantar primary aka saka shi a aji ɗaya Amma kuma bata maida hankali akan bokan shi ga wani rashin ji da yake fama da shi,
Makarantar islamiyar ma ya daina maida hankali saɓanin sauran da suka maida hankali akan kara tun su,
Sanda sukayi saukar Alqur'ani mai girma a lokacin ko talatin bai haɗa ba,
Wannan dalilin yace mahaifin su ya fifita sauran a kanshi dan sai yayi masu abu sai biyar bai mashi sau ɗaya ya rasa mai yake damun Musa tun yana dukan ya gaji sai dai kwai Addu'a yake mashi Allah ya shirya shi,
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda sakanni ke komawa mintuna mintina na komawa awanni awanni na komawa kwanaki kwanaki na komawa satika sarika na komawa watan ni watan ni na komawa shikaru,
A bayan shikara goma sha biyu abubuwa da yawa sun faru da na daɗi da akasin haka a ciki Allah yayi ma Amadu rasuwa,
Sukuma su yaya Abubakar sun gama karatun su suna kasuwanci da gadon da aka raba masu,
Masu kam babu batun karatu tunda ya kai matakin babbar sakandiri abubuwa suka taɓar ɓare domin kam wasu ƴan iskan abokai ya haɗu da su mara sa jin magana su suka koya mashi rashin ji gashi bashida tsoro karshe ma dai barin karatun yayi islamiyar ma tuni ya barta,
Ana haka wasu ƴan garin Kaduna suka dawo funtuwa da zama a nan unguwar su ta jabiri tunda idanuwan sa suka sauka akan Asma'u ɗiyar malam Mamman ya kamu da santa babu ɓata lokaci ya sanar mata da saƙon zuciyar shi ita kuma ta aminci mashi tun suna soyayya a ɓoye har dau aka fara sani daka ƙarshe ya ji yasu su yaya Abubakar akan shi fa aure ake so ayi mashi aure su bashi haƙin shi zai samu muhali yakama kasuwanci,
Yaya Abubakar da yaya Isma'il basu bashi goyan baya saboda suma ba'a daɗe da saka binkin su ba amma kuma ƴanzu ya bijiro da maganar aure haka suka je gida suka tautauna da iyayen su da yake ance abin da babba ya hango yaro ko ya hau kan Tsauni bazai hango haka yasa suka goya mashi baya akan auren domin auren shine samun sauƙi,
Ƴan uwan mahaifin su dasu yaya Abubakar sukaje nema mai auren Asma'u babban farin cikin su bai wuce ƴanda aka amshe su ba hakan na nuna ƴar gidan mutumci ce Allah yasa sanadiyar auren ta ya rage wasu abubuwan,
Ko suka zo suka faɗa mashi ankai kuɗin auren yayi muran sosai kamar ta zuba ruwa a ƙasa yasha haka yaji,
Sukuma