ta ke
yi wa yarinyar, saboda ragowai abincin da te
kawo mata.
Saboda haka Humaida ki kara yin
nazari, wallahi ban dace da ke ba, za ki yi
zaben tumun dare, ina tsoro za ki iya
fuskantar bakin hukunci a gaban Abbanki".
Gabadaya ya gama raunana mata
zuciya tausayinshi ta ke ji.
"Ina kan bakana Mu'allim, ina son
KA AURE NI, zan jure kowane irin
kalubale duk hukuncin da zan fuskanta gaba
zan ci galaba, please hadin kanka kawai na
ke nema".
ko?"
Ta sake dubanshi a raunane.
"Ka sake yin tunani, zan barka a nan
123
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ya kada kai kawai ya fito daga motar,
ya tsaya yana daga mata hannu, har sai da ta
bace wa ganinsa.
*** *** ***
Tun daga soron gidan ya hangi
Umma, yana kokarin sallama ya fasa don jin
abin da ta ke fada da da farko ya tsorata, a
tunaninsa gamo ta yi, saboda jin da ya yi ita
kadai tana magana ba tare da akwai wani ko
wata a tare da ita ba. Ya maida hankalinsa
sosai gare ta, ya kara lafewa a soron.
Tsaye cikin sauya murya.
"Kin yi kyau Umman Mu'allim,
tamkar ba ke ba, kai me za a yi da talauci".
Ta kuma dawo da muryarta na zahiri
tana murmushi ta се.
"Ai muddin Mu'allim na raye ba zan
fidda rai da jin dai ba, dana shi kadai na
mallaka, ga shi ya zame mini tamkar da
goma. Ya dauke min komai".
124
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ta sake sakin murya, ta dauko wata
dinkakkiyar atamfa wadda ke ajiye a kan
kujera.
"Ga wannan ke ma ki sa wa dana
albarka"
Sai kuma ta yi shiru, ta koma ta zauna
ta rafka tagumi, sai ga kwalla. Ta dago kai.
"Zan ga wannan rana Mu'allim ina yi
maka fatan alheri, Ubangiji ya sa in mutu
ina mai farin cikin ka sami sauyin rayuwa".
Da sauri Mu'allim ya koma da baya
gabadaya zuciyarshi ta gama narkewa, a
bayan layinsu ya zauna duk ya gama shiga
damuwa.
Ashe talaucin nan na damun
Ummansa, ashe ita ma na son rayuwa cikin
jin dadi? Bai san sanda ya dauko wayarsa
daga cikin aljihu ba.
Layin Humaida ya shiga lalube, kamar
jira ta ke ringin daya ta dauka.
"Muddin ba za ki sami matsala da
Abbanki ba na zabi ki zama abokiyar
125
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
rayuwata. Ina nufin mu rayu a inwa daya, ki
zamo mata a gare ni, amma sharadi sai
randa na sami akin yi".
Yana ji ta saka karar murna. Da sauri
ya cire wayar a kunne yana murmushi.
Shin son humaida ya ke da gaske ko
kwadayi ne? wani irin farin ciki ya dinga ji
ya mike ya nufo gida.
Tun daga kofar gida ya dinga jin
muryar Malam Musa yana yi wa Umma
tsiya.
"Ai ke kin ji ba ki iya tattali ba, duk
sai kin taru kin kashe kayan, irin wannan in
an samo tattalawa a ke in za a yi biki ko
99 wani fitar sai a yi amfani da su".
Ta dinga dariya.
"Malam tunda na ke da kai ban taba yi
maka kwalliya haka ba, ina son ne ka
tantance da wa ka ke zaune, na hadu ne ko
kuwa?"
Ya kada kai.
126
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Yau kuruciya ta motsa, to ni ma bara
na aje rawanin, ni da na ke zaunc da ke na f
kowa sanin haka. Umman Mu'allim kina da
kyau ko da a cikin tsumma ne ke ba kya
muni, amma da ki ka ce kayan nan ina son
ki dinga amfani da shi in ana wani sha'ani
ne fa da kanki ki ka sanar da ni irin
wulakanci da kyamar da ki ke fuskanta in
kuna wani taro, ko rabar inda ki ke ba a yi,
yanzu ya ki ke ji ke kanki da ki ka fita jiya
cikin kyakkyawar shiga? Ce min fa ki ka yi,
mutane da yawa ba su shaida ki ba".
Ta ce cikin shagwabа6бiyar murya da
ya sa ya dinga jin wani shauki ya dinga jin
shi ma wani ne.
"Ai na sani amma na fi son na yi
maka kwalliya, ka gani ka yaba, ni kuima na
sami lada. Yaushe rabonka da ka yi wata
mu'amala da ni, amma jiya da. na yi
دو kwalliya har...'
Gabadaya suka dinga dariya.
127
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Mu'allim ya yi saurin komawa da
baya yana murmushi da jin kunyar abin da
ya ji suna cewa.
Mu'allim da Humaida sun yi matukar
sakewa da juna, yana matukar sonta
musamman yanzu da ya gama karantar
halayyarta. Tana da son taimako, sam ba ta
da kyasjhi, matsalarta kawai sangarta da
rashin tarbiyya. Wannan kuma ya faru ne
tun daga gidansu, ga wauta sai dai ya
kudurce a ransa zai bi da ita cikin dabara ya
saisaitata yadda ya ke bukata.
Gabadaya ya mance matsalar
mahaifinta, kodayake a kullum tana kokarin
Kwarara masa gwiwa tare da tabbatar masa
da fadin hargagi ya ke nan da lokaci
kankani komai zai daidaita.
Suna zaune a Mr. big, ice cream suke
sha ta dube shi.
"Yau na kusan yin kuka, na zaci ba za
ka zo ba".
128
ん
ni
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ki yi hakuri akwai abin da ya tsare
Та се, "Me ke nan?"
Ya ce, "kin ga ina tashi kafin na fito
sai na dibi kayan Umma da na Abba
99
sa'annan da na kawuna na wanke su
"Wai waye kawun nan?"
"Kawuna yana cikin gidanmu.
"To shi kawun ba shi da 'ya'ya ne?"
Ya kada kai, "Ba shi da kowa bai taba
yin aure ba, ba shi cikin jinsin da ya kamata
ya yi aure, a takaice ba shi da lafiya, ba cin
haka ga shi ba shi da hankali. Kafin ya hadu
da lalurar ba shi da burin da ya wuce ya ga
na zamo wani. Ya yi mini irin abin da uba
na gari ke wa 'ya'yansa. Ina son Kawuna
fiye da kaina, zan iya yin komai domin shi,
zan iya sadaukar da rayuwata don na ga
farin cikinsa"
Ta ajiye ice cream din hannunta.rg
"Ya ya za a yi na san kawunka? Ina so
na ganshi".
129
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
Ya dan yi jum, ta kafe shi da ido cikin
nazarinsa. Ta sanyaya murya.
"Ko ba ka so?"
Ya ce, "Me zai hana?"
"O. K, me zai hana ba za mu je yanzu
ba?"
"Ki bari in sanar a gida ko kin ga in
muka je haka ban yi musu adalci ba".
"Na fahince ka, in kana ganin haka ya
fi shi ke nan, amma ina son ka dauke wa
kanka wannan wahalar gidan, kai namiji ne
irin wannan ayyukan ba su kamace ka ba, in
ka amince min zan kawo wadda za ta dinga
taya Ummanka aiki".
"Ke ba kya taya Ummanki aiki a
gida?"
Ta kalle shi a yatsine.
"Tunda na taso ban taso cikin wahala
ba, ban san ma yadda zan sarrafa hannuna
gurin yin irin wadannan ayyukan ba. Kafin
na tashi daga bacci an kai mini ruwan
wanka. Kafin na fito an gyaran daki an
130
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
dauko kayan da zan sa an ajiye mini a gado,
da na fito za a dinga bin duk inda na taka
ana tsanewa da tawul. Takalmi ma saka mini
a ke yi in har mai madauri ne".
Ya kallo ta cikin murmushi da son ya
zolaye ta, ya nuna ta da yatsa.
"To wannan kwalliyar wa ya ke
miki?"
"Akwai mai zuwa ta yi min".
Zumbur ya ga ta mike cikin duba
agogon da ke daure a tsintsiyar hannunta. Ta
koma ta dafe kai, binta ya ke da kallo kamar
wanda ya ga sabuwar halitta.
"Lokacin baccina ya yi, kaina ya soma
sara mini, na san yanzu Dad zai kira ya ji na
akwanta, ni kuma ba zan yi karya ba zan
gaya masa muna tare, in ya ji ba zai ji dadi
ba, tunda ya shimfida min sharadi kada ka
damu gaf lokacin ya ke da cika... taso mu
tafi".
Kokarin riko hannunsa ta ke, ya basar
a inda ta saba ajiye shi ta tsaya ba tare da ya
131
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
san sun karaso ba, sharadin Dad da ta ce ya
gindaya mata ya ke tunani.
*** *** ***
"Ke ban da abinki Hajara, ai kin san
yaron nan ba zai yi zaben tumun dare ba..."
Ta katse shi, "Malam don ba ka ganta
ba ne, in dai wannan yarinyar ya ke fada ba
zan ba shi goyon baya ba".
"Ko ma ya ta ke shi ya gani ya ce
yana so, in ba za ki fadi alheri ba ki yi
shiru".
Ya maida hankalinsa ga Mu'allim.
"Ni dai abin da na ke so da kai, kada
ka ce za ka tunkari aure yanzu, ka bari sai ka
sami abin yi, yau ka sami abin yi gobe ka zo
mini da maganar aure zan daura maka aure".
Ya dubi Hajara, ta cika tamkar ta
fashe.
"Mu'allim ka ga Umman taka ko?"
132
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Abba abin da Umma ta ke zargi sam
ba haka ba ne, kurum dai yarinyar 'yar masu iko ce".
Da sauri ta dube shi.
"Oh na fahinta, auren kwadayi ka ke
son yi wanda Karshensa nadama ce".
"Yo ke Hajara ban da abinki dana
jarumi ne ba zubin irin wadancan ne da shi
ba, babu laifi idan ya sami abin yi ta
dalilinta wanda na ke yi mishi fata, amma
dai ya kwanta sai an samo za a ba shi shi ne
ban laminta ba. Tashi ka je, Allah ya yi
maka albarka, in ka tashi sai ka kawo ta ta
duba Kawun naka babu laifi".
Ya mike yana shafa keya, gabadaya ji
ya ke Abban nasa na kwarara masa gwiwa a
akan Humaida. Ya bar su Abba na kokarin
kara fahintar da Umma a kan dagewar da ta
yi, da alama ta soma fahintarsa.
*** *** ***
130
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Yana zaune jiran isowarta ya ke yi, sai
dai ya rasa abin da ya sa gabansa ke faduwa,
sam tsintar kansa ya yi da rashin farin ciki.
Zuwanta yana jin wani kunci da tsoro a can
karkashin zuciyarsa, sai dai yana ganin
hakan na da nasaba da yanayin da za ta ga
gidansu, yana jin kamar fargabar hakan ne
ya sa ya ke jin haka. To in haka ne bai
kamata ya ji tsoro ba tunda ta san waye shi.
Hon ta sakar masa, amma da alamun
bai jì ta ba, shin tunanin me ya ke yi? Ta
kashe motar kurum tana kare masa kallo,
gabadaya ya sauya daga yadda ta soma
saninsa. Ya yi kyau har ya gaji, sanye ya
ke da riga shirt ja da bakin wando. A karo
na biyu ta kara sakin wani mahaukacin
hon.
Da sauri ya mike ya nufi gurinta
yana murmushi, ya bude mata motar ta
fito.
134
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
ki".
"Amincin Allah ya tabbata a gare
"Kai ma haka".
Suka doshi kofar gidan gabansa ya
tsananta faduwa, daf da za su shiga gidan
malam Musa ya fito jin karar hon din.
Idanunsa suka hadu da na Humaida,
murmushi bayyane a fuskarta.
"Humaida ga Abbana”. Ya fada yana
kallon Malam Musa.
Ga Ummakinsa lokaci guda ya ga
yanayinsa ya sauya, jikinsa na wani irin
tsuma, ya fidda hannu da kyar yana nuna
ta da yatsa.
"Wace ce wannan?"
"Ita... it... it... itta се".
Ya fada cikin rawar murya.
"Na ce ita ce wa?" Ya tambaya cikin
muryar tsawa.
"Wacca na gaya maka".
"Kana nufin wannan се?"
135
KA AURE NH-1 Bilkisu H.Mund
Ita kanta Humaisa ta gama firgita da
yanayinsa, tsintar kanta ta yi da komawa
bayan Mu'allim. Yana huci ya ce.
"Ban taba tsanarka ba irin yau,
wallahi na yi da na sanin haihuwarka, da
na san za ka hadu da wannan (ya nuna ta
da yatsa) da na kashe ka da hannuna kafin
zuwan wannan ranar. Kaico da kai
Yusufu"
Ya dafe kirji yana tari, da gudu
Mu'allim ya Karasa gare shi zai rike shi, ya
dakatar da shi.
"Kada ka taba ni!" Ya fada yana сі
gaba da tari.
Ya dubi Humaida ya koma ya dubi
Abbansa.
"Abba ka gaya min, na shiga rudu".
Ya sake kallon Humaida da ido fal
kwalla.
"Humaida, Abbana a ina ki ka
sanshi?"
136
KA AURE NI!-1
Muryarta na rawa ta ce.
Bilkisu H.Muhd
"Wallahi ban sanshi ba, ban taba
ganinsa ba, sharri zai yi mini”.
Ya dakatar da ita cikin daga murya.
"Ke! Abbana ne zai yi miki sharri?
Yau kin kara tabbatar mini da cewar ke
mahaukaciya ce, bacin haka zan koma yi
miki kallon dabba"
Ta yi shiru tana dubansa tana son
tuna inda ta sanshi, sai dai iya hangenta ba
ta tuno ba.
"Da gaske na ke yi, me ya sa ba za
ka yarda da ni ba?"
Juyawa Malam Musa ya yi zai shiga
gida, ya yanke jiki ya fadi. Da gudu ya yi
kansa yana kokarin daga shi, cikin yi wa
Humaida tsawa.
"Ki fita ki tafi na сe".
Da gudu ta nufi inda ta yi fakin ta
shiga ta ja motar da karfi a tsorace. Ya
kallo motar yadda ta ke sheka gudu ya
137
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
daga hankalinsa, ya dawo da nutsuwarsa
ga Abbansa ya rike shi suka shige ciki.
*** *** ***
Malam Musa zaune a kan darduma,
Hajara na zaune a gefensa, tunda Mu'allim
ya kawo karfi ba shi da burin da ya wuce
ya ga ya faranta mana, na yi imanin tunda
ka nuna ba ka sonsa da wannan na tabbata
ya barta ke nan".
Ya kada kai cikin raunanniyar
murya.
"Ban ji dadi ba, boyayyar da yaron
nan ke yi mini ya sa na ke burin kullum in
ya zo mini da abu in ba shi goyon baya a
kai, zan iya amincewa da shi a kan duk
abin da ya zo mini da shi, amma ban da
wannan yarinyar, dole ne ya barta muddin
ya amince ni ne ubansa".
Hajara ta sanyaya murya.
138
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Abin ba zai kai ga haka ba, ka
nutsar da zuciyarka, Mu'allim ba zai ba ka
kunya ba, ni na sani. Amma Malam tun
farko sai da na gaya maka cewar
yahrinjyar karuwa ce ba ka yi bincike ba
kawai ka ci gaba da kwarara masa gwiwa".
Ya ce, "Wallahi yadda na ke son
faranta wa yarona rai ko da karuwar ya
dauko muddin yana sonta zan ba shi goyon
baya, saboda yin hakan tamkar jihadi ne
zai zamo ta dalilinsa ta shiryu, shi ya sa ki
ka ga wancan karon ma ban ba ki goyon
baya ba".
"To arama ka sa ni a duhu, me ye
dalilinka na son ya rabu da ita? Ko ban
tambaya ba Mu'allim zai tambaye ka, in
kuma bai ji kwakkwarar hujja ba, zai iya
kafewa".
Ya yi murmushi, "Zan gani kuwa ai
ni ne da shi ba shi ne da ni ba, in har ni ne
139
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
na haife shi dole ya yi yadda na ke so, ba
39
lallai ne sai na gaya masa dalili ba”.
Ya mike ya fita kofar gida, bai dade
da zama ba sai ga Mu'allim, ya yi masa
sannu zai shiga gida ya kira shi.
Ya durkusa cikin girUmmawa.
"Mu'allim zan shaida maka, ina so
ka sani daga yau na tsinke duk wata alakar
da ke tsakaninka da wannan yarinyar".
biyu.
Da sauri ya dube shi, suka yi ido
"Eh haka na ke nufi”.
Ya koma ya maida kai kasa yana son
yin magana, sai dai fuskar Malam ya kasa
barinsa saboda babu annuri ko guda daya a
kan fuskar. Ya mike jiki a sanyaye.
keya.
"Na ga kamar da magana a bakinka".
Ya dawo ya durkusa yana sosa
"Kai na ke sauraro".
Cikin rawar murya ya се.
140
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ka ce in rabu da ita, kuma kai ne ka
Kara karfafa min gwiwa a kanta...
"Yanzu kuma na janye, janyewa ta
har abada". Ya ce da Mu'allim kai tsaye.
"Amma Abba mai ta yi maka, a ina
ka santa?"
Ya auna masa wani mugun kallo,
cike da takaici wai yau shi ne zai kafa wa
dan da ya haifa umarni ya ketare.
Tabdijan! Lallai da sauran rigima.
Mu tara a littafi na biyu, don jin
yadda za ta kasance, tare suke da na dayan.
Mai kaunarku.
Bilkisu H. Muhd.
(By Force)
141
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
DANDANO DAGA
'YAR BABBAN GIDA
Ya kutsa kai dakin da yake jiyo kukanta, ya
hango ta a takure a sakon gado lamarin ya yi matukar
taba masa zuciya musamman da ya yi mata ganin a
hargitse babu gyara. Kwalliyar nan tata mai jan
ra'ayinsa yau kamar ba a taba yin irinta ba a jikin
Sa'adah ba, tun kayan barci ne na daren jiya. Fuskar
nan ta kode ta jeme, idanuwan sun yi luhu-luhu, ga
ruwan hawaye da ya y kaca-kaca a fuskarta, gabadaya
yanayinta ya sauya sai ya ke ganinta kamar ba
Sa'adan tashi ba 'yar kwalisa mai iya daukar kwalliya
da iya zuba dressing irin na daukar hankali ba.
Tausayinta mai yawa ya tsirga masa, tabbas an shiga
babin da zai iya salwantar da rayuwarta, ta sha fada
masa. "Wallahi Mahmood gara na mutu kafin na ga
ranar da za ka yi min kishiya".
"To wai wa ya ja? Ita ce silar komai".
Ya zauna gefenta cikin tattausan lafazi ya ke
magana a gare ta. "Me ya yi zafi har irin. haka
Sa'adah? Ashe ke din ba za ki daure ki zamo jaruma
a cikin mata ba? Yanzu saboda Allah irin wannan da
ki ke yi me sunansa? Wa zai dube ki a yau ya fahinci
ke ce Sa'adahr nan ma'abociyar ado da kyalkyali?
Dube ki yadda ki ka mayar da kanki dalilin wani abu
142
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
da bai taka kara ya karya ba har ki ke neman
sukurkurta kanki, ki ke son ki zamo abar kallo da
nuni a wajen sauran mata...?"
Ya sa hannu ya ke jawo kanta da ta tura
tsakankanin cinyoyinta, ya ke fada mata. "Ki sa
hakuri da juriya a ranki, ki zamo jaruma sai ki ringa
rayuwa shi wannan din wani lamari ne mai girma da
ya zo gare ni daga Ubangiji, ba wai niyyar kaina ba
ne, ko nufin muzanei a gare ki, a'a yi wa lamarin
kallon shirin Allah ne. In ba Allah ba Sa'adah shirin
ya zo daga gare Shi ya ni da na ke da kamar ke zan
jawo wata cikin rayuwarmu? Haba! Haba! Ai wannan
da gani kin san ba yina ba ne, yin Allah ne. saboda
haka maza share hawayenki, ki zamo mai hamdala a
gare Shi, don ba mu sani ba kila wata rahamar ce ya
yi shirin yenta a gare mu, shi ya sa ya aiko da hakan a
gare mu".
Ya sa hannu yana share mata hawayen. Tа
ture hannayensa daga jikinta, ta ke magana a gare shi
da muryarta da ta dushe don azabar kuka. "Babu wani
furucinka da zai yi tasiri a gare ni, domin na riga na
gama fahintar lamarinka game da ni, nid in na zamo
abin ki a gare ka..."
Da sauri ya katse ta. "Wa ya fada miki ke kin
zamo abin ki a gare ni?"
143
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Kai ka tabbatar min da haka tunda har za ka
iya raba soyayyata zuwa ga wani 6angaren". Ya fada
mata cikin lallami. "Ki dauki aurena kaddara
Sa'adah, ba wai wani batu da ke fita a bakinki ba".
Ta juya kafada da girgiza kai ruwan hawayen
na ci gaba da kwaranya daga idanunta, ta ce. "Babu
batun Kaddara a maganar kishiya, ka ci zarafina irin
wannan ks zauna a gabana kana fada min wai
Kaddara? Ina! Wannan sam ba kaddara ba ce, son
zuciya ne kawaj da son muzanci a gare ni".
Ya ce, "To idan ma ba kaddarar ba ce Sa'ada
wa ya ha? Kar ki mance fa komai ya faru ke ce
sanadi, da a ce kina tare da ni a kan kowane ra'ay
nawa kina biyayya a gare ni, da yin rayuwa
kyakkyawa irin ta sauran ma'aurata ta ya za a yi irin
wannan ya faru? Amma ki yi duba ki ga mene ne na
Batanci bai faru daga gare ki zuwa gare n da tallafin
mabaifnki ba..."
Ta katse shi da alama ranta ya kara hauhawa a
Baci. "Na yi maka alkawarin gyara halayena da binka
sau da kafa, da yi maka duk yadda ka ke bukata,
amma kai ma ka yi min alkawarin bayar da saki aa
gare ta tun kafin ta kai ga shigowa cikin gidan nan".
Murjanatu Muhammd Dan-Guru
144
1
du,
OKSHOP
Bayan
Sabon
Gadar
Gari,
194, 0809985IRIO
Kano
nMarubuciyar
FI SONTA? UNACE
СROPASANKAR WABAMBANCI
TARAIRAYA
MATSALAR KAUNA JINI-BIYU
DACEWA
ISAKE
RASHIN RABO
RAKIN KAZAEI KELAR SABO BESTAI KUSKURE
ZAFIN HAWAYENA
ZUMA DA MADACI
KA AURE NI
HARAFI PUBLISHERS
08025433394
Cover graphics: Anka-Graphics 19
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels