lakabi da ta gaban mota.
Matan da za ka nuna su a cikin ko da
Larabawa ne, irin matar da duk lokacin da
ka ke tare da ita za ka ji kanlka ya kumbura,
kanka ya fasu, za ka ji kai wani ne. To in
haka ne me ya sa ba zan amshi tayinta ba?
Saboda ta fi karfinka".
Zuciyarsa ta ba shi amsa, ya yi saurin
bude ido, wani irin sonta mai zafi ya dinga
ratsa ko ina na jikinsa ya dinga murmushi
sai dai a can karkashin zuciyarsa tsoro ya
mamaye shi abin da ya ji kirjinsa na yi ba
abu ne mai sauki ba, ya ya zai yi?
Tsintar kansa ya yi da wani azababben
son jin muryarta. Ya dauko wayarsa ya
shiga laluben layinta. Ya kafe lambobin nata
da ido yana ganin fuskarta a kan wayar ya
soma kiranta, kai ya kanga ringin ya yi
saurin katsewa, to in ya kira ta me zai ce da
ita? Ya maida wayar ya ajiye a wannan dare
bai sami isasshen bacci ba don baccin ma da
92
KA AURE NH-1 Bilkisu H.Muhd
ya samo duk cike ya ke da mafarkinta
barkatai.
Karfe takwas da rabi yana zaune a kan
darduma, lazimi ya ke yi yau kam ko yunwa
bai ji, addu'a ya ke yi Allah ya kawo dalilin
da zai ga Humaida.
Umma ta turo kofa rike da langa a
hannu, ya yi saurin mikewa ya karbe ta. Ba
laifi yau ta dan sassauta fuska, ya karbi
kwanon ya ajiye ya durkusa.
"Umma kin tashi lafiya?"
Ta ce., "Lafiya kalau Mu'allim. Ga
dumame nan ka yi maleji".
"Umma kada ki damu ke ki ci, ni in na
fita waje zan samo".
"A'a mu'allim a sa a baka ya fi a
rataya, ni ma na dan ci”.
"To Umma Kawu fa?"
"Shi ma nasa na nan in ka gama sai ka
ララ
je ka kai masa
"Umma na gode"
93
KA AURE NH-1 Bilkisu H.Muhd
Ta dan yi murmushi, "Allah ya yi maka albarka".
Ya ce, "Amin".
Ta fice.
Ya bude kwanon, tuwo ne na dawa,
wanda bai wuce dan shekara biyu ba ba zai
ishe shi ba, ya kada kai kawai ya soma ci.
Karfe hudu majalissarsu ta cika kowa
na kaawo matsalar gidansa, Mu'allim ya yi
shiru, gabadaya hankalinsa bai gare su, shi
kansa ba zai ce ga tunanin abin da ya ke ba.
wyarsa ta dau ruri, ya zaro daga cikin
aljihunsa, sunan Humaida ya gani ya sauke
ajiyar zuciya.
Wani irin sanyi ya tsarga masa, ya yi
saurin matsawa a gurin, ya latsa kore.
"Abokina". Muryarta ta ratsa
kunnuwansa.
Ya ce, "Kin wuni lafiya?"
"Wallahi lafiya kalau. Ina gayyatarka
plcase za ka yi mini rakiya".
"Me zai hana".
94
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
"Zan iya zuwa na dauke ka?"
Ya ce, "A'a, gaya mini inda zan same ki".
Tana tukain motar cikin nishadi,
lokaci-lokaci ya kan ji gabansa na faduwa,
haka kuma ya dinga satar kallonta wannan
karon ido biyu suka yi, ya yi murmushi.
Kamar ta kai hannu ta shafa fuskarsa,
ta dai basar.
A wani kayataccen restaurant ta yi
fakin, ta sanya an kawo musu kayan ciyeciye da lashe-lashe kala-kala. Sakin jilki ta
yi sosai ta take cikinta yayin da shi ya dinga
ci kamar an sa shi dole, gabadaya jinsa ya
ke yi a takure.
Ta lura da haka, duk da tana takalarsa
da hira hakan bai sa ya sake ba, tunani ya ke
yi tunanin mahaifiyarsa ta ya ya zai bude
ciki yana kwasar irin wannan garar alhalin
ga Mamansa can cikin yunwa da wahala.
"Mu'allim na ga gurin nan bai yi
maka ba, bari mu wuce ko?"
95
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Sai da ta biya kudin suka bar gurin.
Wannan karon hotel ta ja shi, inda ta
dinga dubansa tana tilo masa kayan da za su
dace da fatarsa, sai da ta diba masa saiti
ashirin sannan ta yi 6angaren takalma, naan
ma ta dinga diba tana zubawa a Kwando ban
da su turaruka, agoguna da sauran kayan
kyale-kyale tamkar ba ta san ciwon kudin
ba.
Sai bayan sallar magriba suka yo gida,
a dan nesa da gidansu ta yi fakin, ya fito zai
tafi.
"Ni zan yi maka dakon".
Ta fada cikin sigar zolaya.
Ya ce, "Na me fa?"
Ta ce, "Kayanka mana".
Kawai sakin baki ya yi yana kallonta,
ga wani irin nauyinta da ya dinga ji, jin
komai ya ke yi tamkar a mafarki. Ta yi
tattaki ta karasa gare shi.
"Abokina kalle ni”.
96
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ya dan dago idanunsa yana murmushi.
"Me ya sa za ka yi mini haka, duk
aboki na gari kokarinsa ta ya ya zai faranta
wa abokinsa rai, kai abokina ne, zan iya yin
komai do.min farin cikinka".
Zai sake yin magana ta katse shi.
"Don Allah ka yi shiru, ina neman
i zan karasa da kai kofar gidanku,
boda kayan za su yi maka nauyi".
Kada kai kawai ya yi, suka koma
motar.
A cikin wata dauya kacal shakuwa.
mai karfi ta shiga tsakaninsu, inda gabadaya
tunanin Mu'allim ya sauya, ya amince zai
iya rayuwa da ita, ya yarda da son da ya ke
yi mata, sai dai abin da ya fi daure masa kai, Humaida ba ta taba cewa tana sonsa ba, sai
dai ta ce ya aure ta.
Haka ta 6angaren abokansa irin su
Abdul da Yusuf sun shisshige inda har
Humaida ta kan yi musu hidima, sha'awar
97
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
yadda rayuwar abokin nasu ya sauya suke
yi, kullum za ka ganshi tsaf kamar dan wani
mai iko, sai dai ba ko anini a aljihunsa.
Za ta yi masa komai, sai dai naira
biyar bai taba hada su ba, in ka ga Mu'allim
ya goge jikinsa ya murje har wata 'yar kiba
ya yi, to kullum za ta zo ta dauke shi su tafi
yawo ba za su dawo ba sai bayan magriba.
Haka rayuwarsa ta ci gaba da gudana.
*** *** ***
"Ya kin an babyna, har yanzu fushi a
ke da Dad?"
A shagwabe ta zauna a gefensa.
"Yau dai bari na faranta wa Baby, yau
وو babu inda zani ki yi masa magana ya zo".
Annuri ya sauka a fuskarta, ta mike da
gudunta.
"Dad, ba ni takaitaccen lokaci".
Ta yi cikin dakinta ta dau waya tana
laluben layinsa.
98
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
-
Daga can 6angaren Mu'allim wayarsa
na rike a hannun Yusuf yana jujjuya shi da
ya ba shi.
"In ni ne da wannan dokar da shi zan
yi in ja jari".
Mu'allim zai yi magana wayar ta
soma ruri, da sauri ya mika masa a dokance
ya ke mata sallama. Yana jin dariyarta, bai
taßa jinta cikin irin wannan farin cikin ba.
"Ya aka yi?"
Ta ce, "Yau zza ka zo gidanmu, yau
Dad dina na son ganinka, saboda kai
musamman ya ki fita ofis".
Ras gabansa ya fadi, wani irin gumi
ya gama jike shi.
"Ki yi hakuri, ba zan iya ba".
"Me ya sa?" Ta tambaya.
Ya ce, "Saboda zuwana ba. shi da
fa'ida".
"Manzonmu (S.A.W) ya ce, ka amsa
gayyata idan an gayyace ka".
Ya yi shiru yana nazarin maganarta.
99
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Comon, me ka ke tunani ne?"
"Ki yi hakuri..."
Ya katse wayar. Yusuf ya dinga
tambayarsa cikin damuwa ya ke shaida
masa.
"Ah haba be a man mana, ya za ka
kwafsa mana?"
"Ba haka ba ne ina ji a jikina kamar
wani abu zai iya faruwa".
"Yarinyar na sonka inda akwai
matsala ba za ta nemi ka je ba".
"Haka ne Yusuf bari in neme ta".
Ya bi sahunta wayar ta dinga ringin
tamkar ba za ta dauka ba, gaf ta ke da
katsewa sannan ta daga.
"Hello". Babu amsa.
"Humaida kina kan layi?"
Ba ta yi magana ba sai shesshekar
kukanta da ya dinga ji, dulk ya kidime.
"Humaida ki yi mini magana, me ya
sa ki kukа?"
Nan ma ba ta ce komai ba.
100
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muld
"Please, am sorry ni a wa da zan kasa
amsa gayyatarki? Na yi haka ne kurum don
na gwada ki, yanzu ki turo mini da adireshi
an zo".
Cikin muryar kuka ta ce.
"Na ce da kai, Dad ya ki fita ne
saboda kai, abu mafi muhimmanci a gurinsa
shi ne ofis, amma ya ajiye saboda ya
ganka..."
"Ya isa haka Humaida, na ce da ke
zan zo.
Tunda ya sauka a .motą yanayin
unguwar ya tsorata shi, babu mai karamin
karfi unguwa ce na manyan kusoshi
wadanda suka ci suka tada kai, lambobin
gidan ya dinga bi da kallo. Gidan nasu shi
ne mafi tsari da girma a duk cikin unguwar.
Tuni jikinsa ya yi sanyi, lallai ya yi
ganganci, ya soma shakku a kan soyayyar
Humaida. Ya fi yarda da akwai wata manufa
a ranta, shawara ya ke yi na ya koma ya cire
10
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
ta a rayuwarsa duk da ya san mawuyacin
abu ne ya iya mancewa da ita.
"Saurayi, ko kai ne bakon Humaida?"
Muryar maigadi ya katse masa tunani,
ya kasa magana sai kada kai da ya yi.
"Bismillah shigo ciki".
Duk lokacin da ya cire kafa sai
gabansa ya yi wani irin bugawa. A sace ya
dinga bin ko'ina na gidan da kallo ya zama
tamkar wani dan kauye, a'can nesa ya hango
ta sanye cikin doguwar riga ta shadda ya sha
adon surfa ni.
Da sauri ta nufo shi farin ciki ya kasa
bokyuwa, ya dinga yake a hankali ta sakale
hannunta cikin nasa tana jansa.
"Humaida ke ce kuwa?"
Cikin wani salo ta yi far da idanunta.
"Na sauya maka ne?"
Ta fada tana duban kanta.
"Na lura wannan shigar bakona ya fi
bukata".
102
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ya dan yi murmushi sai dai har
lokacin gabansa bai daina bugawa ba, ita
kanta ta lura da yanayinsa, ta dai basar ne
kurum.
Sai da suka shige faluna har guda uku
inda suka kutsa kai a babban falon. Tsarin
gidan kadai zai tabbatar da gidan 'yan boko
ne, yana kishingide a doguwar kujera rike
da jarida a hannu. Sanye ya ke da singileti
sai gajeren wando, gefensa computer ce.
Daga nesa ya gama kare wa Mu'allim
kallo tsaf ba tare da an fahinci abin da ya ke
kallo ba, lokaci guda ya kawar da kai.
"Wannan karon ba zan biye wa son
ranta ba".ya fada a zuciyarsa.
zama.
"Baby kun Karaso?"
Ya dubi Mu'allim ya nuna masa gurin
"Bismillah".
Gabadaya Mu'allim ya gama karaya,
tun daga kan irin duban rainin da ya samu,
dan dosana duwawu ya yi a gefe, ga wani
103
KA AURE NI-I N!-1 Bilkisu H.Muhd
gumi da ya sauko masa cikin sakanni.
Tabbas ya yi amfani da wannan Karin
maganar da Hausawa ke fadin, labarin
zuciya a tambayi fuska. Ya sani ya ji a
jikinsa arziki ba zai biyo baya ba. yanayinsa
ya nuna ba mutum ne mai mutunci ba,
fuskar nan babu haske. Ya mike zaune ya
ajiye jaridar tare da rufe computer ya dauko
kofi ya zuki lemo tsawon minti daya ya
ajiye kofin. Ita kam Humaida ta kalli uban ta
dubi Mu'allim, akwai shakku a tare da ita.
Daf ya koma tamkar ba shi ba, Dad
mai sakat mata fuska da barkwanci duk
sanda suke tare, amma yanzu ga yadda ya
daure fuska kamar wanda aka yo masa aiken
mutuwar mahaillyarsa. Ba ta gama shan
mamaki ba sai da ta ga ya sake daukar jarida
da alama ya mance da su.
Ta yi gyaran murya. Ya kallo ta,
yanayinta ya yi matukar kular d shi,
damuwa ce kwaro-kwaro ya gani kwance a
fuskarta.
104
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Shi kam Mu'allim ya kai kololuwa
gurin kuluwa gabadaya haushin kansa ya ke
ji, wane karamba ni ne ya kawo shi gidan,
ya aka yi ta shammace shi ya biye mata?
"Mu'allim sunanka ko?"
Ya katse musu tunani, a hankali ya
kada kai.
"Humaida ta zo mini da maganarka,
sai dai yadda na zace ka ba haka na ganka
ba".
Cikin kafe shi da ido Injiniya ya ke
maganar, haka ne ya tilasta wa Mu'allim
sunkuyar da kai. Ya ci gaba da magana.
"Saiurayi, anya kuwa ba ka so kanka
da yawa ba? Me ya sa dan Adam ke son kai
kansa inda matsayina bai kai ba? shin ba ka
yi la'akari da waye kai ba?"
Yana yi masa wani kaskantaccen
kallo ya ke maganar.
"Amma duk da haka bari na yi maka
wata 'yar tambaya".
103
KA AURE NII-1 Bilkisu H.Muhd
Ya yi shiru tsawon mintina biyu,
sannan ya dora da fadin.
"Waye kai? Me ka yaka da har ka iya
tarar aradu da ka? Shin a garin nan waye
ubanka? Gaya mini sunansa na ji".
"Dad!" Humaida ta kira shi da karfi.
Ya dakatar da ita da hannu ya sake
maida dubansa ga Mu'allim.
"Aikin me ka ke yi, ko kuma na ce me
ka ke karanta a wane mataki ka ke a
karatunka? Kodayake idan na tambaye ka ka
yi digiri kamar takardar sakandire na
tambaya, digiri na biyu ka ke yi ko na
hudu?
A zafafe Mu'allim ya mike yana huci.
"Ka jita mo in na tambayo sannan na
dawo na ba ka amsa".
Cikin muryar tashin hankali Humaida
ta fuskanci Dad din nata ta ce.
"Wadannan tambayoyin sun yi rashin
ma'ana, sun yi yawa haka".
Mu'allim ko har ya fice a falon.
106
I
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
Da gudu ta rufa masa baya tana kwala
masa kira, ko bi ta kanta bai yi ba bai ma
san inda ya ke cilla kafafunsa ba saboda
tsananin 6acin rai da tozarcin da mahaifin
Humaida ya yi masa. Komawa ta yi ciki da
gudu tana faman mita, Dad na kiranta amm
ko kallon inda ya ke ba ta yi ba, dakia ta
shige ta kulle kanta.
Me ke son faruwa da rayuwarsa?
Komai ya jagule masa, me ya sa zuciyarsa
ke yi masa zafi? A tunaninsa daga yau zai
tsinke duk wata alaka da ke tsakaninsa da
Humaida, amma zuciyarsa ya kasa laminta,
jinta ya ke ui tamkar ta zamo wani sashi na
rayuwarsa. Ji ya ke yi tamkar ita се numfashinsa. Humaida ta cuce shi, ya ya zai yi, wannan wace irin masifa ce? Me ya sa zuciyarsa ba ta yi la'akari da abin da ya dace da ita ba? Zuwa yanzu ya kamata a ce ya
sanya tsanarta a zuciyarsa, to amma yanzu
ne zuciyarsa ta ke kokarin amsarta, me ya sa?
107
4
slaw
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ya kasa tantance hudubar su Yusuf ne
geke dawainiya da shi inda ya ke shaida masa
bdd kwadaita masa yadda soyayyar Humaida
ai' daukaka darajarsa, Ubangiji ya kan tsaro
aarzikin bawa ta ko wacce irin hanya,
shigowarta rayuwarka alheri ne, yanzu ne ya
kamata ka sake da itą ka gigitata da
soyayyarka, na san za ka iya. Yin haka-zai
sanya rayuwarka ta sauya, in wannan hanya
ta kubuce maka ba ka da wata hanya, ta
dalilinta za ka mallaki dukkan abubuwan da
ka ke muradi, burinka zai cika na son
kyautata wa iyayenka".
Ya sauke ajiyar zuciya ya cije lebe
cikin runtse ido da kada kai.
No, ba haka ba ne. ina son Humaida,
クラ ina matukar sonta.
2
A8 5
*** *** ***
иS967 Yallabai, Humaida ba ta da hankali
99
za ta lahanta kanta.
108
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ci gaba ya yi da bugu kamar zai 6alla
kyauren. Tana zaune a baking ado, kuka
kawai ta ke yi.
"Humaida ki bude kofa mu yi
ララ
magana.
mutu".
Cikin muryar kuka ta ce.
"Dad ba zan bude ba, ku kyale ni in
"Baby zan yi yadda ki ke so".
Ya ce cikin muryar lallashi.
"Please ki bude kin ji".
"Ba za ka yi ba dad, ba ka sona da
kana sona ba za ka wofintar da abin da na
kawo ba".
"Ki buce ki ci abinci kada ki haddasa
wa kanki wani ciwon”.
Har bayan sallar magriba suna faman
lallashi fir ta ki budewa, tun suna jin
motsinta har sun daina. Cikin tashin hankali
Dad ya fita ya samo ma'aikata suka 6alle
kofar.
109
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Hango ta suka yi ta soma fita
hayyacinta, a hannu ya dauke ta tamkar
jaririya, ya nufo sitroom ya kwantar da ita a
doguwar kujera yana jijjigata. Da kyar ta
dawo hayyacinta.
Mom ta hado mata shayi mai kauri
cikin dabara da lallashi suka samu ta sha.
Injiniya ya dube ta yana mamakin
yadda ta yi zuru-zuru, ya kada kai ya ce.
"Babyna na yi miki alkawari muddin
zai amince zan aura miki shi, haka ya yi
miki?"
A hankali ta kada kai.
BAYAN SATI DAYA
A kwanakin nan kullum sintiri ta ke yi
duk inda ta san yana zama ta ke kai shawagi,
sai dai babu duriyarsa kodayake wani fannin
a kan idonsa ta ke zuwa inda ya ke samun
maboya ya 6oye kansa. Koyaushe kokari ya
ke yi ya cire ta a rayuwarsa, duk da yana jin
ba zai iya ba.
110
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Yanzu ne ta ke tunanin kai wa gidansu ziyara, sai dai da ta tuno mahaifiyarsa ya
kan sire, tunanin gargadin da ya yi mata na
game da zuwa gidansu ta ke. Yanzu dole ta
san hanyar da za ta bi ta gama da
mahaifiyarsa.
Kaya ne a zube gaban Hajara tana
faman jujjuya su cike da tsoro tare da
mamaki, turamen atamfa biyar, sai leshina
uku kowane yadi goma-goma sai ambulan
wanda shi ne ta daga tana jujjuyawa.
Mu'allim ya yi sallama cikin kallon
kayan.
"Umma me na ke gani haka?"
"Karaso ka duba, ni ma wani yaro ne
ya kawo wai a bai wa Maman Mu'allim"
Gabanshi ya fadi, ta ci gaba da fadin.
"Amma ina tsammanin makuwa ya yi,
ka ga duba wannan takardar".
Ya karba ya warware, kudi ne 'yan
dubu-dubu guda ashirin, sai wata farar
talarda, ya warware ya soma karantawa.
111
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
'Ina fatan za ka yi wa Dad afuwa a
bisa abin da ya aikata bisa rashin fahinta.
Daga karshe ga kyauta nan na yi wa
ummanmu, saboda ina son ganinta cikin
wadata, kada ka ce a'a'.
Ya sauke ajiyar zuciya, ya saci kallon
Ummansa ta wutsiyar ido gabadaya
idanunta na kansa, ya yi yake.
"Umma kayanki ne ban san ta dawo
ba, 'yar makarantarmu ce, shekara biyu ke
nan rabona da ita. Tana da yawan alkhairi,
dukkan wasu matsalolina ta kan magance
mini, iyayenta masu hali ne".
Kai da ganin yadda ta ke maganar za
ka fahinci akwai rashin gaskiya a tattare da
shi.
"Allah sarki wannan kaya tamkar
kayan lefe, anya Mu'allim?"
"Babu damuwa Umma, za ta iya ba ki
fiye da haka".
"To amma sai ka rike kudin ko?"
112
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"A'a Umma, ki bar shi ai naki ne. sai
ki bada a yi miki dinki”.
Ta dage a kan sai ya amsa, tilas ya
dibi dubu biyar.
A daidaita sahu ne ya sauke Hajara
daga dan nesa da gidan Yusuf ne ya fara
lura da ita ko kadan bai iya shaidata ba, ya
zunguro Mu'allim.
"Ga shi nan kun yi bakuwa, amma
daga fani kanwar Umma ce, na ga kamar ta
baci".
Mu'allim ya kasa dauke ido daga
kanta, la66ansa ne kawai ke rawa, gabadaya
Umma ta dawo kamar 'yar shekara arba'in.
ta lura da kallon da suke mata, ta yi
murmushi daidai lokacin da ta karaso inda
su ke.
"Yusuf kai ne a gidan namu?"
Ya yi mamakin yadda ta canki
sunansa, sai dai ga muryar nan irin ta
Umma. Ya yi murmushi.
"Ni ne".
113
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ya gaida ta, ta amsa tana kokarin
shigewa ciki ya maida kallonsa ga Mu'allim.
"Ya ya aka yi ta san ni?"
Idanun Mu'allim syka kada kamar zai
yi kuka.
"Yusuf ka ga Umma tana bukatar
kulawa, ga shi kai kanka ka kasa gane ta".
Yusuf ya zabura, ya ce.
"Kana son ka ce min Umma cе?"
A hankali ya kada kai.
"Allah ya yi mana tsari da talauci, shi
ya sa na ce ka yi nazari a kan al'amarin
Humaida, ka ga yanzu in ma kyauta ta samo
daga gurin wasu wataran ba za su yi mata
ba, kuma kayan za su tsufa, amma in kana
da abin kanka kuwa za ka iya wadatata.
Mu'allim ka tashi ka taimaki mahaifiyarka,
wallahi shekarunta bai kai a ce ta yi tsufa
haka ba, dubi fa yadda ta juye ta zama
tsohuwa saboda wahala yanzu ka auna ka ga
sauyin da ta samu yau kadai inda a ce za ta
dauwama cikin wannan kulawar haka za ta
114
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
dinga dawowa sabuwa, please ka zauna ka
yi tunani".
Yana alwala ya ji kiran waya, ya zaro
wayar daga aljihu ya duba, Humaida ce. Ya
dan saci kallon Ummansa da ke tsugune ita
ma alwalar ta ke yi, gabadaya idanunta na
kansa. Ya faki idonta ya katse wayar.
A gaggauce ya Kaarasa alwalar ya fita
zai tafi masallaci, kiran Humaida ya sake
shigowa ya danna karbawa ya kara a kunne.
"Ka jira ni yau zan zo".
Muryarta ta ratsa kunnensa.
"Kada ki zo ba na nemanki, me ya sa
ba za ki fita a sabgata ba?"
"O.K ka jira ni in na zo zan gaya
maka dalili..."
ki'.
"Tsaya ni ki gaya mini inda zan same
Yana jiyo dariyarta, ta ce.
"Zan gaya maka amma in ka haura
minti goma za ka gan ni a cikin gidanku".
115
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Tana zaune a cikin wata rantsattsiyar
mota mai duhun gilas, cool music ne ke
tashi, ta ji dirar a daidaita sahu ta fan kallon
gun, daidai lokacin da Mu'allim ke kokarin
sallamar mai sahun ta sauke ajiyar zuciya,
cikin murmushi ba ta taba tsammanin akwai
mutumin da zai iya burge ta har ta ji tana
sha'awar dauwama da shi ba sai Mu'allim.
Yana tsaye yana ta raba ido, tunaninsa
bai kawo ita ce a motar ba, ya ja kawai ya
tsaya cikin sanda ta bude kofar motar ta fito
tana ci gaba da sanda har ta isa inda ya ke
tsaye.
A daidai saitin kunnensa ta daddage ta
zuba uwar kara, gabadaya ya runtse ido tare
da saurin juyowa. Ta tuntsire da dariya,
gabadaya ya ware idanunsa a fuskarta yana
jin wani irin nishadi hadi da sonta.
Yarinyar na da kyau na daukar
hankali, to amma me ya sa ta ke tallan
kanta? Har lokacin dariya ta ke yi cikin tafa
hannu, shi kuma ya gaza dauke manyan
116
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
idanunsa a kanta, a hankali ya soma
nurmushi. Burge shi ta soma yi.
Ta tsagaita dariyarta, ta ce/.
"Ya kamata a ce kai ne ke jirana ba ni
cee jiranka ba".
Ta dubi agogon da ke daure a
tsintsiyar hannunta, karfe biyar da kwata,
"Mintina ashirin na diba a nan kafin ka iso,
me ya sa?"
"Saboda kiran ba mai muhimmanci ba
ne".
Ta yi masa wani irin duba, lokaci
daya ya daure fuska.
"Na ga sakonki, amma kina tunanin
zan amince da ke ne saboda wata bajinta
taki? Gaskiya kin kyi kuskure".
"Kada ka yi tunanin ina yin haka ne
don na sami hadin kanka, ko da ban sanka
ba na hadu da mutum na ga ya cancanci a
taimaka masa na kan taimaka, sam ba
manufata ke nan ba, amma ban ce lallai sai
ka yarda ba. sa'annan na ga har yanzy
117
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
zuciyarka ba ta yi sanyi a kana bin da Dad
ya yi maka ba..."
"Hakan ne ya sa na zo na gargade ki".
Ya katse ta da fadin haka.
"Gargadi? Wane iri?"
"Eh, ina gargadinki da ki fita a
rayuwata
"Tunda na taso ban taba jini na
ra'ayin abu na rasa shi ba ina ji a jikina
mu'amalarmu za ta fore".
"Idan na ce da ke na tsane ki ya za ki
ji?"
Ta yi murmushi, "Uhm zan dubi
fuskarka in har na kalle ka zan ga labarin
zuciyarka a fuskarka. Ta iya yiwuwa ne ka
fada ta wata manufa, amma ni na san ba
haka ba ne".
"Me ya sa ki ke yaudarar kanki?"
"Saboda na san babu namijin da zai
dube ni bai yi burin na zamo mallakinsa ba".
118
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ta yi bala'in ba shi dariya,
musamman yadda ta ke magana cikin
Gadara da nuna isa, ya ce.
da ni".
"Sai ga shi ni babban burina ki rabu
"Karya ka ke yi, wallahi karya ne".
Ta katse shi kai tsaye.
"Na riga na shigo rayuwarka, sai ka
zamo nawa sai na mallake ka”.
Ya ce, "Ko mayya ce nan gani nan
bari".
"Ba mayya ba ce, amma za mu
kasance tare".
Juyawa baya ya yi ya soma tafiya ta
shiga kwala masa kira, bai saurare ta ba. ta
koma ta shiga mora ra bi bayansa, sai da ta
zo daf da shi ta sha gabansa ta tsaya ta fito.
"Mu'allim ka gaya mini, me ye wanda
ba ka so a jikina, ko halayyata me ya sa ka
tsane ni? Yanzu ka rantse ka tsane ni, ka сe
ba ka son ganinaa, ka ce ba ka sona, ni
kulma na rantse zan fita a rayuwarka".
119
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
Gabadaya ya ji ta dauke masa wuta,
ya sanyaya murya matuka.
"Babu dan Adam din da na tsana. Ke
ba sa'ata ba ce, ba ajina ba ce, in na ce zan
yi soyayya da ke na yi wa kaina ganganci,
kowa ya sani ruwa ba sa'an Kwando ba ne.
Ni talaka ne ke 'yar manya ce, na sani
kuruciya ce ke dibanki, in kin zaße ni a
matsayin abokin rayuwa nan gaba da kanki
za ki yi da na sani, don Allah na roke ki, ki
kyale ni".
"Wannan ne kurum hujjarka? Wannan
ne ya sa ka ke son cutar da mu?"
"Ba shi ne kawai ba, dabi'unki sun
zamo abar kyama".
Da sauri ta kalle shi.
"Wace irin kyama?"
"Ina tsoron halayyarku da dabi'unku,
duk da na kwarai ya kan yi kokarin sama
wa yaransa uwa ta gari. Ban taba ganin
mutane kamar na gidanku ba. Al'adun
yahudawa sun yi muku kaka gida, ban da
120
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
wannan zan yi farin ciki idan mace irinki ta
zamo mallakina, matata makusanciyata".
"In ka zauna da ni za ka iya sake
tsarin rayuwata. Zan bi ka ta yadda ka ke so".
"Humaida, ba za ki taba fahintar abin
da na ke nufi ba, shiga mota mu je ki gani”.
Yadda ya ce haka ta yi, suka shiga
mota, wannan karon shi ne mai tukin, kurum
zuba masa ido ta yi tana kallonsa cike da
tunanin inda zai kai ta.
Hanyar sharada ya dauka, inda ya
tsayar da motar daidai kasuwar, ya zuge
gilas ya kalle ta, ya ce.
"Dubi can".
Wani dattijo ta hanga zaune a rana
yana faman dinkin takalmi, gabansa
matattun takalma ne da matattun robobi. Tа
dube shi cikin rashin fahinta. Ya dan jinjina
kai.
"Abin da na ke son fahintar da ke,
wannan dattijon da ki ke gani shi ne
121
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
mahaifina, babana ne shi ne ya haife ni. Ki
dube shi, dubi suturar jikinsa, dubi yadda ya
ke, kalli inda ya ke zaune, ki fara nazari".
Kurum binshi ta ke yi da kallo har
yanzu ta gaza fahintarshi.
Ya tada motar, unguwarsu ya nufa,
nan ma ya yi fakin a dan nesa da gidansu.
Ya numfasa.
"Na san duk lokacin da ki ke bibiyata
ba kya duban unguwarmu da gidan da na ke
rayuwa, ni kawai ki ke duba zuciyarki na
karkata ne a guna. Nan ne gidanmu, a nan na
ke rayuwa ba mu mallaki komai ba sai
wannan rusasshen gidan kasan. Ina son ki
dube shi da kyau duk fadin unguwar nan
babu lalataçcen gida kamar wannan, kowa
ya dubi gidan zai nemi tsari da rayuwa a
cikinsa, mai tausayi da imani shi zai duba ya
ce, Allah Sarki, gida ne wanda ko almajiri in
ya zzo tsallake shi ya ke ba zai yi sha'awar
bara a cikinsa ba".
122
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ummansa ce ta leko da wata karamar
yarinya a gabanta, da sauri ya zuge gilashin.
"Wannan ita ce mahaifiyata, ta rako
waccan yarinyar ne kin ga alamun kamar
yana yi wa yarinyar magana duk da ban ji
abin da ta ke cewa ba, na sani godiya