gori a kanshi".
"Humaida loakcinki ya zo daf kin yi
karatu irin yadda na ke so, kin yi karatun da
za ki san me ye rayuwa, loakci kankani na
ke jira zan yi miki aure, ni ma burina ke nan
ina ta nazarin irin mijin da zai dace da ke,
miji dan gaske. Ina son na aura miki mijin
da ba zan ji kunyar nunawa kowa shi a
matsayin suruki ba".
"Dad ai irinsa na samu na kuma gama
magana na gaya maka ka neme shi”.
"Shi ke nan zan yi yadda ki ka ce, zan
neme shi, ki dan ba ni lokaci mu bi komai a
११ sannu.
61
KA AURE NI!-1
yi".
Ta makale kafada.
"Oh my God".
Bilkisu H.Muhd
"To gaya mini, gaya mini yadda zan
"Ka ga ba da bata lokaci ba, ka je ka
same shi ka yi masa magana gobe a daura
aure, jibi kuma ka gan nki da ciki, gata na
haife. Ka ga na yi maganin gorin Mom, in fa
ba a yi haka ba ran kowa zai 6aci a gidan
nan".
Ya dinga tuntsira dariya, lamarin
Humaida sai ita.
"Shi ke nan, yanzu a ba ni sati guda ayyuka su sassauta mini".
Ta kada kai ita kam Mom yadda
fuskarta ke a daure amma zuciyar nan fari
kwal ya ke, tana jin dadin yadda mijinta ke ji da 'yar tata.
*** *** ***
62
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Majalisar su Mu'allim ta yi fakin daga
dan nesa da su ta fito sanye da shiga irin
tasu ta manya.
Yusuf ya yafito Abdul.
"Kai kalli wata haja can tafe".
Abdul ya dana harshe, ya ce.
"Kai wannan ta gaji da haduwa, ta zo
duniya a sa'a, ga kyau ga masu numfashi.
Amma fa wannan hajan ta fi dacewa da ta
gwamnoni, kalli fa motar da ta shigo".
Hankalin Mu'allim ya kai kan
Humaida, ras! Gabansa ya fadi, me kuma ya
kawo ta nan?
Tana kara kusanto su, wuf! Ya mike
da sauri Abdul ya rike gefen rigarsa.
"Haba Malam, bi a hankali mana,
wannan sam ba kalarka ba ce.
Ya kwace daga rikon da Abdul ya yi
masa cikin sauri ya doshe ta. Ya yi bala'in
daure fuska.
"Duk inda na ke zama kin sani, please
ki gaya mini me ki ke bukata a gare ni?"
63
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ta yi masa kallo mai lumshe idanu, da
sauri ya dauke kai daga gare ta.
"Sunanka na ke bukatar ji.
"Sunana Mu'allim, don Allah ki tafi
ki daina bibiyata kada ki bata mini suna, in
kuma ki ka ci gaba komai zai iya faruwa".
Ta kalle shi a tsakiyar ido.
"Kalaman so ka ke gaya min?"
Ya gama kufula.
"Ke wace irin bagidajiya ce wadda ba
ta san bakar magana ba?"
Ta yi murmushi ta cе.
"Tunda na taso a gidanmu ban san
wannan kalmar ba".
Ya yi shiru kawai yana kallonta,
tsawon mintina biyu ya hada hannayensa
guri daya, ya yi kamar yana rokonta.
"Don Allah ki fita daga rayuwata".
A zafafe ya bar gurin, tilas ta ja jiki
zuwa cikin motarta ta hada kai da sitiyarin
motar ta rasa abin da ta ke ji game da shi,
tana ji a ranta za ta liya jure wa duk
64
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
bala'insa, ba ta taba ganin abin da ya burge
ta kamarshi ba.
Muryarsa yadda ya ke masifa,
fiyarsa da duk wani motsi da gabbansa ke
va yi mata, sam ba ya taba ba ta haushi.
T. dinga murmushi, ta dago kai ta kai wa
sitiyarin duka sannan ta tada motar.
"Mu'allim ba mu fa gane ba, wane
siddabarun ne da kai?"
Yana ji suna ta yi masa tsiya ya
fahinci bugun cikinsa suke son yi, haka suka
gaji da zolayarsa. bai bari sun ji komai а
bakinsa ba, daga karshe ma barin gurin ya
yi.
Tana tsaye a wani loko da ke daf da
layinsu da alamun tashin hankali a tattare da
ita. Tun daga nesa ya hango ta, ya kara
sauri. Tun kafin ya tambaya ta sanar da shi.
"Na shiga wanka da na fito na ga
kawunka ba ya ciki".
Cikin kuka ta ke maganar. A guje ya
kwasa ya yi iya dubansa babu duriyarsa. Ya
65
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
zauna a kan wani dandamali komai ya kunce
masa, idanun nan sun yi jajir.
"Zan tafi, ka kular min da kawunka".
Wannan shi ne sallamarsu da
Abbansa, hankalinsa ya kara tashi, ya ji
zuciyarsa na yi masa zafi.
"Ina Kawu ya ke, wane hali ya ke
ciki? Yanzu haka yana nan yara na
tsokanarsa, yana can yara na jifarsa. Yana
can yana tsince-tsince. Yana can yana jin
kishi da yunwa".
Kwalla suka shiga kai komo a
idanunsa, rayuwarsu da Kawu lokacin da bai
hadu da lalura ba ta dinga dawo masa.
"Ka ga tashi ka dauki roba ga naira
hamsin ka saro pure water, dan abin da ka yi
יי ciniki sai mu yɔ awo
Kawu ya yi caraf, "Ina son ku sani
muddin ina numfashi wannan yaron ba zai
yi talla ba, wannan kam ba zai dauki dako
ba, sai na karatu. Daga yau na dauki wannan
alkawarin, Yaya ka zamo shaida duk lokacin
66
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
da Umman Mu'allim ta dora masa talla sai
na yi mata saki talatin".
Malam Musa ya yi murmushi.
"Me ya sa zza ka ce haka alhalin mu
din ba wasu ba ne?"
"Na sani Yaya, amma ni ina ji a jikina
yarona zai zamo wani, bango majinginarmu
zai zamo wani abu wataran.
Malam Musa ya ce, "Ina fatan haka,
amma ta ya ya hakan zai yiwu alhalin abin
da za mu ci ma yana yi mana wahala, ta ya
ya za ka ci wa Mu'allim irin wannan burin?"
"Ba zan gaza ba yaya, Ubangiji zai
tallafi niyyata, ni na sani burina zai cika, ina
alfahari da fadin Ubangiji cewa, "Ku roke ni
zan amsa muku'. Zan kara jajircewa, zan
hana idona bacci cikin dare na tsaya tsayin
daka ba zan gajiya ba, zan ta rokonSa a kan
Ya tabbatar mini da burina".
Ya janyo hannun Mu'allim ya dora
daya hannun nasa a kansa.
67
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Allah zai zamo gatanka, ni ma zan
zame maka gata daga ni har Yayana kai ne
sanyin idaniyarmu. Ina matukar kaunarka,
Ubangiji ya dora mini sonka, ina kaunarka
fite da komai. Zan yi komai domin ka sami
kyakkyawar rayuwa".
Hawayen da ke cikin idanun' Malam
Musa suka karasa gangarowa kan fuskarsa.
Bayan wani lokaci mai tsawo Kawu
ya sami Malam Musa zaune, ya debi kudi ya
zube masa a gabansa, cikin zaro ido Malam
Musa ke kallonsa.
"Yusuf kudin me na ke gani haka?"
Kawu ya ce, "Na yanke shawarar zan
yi tare saboda karatun Mu'allim".
Malam Musa ya mike tsaye ya shiga kai komo.
"Wannan da man shi ne nufinka a kan
kawai ka bauta wa danka ka ke son jefa kanka cikin halaka? Mun shiga tashin
hankali da yunwa mu kan yi kwanaki ba mu
dora tukunya a cikin gidan nan ba, amma
68
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
ban taba tunanin sanya kaina cikin
mummunar hanya ba a hakan kullum godiya
na ke wa Ubangiji don me ya sa ba za ka yi
oyi da ni ba? In ka jefa rayuwaeka cikin
こ ari ya zan yi? Shin kana son haddasa
mini wani ciwon ne? Kada ka mance, kai ne
kadai shakikina, kai ne sanyin idaniyata, kai
ne uwa da uba da dangina, me ya sa za ka
zabi irin wannan rayuwar?"
Duk Kawu ya gama rudewa.
"Yaya na rasa inda maganganunka
suka dosa?"
A fusace Malam Musa ya ce.
"Ina nufin in dai ta wannan hanyar ka
zaba don ka inganta rayuwar danka to ka
barshi, ka gaggauta sanar da ni inda ka samu
kudaden nan...
"Yaya kafin na ce wani abu ka yi wa
kanka shari'a irin wannan tarbiyyar ka ba
ni? Ina alfahari da tarbiyyar da dan uwana,
'yayana, Babana ya ba ni hakan ne ke kara
65
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
ba ni karfin gwiwar inganta rayuwar
Mu'allim..."
Malam Musa ya dakatar da shi.
"Ya isa, yi mini shiru. Kana son ka ce
ramuwa za ka yi, ko biyana za ka yi gwara
da ka fito ka shaida min hakan. Amma bari
ka ji in ba ka sani ba, wallahi na fi bukatarka
fiye da Mu'allim. Yau in na rasa shi Allah
zai iya ba ni wani, kai ko in na rasaka na
rasa ka ke nan ba za ka dawo ba, ba kuma za
a haifa min wani dan uwan ba. A kan me ka
ke neman maida rayuwarka abin farautar
'yan sanda da sojoji, a kan me? Wallahi
muddin ka gurbata halayyarka ba zan yafe
maka ba.
Barinsa ya yi a gurin cikin sharar
kwalla, bai yi yunkurin binsa ba ya san duk
abin da zai gaya masa ba sauraronsa zai yi
ba.
Ko da safe da ya je ya gaida shi kain
amsawa ya yi, wani irin kaunar yayan nasa
ya dinga ratsa masa zuciya.
70
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
A wannan marran kan a sami mai irin
halinsa za a tauna. Shi kam in bai so
Mu'allim ba Allah sai ya kama shi ta
hanyarsa kawai zai iya biyan yayan nasa,
yanzu ya ke kara jin yayan na zaburar da
shi, ya yi bala'in sanyaya murya.
"Shin aikin gini kauce hanya ne? dako
kauce hanya ne, ko turin kura kauce hanya
ne? Na amince ka je ka bincika wadannan
ayyukan su na ke yi har na tara wannan
kudaden, dubu ashirin da takwas ne, Yaya
ka amince da ni".
Gabadaya jikin Malam Musa ya yi
sanyi, duk sai kunya ta kama shi.
"Ba ka taba yi mini karya ba, na
amince. Amma wadannan ayyukan sun yi
tsauri da yawa, ka yi hakuri na yi maka
mummunar fahinta".
"Ba komai Yaya. Amma ina da
shawara".
Ya ce, "Ina jinka".
71
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Kudin nan a ciki na dibi dubu goma
saura na kawo maka, na kama rumfa a
kasuwar Sharada ina son zan je na siyo
kayan hatsi mu zuba a shagon mu dinga
saidawa. Hakan ya fi wannan sana'ar da ka
ke yi ka ga a hankali rayuwar sai ta yi mana
sauki, ni kuma sai na ci gaba da tarin saboda
wahalar karatun Mu'allim".
Malam Musa ya dinga godiya.
"Kada ka yi mini godiya, yi wa kai ne,
Mu'allim shi ne zai zamo madogararmu nan
gaba, zan iya yin komai domin shi”.
Wani yaro ne ya katse masa tunani,
"Ga kawunka can a bayan layi yara na jifa".
Ai da gudu ya mike. Rumfa ya yi
masa duwatsun da yara ke jifarsa suka dinga
sauka a jikinsa, Cikin wata masifaffiyar
murya tare da tsawa ya ke cewa.
"Kada wanda ya sake jifarsa, yana da
gatansa, ni ne gatansa saboda kawai yana a
matsayin mahaukaci ba kwa gudun hakki,
72
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
me ya yi muku, me ya ke muku? Bai san
komai ba.
Yadda suka ga Mu'allim ya birkice ya
suka fashe a gurin, ya koma yana kade
a jiki.
"Ka yi hakuri, sannu, yara ne marasa
55 tart yya, sannu".
****** - ***
"Sis hantsi fa ya dubi ludayi, wai
wannan Gallagazar mai aikin ba ta gama
girkin ba ne?"
Humaida ta dube shi ta watsar ta
koma tana danne-dannen waya. Ta dan kallo
tare da yatsina fuskа.
"Ba ta ma dora ba, aiki na sa ta".
Ya daure fuska, "Sis kina jin abin da
ta ke cewa ko?"
"Mustapha ya ka ke so na yi?"
"Amma dai fisabilillahi sis ta ya ya za
ta yi haka, karfe biyu saura a ce dan Adam
bai ci abinci ba?"
73
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ya ja tsaki, "Mustapha na ga sai wani
soki burutsu ka ke, kada ka mance da ni da
kai duk zamanta muke yi".
"In ji wa?"
Bai san sa'adda ya yi tambayar ba.
Ta ce, "In ji Dad dinta mana".
Sallamar Adam ya katse su, yana
faman rase-rabe.
"Hajiya ko zan sami yaji?"
Ta ce, "Wane irin yaji?"
Ya ce, "Zan ci abinci ne".
"Ba ni da yaji, kai dai kawai ka fadi
abin da ke tafe da kai, ya ma za a yi ka shigo
har nan tambayar yaji? Ka tambayi masu
aiki mana"
Mustapha ya ce, "Allah ne ya kawo
mini shi, da ma dan aike na ke nema. Sis ba
ni dubu biyu ya karbo mini take away".
Ta bude jaka ta dibo dubu uku ta
watsa mas, dubu daya ya mika wa Adam.
"Karbi, please ka hanzarta dawowa".
74
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ba za shi ba". Humaida ta fada kai
tsaye.
"Kai Adam je ka wanke mini jar
motar nan zan fita".
Ta karbi dubu dayansa ta ajiye, ta
shige daki abinta. Bakin Mustapha ya kasa
rufuwa, ya dubi Mom tamkar ba ta san abin
da ke faruwa ba. Ya yi kwafa.
"Amma wannan yarinyar 'yar rainin
hankali ce, kina jinta ko sis?"
"Uhm Mustapha ke nan, wai ya ka ke
son na yi ne? sam kai ba ka fahinta, a fa
gidansu fa ka ke, ka ke kuma cin arzikinta".
gida".
Ya mike cikin daga kafada.
"Well, Adam bi umarnin 'yar masu
Dalleliyar motar da ta shigo sai
daukar ido ta ke, yana tsaye kawai yana
kallonta kafin ta fito kofar gidansu ta nufa,
inda ya ke tsaye. Ya yi bala'in daure fuska,
wani takaici ne ke cinsa, tsarin suturar
jikinta sam bai dace da 'yar musulmi ba.
75
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ta dube shi tana faman kada makulli,
gabadaya ya kasa cewa komai.
"Ba zan daina ziyartarka ba har sai ka
amsa gayyatata ta zuwa gidanmu, kuma
gobe ma sai na dawo".
"Wai ke mayya ce?"
"Gaya mini duk abin da ranka ke so".
Ya ce, "Kina son bata mini suna, ki
daina wannan shigar kina zuwar mana kofar
gida".
Ta shiga duba ko'ina na jikinta, sam
ba ta ga abin da ya ke ma raki ba.
"Ina kokarin yin yadda na ga kana
ra'ayi don haka na ke takura kaina gurin
sanya kayan da jinsinmu suka fi tu'amali da
shi kamar haka".
Tunani ya ke me zai yi wa yarinyar
nan ta fita a rayuwarsa. Tunda ya ke bai
ktaba samun sabani da mahaifiyarsa ba sai
da ta shigo rayuwarsa, rabon da ya ga sakin
fuskarta tun sa'adda ta kai masa ziyara, bai
76
스
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
san sa'adda ya kai hannu ya rike gefen
rigarta ba, duk don kokarin tozartata.
Da wannan shigar ba za ki taba
mutunci a idanun kowa ba. Da wannan
shigar ba za ki taßa ba da sha'awa ba..
Macen da aka sani da mutunci kamala da
hijabi a jikinta, kuma surarta ba abar kallo
ba ce ga mutanen kwararo, mace mai
hankali ita ke boye surar jikinta ta 6oye
adonta saboda mijinta halalinta shi kadai ya
kamata ta yi wa, zai gani ya ji dadi ya yi
zumudi, sannan ta burge shi ba irinki ba,
wadda kin gama tallar ado a kwararo".
Juyawa ya yi ya shige cikin gida ya
kuma danno, kwakkwaran motsi ta gaza yi,
ji ta yi gabadaya ta tsani kanta, sai dai a can
karkashin zuciyarta Mu'allim kara burge ta
ya ke yi, tana son mutum jajirtacce.
Ta yi murmushi mai ciwo, tare da
kada kaki ta soma tattaki zuwa inda ta ajiye
motarta.
7
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
Ta yi nisa da unguwar su Mu'allim,
Yusuf ya gano ta ya sha jinin jikinsa, ba
shakka Mu'allim ta ke nema.
"Dan iskan nan na son wasa da
damarsa, wallahi muddin yarinyar nan ta
кибuce тasa ba zai taba fita a talauci ba".
Daf da zasta gota shi ta dubi inda ya
ke, kallon sani ta ke masa tabbas yana daya
daga cikin abokan Mu'allim in haka ne za ta
yi magana da shi.
Ta saki hon daidai lokacin da ta yi
fakin motar.
وو" Ji mana
Ta ce da shi. Ya dan dakata.
"Don Allah zan iya yin magana da
kai?"
Ta yi tattaki zuwa gabansa, jikinsa na
rawa, wani irin kamshi mai sanyi ya shaka.
"Na ga kamar na sanka?"
Ya dinga kallonta.
"Please, ko kai ne abokin Mu'allim?"
Da sauri ya jinjina kai.
78
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Та сс, "Idan ba aza ka damu ba, ina
son ka taimake ni da lambar wayarsa".
Ya ce, "Babu matsala".
Wayarta ta mika masa, ya karba ya
shiga dura mata lambobin. Ya gama ya
mika mata, ta karba ta balle post dinta kudi
ta debo dubu gomata mika masa, tuni
hannunsa ya soma skarkarwa tamkar yas
fincika.
Hannunsa ya riga nata isowa gare ta,
ta mika masa sai zare ido ya ke yana jin
komai tamkar a mafarki.
"Na gode Madam".
Ta dan yi takaitaccen murmushi.
"Wannan ba wani abu ba'ne
Ta shige mota za ta tafi, ya ce.
"Shi ke nan abin da ki ke bukata?"
Ta ce., "Ina neman kusanci tsakanina
da Mu'allim, in har ka yi haka zan yi maka komai"
Ya yi murmushi. "Zan yi kokarin ganin tabbatar da haka"
79
KA AURE N1-1 Bilkisu H.Muhd
:Ta kada kai kurum ta ja mota.
*** ***
Shekaru kusan talatin tasowata a
haka na ke ganinku, ba kwa gaba kullum
baya ku ke kara wa, yanzu lokaci ya zo da
ya kamata iyayenka su fanshe dawainiyar da
suka yi da kai, amma kana neman kaucewa.
Mu'allim wannan hanya ce kadai za ka bi ka
cimma dukkan burikanka, addu'ar da ka ke
yi ne Ubangiji ya karba, please ka saurari
wannan yarinyar kada ka yi mana
99 mugunta...
"Ya ishe ka haka Abdul, wannan cin
وو fuskar ya yi yawa".
Caraf Mudansir ya cafe.
"Cin fuska ko gaskiya? Ka gaya mini
in ba wannan hanyar ba kana sa rai da wata
hanyar? Mu'allim ban taba ganin mara gata
irinka ba, duk cikin danginku ba mai rufin
asiri balle ka yi zaton nan gaba za ka sami
wata alfarma ta dalilinsu..."
80
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Yusuf ya katse shi, "Ya isa! Ban gaya
muku don ku ci masa fuska ba, ba a dole lin
yana jin ba ya ra'ayi babu lallai ba tilas".
Ya sassauta murya, "Amma Mu'allim
ka je ka yi tunani".
So su ke ma su ji ta bakinsa amma ya
ki cewa komai sai idanunsa da suka yi jajir
yunwa da bakin cikin maganganun abokansa
sun saukar masa da wani azababben ciwon
kai, tilas ya bar gurin.
Ko da ya koma gida Ummansa ce ke
faman kuka, ga wani irin kaya da ke jikinta
mai kama da tsumman goge leda. Gabadaya
sun yayyage.
Ya dauke kai tare da yin sallama, da
sauri ta goge fuska tare da kirkiro
murmushin dole.
"Mu'allim ka dawo?"
Ya daga kai, ta sake fadin.
"Ya yau ma ba a dace ba ko?"
Ya sake kada kai.
81
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"To Mu'allim kada ka kosa ka ji,
Ubangiji na sane da mu, ya fi mu sanin halin
da mu ke ciki, wataran zai karbi rokonmu ka
ji.
Ya ce, "To Umma".
Ta sake cewa.
"Allah ya yi maka alb arka".
Ya ce, "Amin".
Ya shige dakinsa ya zube a kan
tabarma.
“Auren jari za ka yi muddin ta fito da
kudirinta ka amince, ba a kanka aka fara ba,
ba kuma kwanciya za ka yi ita ta ci da kai
ba, aiki za ta sama maka in ka yi haka da mu
da iyayenka dulk za mu sami albarkaci".
Maganganun Yusuf suka dinga dawo
masa, ya sauke ajiyar zuciya.
"Amma ai ban da tabbacin ba
mahaukaciya ba ce, ko wace iri ce ita babu
ruwanka muddin za ta fidda ka daga kangin
talauci, bakun talauci”.
82
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ya yi saurin mikewa saboda wani irin
iska da ya taso, ya leka tsakar gida yana
kallon Umma na kawar da kayan tsakar gida
da alama an fara yayyafi.
"Ka sauke asabarin nan". Umma ta ce
da shki lokaci daya ruwan ya kece mai
karfin gaske.
Ya mike ko ina ya koma ya kwanta, a
hankali ya soma jin karar wayarsa, ya zaro
wayar daga aljihu yana dubawa, bakuwar
lamba ya gani, ya danna amsa kira tare da
karawa a kunne.
"Amincin Allah ya tabbata a gare ka".
Wata zazzakar murya ta ratsa
kunnensa. Ya kyi shiru yana nazarin inda ya
san wannan muryar. Ta katse tunaninsa da
fadin.
"Sunana Humaida, na san ka mance
da ni da fatan ban takura ka ba?"
Ya ce, "Kin dai kusa, amma kafin nan
ina son yau ki gaya mini me ki ke so".
83
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ina kofar gidanku, ka fito na shaida
maka".
"Kofar gidanmu?" Ya fada cikin
kaduwa, ya maida kai yana kallon wundo
ruwan sama na kara tsugewa.
"Ke kina da hankali? Wai me ke
damunki ne?"
"Mu'allim na san kai mutum ne mai
tausayi tunda ka ga na keto wannan ruwan
na zo ban da nutsuwa, ba zan fito ba kuku ya
gaggauta kwacewa a kofar gudan nan,
Mu'allim ina tsaye har nan da zuwa lokacin
da za ka saurare ni.
Tsaki ya ja ya katse wayar, ya ajiye ya
mike ya shiga sintiri, ya sani zolayarsa ta ke
yi.
Kimanin mintina biyar ya kasa sarrafa
zuciyarsa, yarinyar nan mahaukaciya ce, za
ta iya aikatawa. Da sauri ya bude dakin, ba
kowa a tsakar gidan, ya ji dadin hakan, ga
mamakinsa ganinta ya yi jingine a jikin
84
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
mota kayanta jike sharkaf sai rawar dari ta
ke, ta kankame jiki.
"Lallali yarinyar nan da gaske ta ke".
Wani irin tausayinta ya kama shi, bai
san sanda ya fita a ruwan ba ya nufi inda ta
ke, ba ta gane shi ba gabadaya ta gama
karaya, ta bude motar ta shiga ta kullo.
Hada kai ta yi da sitiyari komai ya kunce
mata, me ya sa ba za ta hakura da shi bа?
me ya sa zuciyarta ta kasa samun sukuni?
Me ya sa ta ke jin in ta rabu da shi tamkar ta
rabu da rayuwarta ne? Me ya sa ba ya taba
ba ta haushi? Duk me ya janyo wannan?
Hakan na nufi ke nan shi ne farin cikinta?
Kuka ya kwace mata, ta cije lebe
zuciyarta na yi mata wani irin zogi da
radadi.
"Oh Allah, me haka ke nufi, wannan
wane irin mutum ne mai shiga rai haka?"
Kwankwasa motar yaa katse ta daga
tunanin da ta ke yi. Ta dan dubo gurin ta
wutsiyar ido ta ganshi sarai amma ta basar.
85
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ya dan yi murmushi cikin tausayinta, ya sa
hannu ya bude motar. Kuka ta ke yi mai
hade da shessheka. Da sauri ya zauna ya
sassauta murya yana kallonta.
"Ki dan kauce wa kofar gidan nan”.
Sai lokacin ta dan dubo shi da ido
jajir, cikin muryar kuka ta ce.
"Saboda kada a ganka da ni?"
Ya dube ta cikin kifta ido, a hankali
ya dinga jin wata kasala na shigarsa,
musamman da ya shaki kamshinta, cike yа
ke da mamakin yadda salon ke son sauyawa.
Ya yi bala'in kaskantar da kai.
"Alfarma na ke nema please, ki yi
abin da na ce".
Tilas ta juya akalar motar dan nesa da
gidan ta yi fakin.
Sai da suka kafe juna da ido zuwa
wani lokaci ya saukar da ajiyar zuciya,
yanayin da ya ji shi a ciki ne ya sanya shi
kawar da kai, sai dai ita har yanzu idanun
nan nata na kafe a kansa, ba ta taba ganin
86
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
mutum kamarsa ba, komai nasa abin
burgewa ne.
Ya dinga dan satar kallonta, shin
wannan wacce irin yarinya ce? Gabadaya ya
sake dago da kai yana murmushi. Ya
numfasa.
"Na sani duk batunki wasa ne, yanzu
ki gaya mini me ki ke bukatar gaya mini?
Ko mene ne fada mini na yi miki alkawari
zan ba ki, zan yi miki”.
Ta yi luuu da ido cikin wani salo na
daukar hankali.
“KA AURE NI!"
Ya dan yi jum kamar yana tunanin
wani abu ya sake maida kai kasa, ya ce.
"Shi ne kawai bukatarki?"
Ta ce, "Kwarai".
Ya ce, "To zan aure ki".
Та се, "Ка yi alkawari?"
Ya ce, "Ban yi ba".
Ta ce, "Saboda me?"
87
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Saboda ban tsara zan yi rayuwa da
mahaukaciya ba!"
Duk da ba ta ji dadin furucinsa ba
hakan bai hana ta kare kanta ba.
"Mu'allim dakata, ni ba mahaukaciya
وو ba ce
"O.K na ji, amma me ya sa ki ke son
na aure ki?"
a
Ta dan yi shiru tana tunanin me za ta
ce masa, sai dai abu mafi burgea
halayyarta ba ta iya karya ba, ba ta karya ko
da rashin kyautawa ta yi ta kan fadi tunda ta
san babu mai iya daukar mataki a kan haka.
"Ke na ke sauraro".
"Tunda na dora ido a kanka na ji ka yi
mini, ka burge ni, kana da kyau ba kasafai a
יי ke samun irinku ba..."
Ya yi saurin katse ta cike da takaici,
ga wani dariya da ta taho masa.
"Ke kuma haka Allah ya halicce ki
daga kin ga mai kyau sai ki nemi ya aure ki?
Gaya mini aurenki nawa, don na san
88
2
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
kyawawa kullum haihuwarsu a ke yi,
wannan shi ne kalar haukan naki".
Ya bude motar zai fita ta yi saurin
riko hannunsa. Ras! Gabansa ya buga lokaci
guda ya dinga jin wata irin kasala, ya ji shi
tamkar an zare masa laka, ga wani irin
yanayi da ya dinga ji da sauri ya zare
hannunsa daga cikin nata ya koma ya zauna
yana maida numfashi.
"Ban taba rantsuwa ba, amma yau na
yi saboda neman yardarka. Na yi rayuwa da
jinsi iri-iri na je kasashe da yawa ban taba
ganin ko jin mutumin da ya burge ni na ke
son mu yi rayuwa a cikin duniya daya,
unguwa daya, gida daya, daki daya kamarkaа
ba. ka amince mini".
Har yanzu mamakinta ya ke, bai taba
jin ko ganin mace irinta ba, wannan akwai
rainin hankali cikin lamuranta. Ya yi bala'in
daure fuska cikin kallonta.
89
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Duk cikin zantukanki ban ji kalmar
so ko guda daya ba, sai dai ina burge ki, ina
da kyau na aure ki"
"Sau tari ina jin mutane na maganar
so, sai dai ban san ya ake soma shi ba, ban
san me ye shi ba, asalima ban yarda da shi
son ba, da na yarda da kalmar so da kai
tsaye cewa zan yi ina sonka, ba zan ce KА
AURE NI ba".
"An kuma".. Ya ce a ransa, ya yi
murmushi a hankali ya dinga jin ta soma
burge hi.
"Ban taba jin an yi aure babu so ba, ya
za a kira wannan auren? Auren jeka na yi ka
ko me?"
"O.K na amince na yarda ka koya
mini yadda zan so ka”.
Ya kyalkyale da dariya bakidaya ban
dariyarki ya sanya ina jin dadin kasancewa
da ke, ba zan koya miki sona ba domin ina
da abin da ya fi so muhimmanci, sai dai ki.
zama kawata, aminiyata that all”.
90
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
A hankali ta kada kai, "O.K zan iya tafiya".
Ta sake kada kai, har ya bude motar
ya fita ba ta iya cewa komai ba, ta bi shi da
ido har sai da ya bace wa ganinta, ta sauke ajiyar zuciya.
A dakin Mu'allim yana kwance sai
faman juyi ya ke yi, lokaci-lokaci ya kan yi
murmushi, musamman in ya tuno hirarsu da
Humaida. Yanayinta na burge shi, ya mike
zaune ya janyo filo ya rungume ya koma ya
kwanta ya lumshe idanu yana wassafo
kamanninta.
Tana da kyau matuka, tana daya daga
cikin matan da kowane namiji ke mafarkin
rayuwa da su, irin matan nan ne wadanda ba
su taba gundura irin matar da in an 6ata
maka a waje da ka shigo gida ka adobe su za
ka ji wani sanyi da nishadi na shigarka. Irin
matar da duk lokacin da ka dora ido a kansu
za ka kasance mai mika godiya ga Allah da
ya azurtaka da ita, irin matar da ko ita kadai
91
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
ka mallaka za ka yi alfahari, irin matar da
ake wa