gaya miki maza. na wahalarwa? Kin taba ganin Mom cikin wahala?"
"No Dad, kai na daban ne".
Ya ce, "Don haka na ke son sama
miki na daban irina".
"Ba za a samu ba Dad! Ina jin labarai
ina kalle-kalle, ina karata littattafai kullum
"9 maza ne ke wahalar da ma
Ya yi dariya.
30
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Baby ai ke yanzu kin wuce wannan
matsayin, kina da komai ko wane namiji
dole ya yi miki biyayya, don haka na ke so
mu bi a sannu ba za ki taba fahintar mai
sonki ba, don haka na ke son ki kama
zuciyarki".
"Dad na gaya maka ba zan taba son
wani dan Adam ba bayan ku ban jin komai
ba game da shi ba, na ga dai kawai mun
dace da juna".
Ya san Humaida da kafiyarta, ya shiga
nazarin ta inda zai 6illo mata, ya sauke
ajiyar zuciya.
"O, tanzu kina da tabbacin sake
haduwa da shi?"
"Ina ji a jikina, kuma na ba shi Katina
na tabbata zai kawo kansa nan ba da dadewa
ba".
"To shi ke nan, na ji. A wace iriyar
mota ki ka ganshi?"
Ta yatsine fuska, ta yi taku uķu ta
tsaya.
31
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
"A sayyadarsa na aga yana tafiya".
Ya sake yin shiru duk alamin 6acin rai
suka bayyana a fuskarsa, ta kafe shi da ido.
"Dad ya na ji ka yi shiru?"
"No, ba komai yanzu mu bari har
zuwa lolkacin da zai kawo kansa sai mu san
me za mu yi, yanzu ki je gida da na dawo sai دو mu sake tattaunawa.
"Dad na gode, ina alfahari da kаi".
Ta soma tafiya da baya cikin daga
masa hannu da dan mumushi a fuskarta.
*** ***
Katon gida ne na gani a yaba tsakanin
get zuwa cikin gidan akwai tazara mai nisa,
yawan bishiyoyi da furannin da ke dashe a
gidan ne ya taimaka gurin rashin wadatar
haske a cikin gidan ba lallai ne matsoraci ya iya shiga ciki ba saboda duhunsa. Hakan ya
sa rai da rai gidan bai rabo da hasken fitilu a
harabar gudan ga motoci nan birjik tamkar kamfanin kera su. Babu abu mafi daukar
32
:
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
hankali a gidan irin lambunsu wanda
swimming pool ya kara kawata shi, ga wasu
irin glass carpet da suka yi luf-luf a kasan
gidan kana taka kafa sai ka ji wani danshi
mai sanyi ya ratsa kafafunka. Gefe daya
gurì ne da aka tanadi kayan motsa jiki da
liluna kala-kala, kana soma tafiya harabar
ma'aikatan gidan za ka fara riska, su ma
sashinsu tamkar giwan wani maikudin, ana
yi wa gidan lakabi da green house, saboda
duk abin da aka kawata gidan da shi kore
ne.
Daga wajen get maigadi da Adam na
zaune rediyo suke sauraro, suka aji wani
gigitaccen horn. Da sauri Maigadi ya mike
jiki na rawa ya hangame get. Mustapha ya
kwaso motarsa a guje sauran kiris ya take
wa maigadi kafa, ya yi tsalle gefe duk abin
da ya yi masa bai hana shi yi masa sannu da
dawowa ba.
Wata yarinya ce danya shakaf manne
a jikinsa, ko kadan maigadi bai ishe shi
33
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
kallo ba balle ya amsa masa. Maigadi ya
gyada kai jiki a sanyaye yaa maida get ya
arufe ya koma gudin Adam ya zauna yana
mita.
"Wannan tsinannen Mustaphan in
Allah ya amince ba zai gama da duniya
lafiya ba sam ba shi da imani bai san darajar
kowa ba, Allah ba zai barshi ba sai ya
lalace".
"Fata na gari". Adam ya katse shi da
fadin hakan, karon mamaki ya kama Adam
hakan na nufin ba ka san ciwon kanka ba”.
Maigadi ya ce da shi.
"Ai komai bai ambata hakan ba
Ubangiji ba zai barshi ba, don ba aya zalunci
ya kuma haramta shi don ina karkashinsa ba
a ce ya maishe ni dabba ba".
"Kai kam na' ga alama zuciyarka ta
gama mutuwa, matsoraci ne kai in ni ne ke
da matsayin da ka ke da shi da yanzu na
kawar da wannan fasikar Adam bai cika son
34
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Mund
kananan maganganu ba don haka ya mike
daga gurin.
Gidan Injiniya Sunusi gida ne wanda
kowa ke rayuwa ba ruwan kowa da kowa
babu wanda ke shiga rayuwar wani, gida ne
wanda suke tutiya da boko daga uwa har uba
sun kai kololuwa gurin akidar boko bacin
akidar bokon sun dauko na Turai sun dora
wa kan na bokon, duk abin da za ka aikata a
gidan in dai harka ne na Turai to daidai ka yi
wayewa ce, don haka kullum Humaida ke
tutiyar ita ma tana da nata 'yancin ta ke
kuma ganin za ta iya yin abin da ta so babu
mai taka mata burki irin rainon da Naninta
ta koyar da ita ke nan.
Nani janat wadda tunda aka haifi
Humaida ita ce mai rainonta, tana wata
shida mahaifiyarta ta yaye ta komai nata ya
koma gurin Janet.
Injiniya Sunusi sam ba sa dawowa gida sai dare, da sun dawo ba su wani bi ta
35
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
kan Humaida, har gwara Mom ta kan leka
har ta sha kanta tare da sumbatarta a kunci.
Da safe ma in za ta fita hakan din ce
ke shiga tsakaninsu Mom laccar ce babu irin
dagar da injiniya Sunusi bai da ita a kan ta a
je aikinta ba, saboda yana tunanin su ba wa
talauci baya har abada, ta nuna masa ita
ra'ayinta ne ba ta na yi ne don wani abin
duniya ba, tana yi ne don rage wa kanta
zaman guri daya, tana yi ne don nishadп
haka ya gaji ya sa mata ido.
Injiniya ya kan aikata duk abin da ya
so da matarsa a gaban kowaye, misali
sumba, rikr ta, ba ta abinci a baki,
tarairayarta da dai sauransu. Kwanciyar aure
ce kawai ba su yi a gaban jama'a, komai
nasu irin na Turai ne kodayake zaiiya
yiwuwa hakan in muka yi la'akari da sirin
shekarun da suka yi a Turai, kuma Turan ma
cikin U.S. 8280
et id Injiniya Sunusi duk da shekarunsa ba
za ka taba ganinsa cikin manyan kaya ba sai
36
:
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
kanana, ita kam Momcy tsulkewa ta ke
tamkar wata 'yar sha biyar, ko da za ta fita
i dai ta dora after dress da dan kwalinsa,
ciyo talkalmi mai tsini ga uwar kwalliya.
kan mance da yawan shekarunta, ta yi
bala'in daukar duniya da zafi, babu ruwansu
da kowa ba su hulda da dangi, manyan masu
kudi su ne abokan mu'amalarsu, su ne
danginsu su ne abokansu su ne a kan komai
nasu
Tun dangi na bibiyarsu har suka koma
sun sanya musu ido, yau inda za ka tambayi
Humaida ta kawo maka sunan danginta
kwaya uku ba za ta iya kawo su ba, sai
abokan Dad da Momcy.
Adam shi ne kadai ta sani a cikin
dangin mahaifinta, sai Mustapha wanda shi
kuma a dangin mahaifiyarta. In ka dauke
wannan ba za hta iya kawo maka kowa ba.
Adam uwarsu daya ubansu daya da
Injiniya, sai dai ba shi da wani fawa a gidan,
ba shi da maraba da 'yan aikin gidan duk
37
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
kuwa da dan ilimin da ya yi ya sha 'yar
murya gurin yayansa a kan ya dauke shi aiki
ko da a kamfaninsa ne har kawo yanzu ya
kasa ba shi gamsasshen amsa, sai dai ya се
ya je gurin Madam su yi maganar, haka zai
je gaban Momcy ya durkusa sai ta gama
jinshi sai ta ce, me ya rasa? Yana ci yana sha
yana sanya sutura bayan nan me ya ke so ko
yana son ne a ce ya zama kamar kyadda
suka zama?
"Halayyarka suna nuna bakin ciki ka
39 ke mana
Haka shi ne furucinta gare shi don
haka ya zuba wa sarautar Allah ido, hatta ga
abincin da zai ci a gidan wanda ma'aikatan
gidan suke ci ne. Dakinsu daya da mai ba
wa furanni ruwa, yayin da shi Mustapha
matsayinsa kullum hauhawa ya ake.
Motar da Injiniya ya hau ita ya ke
hawa, abincin da ya ke ci shi ake ba shi yana
da matsayi mai girma. A daya daga cikin
kamfanin Injiniya. fasiki ne na a zo a gani
38
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
ba shi da mutunci, ba shi da kunya duniyarsa
ya ke ci da tsinke, yau in ka ganshi ya shigo
da wannan karuwar gobe da wata za ka
ganshi, kowa ya san da haka, babu wanda ke
tsawatar masa.
Humaida ce kawai maganinsa, ita din
lambaya daya ce. Wannan ke nan.
*** *** ***
Tana kishingide a doguwar kujera
rimot rike a hannunta channel ta ke
sauyawa, sannu a hankali ta zo inda ta ke
muradi ta aje rimot ta mike ta shiga
rausayawa.
Mom ta fito daga daki da glass cup
rike a hannunta. Ruwan lipton ta ke kurba,
kai tsaye ta nufi soket ta off dinsa. A fusace
Humaida ta juyo suka yi ido biyu da Mom,
ta zumburo baki.
"So na ke yi ki ci abinci".
Mom ta ce da ita.
39
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ina cikin zulumi, babu abin da zan ci sai Dad ya dawo".
"Mai Dad zai yi miki?"
Mom ta tambaya cikin yanayin mamaki.
Humaida ta yatsina fuska, ta ce.
"In ya dawo kya ji".
Abin takaici ko kadan amsar Humaida
bai fusatata ba, sai ma murmushi da ta yi.
"O.K baby ci gaba da gashi".
Neman guri ta yi ta zauna, ta ajiye
kofin hannunta ta janyo wani magazine da
ke kan center table tana karantawa.
"Hello my lovely baby".
Wannan shi ne sallamarsa a duk
lokacin da zai shigo gidan.
Ta yi tattaki cikin ihun murna.
"My sweet Dad".
Tana rike da shi kamar ta shige
cikinsa, suka zube a kan doguwar kujera da
alamun gajiya a tattare da shi. Ya dan kalle
ta.
40
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Baby amma kin ci abinci kuwa?"
Ta shagwabe murya za ta yi magana,
Mom ta taso cikin takun kasaita ta dan rage
tsawo ta sumbaci Injiniya a kunci.
"Welcome my sweety".
Ya kai hannu ya shafi kuncinta, ya сe.
"Amma na ga kamar baby ba tą ci
abinci ba"
Da sauri Humaida ia katse shi.
"Ka san ba zan iya cin komai ba".
Ya ce, "Me ya sa?"
Ta ce, "Saboda akwai maganarmu da
kai, ina tsoron sakamakona".
Ya fadada fara'arsa.
"Oh ni babhy ai wannan karamin abu
ne baby, ba abin da za ki nema ya gagare ki
ina da komai na baiwa komi ba ya wannan
duniyar taki ce".
Ta yi murmushin jin dadi, wannan na
daya daga cikin halayyarsa, fariya.
41
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ina rayuwar ne gabadaya don na
zame miki gata, da zarar ya kawo kanshi zan
san abin yi".
*** *** ***
Daf da magriba Malam Musa yana
tsugune a kofar gida, alwala ya ke daurawa,
Mu'allim sanye da jesi mai taınbarin
Bercelona ya nufi inda mahaifinsa ke
alwala.
"Abba sannu da gida". Ya fada yana
kokarin durkusáwa.
"Yauwa mai sunan manya, ka dawo?"
Mu'allim ya gyada kai.
"Abba ya Kawuna?"
Ya ce, "Yana nan sai dai yau jikin
99
nasa ya matsa masa
Bai tsaya jin karashen maganar ba ya
diba da gudu zuwa dakin, in kana son ganin
tashin hankalin Mu'allim to ka itabа
kawunsa, yana kaunarsa fiye da komai da
kowa.
42
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
Kamar zai fashe da ihun kuka yadda
ya ga Kawu daddaure kamar wani dabba.
"Umma me ya sa ku ka daddaure shi
haka?"
Ta dube shi da fuskar tausayi, ba ta
taba mamaki da irin wannan azababbiyar
kauna da Mu'allim ke wa Kawun nasa ba, ta
sanyaya murya.
"Ba ka ganin yadda ya ji wa kansa
rauni? Dole ce ta sanya muka daure shi, in
ba haka muka yi ba komai zai iya faruwa, ba
ka bira da Abban naka ba ne, shi kansa ya ji
jiki".
Duban Kawun ya ke daga sama har
kasa, idanunsa taf kwalla.
"Amma Umma Kawu ya yi dauda da
yawa".
"Kawunka yana da lafiya kai ma ka
sani دو
Ya kada kai, Kawun nasa ya kafe shi
da ido, Mu'allim cikin muryar rarrashi ya
ce.
43
KA AURE NI-1 Bilkisu H.Muhd
"Kawu ka yi hakuri na sauya maka
wannan kayan ko da ban yi maka wanka
ba".
Ya kai hannu yana shafar fuskar
Kawun nasa.
"Ka yi mini magana yau ko da kalma
daya ce zan yi farin ciki, ina son ka bude
bakinka wanda bai gajiya da furta alkhairi a
gare ni, tunda bakinka ya kulle na rasa farin
ciki, na rasa abokin shawara, baccina ya yi
karnci, zuciyata ta yi rauni".
Ummansa da ke tsaye gabadaya ta
gama karaya, kokarin rushewa ta ke da
kuka. Da sauri ta bar gurin cikin dabara da
rarrashi yana shafarsa ya samu ya sauya
masa kayan, ya ba shi ragowar fumamen
tuwon da Ummansa ta ajiye masa, ya
gwammace shi ya hakura. Ya dora masa da
ruwa, sannan ya samu ya koma dakinsa.
Yana kwance a kan tabarma cike da tunani,
ya tsananta tunaninsa a kan yadda zai iya
fidda iyayensa daga cikin kangin, talauci.
44
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Babu abin da ya fi bakanta masa rai da
sanya shi jin kunya sai in ya dubi kansa
gabjeje da shi a ce. iyayensa wadanda
karfinsu ya gama karewa su ke nema su ba
shi, mahaifiyarsa ta yi surfe, ta yi wankau ba
ta tsinana wa kanta komai ba sai dai ta
tattara kudin ta siya masa sutura, sai dai
yana daga dakinsa yana jin nishinta na
ciwon jiki.
Ya kan yi kuka kamar ransa zai fita,
gari na wayewa za ta mike ta dora a inda ta
tsaya, haka Abbansa zai wuni rana, iska,
ruwa duk du kare a kansa sannan ya samo
ya yo awò gwangwani daya, biyu ya kawo a
dafa. Yana tsaye a kan Umma sai ya ga an
take masa kwano...
Kiran Abbansa ya katse masa tunani,
ya amsa tare da yunkurawa da kyra:
Tsaye ya ganshi a dokin kofa.
Malam Musa ya kafe dan nasa da ido
yana kallon yadda kirjinsa ya jike jagab da
45
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
kwalla ga idanun nan a rine tamkar ya
wanke fuska da ruwan barkono.
"Mai sunan manya me ya yi zafi haka,
me ke faruwa ne? kada ka mance duk halin
da za ka shiga, innalillahi wa'inna ilaihi
raji'un ya kamata ka fada, shi ne maganin
dukkan tsanani, wataran sai labari, me ye
cikin rayuwar? Na san tunaninka duk da ban
shiga zuciyarka ba kawunka, da mu ko? Тo
ka yi hakuri talauci ba abin kunya ba ne, ina
kuma godiya ga Allah da ba ka dauko mini
magana ba, kai ma ka gode wa Allah da ban
zamo mai cin bashi ba, duk talaucin da na ke
fama da shi hakan bai sa na bata wayona ba
shekaru da yawa kawo yanzu, tun tasowarka
babu wanda ya taba yin sallama da ni da
zummar na biya shi bashin da na ci wannan
ma kadai wata baiwa ce, don haka ka yi
hakuri".
Ya fada yana murmushi.
"Ka kula da Kawunka zan je kauye ba
zan wuce kwana uku ba, ka ji ko".
46
KA AURE NI!-1
Ya jinjina kai.
Har kofar gida ya raka shi.
Bilkisu H.Muhd
Washegari ya shiga kujiba-kujibar
tsaftace dakin Kawu, ya dibo kayan da ya
cire masa jiya ya nufi tsakar gida da su.
Umma na shara ya matsa gindin rariya ya
soma wanke su, Ummansa ta kwashe shara
za ta nufi soro ta zuba a mazubin shara, kai
tsaye Humaida ta fado gidan, har tana
bangaje Ummansa..
Da sauri Umman ta dube ta baki bude,
sanye ta ke da wasu damammun kaya, kallo
daya za ka yi mata ka kira ta da karuwa, don
irinsu ne suka fi irin wannan shigar.
"Subhanallahi, baiwar Allah ya
haka?"
Mu'allim ya dago kai da sauri don son
ganin abin da ya ruda Umman tasa. Ido biyu
da Humaida ya yi. Jin komai ya ke yi tamkar
a mafarki, gabansa ya shiga wani irin
harbawa, ga wani irin tsoro da ya lulluße shi
da alamun mamaki karera sanye a fuskarsa.
47
KA AURE NI-1 Bilkisu H.Muhd
Ya mike sosai cikin tamke fuska, bakinsa na
rawa.
"Wa... ya... nuna miki gidan nan, me
kuma ki ke bukata a gare ni?"
Karara kalamansa sun tabbatarwa
Ummansa da ma can ya santa, akwai alaka a
tsakaninsu.
Humaida ta karasa inda ya ke tana yi
masa wani duba. Shagala ta yi da kallonsa.
Kyawunsa ya shahara fiye da ganim da ta yi
masa farkon haduwarsu. Ta maida kallonta
ga gidan a karo na biyu ta sake malida
kallonta gare shi, kallon mai lumshe idanu ta
ke masa, al'amarin tamkar a shirin wasan
kwaikwayo Umma ta ke gani, ta saki baki
cike da al'ajabi, shi kam Mu'allim kunyar
irin kallon da ta ke masa a gaban Ummansa
ya ke ji, satar kallon Umman ya yi, yadda
kya ga bacin rai karara a fuskarta ne ya kara
ruda shi, ya yi bala'in kaurara murya.
"Me ya kawo ki gidanmu?"
48
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Zance na zo". Ta fada kai tsaye, "Kо
ba ka yi farin ciki da hakan ba?"
"I say shut up, na ce me ki ke nema,
me zan yi miki ko kina bina bashi ne?"
Ya karasa maganar cikin daga murya.
Ummansa kam tuni ta shiga sallallami cikin
tafa hannaye.
"A ina ka samo wannan karuwar?"
Ta fada tana kallon Humaida da kayan
jikinta ko bi ta kanta ba ta yi ba balle
kalamanta su daga mata hankali, maimakon
haka ma sai cewa ta yi.
"Ya maganarmu, Dad na son ku yi
magana da shi?"
Bai son ta baro masa aiki, ya fahinci
ba cikakken hankali ne da ita ba, don haka
da sauri ya katse ta.
"Ni ki je ni zan zo".
Yana magana yana satar kallon
Ummansa wacce ke faman watso masa
harare.
49
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Kafarka kafata, na sha wahala na
bata lokaci sa'annan na iya gano wannan
gidan
"Au ba za ka raka karuwar taka ba?"
Umma ta ce da shi.
"Ke tsohuwa ya fa ishe ki haka!!!"
Da sauri ya katse ta cikin daka wata
gigitacciyar tsawa.
"Mahaifiyata ce! Ya ishe ki haka".
"Don mahaifiyarka ce sai ta ce da ni
karuwa?"
Jikinsa har wani tsuma ya ke ya shiga
tankadata.
"Ki fice kada na sake ganinki a cikin
gidanmu. Ni da ke ba mu dace da juna ba".
Yadda ya bude murya hakan ya fi
komai daga mata hankali, ga idanunsa sun
juye zuwa jajaye, ba ta son abin da jama'a
za su taru a kanta, ta san halin talakawa abin
kallo ba kadan ya ke musu ba za ka ga sun
bi shì da kallo, wani zubin ma har sau su
50
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
karo da jifa don haka ta yi saurin ficewa a
gidan.
Ya sauke ajiyar zuciya ya sanyaya
murya.
"Umma ki yi hakuri don Allah, haka
ba zai sake faruwa ba".
Ta dube shi kamar za ta yi kuka.
"Mu'allim wannan shi ne irin
tarbiyyar a muka koyar da kai? Karuwa har
cikin gida da rana tsaka babu kunya?
Yaushe ne ka sauya, yaushe ne ka zamo
haka?"
Cikin rawar murya ya ce.
"Wallahi Umma ba zan ha'ince ku ba.
ba zan yi miki karya ba, ki amince da ni yau
shi ne ganina na biyu da ita, ban san wace cе
ita ba, na fi tunanin ko tana da matsala a
kwakwalwarta..."
"Ba ka santa ba na aga alamar hakan".
Duk sai ya kara kidimewa, wasu
siraran kwalla suka silalo kuncinta, ta jinjina
51
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
kai za ta sake magana ta kasa. Da sauuri ya
fada daki.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
Ya dinga ambata, ya dade bai ganta
cikin wannan yanayin ba.
Duk da kashedin da Dad ya yi mata
hakan bai hana ta dosar kamfanin ba, ko
gabanta ba ta iya gani sosai, daga can nesa
ta hango shi tare da wasu mutane, ga dukkan
alamu rakiya ya fito. Wani mahaukacin birki
ta taka, gabadaya suka tsorata sauran kiris
daya daga cikin bakin ya tsunduma kwata,
da taimakon riko da Injiniya Sunusi ya yi
masa yaa koma ya tsaya.
Ta ballo murfin mota ata fito cikin
kuka ta nufe shi, hankalinsa ya yi matukar
tashi, duk ya gama kidimewa.
"Gaya mini baby".
Ta kaasa magana, ya riko hannunta
yana rarrashi, ta ce.
"Dad a kan wannan maganar ne na je
gidansu ya ki saurarena, ya koro ni,
52
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
mahaifiyarsa ta kira ni karuwa, ya ya zan yi?"
Da sauri ya tari numfashinta da fadin.
"Ya isa haka, ki je gida in na zo sai
mu yi maganar, kin ga yanzu ina da baki.
Ina sallamarsu zan zo gidan".
Ya riko hannuntaa ya sanya ta a mota, duk bakin nasa na tsaye suna kallon ikon Allah, tabbas inda ranka ka sha kallo.
Ya sassauta murya.
"Zak i iya tukin? In ba za ki iya ba in
sa a maida ki gidan?"
Bakin nashi suka shiga kallon-kallo
cikin kada kai da takaici.
"Dad zan iya”
"O.K in kin je ki huta ki ci abinci kada
ki yi tunani yanzun nan zan dawo kin ji".
Ta kada kai ya sumbaci hannunta tare da shafa mata kai ya koma ya rufe mata murfin motar ta tada mota ya shigaa daga mata hannu cikin murmushi, bai saurare su ba sai da ta bace wa ganinsa.
53
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ya kamata ka koya mata abin da
addini da al'ada suka koyar da mu".
Wani dan gaza gani a kawar da kai ya
fada. Maganar ta sosa wa Injiniya Sunusi
rai, ya dubi Alhaji Auwal din wanda shi
kadai ne ke iya gaya masa gaskiya duk cikin
abokan huldarsa.
"Kada ka yi magana ina anusar da kai
saboda gaba".
A fusace Injiniya ya се.
"Me ka ke tsammanin gaba za ta
haifar? 'Yata ita ce kadai na mallaka don na
biye mata abin da ranta ke so me ye laifi? Za
ta je ta yi wa wani ne?"
"Okey, na fahince ka, babu abin da
gaba za ta haifar".
Alhaji Auwal ya mayar da martini. A
fusace injiniya Sunusi ya juya rakiyar da bai
yi musu ba ke nan.
Tsakiyar dare bacci ya kaurace wa
idanunsa, tunanin rigimar da Humaida ke
son debowa ya hana shi sukuni, wannan
54
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
karon dole ya jajirce, wannan karon ba za ta
sami abin da ta ke so ba. Humaida yarinya
ce ba ta san komai ba in ya ce zai biye mata
don gudun bacin ranta za ta gurbata jininsu,
babu abin da ya fi talauci zafi, don wani
fannin talauci kan yi bibiya, ba zai rasa
arzikinsa saboda farin cikin wadda har
yanzu ba ta san wace ce ita ba, ba ta san
ciwon kanhta ba.
Hajiya Zainab ta janyo bargo za ta
kara lullube jilkinta, idanunta fal bacci ga
mamakinta ta hangi Injiniya Sunusi zaune,
da sauri ta ture bargon gefe tana hamma ata
mike ta matso kusa da shi.
"Yallabai lafiya?"
Ta ce a sanyaye. Bai ce komai ba ta
kara shige masa.
"Akwai abin da zai dame ka har ya
hana ka bacci? A tunanina babu abin da
muka rasa, muna da komai".
Ya fuskance ta sosai.
55
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Humaida ce, Humaida ce kadai
matsalata, tana son rusa mini burina a kanta.
Humaida kadai na mallaka duk tanadina a
kanta ya ke, ba na taba son abin da zai
ruguza mata rayuwa.
Ya dakata na tsawon minti biyu.
"Yallabai kai na ke sauraro".
Ya numfasa, "Humaida na son jawo
mini rigima".
Ta dube shi cikin yatsina fuska.
"Ko dai suna son janyo wa kansu
rigima?"
Ya ja tsaki cike da takaici.
"Ki bari mana ki ji karshen zancen".
Hakan ya sa ta tsuke baki.
"Wani yaro ta gani kwanda ba shi da
دو galihu ta dage a kan sai ya aure ta...
Da sauri ta katse shi, ta fahinci inda
zancen nasa ya dosa.
"Okey, na fahinta shi ne ka ke tunani
saboda kana son biye mata? Ni kam ban
56
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
laminta ba, ba za a yi wannan abin kunyar
da ni ba, ba za ta gurbata mana jini ba".
Haka ta yi ta mita ta inda ta shiga ba
ta nan ta ke fita ba. Ya daka mata tsawa.
"Ke kin ga dakata, na ga kina faman
tada jijiyar wuya, ban gaya miki don ki bata
mata ba, abin da kurum na ke so ki yi mata
irin dabarunku na mata don ki nusar da ita.
In kuma ta matsa zan je in ga shi yaron zan iya daukar kowane irin mataki a kansa".
Gabadaya hankalinta ya tafi a kan
game din da ta ke yi, Momy ta fito daga
sashin Injiniya.
"To babyn game, a ajiye wayar nan haka ina son zan yi magana da ke".
Ta yamutsa fuska cikin sigar
shagwaba.
"Mom ki bari na kusa kashe bos din".
"Na ce ki bari haka!" Ta fada cikin
daga murya.
Ta sake kankame wayar.
57
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ni fa sai na karasa, tun dazun fa na
ke son kashe bos din sai da na kusa za ki ce
na ajiye?"
huci.
Takaici ya sa Mom fincike wayar tana
"Game har ya fi maganata, in ce da ke
ki ajiye ki ce sai kin karasa, me za ki karu
da shi a cikin wayar shashashar wofi?"
Ta juya baya cikin turo baki.
"LHaba Momy ya za ki dinga yi mini
tsawa kamar wata zaburarriya? Ni fa ina da
وو' yancin da zan yi duk abin da na ke so".
Mommy ta yi murmushi.
"Humaida har yanzu ke yarinya ce,
amma zan yi maganinki, gabadaya zan yi
sanadiyyar da za ki daina rike waya a gidan
nan in ga ta tsiya".
Humaida ta saki wata dariyar rainin
hankali.
"Ashe za ki takalo rigima ke nan
Mom? Ni fa ko da ki hana ni rike waya gara
kin hana ni abinci, waya ta fiye mini duk
58
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
abin da na mallaka, domin lita ta haska mini
abin da ke kanki ba ki hasko ba, ta sa na san
abin da ke kanki ba ki sani ba".
Yadda ta ga Mom ta daure fuska ya sa
ta mike tana dariya.
ララ "Am sorry mom".
Kokarin shigewa ta ke bedroom ta yi
saurin dakatar da ita.
"Ina son ki sanar da ni abin da ki ka
sani wanda ni ban san shi ba. Humaida kyau
na tabbatar da ke mahaukaciya ce, ba ki da hankali".
"Okey na ji Mom, yanzu gaya mini abu daya wanda ni ban sani ba".
Duk da Mom ta ji ciwon kalaminta sai
ta kanne, ta janyo hannunta.
"Zauna na gaya miki.
Tare suka zauna ta fuskance jta sosai,
ta ce.
"Kin ga abu na farko na yi aure, na biyu na san daukar ciki na kuma san zafin
59
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
haihuwa tunda ga shi na haife ki kina gaya
mini magana...
"Madam ke da wa ki ke faman hakilo
haka?"
Muryar Injiniya ta katse ta, da sauri
Humaida ta mike ta tare shi suka zube a
kukjera, ya dubi Mom.
"Na sha gaya miki ki dinga bin ta a
hankali, saboda har yanzu ba ta gama hada
hankalinta ba".
Ya shafo fuskar Humaida ya koma ya
sa hannu cikin aljihu, katin waya ya dauko
na dubu biyar, ya yi bala'in sanyaya murya.
"Ki yi amfani da shi zawa gobe, ya ya
ne baby ki saki fuska mana ki mance da
Mom dinki, ki gaya mini in kuma akwai
wata matsala".
Ta shagwabe murya kamar za ta yi
kuka.
"Dad, kullum Mom na yi mini gorin
95
aure.
Ya lakuce mata hanci.
60
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Rigimatuna, na ce ki rabu da ita za
mu rana
Ta shiga kunkuni.
"To na ji, gaya mini me ki ke son na
yi a kai?"
Ya tambaya yana kallon Mom wadda
ta yi bala'in daure fuska.
"Dad ka aura mini mutumin nan, na ji
abin da Mom ke yi mini