Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels HAUSABOOK.COM 1 KA AURE IN BILKISU H. MUHD Harafi Publlshers KaAure Ni BILKISUHAMUHD KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd KA AURE NI-1 afiya ya ke cikin tsananin T yunwa da gajiya, lokaci-lokaci yakan kade jikinsa da hankici abin da ya zame masa al'ada ke nan, haka ya nufi unguwarsu, majalisarsu ta gama haduwa. kyar. "Assalamu alaikum". Ya ambata da Sulaiman ya dube shi, da fadin. "Ya abokina, me ye labari?" "Sulaiman na gaji". Ya ce yana kokarin zama. "Yau karfe shida na bar gidan nan na wuni ina bulayin neman aiki, amma babu sa'a, al'amarin ya soma ba ni tsoro ina rokon Ubangiji mahaifana na yi mini sai dai har yau babu nasara, shekara biyar da gama karatu in ko haka ne ban ga amfanin karatun ba". Abdul ya dinga dariya, ya ce. 4 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd "Ai Alhaji tini muka je gano, in ka ce za ka dakata neman na kai, kai ne a wahale musamman a wannan zamanin da rayuwa ta yi tsada, har abada in kai ba wani ba ne ba ka samun muhimmanci ka zama tamkar kare, in ko ka ga ana yi da kai ka san wani ko wani ya sanka, don haka tunda na gama sakandire ban yi ggigin karasawa ba, gwara na yi ma zuciyata a gidada yammain dauki wanka na fito majalissa, na yi ta kallon masu shiga da fita, a haka wataran an samu 'yar masu numfashi ta makale mini, ka ga shi ke nan kakata ta yanke saka". Yusuf ya ja tsaki, ya се. "Lallai kam kana tare da wahala, su kansu 'ya'yan manyan ba son talaka suke yi ba, sun fi dafewa 'yan uwansu masu dala. sr "Eh lallai ba ka san dawan garin ba, Mudan ba shi labari. Ta ya ku ka hadu da Hajiyarka?d wol EeYusuf ya ce, "Lallai Abdul irin auren nan Mudan ka ke son za ka yi ke nan kada 5 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd ka mance matar Mudan fa ta haife shi, ga ta dirkakkiya, ko ka san in kibna ya yi yawa akwai illa?" A fusace Mudan ya kalle shi. "Eh na ji, amma a hakan ba kullum ga shi na ke ciyar da ku, kuma tunda abin hakа ne an yi yanke ta gille". Abdul ya gintse dariya a ciki. "A'a aboki, afuwa". "Allah na rantse kowa sai ya gane kurensa, ashe idanunku na kan matata? Тo daga yau gidan nawa ma kada wanda ya kara shigar mini". "Kyale su Mudan, wadannan ba su san ciwon kansu ba”. Sadik ya fada. "Wallahi ko ni na sami matar da ta fi taka tsufa aura zan yi, yanzu ba ga shi ba ni da na auri 'yar malam shehun ina ta fama ba, shegiya daga an tabata sai ciki, in gari ya waye ba za ka ga 'ya'yan kowa basai nawa su ne bin layin kosai, ko na waina, shekara hudu da aurc 'ya'ya hudu mai za ayi da 6 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd haka? Don haka gabadaya na kaurace wa shegiya na gwammace na yi ta bankan kanwa" Mu'allim da tun dazu bai ce komai ba ya ja tsaki. "Kuna shiga hurumin da bai dace ba, Sadik wannan bai dace ba". Ya mike gida ya shige, suka bi shi kawai da kallo. Mudansir ya ce. "Rashi ke sanya shi zafin zuciya, ku kyale shi gwara ma ya tafi don in ba haka ba sai mu kwashi 'yan kallo a nan". *** *** *** Malam Musa mai ido daya sunan da aka fi kiranshi da shi ke nan, talaka ne tilis wanda babu cin yau ba na gobe, domin in ya yi buga-bugarsa ya sami na masara ba lallai. ne ya sami na rana ba, duk aikin da ya samu ya kan taba, sai dai ya fi tsayawa ga likin takalmi ko rufin laya in ta samu. Duk da talaucinsa bai hana jama'ar 7 unguwa KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd Kaunarsa ba, mutum ne shi mai iya mu'amala da kowa. Jama'ar unguwa ba su taba kosawa da shi ba duk da cewar mafi akasarin jama'ar da ke unguwar ba masu karfi ba ne, amma hakan bai hana in an ci an rage a aiko musu ba. Duk illahirin unguwar sukan yi masa kara sun san halin da suke ciki, domin talaucinsa ya wuce tsammani. Mariya matar Musa mace ce jajirtacciya mai tsoron Allah da sanin ya kamata, za mu iya cewa kusan ita ce karfin gidan. Ta kan yi komai don ta faranta wa tilon dansu, ta kan yi duk wani aikin karfi don ta gata taimaka wa Mu'allim. Wani fannin in abin ya dagule musu haka Malam Jafar zai zauna yana kwalla, ta kan danne tata damuwar ta shiga nusar da shi, musamman wwani fannin ya ke fadin mai ke faruwa da su, mai ya ke ma Ubangiji da Ya yi musu irin wannan jarrabawar? Abin ya yi tsauri. 8 KA AURE NI!-1 Ta kan katse shi da fadin. Bilkisu H.Muhd "Mai ya sa ba za ka zamo mai godiya ba, ina laifi da Ubangiji ya bar mu da lafiyarmu? Ka sani duk talaucinmu akwai wadanda suka fi mu, wadansu ma ba cin ya jarrabe su da talaucin har da rashin lafiya ya P dora musu. Ba ka tunanin an iya ba mu arziki ta hallakar da mu?" Kalamanta sun sassauta zuciyarshi,. "Mariya, na fahince ki, ni babu -abin da ya fi daga mini hankali sai in na dubi Baba Karami, yau da a ce yana da lafiyarshi ba za mu shiga duk wannan halin ba. Baba Karami yaro ne mai nasibi tun yan karaminsa, ya ya ba zan ce ba duk abu ya yl mani yawa, lalurarsa ya tafi mini da dukkan farin cikina". enadse Ihun Baba Karamin ne ya katse musu hirarsu, da gudui suka mike har suna rige- rige. Gwara kanshi ya ke da garu yana kuma ci gaba da tsala ihu, ga jini nan na ta 9 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd fita a kansa, duk da ya san yanayin haukan nashi bai hana shi dosar dan uwan nasa ba. Ciwo da yakushi ya sha shi, ya samu da kyar ya daddaure shi yana goge mishi jinin fuskarshi cikin zubar hawaye, kafin su bar gurin har kansa ya kumbura. Mariya ta hada yayi ta kyatta ashana ta cinna, ta dora ruwa ya yi dumi, ta shiga gasa wa Malam Musa inda Baba Karami ya jijji masa ciwo, sannan ta nufe shi shi ma tana gasa mishi kai. Ta koma gurin Malam Jafar wanda ke zaune ido jajir. "Wannan rayuwar da mu ke ciki wataran komai zai zamo labari, narar da Mu'allim ya sami aikin yi, sai dai in na tuna da yanayin da Baba Karami ke ciki na kan tsinci kaina cikin tashin hankali, burina Babnna Karami ya amfana da ilimin da ya sadaukar da ransa da kuma duk abin da ya mallaka ya hana ma kansa jin dai ya hana makansa sutura da abinci mai dadi, ya bautar dakansa duk don Mu'allim ya yi 10 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd rayuwar farin ciki, ya yi rayuwar da ta bambanta da tamu". Ta sanyaya murya tana duban Malam Musa. "Amma na sani Ubangiji yana ji yana gani, in dai addu'ar uwa na amsuwa ga danta na sani burina zai cika, Mu'allim zai taka wani matsayi na ban mamaki, sai kawunsa ya samu lafiya ya yi alfahari da shi" lam Musa kawai bin ta ya ke da ka koma ya yi murmushi mai bayyanar da tsantsar ciwo. "Yaushe ne za mu ga wannan ranar? Kullum tsufa kara kama mu ya ke yi, ba na tsammanin ganin wannan ranar sai dai ina yi mishi fitan aixlairi a cikin rayuwarsa. Wallahi ina tausayin yarona, kullum ruwa da iska a kanshi ya ke karewa yawon neman aiki, káico da wannan rayuwa, talaka ya shiga uku, ka yi karatun da ake bukata, amma aiki ya gagara samuwa, in Allah ya 11 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd yarda yarona ba zai yi rayuwar da muke yi ba". Sallamar Mu'alim ce ta katse musu hira, ya risina. "Abba sannunku da gida". Malam Musa ya dube shi da fuskar tausayi. "Yauwa sannunka, kai ne da sannu. Allah ya yi maka albarka". "Amin Abba". Ya amsa yana murmushi, addu'arsu ce ke sanyaya mishi zuciya a kullum ba su kosawa da sanya mishi albarka. "Ya Ubangiji ka billo min da hanyar da zan faranta musu. Ina son iyayena su ji dadina, su yi alfahari da ni kafin su koma gare Ka, ko ni na koma gare Ka". Ya fada a ransa. Ya mike jiki a sanyaye ga wani irin jiri na dibarshi ya nufi falo, wanda ko daben kasa babu sai wata tabarmar karauni da ke shimfide. Ya zube a kai yana maida wata 12 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd wahalalliyar numfashi, yana son tambayar abinci yana jin nauyin hakan. Ya ja karamin tsaki, shi bai kawo ba ya zai yi ya tambaya, abin da kunya kam. Hamma ya dinga zabgawa, idanunshi suka yi jajir, ya sake jan tsaki yunwa ba ta yi ba, wannan rayuwar da suke ciki hatsari ce, dole ne ya nemi mafita. Ya kallo inda Ummanshi ke zaune da wata kodaddiyar atamfa duk ta sha faci, dinkin allurar hannu. Ya rankwafar da kai. "Da izinin Allah wataran sai sun yi farin cikin haihuwarsa, sai sun yi alfahari da shi, sai ya nema wa kawunsa magani, sai ya nemi arziki ta kowacce hanya ba zai yi sata ba, bacin wannan zai yi komai don ya zama wani. Tuntuni yana da burin zama wani yadda ake fadin ya hadu rashi ne kawai ya yi masa cikas, to zai nemi kudi. 13 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd Yana kallon Abbansa ya mike ya zari takalmi wanda ya sha liki ta ko'ina, ya nufi waje. Tsawon awa guda yana kwance dafe da ciki. Wata yarinya wadda ba ta wuce shekaru hudu ba ta yi sallama rike da kwano a hannu. "Umma wai ga shi in ji Mama". Mu'allim ya maida hankali gurin, cikin sauri Umman ta mike ta karba. "Kai masha Allah, abinci muka samu haka kai madallah, na gode, Allah ya saka da alkhairi ya jikan iyaye ya raya ku". Mu'allim ya ji kamar ya fashe da ihun kuka a duk lokacin da jama'ar unguwa suka yi mata irin wannan ragoyi-ragoyin abincin, ya ji tana rangada wannan godiya da addu'a kamar wata marokiya, ya kan ji tamkar zuciyarshi za ta fashe, wani abin takaicin ma sai ka ga yadda abincin ya ke, wanda da gani guntattatakin jagwalgwalon abincin 14 KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd yaransu ne haka za kaga tana farin ciki da murna tamkar an yi mata kyautar naman kaza. Mai sunan manya". Sunan da ta ke kiranshi da shi ke nan, ta kwalla masakira. "Ka fito ka ci abinci na san yunwa ka ke ji". Ya mike ba don ya so ba, don kawai kada ta ga ya gwale ta. Ta dire masa kwanon a gabanshi. "Maza ka ci na wanke kwanon amaida shi ko?" Ya kada kai kurum yana kallon kwanon, duk ya sha lamba ga abincin har da guntattakin burodi, ga wasu kananan gashi a ciki. "Umma ni fa a koshe na ke". Ya ce cikin gajiyayyar murya. Ta yi murmushi, a tunaninta wayo ya ke so ya yi musu don su ci kamar yadda ya saba. 15 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd "Na san abin da ka ke nufi, na sani ka fi mu bukatar ci, ji yadda ka koma duk ka yi ramar wuni daya". Ya sake sanyaya murya. "Umma na ce na koshi da gaske, na ci abinci, ki juye ki ba ta kwanon". Kafin ta sake magana ya dauki roba a kwando ya juye abincin, da kansa ya dauraye kwanon ya mika wa yarinyar. Ta mike ta raka ta har soro tana faman rangadagodiya, duk tausayinta ya kama shi, kwalla ne ke kokarin saukowa kan kuncinsa. Ya yi kokarin maida shi. *** *** *** Majalissar su Mu'allim. Hira ake faman yi, Sadik a gefe ya rafka uban tagumi, lokaci-lokaci ya kan doka tsaki, Yusuf ya tabo shi. "Mutumin ya aka yi haka?" Ya kara jan tsaki, ya се. 16 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd "Yusuf, Amina yanzu ma wai ciki ne da ita wata biyu kacal da haihuwa amma wai har ta sami wani cikin, mace kamar mage yanzu na ce ta zo na kai ta a cire shi ne ta ce in na gaji in sake ta, ai hahuwa baiwa ce, ka ji fa! Wallahi sai ma ka ga 'ya'yan bini in bi ka, ni kam na gaji, ina tunanin ta yadda zan rabu da ita, cuta ce dai ta riga ta cutar da ni, don na san babu wadda zan aura ta iya daukar dawainiyarsu". Yusuf ya dinga kyalkyala dariya har yana rankwafawa, Mudan ya ce. "Ni kam yanzu bakina alaikum ni da tsohuwata, komai sai dai a yi mini. Yanzu da kudi aka ce mini ga budurwa ko a ce ga yarinya ban niaura, aurensu matsala ne, sai kuna zaune su yi ta yi maka sakarci da shagwaba, in ba su ga dama ba sai su dage akan sai ka siya musu kayan kwalliya, ko su ce ba su da bra ko pant, ni kuwa tawa duk ba ta sanya wani bra balle pant". 17 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd Nan suka kara shekeewa da dariya har da ihu da tafi, gogan kam yana gefe yana tunanin ta wacce hanya zai sami aikin yi. Yaro ne ya doshi majalissarsu da wasu manyan kuloli, ya zube a gabansa. "Ga shi inji Hajiya". Ya fada yana kallon Mudan. Ai tuni ransa ya fashe. دو" Ka je ka ce ta ba da ruwa mana. Yaro ya ce, "Ai lemo ta ke hadawa". "O.K, ka ce ina yi mata sannu". Yaro ya tafi, su Yusuf tuni an gyara zama. Ya fara kokawar bude kulolin, Sadik ya tabo Mu'allim. "Ta fadi gasassa, Hajiyarmu ta yunkuro". Sai da ya yi kamar ba zai ci ba, kamshin abincin ya daki hancinsa, tuni ya gyara zama ya shiga ci, cike da tunani barkatai a can karkashin zuciyarshi tausayin kanshi ya ke yi da rayuwar da suke ciki shi da mahaifansa. 18 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd *** *** *** Tun daga nesa ta gano shi, ta kasadauke idanunta daga kanshi, tun tasowarta ta ke ganin jinsin mutane iri-iri amakarantarsu a unguwarsu, a kasashen waje, 'ta;yan mulki da 'ya'yan manyan kusoshi, amma ba ta ga wanda ya gigita tunaninta ba kamar wannan. Vyawunsa ya shahara, wani irin kyav ne da shi, komai na jikinsa yana da burgewa, idonsa, yankan bakinsa dan karami, gashin kansa tamkar na larabawa, irin mazan nan ne da ake wa lakabi da giant.. abu guda ne ya rage wa kywaunsa armashi, wato suturar jikinsa wadanda dukkaninsu ba za su wuce dubu daya da dari biyar ba. Sai takalman kafarsa na danko. Ta cje lee tare da kai wa sitiyarin mota duka. 19 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd "Oh shet! A nan matsalar ta ke, talaka! Wannan ya fi dacewa da dan sarauta!" A hankali ta ji ya soma burge ta, za ta so ya zama mallakinta nata ita kadai. Mace ce mai matukar son duk abin da ya ke da kyau, don haka duk abin da ya dangance ta ya kan zama mai matukar kyau. Ta san ta kan abu mai kyau, don haka Dad dinta ya ba ta zabi akan sabon gidan da suka koma, ita ce ta wassafa irin ginin da ta ke so, bai ja ba ya yi yadda ta ke so, gidan ya yi fiye da tunanin Dad din nata. Ta kuma tsara yadda ta ke son bedroom da sitroom dinta ta ke bukatar ya kasance, har ma da bandakinta. Ta sake maida kallonta gaMu'allim wannan karon takardun da ke rike a hannunsa sun zube kasa, ya durkusa yana kwashewa. Ya mike yana kade jiki da hankicif. Ta sauke ajiyar zuciya. 20 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd "Ya kamata a ce ya fi haka haske, rana ta dafar da shi, asalinsa fari ne ga yadda 99 ya tsaya a wahalallliyar ranar nan Tana son fitowa daga cikin motar, sai dai kwalliyar ranar ne ke ba ta tsoro. Kokarin tsallaka titi ya ke, ta saki wata gigitacciyar hon, duk sai ya rikice ya kalio inda motar ke tsaye cike da takaici. Bai ga kowa ba, duk da yana cike da jin haushin mamallakin motar hakan bai hana shi jinjinawa ba. Tuni ya nutsu ya dauke kai daga kallon gurin, a karo na biyu ta sake sakin wani hon din, wanda ya fi na farko rikitarwa. Ya gama tsarguwa ya tabbata shi ake yi wa hon din, to sai dai me? Kaf mutanen da ya sani babu wanda ya taba mallakar karamar motar ma balle wannan, don haka bai yaudari kansa da zuwa gurin ba balle a gwale shi. Hakan ya burge ta, tare da kara masa wani matsayi a zuciyarta, da alama mai aji ne. 21 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd Ta saki murmushi, ta bude murfin motar ta zuro kafafunta, wani irin takalmi ya gani mai masifar tsini. Da sauri ya basar saboda ganin da ya yi tana doso inda ya ke, ko dar bai ji ba a zuciyarsa, don ya san babu wanda zai ce ya ci masa wani abin.. Ta ja tunga ta tsaya a gabansa tana faman taunar cingam, wani irin iska mai karfi ya taso cak ya dauke yalolon gyalen da ke yane a kanta ya watsar da shi kan fuskarsa. Wani turare mai sanyiya shaka, gabadaya ta kankame jiki ba ta sami damar aiwatar da komai ba, da alama a tsorace ta ke. A hankali iskar ta lafa, ta koma ta kafe shi da ido, gyalenta ya mika mata, ta sa hannu ta karba tana yi masa kallo mai lumshe yadda ta dinga bude ido tana rufewa shi ya fi komai rikita shi, ya dinga jin wani abu a jikinsa, wanda ya kasa fahintar mene ne ya shiga shakku ya hau waiwaye- waiwaye. 22 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd Yanzu ya fi tsammanin ko shi kadai ke ganinta musamman yadda ya ga hankalin jama'ar da ke gilmawa babu wanda ke kallon inda suke. Ya maida ido kanta yana satar kallonta, tun daga kafafunta har zuwa fuska. Karamar riga ce a jikinta wadda ta manne a fatar jikinta, hakan ya taimaka gurin bayyanar duk wata baiwa da mahaliccinmu ya yi mata, sai siket wanda bai wuce kaurinta ba, ga wani tsage daga tsakiyarsa a zahiri duk wani dan Adam da ya dora ido а kanta kallo daya ba zai wadace shi ba, sam ba ta da makusa. Tana da kyau daidai nata, manyan idanunta su ke kara fito da ita, su ke kara mata kwarjini, hancinta bai cika tsayi ba. Dimple dinta kan lotsa duk lokacin da ta ke magana ko murmushi, hakan na daya daga cikin abin da ke kayata fuskarta, wankan tarwada ce tana da haiba, fatarta a murje subul-subul, kai da gani ka san an ci an tada 23 KA AURE NI!-I Biikisu H.Mutin kai sai dai akwai sangarta a tattare da ita, "KA AURE NI". Ta katse masa tunani da fadin haka, ya yi saurin dubanta ta sake maimaita, "KA AURE NI". Ya sake ware idanunsa bakidaya a kan fuskarta da alamun mamaki kwance a fuskarsa yanayinta mai sanyi in ka dube ta ba za ka yi zaton in ka sa yatsa a bakinta za ta iya cizawa ba, ZA KA AURE NI? Yanzu kam ganin komai ya ke yi tamkar a mafarki ya yi saurin kawar da kai. "Wannan wace irin mace ce?" ya fada a ransa tare da sake tamke fuska, ya soma kokarin barin gurin ta yi saurin shan gabansa, "Za ka aure ni?" Yanzu kam abin nata ya soma ba shi dariya, daga dukkan alamu kunnenta babu dadi, amma bara ya biye mata ya ga iya gudun ruwanta. Cikin karfin hali ya bude baki ya ce. "Zancenki ya fi kama da zolaya ko na ce tatsuniya. 24 KA AURE NII-1 Bilkisu H.Muhd "Ka amsa min tambaya ta, don na tabbatar maka da ba mafarki ka ke ba". "O.k shi ke nan, me zai hana na yi yadda ki ka ce?" Ta yi murmushi tare da 6alle 'yar Karamar post din da ke rike a hannunta, ta dauko wani dan karamin kati ta mika masa, ba ta sake cewa komai ba ta daga masa hannu. "Bye-bye". Yana kallo ta shige motarta ta tada shi sai da ta bace wa ganinsa ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya ya zuba wa katin ido yana jujjuya shi a hannunsa, adireshinta ne a jiki da lambar wayarta. Ya jinjina kai. "Inda ranka ka sha kallo, ga ta dai kalau da ita ba alamun da suke nuna tana da tabin hankali, sai dai in ta yi magana". Ya daga kafada tare da tabe baki. *** *** *** 25 KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd Babban boadroom ma'aikata ne cike sun tattara hankali kan bayanin Injiniya Sunusi wanda a ke wa lakabi da Injiniya Bature ga dukkan alamu shi ne mamallakin kamfanin, yadda suka nutsu zai tabbatar maka da cewar meeting din mai muhimmanci ne. "Humaida". "Dad! Dad!! Zai aure ni". Injiniya Bature ya ce, "Wa?" Da alamun ya mance inda ya ke. M.D ya yi gyaran murya hakan ya fargar da shi abin da suke gudu shi ne ya faru. "Please ina son ku ba ni guri zan gana da baby". Al'adarsa ce hakan, Humaida ta fi komai da kowa muhimmanci ya kan bar duk abu mai muhimmanci don ba ta hakkinta, rashin hakan ba karamin tashin hankali zai ja masa ba. 26 KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd Jama'ar sun gama ficewa, ya maida kallonsa gare ta, tsaye ta ke kerere, ya yi murmushi cikin kada kai, bai taba ganin aibunta ba duk da rashin ladabinta. "Baby me ki ke bukata?" Cike da rashin damuwa ta cе. "Dad yau mun hadu da shi, na ga ya dace da ni. Bai fahinci inda ta sa gaba ba. "Wai baby ban ce da ke ko me ye ki dinga bari sai na dawo gida ba?" Та се, "Вa zan iya ba ne, lokacin zai yi mini tsawo". Ya daure fuska, ya cе. "Ko me ye na ce da ke ki dinga bari na dawo". Ta yi raurau da ido za ta yi kuka. Da sauri ya sassauta fuska. "O.k shi ke nan, ya isa na fahince ki, gaya mini waye shi, a ina ya ke, ya sunanshi?" 27 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd Ta dan yi jum! Ya dan daki desk din da ke gabanta. "Babu na ba ki dukkan hankalina da lokacina, ina son jin abin da ki ke son sanar da ni". Cikin yanayin shagwaba ta ce. "ad ban san sunansa ba, wannan shi ne babban kuskurena, kuma yau ne na fara ganinsa". "Haba baby, ya ki ke abu kamar ba wayayyiya ba, a ina ki ka taba ganin an yi haka? Ina son ki sani ke fa ba irin 'ya'yan nan ba ce marasa galihu, ke fa 'yar gata ce 'yar gaske muna matukar sonki, muna yin komai dominki, don haka ba za ki auri miji irin na kowa ba, ke 'yar gata ce rayuwarki na da matukar muhimanci, ki yi tunani وو mana. A wahalce cike da kosawa ta ce. "Ban san tunanin me ka ke son na yi ba alhalin kai da kanka ka sanar da ni illolin da yawan tunani ke haddasawa., ka siya 28 KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd mini laptop ka aje mini radiyo, talabijin da sauran ababen debe kewa duk don kada na dinga tunani, amma yau da kanka ke son gayyato mini shi, me ya sa? Tunda na taso a rayuwata abin da na nema a lokacin ake yi mini shi. Ba ni... un go ba a cewa sai lokaci kaza, alkawari ne da ka daukar mini ba zan taba neman abu na rasa ba, please ka zamto mai cikawa, yin biris zai sanya na yi zaton ka soma kosawa". Ya kalle ta tare da sanyaya murya. "ke ce kwaya daya wadda na fi imuwa da ita duk wannan nema da na ke yi te na ke ma wa don ke na ke tare da dukkan jama'ar nan da ki ka gani, dominki na ke katsewa kai na bacci da duk wani jin dadi don na haßaka dukiyarki don kada bayan ba taina ki shiga halin ha'ula'I ki wulakanta, amma ki yi tunanin zan iya kosawa da ke?" Juya masa baya ta yi. 29 KA ANIi-1 Bilkisu H.Muhd "Dad, a wannan gabar wannan mutumin ya fi duk abubuwan da ka lissafa muhimmanci". "O.k baby na fahince ki, kina nufin shi ki ke so?" "No Dad, ba haka na ke nufi ba, kai kanka ka sani so karya ne, so ya fi komai wahala. Ba zan so wani dan Adam ba balle ya wahalar da ni,"babu abin da ke cikin soyayya face wahalarwa, musamman namiji. Ta yi matukar ba shi dariya. "Wa ya

Chapter 1 of 5