An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HAUSABOOK.COM 1
KA AURE
IN
BILKISU H. MUHD
Harafi Publlshers KaAure Ni
BILKISUHAMUHD
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
KA AURE NI-1
afiya ya ke cikin tsananin T
yunwa da gajiya, lokaci-lokaci
yakan kade jikinsa da hankici
abin da ya zame masa al'ada ke nan, haka ya
nufi unguwarsu, majalisarsu ta gama haduwa.
kyar.
"Assalamu alaikum". Ya ambata da
Sulaiman ya dube shi, da fadin.
"Ya abokina, me ye labari?"
"Sulaiman na gaji". Ya ce yana
kokarin zama.
"Yau karfe shida na bar gidan nan na
wuni ina bulayin neman aiki, amma babu
sa'a, al'amarin ya soma ba ni tsoro ina
rokon Ubangiji mahaifana na yi mini sai dai
har yau babu nasara, shekara biyar da gama
karatu in ko haka ne ban ga amfanin karatun
ba".
Abdul ya dinga dariya, ya ce.
4
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ai Alhaji tini muka je gano, in ka ce
za ka dakata neman na kai, kai ne a wahale
musamman a wannan zamanin da rayuwa ta
yi tsada, har abada in kai ba wani ba ne ba
ka samun muhimmanci ka zama tamkar
kare, in ko ka ga ana yi da kai ka san wani
ko wani ya sanka, don haka tunda na gama
sakandire ban yi ggigin karasawa ba, gwara
na yi ma zuciyata a gidada yammain dauki
wanka na fito majalissa, na yi ta kallon masu
shiga da fita, a haka wataran an samu 'yar
masu numfashi ta makale mini, ka ga shi ke
nan kakata ta yanke saka".
Yusuf ya ja tsaki, ya се.
"Lallai kam kana tare da wahala, su
kansu 'ya'yan manyan ba son talaka suke yi
ba, sun fi dafewa 'yan uwansu masu dala.
sr "Eh lallai ba ka san dawan garin ba,
Mudan ba shi labari. Ta ya ku ka hadu da
Hajiyarka?d wol
EeYusuf ya ce, "Lallai Abdul irin auren
nan Mudan ka ke son za ka yi ke nan kada
5
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
ka mance matar Mudan fa ta haife shi, ga ta dirkakkiya, ko ka san in kibna ya yi yawa
akwai illa?"
A fusace Mudan ya kalle shi.
"Eh na ji, amma a hakan ba kullum ga shi na ke ciyar da ku, kuma tunda abin hakа
ne an yi yanke ta gille".
Abdul ya gintse dariya a ciki.
"A'a aboki, afuwa".
"Allah na rantse kowa sai ya gane kurensa, ashe idanunku na kan matata? Тo
daga yau gidan nawa ma kada wanda ya kara shigar mini".
"Kyale su Mudan, wadannan ba su
san ciwon kansu ba”. Sadik ya fada.
"Wallahi ko ni na sami matar da ta fi
taka tsufa aura zan yi, yanzu ba ga shi ba ni
da na auri 'yar malam shehun ina ta fama
ba, shegiya daga an tabata sai ciki, in gari ya
waye ba za ka ga 'ya'yan kowa basai nawa
su ne bin layin kosai, ko na waina, shekara
hudu da aurc 'ya'ya hudu mai za ayi da
6
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
haka? Don haka gabadaya na kaurace wa
shegiya na gwammace na yi ta bankan
kanwa"
Mu'allim da tun dazu bai ce komai ba
ya ja tsaki.
"Kuna shiga hurumin da bai dace ba,
Sadik wannan bai dace ba".
Ya mike gida ya shige, suka bi shi
kawai da kallo. Mudansir ya ce.
"Rashi ke sanya shi zafin zuciya, ku
kyale shi gwara ma ya tafi don in ba haka ba
sai mu kwashi 'yan kallo a nan".
*** *** ***
Malam Musa mai ido daya sunan da
aka fi kiranshi da shi ke nan, talaka ne tilis
wanda babu cin yau ba na gobe, domin in ya
yi buga-bugarsa ya sami na masara ba lallai.
ne ya sami na rana ba, duk aikin da ya samu
ya kan taba, sai dai ya fi tsayawa ga likin
takalmi ko rufin laya in ta samu. Duk da
talaucinsa bai hana jama'ar
7
unguwa
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Kaunarsa ba, mutum ne shi mai iya
mu'amala da kowa.
Jama'ar unguwa ba su taba kosawa da
shi ba duk da cewar mafi akasarin jama'ar
da ke unguwar ba masu karfi ba ne, amma
hakan bai hana in an ci an rage a aiko musu
ba. Duk illahirin unguwar sukan yi masa
kara sun san halin da suke ciki, domin
talaucinsa ya wuce tsammani.
Mariya matar Musa mace ce
jajirtacciya mai tsoron Allah da sanin ya
kamata, za mu iya cewa kusan ita ce karfin
gidan. Ta kan yi komai don ta faranta wa
tilon dansu, ta kan yi duk wani aikin karfi
don ta gata taimaka wa Mu'allim. Wani
fannin in abin ya dagule musu haka Malam
Jafar zai zauna yana kwalla, ta kan danne
tata damuwar ta shiga nusar da shi,
musamman wwani fannin ya ke fadin mai
ke faruwa da su, mai ya ke ma Ubangiji da
Ya yi musu irin wannan jarrabawar? Abin
ya yi tsauri.
8
KA AURE NI!-1
Ta kan katse shi da fadin.
Bilkisu H.Muhd
"Mai ya sa ba za ka zamo mai godiya ba, ina laifi da Ubangiji ya bar mu da lafiyarmu? Ka sani duk talaucinmu akwai
wadanda suka fi mu, wadansu ma ba cin ya jarrabe su da talaucin har da rashin lafiya ya
P
dora musu. Ba ka tunanin an iya ba mu arziki ta hallakar da mu?"
Kalamanta sun sassauta zuciyarshi,.
"Mariya, na fahince ki, ni babu -abin
da ya fi daga mini hankali sai in na dubi
Baba Karami, yau da a ce yana da lafiyarshi
ba za mu shiga duk wannan halin ba. Baba
Karami yaro ne mai nasibi tun yan karaminsa, ya ya ba zan ce ba duk abu ya yl
mani yawa, lalurarsa ya tafi mini da dukkan
farin cikina". enadse
Ihun Baba Karamin ne ya katse musu
hirarsu, da gudui suka mike har suna rige- rige.
Gwara kanshi ya ke da garu yana
kuma ci gaba da tsala ihu, ga jini nan na ta
9
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
fita a kansa, duk da ya san yanayin haukan nashi bai hana shi dosar dan uwan nasa ba.
Ciwo da yakushi ya sha shi, ya samu da kyar ya daddaure shi yana goge mishi jinin fuskarshi cikin zubar hawaye, kafin su bar gurin har kansa ya kumbura.
Mariya ta hada yayi ta kyatta ashana
ta cinna, ta dora ruwa ya yi dumi, ta shiga
gasa wa Malam Musa inda Baba Karami ya jijji masa ciwo, sannan ta nufe shi shi ma
tana gasa mishi kai. Ta koma gurin Malam
Jafar wanda ke zaune ido jajir.
"Wannan rayuwar da mu ke ciki
wataran komai zai zamo labari, narar da
Mu'allim ya sami aikin yi, sai dai in na tuna
da yanayin da Baba Karami ke ciki na kan
tsinci kaina cikin tashin hankali, burina
Babnna Karami ya amfana da ilimin da ya
sadaukar da ransa da kuma duk abin da ya
mallaka ya hana ma kansa jin dai ya hana
makansa sutura da abinci mai dadi, ya
bautar dakansa duk don Mu'allim ya yi
10
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
rayuwar farin ciki, ya yi rayuwar da ta bambanta da tamu".
Ta sanyaya murya tana duban Malam
Musa.
"Amma na sani Ubangiji yana ji yana gani, in dai addu'ar uwa na amsuwa ga danta na sani burina zai cika, Mu'allim zai
taka wani matsayi na ban mamaki, sai
kawunsa ya samu lafiya ya yi alfahari da
shi"
lam Musa kawai bin ta ya ke da ka koma ya yi murmushi mai bayyanar
da tsantsar ciwo.
"Yaushe ne za mu ga wannan ranar?
Kullum tsufa kara kama mu ya ke yi, ba na
tsammanin ganin wannan ranar sai dai ina yi
mishi fitan aixlairi a cikin rayuwarsa.
Wallahi ina tausayin yarona, kullum ruwa da
iska a kanshi ya ke karewa yawon neman
aiki, káico da wannan rayuwa, talaka ya shiga uku, ka yi karatun da ake bukata,
amma aiki ya gagara samuwa, in Allah ya
11
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
yarda yarona ba zai yi rayuwar da muke yi
ba".
Sallamar Mu'alim ce ta katse musu
hira, ya risina.
"Abba sannunku da gida".
Malam Musa ya dube shi da fuskar
tausayi.
"Yauwa sannunka, kai ne da sannu.
Allah ya yi maka albarka".
"Amin Abba". Ya amsa yana
murmushi, addu'arsu ce ke sanyaya mishi
zuciya a kullum ba su kosawa da sanya
mishi albarka.
"Ya Ubangiji ka billo min da hanyar
da zan faranta musu. Ina son iyayena su ji
dadina, su yi alfahari da ni kafin su koma
gare Ka, ko ni na koma gare Ka". Ya fada a
ransa.
Ya mike jiki a sanyaye ga wani irin
jiri na dibarshi ya nufi falo, wanda ko daben
kasa babu sai wata tabarmar karauni da ke
shimfide. Ya zube a kai yana maida wata
12
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
wahalalliyar numfashi, yana son tambayar
abinci yana jin nauyin hakan.
Ya ja karamin tsaki, shi bai kawo ba
ya zai yi ya tambaya, abin da kunya kam.
Hamma ya dinga zabgawa, idanunshi
suka yi jajir, ya sake jan tsaki yunwa ba ta yi
ba, wannan rayuwar da suke ciki hatsari ce,
dole ne ya nemi mafita.
Ya kallo inda Ummanshi ke zaune da
wata kodaddiyar atamfa duk ta sha faci,
dinkin allurar hannu. Ya rankwafar da kai.
"Da izinin Allah wataran sai sun yi
farin cikin haihuwarsa, sai sun yi alfahari da
shi, sai ya nema wa kawunsa magani, sai ya
nemi arziki ta kowacce hanya ba zai yi sata
ba, bacin wannan zai yi komai don ya zama
wani.
Tuntuni yana da burin zama wani
yadda ake fadin ya hadu rashi ne kawai ya
yi masa cikas, to zai nemi kudi.
13
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Yana kallon Abbansa ya mike ya zari
takalmi wanda ya sha liki ta ko'ina, ya nufi
waje.
Tsawon awa guda yana kwance dafe
da ciki.
Wata yarinya wadda ba ta wuce
shekaru hudu ba ta yi sallama rike da kwano
a hannu.
"Umma wai ga shi in ji Mama".
Mu'allim ya maida hankali gurin, cikin sauri Umman ta mike ta karba.
"Kai masha Allah, abinci muka samu
haka kai madallah, na gode, Allah ya saka
da alkhairi ya jikan iyaye ya raya ku".
Mu'allim ya ji kamar ya fashe da ihun
kuka a duk lokacin da jama'ar unguwa suka
yi mata irin wannan ragoyi-ragoyin abincin,
ya ji tana rangada wannan godiya da addu'a
kamar wata marokiya, ya kan ji tamkar
zuciyarshi za ta fashe, wani abin takaicin ma
sai ka ga yadda abincin ya ke, wanda da
gani guntattatakin jagwalgwalon abincin
14
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
yaransu ne haka za kaga tana farin ciki da
murna tamkar an yi mata kyautar naman
kaza.
Mai sunan manya". Sunan da ta ke
kiranshi da shi ke nan, ta kwalla masakira.
"Ka fito ka ci abinci na san yunwa ka
ke ji".
Ya mike ba don ya so ba, don kawai
kada ta ga ya gwale ta.
Ta dire masa kwanon a gabanshi.
"Maza ka ci na wanke kwanon amaida
shi ko?"
Ya kada kai kurum yana kallon
kwanon, duk ya sha lamba ga abincin har da
guntattakin burodi, ga wasu kananan gashi a
ciki.
"Umma ni fa a koshe na ke".
Ya ce cikin gajiyayyar murya.
Ta yi murmushi, a tunaninta wayo ya
ke so ya yi musu don su ci kamar yadda ya
saba.
15
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Na san abin da ka ke nufi, na sani ka
fi mu bukatar ci, ji yadda ka koma duk ka yi
ramar wuni daya".
Ya sake sanyaya murya.
"Umma na ce na koshi da gaske, na ci
abinci, ki juye ki ba ta kwanon".
Kafin ta sake magana ya dauki roba a
kwando ya juye abincin, da kansa ya
dauraye kwanon ya mika wa yarinyar. Ta
mike ta raka ta har soro tana faman
rangadagodiya, duk tausayinta ya kama shi,
kwalla ne ke kokarin saukowa kan
kuncinsa. Ya yi kokarin maida shi.
*** *** ***
Majalissar su Mu'allim.
Hira ake faman yi, Sadik a gefe ya
rafka uban tagumi, lokaci-lokaci ya kan
doka tsaki, Yusuf ya tabo shi.
"Mutumin ya aka yi haka?"
Ya kara jan tsaki, ya се.
16
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Yusuf, Amina yanzu ma wai ciki ne
da ita wata biyu kacal da haihuwa amma wai
har ta sami wani cikin, mace kamar mage
yanzu na ce ta zo na kai ta a cire shi ne ta ce
in na gaji in sake ta, ai hahuwa baiwa ce, ka
ji fa! Wallahi sai ma ka ga 'ya'yan bini in bi
ka, ni kam na gaji, ina tunanin ta yadda zan
rabu da ita, cuta ce dai ta riga ta cutar da ni,
don na san babu wadda zan aura ta iya
daukar dawainiyarsu".
Yusuf ya dinga kyalkyala dariya har
yana rankwafawa, Mudan ya ce.
"Ni kam yanzu bakina alaikum ni da
tsohuwata, komai sai dai a yi mini. Yanzu
da kudi aka ce mini ga budurwa ko a ce ga
yarinya ban niaura, aurensu matsala ne, sai
kuna zaune su yi ta yi maka sakarci da
shagwaba, in ba su ga dama ba sai su dage
akan sai ka siya musu kayan kwalliya, ko su
ce ba su da bra ko pant, ni kuwa tawa duk ba
ta sanya wani bra balle pant".
17
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Nan suka kara shekeewa da dariya har
da ihu da tafi, gogan kam yana gefe yana
tunanin ta wacce hanya zai sami aikin yi.
Yaro ne ya doshi majalissarsu da wasu
manyan kuloli, ya zube a gabansa.
"Ga shi inji Hajiya". Ya fada yana
kallon Mudan.
Ai tuni ransa ya fashe.
دو" Ka je ka ce ta ba da ruwa mana.
Yaro ya ce, "Ai lemo ta ke hadawa".
"O.K, ka ce ina yi mata sannu".
Yaro ya tafi, su Yusuf tuni an gyara
zama. Ya fara kokawar bude kulolin, Sadik
ya tabo Mu'allim.
"Ta fadi gasassa, Hajiyarmu ta yunkuro".
Sai da ya yi kamar ba zai ci ba,
kamshin abincin ya daki hancinsa, tuni ya
gyara zama ya shiga ci, cike da tunani
barkatai a can karkashin zuciyarshi tausayin
kanshi ya ke yi da rayuwar da suke ciki shi
da mahaifansa.
18
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
*** *** ***
Tun daga nesa ta gano shi, ta kasadauke idanunta daga kanshi, tun
tasowarta ta ke ganin jinsin mutane iri-iri
amakarantarsu a unguwarsu, a kasashen
waje, 'ta;yan mulki da 'ya'yan manyan
kusoshi, amma ba ta ga wanda ya gigita
tunaninta ba kamar wannan.
Vyawunsa ya shahara, wani irin
kyav ne da shi, komai na jikinsa yana da
burgewa, idonsa, yankan bakinsa dan
karami, gashin kansa tamkar na larabawa,
irin mazan nan ne da ake wa lakabi da
giant.. abu guda ne ya rage wa kywaunsa
armashi, wato suturar jikinsa wadanda
dukkaninsu ba za su wuce dubu daya da dari
biyar ba. Sai takalman kafarsa na danko.
Ta cje lee tare da kai wa sitiyarin
mota duka.
19
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Oh shet! A nan matsalar ta ke,
talaka! Wannan ya fi dacewa da dan
sarauta!"
A hankali ta ji ya soma burge ta, za ta
so ya zama mallakinta nata ita kadai. Mace
ce mai matukar son duk abin da ya ke da
kyau, don haka duk abin da ya dangance ta
ya kan zama mai matukar kyau.
Ta san ta kan abu mai kyau, don haka
Dad dinta ya ba ta zabi akan sabon gidan da
suka koma, ita ce ta wassafa irin ginin da ta
ke so, bai ja ba ya yi yadda ta ke so, gidan
ya yi fiye da tunanin Dad din nata. Ta kuma
tsara yadda ta ke son bedroom da sitroom
dinta ta ke bukatar ya kasance, har ma da
bandakinta.
Ta sake maida kallonta gaMu'allim
wannan karon takardun da ke rike a
hannunsa sun zube kasa, ya durkusa yana
kwashewa.
Ya mike yana kade jiki da hankicif.
Ta sauke ajiyar zuciya.
20
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
"Ya kamata a ce ya fi haka haske,
rana ta dafar da shi, asalinsa fari ne ga yadda
99
ya tsaya a wahalallliyar ranar nan
Tana son fitowa daga cikin motar, sai
dai kwalliyar ranar ne ke ba ta tsoro.
Kokarin tsallaka titi ya ke, ta saki wata
gigitacciyar hon, duk sai ya rikice ya kalio
inda motar ke tsaye cike da takaici. Bai ga
kowa ba, duk da yana cike da jin haushin
mamallakin motar hakan bai hana shi
jinjinawa ba.
Tuni ya nutsu ya dauke kai daga
kallon gurin, a karo na biyu ta sake sakin
wani hon din, wanda ya fi na farko
rikitarwa. Ya gama tsarguwa ya tabbata shi
ake yi wa hon din, to sai dai me? Kaf
mutanen da ya sani babu wanda ya taba
mallakar karamar motar ma balle wannan,
don haka bai yaudari kansa da zuwa gurin
ba balle a gwale shi. Hakan ya burge ta, tare
da kara masa wani matsayi a zuciyarta, da
alama mai aji ne.
21
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ta saki murmushi, ta bude murfin
motar ta zuro kafafunta, wani irin takalmi ya
gani mai masifar tsini. Da sauri ya basar
saboda ganin da ya yi tana doso inda ya ke,
ko dar bai ji ba a zuciyarsa, don ya san babu
wanda zai ce ya ci masa wani abin..
Ta ja tunga ta tsaya a gabansa tana
faman taunar cingam, wani irin iska mai
karfi ya taso cak ya dauke yalolon gyalen da
ke yane a kanta ya watsar da shi kan
fuskarsa. Wani turare mai sanyiya shaka, gabadaya ta kankame jiki ba ta sami damar
aiwatar da komai ba, da alama a tsorace ta
ke.
A hankali iskar ta lafa, ta koma ta kafe
shi da ido, gyalenta ya mika mata, ta sa
hannu ta karba tana yi masa kallo mai lumshe yadda ta dinga bude ido tana rufewa
shi ya fi komai rikita shi, ya dinga jin wani
abu a jikinsa, wanda ya kasa fahintar mene
ne ya shiga shakku ya hau waiwaye- waiwaye.
22
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Yanzu ya fi tsammanin ko shi kadai
ke ganinta musamman yadda ya ga hankalin
jama'ar da ke gilmawa babu wanda ke
kallon inda suke.
Ya maida ido kanta yana satar
kallonta, tun daga kafafunta har zuwa fuska.
Karamar riga ce a jikinta wadda ta manne a
fatar jikinta, hakan ya taimaka gurin
bayyanar duk wata baiwa da mahaliccinmu
ya yi mata, sai siket wanda bai wuce
kaurinta ba, ga wani tsage daga tsakiyarsa a
zahiri duk wani dan Adam da ya dora ido а
kanta kallo daya ba zai wadace shi ba, sam
ba ta da makusa.
Tana da kyau daidai nata, manyan
idanunta su ke kara fito da ita, su ke kara
mata kwarjini, hancinta bai cika tsayi ba.
Dimple dinta kan lotsa duk lokacin da ta ke
magana ko murmushi, hakan na daya daga
cikin abin da ke kayata fuskarta, wankan
tarwada ce tana da haiba, fatarta a murje subul-subul, kai da gani ka san an ci an tada
23
KA AURE NI!-I Biikisu H.Mutin
kai sai dai akwai sangarta a tattare da ita,
"KA AURE NI". Ta katse masa tunani da
fadin haka, ya yi saurin dubanta ta sake maimaita, "KA AURE NI".
Ya sake ware idanunsa bakidaya a kan
fuskarta da alamun mamaki kwance a
fuskarsa yanayinta mai sanyi in ka dube ta
ba za ka yi zaton in ka sa yatsa a bakinta za
ta iya cizawa ba, ZA KA AURE NI? Yanzu
kam ganin komai ya ke yi tamkar a mafarki
ya yi saurin kawar da kai.
"Wannan wace irin mace ce?" ya fada
a ransa tare da sake tamke fuska, ya soma
kokarin barin gurin ta yi saurin shan
gabansa, "Za ka aure ni?"
Yanzu kam abin nata ya soma ba shi
dariya, daga dukkan alamu kunnenta babu
dadi, amma bara ya biye mata ya ga iya
gudun ruwanta. Cikin karfin hali ya bude
baki ya ce.
"Zancenki ya fi kama da zolaya ko na
ce tatsuniya.
24
KA AURE NII-1 Bilkisu H.Muhd
"Ka amsa min tambaya ta, don na
tabbatar maka da ba mafarki ka ke ba".
"O.k shi ke nan, me zai hana na yi
yadda ki ka ce?"
Ta yi murmushi tare da 6alle 'yar
Karamar post din da ke rike a hannunta, ta
dauko wani dan karamin kati ta mika masa,
ba ta sake cewa komai ba ta daga masa
hannu.
"Bye-bye".
Yana kallo ta shige motarta ta tada shi
sai da ta bace wa ganinsa ya sauke wata
doguwar ajiyar zuciya ya zuba wa katin ido
yana jujjuya shi a hannunsa, adireshinta ne a
jiki da lambar wayarta. Ya jinjina kai.
"Inda ranka ka sha kallo, ga ta dai
kalau da ita ba alamun da suke nuna tana da
tabin hankali, sai dai in ta yi magana".
Ya daga kafada tare da tabe baki.
*** *** ***
25
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
Babban boadroom ma'aikata ne cike
sun tattara hankali kan bayanin Injiniya
Sunusi wanda a ke wa lakabi da Injiniya
Bature ga dukkan alamu shi ne mamallakin
kamfanin, yadda suka nutsu zai tabbatar
maka da cewar meeting din mai muhimmanci ne.
"Humaida".
"Dad! Dad!! Zai aure ni".
Injiniya Bature ya ce, "Wa?"
Da alamun ya mance inda ya ke.
M.D ya yi gyaran murya hakan ya
fargar da shi abin da suke gudu shi ne ya
faru.
"Please ina son ku ba ni guri zan gana
da baby".
Al'adarsa ce hakan, Humaida ta fi
komai da kowa muhimmanci ya kan bar duk
abu mai muhimmanci don ba ta hakkinta,
rashin hakan ba karamin tashin hankali zai
ja masa ba.
26
KA AURE NI!-I Bilkisu H.Muhd
Jama'ar sun gama ficewa, ya maida
kallonsa gare ta, tsaye ta ke kerere, ya yi
murmushi cikin kada kai, bai taba ganin
aibunta ba duk da rashin ladabinta.
"Baby me ki ke bukata?"
Cike da rashin damuwa ta cе.
"Dad yau mun hadu da shi, na ga ya
dace da ni.
Bai fahinci inda ta sa gaba ba.
"Wai baby ban ce da ke ko me ye ki
dinga bari sai na dawo gida ba?"
Та се, "Вa zan iya ba ne, lokacin zai
yi mini tsawo".
Ya daure fuska, ya cе.
"Ko me ye na ce da ke ki dinga bari
na dawo".
Ta yi raurau da ido za ta yi kuka. Da
sauri ya sassauta fuska.
"O.k shi ke nan, ya isa na fahince ki,
gaya mini waye shi, a ina ya ke, ya sunanshi?"
27
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
Ta dan yi jum! Ya dan daki desk din
da ke gabanta.
"Babu na ba ki dukkan hankalina da
lokacina, ina son jin abin da ki ke son sanar
da ni".
Cikin yanayin shagwaba ta ce.
"ad ban san sunansa ba, wannan shi
ne babban kuskurena, kuma yau ne na fara
ganinsa".
"Haba baby, ya ki ke abu kamar ba
wayayyiya ba, a ina ki ka taba ganin an yi
haka? Ina son ki sani ke fa ba irin 'ya'yan
nan ba ce marasa galihu, ke fa 'yar gata ce
'yar gaske muna matukar sonki, muna yin
komai dominki, don haka ba za ki auri miji
irin na kowa ba, ke 'yar gata ce rayuwarki
na da matukar muhimanci, ki yi tunani
وو
mana.
A wahalce cike da kosawa ta ce.
"Ban san tunanin me ka ke son na yi
ba alhalin kai da kanka ka sanar da ni illolin
da yawan tunani ke haddasawa., ka siya
28
KA AURE NI!-1 Bilkisu H.Muhd
mini laptop ka aje mini radiyo, talabijin da
sauran ababen debe kewa duk don kada na
dinga tunani, amma yau da kanka ke son
gayyato mini shi, me ya sa? Tunda na taso a
rayuwata abin da na nema a lokacin ake yi
mini shi. Ba ni... un go ba a cewa sai lokaci
kaza, alkawari ne da ka daukar mini ba zan
taba neman abu na rasa ba, please ka zamto
mai cikawa, yin biris zai sanya na yi zaton
ka soma kosawa".
Ya kalle ta tare da sanyaya murya.
"ke ce kwaya daya wadda na fi
imuwa da ita duk wannan nema da na ke yi
te na ke ma wa don ke na ke tare da dukkan
jama'ar nan da ki ka gani, dominki na ke
katsewa kai na bacci da duk wani jin dadi
don na haßaka dukiyarki don kada bayan ba
taina ki shiga halin ha'ula'I ki wulakanta,
amma ki yi tunanin zan iya kosawa da ke?"
Juya masa baya ta yi.
29
KA ANIi-1 Bilkisu H.Muhd
"Dad, a wannan gabar wannan mutumin ya fi duk abubuwan da ka lissafa muhimmanci".
"O.k baby na fahince ki, kina nufin shi ki ke so?"
"No Dad, ba haka na ke nufi ba, kai
kanka ka sani so karya ne, so ya fi komai wahala. Ba zan so wani dan Adam ba balle
ya wahalar da ni,"babu abin da ke cikin
soyayya face wahalarwa, musamman
namiji.
Ta yi matukar ba shi dariya.
"Wa ya