ce tayi sanadiyar auren su, don shi baiga abunda zaiyi da ramlart ba, ya aure tane bisa umarnin Hajja amma kuma abun da yagani ya basa mamaki, meya sa Ramlart ta ke son cutar da Hajja tabbas akoi wani abu daya kamata ya sani .
Jin ana kiran sallan azahar ne yasa ya tashi, ya nufi toilet din dake cikin falon, alwala yayi yafito, ba bata lokaci ya nufi masallacin dake cikin gidan ,inda anan ne yake sallah tare da sauran jama'ar unguwar in dai yana gari, to jam'i baya wuce shi.
Yau takama Ranar Monday ne, a gidan Alhaji Abdullahi Turaki sun tashi da shirye shiryen, taryan mai gidan , Wato Alhaji Abdullahi Turaki a yaune jirgin sa zai sauka a Nigeria daga Saudiyya , dan ya kwashe kimanin wata daya kenan baya kasar yane yin Umrah, kuma a yau ne jirgin su zata sauka a Nnamdi Azikiwe international airport, hakan yasa kowani ma aikaci na cikin gidan ya ke kokarin ganin cewa ya kammala aiyukan sa a kan lokaci, duddah cewa har yanzu Hajja tana asibiti ba a sallamo ta ba.
Hajja zaune a bakin gadon dake cikin VIP ward. Tana cikin shiga ta alfarma, ta cire kayan asibitin,fuskarta na cike da annuri , a gefe guda tana gudiya ga Allah da ya azurta ta da samun lafiya, bayan ta cire tsammani. Dr Farida ce ke rik'e da wasu, takardu cikin kulawa, take duba takardun.
Hajja ta kalleta tace .
"Likita, Allah ya saka da alheri, nagode kwarai da gaske. Gaskiya na ji daɗin irin kulawar da kika bani. Har cikin zuciyata na keji kamar ƴa ta ce ke."
Wani irin cute smile Dr Farida ta sake tare da d'an lumshe idon ta, chan kasan zuciyarta tana jin wani irin sanyi yana ratsata a hankali tace:
"Alhamdulillah Hajja. Ni ma na ji daɗin zamana tare da ke." Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana, nima kamar dadata nake Jin ki a raina.
Hajja tace.
"Zan so sanin inda kike zaune...ko zamu ci gaba da zumunci, kinga watarana zanga dadar taki nima, sai muyi zumunci, takarasa maganar fiskar ta d'auke da murmushi."
da ɗan murmushi, Dr Farida tace:
"Zan baki address ɗinmu Hajja, ai zumunci alheri ne, kuma dada ta zataji dad'i,kullum sai ta tambayeni jikin ki."
Jin hakan ne yasa Hajja kara jin dad'i ,haka Dr Farida ta rubuta ma Hajja address dinta , karb'ar takardar Hajja tayi tare da bawa Lami mai aikinta ta saka mata shi a cikin jakarta.
A dai dai lokacin, ne AA Turaki ya shigo cikin dakin, kamar kullum yauma yana sanye da wasu hadaddun fararen suit wanda aka kashe makudan kud'ad'e wajen sayan su, ba karamin kyau yayi ba, Sani PA ne a bayan sa, batare da ya Kalli kowa ba ya wuce wajen da Hajja take zaune direct, har kasa ya tsuguna ya gaishe ta, cike da farin cikin ganin shi Hajja ta shafa kanshi tare da jero masa addu'oi .
Haka yasa su Lami suka kwashe duk wani abu da Hajja take bukata , sauran kayan kuma haka Hajja tace wa Dr Farida, arabawa mabukata.
Dakan shi ya kama hannun Hajja haka ya riketa har jikin wata bakar mota Rolls Royce a hankali ya taimaka mata ta shiga, bayan ta shiga ne shima ,ya shiga ya zauna a gefen ta, haka motocin suka shiga tafiya a cikin nitsuwa, Hajja ce take dağawa Dr Farida hannu, dake tseye tana kallon tafiyan su Hajja.
Haka kawai takejin son matar a cikin zuciyar ta duddah d'an nata sam bashi da hali sai na girman kai amma Allah ya gani itakam tana son tsohuwar, ganin motocin sun fita daga cikin harabar asibitin ne yasa Dr Farida ta juya domin komawa cikin Office din ta.
💫 ƘAUNA DA KADDARA 💫
✍️Mrs Alkali
Page 1️⃣3️⃣
Da misalin karfe 8 30pm na dare Babban falo na cikin gidan AA Turaki. Kowa yana zaune – Hajja, Alhaji Abdullahi Turaki, AA Turaki da Ramlart. cike da natsuwa, suke zaune da alama akoi wata muhimmiyar taron da zasu gabatar, ganin yanda kowa ya natsu ya bawa zaman muhimmanci.
AA Turaki ya yi gyaran Murya,a lokaci guda yana kallon kowa da ke cikin falon, da idanun sa masu kaifin basira:
"Alhmdulillah, nagode da ku ka halarci wannan zaman .Yana da muhimmanci a san gaskiya, musamman idan lafiyar mahaifiya ta shiga hadari, yana da muhimmanci, a san waye yake da alhakin faruwar hakan."
Ramlart ce ta daure fuskar ta, hannunta na Wani irin rawa. Ta kama hijab dinta da karfi ta rike ,don boye damuwar ta. Hajja na kallonta,cike da mamakin ganin yanda yanayin ta ya sauya a lokaci guda, Alhaji Abdullahi ya zuba idanun sa cikin natsuwa, yana karewa kowa kalloh ,dan bakaramin mamaki ya shiga ba da aka sanar dashi cewa Hajja taci wani sinadari a cikin abinci, wanda hakan harya kaita ga kwanciya a asibiti, Dan haka ne ma ya sa shi ya dawo cikin gaggawa.
AA Turaki ya juyo da remote, dauke a hannunsa ya danna yana cewa:
"Ga wani abu da zan so kowa ya kalla..."
Ya kunna TV, ya buɗe CCTV footage na kitchen na sashin Hajja.
Kamar wutar lantarki ne ya d'auke a dakin – shiru ne ya ratsa ko ina. Ramlart ta saki wani ihu cikin firgici, ta kifa kanta a gwiwa tana rusa kuka.
cikin kuka tace:
"Wallahi... Sharrin shaidan ne... Na yi kuskure kuyafe mini!"
Cike da mamaki da radadin zuciya Hajja da take cikin shock din abunda idanwan ta suke gane mata tace:
"Ke ce? Ramlart... Me na miki har kika son kashe ni?" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.
Alhaji Abdullahi ne ya tashi tsaye, ya dube ta da idanu masu cike da rashin yarda, na yanda ramlart tayi disappointing nasa, yace.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Me nake gani haka ".
AA Turaki ne ya natsu yana kallon mahaifinsa, cikin Wani irin murya yace.
"Ina son ka min izini in sake ta. Wannan ba matar aure bace... Ba zan iya ci gaba da zama da ita ba." Ya karasa maganar cikin zafin rai.
Hajja ce ta yunkuro tana share hawayen ta tace
"Ni dai dama, na zaci ta kirki ce shiya sa na zaɓa maka ita , sabi da na yaba da hankalin ta!amma a yau ba zan hana Ka sake ta, ba Yero i!"
Alhaji Turaki ne ya daga hannu, yace
"A'a... a dakata da yanke hukunci. Wannan lamarin sai mun tattauna da iyayenta. Ba a yanke hukunci cikin fushi. Zamu tuntubi magabatan ta, in rai ya baci bai kamata hankali ya gushe ba."
Alhaji Abdullahi cike da gargaɗi yace.
"Ramlart, abin da kika aikata babbar fitina ce. Amma tun da kin karbi laifinki zamu ci gaba da bincike. Ba zamu yanke miki hukunci a cikin fushi ba."
Hajja ce ta share hawayen ta, tare da cewa.
"Ramlartu kinbani mamaki , amma kisani ba zan sake yarda da ke cikin sauƙi ba."
*Ramlart ce ta rushe da kuka, ta rarrafa kusa da AA Turaki tana kokarin riƙe kafafun sa tace.
"Don Allah... kayi hakuri. Ka bani dama na gyara..."
Wani irin kallo AA Turaki ya jefa mata a lokaci guda ya miƙe, yana duban ta da tsananin bacin rai a fuskar sa Yace:
"Ba ni da damar yanke hukunci yanzu... Kamar yan da Baffah ya ce ba za'a yanke miki hukunci a cikin fishi ba, amma nasan daya – bana jin zan iya sake aminta da ke a karo na biyu."
Wani irin kuka mai karfi Ramlart ta saki .
A bazata suka ji saukan muryan AA Turaki "Hajja kuyi hakuri amma ina son ramlart ta bar gidan nan har zuwa lokacin da Baffah ya gama binciken sa".
Hajja da Alhaji Abdullahi Turaki suna gefe suna sauraron sa cikin mamaki da kulawa.
Ramlart ta saki hawayen nadama tana kokarin yin magana, amma bakinta ya kasa furta komai.
Cike da dottaku Alhaji Abdullahi Turaki yace.
"Ramlartu, ki karɓi maganar mijinki da zuciya mai kyau. Ki koma gida, ki nutsu. Ki bani Lokaci na gana da iyayen ki kamar yanda suka bamu amanar ki Insha Allahu za a miki hukunci bisa adalci".
Cikin kunar Zuciya Hajja tace.
"Alhaji da kayi hakuri ka bar yaronnan ya sauwake mata, karfa kamanta rayuwata taso ta salwantar".
Alhaji Abdullahi ne ya dagawa Hajja hannun alamar yagama yanke hukuncin sa.
Ramlart ce ta miƙe a hankali, kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki. juyawa tayi da kwalla a idonta, zuciyarta cike da rauni da mamakin irin wannan hukunci daga gidan da take tunanin tana da iko da shi, ta gama mallakar shi, shin tayaya ma tayi sakacin mantawa da cewa za'a iya samun CC camera a kitchen, haka ta ja kafafun ta ta wuce zuwa part din ta domin iban kayan ta da zata tafi da su, a gefe guda kowa zuciyar ta na cike da tsoro da fargaban abunda zata fad'awa iyayen ta.
💫 ƘAUNA DA KADDARA 💫
✍️Mrs Alkali
Page 1️⃣4️⃣
UNGUWAR WUSE II ABUJA
Gida ne mai dauke da ginshiƙai masu salo na zamani .
Alhaji Musa Ibrahim tsohon ma’aikacin gwamnati ne wanda yayi aiki har tsawon shekaru fiye da 30 a Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida kafin yayi ritaya. Mutum ne mai gaskiya, rikon amana da tsananin tsoron Allah. Bayan ritayarsa ya koma harkar koyarwa a masallacin unguwa da hidimar al’umma.
Yana tare da matar sa Hajiya Rakiya, uwargidan Alhaji Musa, mace ce mai nutsuwa da kamun kai, ta taso da 'ya'yanta cikin tsantsar tarbiyyar addini da mutunci. Yaya biyu mata Allah ya azurta su da samu , Aunty hauwa da kuma autar ta ramlart,Ta kasance uwa ta gari, mai tausayi da hakuri, kullum cikin rokon Allah da yi wa 'ya'yanta fatan alheri. Tana da nutsuwa da girmama kowa da kowa, komai matsayinsa.
A yanzu aunty hauwa tana gida a gaban iyayen ta tare da ya'yan ta guda biyu, sakamakon mijin ta da Allah yayiwa rasuwa kimanin watanni biyar dasu ka wuce, aunty hauwa macece mai sanyin hali da tsaron Allah, Şaban'ın ramlart da tun tashin ta ta kasance mai tsiwa da son abun duniya, amma a tashi d'aya baza ka taba gane hakan ba sai ka zauna da ita na tsawon lokaci, babu irin nasiha da fad'a da ba a mata a gidan shiya sa ma take badda sawo tana zuba iya shegen ta batare da sanin iyayen ta ba ita da aminiyar ta zuly.
Misalin karfe 8 00am na safe a daidai lokacin da Ramlart ta iso gidan su da jaka a hannun ta. Fuskar ta cike da damuwa da tashin hankali, amma duddah hakan tana ƙoƙarin danne komai, bata son a fahimci hakan.
Hajiya Rakiya zaune take A babban falon gidan, mata ce mai kamala tana sanye da hijabi, hannun ta na rike da littafi tana karatun Qur’ani. Alhaji musa, dattijo mai kamala yana zaune a gefen ta yana karanta jaridan daily trust. Agefe guda wasu yara biyu ne da ke wasa a gefe, suna ta ya'n tsalle tsallen su.
Aunty Hauwa ce ta shigo daga kitchen tana ɗauke da tray, a hannun ta.
A daidai lokacin ne ramlart ta turo k'ofar falon bakin ta d'auke da sallama.
Aunty hauwa ce ta amsa mata tare da juyawa, ganin kanwar ta ne yasa ta saki wani murmurmushi tare dacewa.
"Laa! Ramlart! Masha Allah, sannu da zuwa." Kece a gidan yau .
Yaran ne suka tashi da murna suka rungume Ramlart suna ihun ganin ta tare da cewa.
"Aunty Ramlart! Aunty Ramlart!" Oyoyohh.
Mami dake karatun Qurani ne ta juyo jin irin ihun da yaran keyi na murnan ganin ramlart din, ganin ramlart da tayi da jakane yasa ta rufe littafin hannun ta tare da ajiye shi a gefen table d'in dake kusa da ita tace.
"Ramlart? Lafiya kike tafe da sassafe haka ba tare da sanarwa ba?"
Wani irin murmushin dole RAMLART ta ƙoƙarta ta kwakulo shi a fatar baki tace.
"Wallahi Mami, kawai na gaji ne da komai. Ina bukatar hutu. Zuciyata na bukatar natsuwa, shine nace barin zo na ganku."
Sai a lokacin ne Baba ya kalle ta sosai kafin yace
"Ramlart, akwai abinda ke damunki. Ki gaya mana gaskiya. Mun san halinki."mu muka haifeki.
RAMLART ce ta zauna a ƙasa, ta dora kai a gwiwar Mami tace .
"Baba, Mami… babu wani abu. Komai dai dai yake. Ku yarda da magana ta hutawa nazoyi."
Mami ce ta shafa bayanta, cikin hikima tace.
"Ko da wani abu ne, ki sani iyayenki muna tare dake. Amma kina buƙatar fadin gaskiya don samun mafita, sabi da haka in akoi damuwa kisanar da mu."
Wasu hawaye ne suka gan garo mata, RAMLART ta sa hannu ta ɗan share hawayen, tana kallon gefe, sabi da bata son su fahimta:
"Na sani Mami... Amma yanzu ba zan iya ba. Kawai ku yarda dani."
Ta karasa maganar cikin karfin hali yayin da zuciyarta ke cike da tsoro da nadama – amma har yanzu ba ta da ƙarfin fadin abinda ya faru, wa su baba , dan kuwa tasan kwanan zancen .
Da misalin karfe 9 30pm na dare , falon ya lafa da hayaniya. Baba da Mami sun wuce ɗaki, yaran Aunty hauwa suna bacci, a d'akin su.Aunty Hauwa tana zaune da Ramlart a cikin falo, suna kallon wani series.
Aunty Hauwa ne ta zuba mata ido, tana kallon fuskarta da ke nuna alamar damuwa da ƙin gaskata cewa komai lafiya yake kamar yadda tafad'awa iyayen nasu.
Cikin murya mai rauni, cike da tausayi, Aunty hauwa tace:
"Ramlart... Kince komai lafiya, amma ni ‘yar uwa ce gareki. Kina cikin wani irin hali... kuma duk duniya bayan iyayen mu ba wanda yake fahimtar ki sama dani, idan ba ki fad'a mini damuwar ki ba wazaki fad'a wa."
Ramlart ta ɗan ɗaga ido, ta ƙara sadda kai Ƙasa, tana wasa da yatsun hannunta.
"Wallahi Aunty... Ina jin Wani irin Abu a raina, amma bani da ƙarfin gaya muku komai."
Cikin nazarin ta Aunty hauwa tace .
"Toh ki saurari zuciyarki. Idan akwai wani abu da ke cutar da ke a ciki, wallahi bayan iyayen mu dani ‘yar uwar ki ba wanda zaki iya fad'awa damuwar ki. Duk abinda zai faru, kisani muna tare da ke . Amma kisani ita gaskiya zata iya fitar da ke daga cikin duhu."
Jin abun da Aunty hauwa ta fad'a ne yasa Ramlart ta fashe da kuka, Aunty Hauwa ta rungume ta. Sai da ta dan yi kuka sosai kafin ta lafa, ta na ta sauke ajiyar Zuciya.
Cikin sanyi murya RAMLART tace .
"Aunty... Na shiga uku. Na aikata abu da har yanzu ban yarda da kaina ba... Amma ina jin tsoro, bana son su baba susani, in sunji zasuyi fishi dani."
*(Aunty Hauwa ta dafa kanta, tana girgiza kai da tausayi.)*
Aunty hauwa ce ta dafa kafadar ta tace .
"Ina tare da ke, ko me kika aikata. Amma dole ne ki tunkari su baba da abin da kika aikata. Idan ba yanzu ba, gobe zai iya bayyana. Karki bari shaitan ya ci gaba da rinjayar ki a al amuran rayuwar ki."
Ramlart ta share hawayenta, tana jinjina kai, alamar ta gamsu da maganar Aunty hauwa
Baba ne zaune a gefen gadon sa Mami ne ke shafa masa man zafi a kafafun sa, sanye yake da farar jallabiya .Haske kadan ne a cikin ɗakin.
Cikin nitsuwa Mami tace "Baban ramlart ,kasan fa har yanzu Ramlart bata ce mana komai ba akan dalilin zuwanta gida,kuma bata taba kwatanta hakan ba."
Ajiyar Zuciya Baba ya sauke yace"Na lura da ita tun lokacin da ta zo. Da alama akwai abinda ke damunta amma tana boyewa."
Cikin nitsuwa Mami tace:
"Na tambaye ta cikin lallama, sai tace hutu kawai take bukata. Amma ni uwa ce, ina ji a zuciyata akwai wani abu fiye da hakan."
Baba da ke kallon Mami yace:
"In har akwai wata matsala tsakaninta da mijinta, zai fi kyau mu bar ta ta bayyana da kanta. Amma in hakan ya gagara, zan tuntub'i Alhaji Abdullahi Turki sai muji me ke tafiya."
Mami ce ta dan girgiza kai tace:
"Allah ya shiryeta. Ina fatan kar hakan da muke tsoro ne ya faru... kar dai zaman aurenta ya fara tangal-tangal."
"Bana son kisaka damuwar komai a ranki Duka rayuwar jarabawa ce. Amma , dole mu yi addu’a sosai akan yaran mu." Cewar baba dake Shirin kwanciya dan tagama shafa masa man zafin.
Mami ce tace "insha Allahu, Zan yi azumi gobe, in roki Allah ya warware mata komai. Koda akwai kuskuren ta, Allah ya gyara tsakaninsu, dan inaji ajiki na zuwan nata bana banza bane."
Hakan yana da kyau Allah ya kaimu goben cewar baba.
💫 ƘAUNA DA KADDARA 💫
✍️Mrs Alkali
Page 1️⃣5️⃣
Misalin qarfe 5:30pm na yanma motar Alhaji Turaki ne ke shigowa harabar gidan, tare da ta AA Turaki, a yau bai dauko bodyguard din sa ba daga Motar su Hajja sai motar shi da driver ke jan shi a baya.
Alhaji Musa da Mami suna zaune a falo, yayin da Ramlart take gefen Mami da hijab a jikinta, amma fuskarta cike da shakku da jin nauyin su don sun titsiyeta a gaba sai ta fad'a musu dalilin zuwan ta gidan.
Jin an bud'e gate d'in gidan ne, ga kuma karan motoci alamar sun shigo harabar gidan ne ya sa baba ya daka ta da tambayar ramlart.
Ba a jima ba suka ji an yi nocking din kafar falon, ramlart ce ta tashi da sauri ta nufi k'ofar falon dama tana Allah Allah tasa mu dama ta zullewa su baba sai gashi dama ta samu, bud'e k'ofar tayi batare da tayi tsammanin ganin sa ba ta ganshi tsaye a bakin k'ofar.
Yayi shigar alfarma; yau babban riga fara wacce ta sha ɗinki na zamani, a jikin shi ,ga agogon Rolex mai uban tsada a hannun shi, wasu takalma half cover shoes black in colour masu tsada ne sanye a kafafun sa, ga wani sassanyan kamshin turare mai daɗin ƙamshi, da yaci ka wajen, a hankali ya tako , cikin nutsuwa da izza, fuskarsa cike da kwanciyar hankali da tsantsar kamewa. Kamar wani saraki, haka ya shigo cikin falon bakin sa dauke da sallama kasa kasa.
Ramlart ce ta zuba masa ido, kamar yau ta fara ganin sa.
Idanunta suna ƙara gaskata mata cewa babu wani da'namijin da ya kaisa kyau. zuciyarta ce ta buga da karfi, kamar ana buga gangar yaki. Har ya wuce ta bata sani ba Ta zuba masa idanu tanabin sa da kallo ba tare da ta iya ɗauke idanunta ba. tayi matuƙar rikicewa. A zuciyarta tana jin Wani irin ciwon son sa yana kara tasowa a cikin zuciyar ta.
Jin sallama ne ya katse mata tunanin ta ganin Baffah da Hajja ne yasa ta sunkuyar da kanta kasa , zuciyar ta na dukan uku uku, shikenan tata ta kare, dan batayi zaton cewa yana tare da su Hajja ba.
Cikin wani juyin zuciya, Ramlart ta daure ta sunkuyar da kai amma zuciyarta na mata kuna .
Shi kam AA Turaki yana shiga cikin falon , ya gaishe da su Mami cikin mutunci da ladabi, suka gaisa da su baba. Sai dai ko ɗaya bai kalla inda Ramlart ta ke tsaye ba, da alama bai san ma da wanzuwar ta a wajen ba.
hakan da yayi ya kara sosa ran Ramlart – a hankali ta dafe ƙirjin ta dake mata barazanar tarwatsewa, tana kokarin boye hawayen ta. A cikin zuciyarta, ta tabbatar da abu guda: soyayyar ta ga AA Turaki har yanzu ba ta mutu ba… kuma bazata iya rayuwa ba tare da shi ba.
A lokacin da Hajja da Baffah suka ƙaraso cikin falon, Alhaji Musa, ne ya mike tsaye cikin murnar ganin su ,ya tarbe su da fara’a, ya rungume abokinsa Alhaji Abdullahi cike da farincikin ganin aminin nasa,Mami cikin murna da farin ciki ta gaida Hajja da fara’a. Aunty Hauwa ma tana falon tare da ‘ya’yanta haka suka gaisa da su Hajja cikin sakin fiska .
Alhaji Musa yana murmushi yace:
"Wallahi wannan ziyara da kuka kawo mana, ta faranta mana rai sosai. Mun ji daɗin ganinku."
Cikin nitsuwa Hajja tace:
"Mu ma muna godiya da irin karamcin ku. Mun zo ne saboda zumunci, da kuma wata muhimmiyar magana."
AA Turaki yana zaune cikin nutsuwa, kai kace baya cikin falon yanda ya kame yana danna wayar sa kamar ma baya wajen, ga Hajiya ramlart dake rakube a gefe tana aikin kallon sa.
Alhaji Abdullahi Turaki ne ya gyara zaman sa tare da cewa:
"Alhaji Musa, Hajiya Rakiya… akwai wani al’amari mai nauyi da ya shafi ‘yar mu wato Ramlartu .
Wani irin bugawa ƙirjin ramlart yayi ,har wani jiri jiri take ji yana kok'arin ibanta, da kyar ta iya seta kanta, duk wani addu'a da yazo bakin ta karantashi kawai takeyi, jin Baffah yaci gaba da cewa"Mun tabbatar da cewa ita ce ta sakawa Hajja wani sinadari a abinci, wanda hakan yayi sanadiyar kwanciyan Hajja a asibiti…"
Kuma Likitocin sun gano hakan ne ta hanyar gwaji inda board na asibitin suka had'a meeting naganin cewa sun tsanan ta bincike angano mai laifin, ganin hakan ne yasa Aliyu ya nemi alfarma yadakatar da su inda ya tabbatar musu dacewa zai dauki mataki da kan sa, bayan bincike da aka gudanar ansamu ganin hoton Ramlartu ta cikin CC camera in da aka tabbatar da cewa ita ce ta aikata hakan ,hakan ne ma yasa mijin ta ya umarce ta da ta dawo gida, toh kaji wannan ne dalilin zuwan mu .
Ai a lokacin baba ji yake kamar lokacin ya tsaya masa baya tafiya, kowa dake dakin yayi shiru har Aunty hauwa da ta cika musu gaban su da abubuwan motsa baki cike da mamaki suke kallon ramlart dake rakube a gefe kamar muna fuka. Ramlart na rakube a gefe, ta sunkuyar da kai kasa.
Cikin fishi Alhaji Musa ya kalle ta fiskar nan babu alamar rahama a tattare da ita cikin tsawa yace.
"Ramlart! Wannan ai ba laifi bane kawai, wannan keta mutunci ne da rashin hankali! Abinda kika aikata ya wuce a yafe miki da cikin sauki, kisan kai fa kike kok'arin yi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un baba ya kara maganar cike da rauni."
Cikin kuka Mami tace"Na yarda da tarbiyyar da muka baki ba haka take ba. Me ya rinjaye ki har kika aikata hakan?"
Cikin bacin rai Aunty Hauwa ta matso tare da zabga mata wani lafiyayyan mari, wan da yasa jinta ya d'auke na wucen gadi, ta sake dağa hannun ta zata sake zabga mata taji Baffah yace kull kull hauwa'u barta haka, ai shi duka baya gyara sai dai ma ya sake lalatawa dan haka addu'a zaki mata, Wani irin kallon zamu had'u Aunty hauwa ta mata tare da cewa.
"Na rasa dalilin da zai sa ki hallaka kanki da hannunki. Wannan kuskure ne babba!, kuma ina mai tabbatar miki da sai kin girbi abunda kika shuka."
Cikin miryan kuka Ramlart tace "Na tuba… na yarda da kuskurena. Don Allah ku yafe mini…wlh sharrin shaidan ne bazan karaba wlh na tuba."
Cike da ta kaicin ta Alhaji Musa ya juya zuwa ga Alhaji Abdullahi Turaki yace ."Wallahi in har wannan abun ramlart ta aikata , to sai dai ta zauna a nan gidan. Ina son Ka umarci Aliyu da ya sauwake mata ta dawo nan ta zauna … tunda ta zubar da mutuncin ta."
Cike da jin nauyin shi Alhaji Abdullahi Turaki yace "Alhaji, ba karamin nauyi na ji ba, dana kawo maganar gaban ku sai dai kuwa ba yadda zanyi ne ya zama dole kusan da maganar a matsayin ku na iyayeh a gare ta. Amma ina rokon ku daku dubi girman zumunci, da girman mutuncin mu, ku yafe mata. Mu ma muna bakin cikin faruwar hakan. Amma in ba damuwa, a bata dama ta biyu ta gyara. Allah yana yafe wa bawansa, mu ma mu yafe mata, hakan zai sata ta gyara kura kuran ta na baya."
Hajja ce ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli AA Turaki wanda bai ce komai ba, kamar ma wanda baiya wajen.
Cikin nitsuwa Hajja tace "To… kamar dai yadda Alhaji ya fad'a Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare kuma ace mu bayin sa , dan haka nima na yafewa ramlartu ,Amma fa wannan kuskuren ba ƙarami bane, sabi da haka saita kiyaye gaba duddah har yanzu bamu san dalilin ta na aikata hakan ba."
Shi dai AA Turaki bai ce komai ba, sai ma wayar sa da ya ci gaba da dannawa, amma a chan cikin kasan zuciyar sa bakaramin haushi yake ji ba, a zaton sa Hajja zata sa ya rabu da ramlart amma sai gashi sun buge da yafe mata, duddah iyayen ramlart sun chanchan ci fiye