Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
a cikin wani luxury café da ke Maitama. Anguwar na da nutsuwa, kuma wurin ya kasance mai tsit, babu hayaniyar komai. Ramlart ta ke zaune cikin shigar mata masu class, sanye da riga da skirt na zamani, ga wasu manya gilashi a idonta, hannunta sanye da agogo mai tsada. Zuly kuwa ta na zaune fuskarta cike da kwalliya , irin na ya'yan masu kudin nan marassa jin magana . Zuly ce ta zuba ido cikin na Ramlart tace . “Yanzu fa, da gaske Hajja ce ta fara shiga tsakanin ku da AA Turaki? ai kuwa ya kamata muta ka mata birki dan bazai yiwu taci zamanin ta ba sannan a yanzu tace zata had'a da naki ba, never wlh . Wani irin ɓacin rai ne ya ziyarci fiskar Ramlart tace. “Zuly... ke kanki kin san ba ta taɓa sona ba, Tun farko, ita ta shigo da ni saboda biyayya, ba domin ta yarda dani ba, sai don cikan burin ta akan danta, Yanzu kuma tana kokarin rabani da mijina.” ZULY ce ta harare ta tace . “To, me muke jira? Kin dai ce min tana issue n zuciya da hawan jini. Me zai hana mu taimaka mata ta huta da wuri kawai?” ta karasa maganar tare da shekewa da Wani irin dariya. Ramlart ta lumshe ido, tana sauke numfashi. A zuciyarta, akwai rudani tsakanin gaskiya da makirci, amma kiyayya ta fi karfi a zuciyar ta. cike da zafin rai Ramlart tace . “In har hakan ne hanyar da zai sa ya dawo gareni... zan iya yin komai.” ZULY ta d'an yi murmushi tace . “To sai mu fara da abincin ta, Zan samo wani sinadari da ke kara tashin zuciya a jikin masu ciwon zuciya. Karki damu sai ki ringa sa mata a tea ko soup ɗinta, da zaran taci ko da sau d'aya ne uhumm... sunan ta sorry.” takarasa maganar cike da makirin murmushi. “Hakan zai yi, Amma sai dai mu yi hankali. Ba zan so a gane cewa ni na janyo hakan ba.” cewar Ramlart da ta gama yarda da maganar ZULY. Zuly ce tace. “Ki bar min wannan. Ai ni ce master planner. Kuma fa... idan ta mutu, babu mai hana ki warwasawa da mijinki kin ga gaba d'aya hankalin sa zai karkata kan ki ne, tun da bamu da matsala da wanchan Tsohon na shi kin ga sai kici karen ki babu babbaka.” Ramlart ta lumshe ido tana murza zoben dake hannun ta, A cikin zuciyarta, soyayya ta rikide zuwa kishi, kishi ya rikide zuwa makirci. don kuwa ji takeyi zata iya kawar da kowa akan hanyar ta muddin zai shiga tsakanin ta da AA Turaki. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 7️⃣ Monday morning misalin karfe 8:30 na safe. Ramlart ce tsaye hannun ta rike da wani farin leda. Ga Kayan tea da kayan girki suna nan a jere, a gaban ta da alama an kammala break fast ne. Cike da annashuwa ta bud'e ledan wani irin farin sinadari ne a ciki, Dan kad'an ta ibo ta zuba a cikin flaks din tea, da sauri ta d'an girgiza shi ta yadda ba za'a gane an saka komai ba, nan da nan ya narke a cikin tea d'in, karkad'e hannayen tayi ,ta juya gefe da gefe ganin ba wanda yake Kallon tane ya sa ta sauke ajiyar Zuciya tiren ta dauka ta nufi falon Hajja. Hajja na zaune, tana karanta Qur’ani a hankali, Ramlart ta shigo da tray mai dauke da tea da snacks. Cike da fara'a RAMLART ta ajiye tiren tare da cewa. "Hajja, ga tea dinki… ." HAJJA ce ta kalle ta fiskar ta d'auke da murmushi tace. "Allah ya miki albarka Ramlartu, yau kin kawo mani abun kari da wuri, kamar kinsan cikin nawa bakomai." Takara sa maganar tare da, karba, ta fara shan tea d'in da ramlart ta zuba mata a cup. Bayan mintuna kadan, Hajja ta fara motsa jikinta da wani irin ɗan sanyi, ji take kamar bugun zuciyar ta ta karu. Cike da karfin hali HAJJA tace. "Ah… Ramlart… zuciyata… kamar tana bugawa daban…" Bata karasa maganar ba ,Ta kama kirjin ta, Cikin minti daya, ciwon ya tsananta, jikin ta ya birkice Jikinta ya fara rawa kamar na maijin sanyi. shigowar shi parlourn kenan yana waya da PA ɗinsa, yana magana a waya "Cancel all appointments for this week, I need to… maganar ce ta makale hango mahaifiyar sa tana riƙe da saitin zuciyar ta, a lokaci guda tana faduwa a jikin kujera. Hajja!!" Ya kira sunan ta da mugun karfi. Da sauri Ya ajiye wayar, ya ruga zuwa da d'an sassarfa zuwa gareta. Ganin sa da tayi ba tare da tsammanin sa bane yasa ,Ramlart ta tsaya cak cike da kame-kame na rashin mafita. "Ramlart! Meye hakan? Kira driver! Kira masu taimako!" Cike da tsoro ramlart takira driver A take aka tara mutane, aka kwashe Hajja cikin mota. Wata mota Black Lexus SUV, a ka sanya Hajja tare da AA Turaki yana riketa da ita a kafadar sa. Bodyguards da Sani PA sun biyo su da wata motar gefe, tare da ramlart, kowa hankalin sa a tashe . Suna isa aka wuce da Hajja ,cikin Emergency Ward. Likitoci suna ta kai-komo, suna bata agajin gaggawa. Dr. Imam da wasu nurses ne suka karɓe ta , haka suka rufu akan ta domin ceto rayuwar ta. NATIONAL HOSPITAL ABUJA, ICU Waiting Area. AA Turaki na zaune a bench kusa da ICU, yana kallon kofar dakin da mahaifiyarsa, ke ciki. PA dinsa da bodyguard din sa sun tsaya d'an nesa kadan da shi kowa ka kalli fiskar shi yana cikin tashin hankali. Ramlart na zaune a gefensa, tana kuka mai sauti, sai yarce majina takeyi a jikin mayafin ta , idanun ta duk sun kumbura saboda kuka. cikin kuka mai sauti Ramlart ta ce. "Honey… na shiga uku! Hajja fa! Allah ka dubemu… Hajja zata mutu shi kenan mun shiga uku…" ta karasa maganar tare da jan dogon majina. *Dan juyowa yayi kadan yana kallonta da wani irin kallo mai cike da ma'anoni masu yawa, sai dai yabarwa rai. A hankali Ya ɗan ja numfashi amma har yanzu bai ce mata komai ba, kauda kan sa gefe yayi, d'an ji yake yi kukan nata na damun sa. A cikin ICU, Likitoci biyu ne suke magana Dr. Imam na hannun dama, yana duba takardu, d'an dago kansa yayi yana fadin... "Symptoms ɗinta sun nuna hypertensive crisis ne tare da cardiac complications. But there’s something strange…" DR. RACHEAL ne yace: "Yeah… Her vitals suddenly dropped after ingesting something. Did you run tox-screen?" Yakarasa maganar tare da kallon fiskar Dr İmam. DR. IMAM ne yace: "Just ordered it. Meanwhile, let’s call in Dr. Farida, she’s one of the most trusted consultants here. She might help manage the case, especially now that there’s suspicion of induced triggers." DR. FARIDA tana cikin Office dinta tana duba case file, Nurse Mary ce ta shigo tare dacewa . "Doctor Farida, you’ve been requested to assist in managing a critical case in ICU — Hajiya Habiba Turaki. Dr. Imam asked specifically." Cike da nitsuwa Dr Farida ta ɗaga kai tana kallon nurse mary , kafin tace. "Alright. Give me the patient’s file and vitals. Let’s go immediately." Ta miƙe, ta ɗauki coat da stethoscope dinta, suka nufi İCU AA Turaki na nan har yanzu, yana kai da kawowa. Ganin Dr Farida ta shiga ciki ne yasa , Ramlart ta ƙara fashewa da kuka sosai, kamar za ta zube a kasa, "Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, shikenan munrasa Hajja, ganin bai kulata bane yasa, A hankali ta leƙa ta kalli AA Turaki da gefen ido, tana jiran ya kalle ta, ko ya mata magana, Amma ya ƙi kallonta, asalima kamar baisan da wanzuwar ta a wajen ba . A cikin ICU, DR. FARIDA na duba Hajja tana kokarin yin bayanin abun da tagani ga Dr Imam. DR. FARIDA ne tace: "Heart rate’s unstable. We need to stabilize her BP first. Tox-screen result is vital — I suspect some external compound triggered this. Alert me as soon as the lab result is ready." DR. IMAM ne ya kalleta yace: "Understood. I’ve already instructed the team." DR. FARIDA ne ta matsa kusa da gadon Hajja tana murza hannunta a hankali, tana karanta mata ayatul kursiyu, a zuciyarta, ta na tofa mata ,haka kawai takejin tausayin tsohuwar duddah zata girmi Dadar ta . A hankali Dr Farida tace. "Allah ya yaye miki wannan cuta…" Ganin AA Turaki yatafi masjid ne yasa ramlart ta ciro wayar ta a jakan ta numbern zuly takira direct tana dagawa tace. " Ke zuly muna cikin bala'i kin san kuwa na sakawa Hajja maganin nan da safe a cikin tea d'in ta na safe, tana sha ba wani Bata lokaci maganin yayi reacting a jikin ta, kuma AA Turaki yaga lokacin da nake tare da ita, yanzu haka gamu nan a national hospital wlh duk na tsorata gani nake kamar asirin mu zai tonu".takara sa maganar tare da goge wani zufa da ya yanko mata tun daga saman kanta. Cike da karfin hali ZULYtace. "Ki nutsu mana! Kin manta da sabon matakin da zamu dauka ne? Ki nuna damuwa sosai, ki ci gaba da rike zuciyar shi da tausayi , karki bada kafar da zai zargi wani abu dağa gare ki, ko da yaso zargin ki ki tanadi wasu dalilai da zai hana ya zargeki kai tsaye haba be Wise mana sai kace wata local." Bata kashe wayar ba sai da ta tabbatar da cewa ta gama daukan shawarwarin da zuly ta bata , sabi da haka tana kammala wayar, ta sab'i jakan ta ranta fess ta nufi komawa gida batare da tajira shigowar AA Turaki ba. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 8️⃣ Lab Department, National Hospital – An kira Dr. Farida domin karɓar sakamakon gwajin Hajja wanda aka mata da misalin karfe 9 30am na safe . Dr. Farida na tsaye a gaban Lab technician, tana karɓar takarda da sakamakon tox-screen da blood analysis. Bayan ta gama karantawa ne , fuskar ta cike da damuwa , had'e da mamaki. A hankali a cikin zuciyarta ta furta: “Ya Salam… ta sha sinadarin da ke haddasa hawan jini da matsin zuciya… This isn’t accidental.” Cike da son tabbatar wa Ta kalli Lab technician din tace. "Shin kun tabbatar da wannan sakamakon? Wannan compound ɗin wani nau’i ne na slow poison da ke aiki a jiki cikin sa’a da awa." TECHNICIAN D'in ne yace: “Yes Doctor. An tabbatar, kuma an gano traces of a rare chemical—*Digoxin derivatives*—da ke da strong cardiac effect, especially for hypertensive patients.” A hankali Dr. Farida ta ja numfashi, ta rufe takardar , sannan ta fice tana nufar Office din Dr. Imam. Dr. Imam na zaune yana rubuce-rubuce, Dr Farida ta turo kofar ta shigo da takarda a hannunta. Bayan ta mika masa result din ne tace masa. "Dr Imam, there's more to this. Hajiya Habiba Turaki,was poisoned." Cike da mamaki DR. IMAM ya d'ago kansa tare da cewa: "What?! Are you sure?" DR. FARIDA tace: "Positive. The test confirmed it. Yakamata mu yi report zuwa board. Wannan ba cuta ce ta yau da kullum ba — wani ya sanya mata wannan sinadarin da gangan." Cike da damuwa DR. IMAM Yace:* "Then we have to inform the family and call security for investigation." AA Turaki na tsaye a waiting area na ICU don har yanzu bawani bayani bai samu ganin ta ba, yana kiran PA dinsa a waya, Dr. Farida ce ta iso cikin sauri tace. "Mr. AA Turaki, I need to speak with you in private please." Ta wuce Office din ta, cike da karfin zuciya ya bita a baya, bayan shigar su cikin Office din ne. DR. FARIDA tace. "Mun gano wani abu a jikin Hajiya Habiba Turaki. An samu evidence na wani sinadari mai hadari a jikin ta… It’s poison. Ba ciwon zuciya kawai bane ya haddasa mata hakan." Ji yayi komai nasa ya tsaya cak, Idanunsa sun cika da tashin hankali, da bacin rai. Cikin wata irin Murya mai kauri yace. "Poison? Waye zai aikata hakan a gare ta? Waye zai cutar da Hajja?!" A hankali kwakwalwar sa ta tuno masa da ramlart,A take idanun sa suka yi ja. Ba tare da ya ce mata komai ba, ya juya ya fita daga cikin Office din. NATIONAL HOSPITAL ABUJA – BOARD MEETING ROOM AA Turaki na zaune a gaban babban teburin Board din asibitin tare da Chief Medical Director (CMD), Dr. Imam, Dr Farida, da wasu manyan likitoci. CMD ne yayi jaran murya tare da cewa: "Mr. AA Turaki, considering the results from Dr. Farida’s toxicology report, we’re prepared to report this to the authorities for full investigation. This is a serious criminal matter." cikin nutsuwa da kamala AA Turaki yace : "Ba sai kun dauki matakin doka ba. I appreciate your concern, amma I will handle this internally. It's a family issue and I believe it’s best managed within our home. Please respect my request." Dukan su sai Suka kalli juna, suka gyada kai, saboda girman sunan sa da matsayin sa a kasar. . CMD yace: "As you wish, Sir. But we’ll keep the report confidential for now. We’ll proceed only if you authorize us." AA TURAKI cike da jin dad'in yan da suka amince da request nashi yace: "Na gode, da kuka fahimce ni". ICU – DAKIN HAJJA Dr. Farida na zaune a gefen gadon Hajja. Tana daidaita IV drip sannan tana tausa mata hannaye da lallami, yayin da Hajja ke bacci mai nauyi. A hankali kamar mai tsoron tashin ta DR. FARIDA ta ce : "Ya Allah ka bata lafiya… kamar mahaifiyata ta nake jin ta a zuciya ta ." Wata Nurse ce ta shigo, ta mika mata wasu results, sai ta duba tare da gyada kai cike da kulawa, Ta tsaya bakin gado, ta sumbaci hannun Hajja cike da tausayin ,ta tafita daga d'akin. TYCOON MANSION Ramlart ne ta shigo cikin fargaba, sai dube-dube take da sauri, ta rufe kofar dakin ta. Ta fada kan gadon ta tana shakar wani dogon iska. A zuciyar ta ta ce. "Alhamdulillah… Na fita daga wannan abun na dan lokaci. Yanzu dai ba wani zargi kai tsaye… Insha Allahu, zan sami hanyar kare kaina zuwa gaba." Da sauri Ta dauki wayar ta, ta kira Zuly, ringing d'aya ta dağa. RAMLART ce ta ce: "Zuly, na koma gida,AA Turaki bai zarge ni ba, kuma da alama doctor's din basu gano komai ba, amma kuma wlh na tsani wannan likitar Dr Farida take ko wa." Zuly ce tayi shewa tace . "Kai mutumiyar baki da dama me kuma ya had'a ki da wata Dr Farida, ke dai tunda asirin ki bai tonu ba sai ki godewa Allah". Haka suka gama wayar cike da Nishad'i na samun nasara. Dr. Imam na tsaye a bakin kofar ICU, yana jiran fitowar Dr. Farida. Da ta fito daga dakin Hajja, sai ya mika mata wani mini flask mai shegen kyau da coffee a ciki, Wani irin cute smile ya ke mata, na zallan Love. Cikin shaukin so DR. IMAM yace: "I know you barely slept. Na kawo miki coffee. You’re really amazing Farida… I wish kina fahimtar yadda zuciyata ke bugawa a kanki." Cikin shauki Dr İmam Yana kokarin kama hannunta. da murmushi d'auke a fiskar ta ta ja hannunta baya kadan: "Thank you, Dr. Imam. I appreciate your concern… Amma my patience is my priority for now." Murmushi su kayi dukan su, atare su ka juyo A lokacin ne AA Turaki ya karaso cikin Ward din sai dai kamin ya iso kusa da su, ya dan tsaya kadan, yana jin kowane kalma da Dr İmam yake fad'a mata a cikin zuciyarsa, haka kawai yaji abun ya basa haushi, Wani irin bugun zuciya ya keji kamar za ta fito, waje, wato su ba condition d'in Hajja bane a gaban su ba, ta Love d'in su suke yi, tsofai tsofai da su, Idanunsa suka kada sukayi ja, a hankali idanun sa suka tsaya a jikin Dr. Imam da Dr. Farida, wani irin kallo mai dauke da ma'anoni yake musu. Zuciyarsa cike da fushi, dan ya tsani abun da zai saka Hajja a wani condition, sai gashi Likitocin da suke dubata ne suka buge da soyayyah, kawar da kwayar idon sa yayi ,sai ya kama hannun agogon hannunsa ya duba time da dan karfin murya, yace . "PA… Let’s go. I’ve wasted enough time watching unnecessary conversations." Cikin sauri PA dinsa ya matso , tare da bud'e masa kofar, yad'an ja da baya, bayan ya wuce, san nan ya bi bayansa. Bodyguard d’insa biyu masu siffar karfi, suka tsaya a dan nesa suna jiran sa. Dr. Farida ce ta koma cikin Office din ta zuciyarta na ci gaba da harbawa da sauri. Duk da bata fahimci dalilin sa na fad'in hakan ba , Amma zuciyar ta cike take da tsoro. A bangaren AA Turaki, bayan ya shiga ya duba jikin Hajja ,har yanzu tana kwance kamar mai bacci, haka ya fito su PA da bodyguard din sa suka take masa baya, da sauri yake tafiya, zuwa parking lot. PA dinsa na kokarin bin sa da sauri yana kok'arin yi masa magana, amma ganin kamar yanayin sa ya chanza sai bai ce komai ba. cikin kulawa Sani PA yace. "Sir… are you okay? Shall I cancel the rest of the day’s schedule?" Cikin kokarin danne fushinsa yace: "Cancel everything. I don’t want to see anyone today." Yana gama fada'r haka Ya bude motar da kansa ya shiga, batare da ya jira sun bud'e masa ba, Motar tana dauke da kamshi na musamman, interior nata executive ne da hasken LED masu taushi. Ya zauna, ya lumshe idanu yana jin zuciyarsa na bugawa da mugun karfi. Bayan fitar sa daga d'akin Hajja, Dr. Farida ce ta shigo tana duba drip na Hajja, ta gyara mata bargo. Hannunta na rike da yatsunta a hankali, Hajja ta bude idonta kadan ta kalleta, idonta na dauke da rauni, amma cike da godiyar Allah da kwanciyar hankali, ta karasa bud'e su . Cikin raunin Murya Hajja tace. "Likita… na gode. Allah ya saka da alkhairi." Fiska cike da murmurmushi Dr Farida tace . "Ameen Mama. Allah ya baki lafiya." D'an murmusawa Hajja tayi, jin takira ta da suna mama, cike da kulawa ta kalleta tace. "Ki kirani da Hajja" ,haka Da'na yake kira na. Wani irin faduwar gaba ce ta riski Dr Farida, aranta tace. "Uhumm wannan d'an naki mai shegen fad'in rai duk yabi ya cikawa mutane asibiti da guma ka , wai su bodyguard din sa, sai kace akan sa aka fara tsaron lafiya". Muryan Hajja ce ta katseta. " İna wanda suka kawo ni nan", cewar Hajja. Cikin girmamawa Dr Farida tace. "Basu jima da fita ba amma I'm sure zai dawo anjima." Tana gama fada'r hakan, Ta kamo hannunta tana bubbugawa a hankali, Ta dago ta kalli Nurse d'in dake cikin dakin tace. "Please, call me immediately if anything changes. I’ll be in my office." Tana gama fad'an haka , Ta juya ta fita, tana kokarin mayar da zuciyarta da hankali akan aikin ta – duk da kalaman Dr. Imam da fushin AA Turaki na ci gaba da juya mata lissafi, a cikin zuciyar ta. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 9️⃣ AA TURAKI’S MANSION, PRIVATE MASTER SUITE. Da dare misalin qarfe 10 30pm duhun dare ya mamaye ko'ina,a cikin wannan, katafaren gidan mai alfarma, Fitilun chandelier ne su ka haskaka farfajiyar babban falon sama, kai kace dare batayi ba. Ramlart, ce ta fito cikin kayan bacci masu siririyar hannun lace, suna d'auke da launin ja, sun gama bayyana surar jikinta, Wani irin ƙamshi na musamman ne yake tashi daga jikinta , turaren da zuly ta kawo mata ne na maganin tada sha’awa , wanda zai jawo hankalin AA Turaki zuwa gare ta. A hannunta, tray ne dauke da tea da snacks, zuciyarta cike da niyyar jan hankalin AA Turaki da mallake zuciyarsa, gaba d'aya. Cike da yanga Ta karasa bakin kofar dakina sa, a hankali ta tura k'ofar cike da yanga, kamar wata jarumar Indian film. AA Turaki na zaune a kan sofa da ke cikin d'akin nasa yana duba wani file na Business d'in sa, jin an bud'e k'ofar d'akin ne yasa ya dago idon sa ya kalleta, cike da nitsuwa ya sauke files din, ya dan kame, yana kallonta, shiru ne ya biyo baya na Dan wani lokaci. Cikin murya mai sanyi RAMLART tace. "Naga kana aiki ne shiya sa na kawo maka tea, d'in nan, na ce bari na tayaka hira, ta karasa maganar cikin kwantar da kai." Ganin baice mata komai bane ya saTa karaso, ta ajiye tray din a gefe, sai ta tsaya gabansa. Cikin salo, ta fara shafa kafadarsa, a hankali take shafa shi har zuwa kirjinsa, tana narkewa cikin jikin shi . AA Turaki ya bita da ido, bai ce uffan ba Sai ma ya mika hannun shi ya kamo ta shima, a hankali suka fara romancing din juna, har cikin ransa ya ke kin hakan, amma ya kasa controlling din kan shi, haka ya ci gaba da ya'mutsata, wani irin yarrrrrrr ramlart take ji yana yawo a jikin ta, wannan ne karo na farko a rayuwar auren su, da AA Turaki ya saki jiki yana romancing din ta yanda ya kamata, ba karamin dadin hakan takeji ba, sai wani bank'arewa take yi tare da shishahid'ewa ,sai da ya bari har ta sake jikin ta sosai, ta dinga shafe shi, Wani irin murmushint gefen baki ta sake, cike da jin dad'in nasaran da tayi akan sa. Tana cikin jin dad'in abun da yake yi mata ne, Sai kawai taji ya dakata. Ya dan ture hannunta a hankali. Cikin natsuwa ya mike, ba tare da ya ce komai ba, ya nufi toilet, yana jin wani irin jiri yana kok'arin iban shi. tsayawa cak, ramlart tayi, zuciyarta na bugawa, da sauri sauri, jikin ta har rawa yakeyi, kunnuwan ta suna sauraron karan, ruwan shower na dukan tiles, daga cikin toilet d'in,Kamar wadda aka saka a cikin ruwan sanyi, jikin ta duk ya mutu muruss, dakyar ta ta shi ta zauna a gefe tana hawayen bakin ciki. Bayan wani lokaci, AA Turaki ya fito cikin riga da wando na pyjamas masu matuƙar tsada, jikin sa yana fitar da ƙamshin turaren The King mai daddadan kamshi. Cikin Wani irin yanayi Ya shimfida prayer mat dinsa, ya tsaya, ya tada sallar nafila, Cikin nutsuwa, ya dinga rokon Allah lafiya ga mahaifiyarsa. Ganin yan da yayi banza da ita ne yasa Ramlart ta kara fashewa da kuka, tana jin haushin abinda ya faru. Bayan ya idar da sallah, bai kalle ta ba, ya nufi gado, ya haye gado cikin shiru batare da ya kulata ba, ya kwanta yana Mai karanto addu'ar bacci. Ramlart ce ta tsaya, tana kallon sa, zuciyarta cike da fushi da kunci, wani irin bakin ciki ne ya turnuke ta, Ta kama hijab dinta ta dai dai ta shi a jikin ta, sannan ta fita cikin sauri, kamar wacce zata tashi sama. Bayan ta koma dakin ta, ta fad'a saman gadon ta cikin takaici, Ta dauki wayar ta kira Zuly. Cikin sheshsheqan kuka RAMLART tace . "Zuly… kin san me ya yi mini kuwa? Ya barni tsirara bayan ya gama jagwalgwalani, Yaje yayi alwala! Yayi salla! Wani irin wulakanci ne wannan?" Cike da kara kunna ta ZULY tace . "Yanzu nan, zan biyo ta gidan ki ,maza tashi ki shirya, Ni da Al’ameen za mu zo mu dauke ki, Zamu wuce club! Enough is enough, Ramlart. Wannan wulakanci ya isa haka! Sai kace ba babban yârnya ba zaki tsaya yana wulakanta ki, haba mana sai kace kin manta kece fa Ramcy baby The babbar yarinya mai babbar harka, haba karki ba dani mana ke da maza suke rububin ki sai ka ce kin manta dan fa kin nace masa ne wlh , shine har ya samu damar wulakanta ki." Ramlart ce ta share hawayenta, zuciyarta ta cika da bakin ciki, tace zuly kina ganin....! Bata bar ta ta karasa maganar ba tace . "To shikenan! Ki shirya yanzu, Za mu fito ni da Al’ameen mu d'auke ki, Tonight, you must forget him. Let’s go to club wannan damuwar sai mun danne ta!" Ramlart ta share hawayenta, ta miƙe da sauri, cike da fushi ta nufi cikin close set d'in ta, tafara shirya kanta. Ramlart ce tsaye a gaban madubi, cikin shigar ta mai jan hankali – fitted black gown da takalman golding masu tsini sanye a kafarta, Ta feshe jikinta da turaren ta mai ƙamshi da ƙarfin gaske, Gashin kanta gyare yake tayi parking d'in shi, light makeup mai haskaka fuska tayi, Wayan tane a kunnen ta. A hankali tace . "Zuly, na shirya…

Chapter 4 of 7