Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
yake tafiya a gaggau ce ganin ya nufi hanyar fita daga Ward din ne yasa, tun kafin isowar su PA ya sanar da bodyguard din da su kasance cikin shiri, hakan ce kuwa tafaru suna fita aka bude masa mota ya shiga, jin ya zauna a kan sit din motar ne ya sa ya lumshe kyawawan idanun shi , a hankali yake sauke ajiyan zuciya, sunan Allah kawai ya ke iya ambata a kasan zuciyar sa, jin motocin sun fara tafiya ne ya sa ya d'an gyara zaman sa, Wani irin matsanan cin ciwon kai yake ji, ga gajiyar tafiya da ya kwaso, abun duk ya hade masa . A bangaren ramlart kuwa tun tana saka ran dawowan mijin nata har ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido. Zuwa yanzu Zuciyar ta tashiga tashin hankali da firgici wanda ita kanta ba ta san adadin shi ba, ganin bini bini tana kallon bakin kofa ne yasa aunty hauwa tace "lafiyan ki kuwa ramlart" ganin kar anty hauwa ta rafko jirgin ta ne yasa tace "lafiya qlu anty" daga haka bata sake ce mata komai ba , sai ma zame wa da tayi ta kwanta a bisa gadon jinyar tata tare da lumshe idanun ta kamar mai bacci. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 2️⃣ Yayin da motoci suka shigo babban katafaren gidan AA Turaki a Maitama Abuja, wata ƙofar ƙarfe mai ƙyalli ta buɗe da kanta ta hanyar automatic. Wani irin babban mansion ne, na zamani amma an kawata shi da hadin kayan gargajiya da na zamani, hakan sai yasa ya zama na musamman zaka jima baka ga mansion irin sa ba . Gininsa gwanin ban sha’awa ne, wanda ya sha gyare-gyare daga lokacin da ya gina shi , kasan cewar bai manta asalin sa bane yasa ya zaɓi kawata gidan nasa da Kayan gargajiya game da na zamani. Akwai fitulun wuta masu ba da sanyi da wani haske na Musamman ,a gefen titin cikin gidan, ga wasu flowers da tsire-tsire masu fidda ƙamshi na Musamman ,. Motar sa limosine da ya ke ciki ne ta tsaya a gaban babban foyer, bodyguards dinsa, guda biyu suka buɗe masa ƙofa, yayin da ya bar sauran bodyguard din sa a chan parking space dake haraban gidan. A hankali ya fito, fuskarsa cike da natsuwa amma idanuwansa na bayyanar da damuwa, Tattare da gajiya da ɗan ɓacin rai, yana sanye da suits mai tsada, amma haryanzu babu walwala akan fiskar sa, fuska tana ɗaure tamau kamar wan da bai taba dariya ba, a hankali ya ja wani irin numfashi mai sanyi, cikin nitsuwa ya fara takawa cikin main parlourn gidan ya nufa, da sallama d'auke a bakin sa ya shiga cikin parlourn sai dai kamar ko yaushe idan yayi sallamar bai zama lallai mutum ya ji sa ba. Wata mace ce mai kusan shekaru 60, kyakkyawar, gaske doguwa, mai launin fata fara sol, irin mai sanyi da kyan ido irin na Fulani usuli. Sanye take da atamfa mai Holland da gyale wan da ta lulluɓe saman kanta da shi, kana ganin ta kaga jin dadi a tare da ita. Tana zaune a kan farfajiyar da ke kusa da living room, kallo d'aya zaka mata kasan cewa akoi wani abu mai muhimmanci da take jira. Ganin wanda ya shigo ne ya sa ta fad'a'da murmushin ta. "Yeroh !"Ta ce da murmushi mai sanyi akan fuskar ta, a lokaci guda kuma ta tashi tsaye tana mai cewa, "Lale marhaban da dawowa daga London." Cike da d'an sassarfa Ya ƙaraso ya durƙusa a gabanta ya na mai riƙe hannunta, a lokaci guda , ya sunkuyar da kansa kasa. Ganin irin halin da tagan sa a ciki ne ya sa ta kara zuba masa ido, kallon sa tayi na Yan mintuna, Tuni ta fahimci baya cikin walwala, duddah hakan ba wani sabon abuba ne a gare ta amma sai take ganin kamar na yau din ya sha banban dana sauran lokutan. Cike da na tsuwa tace "Alhaji ya ce mini ka biya ta a sibiti , to Yaya jikin ramlatun, ? Yanzu ace muna gida d'aya ramlatu ta kasa fad'a mana cewa bata da lafiya, sai dai kawai Muji cewa tana asibiti." Dago kansa yayi daya ke jin ya bala'in yimasa nauyi, kallon mahaifiyarsa,ya yi a hankali ya ɗan sauke numfashi. "Mun same ku lpy? Shine abun da yafara fad'a , kafin ya sake cewa jikin ta da sauƙi, amma..." Sai kuma d'an tsaya, yana juyar da kan sa gefe guda, yana ƙoƙarin ɓoye hawayen da suka cika idanunsa, baya son Hajja ta gansa a irin wannan yanayin . A hankali Hajja tace: "Yeroh ..!Na san murmushinka haka zalika nasan kukan ka, sabi da haka" ko fe'ihh" Me ya faru?" Ta karasa maganar cikin harshen fulatanci. muryarsa a rauna ne, yana jin zuciyarsa kamar an tsinke ta, kamar zata faso ƙirjin sa ta fito waje. "Abu ne mai nauyi, Hajja Wani abu ya faru da bazan iya furta shi cikin sauƙi ba..." A dai dai lokacin ne Alhaji Abdullahi Turaki, mahaifin sa, ya shigo daga sashen karatu, na cikin gidan. Alhaji Turaki dattijo ne mai kusan 70yrs, dogo, ne fari, fuskar sa a cike da nutsuwa da dottaku, cikin nitsuwa Ya zauna yana kallon ɗansa d'aya tilo cike da kulawa. " A duk in da namiji yake an san shi da gwagwarmaya da kuma jure ƙaddarah, don haka baka da wan da zaka fad'a wa matsalar ka bayan nida mahaifiyar ka, sabi da duk wani abu da ya same ka ba kai kaɗai, ya shafa ba har da mu" Alhaji Abdullahi ya kara sa maganar tasa cike da hikima da son karantar yanayin d'an nasu. Wani irin yawu ya haɗiye masu dacin gaske, kamar wanda akayi wa dole ya ce: "Doctor tace... Ramlart na iya rasa damar sake haihuwa gaba ɗaya, Kuma... wannan ba shine karo na farko da ta yi amfani da abortion pills ba." Wani irin shiru ce ta ratsa tsakiyar family lounge, din, Hajja ce ta saki ajiyar zuciya, a hankali ta koma dabaya ta zauna deb'es a kan lallausan sofa, hawaye na kokarin cika idonta, wani irin tausayin ɗanta da halin da suka tsinci kansu a ciki shekarun baya ya dawo mata sabo fill a zuciyar ta ji takeyi kamar ma yanzu ne abun yake faruwa da su. "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un..." Shine kawai abun da bakin ta ya iya furtawa. Alhaji Abdullahi Turaki ne ya girgiza kai, fiskar sa dauke da tausayi yace "Zamuyi magana da ita, in ta samu lafiya Amma ina son kai ka kwantar da hankalinka, Aliyu Allah yana jarabtar bayinsa masu imani." A hankali ya miƙe yana kallon su, yana jin yadda zuciyarsa ke cike da ƙunci amma yana samun sauƙi da d'an sassauci da ganin irin kulawarsu, a gare shi. “ cikin sarkewar murya yace Zan shiga ɗaki inyi sallah, ina so in huta .” daga haka bai sake cewa komai ba ya juya cike da sassarfa yana jin kamar gangan jikin nasa zata gaza daukar sa. A haka Ya nufi ɗakin sa mai kama da suite dake bisa babban bene na gidan wanda a cikin sa ya ke tattare da komai na more rayuwar duniya, office, library, da bedroom mai kyau kamar na hotel, kitchen da toilet. Zuciyarsa cike ta ke da damuwa… amma a ƙarƙashin zuciyar sa, akwai wani sabon damuwa da yake ji tunani yake akan maganar da Dr. Farida ta fad'a masa. Bayan ya shige ciki, parlourn ya rage saura Hajja da Alhaji , shiru mai nauyi ne ya wanzu a cikin babban falon gidan. Kowa na cikin tunani, kowa da abun da zuciyar sa take saka masa. fuskar Hajja ta fara baiyana fargaba da shakku, a hankali Ta ɗago idonta, ta kalli mijinta da yanayin da ya jima rabon da yagan ta a cikin sa a tare da ita , cike da fargaba da jin tsoro tace "Alhaji… Ina jin tsoro. Tsoron gaskiya. Kar dai ace… kar dai ace wannan kaddarar da muke gujewa shekaru fiye da ashirin ne ke neman biyo mu." Cike da mamaki Alhaji yake kallonta cikin tashin hankali yace: "Kaddara kuma? Habiba me kike nufi?" Hajja ce ta sauke ajiyar zuciya, mai nauyi: "Shekaru ashirin da ɗaya kenan da muke kok'arin ɓoye sirrin nan, Ka manta da abinda muka tafka? Wane hukunci muka tsallake mu ka gudu sabi da kunyar duniya? Yau ga ɗanmu , shekara biyar kenan da auren sa da Ramlartu… amma babu ɗa, babu diya, Yanzu kuma ga wata magana wai maganin zubar da ciki take sha ? Astaghfirullah! Wannan ai ba al’ada bace mai kyau." A hankali ta girgiza kai , idanun ta cike da hawaye tace "Na san yaron nan bai ya son wannan auren , Bai taɓa soyayya da ita ba, Ka duba yadda damuwa ke bayyanuwa a fuskar sa, a mai makon ya samu nitsuwa da farin ciki. Biyayya ce kawai ta sa ya auri Ramlart, Bai dade da dawowa daga asibiti ba, yanzu, amma kallon sa da nayi ya bayyana yanda zuciyarsa ke cikin rauni, da tashin hankali ko da kuwa bai furta hakan da bakin sa ba ni mahaifiyar sa ce ina iya fahimtar sa koda kuwa baice komai ba". A hankali Ta share kwalla da gefen mayafinta. "Duk da cewa ya a zabtu a baya kuma ya jure, amma na tabbata yana cikin azabar rashin haihuwa, a halin yanzu." Cikin hanzari Alhaji ya miƙe damuwa na sake baiyana a saman fiskan shi, yace: "Kull kull kull, Habiba! Nace maki kar na kara jin wannan zancen. Kaddara? Me yasa kike kokarin tona abin da muka rufe da addu'a a tsawon shekaru? Wannan irin maganar taki ne kike so ya jawo mana matsala, gaskiya?" Saba babban rigan sa yayi da sauri Yana tafiya a cikin falon, ya Dan tsaya yana kallonta da fushi amma cike da d'an rudani yace "Mu da muka rasa mafita sai muka yanke hukunci mai nauyi, yanzu kina kokarin dawo da tunanin da muka binne da hawaye? Wallahi bana son jin wannan zancen a cikin gidan nan!". Ya Dan numfasa da ƙyar, yana ƙoƙarin kwantar da zuciyarsa, yace "Wannan fa yaro ne da nake alfahari da shi, mai hankali da mutunci, karki manta yana da kima da da raja a idon duniya, Sai mu ɓata masa goben sa saboda abinda muke ɓoyewa a baya? Wallahi Habiba, ki dakata da wannan shirmen na kin." cikin murya mai rauni Hajja tace: "Toh me kake so na yi? Zuciyata cike take da tsoro… kai ka kalle shi, yaushe rabon da na ga ɗana yana dariya da walwala na gaske? Me zai hana na firgita, Abdullahi?" Ta karasa maganar tare da kiran sa da asalin sunan sa . Shiru ya sake cika dakin, na yan mintuna. Alhaji ne ya share gumin da ke kansa da hannunsa, a lokaci guda ya kalli matarsa cikin kallo mai zurfi,da nazari, amma bai ce mata komai ba, Sai ya juya a hankali, yana tafiya zuwa dakinsa, zuciyar sa cike fall da damuwa. Ba zato ba tsammani taji saukar Muryar sa. "Ki ci gaba da addu’a, Habiba, Wannan kadai ce mafita da muke da ita a halin yanzu." Yana gama fada'r haka Ya fice ya bar ta a falon, tana kallon bayansa, a hankali ta runtse idonta , hawaye na rige rigen gangaro wa a saman fiskan ta. A cikin katafaren dakinsa mai fadi da tsari, a hankali ya shigo , fuskarsa cike da damuwa, da nauyin abinda Dr. Farida ta sanar masa. Dakin nasa na alfarma ne, wanda yasamu gidauniyar ginin zamani, mai tsarin luxury design, tiles d'in dakin masu haske ne ,gadon nasa King-size ne, mai dauke da gadon fata da lallausan katifa , TV screen mai fadi,manne a bango, fitilun da ke fitar da haske mai launin fari da light blue ga kuma zane-zanen classic art manne a bangon dakin. Aword da abubuwan kyauta daga kasashen waje suna shimfide akan wasu shelf na ado . A gefe kuma akwai wardrobe din zamani wan da ake bude ta da fasahar "fingerprint". Cikin nitsuwa ya tsaya a gaban madubi, yana kallon fuskar sa dake nuna alamun gajiya, damuwa, da tsantsar karfin zuciya, a hankali Ya dafe kansa kadan, sannan ya fara tafiya toilet ya shiga domin yayi wanka. Wankan sa ya yi da ruwa mai dumi, da sabulun sa mai kamshi wanda yake odern sa daga Qatar, sannan ya fito yana sanye da farar doguwar rigar sleeping gown mai laushi, da santsi. Bayan ya fito, ya shimfida dadduma a wani sashe na dakin da aka ware don sallah, Ya rama sallolin da suka wuce shi, ya karanta addu'oin sa cikin kwanciyar hankali, Bayan kammalawa, ne ya zauna na dan lokaci cikin shiru mai karfi, yana tunanin abinda ya faru d'azu a asibiti. Zuciyarsa ce ta buga sau daya da karfi, Ya jingina da bango, sannan na dan Wani lokaci a hankali ya mike da d'an sassarfa ya nufi wata madai dai ciyar drawer da aka kulle da key, ya bude ya dauko Wani d'an kwandon da ke d'auke da kwalabe, na magunguna, a ciki ya zabi daya sannan ya sha, yana kallon maganin kamar wan da yake son tambaya: "Shin yaushe zan daina shan wannan magungunan ne?". Ya tambayi kansa. Bayan ya sha maganin, hayewa yayi kan gadonsa mai laushi, gadon da aka lullube da farin duvet mai dumi sosai, da kamshi na musamman. Cikin nitsuwa Yayi kwanciyar shi yana kallon silin d'in dakin, idanunsa na cike da hasken da ke kunshe da zafi da tarihi na shekarun baya. Kafin ya ankara, wani bacci mai nauyi ya dauke shi, sabi da maganin da yasha ma yana saka bacci, ga gajiya da ya taru masa. Nan take ya lula duniyar mafarki in da ya dauke shi, zuwa shekaru 21 da suka wuce lokacin kuruciyarsa, abubuwan da ya tsananta yarda cewa ya riga ya manta da su, ya gama shafe su a babin rayuwar sa sai ga shi a kullum in ya kwanta bacci sai sun dawo masa a mafarki. 💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 3️⃣ Aliyu Abdullahi Turaki shi ne cikakken sunansa wan da akeyi wa lakabi da AA Turaki, in da mahaifiyar sa kuma take kiran sa da suna "Yero" kasancewar sa d'an fari a gunta kuma da d'aya tiloh a gurin su, Alhaji Abdullahi Turaki bafulatani ne daga rugagen Gembu, cikin tsaunukan Mambila Plateau, wanda ya tashi cikin arziki na noma da kiwo asalin Mahaifinsa makiyayi ne mai daraja, amma daidai gwargwado ,mutumin kirki, ne amma babu isasshen ilimi, sai tarbiyya da gaskiya a wanchan lokacin. Aliyu tun yana yaro, yana da hangen nesa da kwadayin canza rayuwarsa da ta iyayen sa, Duk da halin rashin wada ceccen ilimi da suke ciki a yankin su, haka ya dage da karatu yana tafiya makarantarsu mai nisan gaske daga gida, a koda yaushe, kafin wata ƙaddarah ta gifta musu, su ka baro ainihin yankin su sukayi hijira zuwa garin kano, anan garin kano ne Aliyu yaci gaba da karatun sa na secondary bayan doguwar jinya da sha fama da ita wanda iyayen sa suka cire rai da tashin sa cikin ikon Allah da karfin addu'ar su Allah ya sake daga kafad'un sa sai dai ya kamu da ciwon zuciya da ake kira da mild heart condition, saka makon damuwa da ba'cin rai da ya shiga a baya. Bayan ya kammala karatun secondary school, da sakamako mai kyau, ya fito sabi da kwazon sa, a haka ya samu ya jona jami'ar Ahmadu Bello University , in da ya karanci business administration, bayan ya kammala ne ya fito da result in da ya zama first class ya samu scholarship daga wata NGO, Bayan ya gama digirin sa na farko, ya samu damar zuwa UK inda ya yi Master’s a fannin International Business Management a London School of Economics, bayan nan ne ya jona degree din sa na uku a UK wato Phd , bayan haka ya karbi horo na musamman daga Executive Education domin kara kwarewa a harkar jagorahn ci da nazarin kasuwan ci, Daga nan ne rayuwa ta fara sauyawa, inda yafara halartar tarurruka na musamman kamar su , project management profession, Business networking, digital marketing da sauran su. Yana da kwarewa, hikima, da iya sadarwa da kowa, hakan yasa bayan ya dawo Najeriya, ya kafa kamfanin farko mai suna Turaki Global Ventures, wanda ya fara da kasuwancin shigo da kayayyaki daga kasar China da Turkey. Zuwa cikin shekaru 10, AA Turaki ya zamo jigo a harkar kasuwanci a Afrika. Yana da manyan kamfanoni a fannoni da dama kamar su: - Turaki Holdings Ltd – kamfani na kudi da hannayen jari - Turaki Oil & Gas – yana da rijiyoyin man fetur a Najeriya da Angola *Turaki Real Estate – gini da mallakar manyan gine-gine a Dubai, Abuja, Accra, da Istanbul - Turaki Agro & Food Ltd – kamfani mai sarrafa kayan gona da fitarwa zuwa waje - Turaki Airlines (JV project)– wani kamfani da ke tattaunawa da gwamnatin kasar Qatar akan kafa jirgin sama Duniya ta sanshi a matsayin "Africa's Silent Billionaire", saboda hankali da natsuwarsa, baya shiga barkwanci da fallasa sirrin rayuwar shi. Hukumar Najeriya (Federal Government),ta ba shi lambar girmamawa, saboda gudunmawarsa ga ci gaban tattalin arziki, har ta zuba hannun jari a daya daga cikin kamfanoninsa na makamashi da man fetur. Kasashe kamar UAE, Turkey, UK, China, Qatar, da Saudi Arabia suna da hannun jari a kamfanoninsa – sannan ya kasance memba ne a International Business Council. Tattaunawarsa da kasashen duniya kan batutuwan kasuwanci da cigaban Afirka sun sa ana kiransa "Voice of Emerging African Capitalists". 5 YEARS BACK... A lokacin da harkokin sa su ka kan kama ,zuwa wannan lokacin AA Turaki ya zama babban business tycoon a Africa baki daya, zuwa lokacin ya tattara iyayen sa sun koma Abuja da zama, duddah shi kan sa bai cika zama a Nigeria ba. Hajiya Habiba wacce yake kira da Hajja tana zaune a kan kujera mai lallausan fata, a hankali ta gyara mayafinta . Aliyu Turaki ne zaune a gaban ta ya na zaune cikin natsuwa, yana sauraron mahaifiyarsa. da murmushi Hajja tace "Yeroh yau kimanin shekara talatin da biyar fa kayi... Ba aure lokaci yayi da zaka samu mace mai tarbiyya da zaka kira taka. Ga Ramlartu nan ’yar kawata ce, naga halinta tun tana da hankali naya ba da halinta. Yarinya ce mai ladabi da hankali. Kuma ta na girmama ka sosai, uwa uba kuma tana mutuwar son ka." Cikin nitsuwa Aliyu ya dago kai kadan, ya kalli mahaifiyarsa, sai ya sauke ajiyar wata nannauyan ajiyar zuciya. "Ina jin ki Hajja, Idan kina ganin hakan shine mafi alheri, a gareni na yarda da zabin ki." "Ya amince da auren ba tare da soyayya ba... saboda biyayya da girmama mahaifiyarsa. Auren da aka daura cikin girma da kima amma zuciyar sa ba ta tare da auren, sabo gan gan jikin sa ne kawai a auren." Haka ya ke zaman aure da ramlart duddah baya son ta amma bai taba yi mata wulakancin akan hakan ba , sai dai ita kanta ta san zuciyar Aliyu Turaki ba mallakin ta bace. *********** CİGABAN LABARİ GWARİNPA ESTATE. Anguwar tana cikin wurare ne da gwamnati ke ware wa manyan ma’aikata. Unguwa ce mai tsari, tsafta da tsaro. Gidan da Dr. Farida ke zaune da mahaifiyarta da ɗanta yana cikin layi mai natsuwa Da babu hayaniya, a kusa da babban titin Estate din. Kamar kullum, Dr. Farida ta iso gidan da motar ta Toyota Corolla 2021 – metallic grey, motar da asibitin National Hospital Abuja ya tanada mata a matsayin wani daga cikin fa’idar matsayinta a asibitin. Motar ta tsaya a gaban gate din gidan, Gate man ne ya ruga da gudu ya bude, ganin motar ta ne yasa shi washe baki tare da gaishe ta yace "Welcome madam!" tana amsawa da murmushi d'auke akan fiskar ta, kutsa motar tata tayi cike da nitsuwa take tukin, d'an madai daicin parking space din dake cikin gidan ta nufa , parkin tayi tare da tattaro jakan Office din ta ta fito, had'e da rufo kofar motar, main parlourn ta nufa. Cikin gidan, akwai kyakkyawan bungalow mai bene guda Daya, an tsara shi cikin salo irin na zamani, Gidan yana da veranda wan da aka kawata da furanni masu dad'n kamshi, a gefe guda akoi kujerun hutawa. A cikin parlorn kuwa komai yana nan tsaf tsaff da shi ga kyawawan labulaye, kayan dakin masu simple ne babu hayaniya amma masu tsada,ne ga wani kamshi na turaren wuta da yake tashi, mai sanyaya zuciya. A cikin gidan, tana tare da mahaifiyarta Hajiya Zainab wacce take kira da Dada dattijuwar mace mai launin fata, mai dan haske amma ba sosai chan ba, tana da kamun kai da halin kirki, da ɗanta Ameer kyakkyawan saurayi mai shekaru 14, fari ne sol, yana dauke da idanu masu kama da na uwarsa Dr farida. Dr. Farida ne ta shigo cikin gidan cikin nutsuwa, tana sanye da kayan aikin ta, a hankali ta jingina da ƙofar parlor, tana kallon ɗanta, Ameer mai shekaru 14, kyakkyawan yaro ne da ya jima yana bin sahun mahaifiyar sa. Yana da fata mai haske da laushi, fuskar sa na d'auke da annuri da manyan idanu irin na mahaifiyarsa, A lokacin yana zaune kan kujera yana karanta wani littafin sa na school wanda aka basu homework. "Ummi welcome!" Ameer ya miƙe da sauri ya na mai rungume mahaifiyartasa. Ba shiri Dr Farida ta saki murmushi, tare da cewa “Nagode masoyina, ka kammala karatun ka kenan?” Mahaifiyarta, Dada ce , ta fito daga ɗakin girki rike da flask, a hannun ta. fuskan dattijuwar na d'auke da nutsuwa da hikima. “Farida, sannu da dawowa, lale maraba , da gani Kin gaji da aiki?” ta karasa maganar tare da zuba mata idanun ta. “ cike da nitsuwa tace Eh Dada, wallahi yau rana ce mai nauyi a gare ni yau na duba petient da yawa,” Farida ta ce yayin da take kokarin cire hijabin ta a lokaci guda tana kaiwa kan kujeran dake cikin parlorn. Dada ce ta ajiye flask din a kan table, ta zauna kusa da ita, tana kallon ta cike da tausayin rayuwar yâr tata dake cike da jarrabawa da kaddarah. “Farida,” dada ta fad'a cikin tausasawa, “Na san rayuwar ki ba abu bane mai sauki , Kin jure abubuwa da dama, amma Allah zai saka miki, ki Duba Ameer, ya girma cikin tarbiyyar da kika bashi , hakika ke din kin cika mai juriya.” A hankali Dr Farida ta juyo, idonta ya gama cika da ƙwalla amma bata bari ta zubar da su ba. “Dada, kin yi ƙoƙari, a rayuwar mu, Ban taba jin nauyin rayuwa irin yau ba, Amma na godewa Allah da ya bani ke a matsayin ki na mahaifiya ta.” Ameer ne ya matso kusa, da ita ya dafa kafaɗar ta, yace. “Ummi, I’m proud of you.” Mee too shine abunda ta iya fad'a masa tare da sake rungume shi tana mai sauke ajiyar zuciya. Duk da cunkoson aiki da raɗaɗin abubuwan da suka gabata, arayuwar ta Dr Farida tana jin kwanciyar hankali a cikin wannan ƙaramin gidan nata tare da yaron ta da kuma mahaifiyar ta da ke ci gaba da ba ta ƙarfin guiwa akan rayuwa. Dr. Farida ta daga kafarta a hankali ta mike inda take zaune a falon su, tana na mai kallon Ameer ,fuskar ta cike da nutsuwa da kwanciyar hankali, Tana murmushi kadan yayin da take duba lokaci a agogon bango. Cikin natsuwa da tsafta irin ta likita mai kamala, ta mike tsaye tare da cewa. "Dada Zan shiga na kimtsa jikina," ta karasa fada cikin d'an fara'a, tana kallon mahaifiyarta da dan nata. Cikin nitsuwa Ta nufi dakin ta, tana taka tiles din fale-falen, kamar wacce bata son taka kasa kan bene masu sheki da kyan gani, ta nufa . Dakin nata dan madai dai ci ne da ya cika da tsari da tsafta an kawata shi da kyawawan labulaye masu launin shudi da beige. Gado ne mai dan faɗi, ya na lullube da farin bedsheet mai laushi da tawul dinta nade a gefen pillow. A jikin bango kuwa akwai mirror mai fadi, wardrobe mai launin itace, da shelf ɗin da aka jerawa kayayyakin kula da fata da perfumes masu ƙamshin, gaske . Cike da nitsuwa Ta shige bathroom nata, wanda ke hade da dakin. Tana shiga ta kunna

Chapter 2 of 7