ruwan zafi ta dan surka dana sanyi yanda zai yimata dad'in amfani, ta shiga wanka tana jin sanyi da d'an nutsuwa a zuciyarta.
Bayan ta fito, ta shirya cikin kayan shan iska marassa nauyi masu shegen kyau, ta sanya turare wanda ya lullube dakin gaba d'aya da ƙamshi mai shegen dadi.
A mai makon ta zauna ta huta sai ma Ta sake fitowa zuwa falon su, inda mahaifiyarta dada ke dora abinci a kan dining table.
Yayin da Ameer na gefe yana ta buga game a waya yana dariya shi kad'ai.
A hankali Dr. Farida ta zauna a gefen su cikin jin daɗin kasancewa da iyalanta.
Ta dora hannunta a kafaɗar ɗanta tana kallon Dada dake kok'arin saving d'in su abinci tace.
"Allah ya bar min ku, Dada na, na gode da zama ginshikin farin cikin Rayuwa ta."
Cike da kulawa Dada ta d'an girgiza kanta tare da cewa.
"Allah ya barmu da kaunar juna ungo maza karb'a kifara cin abincin kar ya huce"
Haka ta gama saving din su gaba d'aya wajen ne ya d'auki shiru kowa ya maida hankali akan cin abincin sa dama haka al adar su take in amfara cin abinci to fa ba a magana sai an kammala.
💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫
✍️Mrs Alkali
Page 4️⃣
Ranar Wednesday da safiya, hasken rana ya ratsa tagar dakin da Ramlart ke ciki a Obstetrics and Gynaecology Department.
Tana kwance kan gado cikin wani irin shiru mai nauyi, Idonta a rufe, suke ruff kamar mai bacci ,amma tunaninta yana yawo kamar iska mara iyaka, Kusan kwana biyu kenan da AA Turaki ya zo duba ta tun wanchan ranar bai sake leƙo asibitin ba, bashi ba alamar sa, Ba saƙo, ba waya, ko da kuwa takira wayar sa baya shiga, Cikin zuciyarta tana yunkurin kwantar da hankalinta, amma rudani da tsoro sun cika ta.
Anty Hauwa ce ta zauna a gefenta tana karanta addu’oin azkar cikin nutsuwa, Ramlart ta juyar da kanta gefe kamar mai jin barci, tana ƙoƙarin boye damuwarta, sabi da bata son Aunty hauwa ta fahim ta, Amma chan cikin zuciyarta ji take kamar za ta fashe da kuka, tsabar tashin han kalin da ta shiga.
“Ko dai Dr Farida ta sanar masa ne? Ko dai gaskiyar da na ke boye wa ne... Shike nan ya gaji da ni?” ta furta cikin ranta, tana runtse idon ta da ƙarfi.
Sai da Anty Hauwa ta tashi don yin sallah n walaha a masallacin cikin asibitin, nan ne Ramlart ta bude idonta da sauri, Ta kama pillow da hannunta biyu, ta matse shi sosai tana kokarin danne hawayen da suka taru a idonta.
A wannan lokacin, ne ƙarar bude ƙofar ya katse shirun nata, Nurse ce ta shigo da takarda a hannunta.
"Madam Ramlart, Dr Farida ta aiko da takardar sallamar ku daga asibitin."
Ramlart ta kura wa nurse ɗin ido, da d'an mamaki da firgici, ta sa hannu Ta karɓi takardar da hannunta dake rawa, Idonta ne ya sauka kan saƙon Dr Farida cikin rubutun masu kyau da tsafta:
“Based on medical recovery and psychological observation, the patient is hereby discharged for home-based care. Further appointments will be communicated if necessary.”
Hannunta na rawa ta ajiye dakardan akan cinyar ta a lokaci guda Ta lumshe idon ta, zuciyarta cike da fargaba.
Ba kawai sallamar ba ce ba taso ba, a'a sai dai wani ɓangare na zuciyarta ya tabbatar da cewa yanzu abubuwa za su fara canzawa.
“Shikenan... ko da gaske Aliyu ya san gaskiya , san nan zai iya fita gaba ɗaya daga rayuwata?” ta tambayi kanta cikin kame-kamen zuciya da kuka.
Aunty hauwa ce ta shigo,cikin dauriya da Karfafa wa kanta guiwa ta mikawa Aunty hauwa takardan, ganin anyi discharge din su ne yasa aunty hauwa takira musu motar family drivern da ya kawo su.
Bayan sallamar su daga asibiti, aka dawo da Ramlart gida cikin motar family driver, Tana zaune a baya tare da Aunty Hauwa, zuciyarta cike da shakku da fargaban , abun da zata tarar.
Motar na tsayawa a gaban katafaren gidan AA Turaki dake Maitama, Ramlart ta sauka cikin nutsuwa amma zuciyarta na bugawa da ƙarfi, Aunty Hauwa ta kalleta tana murmushi mai taushi tace .
“Ki kula da kanki kinji? Ki huta da kyau, zan wuce gida yanzu in duba su Momy da yara, na san warhaka duk sun gama damunta”
A hankali Ramlart ta rungume ta jikin ta duk yayi sanyi tace “Nagode sosai Aunty. Allah ya saka da alheri.”
Bayan ta rakata har bakin ƙofa, ta koma cikin gida kai tsaye ta nufi part ɗin Hajja, mahaifiyar AA Turaki.
Tun kafin ta shiga ciki sosai, kamshin turaren dakin da shaukinsa ya ratsa hancinta, amma duddah haka bai rage mata tsoro da fargaba ba.
Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka Ta shiga dakin cikin ladabi, ta zauna a gaban Hajja wacce ke zaune kan kujera tana jan tasbihin ta.
Hajja ce : ta dago kai da wani ƙyalli cikin idon ta tace “ Ramlart, kin dawo Lafiya?, ya jikin naki.”
Cike da kunyar kanta Ramlart tace: “Eh Hajja...jiki da sauki nagode da addu’arku.”
Hajja ta aje tasbihinta, ta gyara zama kamar mai son fad'ar wani abu.
“Na yi shiru ne ban ce komai ba tun da kike asibiti, Amma yanzu dole ne na fada, Wannan halin da kika jefa kanki da ɗanmu a ciki, ba abu ne da zan iya rufe ido a kai ba.”
Ramlart ta saki ajiyar zuciya, ta sauke kai ƙasa.
Hajja taci gaba da cewa: “Shan maganin zubar da ciki? Auren shekaru biyar babu haihuwa, yanzu kuma sai ki jefa kanki cikin barna? Kin san irin raunin da kika jefa ɗanmu ciki kuwa?”
Ramlart ta dafe ƙirjinta da hannayenta biyu, hawaye na zubo mata, akan kuncinta tace.
“Hajja… wallahi nayi nadama ,Na tuba… bazan sake ba, ki yafe mini , sharrin shaidan ne.”
Sai da Hajja ta kalle ta na tsayin lokaci kafin ta ɗan sauke muryar ta kasa tace.
“Toh idan da gaske kike, ki nuna hakan da kyakkyawan hali, ba da baki kawai ba, Saboda abin da kika aikata na iya hanaki samun haihuwa har abada.”
Ramlart ta share hawayenta, ta juya da ƙyar, ta fice daga part ɗin cike da kunya da danne danne.
Bayan ta fito daga bangaren Hajja, Ramlart ta shige part ɗinta cike da rudani da tashin hankali, Jikinta ya yi sanyi zuciyarta na bugawa da karfi.
Kalaman Hajja sun daki kunnenta fiye da yadda take tsammani.
Cike da tsoro da matsin lamba, ta janyo wayarta daga cikin jakarta, ta danna lambar kawarta Zuly,tana dağa wa.
cikin rawar murya ramlart tace:
Hello... Zuly… please ki same ni a chat yanzu yanzu… wani abu ya na shirin faruwa… we are in trouble!
ZULY ce tace:
Lafiya? Me ya faru kuma?
Wani irin tsaki, ramlart ta sake ,hawaye na kokarin zubo mata tace:
An gane Zuly! Wallahi Hajja ta yi min zancen pills… kuma daga ni cewa tana da hujjojin da ke nuna ina sha.
Bata bayyana komai ba sosai, amma na gane cewa suna zargin na!
cikin firgici Zuly tace:
What?! Ta yaya? Waye ya tona mana asiri?
Cikin tashin hankali RAMLART tace :
Ban sani ba! Amma naga alamar Dr. Farida ce ta sanar da AA Turaki, shi kuma tabbas ya gaya wa mahaifiyarsa, kin san shi Mama's boy ne, Kuma yanzu wallahi na shiga uku… bansan yadda zan fita ba.
zama tayi a bakin gado, ta rungume pillow, zuciyarta na tafasa.
ZULY ne tace:
Calm down babe... ki nutsu. Sai mu nemi wata hanya, kema kinyi ganganci da kika yarda aka kaiki family hospital,ke da zakije private hospital inda muka saba zuwa ,haba ramlart saikace ba Wise ba .
Yanzu dai Ki ci gaba da nuna nadamar ki a gaban idon su.
Ki dinga nuna kamar kin chanja. Sannan... sai mu shirya sabon matakin da ya dace ,Wannan ba karshen komai bane, sai dai mafarin lamarin.
Ajiyar Zuciya ramlart ta sauke tace..
"Zuly wlh bansan ya akayi ba kawai dai na tashi na tsinci kaina national hospital tare da Aunty hauwa, yanzu dai ba wannan ba, kin san kuwa Hajja tana kok'arin shiga sabgata kuma na lura itace matsalata a cikin gidannan, tsohuwar tana bani ciwon kai wlh."
Cike da zafin rai ZULY tace:
Sai mu fitar da ita gaba ɗaya. Wannan game ne yanzu... kuma dole mu ci.
RAMLART ce ta shaki iska sannan tace:
Na yarda dake Zuly… amma wallahi bana jin dadin wannan zaman da nakeyi a gidan nan, ke dai kin riga da kinsan komai, kyansa da dukiyar sa nake so,Idan mahaifiyar sa ta cigaba da shiga rayuwar mu… zan iya rasa komai.
Kin san da cewa bayan kin kawo mini pills din ,bayan tafiyarki nayi amfani da su ,kamar dai yadda aka saba, kwatsam sai ciwon ciki ya turnuke ni ,tsabar wahala ban san lokacin da nakira aunty hauwa ba a waya ,shine fa tazo ta kai ni a sibitin,kin san in ba haka ba da asirin mu bazai tab'a tonuwa ba.
Ke dai karki samu damuwa kawata da zaran mun had'u komai zai dawo dai dai, cewar zuly.
Ramlart ta kashe wayar a hankali, ta jingina da jikin kujera tana kallon bango, zuciyarta na shirya mata sabon makirci mai cike da hadari...
💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫
✍️Mrs Alkali
Page 5️⃣
Bayan sallar isha’i, da misalin karfe 9:30pm Dare ya lullube garin, iska mai sanyi na kadawa ta window.
A hankali Ramlart ta turo kofar dakin ,Tana sanye da doguwar riga ta satin mai launin shudi, da santsi, Fuskarta cike da nadama da tsoro a lokaci guda.
AA Turaki yana tsaye a gaban mirror yana cire agogon hannunsa, d'an bai jima da shigowa gidan ba,ido ya zuba mata yana kallonta ta cikin madubi.
A hankali RAMLART tace.
"Na shigo ciki, Honey?"
ba tare da waiwaya ya kalle ta ba yace:
"Kin shiga ai tuni... tun da kika yanke hukunci da kanki kina shan magungunan da zasu zubar miki da ciki ba tare da shawara ba."
A hankali kamar wata munafuka, Ramlart ta karaso kusa da shi, ta tsaya daidai bayan sa, ta sa hannayen biyu ta rungume shi tabaya, ta kontar da kanta a bayan sa tare da lumshe idon ta tana kokarin dakatar da sauk'an hawayenta.
Cikin Muryar kuka tace.
"Dan Allah kayi hakuri. Ba haka nake so ba... kawai tsoro ne... kuma shawarar kawata ce."
Cikin nitsuwa ya juyo cike da izzah, kyawawan Idonsa ya zuba mata, wan da ya sa tafara diriri cewa .
Kamar wanda bazai ce komai ba a bazata taji saukar Muryar sa.
"Shawarar kawarki ce? Kina da miji, amma har kawarki ce ke tsara miki rayuwar auranki? Wannan ba ƙaramin gazawa bane Ramlart."
Shiru ne ya biyo baya, Ramlart ta sunkuyar da kai Ƙasa alamar ta yi nadama.
cikin kakkausan murya yace:
"Wani irin tsoro ne ya hana ki son haihuwa? A ina kika ajiye tsoron Allah? Kina sane da irin sharrin da zubar da ciki ke da shi? Kina sane da cewa Allah ya haramta hakan?"
Ramlart ta fashe da kuka tare da cewa.
"Wallahi ban san zai kai haka ba. Nayi kuskure... dan Allah kayi hakuri..."
Kai tsaye yake kallonta:
"Ba fushi nake da ke don na rasa ciki ba, Ramlart.
Fushi nake da zuciyarki mara tsoro da biyayya ga Ubangiji.
Abin da na ke nema ba kawai haihuwa ba ce , ina neman mace mai daraja, mai tsoron Allah da sanin hakkin aurenta."
Cikin nitsuwa Ya juya, ya zauna a gefen gado, Ramlart ta biyo shi tare da durƙusawa a gaban sa cikin kuka tace.
"Na tuba... wallahi bazan sake ba..."
ya dauki lokaci kafin ya kalleta, kamar mai karantar yanayin ta, gently yace.
"Allah ya sa ki tuba daga zuciyar ki, Amma ina so ki sani... ki kiyaye sake faruwar hakan a karo na biyu."
Yana gama fada'r hakan ya mike, ya shiga bandaki.
Ramlart ta tashi daga durƙushewar da tayi a ƙasa, tana kok'arin share hawayen ta, gefen gadon ta samu ta zauna tana ta kok'arin danne zuciyar ta.
Baiyi tsammanin har yanzu tana cikin ɗakin ba, ya fito daga bathroom yana shafe lallausan gashin kansa da towel, yana sanye da dogon robe mai launin fari, ruwa na diga daga gashinsa.
Fuskarsa na nuna alamun gajiya da rashin walwala.
Ramlart, wacce ke tsaye kusa da gado , ta nufo shi da murmushi da iyeyi a d'auke a fuskarta.
Cikin muryar raɗa-raɗa tace:
"Honey... dan Allah kayi hakuri. Na gane kuskurena, Ka gafarce ni…"
Tsayawa yayi cak, Ya kura mata idon sa masu kara birkita mata lissafi, Wata irin ƙunya da bacin rai na bayyana a saman fuskarsa, Bai ce mata komai ba, ya wuce ta gefenta yana dan girgiza kai.
Cike da iyeyi ta sake matsowa kusa, dashi ta ɗora hannunta a kafadarsa.
cikin sanyin murya tace:
"Wallahi, ina kaunarka, Duk abinda nayi saboda tsoro ne…"
Cike da takaici, ya fizge kafadarsa, cikin kakkausan Murya yace .
"Don Allah ki fita daga daki na kafin na rasa haƙuri na! Ki fita Ramlart!"
tsayawa tayi, idonta na cikowa da hawaye, amma kafin ta iya ƙara wata magana, ya tura ta da hannunsa har ta ja da baya kad'an.
Bai bata lokaci ba, ya karasa bakin ƙofa, ya bud'e kofar, ya nuna hanyar da yatsar sa da karfi yace.
"Get out!!"
Wani irin kuka mai rauni, Ramlart ta sake tare da ficewa da sauri, tana share hawayen ta.
rufe kofar ɗakin yayi da ƙarfi sannan ya juyo, ya tsaya na dan lokaci kamar yana tunanin wani abu.
Cikin nitsuwa Ya karasa gaban wardrobe ya ɗauko pajamas dinsa masu taushi, ya shirya jikinsa cikin natsuwa kamar babu abinda ya faru.
Daga nan ya nufi gado, ya shimfiɗa kansa kan babban pillow mai santsi, ya rufe idonsa cikin natsuwa.
Kamar wanda ya rasa nutsuwar sa, ya juyo gefe guda yana kallon bangon dakin.
A zuciyarsa yana tunani, rayuwar sa maiciki da kaddarah.
Ramlart da guduTa fado saman gadonta da karfi, ta juyo ta kwanta tare da kifa cikin ta a kan gadon, daya hannunta na rike da wayarta.
Tana fitar da numfashi da sauri, idanunta sun kada da sunyi jawur da hawaye .
cikin takaicin abunda AA Turaki ya mata tace
"Haba na shiga uku... Kamar ni Ramlart ya ke korata daga dakin sa? Ni matar auren sa!"
Cike da bacin rai Ta kamo wayarta, ta shiga contact ta danna sunan Zulya a cikin lambobin ta.
Bayan kiran ya shiga, tana Jin Zuly ta dağa tafara magana kawai cikin kunar zuciya.
"Zuly! Wallahi na gaji! Ni Turaki ya kora daga dakin sa kamar wata ‘yar aiki!"
ZULY ce tace .
"What?! Haba mana! Me kikayi masa har ya kai ga hakan?"
cike da fushi ramlart tace.
"Babu abinda nayi masa! Na je ne kawai domin na bashi hakuri akan maganar abortion... Amma wallahi ya na fitowa daga bathroom, ya kalleni kamar wata house maid, ya gwasale ni sannan ya turoni waje ya kullo kofa!"
cikin dariyar rainin wayo Zuly tace .
"To yanzu ya kamata ki gane cewa wannan mutumin bai taba sonki ba a cikin zuciyar shi.
Kawai biyayya ce ta sa ya aure ki. Hajja ce ta tilasta shi. Kuma ki tuna kin riga kin fada cikin auren da ba soyayyah sabi da haka zaɓi yana gare ki."
Wani irin hawayen bakin ciki ne suka shiga sauko mata kafin tace.
"To ya kike ganin zan yi yanzu Zuly?"
Cike da makirci Zuly tace
"Ki daure zuciyar ki, ki daina zama mai rauni, a duk san da ya wulakanta ki.
Ki saka a ranki cewa ba zaki bari wannan auren ya zama nasara a hannunsa ba.
Idan ba zai girmama ra'ayin ki ba, to zai ji da consequences.
Shiya sa nace Ki riga ki fara da samun wata hanya da zai daina tunanin wata mace face ke ko da uwar sa ce dan a yanzu na lura ita ce babban matsalar ki."
share hawayenta tayi kafin tace.
"To Zuly... ki fada min abin da zan fara da shi."
Wani irin shewa Zuly tayi tare da cewa
"Kar ki damu... zan turo miki wasu abubuwa na musamman da zasu fara aiki cikin kwana biyu. Sai ki kula da komai yadda nace, nan ba da jimawa ba, za ki fara juya shi kamar yadda kike so. "
A hankali ramlart tace.
"Zan bashi darasi da ba zai taba mantawa ba..."
Daga haka ta kashe wayar tare da kwanciya abunta, ranta cike da sake sake.
Wani fili ne mai cike da kore-koren ganye da bishiyu, ga wani irin iska mai sanyi yana kadawa.
Rana ta d'an hasko kadan daga sama, wata ƙaramar yarinya ce ‘yar kimanin shekara 15, kyakkyawar fulaniya ce, tana sanye da rigar atamfa da gyale a kanta.
Idon ta cike da hawaye, tana kuka sosai, Hannunta na rike da wa wani yaro, karami, kyakkyawan gaske .
Cikin kuka YARINYAR tace.
"Ka tafi ka barni... Ka manta da alkawarin ka... Ka manta da ni..."
AA Turaki, wanda ya tsaya can nesa, da yarinyar, yana kallonta cike da rudewa, yana kokarin karasowa kusa da ita.
"A’a... ban manta ba. Ki tsaya... don Allah kar ki tafi..."
Sai kawai gani yayi tana juya baya, tana tafiya a hankali har cikin wani duhu mai sarkakiya.
Yana kokarin bin ta amma yaka sa yin hakan .
Cikin firgici ya buɗe idonsa, numfashinsa ya fara hawa sama da ƙasa.
Murya cikin wahala yace.
"Subhanallah... Pullo a'm (Fulani nah)? Ita ce fa…"
A hankali ya shafa saitin Zuciyar sa cikin raunarniyar Murya yace . "Kiyafe mini" har yanzu kina raina ƙaddarah ce taraba mu.
Yana rik’e kirjinsa, yana jin wani irin ciwon zuciya da alama ciwon zuciyar na son tashi.
Jikin sane yafara girgiza kamar mai shirin faɗuwa, Ƙasa .
Cikin sauri da wahala, ya mika hannu ya buɗe drawer na gefen gadon sa.
Ya ɗauki kwalin magani na ciwon zuciya (nitroglycerin capsules), ya bud'e, ya dauki daya, ya saka a bakinsa, ruwan da ke ajiye a gefen bed site drower ya dauka ya sha .
Cikin mintuna kaɗan, numfashinsa ya dan daidaita, yana ƙoƙarin komawa normal .
A hankali Ya jingina da gado yana rike da kirjinsa har sai da ya sauke ajiyar zuciya, da alam yaji relief.
cikin raunin murya yace .
"Allah ka kare min su... kada ka bari wani abu ya cutar da su, su di'n rayuwata ce..."
A hankali Ya lumshe idonsa, yana jin jikin sa na sanyi.
Bacci mai nauyi ya sake ɗaukarsa, a wannan karon baccin da ya fi na farko nisa, cike da gajiya da kumburin zuciya.
💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫
✍️Mrs Alkali
Page 6️⃣
GWARİNPA ESTATE.
Dr. Farida ta fito daga dakin ta cikin shigar aiki ,medical scrubs masu launin sky blue, farin lab coat a saman, su tana ƙamshin turare mai shegen dad'i da sanyaya rai, Gashinta yana sanye da medical cap.
A hankali Ta sauko zuwa falon, murmushi d'auke a saman fiskan ta.
cike da annashuwa tace.
"Assalamu Alaikum Dada… Good morning Ameer." Ta karasa maganar tare da kallon su.
cikin farin ciki dada ta ce.
"Wa alaikumus salam, ya'r albarka. Allah ya sa alheri ya cigaba da bibiyar rayuwar ki, har kin kammala shiri kenan?"
AMEER dake shirye tsaf cikin uniform din makaranta yace.
"Yes Ummi! Na shirya… kawai ke nake jiran kizo muyi breakfast ."
Dada ce tace.
"Ku zo ku ci kafin lokaci ya kure… ba zan yarda ku fita cikin yunwa ba."
Dariya Dr Farida tayi tare da zama akan d'aya daga cikin kujerun dake jere a dinning table din.
tea, bread, kwai, da fruits, sai flask da dada ta d'aura a tsakiyar table din.
AMEER dake shan kankana ne yace.
"Ummi, dada… zan iya kunna TV in duba morning news?"
Dr FARIDA ta kalli Umma, ta gyada kai a hankali tace.
"To na baka mintuna uku kawai."
Cikin jin dadi Ameer ya dauki remote, ya bude channel na Africa Sunrise News.
Ya samu Ana maimaita wani exclusive interview da babban Business Tycoon AA Turaki.
Sanye yake cikin manyan kaya, yana magana cike da nutsuwa da izza, yana bayyana irin taimakon da yake baiwa matasa da sabbin entrepreneurs, dakuma nasarorin da ya samu a rayuwa da irin gwagwarmayar da yasha kafin taka matakin.
Cike da nitsuwa yake jawabi a cikin TV
"...muna kokarin ganin an samu cigaba, musamman a fannin ilimi da lafiya. Kowa yana da damar cigaba matukar yana da niyyar aiki tukuru."
Ameer ne ya ke kallon shi cike da sha’awa.
Sai ya kalli Dr Farida yace.
"Ummi..! kin ga wannan mutumin ina matukar kaunar sa, nima irin sa nake so na zama idan na girma, amma ummi kin taba ganin AA Turaki?
Cike da basarwa, Dr Farida ta daure fuska tana kai bread cikin bakin ta tace.
"AA Turaki? A'a… ban sanshi ba sosai kuma ban taba ganin sa ba."
Dada ce ta dauki remote cikin sauri ta kashe TV din, tace
"Toh baki abun magana ba kaga lokaci na tafiya ba ne, Za ku makara fa.
Dr Farida ne tace.
"Tashi mu wuce kafin traffic ya fara."
Takara sa maganar tare da miƙewa a lokaci guda kuma tana goge bakinta da tissue.
Ameer ya tashi yana murmushi, Dr Farida ta mike ta dauki jakar aikinta, tana kokarin boye sauyin yanayin fuskarta.
"Okay ummi, cewar Ameer da ya bi bayan ta hannun sa rike da jakar makarantar sa.
A haka Suka karasa mota wata silver Toyota Corolla 2021, mai dauke da plate number na National Hospital.
Ta bude masa kofar baya, ya zauna. Ita kuma ta shiga driver's seat, ta kunna mota, suka kama hanya.
Ameer yana zaune yana kallon ta ya saki wani cute smile yace .
"Ummi, kin fi kowa kyau a cikin wannan uniform din ba kiga yadda kike da kyau ba."
murmushi ta sake tare da cewa.
"Kai Ameer, baka gajiya da shirme wlh."
Haka Dr Farida ta sauke shi a makaranta, ya yi mata bankwana.
İta kuma ta ci gaba da tafiya zuwa asibitin, dan da alama yau ta kusa makara.
Dr Farida tana parking a filin ajiye motoci na ma’aikata, tana jin sautin iska da shigowar wasu motocin cikin harabar parking lot din.
Wani black Toyota Camry ya shigo a dai-dai lokaci daya da ita.
Dr. Imam, ne cardiologist Dr ne a cikin asibitin wato likitan da ya shafi bangaren zuciya, ya fito cikin sauri da murmushi, yana nufeta tare dacewa.
"Dr. Farida! Good morning.
Ya Subhanallah, yau kin kara kyau fiye da kullum my Love."
Cike da nitsuwa Dr Farida ta dauki files dinta, ta juya tana fuskantar sa, tare da rufe murfin motar sa tana dan murmushi mai had'e da natsuwa da class tace.
"Good morning, Dr. Imam.
Ka ga lokacin aiki na Kara matsowa, ga shi yau mun makara ?" Tana fad'an haka ta wuce ta gaban sa.
Da sauri Dr İmam yana bita a baya, yana takawa a hankali yace.
"Wallahi har yanzu bana jin dadin yadda kike kaucewa maganar da ta shafi tsakanin mu dake.
Dr Farida, wannan zuciyar tawa tana bukatar kulawarki… ina da rauni akan soyayyar ki."
A haka Suka karasa harabar Office din OB GYN, suka shiga cikin block din a tare.
Bud'e office din ta dake jare tsaf tayi, ga wani irin ƙamshin Air freshner dake tashi wanda ya gauraya da asalin ƙamshin turaren jikin ta, DR. IMAM ne ya zauna a wata kujera da ke kusa da teburin ta ya sake cewa .
"Ni fa bana jin dadin yan da kika ki bani dama, Kin san zan iya turo iyayena a gobe in kin yarda. Amma sam kin ki ki bani daman hakan..."
Bayan Dr FARIDA ta zauna tana gyara files, cike da hikima da kame kai irin na matan da suka san kansu tace.
"Dr. Imam, kasan ina girmama ka. Kaima ka san yadda rayuwa take… akwai abubuwan da nake kokarin warwarewa kafin in baka damar turo da magabatan ka.
Dan Allah, ka je ka duba patients dinka, kaga Time ya küre,Idan ka gama, sai ka dawo mu karasa maganar."
Cike da so DR. IMAM yake kallonta .
"To, amma sai kin yi alkawarin cewa zaki shigo Office dina kafin na tashi."
murmushi, Dr Farida tay tana gyada kai alamar ta amince da hakan.
"Na amince. In Allah ya yarda."
DR. IMAM ne yace
"Okay, zanyi hakuri Zan jira amincewar ki."
Yana gama fadar haka Ya mike, ya fita ya nufi cardiology Ward in da a chan office din sa yake, Dr Farida ta sauke ajiyar zuciya a hankali, tana kallon kofar da ya fita, tabbas Dr İmam ya chanchanci a so shi, sai dai kuma zuciyar ta ta jima da rufe wannan babin a cikin rayuwar ta.
Cikin zuciyar ta tace.
"Allah Ka bani ikon zaben abun da zai amfaneni a rayuwa..."
Daga nan taba wa patients din ta damar shigowa ta hanyar kada yar kararrawar dake gaban teburin ta .
******
Zaune suke , a Wurin da suka saba haduwa ne, wata Private lounge