Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
ku tsaya a bakin gate yanzu nake fitowa , Ku tsaya a gefe kada mai gadi ya lura da ku." Tana gama fada'r haka Ta kashe wayar, ta ɗauki small purse da wayar ta Ta jefa light jacket a kafadarta, sannan ta fice da sauri cikin natsuwa, kamar babu wani abu dake damun ta. Zuly da saurayinta Al’ameen suna cikin wani sleek black car ,clean tinted Camry, parked a gefe kadan da gate. Zuly na kallon agogon hannun ta tace. "Wannan yarinyar idan bata fito yanzu ba, mai gadi zai iya zargin wani abu." Ramlart ce ta fito tana tafiya a hankali kamar wadda take tsoron wani ya ganta, a hankali Ta kalli gefen dama da hagunta, sai kuma ta sauke numfashi, ta tura gate ɗin a hankali ta buɗe ta fita. Da sauri Zuly ta buɗe mata kofar kafin ta ƙaraso su. Cike da tsokana ZULY tace . " The babbar yarinya Na ce miki yau sai mun bude sabuwar shafi, Ramlart ki saki zuciyar ki ki morewa rayuwar ki!" RAMLART ce ta zauna a baya, tana tafa hannun ta tare da cewa. "Yau raina cike yake da damuwa Let's go burn the night." Al'ameen ne ya ja motar a hankali suka bar harabar gidan. A cikin duhun dare, fitilun club din na haskakawa ta ko'ina da launuka masu rikitarwa, Muryar DJ ne kawai yake tashi yana busa waka mai cike da karfin sauti. ZULY da RAMLART ne su ka shigo cikin mota mai launin baki, Al’ameen saurayin zuly yana driving d'in su . Ramlart ta fito daga mota cikin black doguwar rigar ta mai sheƙi da cut-out, sanye da takalmi mai tsini da jan lalle a hannunta. Idonta na ɗauke da jan eyeshadow, da hancin ta da kunnuwa ta ke dauke da set d'in jewelry na gold ga gashin ta taya sha gyara na “slay queen” salon. Cikin dariya zuly ta ce. "Yau sai kin sha iska, yanzu ne duniya zata ga Ramlart!" Suna dariya suka shiga ciki, club din cike yake da mutane – wasu na rawa, wasu na sha, wasu na zaman romancing din juna. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH💫 ✍️Mrs Alkali Page 1️⃣0️⃣ VIP SECTION – CLUB Ramlart zaune kusa da Al’ameen da Zuly, suna dariya suna shan drink (non-alcoholic mocktail) fiskar su cikin nishaɗi. Ramlart tana tura hotunanta a Snapchat da Instagram story –nata, ta rubuta, “living my best life” caption, d'in ta. ZULY ce ta leƙa wayar Ramlart tace. "Yauwa ta waje na sai dake haka nake so, kiyi komai ba komai , wlh, a duniya muke ,aljannah ta mai rabo ce." Cike da Nishad'i RAMLART tace . "Zan koya masa rayuwa! Naga yanzu shi da soyayyarsa suna son su dawo mini jidali, ya kamata ace kowa ya ji da kansa, wannan lokaci nane." Takara sa maganar tare da juya wayarta, tana kallon hoton AA Turaki a profile picture dinsa, ta ɗan langwabar da kai tace. "In har ni Ramlart ce, sai na mallake zuciyar ka, babu wata ya' mace da zan bawa damar mallakar zuciyar ka, i promise u that, ta ƙarasa maganar tare da juya manyan idanun ta." Muryar DJ ya ne ya ɗaga wajen da sauti, nan take suka sake shiga cikin nishaɗi. Sannan Ramlart ta miƙe da ƙarfi ta fara rawa a dance floor, tana janyo hankulan mutane, zuwa kanta. Zuly ce tayi dariya tare da kallon al'ameen dake manne a jikin ta, cikin narke wa tace masa baby. "Yau dole club ɗin nan ya ƙonu da sunan mu!" Sabida babbar yarinya ta baiyana, murmurmushi al'ameen yamata tare da ci gaba da shafa jikin ta. Hasken disco lights na ta yawo, music mai ratsa jiki yana tashi. Dancers sun cika dance floor, ana rawa da annashuwa. Ramlart na tsakiya cikin masu rawa, tana juya jiki da salon rawa mai jawo hankalin mai kallon ta, Hannunta a sama, idonta a rufe, tana jin music din har cikin zuciyar ta. Wani gaye, kyakyawa, cikin kaya masu tsada yana zaune a VIP table yana shan drink. Daga can yana hango Ramlart, a hankali ya tsaya kallon ta yana murmushi, a lokaci guda yana kai drink bakin sa yace. “Wannan cikar ba zata kubuta ba a daren nan dole ne na kasan ce yare da ita.” Cike da boomcing Ya mike ya nufo dance floor kai tsaye, yana tafiya yana bubbudawa, kamar wani sarki, sai Da ya ƙarasa kusa da Ramlart sai ya ɗan tabo hannunta a hankali Ramlart ta buɗe ido ta kalle shi, sai ya ɗan yi mata murmurmushi tare da rage sautin Muryar shi kamar mai rada yace. “Ni da ke sai mun karya wannan dance floor tare in ba damuwa ina son muyi dancing tare.” Ramlart ta yi murmushi, sai ta bashi hannun ta, Suka fara rawa tare, jikin ta a jikin sa. Music yana ta Kara karfin sauti, A hankali sai ya sanya bakin sa a kunnenta yana cewa. “Na shirya baki daren da bazaki taba mantawa da shi ba in kin shirya let's go…” A haka ya rika janta zuwa VIP section, inda aka kawata shi da curtains masu haske da d'aukar hankali ,nan fa ya shiga romancing din ta cike da kwarewa, a haka ramlart ta fita daga cikin haiyacin ta, har ya samu nasara ya biya bukatar sa, da ita, Bayan mintuna kadan, ramlart ta fito daga wajen gashinta sun dan bazu, murmushi take cike da gamsuwa. Ramlart tana shirye-shiryen tafiya, tana gyara dan kwalin ta da d'an lullubin veil din ta, Gayen yana tsaye yana kallon ta da murmushi, yana da confidence irin na wanda yasan ta kan bariki, Wurin shiru ne, fitilar lounge din na launin ruwan hoda da blue suna ba da haske na musamman , wanda yake kara musu shauqi. A hankali yake matsowa kusa da ita, yana kallon ta cike da shauki , yace. "Kin cancanci fiye da haka, Ramlart… amma na bar miki wani abu a matsayin tunawa da wannan daren." Ya ciro wata bundle na kudin kasashen waje – euro da dollars – ya saka a hannunta, sannan yace . "Ga wannan… just for your time and your shine." Ramlart ta karba, tana murmushi tana kallon sa da murmushin da ta saba amfani da shi wajen nuna farin ciki da yaudara. Cikin d'an basarwa ramlart tace. "Wannan fa ?." Ya dauko wata karamar card mai sheki, ya mika mata. Akan card din: sunansa, lambar waya, da adireshin email ne. Kallon ramlart yayi yace. "Sunana Majeed Ibrahim Jatau, kuma mahaifina shine Honourable Senator Ibrahim Jatau – sanannen dan siyasa a kasar nan." Ramlart ta zaro ido waje, sai kuma ta saki murmushi cike da farin ciki da burin sabuwar hanyar daukaka da ta zo mata a cikin sauki. Tace. "Oh wow… nice to meet you, Majeed." MAJEED ne ya Dan matso kusa da ita. "Kuma wannan – card ɗin nan – ya bude miki kowanne kofa idan kina bukatar wani abu let me know." Yana gama fada'r haka Ya lumshe ido yana sumbatar goshin kafin yace. "Let’s say this is not goodbye… it’s just the beginning." Ya juya cikin class, na yara marassa jin magana, ya bud'e mota ya shiga. Ramlart ta tsaya tana kallon bayan motar na barin wajen, tana lumshe ido cike da tunani da wani sabon tunani a cikin ranta. Zuly na jiran ta a gefe tana mata dariya. “Na faɗa miki... wannan shine maganin ciwon tunani, amma kinbi zaki kashe kanki a banza akan wani da namiji.” RAMLART ce ta busa iska a bakin ta tare da cewa . “Hmmm, ai yanzu naji sauƙi. Let’s go... kafin wancan mutumin ya tashi ya san bana cikin gidan.” Haka al'ameen ya yi driving d'in su, Suna isa bakin gate na gidan, Ramlart Ta gyara shigar ta, ta feshe jikin ta da turare sannan ta ɗan dafa hannun ta a jikin k'ofar motan. ZULY ce ta sheke da Wani irin dariya tace. “Ki tabbatar baki bar wani alamar da zata nuna cewa kin fita, club.” RAMLART ce ta juyo tana kallon Zuly tace. “Don’t worry. Nasan gidan nan fiye da yadda su ke tunani. Allah ya saka da alheri Zuly.” ZULY ce ta daga gira tana dariya tace. “Alherin club ko? Hahaha... Mun kusa cin nasara, bestie.” Ramlart ta yi sallama da su, ta rufe kofar mota sannan ta ratsa ta bayan wani bangon ginin gidan inda take da wata sirrin hanya ta musamman da take shiga daga baya ba tare da an lura da ita ba, ta yi wuff ta shige ciki, A hankali, ta shiga gidan cikin nutsuwa tana duba gefe da gefen ta domin tabbatar da cewa kowa yana bacci, babu wanda ya ganta. A dai-dai lokacin, ake kiran sallan asuba ya fara tashi daga masallacin anguwa dana cikin gidan AA Turaki, Gidan na cikin shiru, haka Ramlart ta kutsa kanta zuwa part ɗinta tana mai sauke ajiyar zuciya, dayiwa Allah godiya, naganin babu wani mahluqi da ya ganta. Bayan shigan ramlart Cikin dakin ta, ta cire veil da takalman ta high heels dinta sannan ta zauna akan gado tana kallon kyautar kudaden da Majeed ya bata da card ɗinsa. Wani murmushin jin dadi ne ya subuce a saman fiskarta a hankali ta furta. “Senator’s son… hmm. Ramlart, kin soma samun hanyar da zata sa ki mallaki duniya, yadda kike so.” Batare da ta gabatar da sallan asuba ba ta kwanta. Ba da jimawa ba, barci mai nauyi ya dauke ta. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 1️⃣1️⃣ Da gari yawaye, Ramlart na kwance akan gado tana kallon katin da Majeed ya bata. Ta duba sunansa a jikin katin: “Majeed Ibrahim Jatau– Son of Senator Ibrahim jatau, CEO MJ Holdings”. A gefe, an nannade wasu daloli da euros cikin wata leda mai kyau, ta sanya hannu ta d'auke su. Wani irin shewa RAMLART tayi tace. “CEO... kuma ɗan Senator... Hmmm! Wannan kam dama ce da ba zan bari ta wuce ni ba. In na rasa soyayyar ka, tabbas zanso nayi gogayyah da kai a wajen tara dukiya.” Tana gama fada'r haka ta miƙe, ta nufi mirror tana kallon kanta. Tana murmushi da gamsuwa da kyan jikinta, wayar ta ta dauka Ta latsa layin Zuly, cikin magagin bacci zuly ta d'auki wayar. RAMLART ne ta ce da Zuly ... “Zuly... This guy is different. Yana da kudi, yana da matsayi, kuma yasan yadda ake treating mace. Ya bani cash da card... Can you imagine? Card!” Dariya ZULY tayi tace.. “Toh fa! Kin ga kuwa muna kama hanyan, zama billionaires Yanzu sai ki dinga kula sosai, ki ƙara burgeshi – you never know, maybe kin samu sabon rayuwa daga can, kinga kema zaki shiga cikin jerin manyan, matan da za'a dinga gogayyah da su a kasar nan, kinga gara ki tsaya da kafafun ki kema.” RAMLART ce tace “Wallahi! Pha Ni dai yanzu zan dinga zama on standby. Daga Turaki sai Majeed. Duniya daɗi, kinga na jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya.” Tana fad'ar haka Ta kashe wayar tana dariya, sannan ta nannaɗe katin da kudaden, ta saka a cikin drawer dinta na sirri. Ta haye gado tana murmushi cike da farin cikin irin kamun da tayi. GWARİNPA ESTATE Yamma ce sakaliya mai cike da Wani irin iska mai d'auke da sanyi, Dr. Farida ce ta dawo gida cikin gajiya amma fuskarta na dauke da murmushi mai kwantar da zuciyar ,mai kallon ta, Tana daure da hijabi fari mai laushi, ta shiga falon gidan hannun ta na d'auke da jakar ta. DADA ce ta fito daga daki " Lale maraba da likita bokan turai, sannu da zuwa ya masu jinyan." DR. FARIDA ce ta zauna a kusa da ita tace.. "Alhamdulillah Dada, wallahi naji dadin ganin Hajja ta samu sauki. Tayi responding da kyau sosai, kuma cikakken hanzari ne yasa ba ta shiga koma baya ba." Murmurmushi DADA tayi tace.. "Allah yayi miki albarka, Allah ya kara kare ki daga sharrin masu sharri." Ameen dada'amm cewar Dr Farida. Ameer ne ya shigo cikin falon, yana dariya fiskar sa dauke da walwala yace. "Ummi na, please… kice zamu fita yau! Kinga jiya Na gama exams, kuma yau Saturday ne!" DR. FARIDA ce ta kalleshi da gajiya d'auke a saman fiskan ta amma hakan baisa murmushin saman fiskarta bacewa ba. "Ameer ka bari gobe mana… Dada na gaji sosai." AMEER ne ya hada hannuwansa alamar yana roƙon ta yace . "Wallahi na yi alkawari da friend dina Ahmed! Dan Allah Ummi, koda minti talatin ne." DADA ce ta kalli Dr Farida tace. "To ki yi hakuri, ki kaishi mana, Bawan Allah yana jin dadin fita dake sai dai baki da lokacin sa." Dr. Farida ta mike, ta nufi dakin ta domin canza kaya. Bayan lokaci kadan ta fito cikin simple gown mai launin blue sky, hijabi ta d'aura a akai wanda hakan ba karamin fito da ainihin kyanta yayi ba. Murmurmushi DR. FARIDA tayi tace.. "To mu tafi… Amma wallahi minti talatin d'in kawai." Haka sukayi bankwana da Dada sannan suka fita. Ameer ya bude mata motar, suka shiga ,Suka nufi wajen shan ice cream da fiskar su d'auke da dariya Nishad'i suna Dan taba hira tsakanin uwa da ɗa. MAITAMA PARK Ameer na shan ice cream cike da annashuwa yayin da Dr. Farida ke dan shakatawa a gefenta tana kallon sa tana murmushi. wayarta ce ta fara ringing – emergency call daga hospital. DR. FARIDA ta kalli sunan da ke kan screen din, ta d'an daure fuskar ta dan batayi tsammani ba. "Ohh… My God." AMEER ne yace "Who’s calling Ummi?" A hankali DR. FARIDA tace: "Hospital ne, emergency ne. Amma…" Cike da farin cikin jin hakan AMEER yace . "Zamu je?! Zamu je asibitin da kike aiki?! Yessss!" *Ta d'an kalle sa da mamakin yan da taga yana murna, sannan ta girgiza kai da dariya a saman fiskarta tace. "To shikenan. Amma ka yimini alƙawari, bazaka sani headache ba, zaka nitsu bana son fitinah." AMEER ne yace. "Yes ummi nayi Alkawari!" Haka ta shiga Motar ta ta juya da sauri, ta d'auki hanyar da zata kaisu hospital, duk da cewa ba haka Dr. Farida ta tsara ranar ta ba. Amma ya zatayi, haka taci gaba da driving d'in su, shi dai Ameer sai murna yakeyi for the first time da zai je asibitin da ummin sa take aiki , sabi da haka ya kasance cikin farin ciki. Bayan wani lokaci, Dr. Farida ta kammala duba marar lafiyan da da aka kawo a bangaren gaggawa wato emergency Ward. Hannunta dauke da medical file, fuskarta cike da gajiya amma annurin fiskar ta yana nan bai bace ba. Tana tafe a hankali tare da Ameer a gefen ta, wanda ke kallon kowane sashe na asibitin cike da sha'awa. dakin da Hajja ke kwance Suka nufa, bayan an mayar da ita VIP room saboda saukin ciwon da tafara samu. AA Turaki na zaune a gefen gadon, cikin manyan kaya masu tsari, fuskar sa cike da nutsuwa, amma akwai alamun damuwa, a tattare da ita. PA dinsa, tsaye a gefe yana duba wayar sa lokaci-lokaci. A gefen gadon, Hajja na zaune cikin rigar asibiti, tana dan dariya da alama wata maganar ce ta sata dariya d'an hira suke d'an tab'awa ita da d'an nata. gently,sukaji ana buga kofar dakin, a hankali kuma aka turo kofar. DR. FARIDA ce ta shigo cikin murya mai sanyi tace: "Assalamu Alaikum." HAJJA ce ta washe baki , fiskar ta d'auke da farin ciki ganin ta, tace: "Wa alaikumus salam. Masha Allahu! Gata nan! Doctor Farida… laleh maraba da yâr albarka!" Cike da sakin fiska Dr. Farida ta karaso , sannan ta matsa kusa da Hajja tana kallon fuskar ta , cikin sakin fiska tace "Alhamdulillah, naji dadin ganin ki cikin walwala, Hajja. Hakan Yana nuna alamar sauki yafara samuwa, alhmdullah!." HAJJA ce ta kamo hannunta, tace: "Ke kika cancanci godiya. Allah ya saka miki da alkhairi. Nagode kwarai da gaske , Allah yayi albarka." Cike da girmamawa Dr Farida tace. "Ameen Hajja nima nagode da addu'a". AA Turaki ne ya dago kai yana d'an kallon su. Jin yanda Hajja ta sake da wannan likitar saikace sunjima da sanin juna. A dai dai wanna lokacin ne Ameer ya shigo d'akin bakin sa dauke da yar karamar sallama, daman ya dan shiga restroom ne , shiyasa Dr Farida ta fad'a masa numbern dakin da zai same ta in ya fito. Hajja ce ta d'an juyo ta kalleshi, tare da cewa. "Shi kuma wanene wannan yaron wa yake nema a nan?" Dr. Farida ce ta kalli Ameer, ta dan sosa gefen kanta tace. "Danane… Sunansa Ameer." Hajja ce ta washe baki tare da sake kallon Ameer tana murmushi tace. "Ay mashaa Allah. Yaron ki ne, Abu yayi kyau, Kai yaro, zo nan."ta karasa maganar tare da yafito Ameer da hannun ta da baya d'auke da drip. Cike da ladabi Ameer ya karaso , ya gaishe da ita. Hajja ta amsa cike da fara'a a saman fiskar ta tace . "Allah ya raya shi ya sa ya zama abin alfahari kamar mahaifiyarsa." Murmurmushi Dr. Farida tayi tare da zama a kusa da Hajja, tana kallon result din na'urar dake recording din lafiyarta. A hankali Dr Farida ta Kalli Hajja tace. "Masha Allah, an samu cigaba sosai jiki na ta samun lafiya, may be nan da dan wani lokaci za a iya discharge d'in ki , sai kici gaba da karb'an drugs daga gida". Hajja ce tace "alhmdullah nagode wa Allah, kin ga yanzu ya ke cemin ya kama ta a sallame ni haka , kin san shi yafi son a kula dani a gida, Hajja ta karasa magabar cike da barkwan ci". Jin abun da Hajja ta fada ne yasa Dr Farida ta d'an juya ta kalla direction da Hajja ta nuna mata da yatsa. Wani irin dumm dumm gaban ta ya yanke yafad'i , ganin mutum , a zaune a gefe d'aya, fiskarnan a murtuke ba alamar fara'a kan sa a sunkuye sai danna wayar sa yake hankali konce kamar ma baisan da wanzuwar su a cikin d'akin ba. Sani PA dinsa na tsaye a dan gefe da shi. Ameer ya kalli wajen shima, sake rufe idanun sa yayi ya kara bud'e su, ganin kamar a mafarki ,yau gashi ga role model din sa a go aban sa zahiri muraran ba a cikin TV ba ,kamar yanda ya saba ganin hirarrakin sa a gidajen tv, da sauri ya matso kusa da AA Turaki cikin ladabi, jin dadi yace. "Good morning, sir." Cikin mamaki AA Turaki ya dago kai , yana kallon yaron. Wani kyakkyawan yaro ya gani a tsaye a gaban sa , bai san san da wani murmushi mai nauyi da kwarjini da annuri ya bayyana a saman fuskarsa,ba, cikin nitsuwa da kamewa yace. "Good morning, young man, how are you doing. Cikin murna Ameer yace. "I'm fine sir." "Kullum ina kallonka a TV Sir , yau kuma gashi na gan ka da ido. Kai ne Mr. AA Turaki, ?" Ya karasa maganar cikin sigar shirme irin na yara masu kananun shekaru. Wani irni cute smile ya sake masa.Wannan karon murmushin nasa ya kara bayyana, sosai har Dr. Farida da ke gefe ta kura masa ido ba tare da tasan da hakan ba,tana mamakin yadda fuskar sa ta canza da annuri, a lokaci guda.Ganin haka, sai ta dan janye idonta cikin kunya, ta kawar da kanta gefe. AA TURAKI yana kallon Ameer, yace Mr young man: "To ya sunanka?" Cike da farin ciki AMEER yace sunana. "Ameer." AA TURAKI ne ya dan shafa kan shi kafin yace: "Ameer... Nice name, kana da guts. Me kake so ka zama nan gaba?" Ya jiho masa tambayar a bazata . Wani irin dad'i ne ya ziyarci AMEER jin tambayar da AA Turaki ya ke masa, cike da yaranta yace: "Ni ma ina so in zama business tycoon kamar kai. In yi kasuwanci a duniya, in taimaka wa mutane da yawa." AA Turaki ne ya dago hannun sa ya dafa kafadar Ameer, cikin murmushi wanda ya ke fitowa daga kasar, zuciyar shi. Hajja ce ta kalle su, idonta cike da mamaki d'an nata ganin ya sake da yaron a lokaci guda, ji tayi Ameer ya sake kwanta mata a rai, sai taji ina ma ace Ameer jikanta ne. Tun shekaru 21 da suka wuce baya bata sake ganin murmushin a saman fuskarsa ba sai yau da ya had'u da Ameer.Wannan yarinya... da yaron nan, suna da wani abu mai karfi a tattare da su.” nan taji Dr Farida ta dad'a burgeta. Cikin nitsuwa, AA Turaki ya zaro wallet dinsa ya dauko bandir din kudi da wani card mai design dake d'auke da sunansa na Musamman. Ya mika wa Ameer, tare da ce masa. "Ka rike wannan. Za ka iya tuntubata duk lokacin da kake bukatar shawara. Na yarda kai yaro ne mai cike da buri." Cikin farin ciki Ameer ya karba ,a lokaci guda ya ruga da gudu ya rungume Dr. Farida yana fadin “Thank you, Ummi!” yau kinsa na had'u da roll model d'ina. Hajja ce ta kalli Dr Farida da murmushi, d'auke a saman fiskan ta,cikin tausayi ta ce: "Doctor, dan Allah... wa ya haifi wannan yaro? Ina son in san mahaifinsa." Haka kawai naji kun kwantamin a rai, ina jin Ameer kamar jikana wlh. Dr. Farida ta dan saki numfashi, ta sosa gefen gashinta cikin nutsuwa tace. "Mahaifin sa Ya rasu tun yana karami... A yanzu ni da mahaifiyata muke kula da shi." Hajja ta dafe zuciyarta cike da tausayawa, tace . "Subhanallahi...!Allah ya jikansa. Yaro irin wannan... dole ka yi alfahari da shi." Nasan da mahaifin shi yana raye shima zai yi alfahari da shi. Jin yanda Hajja ta dage tana ta zuba surutu ne yasa ,AA Turaki ya mike tsaye tare da PA dinsa. yana kallon Hajja yace . "Hajja Zan dawo daga baya , ki huta, lafiya." Ya da. matsa kad'an,ya kalli Ameer da murmushi, kad'an sannan ya daga masa hannu, irin bye bye d'in nan sannan yace . "Be good, Ameer. Ka kula da kanka sosai." Dariya AMEER yayi yace "Yes sir!" Bai sake cewa komai ba, daga haka Suka fita tare da PA dinsa, yana tafiya cike da wani nau’in annuri da su kan su bodyguard din sa ba su saba gani a tare da shi ba. 💫 ƘAUNA DA KADDARA💫 ✍️Mrs Alkali Page 1️⃣2️⃣ Zaune yake a cikin babban falon sa, ya lumshe idanun sa yana nazari. Wayarsa na riƙe a hannunsa , tunani yake yi a game da ciwon Hajja , jin wayar sa ta fara ringing ne ya sa shi bud'e kyawawan idanun nashi a hankali ya duba wayar , ganin sani PA ne ke kiran nashi yasa shi yin picking call din cikin girmamawa PA ya gaishe shi,bayan gaisuwar ne ya d'aura da cewa. "Mun samu access din CCTV footage na kitchen din Hajja! Kamar yadda ka bukaci a duba ranar da Hajja ta kwanta ciwo..." A hankali ya sauk'e ajiyar Zuciya, cikin wata irin Murya yace. "Ina bukatar flash drive d'in yanzu". Yana gama fada'r haka ya kashe wayar, ba a fi minti biyu ba sai ga sallaman PA, bayan ya samu izinin shigowa ne , ya mika masa wani flash drive yana fadin: "Yes sir, an aiko mini da shi kai tsaye daga Head of Security. Ba wanda ya san da wannan footage din." Ganin ya karb'a flash d'in ne yasa sani PA yimasa sallama ya wuce. Karb'ar flash d'in yayi tare da saka flash din a laptop din sa, dake ajiye a table din dake gaban sa. A hankali ya latsa play. Kamera ta dauki cikakken lokacin da aka dafa tea na Hajja. Sai gashi a cikin video, ya bayyana mace sanye da veil ,tana had'a tea. Ta zuba wani abu a cikin flask din tea, ta juya ba tare da an hango fuskarta sosai ba. A hankali , ya kame zuciyarsa, ya saki Wani irin huci, baya son hasashen shi ya zama gaskiya, matsa play forward yayi tare da sake zubawa laptop din idanun sa... A lokacin da ta juyo kafin ta fita dağa cikin kitchen din, fuskar ta bayyana kadan , Wani irin bugawa zuciyar sa tayi, tabbas wannan fiskar Ramlart ce, hasashen sa ya zama gaskiya baya bukatan karin bayani. A hankali,ya dağa kansa yana jin jikin sa ya dau sanyi. Zuciyarsa ta na wani irin bugawa da karfi. Idanunsa sun kada, a lokaci guda,hannunsa ya dunk'ule da karfin gaske, yana jin kamar ya fashe da ihu, ko zai ji saukin abunda ya taru masa a cikin Zuciya. Magana yake da zuciyar sa "Ramlart...? Me Hajja ta mata take son hanlakata...? " Ya dafe kansa, dake barazanar fashewa.Duniya ta fara juyawa a idanunsa. Hankalinsa ya tashi. A lokaci guda, ya gane cewa rayuwar, Hajja ya shiga cikin hadari , tabbass in dai har ramlart zata iya aika tawa Hajja haka tabbas mata ba abun yarda bane duba da yanda Hajja take son ta, hasalima ita

Chapter 5 of 7