Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫 (Love and Destiny) Na UMMUH EYSHAL Mrs. Alkali بسم الله الرحمن الرحيم *Da sunan Allah me rahma me jin kae,Godiya ta tabbata ga ubangijin talikae wanda yabani damar fara rubutamuku wannan littafin,Amincin da taslimi sukara tabbata ga annabin mu annabin rahma annabi muhamammad salallahu alaehi wasallam* *Sadaukarwa* Na sadaukar da wannan littafi ga maigidana, masoyi na, ginshikin farin cikina kuma uban Ya'ya na. Nagode da ƙauna, fahimta, da goyon bayan da ka ke bani a kowane mataki na rayuwa. Haka kuma ga yayana kuma ɗan uwana na jini, *Bashir Ahmad Musa*, wanda kalmominsa suka zame mini garkuwa a lokacin da zuciyata ke da rauni. Ku biyun kun taka rawa ta musamman a rayuwata — wannan rubutu sadaukarwa ce gare ku, alkhairin Allah ya kaimuku a duk in da kuke. *Gabatarwa* Rayuwa wani tafarki ne mai cike da sirrika da sauye-sauye da ba kowa ke iya hango su ba. Akwai lokutan da burin zuciya ke bijirewa kaddara, sai dai a ƙarshe, abinda Allah ya rubuta shi ne zai tabbata. Littafin *Ƙauna da Kaddarah* ya ƙunshi labarin wata mace da ta fuskanci ƙalubale daga kuruciya zuwa girma, cikin soyayya da ciwon zuciya, tsanani da juriyar rayuwa. Kaddara ta raba ta da farin ciki, amma soyayya ta nemi hanyarta ta dawo da shi. Wannan littafi ba wai labarin soyayya bane kawai, har ila yau yana ɗauke da darussa na rayuwa, hakuri, yanke shawara, da ƙarfin zuciyar mace da namiji a lokacin da jarrabawa ta same su. Ina fatan wannan littafi zai tabo zuciyar ki/ ka, ya baka nishadi, da kuma zurfin tunani game da yadda kaddara ke tafiyar da rayuwar mutum. GARGADI *Labarin littafin ƘAUNA DA KADDARAH ƙirƙirarran labari ne, idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, arashi ne.* Wannan littafin mallaki na ne Ban lamunci a juya mini littafi, ta kowace irin siga ba, sai da izinina❗ Page 1️⃣ *"National Hospital Abuja, Garki – Area 11, Central Area, Abuja."* Misalin qarfe 12:30am na rana, sautin karar motoci masu sirri ne ya karade harabar asibitin National Hospital Abuja. Wata mota kirar SUV ce mai gilashi mai duhu ta shigo cikin nutsuwa, tana jagorantar tawagar, motocin ,Bayanta kuma motar limousine baƙa, ce ta biyo, tana tafe cikin natsuwa kamar ba tafiya take ba. A karshe, wasu motoci biyu na tsaro (escort vehicles)suka rufo musu baya, kowacce dauke da ma’aikatan tsaro masu rigar fata da tabarau masu duhu sanye akan fiskar su. Ma’aikatan asibitin da marasa lafiya da ke kai kawo a harabar asibitin ne, su ka tsaya suna kallon tawagar motocin ,ba tare da sanin wanene ya iso ba. A lokacin ne wani daga cikin masu tsaron ya fita daga motar gaba, ya duba gefen kofar motar limousine, d'in sannan ya bude cikin ladabi da nitsuwa. Da sauri wani matashi da akallah zai kai shekaru 37yrs ya fito ya tsaya a bakin mota limousine d'in da alama yana jiran fitowan uban gidan nasa ne. Shiru wajen yayi na wasu mintuna a kallah ya kusa 5 minutes . Kafafunsa ya zuro a hankali sanye suke cikin takalma masu sheƙi baƙaƙen designer cover shoes na Louis Vuitton. a hankali ya fito daga cikin motar, kai kace shugaban ƙasa ne. Dogon mutum ne mai surar jarumta, fuskarsa cike da nutsuwa da kamala, yana da dan kauri kad'an amma ba sosai ba, fari ne irin sosai din nan, don har yellow -yellow fatar sa tayi, kana ganin sa kaga farin bafulatanin usuli, kamar zaka taba fatar sa jini ya fita sabi da hasken sa . Sanye yake da bak'in suit na alfarma – custom-tailored Italian design wanda ya zauna a jikinsa luf-luf tamkar an zana shi ne sabi da shi. Shirt dinsa fara ce mai sheƙi, da silin tie mai launin royal blue. Hannunsa ɗaya na daure da wristwatch mai tsada (Rolex), ɗayan kuma yana riƙe da jakar laptop ta fata da sauri PA ya karbi jakan laptop din nasa tare da dan rusuna masa, alamar girmamawa. Fuskar sa a had'e take ba ta da alamar murmushi amma akwai nutsuwa mai cike da kamala da daraja, akanta. idanuwansa kuwa sun nuna gajiya alamar yafito daga doguwar tafiya , Duk da hakan, in ka kalle shi baza ka iya gane hakan kai tseye ba sa bida korjinin sa da girma da izza. Cikin nitsuwa da kasai ta ya fara takunsa na ingarman namiji maiji da lafiya. P.A din sa ne ya take masa baya ,sauran bodyguard din kuma anan aka barsu a kame kamar wasu marassa rai. Kamshin turarensa ya cika iskar da ke zagaya harabar asibitin. İn ka kalli yadda ya ke tafiya cikin nitsuwa da kasaita, zaka dauka ba shi da wata damuwa a tattare da shi. Haka jama'ar dake wajen sai matsawa sukeyi wasu na kus kus din sa, Wannan shi ake kira banza a banza dan kuwa bai san ma da zaman su ba bare yasan sunayi, haka yaci gaba da sa kai cikin asibitin Sani P.A na biye da shi abaya, duk in da ya wuce sai ya barmusu tsarabar kamshin turaren sa mai sanyaya rai. Obstetrics & Gynaecology Department naga an rubutu a saman department din da ya shiga, da alama asibitin ba bakon sa bane Duk da takunsa mai nauyi da izza, akwai gajiya da damuwa a fuskarsa, amma ba kowa ne zai fahimci hakan ba, Likitoci da nurses ne suka shiga matsawa gefe, suna ba da hanya cikin girmamawa suna miko gaisuwar su ,hannun sa kawai yake daga musu alamar yana amsa gaisuwar da suke masa. Da sauri wata Nurse ta shiga gaban su , da alama sun san da zuwan sa, da Sani PA su ka gaisa , haka tayi gaba domin yimusu jagora , shi ko uban gayyan ko a jikin sa bai nuna ma alamar ya san da wanzuwar wata halitta atare da su ba, dama chan tafiyan kurame ake yi a tsakanin sa da Sani PA. Wani dan corridor ta bi da su a saman shi an rubuta VIP Ward , basuyi wani tafiya mai nisa ba , a kofar wani d'aki ta tsaya , asaman d'akin an rubuta Ward B3 Room 2, cike da yauki ta juyo ta kalli Sani PA tace "This is the room Sir". Sani PA ne yace "thank you nurse" Cike da salo na jan hankali tace "ur wlcm sir" Ganin bai sake ce mata komai bane yasa Nurse d'in juyawa a sukwane. D'an matsawa baya kad'an PA yayi ya Dan kame alamar girmamawa. A hankali cike da nitsuwa, kamar wanda akayiwa dole ya saka farin hannun sa ya Murda handle d'in kofar d'akin a hankali ya saka kan sa cikin d'akin bakin sa d'auke da sallama kasa kasa kamar wanda baya son yin maganar. Dakin ya kasance mai kyau da tsafta sosai, an kafe shi da lafiyayyun gadon asibiti na zamani, masu ikon daidaita kwanciya da tashi bisa jin daɗin mara lafiya. Bangon dakin an shafe su da light cream colour, yana ba da nutsuwa da kwanciyar hankali, ga me kallon sa, A gefe guda kuma, akwai window mai feshin gilashi, wacce ke barin hasken rana ya dinga shigowa a hankali. An tanadar da split AC, refrigerator, plasma TV, da kuma kujera mai laushi domin mai jinya da wanda ke kula da ita. A gefen gadonta kuma, akwai small digital monitor wanda ke duba motsin jini da numfashi lokaci-lokaci. Wata mata ce Jikinta na kwance a gadon asibitin, sanye take da riga mai launin fari da alama rigar marassa lafiya ce ta asibitin, fuskar ta kumbure kaɗan, ta rame tayi fayau da ita. Idonta a rufe suke ruf, amma numfashinta na tafiya daidai — alamar cewa jikinta na ƙoƙarin murmurewa, zata iya farkawa ako da yaushe. Anty hauwa ce zaune a gefen gadon, tana riƙe da hannunta, tana shafa fuskarta lokaci-lokaci, tana karanta addu’o’i tana tofa mata, Tunanin irin azabar da yâr uwar ta ta sha yana bayyana a saman fuskarta, amma a lokaci guda, zuciyarta cike da godiya ga Allah cewa ta tsira da rainta. A hankali a ka bud'e kofa , cikin nitsuwa ya shigo, bakin sa d'auke da sallama kasa kasa, Sanye yake da black designer suit, fuskarsa cike da damuwa da gajiya, golding eyes din sa ya zuba mata , Kallon farko da ya yi mata ya ya fahimci cewa bakaramar wahala ta sha ba , ramlart ce yanzu kwance ba hayaniya, ba tsiwa, kamar mai bacci, amma kuma ba barci ba ne mai nutsuwa dagani kasan barcin wahala ne. A hankali Ya matso kusa, ya tsaya, yana kallon ta daga sama har ƙasa. Kamshin turarensa mai tsada ne ya cika ɗakin gaba d'aya. Anty hauwa ta miƙe a hankali, ta d'an basar gaishe sa ta shiga yi, ba yabo ba fallasa haka ya amsa mata, babu wata sakewa a tsakanin su, ganin hakane yasa aunty hauwa ta nufi hanyar fita daga d'akin domin bashi waje ya gana da matar sa, cikin nitsuwa Ya zauna a gefen gadon, ya kama tafin hannunta a hankali, yana shafa shi cikin tausayin ta dana kan sa. Ya lumshe idonsa, ya dafe kansa kaɗan, cikin zuciyar sa yake furta, " “Ya Allah, kai ne Mai kowa da komai... na yarda da ƙaddararKa. Na amince da rabonKa. Amma Ya Allah, sai yaushe? Sai yaushe zan riƙe ɗana a hannuna, in ji kamshin jikinsa, in kalle shi ya kirani ‘abba’? Kullum ina karanta ‘Laqad khalaqnal insana fi ahsani taqwim’... amma me yasa ni kake jarabta na da wannan jinkirin?, ya Allah idan hakan yana da nasaba da kaddarah n da ta fad'amini a shekarun baya , Allah na tuba ya Allah ka yafe mini kurakurai na" Ya runtse idonsa da karfi, yana jin wani irin turirin zafi na fita daga kasan Zuciyar sa, a hankali ya shaki iska mai sanyi, yana jin nauyin hawaye a cikin zuciyarsa amma bai bari suka sauko ba. Zuciyarsa ta ci gaba da kuka cikin tawakkali da nadama, batare da ya bar hakan ya baiyana a saman fiskar sa ba. A hankali idanuwanta suka fara motsi Kamar wacce ta farka daga duhun mafarki, a hankali ta ke bude su ganin bata gani sosai ne ya sa ta d'an lumshe idanun a hankali, ta sake buɗe su a hankali, fitilar dakin ta dinga haskawa a cikin idanun ta, tana dauke mata idanu, don har yanzu dishi dishi take gani. A hankali ta d'ago kanta Tana kallon sama, ba tare da fahimtar inda take ba a farko, zuciyarta na dukan uku uku, sannu a hankali. Ta motsa hannunta kaɗan wan da aka sanya masa drip, sanyi ya ziyarci ilahirin jikinta, gaba d'aya. Sake lumshe idanuwan ta tayi, hancinta na kara shako mata sassanyan kamshin sa da yaza me mata jiki , ako da yaushe takan ji hakan ko da ace kuwa baya kusa da ita ,sake bide idonta tayi, cikin sa'a ya sauka akan fuskar sa dake zaune a gefen gadon, yana dubanta da ido cike da tausayi tare da wani irin yanayi mai wuyar fassarawa, duddah ba sabon abu bane a wajen ta ta saba ganin sa a cikin irin wannan yanayin musamman a duk lokacin da tasamu misscarage, sai dai kuwa a wannan karon yanayin da tagani a tattare da shi ya sha ban ban da sauran lokutan baya. Idanunsu ne suka haɗu, na shi ya cika da Wani irin yanayi mai wuyar fassarawa tare da damuwa, na ta kuma sun cika da tsoro da ruɗani da kuma fargaba a lokaci d'aya ,Bata iya ce masa komai ba, sai ta ɗan yunkura ta ce "Honey... ina ne nake...? Yaushe ka dawo daga london d'in?" Haka ta jerasa masa tagwayen tambayoyi ajere . A hankali ya riƙe hannunta da ya damke shi da sauri, yana girgiza kai, ya ce cikin muryar da ta ke cike da jarumta da murɗewa yace "Lafiya kike ramlart.. kina lafiya yanzu... ki huta, komai zai dawo daidai in sha Allah." Ya kara sa maganar cikin Wani irin classy husky voice dinsa, yan da kasan ba shi yake maganar ba. Sanin da tayi baya son hayaniya ne yasa Zaman kurame suka shiga yi a tsakanin su, kowa da abun da yake sakawa a cikin zuciyar sa. A hankali aka kwankwasa ƙofar d'akin. "Excuse me, sir," wata nurse mai sanye da uniform mai tsafta da badge ta shigo da takarda a hannunta. Ko dago kai da baiyi ba bare asaka ran zai amsa mata, sanin waye ne shidin ya saka ramlart dake konce cewa "Yes, nurse?" ƙarasowa tayi cikin girmamawa, ta fara duba ramlart d'in, tana ya'n rubuce-rubucen ta a takardar chart ɗin jikinta, sai da tagama duka sannan ta juyo da murya mai yauƙi tace: "Sir, I just came to check on madam. Her vitals are stable for now, and she’s responding well to the IV." gyada mata kai yayi, yana fitar da numfashi a hankali. Ganin ya kulata ne yasa Sai ta ƙara langwabe murya tace: "Also, Dr. Farida — the OB-GYN (obstetrics & gynaecology) in charge — asked me to inform you that she would like to see you in her office as soon as you're able. She said it’s important, but no need to panic." Idon sa ya ƙanƙance kaɗan, ya gyada kai a hankali, harta cire ran zai mata magana kamar daga sama taji husky voice dinsa yace "Thank you, nurse. I’ll be there shortly." Da sauri nurse din ta kalle sa sai dai ganin kamar ba shine yayi maganar ba yasa ta kama kanta, duddah yan da take jin muryan yana kara yimata gezo a cikin kwanyar kanta. D'an murmusawa tayi cike da girmamawa, ta juya ta fita cikin yanga da yauki. Kallon ramlart da ke kwance, yayi, a hankali ya miƙe , cikin zuciyar sa yake magana : "In sha Allah, komai zai daidaita..." Ganin kamar bacci ne ya d'auke ta ya sa Ya fice daga ɗakin cikin natsuwa da izzah, a bakin kofar ɗakin ya samu Sani PA a tsaye, sabanin aunty hauwa dake zaune akan d'aya daga cikin kujerun da aka kawata wajen dasu, baice musu uffan ba yanufi hanyar zuwa ofishin Dr. Farida in da yaga nurse din tayi , Sani PA ne ya take masa baya, hannun sa rike da jakar laptop din sa. Aunty hauwa kam tabe baki tayi, tare dacewa "İkon Allah ayi mutum da shigen miskilanci da fad'in rai Allah dai ya yaye maka" Takara sa maganar tare da tura kofar dakin ta shiga ciki. Jin muryan Aunty hauwa ne yasa ramlart ta bud'e idanun ta ,da ma chan bawani bacci da ya kwashe ta , kawai dai tarasa me yake mata dad'i ne jin cewa doctorn tana neman sa, fatan ta dai Allah ya sa kar asirin ta ya tonu. Cikin takun sa na gwarazan maza ya ke bin bayan Nurse din , dake ta yauƙi a gaban sa . Wan da a wajen sa ma bai san tanayi ba dan ko daga kansa ya kalleta baiyi ba ko sau daya, inda kafar sa ta ke taka wa kawai yake kallo. D'an tsayawa tayi tare da pointing wani bakin Office da aka rubutu "Dr. Aishatu Abubakar Modibbo, MBBS, FWACS" *Consultant Obstetrician & Gynecologist* *Specialist in Women’s Health, Pregnancy & Fertility Care* Juyawa nurse din tayi, tanufi reception. Ofishin Dr. Farida, yana cikin sashen OB-GYN, babban ofishi ne mai tsafta da sauƙin kallo. A gefe akwai ɗan teburin karatu, da takardun kiwon lafiya an ɗora su a jere. Zaune take akan kujeran ta na office din Fuskarta a lumshe, tana kallon wani chart na sakamakon gwaji. Tana sanye da jamfa na wani material fari mai ratsin purple d'in flowers a jiki, farar lab coat mai dauke da tambarin sunan ta daga sama wanda aka rubuta Dr.AA modibbo da manyan Baki a jiki, hijabinta neatly tucked, babu rini — alamar mace mai natsuwa da tsoron Allah,duk sun baiyana a gareta akallah zata kai shekara 35yrs , i danun ta sanye suke a cikin farin glashi da alama Medicated ne, kallo daya zakayiwa fuskar ta kasan cewa Allah ya zuba halitta a wajen da alama tana da halittan gashi dan ga alamar shi nan ya nuna a saman goshin ta duddah ta sanya hula da hijab hakan bai hana shi baiyana kan sa ba, tana da cikar gira ,bakake ne irin sosai dinnan, sannan bakin ta yana dauke da pinkish red in color, labbanta suna da d'an kauri kadan, tana da manyan idanuwa masu d'auke da ayes lashis masu dan tsayi, san idanun sun kasan ce lulu ayes ne, duddah a zaune take hakan bai hana baiya nar yanayin halittar jikin ta ba, tana da d'an kiba kad'an amma ba sosai har chan ba, da alama tana da d'an tsayin ta dai dai misali don ba za'a kira ta da gajera ba, fatan jikin ta tsaka takiya ne dan baza'a ce mata fara sol ba sannan kuma baza a kirata da chocolate colour ba, da ganin fatan kasan yana samun kulawa ta musamman hakan ne ma ya sa kalan skin d'in ta ya fita so special dan da wuya kaga mutum mai irin skin d'in ta. Jin an kwankwasa ƙofar ba tare da ta d'ago kanta ba cikin nitsuwa tace "Come in," . Cikin izzah da kasaita wanda suka bi jinin jikin shi batare da shi kan shi yasan da hakan ba ya shigo, sanye da black suit d'in sa mai kyau da ɗan ƙyalli, fuskarsa tamke tamau kamar wanda bai taba dariya ba, dan lumshe idanun sa yayi jin yan da ya shaki daddadan kamshin dake cikin office din, wannan karon ma shi kad'ai ne ya shigo , da alama PA yana jiran sa a waje, Hannunsa yana riƙe da agogon hannu, na Rolex alamar yana cikin sauri ya kosa ya cire kayan. Jin shiru ne ya sa ,Dr. Farida ta tashi daga kujerarta cikin ladabi da nitsuwa ba tare da ta dago ta kalle sa ba tace "Good afternoon, Mr. Turaki," ta ce da muryan ta mai laushi, da sanyi, d'an miƙa hannun ta tayi ta na nuna masa kujerar dake gaban nata, in da ta ke ajiye mutane idan sun zo ganin ta. Tariga da tasan shine mijin matar da akayiwa wankin ciki d'azu bayan tasamu misscarage, d'an Nurse ta kirata daga reception ta sanar da ita iso war sa dan haka bata bukatar bayani. "Good afternoon, Doctor,"ya amsa, cikin Wani kamilalliyar mirya, a lokaci guda kuma yana zama a kan kujeran da ta nuna masa ,cikin kwanciyar hankali. A nitse ta zauna, ta ɗan duba takardan dake gaban ta kafin ta ce: “Mr. Turaki, I’ll go straight to the point. Your wife’s miscarriage… wasn’t spontaneous.” AA Turaki ya ɗaga gira, cike da mamaki da ɗan razana. “I’m listening,” ya ce, yana ƙara maida hankalin sa gare ta . Dr. Farida ta nisa a hankali tace: A“Lab results and examination show clear signs of chemical induction. A drug — most likely misoprostol — was used recently. But that’s not all. The damage done to her uterine lining suggests that… this isn’t the first time.” Kamar ba zai iya magana ba, wani irin zafi da zogi yaji zuciyar sa tana masa,karon farko da ya d'ago kan sa gaba daya ya zuba mata ido, wani irin faduwar gaba ce ta riske shi a lokacin da ya Kalli fiskarta, Wani irin yanayi da ya shiga a da Chan baya ya na sake dawo masa, jin kansa ya sara masa da mugun karfi ne yasa shi rintse idanun sa da mugun karfi, tunowa da yayi a inda yake ya sa shi a ro jarumta ya dake, tare da bud'e idanun sa da suka gama rinewa, daga fari zuwa launin ja, sabi da bakin cikin abun da kunnuwan sa sukeji masa, jikinsa a sanyaye, idanuwansa suna cike da rashin fahimta, cikin kamilar muryan shi yace “Are you saying she intentionally…?” Dr. Farida ta ɗaga hannu cikin kwantar da hankali tace “I’m not accusing her. But medically, what I’m saying is… her womb is no longer as strong as it used to be. If care isn’t taken, she may never conceive again naturally.” Wani irin sanyi da nauyin damuwa ya sauka a zuciyar sa, sunkuyar da kan sa kasa yayi, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, tamkar ana tsaga masa kirji ji yake yi kamar ciwon sa na barazanar tashi . “Why… why would she do that?” Ya furta ƙasa-ƙasa batare da sanin cewa maganar ta fito waje ba. Dr. Farida ne ta ce : “There could be a thousand reasons. Fear. Pressure. Regret. But for now, she needs healing — physically, emotionally, and spiritually. And she needs you more than ever.” Turaki ya dafe kansa, numfashinsa ya yi nauyi. a hankali yace: “So… there’s no hope?” Dr. Farida ta kalli sa kai tsaye: “I didn’t say that. There are assisted options. But it will take time, patience, and strong commitment. From both of you.” Ya lumshe idanu, sannan ya ce: “Thank you, Doctor… for your honesty.” Dr. Farida ta gyada kai tace: “It’s painful, but you deserved to know the truth. I’ll be here to guide you both… medically and emotionally.” Ya miƙe, jiki ba ƙwari, amma yana jin wata irin kauna da rauni da su ka haɗu a zuciyarsa, Allah ya gani yana son ya'ya duddah ba auren soyayyah sukayi da ramlart ba ya so ace ta haifa masa yara, saidai kash wani gurbaceccen tunanin ta ya ja ta aikata aikin da zatayi nadama a karshe, cikin karfin hali Ya fice a hankali, zuciyarsa na neman amsoshi fiye da wan da likita ta bashi. Ganin irin halin da Ogan nashi ya fito ne yasa ka PA take masa baya cikin hanzari, ganin yanda

Chapter 1 of 7