Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
me zai ce ba ya kama hannunsa suka fito daga dakin, suma suna mara musu baya. Idanunsa yayi ja har da hawaye a ciki ga hannunsa dake zubar da jini, ganin zasu fita daga falon ne yasa ya ce.  Where?.  Gurinta. Cewan Juraij yana jan shi. Turjewa yayi yaki tafiya ya ce.  Me zan ce mata?.  Kana son ta.  Tana Makaranta ai.  Muje gidan idan bata nan sai muje school din. Juyawa yayi yaga Momi da su Anas yana cewa.  Bazan iya ba, I can t Momi. Momi ta gyada masa kai ta ce.  Zaka iya, kuje zaka iya. Jan hannunsa Juraij yayi suka nufi get masu aiki na kallon su, ta karamin kofa suka fita, tafiya kadan suka yi suna tsayawa a bakin get din gidan, kwankwasawa Juraij yayi mai gadi ya bude musu, ganin Senate ne ya saka shi cewa.  Alhaji da kansa. Murmushi ya kwakulo ya masa Juraij na tambayan shi.  Bhatool tana nan?.  Eh Yallabai yanzu ta shigo tana masifa. Basu kula shi ba suka nufi cikin falon. *Bhatool* Mai machine yana ajiye ta ta bashi kudinsa ta nufi get, bugawa ta shiga yi tana fadin.  Zaka bude ko sai na balla get din. Da gudu mai gadi ya bud e yana cewa.  Ina band aki ne ayi hakuri Hajiya. Hararan shi tayi tana cewa.  Yanzu zaka matsamin ne ko sai na buge ka?. Da sauri ya matsa mata ta shige tana masifa, a falo ta wurgar da handbag dinta tana kwalawa Yaya Karima kira.  Yaya Karima!!. Yaya Karima tana daki ta kwanta kenan taji kiran, da sauri ta fito tana cewa.  Bhatool lafiya?. Fashewa tayi da kuka tana zama a k asa, da mamaki Yaya Karima ta iso gurin ta tana dafata ta zauna ta ce.  Me ya faru?. Kasa tsayar da kukan nata tayi tana fadin.  Yaya ni na hakura da Makarantan nan. Cike da mamaki ta ce.  Me kuma ya faru? Me aka miki?. Nan ta bata labarin komai bata boye mata ko daya ba, ta karashe tana kuka. Shuru Yaya Karima tayi, gefe guda na zuciyarta na tuna mata da Senate, kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce.  Dago fuskarki ki kalle ni Bhatool. Da idanunta da suka danyi ja ta dago tana kallon ta. Yaya Karima ta ce.  To ke waye kike so?.  Yaya burgeni kawai yake yi.  Waye ne shi din?. Shuru tayi kafin tayi magana suka ji sallaman Juraij da Senate, lokaci daya zuciyarta ya tsinke ta kalli Yaya Karima wacce ke sakin murmushi tana fadin.  Yau Senate ne a gidan. Murmushi ya mata suna k arasowa cikin falon, gaishe da ita suka yi ta amsa tana tambayar su Momi suka ce tana lafiya. Idanunsa na kan Bhatool da taki juyowa dan kukan da tayi ya saka idanunta ja. Yaya Karima ta ce.  Bari na dauko muku ruwa ko. Ta fada tana nufan fridge. Juraij yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa.  Anuty da kin bari daga gida muke fa, dama gurin Bhatool muka zo.  Dum-dum haka taji zuciyarta na bugu, yayin da Senate yayi saurin dafe saitin zuciyarsa yana karanto addu a duba da yanda lokaci daya ya harba masa. Yaya Karima ta ce.  Laifi ta muku ko?. Ta fada tana dariya.  A a mun isa ta mana laifi. Dubanta Yaya Karima tayi tare da cewa.  Bhatool baki ji ance anzo gurin ki ba. Jinjina kai tayi tana cewa.  Naji Yaya. Kafin ta mike ta ce.  Ina zuwa bari na shiga daki na fito. Tayi sauri ta yanda kar a ce ta tsaya. Yaya Karima ta zauna tana duban su ta ce.  Me ya faru?. Kallon Senate Juraij yayi kafin ya ce.  Anuty wannan na rako fa. Ya nuna Senate kafin ya cigaba da cewa.  Wai Bhatool& .. Saurin katsai shi yayi ta hanyar buge k afarsa yana marairaya ido. Tsaki Juraij yayi yana cigaba da cewa.  Wallahi Anuty hauka ya fara yi akan Bhatool. Runtse ido Senate yayi saboda kunyan da yaji lokaci daya ya kama shi, Yaya Karima ta ce.  Ikon Allah, wai Senate har yanzu tsoron ne da kai? Tsoron ma na Bhatool?. Juraij ya ce.  Hmmm!!! Shi ne yau na jawo shi nace yazo ya fada mata ko zamu samu sauki. Yaya Karima ta dubi Senate da kyau ta ce.  To idan kana tsoron ta taya zakuyi zaman aure kenan? Ko ka taba ganin inda miji ke tsoron mata?. Girgiza mata kai yayi, ta cigaba da cewa.  Ka cire tsoro ka ajiye shi a gefe ka tunkare ta da zancen. Gyada mata kai yayi kafin ta mike ta ce.  Bari na kira ta. Ta nufi dakin da Bhatool ke ciki. Da sauri ya dubi Juraij zai yi magana ya ga ya ciro waya yana tashi da alama kiransa aka yi.  Inna illahi!!  Ya furta a zuciyarsa kafin yaji wani bangare na zuciyarsa na ce masa.  Zaka iya, idan baka fada mata ba wani ya rigaka fa kamar yanda wancan ya rigaka Ji yayi wani kishi ya tokare masa makoshi lokacin da yaji ta ce. < Ce masa nayi ina da wanda nakeso>. Ko da Yaya Karima ta shiga dakin ta same ta zaune da waya a hannu tana dannawa, kusa da ita taje ta zauna tana cewa.  Bhatool!!!. Ta kira sunanta. Mayar da hankalinta tayi zuwa gareta baki daya tana amsawa.  Bhatool baki fadamin wanda kikeso ba?.  Yaya burgeni kawai yake yi.  Waye ne shi din?.  Dan Momi ne. Ta fada tana turo baki gaba ta dauke kai.  Ke bana son shirmen kin nan fa, dan Momin bashi da suna ne.  Yaya Karima Senate ne fa. Sakin baki tayi tana kallon ta.  Shi sonta yake, ita kuma burge ta yake, me hakan ke nufi?. Sanin babu mai bata amsa ne ya saka ta dubi Bhatool me kyau ta ce.  Ke ko dai son shi kike?. Da sauri ta juyo tana girgiza kai. Yaya Karima ta yi murmushi tana rike hannunta ta ce.  Bhatool kin san Senate baya surutu, kuma baya kula mata ko?.  Yoo to ni Yaya taya zan sani.  Ungo naki=ؐ ai fada miki nake yanzun ba wai kin sani ba.  To ina ji. Ta ajiye wayanta ta zuba mata ido. Tsaki Yaya Karima tayi tana tashi ta ce.  Ki je falo yana neman ki. Dariya tayi tana cewa.  Allah yasa outing zamu fita ya kashe min zuciya da kudi. Kallon ta Yaya Karima tayi tana tsaki ta fita. Mayafin Abayan jikinta ta yafa ta fito falon. Yana zaune yayi shuru kamar maraya, kamar mutuniyar kwarai ta iso da sallama a bakinta. Amsawa yayi ba tare da ya dago ya ganta ba, a kujeran dake kusa da nashi ta zauna bayan ta gaishe shi ya amsa. Shuru ne ya biyo baya babu wanda yayi magana tsawon mintuna, kafin da kyar ya dago da kai ya kalle ta yana fadin. Legend's pen 08129553971 14- *HASASHEN SOYAYYA*d' =%>y _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen) ' *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)=؋=* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =O=ث* _Page 14_ Da sauri ta d aga kai ta kalle shi, jinjina mata kai yayi yana cigaba da cewa.  Za ki iya aure na?  Uhm& . Uhm& . Ni wai?. Ta nuna kanta tana kallon shi. Gyada mata kai yayi yana mikewa tsaye ya zuba hannunsa a aljuhun wandonsa ya ce.  Kiyi shawara kafin ki yanke amsa, na baki daga yau har zuwa lokacin da kika ji kin amince. Ya ajiye mata kudi da bai san nawa ba ya tafi. Da ido tabi bayansa har ya fita kafin ta kalli kudin, dariya kawai tayi dai-dai lokacin da Yaya Karima ta fito.  Yaya wai fa tambaya na yake zan iya auren shi, can t believe it wai wannan handsome guy din ke cewa zan iya auren shi, to ai ko baya gani ne sai na aure shi balle kuma yana kallo. Ta karashe da wani murna a tattare da ita. Dariya ita ma Yaya Karima tayi tana fadin.  To ke me kika ce masa?.  Yaya me zance masa kuwa, barshi na dan wainasa a tunkunyar masa tukun, na ja masa aji sosai kafin nayi accepting. Murmushi kawai Yaya Karima tayi ta ce.  Kar ajin dai ya tsinke. Tashi tayi ta nufi dakinta bayan ta bawa Yaya Karima kudin ta ce ta ajiye mata. *Senate* Yana fitowa a falon ya sauke wani lafiyayyar ajiyar zuciya yana dafe saitin zuciyarsa, lumshe ido yayi yana jin wani karfin guiwa. Dafa sa da akayi ne ya saka shi bude ido ba shiri yana sauke su akan Juraij, dariya Juraij ya fara masa yana cewa.  Wani irin tsoro ne haka Senate. Hararan shi yayi yana nufan hanyar fita, shi ma ya mara masa baya yana tsokanan sa amma ya mantar dashi har suka shiga gidan su. A falo suka tarar da Momi, Anas da Salman sun zuba tagumi suna jiran me zai je ya dawo. Momi na ganinsa ta mike ta iso gurin shi tana zuba masa ido alamun tanaso taji karin bayani. Dariyan da Juraij ke yi ne ya saka Anas cewa.  Ya kwafsa ko?.  No bai kwafsa ba. Ya fada yana dariya kafin ya ce.  At last ya fada mata yana sonta. Lokaci daya suka saki murmushi, Momi bata san sanda ta rungume shi ba tana cewa.  Babana ya zama jarumi. Murmushi kawai yayi yana fadin.  Momi dama jarumin ne tun a baya, kuma In Sha Allah ta sanadiyarta na canza, na zama jarumi. Sakin shi Momi tayi tana jan kumatunsa ta ce.  Better. Salman yayi murmushi ya ce.  Shikenan ai yanzu sai kar ka kashe kanka ko. Rarumo filon kujera yayi yana wurga masa, da sauri ya matsa yana dariya da fadin.  Senate na Bhatool. Dariyan da ya dade bai yi ba yayi yana shafa sumarsa ya ce.  Fadi da k ara Senate na Bhatool kuma Bhatool na Senate. Dariya falon suka saka kafin aka zauna ana hira ana zolayan shi, har su Salman da Juraij suka tafi *Washe gari* Rawar kai, ya mantar da Bhatool tashin hankalin dake makaranta. Hakan yasa ta shirya tun wajen arfe bakwai, so take taje ta kaiwa awayenta gist Winan. arfe 7:45 a bakin gate Win YSU tayiwa Bhatool, tana tafe tana danna wayarta. So take takira wata cikin awayenta taji ko sun araso cikin school. Horn din taji anayi mata a baya, hakan yasata waigawa a fusace, wa zata gani?. Dr Hashim.  Ya Allahu. ta furta kaman tayi kuka, a hankali ya kawo motar kusa da ita.  Bhatool. Ya maganar mu. Murmushin dole ta jawo tayi sanan tace.  Nayi shawara, zanzo office Winka anjima.  Okay. kawai yace yaja motarsa, da harara tabi motar tasa. Wayarta ce tayi ara alamun kira.  Wai Suhaima ina kikasa wayarki ne.  Ina kan mashin. sai yanzu na sauka, Kinzo school din ne?.  Da banzo ba, zan kiraku?.  Okay gani nn shigowa. Kashe wayar tayi ta nufi wajen da suke zama kafin su shiga hall. A wajen ta tarar da su Janah suna zaune, dan su tsarin su sai sun hadu baki daya zasu shiga class tare, yanzu ma takirasu sabida tayi tunanin ko sun shiga. Sabuda bata ce dasu zata zo ba. arasawa tayi ta zauna, tare da fadin.  Amarya wace zatayi miki make-up?. Da kallo suka bita, su sunanan cikin tashin hankali da fargaba, ita tana nan tana musu zancen make-up.  Kikace bazakiyi make-up?. Wata uwar dariya Bhatool tayi, sanan tace.  Ai yanzu banza ta faWi, arzii yazo, gayu sai yaci uban na daa. Legends pen 08129553971 15- *HASASHEN SOYAYYA*d' =%>y _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen) ' *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)=؋=* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =O=ث* _Page 15_ Da ido suke kallonta, ita kuwa sai zuba take.  Yanzu ba wannan Bhatool da kuka sani bace, anwar Abdul, yanzu yayar Abdul ce. Ko yaya karima ma sama nake da ita.  Bhatool. Bamu labari me ya faru?. Suhaima da bata dade da arasowa ba ta faWa, gyara zama Bhatool tayi sannan ta ce.  Ashe Abba, ba iya Yaran can yabawa amana ta ba?, can you girls remember that cold, giant, handsome and classy guy dake zama inda muke a garden?. aga kai suka yi duka, tare da faWin. Yes!. cike da mamaki.  To shima Abba ya bashi amanata, jiya nan ya ajiyemun kudi. Ban dubasu ba sai yau naga 150k.  150k!. suka fada gaba dayan su cike da mamaki.  Yes, 150K. Bhatool ta maimaita.  Bhatool, kina cikin Alheri dumu-dumu.  Wallahi faa, and guest what? .  What?!. Suka sake fada.  Wai yana sona.  Ayirrrrr, Bhatool tayi goshi. Jannah ta fada kamar tayi rawa.  Amma kema kince kina sonsa ko?. Suhaima ta tambayeta.  Haba mana gurls, atleast ai ya kamata naja Class ko yane.  Eyh.. Amma kija a hankali. Jannah ta fada, sai kuma tace.  Dr Haisam fa?. Dariya Bhatool tayi sannan tace.  Wasa zanyi dashi, zance mai na aminci, amma ya jira mugama 100lvl mushiga 200. Sai ayi engagement da munje 300 sai ayi auren. Nasan shi wanan bazai fi six months ba, za ayi komai a gama.  Har bikin!?. Cewar Suhaima cike da mamaki.  To mai zanjira Allah yakawo mun miji. Dariya sukayi baki daya, daga nan suka shiga class. *Senate* 07:45 yaaraso ofar gidan Yaya Karima, sai dai mai gadi yace mai tun 07 Ta fita. Komawa gida yayi rai babu dadi kwata-kwata. Har yanzu bai samu amsa daga wajenta ba, sannan yanaso yaji jiya akan wa take magana. Domin kasa bacci yayi gaba Waya, da tunanin maganar ya kwana. Bai san yana da kishi har haka ba.  Good morning Momy nah. ya faWa bayan ya shigo falon.  Morning, angon Bhatool. Murmushi yayi sannan yace.  Momi har da ke.  Ni dai yanzu zo ka zauna anan. zuwa yayi ya zauna, Momi ta kalleshi.  Yanzu zuwa yaushe kakeso, a saka bikin nan. Sabida nima na matsu, duk awayena sun fara aurar da yaransu. Har da masu jikoki. Dariya Senate yayi, sannan yace. Momi nima bansani ba.  Zan fara zuwa nayi magana da yayarta, sai asamu iyayenta. *Bhatool*  Haba Abdul, tunda nace kazo ina son ganinka ai kasan ganinka nakesonyi. Nifa yayarka ce. bhatool dake waya ta faWa, shiru tayi Sannan ta ara cewa.  Idan kuWi ne zance sai kazo, ai fada maka zanyi, ni yanzu turumun account number dinka na sama ko 10k ce dan kasan ni yanzu kuWi basu bane matsala ta.  Shikenan sai kazo. daga haka ta kashe wayar ta juyo ta kalli su Suhima tace.  Shi kadai ne Hope dina, sanan bani da wani wanda zai tsayamun daya wuce shi.  Hakane Bhatool, sanan zai baki mafita sosai. Domin tabbas Dr Haisam ba karamin makirin mutum bane.  Nasani wallahi Suhaima, kinaji yadda mukaji  yan accounting dazu suna magana, kamar damu suke.  Wallahi kiga dai yace zaki aureshi, to itama awarsu yace zata aureshi. Mai hakan ke nufi. Jannah kuma ta faWa.  Alllah ya tsare mu baki daya, ni Abdul din ma idan yazo tare zamu tafi.  Gwanda ki bishi Bhatool, wallahi banason ganinki a makarantar nan.  Ke kuma da tsoro kike Jannah. Ba afi minti goma ba Abdul yazo makatantar, kiranta yayi a waya ya sanar da ita yazo.  jirani bakin gate. ta fada tare da kashe wayar.  Ladies yazo, sai munyi waya. . Wait baki amshi cards dinki ba, banjin zan sake shigowa school. Suhaima ta fada tana bude jakarta.  ibi. ta fada tana miamata jakar.  Kala nawa ne. ta tambayeta.  Dinner, kamu, mothers eve. Su kadaine masu card, bridal babu, henna ma babu card.  Okay, kowanne ban biyar, zanbawa senate da abokinsa, nabawa Yaya karima da mijinta sai abdul.  Okay. Suhaima ta fada tana lissafa mata. Ga six nan ma ko zaki kara wani, ku nawa-nawa zan baku. ta tambayesu Jannah. Bhatool dai amsa taita huce, sauri-sauri ta karasa bakim gate. Motar Abdul ta gani da sauri ta nufi motar tare da budewa ta shige a kan idon Senate da zuwansa kenan zai shiga Makarantar. Ji yayi zuciyarsa ta harba da karfi, da sauri ya fara karanto addu a yana Astagfirullah a zuciyarsa, yana gani ta shiga motar tana murmushi, gashi baya ganin ko waye ne dan tinted glass ne. Numfashi ya sauke ganin motar ya bar gurin kafin a fili ya furta.  Bhatool!!. Yana dafe saitin zuciyarsa dake masa zafi. Ta da motan yayi ya bar gurin a 360 ransa a bace, yana isowa get din unguwarsu yaga motar tana fita alamun ya ajiye ta ta shiga gidan Yaya Karima. Har zai tare shi sai kuma ya fasa ya wuce ya nufi get din su, horn ya danna mai gadi ya bud e masa, ya cinna hancin motar ciki yana parking, ya dade a ciki kafin ya furzar da iska yana fitowa ya nufi dakinsa direct. ~~~~~~~~ Ko da Abdul ya ajiye ta a kofar gidan Yaya Karima sai ta ce.  Abdul ga card na event din Suhaima, na Dinner, Kamu, nasan baza kazo Mothers eve ba.  Abun naku har da mu ne?. Ya tambaya yana amsa tare da ajiyewa. Hararansa tayi tana cewa.  Kai ka sani kuma, sannan idan zaka zo Hilis ka shigo da kudi na kari.  Uhm naji fita zan koma kasuwa. Ya fada yana yiwa motar key. Tabe baki tayi ta fita daga motan ta shiga gidan Yaya Karima shi kuma yaja motarsa ya wuce. Da sallama ta shiga falon, Yaya Karima na amsawa dan tun dazu zaman jiranta take ta dawo taji ya suka kare da Lecturer din.  Yaya Karima ya gida?. Bhatool ta fada zata wuce d aki.  Ke, tun dazu fa ke nake jira amma kinzo zaki wuce. Cewan Yaya Karima tana jin kamar ta kai mata duka. Reverse tayi tana cewa.  Sorry Yayata ta kaina, me ya faru? Me kike jira?. Hararanta tayi tare da fadin.  Ya kuka kare da Lecturer din naku?. Dariya tayi tana fadin.  Ohh wai Dr Hashim? Ai wasan buya muka tayi dashi har na fito, nace zan same shi a office anjima shine na kira Abdul nace yazo ya dawo dani. Ajiyar zuciya Yaya Karima ta sauke ta ce.  Alhamdulillah!!! Yanzu ina Abdul din?.  Ya koma kasuwa abin shi.  Baku da kirki dukan ku, tunda yazo har get ina laifin ya shigo mu gaisa yaci abinci. Ta fada ranta a bace. Tabe baki Bhatool tayi ta nufi daki tana cewa.  To ki kirasa ki masa fada mana, amma kin wani sakani a gaba kinamin fada da rungumeman cikin naki& Legends pen 08129553971 '< 16- *HASASHEN SOYAYYA*d' =%>y _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen) ' *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)=؋=* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM =O=ث* _Page 16_ TaSe baki Bhatool tayi ta nufi Waki tana cewa.  To ki kirasa ki masa faWa mana, amma kin wani sakani a gaba kinamin faWa da rungumeman cikin naki. Yaya Karima ta ce.  Allah ya shirye ki idan mai shiriyar ce, amma ke kam Bhatool halinki sai ke, mijinki ya shiga uku. Dariya Bhatool ta mata tana bud e kofar ta lek o ta ce.  Cewa za kiyi Senate ya shiga uku dan shine Nurul Hayat dina, kuma Zauj dina. Ta rufe kofar tana cigaba da dariya. Girgiza kai kawai Yaya Karima tayi sannan ta wuce d akinta. *SENATE POV* Tun da ya shiga d akinsa bai fito ba sai guraren sallan Mangrib, dan sallan Azahar ma a d aki yayi, haka kuma bai kula kowa ba ciki kuma har da Mom, dan yau jinsa yake wani iri duk a burkice. Sauk owa ya fara yi daga upstairs yana jin hayaniya, sake tamke fuska yayi lokacin da ya lura da su Juraij ne da Salman da Anas, sun tusa Mom a gaba suna hira kuma duk akan yanda za ayi bikin Senate din ne. Kallo daya ya musu yana tura baki a ransa ya ce.  Gaibu kenan, ko accepting dina fa bata yi ba amma sun zage sai shirye-shirye suke. Mom ce tayi murmushi tana tasowa tazo gurin shi tana kama shi ta ce.  Son kazo mu zab a wani event da wani event zamu yi.  Mom kuje ku zaSa. Ya faWa yana wucewa ya fita daga parlon. Baki a sake suka bisa da ido kafin Juraij ya ce.  Idan kun ga haka to shi da Bhatool ne.  Kai da kasani kuma, kila ko bata masa magana bane yasa yau ransa duk a bace, kamar wanda aka masa bushara da wutan jahannama. Cewan Anas. Salman yayi murmushi ya ce.  Ku dai gulma ne naku, ai gwara shi ya nemo wacce yakeso duk da tana bashi headache, amma ku fa? Ko ince mu fa? Kamar wanda basu da farin jini ko haske a rayuwar su. Dariya Anas yayi yana cewa.  Cewa zakayi kamar wanda bakin iyaye ya bisu, ni fa tunda nake babu macen da ta taSa cewa tana sona, anya ma ba aljana bace ta aure ni?. Juraij ya daura da cewa.  Ko dai ta aure mu dai, dan nima haka ne lakamtu summa lakamtu. Mom ta zauna tana fadin.  Ku tashi ku tafi masallaci, ku fake da cewa aljana ta aure ku, ku dai kuka auri aljanun tunda kune kuka ki auren. Da haka suka tashi suka tafi masallaci. Ana idar da salla ya fito ya nufi hanyar gidan Yaya Karima, Juraij na cewa ya jira shi amma yayi banza dashi. wanwasawa yayi mai gadi ya buWe, ya tambaye shi.  Bhatool na nan?. Ya ce.  Tana nan, dazu ta dawo daga Makaranta.  Ban tambaye ka ba Malam. Senate ya fad a yana nufan hanyar falon, dan shi fa jinsa yake dai-dai da kowa yanzu, duk haushin biyu ya taru masa ya masa yawa, ya rasa waye ne na Makarantar ga wanda ya kawo ta dazu. A bakin kofar ya tsaya yana sallama. Fitowan ta kenan taji sallaman shi, da mamaki ta ce.  Kamar Senate nake ji. Yaya Karima da itama fitowarta daga kitchen ta ce.  Shi ne ma ba kama ba. Tabe baki tayi tana komawa d aki dan dauko mayafi. Yaya Karima ta amsa masa tana cewa.  Haba Senate gidan ne sai kace bak on ka, ka wani tsaya daga waje. Dan sosa keya yayi kafin ya shigo kansa a k asa, ya durkusa yana cewa.  Ina wuni?.  Lafiya ka tashi ka zauna. Tashi yayi ya zauna yana ta kwakulo murmushin dole, Yaya Karima ta danyi murmushi

Chapter 6 of 8